sani ba?" Yanayin yadda ta yi maganar kamar wata marainiya, sai da ya so karya masa zuciya. Ya girgiza kai sannan ya ce
"Babu wani abu da kika yi mini Janan. Ni ma ina duba miki abin da ya fi dacewa da rayuwarki ne. Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ki ci gaba da addu'a. Duk abin da yake alkairi, Allah Ya kawo miki shi." Lumshe idanunta Janan ta yi cike da sarewa da lamarin nan. Shin ita kam ina za ta saka kanta ta ji sanyi? Yah Farouk ɗin ma da take sakawa rai ga abin da yake faɗa mata? To me ya sa ba za su fahimci ita ba aure take so ba? Ita ba ta son wani aure, tana so ta ci gaba da kasancewa da su a rayuwarta. Me ya sa za su tarwatsa mata farinciki ta hanyar shigo da zancen aure a hanyarta? Ita ba ta so ko kaɗan.
Cikin farar shaddar riga ɗinkin babbar riga ya shirya, ya yi matuƙar kyau, kayan sun matuƙar amsar shi. Sai zuba ƙamshi yake yi, hakazalika fuskarsa cike da annuri. Tsaff ya gama shiryawa, ya ɗauki mukullin motarsa ya fito daga ɗakinsa. Yau ɗin bai san wacce irin rana zai kira ta ba, rana mafi muhimmanci a rayuwarsa ko kuwa mene ne? Domin kuwa tun da Abee ya kira shi a jikinsa yake ji alkairi ke kiran sa. Kuma in Allah Ya yarda addu'arsa ta samun damar mallakar Aysha ce ta karɓu.
Tun kafin ya ƙarasa fitowa cikin parlourn yake hango ta tsaye tana kallon sa. Sai ya sakar mata murmushi sannan ya ƙarasa. Kafin ya kai ga furta komai Nafisa ta ce
"Ina za ka je?" Ta jefa masa tambayar, da yanayin yadda ta yi magana sai ka ɗauka uwarsa ce ke magana. Cike da mamakin yanayin yadda ta yi tambayar ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce
"Ina zan je?"
"Eh haka na ce, ina za ka je? Ko ba za ka faɗa mini ba ne." Ta sake jefa masa tambayar, ita kaɗai ta san yadda take jin zuciyarta na wani irin bugawa, hakazalika zuciyarta a kusa take, tana ji ne kamar kawai ta fashe da kuka ko ta samu sauƙin abin da take ji.
"Inda kika aike ni." Ya jefa mata maganar bayan ya sarƙafe hannayensa a ƙirji yana kallon ta ido cikin ido. Ita abin har mamaki yake ba ta. Adam ɗin da ke shakkar yi mata magana, yau shi ke kallon cikin idanunta yana faɗa mata magana. Lallai dole ba za ta yarda a je wajen Malam don ya yi musu aiki a kan budurwar Adam ɗin ba, tun da ta san ana yin nisa komai zai iya warwarewa. Amincewa da shawarar yayarta ba ƙaramin kyan kai ta yi ba.
"Je ka." Ta faɗa tana yin gefe alamar ta ba shi hanya ya tafi. Mamaki ne ya kama shi, don haka ya buɗe idanunsa ya zube su a kanta cike da mamaki. Da gaske take? Ya tambayi kansa. Jin ba ta sake cewa komai ba ya sanya shi sauke ajiyar zuciya cike da gajiya da halayen Nafisa. Wallahi in dai haka kishi yake, ya gwammace a ce kwata-kwata ma matarsa ba ta kishi a kansa, wannan masifa har ina? A hankali ya soma takawa, sai dai kafin ya yi taku uku, ya jiyo muryar Nafisa ta ce
"Adam." Juyawa ya yi ya kalle ta, kafin ya kai ga amsa kiran, sai ji ya yi ta watsa masa abin da ke cikin plate ɗin da ke hannunta. Wanda shinkafa ce da miyar manja, wadda kayan miya suka yi shane-shane cikin mai.
"Wallahi ba ka isa ba Adam. Duk rawar jikin nan da kake ai na san inda kake ƙoƙarin zuwa. Kana ta washe baki ana ƙoƙarin ba ka auren yarinya, to wallahi mu zuba ni da kai mu gani. Ko da za ka kwana kana saka kaya a cikin gidan nan a yau ɗin nan ni kuma zan ɓata gabaɗaya lokacina wajen ɓata su. Wallahi Adam ba ka isa ba ka yi kaɗan ka ci amanata." Ta faɗa cikin ɗaga murya, hawaye na sauka a kan kuncinta. Kallon jikinsa Adam ya yi cike da mamaki, bai taɓa tunanin haukan Nafisa zai ba ta shawarar aikata haka ba. Yanzu me ta aikata kenan? Tana ganin hakan da ta yi shi ne zai hana shi zuwa wannan kiran da aka yi masa? Kiran da yake tunanin zai zama sanadiyyar shimfiɗa sabuwar rayuwarsa? Ita wannan abun da take yi ma ba ta san sake fice masa a rai take ba? Gabaɗaya sake sire masa take yi ba? Bai ce ko uffan ba, ya zare babbar rigar sannan kai tsaye ya wuce ɗaki.
"Ka je kowanne kaya ne ka saka ina nan mu zuba ni da kai ɗan halak ka fasa. Wallahi sai dai ka haƙura in dai ina cikin gidan nan a raye." Bai ce da ita ko uffan ba, don ya san idan ya ce zai buɗe baki ya yi magana, babu lallai magana mai daɗi ta fito daga bakinsa. Bai kuma san iya inda abun zai tsaya ba. Don haka kai tsaye ɗakinsa ya faɗa. Bayan wajen mintina goma ya fito shirye cikin wata sabuwar shigar da ita ma ta yi masa kyau, amma ba kamar na ɗazu ba da ya riga ya gama tama musu.
"Nafisa! Wallahi idan har kika sake kika yi yunƙurin aikata wani abu a kaina a yanzu haka, to tabbas na rabu da ke har abada." Ya yi maganar fuskarsa a tamke, wadda hakan ke nuna mata da gaske yana nufin abin da ya faɗa. Amma a ajiye yanayin fuskarsa a gefe, shin da gaske yake idan ta yi hakan ya rabu da ita saboda ba shi da man kai? Kamar wata saƙaguwa haka ta bi shi da kallo lokacin da yake ficewa daga ɗakin. Har ta sake yunƙurin yin wani abu, amma sai zuciyarta ta kwaɓe ta da sauri. Idan dai har ba so take ƙarshen zamanta ya zo ba, to ya zama dole ta kama kanta a iya yanzu dai, tun da furucin nasa a kan yanzu ne kawai ya yi.
Sanye cikin ƙananan kaya ya fito daga ɗakinsa cikin shiri hannunsa ɗauke da mukullin motarsa. Da mamaki yake kallon mutumin da yake shigowa cikin gidan. Kafin ya kai ga gama tunanin, wayarsa ta soma ruri. Kallon wayar ya yi, ganin Abee ke kiran nasa ya sanya shi ɗagawa, daga can ɓangaren ya ce
"Farouk, ga baƙo nan na yi, ka shigo da shi parlour." Bai iya amsawa ba, saboda yadda ya ji gabansa ya tsinke ya faɗi, daidai lokacin da ya sauke idanunsa a kan Adam da yake ƙarasowa. Hannu ya miƙa masa fuskarsa ɗauke da murmushi yana faɗin
"Barka da wannan lokacin Yayanmu." Lumshe idanunsa Farouk ya yi yana jin wani irin ɓacin rai na taso masa. Sai dai tuna a inda yake ya sanya shi buɗe su kafin ya miƙa masa hannu a nutse ba tare da ya iya furta komai ba.
"Fatan na same ku lafiya." Adam ya sake faɗa. Sai a lokacin sannan Farouk ya yi ƙarfin halin faɗin
"Alhamdulillah, mu je ko?" Ya yi maganar duka lokaci ɗaya. Babu musu Adam ya bi bayan Farouk da ya yi gaba. Kai tsaye parlourn suka wuce, inda Abee ke zaune yana jiran shigowar su. Ko da ya kai shi ɗakin, akwai inda yake ƙoƙarin zuwa dama. To amma sai ya ji tamkar kar ya fita. Zai so ya ji abin da za su tattauna da Abeen, duk da ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi. To ko ma dai mene ne zai so a yi a gabansa, duk da ba shi da tabbacin ko zuciyarsa za ta iya jurewa. Sai kuma kawai ya kalli Abee ya ce
"Bari na je Abee."
"A'ah, Farouk idan ba sauri kake yi ba ka zauna mana." Shiru ya yi yana nazarin maganar Abeen. Ko da saurin ma yake yi, zai iya ajiyewa ya zauna ya saurari abin da za su tattauna ɗin, ballantana kuma ma ba saurin yake yi ba. Hakan ne ya sanya shi neman waje ya zauna jikinsa a matuƙar sanyaye.
Cike da girmamawa Adam ya gaishe da Abee, Abee ya amsa cikin zuciyarsa yana jin lallai in sha Allah, Ayshar ta yi dacen miji, saboda nutsuwa da hankalin Adam ɗin da ya gani.
"Wato Adam, na san za ka yi mamakin wannan kiran da na yi maka. To idan muka yi duba da dalilin kiran kamar hakan ba abin mamaki ba ne." Daga haka Abee ya ɗan dakata, sai kuma ya ɗora da
"Da gaske kana son Aysha ko? Kuma ka zo ne da niyyar auren ta?" Ya tambaya kai tsaye yana kallon sa. Murmushi Adam ya yi yana sake yin ƙasa da kansa sannan ya ce
"Ƙwarai kuwa Abba, ina son ta sosai. Kuma a shirye nake da na aure ta a duk lokacin da aka ba ni dama. Sai dai abin da ban sanar ba tun a wancan lokacin shi ne ina da aure, sai dai har zuwa wannan lokacin da nake magana, Allah Bai ba mu haihuwa ba." Da sauri Farouk ya ɗaga idanunsa ya zube su a kan Adam ɗin da ke magana. Aure kuma? Idan dai har da gaske su Abee suke za su aurar da Janan ɗin, kenan mai aure za ta aura? Ba batun auren ne ya fi damun sa ba, a'ah, wace ce matarsa? Yaya halayenta suke? Don kuwa idan dai har Adam zai auri Janan to sai sun tabbatar da halayen matar tasa. Sai sun san wace ce ita. A hankali kuma sai ya ji tausayin ƙanwar tasa na kama shi, ita ɗin dududu ma nawa take da za ta je gidan kishiya? Ya lumshe idanunsa yana buɗe su lokaci guda, daidai lokacin da Abee ya ce
"Ikon Allah! Allah Sarki! To amma hakan ba damuwa ba ne, har kullum alkairin Allah shi muke nema. Ina so in sanar da kai cewa, na ba ka sati ɗaya ka turo iyayenka, ka sanar da su idan sun tashi zuwa su taho da sadaki, don kuwa a lokacin nake so a ɗaura auren ka da Aysha, duk wasu shirye-shiryen biki a yi su daga baya. Zan saka a yi mini bincike a kanka, ba kai kaɗai ba har da matarka, da komai da ya kamata na sani kafin na ɗauki 'yata in ɗamka maka. Idan dai har na samu abin da nake buƙata, to kamar yadda na faɗa, cikin sati ɗaya nake so a gama komai."
Gyara zamansa Adam ya yi, cikin wani irin farinciki, ji yake yi kamar irin waɗannan mafarkan da ya saba yi ne yau ɗin ma yake yi. Shin da gaske Janan ɗin ke ƙoƙarin zama mallakinsa nan da sati ɗaya? Gabaɗaya ya kasa magana sai murmushi kawai da yake yi, don ya ma rasa da wanne baki ya kamata ya buɗe ya yi wa Abee godiya, ko ya buɗe ɗin ma yana ganin kalaman bakinsa sun yi kaɗan su isa wajen yin godiya.
A hankali Farouk ya miƙe idanunsa runtse, ya yi ƙoƙarin buɗe su cike da fatan ya iya saita kansa. Wani irin bugawa zuciyarsa take yi, i zuwa yanzu kam yana ji kamar ba zai iya jurewa ba, kamar zuciyarsa ba za ta iya ɗauka ba. Shin babu wanda zai iya fahimtar halin da yake ciki ballantana ya kawo masa ɗauki? Shin ya rufe ido ne, wajen bayyanar da sirrin zuciyarsa, wanda hakan ka iya jawo babbar matsala? Ko kuwa dai ya ci gaba da barin abun a zuciyarsa har zuwa lokacin da za ta iya ɗauka, zuwa lokacin da ta gaji ta ɗauki matakin da ta ga ya dace da ita?
"Farouk.." Abee ya kira sunansa ganin ya miƙe, kuma kwata-kwata ya ma kasa gane yanayin da yake ciki. Sai da ya sake lumshe idanunsa sai ka ce wanda ya sha wani abu, sannan ya yi azamar nemo inda nutsuwarsa take kana ya ɗan wanzar da murmushi a kan fuskarsa, murmushin da da ya san yadda ya yi nasarar bayyanar da damuwar da ke danƙare a cikin zuciyarsa, da bai yi ba.
"Bari na je Abee." Da ƙyar ya iya fizgo hakan ya faɗa yana ƙauracewa kallon da Abee ke yi masa. Bai iya jira Abeen ya ce komai ba ya miƙa wa Adam hannu suka gaisa sannan ya yi wuff ya fice daga ɗakin.
Daga haka sai na ce mu haɗu a last page na Book 1, wanda daga nan ne za mu shiga gundarin labarin, don gabaɗaya nan shimfiɗa ce muke yi, babu abin da aka yi. 🥱🤓
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 29-30
Bin sa da kallo Abee ya yi yana ƙoƙarin nazartar yanayinsa. Sai dai bai ba shi wannan damar ba, don haka Abee ya dawo da dubansa cikin ɗakin, daidai lokacin da Adam yake faɗin
"Na gode sosai Abba, Allah Ya saka da alkairi, Ya ƙara girma. Na gode da wannan karramawar. Kuma in sha Allah nan da sati ɗaya zan turo iyayena. Allah Ya ƙara girma." Shi ne abin da ya iya faɗa kawai. Don yana ganin su ne iya kalaman da zai iya ambata, waɗanda za su nuna irin farincikin da yake ciki. Murmushi kawai Abee ya yi kafin ya ce
"Ameen." Daga haka Adam bai ƙara mintina masu yawa ba, ya yi sallama da Abee ya fice daga gidan, fuskar nan tasa har lokacin ɗauke da annurin da ya kasa ɓoyuwa. Yau ɗin jin sa yake wasai, jin sa yake kamar an yi masa albishir ɗin da ba a taɓa yi masa irin sa ba.
Da ƙyar yau ɗin ta iya zuwa islamiyya saboda yadda take fama da tsananin ciwon kai. Gabaɗaya haushin 'yan gidan nasu take ji, tun da sun kasa saurarar ta, sun kasa fahimtar ta. Don haka tun tana magiyar har ta gaji ta haƙura. Lokacin da aka taso su, ita ɗaya ta taho, don a da tare suke tafiya da Fa'iza, tun kuma da suka rabu ya zamana ita kaɗai take tahowa idan an tashi. Daidai lokacin da take ƙoƙarin shiga gida Zaki da tun ɗazu yake bibiyar ta cikin mota ya ce
"Zahiri ita ce." Ya ƙare maganar yana murmushi. Dariya wanda ke zaune a mazaunin mai zaman banza ya yi kafin ya ce
"Ta haɗu." Wani banzan kallo Zaki ya jefa masa sannan ya ce
"Me kake nufi?" Kafaɗarsa ya ɗaga kana ya ce
"Babu komai, kawai ina taya ka yabon ta ne."
"Ba na buƙata." Ya ƙare maganar yana shafa haɓarsa, idanunsa na sake hango masa surar yarinyar da yake iya hange duk kuwa da tana cikin hijabi. Sun kai wajen minti ɗaya a haka ba tare da Zaki ya ce komai ba, har lokacin tunani kawai yake yi. Kafin zuwa can ya tashi motarsa daidai lokacin da ya soma faɗin
"A daidai wannan lokacin kenan take dawowa daga makaranta. A samu a ɗakko mini ita, na dare ɗaya dai in shana ko da ban kai linta ba, in ɗan rage zafi. Hakan zai saka ta ji tsoron sake marin wani halittar. Musamman ma kuma MuhammadAali." Jinjina kai wanda yake faɗa wa maganar ya yi kafin ya ce
"An gama Zaki." Daga haka babu wanda ya sake cewa uffan Zaki ya ja motar suka bar wajen cike da zumuɗin son kasancewa da yarinyar. Sai dai kafin su yi nisa wayarsa ta soma ruri. Da hannunsa ɗaya ya yi amfani wajen amsawa, ya yin da ya ci gaba da driving. Daga can ɓangaren Alhaji Maude ya ce
"Kana ina ne?"
"Ina kan hanyar aikin da ka saka ni ne."
"Ka zo ina neman ka yanzun nan." Alhaji Maude ya faɗa cikin ba da umarni. Da mamaki Zaki ya sauke wayar ya kalli mai kiran nasa don sake tabbatarwa. Ya ɗauka zai ji ya nuna farinciki ne tun da yana ƙoƙarin aikata abin da ya umarce shi ne. Sai dai kafin ya kai ga cewa komai Alhaji Mauden ya katse kiran tun da ya tabbatar da ya ji abin da ya faɗa. Wannan dalilin ne ya saka shi kai tsaye ya wuce inda ya tabbatar zai same shi. Don da ba ya nan, zai sanar da shi inda zai zo ya same shi.
Yana tsaye sanye cikin manyan kaya kamar koyaushe. Hannayensa duka biyu saƙale a bayansa yana zagaye ɗakin.
"Yallaɓai." Zaki ya faɗa bayan ya shiga. Sai a lokacin sannan Alhaji Maude ya dakata ya kalli Zaki ya ce
"Me kake ƙoƙarin aikatawa?" Ya jefa masa tambayar kai tsaye.
"Abin da ka saka ni. A kan yarinyar da ta mari MuhammadAali."
"Rabu da ita. Manta da lamarinta." Ya faɗa ransa a matuƙar ɓace. Cikin wani sabon mamakin Zaki ya ci gaba da kallon Alhaji Mauden. Kafin ya kai ga cewa komai Alhaji Maude ya ce
"Ina ganin kamar muna yin duk waɗannan abubuwan ne saboda MuhammadAali? Muna yi don ya san har yanzu mu muna tare da shi duk da ya guje mu? Muna yi ne don hakan ya sake dawo da shi cikin mu? Amma ka ga hakan yana tasiri? Anya kuwa hakan yana tasiri?" Ya jefa masa tambayar cikin ɗaga murya. Shiru Zaki ya yi ba tare da ya san me zai ce ba. Shi ya ƙagu ya ji inda yake so ya je, ya kuma ji me yake nufi.
"Lokaci ya yi da za mu haƙura da bin MuhammadAali ta laluma da kuma ta ƙarƙashin ƙasa, tun da na ga duk wani abu da muka yi masa hakan bai dame shi ba. Don haka lokaci ya yi da za mu biyo masa ta fuska da fuska. Muna da ƙarfin ikon da za mu yi masa ko ma mene ne muka ga dama, wanda zai dawo da shi cikin mu. Don haka a bar wannan aikin da na saka ku, ku mayar da hankali a kan duk wani takunsa, da kuma duk wani abu da ke cikin rayuwarsa, sauran ku bar shi a hannuna." Shiru Zaki ya yi bayan gama saurarar abin da Alhaji Mauden ya faɗa. Shi duk wani abu da ya faɗa hakan bai dame shi ba. Sai ma ganin dacewar hakan da ya yi, to amma abu guda ne ya sanya ya ji wani irin ɓacin rai na taso masa. Tun farko me ya Yallaɓan zai lasa masa zuma a baki? Lokacin da ya ga Janan, ai bai ji komai a kanta ba, sai bayan da Alhaji Mauden ya yi musu magana a kanta sannan ya ji wani abu ya ɗarsu a ransa. Yanzu kuma da ya ga halittar yarinyar a fili sosai, sai ya ji gangar jikinsa ta kwaɗaitu da son kasancewa da ita. Ta yaya kuma yanzu za a ce ya watsar da lamarinta? Ai ba ya tunanin hakan mai yiwuwa ne. Shi dai kam a wannan lokaci yanzu ba ya tunanin akwai wanda zai iya hana shi abin da ya yi niyya. Ya ga Janan, kuma ko'ina na jikinsa sun yi kwaɗayin kasancewa da ita, don haka sai ya cika burinsa a kanta. Sai ya yi tarayya da ita ko da na lokaci ɗaya ne, daga nan kamar yadda Yallaɓan ya faɗa sai ya manta da ita.
Sai a lokacin sannan Oga ya yi murmushi jin abin da Alhaji Maude ya faɗa. Shi sai yanzu ya ji daɗi, sai yanzu ne zai saki jiki ya yi wa Alhaji Mauden aiki a kan MuhammadAali, wanda yake fatan zai zama sanadin da zai saka har abada MuhammadAali ba zai ci gaba da aiki tare da su ba. Shi da ma burinsa kenan ya maye wa Alhaji Mauden gurbin MuhammadAali, ya zamana ya zama ɗan gaban goshinsa kamar yadda MuhammadAalin yake. To maganar da ya faɗa yanzu za ta zama tsani wajen cikar burinsa. Zai taimaka wa Alhaji Maude wajen ko ma mene ne yake so a yi masa a kan MuhammadAali, amma fa don cikar burinsa ba wai na Yallaɓan nasu ba.
Tsaki ya ja a karo na barkatai, ya sake duba kan mudubin, idan har bai manta ba, kamar a nan ne ya ajiye takardar da yake nema. To kenan ina ta shiga? Ko kuwa dai ya manta ne ya canja mata waje? Ƙarasawa ya yi ya ci gaba da duba cikin ɗakin, har zuwa lokacin da ya buɗe bedside drawer yana dubawa. A karon farko ya ga hoton da ke a juye, don haka bai damu da ko na mene ne ba, har sai lokacin da garin ɗakko takardar da ke a ƙasa ya saka hoton ya juyo. Kamar da wasa idanunsa suka sauka a kan hoton. Da sauri ya runtse idanunsa ba tsawon sakanni kafin ya buɗe su a kan hoton. Bai taɓa tunanin abin nasa har ya kai haka ba. Bai taɓa tunanin dattin da ya tabbatar ya shiga ƙwaƙwalwasa har ya kai haka ba. Ko da ya buɗe idanun ma ita ɗin dai ya sake gani cikin hoton. Kamar wanda ke ji tsoro, ya sanya hannunsa ya ɗauka yana kafe ta da idanunsa. Abin da bai fahimta ba, da gaske ita ɗin ce cikin hoton? Ko kuwa dai har ta kai ga ta fara yi masa gizo? A hankali ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya ankara ba ya ji an karɓi hoton. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalli Al-ameen da ke tsaye hannunsa ɗauke da hoton da ya karɓa. Bai kai ga cewa komai ba Al-ameen ɗin ya ce
"Sorry, na ajiye shi ne." Ya yi maganar yana shirin barin wajen. Da sauri MuhammadAali ya ce
"Al-ameen."
"Na'am." Ya faɗa yana juyawa ya kalle shi bayan ya dakata. Sai da ya yi amfani wajen nuna hoton da ke hannunsa sannan ya ce
"Wace ce ita?" Ɗan shiru Al-ameen ya yi kafin ya yi wani yaƙe cikin basarwa ya ce
"Oh! Wannan? Kar ka damu da ita, wata yarinya ce." Shi ne abin da ya faɗa don gabaɗaya ya ma rasa ina zai kama. Ganin kallon da Muhammad ɗin ya ci gaba da yi masa ne ya sanya shi saurin dafa kafaɗar Muhammad ya ce
"Ba abin da kake tunani ba ne wallahi. Na faɗa maka wancan karon ma kuskure ne aka samu." Sai ya sauke ajiyar zuciya kawai yana jinjina kai. Daga haka Al-ameen ya jefa hoton cikin aljihunsa kafin ya fice daga ɗakin. Bin sa da kallo Muhammad ya yi yana tuna maganganun da ya faɗa. Ko kusa ko alama bai ji hankalinsa ya kwanta da abin da ya faɗa ba. Abin da bai sani ba, ko don ya kasance cikin kasa manta wadda ke cikin hoton ne, ko kuwa dai ko ba ita ba ce ba, ba zai yarda da abin da Al-ameen ɗin ya faɗa ba. Kamar wanda aka tsikara, ya ɗauki takardar, da yake da ma a shirye yake, sai kawai ya ɗauki mukullin motarsa ya fice daga ɗakin. An yi sa'a lokacin Al-ameen ke ƙoƙarin shiga motarsa bayan ya fito daga sashen Mamansa. Don haka a cikin motar tasa ya jira har sai da ya fitar da motarsa daga cikin gidan kafin ya bi bayansa. Don kuwa haka nan kawai hankalinsa ya kasa kwanciya. Bai yarda da shi ba ko kaɗan, tabbas akwai wani abu da yake ɓoyewa. To amma ko ma mene ne zai gano shi.
Cike da takatsantsan yake ci gaba da bin Al-ameen ɗin, har zuwa lokacin da ya saukar da motarsa zuwa cikin layi. Sai da ya jira ya yi nisa kafin ya bi bayansa. A hankali yake bin sa cike da ƙwarewar da ya san ba zai gan shi ba. Don ya riga ya saba da hakan tun lokacin da ya yi aiki da Alhaji Maude. Yana zaune cikin motar yana jira ya ga abin da zai faru wayarsa ta fara ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma ganin mai kiran nasa ya sanya shi kara wayar a kunnensa.
"Malam wai ba za ka dawo ba ne?" Ya jefa wa Saleem tambayar har lokacin idanunsa a kan motar Al-ameen. Murmushi Saleem ya yi daga can ɓangaren kafin ya ce
"Wallahi Dada ce ta kira ni ba ta da lafiya"
"Shi ne ba ka sanar da ni ba?"
"Idan na sanar da kai, za ka je ka duba ta ne?" Ya jefa masa tambayar kai tsaye. Iska Muhammad ya fesar, don ya fahimci yanayin yadda Saleem ɗin ya yi magana. Sai da ya ɗan yi jimm, kafin ya ce
"Ka yi haƙuri, amma aƙalla zan kira na yi mata ya jiki. Kodayake manta da wannan, in sha Allah zan je na gaishe ta a wannan karon."
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 24