Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sai a lokacin sannan Saleem ya yi murmushi ya ce "Allah Ya yarda." "A miƙa mini gaisuwa zuwa gare ta." Jinjina kai Saleem ya yi kamar yana gaban Muhammad ɗin kafin ya ce "In sha Allah." Ya san tun da Muhammad ɗin ya faɗa zai je ya gaishe da mahaifiyar tasa ne. Duk kuwa da nisan garinsu. Wanda yake sakawa sau da dama yake yi wa Muhammad ɗin uzuri. Kuma idan nisan ne ma kawai da sauƙi. To idan aka je sai an sha uwar tafiya cikin kwazazzabai kafin a kai ga zuwa ƙaramin garin nasu. Suna waya sosai da mahaifiyar Saleem ɗin. Don hatta Baba ya san ta da mahaifinsa, saboda yadda suke yawan kira su yi godiya, saboda ɗawainiyar ɗansu da ake ɗauka duk lokacin da ya sauka a Kano. Sanye take cikin uniform ɗin islamiyya, fitowar ta kenan daga gida, duk da ta makara, amma ba ta da ƙwarin da za ta yi sauri, saboda yadda jikinta ke a matuƙar sanyaye. Tafiya take kamar wadda ba ta da laka, gabaɗaya zuciyarta a cunkushe take. Tun lokacin da aka yanke hukuncin aurar da ita ga Adam ba ta sake yin waya da shi ba. Don ji take har shi ɗin ma haushin sa take ji. Tun da da bai ce yana son ta ba da duk haka ba ta faru ba. Ta gaban motar Al-ameen ta zo ta gifta, ta wuce, ba tare da ta san yadda ya kafe ta da idanunsa ba. Bai daina kallon ta ba, har sai da ta ɓacewa ganin sa. Dawo da kansa baya ya yi ya kwantar a kan kujerar da yake kai fuskarsa ɗauke da murmushi. Girgiza kai ya shiga yi kamar wanda ke tare da wani. Sam wannan ba irin matan da za a ɓata wa rayuwa ba ne. Gabaɗaya nutsuwa da hankali sun gama bayyana a tattare da ita. Don haka duk ƙudurin da ya yi, da kuma alƙawarin da ya ɗaukar wa Yayar Nafisa, na cewar za a ɓa ta wa yarinyar rayuwa, hakan ba zai yiwu ba. Sai yanzu ya gane kuskuren da ya so aikatawa a baya. Abu ɗaya ne yake ganin shi ne ya dace, wanda idan har hakan ta faru, zai zamana babu Adam, babu auren ta. Wanda idan hakan ta faru ya san zai dafe kuɗaɗensa ya koma gefe ya yi shiru. Kamar yadda ta wuce ta gaban motar Al-ameen, haka ta wuce ta gaban motar MuhammadAali. Wanda duk da yadda yake kwaɓar kansa, amma ya kasa har sai da ya bi ta da kallo. Runtse idanunsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa. Shin me yake damun sa ne? Me yake shirin faruwa? Mene ne yake ji dangane da yarinyar? Duk kansa yake yi wa tambayar, duk da ya san babu wanda zai ba shi amsa. Yana tsaye a wajen Al-ameen ya tashi motarsa ya bar layin. Bin sa ya yi da kallo zuciyarsa cike da saƙe-saƙe. Tabbas akwai wani abu da Al-ameen yake ɓoyewa. Tabbas akwai wani abu da yake shirin aikatawa a ɓoye. Akwai wani abu da yake faruwa wanda ba ya so kowa ya sani? To amma mene ne abin da yake ɓoyewa ɗin? Mene ne haɗin sa da yarinyar? Mene ne ya saka ya ajiye hotonta? Hoton nata da ke nuna an ɗauke ta ne ba tare da ta sani ba? Hakan na nufin tabbas akwai wani ɓoyayyen abu da ya kamata ya sani. Iska ya fesar daga bakinsa yana jin yadda kansa ke ɗan sarawa. A hankali ya kai hannunsa kan goshinsa ya shiga shafawa a hankali zuciyarsa cike fall da saƙe-saƙe. Ya kai wajen mintina biyu a wajen, kafin ya tayar da motarsa ya fice daga layin, ya ɗauki hanyar inda zai je. Sai da ya je inda zai je sannan ya yi parking na motarsa. Har ya kai hannunsa da niyyar buɗe ƙofar, idanunsa suka sauka a kan Maimuna, wadda ke ƙoƙarin shiga cikin wani restaurant. Da sauri ya lumshe idanunsa sannan ya buɗe su a kanta. Idan dai har bai manta fuskar ba, tabbas wannan ce Maimuna, matar da Baba ya taɓa aura. Matar da ta yi ƙoƙarin ɓata musu suna. Bai fito ba, har sai da ya bari ta shige ciki sannan da sauri ya buɗe motar ya fice ya bi bayanta. Kamar waɗanda ke ƙoƙarin tashi sama haka suka yi wuff suka fice daga restaurant ɗin ta ƙofar baya. Kai tsaye cikin mota suka faɗa, ya yi azamar tayar da motarsa ya fige ta da wani irin gudu kamar zai tashi sama. Sai da suka yi nisa, sannan Maimuna ta sauke ajiyar zuciya. "Don Allah rage gudun nan." Ko kallon ta wanda ke driving ɗin bai yi ba, har sai da ya sake yin nisa sosai kafin ya sassauta gudun ya jefa mata wani kallo ya ce "Wannan wacce kalar kasada ce? Garin shegen sakacinki ga shi nan kina ƙoƙarin ki ɓata mana aiki. Yanzu da Muhammad ya gan ni tare da ke me zan ce masa? Ta yaya zan kare kaina a wajensa?" Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke sannan ta ce "To yanzu dai tun da bai gan ka ba ai shi kenan ko?" "Ina tambayar ki idan da ya gan ni ne." Ya jefa mata maganar yana bin ta da wani irin kallo, wanda ya sanya ta saurin sake ba shi haƙuri. Sai a lokacin sannan ya ja ƙwafa kafin ya ci gaba da driving ɗinsa. Bayan shuɗewar wajen mintina biyu Maimuna ta ce "Wallahi na gaji da ɓuya ne, na gaji da ɓoyewa. Na yi abu ga shi ya zo ya sha mini kai. Ina tsoron ranar da za a kama ni, wadda na san dole ne na bayyana gaskiyar al'amari. Don Allah ku san yadda za ku yi da ni, don gabaɗaya ba ni da sakewa, ni da garina." Shiru ya yi kamar bai ji abin da take faɗa ba. Don ya gama ƙuluwa da ita. Sai dai tun da dai har MuhammadAalin bai gan shi ba to da sauƙi. Hakan ne ya sanya shi faɗin "Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki. Za a samo miki mafita, wadda za ta saka ki daina ɓuya saboda gudun kar a kama ki. Ki daina damun kanki, ni na miki alƙawarin samar miki mafita." Ya ƙare maganar yana jinjina kansa, don ya tabbatar mata da abin da yake faɗa. Wuff ta yi ta fice daga gidan cike da fatan babu wanda ya gan ta. Tana sanye cikin riga da zani, ta kima uban mayafin Inna da ta gan shi a kusa kafin ta fito. Tafiya ta ci gaba da yi da sauri tana fatan Allah Ya haɗa ta da chemist a nan kusa. Tafiya ta dinga yi, har sai da ta soma gajiya ba ta samu ba. Dakatawa ta yi tana sauke numfashi hannayenta duka biyun a kan guiwarta. Hanya ta ci gaba da hange, ita dai har lokacin ba ta wani hango wani waje da ya yi mata kama da chemist ba. Ta yi tafiya mai tsayi sosai kafin ta kai ga wani ƙaramin waje da ya yi mata kama da inda ake siyar da magani. Kai tsaye ta afka ciki. Ta samu mutane da yawa a ciki, ba ta ce komai ba ta ci gaba da kallon abin da ke faruwa. Har sai da aka ragu sannan ta ƙarasa ta miƙa kuɗin da ta ɗakko a jakar Inna ta ce "A ba ni maganin bacci." Kallon ta wanda ya fi kusa da ita ya yi kafin ya ce "Ina takardar da aka rubuta miki?" Wani irin bugawa ta ji zuciyarta ta yi. Ita ina ta wani san dole sai an rubutawa mutum sannan za a ba shi magani? Ita a ƙauyensu idan ba su da lafiya ba kawai zuwa suke yi su karɓo maganin da suka saba sha su sha ba? "Rubutawa kuma?" Ta jefa masa tambayar tana ƙanƙantar da idanunta. Jinjina mata kansa kawai ya yi yana ci gaba da abin da yake yi. Ta yi shiru tana ji kamar ta fasa ihu saboda takaici. Sai da ta taƙarƙare sannan ta fasa ihu tana faɗin "Don Allah ka taimaka ka ba ni. Wallahi idan na koma gida ban siyo wa Innata ba za ta iya ɓalla ni. Don Allah ka taimaka ka ba ni ba don halina ba." Cike da mamaki duk hankalin mutanen wajen ya dawo kanta. Suka shiga kallon ta ganin yadda take kuka da gaske. "Kin ga, je ki kawo katin sai a ba ki." "Na manta da katin ne fa a gida. Kuma daga nan zuwa gidanmu da nisa wallahi. Kafin na koma ma aiki ne. Ka taimaka wa rayuwata ka ba ni." Ta sake faɗa tana kukan dai. Ta fi mintina biyar a shagon ana ta tataɓurza da ita. Daga ƙarshe dai da suka gaji suka ba ta don su samu sukuni. Sai a lokacin sannan kukan nata ya ɗauke, ta ɗauka tana ajiye kuɗin lokaci guda tana faɗin "Yawwa na gode." Daga haka ta fice daga chemist ɗin. Ɗaya daga cikin masu bayar da maganin ya ce "Daga gani ka san irin 'yan ƙauyen nan ne da ba su ma gama sanin kan gari ba." "Alamu sun nuna haka." Ɗayan ya faɗa yana ci gaba da abin da yake yi. Cikin farinciki take tafiya, ji take kamar ta taka rawa saboda daɗi. Ta tabbatar yau kam burinta zai cika. Da wannan maganin baccin za ta samu cikar burinta, wanda zai zamo sanadiyyar auren ta da Muhammad. Tun kafin ta shiga gidan take hango Baba da ke sakkowa daga motarsa. Sai ta tsaya tana ci gaba da leƙawa cike da fatan ya shige kafin ta kai ga shigowa. Sai dai ta kai wajen mintina biyu har lokacin bai shige ba. Don haka cikin dabara ta shigo gidan, tana takawa cike da takatsantsan don kar ya gan ta. Sai dai kamar daga sama ta tsinto muryar Baban ya ce "Hamida." Sandarewa ta yi kamar irin wadda 'yansanda suka rutsa da bindiga. Ta kwaɓe fuska tana ji kamar ta fasa ihu, lokaci ɗaya kuma tana laluben abin da ya kamata ta faɗa, don tun kafin ya yi magana ta san tambayar da za ta fito daga bakinsa. Kamar kuwa ta sani, sai ji ta yi ya ce "Daga ina kike?" Ya yi maganar bayan ya ƙaraso wajen da take. Da sauri ta ɓoye maganin hannunta tana juyawa har lokacin tana laluben abin da za ta faɗa. "Baba leƙawa waje na yi na ga yanayin unguwarku." Ta yi saurin faɗin hakan tun kafin Baban ya zargi wani abu. "Shi ne kike ta laɓewa haka?" Ya sake jefa mata tambayar. "Eh Baba, na san idan na ce a bar ni na je, babu lallai a nar ni, shi ne na saci jiki na fita." Ta sake faɗar hakan cike da fatan Baban ya yarda. Numfashi Baban ya sauke kafin ya ce "To ya yi. Mu je." Dakatawa ta yi jin abin da ya faɗa. Su je ina? Ta tambayi kanta. Sai da ta ga ya yi gaba, sannan ta tuna ashe fa gidansa ne ko? Sai ta bi bayansa suka shige sashen nasa. Kai tsaye ɗakin Innar ya nufa saboda ta ce tana son ganin sa. A ɗakin ya tarar da Hajiya Zainab (Maman Al-ameen) bayan sun gaisa, sai ya ƙarasa ya nemi waje suka gaisa da Inna. Shiru ya yi, ya yi tunanin ko Hajiya Zainab ɗin za ta tashi ta fita, sai ya ji shiru, bai ga kuma alamar za ta fita ba. Ita dai Hamida da ma a parlour ta dakata, sai ta ga ficewar kowa daga ɗakin sannan za ta je ta yi ajiyarta. "Abbas." Inna ta kira sunan Baba. "Na'am Inna." "Na ji shiru." Ta faɗa tana kallon sa. Ko ba ta yi dogon bayani ba, ya fahimci abin da take nufi. Don haka ya gyara zamansa, kafin ya kai ga cewa komai ta ce "Ko sai na maka ƙarin bayani? To na ji shiru ban ga an fara shirye-shiryen ɗaurin auren Hamida da Muhammad ba." Numfashi Baba ya sauke a hankali kafin ya ce "Inna, ina nan ina ƙoƙari wajen ganin an yi komai ba tare da an tauye wa wani ɓangaren haƙƙi ba. In sha Allah za ki ji ni nan kusa." "Abbas kar dai ka ce mini tantama kake yi a kan wannan abu da na yanke? Yanzu don ba ni na haife ku ba, shi ne kake ganin ban isa na yanke abu a cikin zuri'arka ba?" Ta ƙare maganar a marairaice kamar mai shirin fashewa da kuka. "Inna don Allah ki bari. Idan kina faɗar haka ina jin gabaɗaya babu daɗi. Ki ba ni lokaci Inna don Allah. Idan dai har yaron nan ya amince da auren nan ko a gobe kike buƙata a ɗaura ba zan taɓa musa miki ba" Dagalo Inna ta yi tana kallon Baba. Ai ita gabaɗaya ma sai yanzu ne ta fahimci inda komai ya dosa. Ashe ga inda matsalar take. Cike da mamaki ta ce "Yanzu kai Abbas a matsayinka na mahaifin yaron nan, ba za ka iya yanke hukunci ga rayuwarsa ba? Ba za ka iya ce masa ga abu kana so ya yi ba? Eh lallai da sake." Ta faɗa tana jinjina kanta. Girgiza kansa Baba ya yi kafin ya ce "Sam yadda kika fahimci al-amarin ba haka yake ba Inna. Kawai buƙata nake ki ba ni lokaci in bi komai a sannu, ba sai an tursasa ba. Ba dai kuna zaune cikin gidan nan ba, idan dai har haka ne, in sha Allah za a samu ranar da Muhammad da kansa zai ce yana son Hamida, ya amince da auren ta. Tun da ba daina yi masa maganar auren zan yi ba. Kawai dai abu ɗaya nake so ki yarda da shi Inna, don Allah ki bar shi ya amince. Ba wani lokaci mai tsayi za a ɗauka ba." Shiru Inna ta yi bayan gama sauraron abin da Baban ya faɗa. Lallai ma! Wato so yake kawai dai ya ce auren nan ba zai yiwu ba. Idan ba haka ba, ta yaya ma MuhammadAali zai ce ya amince da auren Hamida? Ta yaya? "Inna, kamar yadda Baban Muhammad ya faɗa ni ma sai na ga kamar hakan shi ya fi dacewa. Kuma kamar ma ita Hamidar sai ta fi daraja a wajen Muhammad ɗin." Hajiya Zainab da ta gama fahimtar duk wani abu da yake faruwa ta faɗa tana kallon Inna. Kamar Innar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta gyara zama ta ce "To shi kenan." Shi ne abin da ta iya furtawa kawai saboda takaici. Haushin kuma Zainab ɗin na saka mata baki a magana na kama ta. Da wannan damar Baba ya yi amfani wajen miƙewa, ya yi sallama da su ya fice daga ɗakin. Dukkansu bin sa suka yi da kallo kowa da abin da yake saƙawa cikin zuciyarsa. Ita dai Hajiya Zainab sam ba ta san abin da ke faruwa cikin gidan ba sai yanzu. Shi ya sa fa ba ta son zaman nan nata a gida ko kaɗan. Shi kuma Abban Al-ameen kodayaushe ya fi so ta zauna a sashenta. Saboda ya san halinta ciki da bai. Akwai ta da son gutsiri tsoma, shi kuma ba ya so a ce komai matarsa tana ciki, musamman a abu mara kyau, shi ya sa yake yawan umartar ta da ta zauna a gida. Yau ma don wajen Inna za ta je ne shi ya sa ya bar ta. Sai ga shi daga zuwanta ta samu jarida. Ashe abin da ke faruwa cikin gidan kenan tana can ta yi ƙwam a ɗaki? Aure tsakanin Muhammad da Hamida? Anya kuwa abu ne mai yiwuwa? Kuma ma me ya sa rana tsaka Innar ta zo da maganar? Shin su bai ci a ce sun yi tunanin wani abu ba, tun da duk ɗin su sun san wace ce Inna? Kai ita dai haka nan kawai ba ta yarda da al'amarin ba, tabbas akwai dai wani abu da Innar ke ɓoyewa wanda su babu lallai sun gane, tun da suna ɗaukar ta ne a matsayin mahaifiya. Idan ba haka ba rana tsaka ta kawo musu batun aure su fara ƙoƙarin amincewa? Ita wallahi fatanta ma ɗaya, Allah Ya sa kar su amince, Allah Ya sa su bijirewa Innar, a nan ne duk wasu halayenta za su fito, za kuma su fahimci dalilinta na son a yi auren. A karo na biyu ta sake kallon Abee da ke ta shirin sa. Har ya gama tsaff sannan ya ƙarasa inda take a zaune ya nemi waje ya zauna. "Ummee." Ya kira sunanta a hankali. Sai da ta sauke numfashi a hankali kafin ta ce "Na'am. Ka shirya?" Sai ya jinjina kai kawai yana ci gaba da lura da yanayinta. "To shi kuma sanyin jikin na mene ne?" Girgiza kanta Ummee ta shiga yi kafin ta ce "Abee ya zama dole jikina ya yi sanyi. Ka fi kowa sanin yadda abubuwa ke tafiya. Ban san a yadda al-amarin zai zo a wannan karon ba." Da ma ya san abin da take tunani kenan, don ya kwantar mata da hankali, sai ya yi murmushi sannan ya ce "Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki. Babu abin da zai biyo baya sai alkairi in sha Allah. Ke dai kawai ki bi ni da addu'a." "In sha Allah." Ummee ta faɗa har lokacin jikin nata a sanyaye. A ɓangaren Janan kuwa kai tsaye ɗakinta ta wuce bayan ta yi sallar isha'i. Sai a lokacin sannan ta tuna da takardar da wani mutumi ya ba ta lokacin da ta dawo daga islamiyya. Gabaɗaya ta manta da ita ma, saboda yadda zuciyarta ke a matuƙar cunkushe, sai dai tun da ta ji an ce daga Adam ne, sai ta ji ta kwaɗaitu da son ganin mene ne a cikinta. Sai dai kafin ta dawo gida har ta manta, saboda yadda zuciyarta ta sake faɗawa cikin sabon tunanin da ya aure ta. Su ma 'yan gidan gabaɗaya sai take ganin sun canja mata, sun daina mata wannan son da suke yi mata fiye da kowa a cikin gidan, tun da ga shi suna ƙoƙarin yi mata abin da ba ta so. Neman waje ta yi ta zauna a kan gadonta bayan ta ɗakko jakar makarantarta da a ciki ne ta ajiye ta. Ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, don duk da ba ta cikin yanayi mai daɗi sai da ta ji farinciki ganin saƙo daga Adam ɗin. A nutse ta buɗe takardar cike da zumuɗin karanta abin da ta ƙunsa. "Amincin Allah Ya tabbata a gare ki Aysha. Na san za ki yi mamakin ganin wannan saƙon daga gare ni. Na san dole ki yi mamakin me ya sa ban zo da kaina ba? Idan wani abu nake so na sanar da ke me ya sa ban tako ƙafata na zo ba? Me ya sa ban kira ki na yi miki magana ta waya ba? Ki yi haƙuri, ban san da wanne ido zan kalle ki ba, ban san da waɗanne kalamai zan yi amfani wajen sanar da ke abin na yanke ba. Aysha ina son ki, ina matuƙar ƙaunar ki fiye da yadda kike tunani. Sai dai auren mu ba zai yiwu ba, ba zan iya auren ki ba, tun bayan da na ji wani ɓoyayyen abu a kanki, wanda ban riga na yanke hukunci ba, sai da na ji tabbaci daga majiya mai ƙarfi. Na yi tunanin in boɗare kawai in aure ki, sai dai na san ko ma mene ne iyayena ba za su taɓa amincewa ba. Ki yi haƙuri Aysha, na so ki, na kuma so auren ki, to ashe ke ɗin ba rabona ba ce. Da wannan nake cewa, ina yi miki fatan alkairi a rayuwarki." Wani irin bugawa zuciyar Janan ke yi tun lokacin da ta fara karanta takardar. Ita gabaɗaya ta kasa gane inda takardar ta dosa. Ta kasa gane me yake nufi da waɗannan kalaman nasa da suka fi mata kama da wata muguwar guduma ce ake buga mata. Abu ɗaya ta fahimta, Adam ma ya rabu da ita kamar yadda Khaleed ya rabu da ita. Shin me idanunta ke nuna mata? Da gaske wannan ɗin rubutun Adam ne? Da gaske Adam ke sanar da ita ya rabu da ita? Da gaske shi ma ya rabu da ita? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ta samu damar ambata a kan laɓɓanta daidai lokacin da wasu uba-uban hawaye suka yi nasarar rufe mata ganin ta. Girgiza kanta ta shiga yi kamar wata zararriya. "A'ah! A'ah!" Abin da take iya furtawa kenan tana ci gaba da girgiza kanta. "Ba Adam ba ne. Wannan ba Adam ɗina ba ne." Shi ne abin da take iya faɗa kawai cikin tsananin tashin hankali. "Janan." Yah Farouk da shigowar sa cikin ɗakin kenan ya ambata yana kallon ƙanwar tasa. Don ya zo ne ya kira ta ta fito su yi hira kafin dawowar mutanen gidan. Saboda Ummee ta fita wajen aikinsu tun ɗazun bayan Abee ya rarrashe ta a kan ta je. Ya yin da Abee ba ya nan. Ba ta ma san ya kira ta ba. Kawai tana tsaye ne jikin gadonta idanunta a kan takardar da ta yi nasarar zamewa daga hannunta. Haka nan kawai ya ji zuciyarsa ta buga, sai ya ƙarasa cikin ɗakin yana ci gaba da kallon ta. A karo na biyu ya ce "Janan." Nan ma dai ba ta amsa ba, har kuma lokacin idanunta na kan takardar. Jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, hakazalika kukan nan har zuwa yanzu ya kasa fitowa saboda tsananin tashin hankali. Zuciyarta kuwa wani mahaukacin bugu kawai take yi, kamar wata zararriya, ta kasa ko da kwaƙwƙwaran motsi ne. Yadda ya ga tana ta kallon ƙasa ne ya sanya shi kallon abin da take kalla. Sai ya ƙarasa da sauri yana saka hannunsa ya ɗauki takardar da ke a baje a ƙasa. Haka nan kawai ya ji yana tsoron karanta abin da ke cikin ta. Haka dai ya ɗame zuciyarsa ya fara karantawa. Tun kafin ya kai ƙarshe ya soma jin bugun zuciyarsa na ƙaruwa, ya kuma fahimci inda rubutun ke ƙoƙarin zuwa. Kamar kuwa ya sani, sai ga shi ya ƙare da irin ƙarewar da takardar da Khaleed ya rubuto mata ta ƙare. Shiru ya yi na tsawon lokaci ba tare da ya ce komai ba. Shi kaɗai ya san irin ɓacin ran da yake ji, shi kaɗai ya san irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki. Shin me ya sa maza suke haka ne? Me ya sa maza ke amfani da damar da Allah Ya ba su wajen yaudarar matan da suka gama mallaka musu yarda? Wacce irin yarda ce Janan ba ta ba wa Adam ba? Shi dai ga shi ya karanta wasiƙar, ya ji kuma ya faɗi dalilinsa na rabuwa da Janan ɗin, to amma kwata-kwata bai fahimci inda yake ƙoƙarin zuwa ba, ko kusa ko alama bai gane abin da yake nufi ba. Me ya ji a kan Janan ɗin? Wanda har ya saka iyayensa ba za su amince ya aure ta ba? Mene ne kuma ya ji daga majiya mai tushe? Shi gabaɗaya ya kasa ganewa. Abu ɗaya zuciyarsa ta fi riƙewa, shi ne Adam ya yaudari ƙanwar tasa. Wato dai an yaudare ta a karo na biyu. Kamar wanda ya tuna wani abu, sai ya ajiye takardar, sannan ya fito da wayarsa ya yi danne-danne na wasu sakanni kafin ya danna kiran number ɗin Adam, ya saka ta a handsfree sannan ya yi shiru yana saurarar yadda ringing ɗin ke bugawa da bugun zuciyarsa. Ringing 1_2 Adam ya ɗaga. Amsa sallamar da ya yi masa ya yi a gaggauce kafin ya ce "Kai ne ka turo da takarda zuwa ga Aysha?" Ya tambaya kai tsaye, cike da fatan Adam ɗin ya ƙaryata hakan. Sai dai ga ɗimbin mamakinsa, sai ji ya yi ya ce "Eh ni ne." Runtse idanunsa Farouk ya yi, lokaci guda yana datse kiran. Daidai wannan lokacin da kukan da ya riga ya gama haɗa kansa ya ƙwace mata. A hankali Farouk ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani irin ɓacin rai na sake turniƙe shi. Shin me ya sa Adam ɗin zai yi haka? Me ya sa zai fake da wani banzan uzurinza da ya san zato ne kawai ya ce ya fasa auren ƙanwar tasa? Yarinyar da

Chapter 23 of 24