ce komai ba. Sai ya nemi waje ya zauna, ya ce
"Zo nan autar Daddy." Ya yi maganar yana nuna ƙasan inda yake zaune. Babu musu ta tashi ta koma inda ya nuna mata ɗin.
"Kina ji na? Wani abu nake so da ke."
"Tam Daddy." Ta ba shi amsar, sai ya ci gaba da faɗin
"Yanzun nan yayanki Muhammad ya shigo da abokinsa Saleem gidan nan, ki tashi ki samar musu coffee ki kai musu na san za su ji daɗi. Ko babu komai za a faranta wa Saleem ɗin rai a matsayinsa na baƙonmu ko?" Ya ƙarasa maganar da sigar tambaya. Ita kam yau ta ga ta kanta a wajen Daddy. Yau ma dai sake tura ta zai yi wajen Muhammad ɗin, salon ya sake dizga ta kamar ranar nan? To amma kuma ta san halin Daddyn nata, tun da har ya yi mata magana cikin laluma gwara tun wuri ta kama kanta ta aikata abin da ya umarce ta. Don haka jiki a matuƙar sanyaye ta miƙe ta wuce kitchen.
"Yawwah Ammeeyna." Ya faɗa lokacin da take dab da shiga kitchen ɗin.
Bayan shuɗewar wasu mintina, yana nan zaune ta fito daga kitchen ɗin. Zuwa lokacin ta saki mayafin ta yafa shi.
"To Allah Ya ba da sa'a." In ji Daddy ƙasa-ƙasa. Ita ba ma ta san me ya ce ba, ta fice daga ɗakin. Kai tsaye sashensu Muhammad ɗin ta wuce.
"Bari na samu na watsa ruwa." Saleem ya faɗa ba don yana buƙatar jin amsa daga bakin Muhammad ɗin ba, lokaci guda kuma yana shige wa cikin bedroom ɗin. Bai ce da shi komai ba ya ci gaba da danna wayarsa. Daidai lokacin da Ammeey ta shigo hannunta ɗauke da coffee ɗin da sallama ɗauke a bakinta. Da matuƙar mamaki Muhammad ya ɗaga idanunsa ya kalle ta lokacin da take kallon gefe tana jiran ba ta umarnin shigowa.
"Ke!" Ya faɗa yana kallon ta cike da mamaki. Wai yaushe yarinyar ta zama haka ne? Waye yake saka ta kawo musu abinci bayan ba haka ne yake faruwa cikin gidan ba? Su da kansu suke zuwa su ɗauko su kawo sashensu, sai dai idan wani lokacin ba su karɓa da wuri ba ta kawo musu. To amma ya ga yanzu kamar abin daban ne, don yanzu dai kam ba lokacin cin abinci ba ne. Kuma duk wasu alamomi sun nuna ba abinci ne ta kawo ba, saboda iya cups da yake iya hangowa. Kamar ta san me yake raya wa cikin zuciyarsa ta ce
"To Daddy ne ya ce in kawo muku."
"Daddy!" Ya faɗa a kan laɓbansa. 'Me ya sa Daddyn ya damu yake kula wa da shi a kwana biyun?' Tambayar da ta fara zuwa kwanyarsa kenan. 'Anya kuwa?' Ya raya hakan cikin zuciyarsa. Yana da wani hali, gaskiya bai cika saurin yarda da mutane ba. Halinsa ne rashin sakin jiki da mutum gabaɗaya ko da kuwa sun daɗe. Shi ya sa ko yaya mutum ya tsiro da wasu sabbin halayen da ba na shi ba, to sai ya fara bincikar hakan, da kuma gano dalilin hakan kafin ya saki jikinsa. Daddy ƙanin Baba ne, to amma halayensu sun sha bamban da na Baban, har ma da na Abba. A nutse ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce
"Zo ki ajiye ki je.. Ba ki ga an yi baƙo ba? Kar in sake ganin ki a nan." Ya yi maganar kamar ba ya so a ji abin da yake faɗa. Da ma ita ma so take ta ajiye ta fice, don haka tun kafin ya dire maganar ta ƙaraso ta ajiye sannan ta miƙe.
"Islamiyya fa?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ta tsammata ba.
"Ai yau Alhamis." Ta ba shi amsar kai tsaye, lokaci guda tana miƙewa. Ta wani murguɗa bakinta cikin zuciyarta tana raya ko ina ruwansa da islamiyyarta? Wani feleƙe a wajensa da ba ta so shi ne ya yi mata maganar islamiyya, ko ya yi mata magana a kan sallah ko karatu. Ta ga dai shi ɗin ma ba wani addini gare shi ba, daɗewar ma da su Baba ke yi a masallaci shi duk ba ya yi. Wasu sallolin ma sau nawa tana ganin sa yana yin su a gida ba a masallaci ba. Karatun ma kansa ita ba ta ganin sa yana yi, kuma sai ya zo ya yi ta takura wa mutane, bayan kuma shi ya kamata a takurawa. Jin tunanin da take yi kamar a kan bakinta take faɗa ya sanya ta saurin kama bakinta ta yi gaba, tana tunanin idan ya ji ya za su ƙare?
"Ke.." Ta jiyo muryar Yah Al-ameen. Ta tsorata da gaske, don ta ɗauka ko Muhammad ɗin ne ya biyo ta.
"Yah Al-ameen ina wuni?" Ta faɗa bayan ta ɗan tura baki saboda yadda ta ji haushin tsorata tan da ya yi.
"Lafiya ƙalau, Muhammad na ciki?" Ya tambaye ta don ya san daga can ta fito. Sai ta jinjina kai kawai, daidai lokacin da Al-ameen ɗin ya yi gaba shi ma ba tare da ya sake cewa komai ba. Ta taɓe baki tana wucewa a zuciyarta tana ta mita ita ɗaya.
Yana zaune a kan wata kujera, sanye cikin ƙananan kaya da suka matuƙar amsar jikinsa. Hannunsa ɗauke da lemo wanda lokaci zuwa lokaci yake sipping. A nutse ya juya hannunsa ya dubi agogon da ke a ɗaure. Daidai lokacin da sallamar Khaleed ɗin ta ziyarci kunnuwansa.
"Wa alaika salam." Ya amsa sallamar tasa yana ɗaga idanunsa ya kalle shi, cikin ƙanƙanin lokaci yana iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya nazarce shi.
"Barka da wannan lokacin Yah Farouk." Ya faɗa kamar yadda ya ji Janan ɗin na kiran sa da hakan.
"Barka dai.. Ka zauna." Yah Farouk ya faɗa yana nuna masa wajen zama. Babu musu ya ja kujerar ya zauna lokaci guda yana furta
"Ina godiya." Jinjina kansa kawai Farouk ya yi ba tare da ya ce komai ba. Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintina har biyu, a nutse Farouk ya ɗan ciji leɓensa na ƙasa sannan ya ce
"Ba wani dalili ne ya sa na ce ka zo ina son ganin ka ba, sai don so nake na ga wanda ƙanwata take tare da shi har take matuƙar so. Sai dai kuma idan babu damuwa ina da wata tambaya a gare ka."
"To ina jin ka." Khaleed ya faɗa bayan ya gyara zama yana ɗan murmushi.
"Me ya sa ka zaɓi haɗuwa da Aysha a wani wajen daban maimakon gidansu? Ina nufin me ya sa kai tsaye ba ka zo gida ba?"
"Yah Farouk na ga ba ta so na zo gidan ne, ni kuma ba na son ɓacin rai ranta, shi ya sa ban zo ba."
"Ba wannan ba, ina magana ne a kan tun da ka fara ganin ta. Me ya sa kai tsaye ba ka zo gida ka nemi izini ba ka fara yin magana da ita a waje?" Numfashi Khaleed ya sauke kafin ya ce
"Na yi laifi tabbas, amma a yi mini afuwa. Soyayyar Aysha ce ta saka na kasa yin wannan tunanin tun farko. Na yi laifi tabbas." Shiru ne ya sake wanzuwa a wajen na tsawon lokaci, har sai da Khaleed ya sake faɗin
"A yi haƙuri." Sannan Farouk ya ce
"Shi kenan.. Idan har da gaske kana son Aysha, na ba ka sati ɗaya ka turo iyayenka a zo a yi magana. Kar ka damu da abubuwan da ta faɗa maka, ajiye su a gefe, ni nan zan shige maka gaba, tun da har kuna son junanku."
"To in sha Allah. Na gode sosai Allah Ya saka da alkairi. In sha Allah iyayena kuwa za su zo in sha Allah." Khaleed ya faɗa. Ko minti ɗaya Farouk bai ƙara ba ya miƙe, ya miƙa wa Khaleed hannu suka gaisa sannan ya wuce hannunsa guda ɗaya ɗore a kan sumar kansa ya wuce inda ya ajiye motarsa. Khaleed ya bi shi da kallo har ya ɓace wa ganin sa sannan ya miƙe shi ma ya kama hanya.
A yi maneji da wannan, in sha Allah gobe za mu haɗe.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 10
Tsaf ta gama shiryawa cikin uniform ɗinta ta sauko ƙasa inda 'yan gidan ke jiran ta su karya. Ta mugun jin daɗin ganin Yah Farouk, don haka da sauri ta ƙarasa ta ja kujerar kusa da shi ta zauna.
"Barka da safiya Yah Farouk." Ta faɗa cike da fata iri-iri a cikin zuciyarta. Sai da ya ɗan kalle ta kafin ya mayar da kansa kan wayar da yake dannawa ya ce
"Barka dai Aysha."
Har suka gama karyawar Yah Farouk bai ce da ita komai ba. Zuwa can ya ja kujerar da yake kai baya sannan ya ce
"Ummee, Abee.. Bari na je.. akwai inda nake son zuwa."
"To Allah Ya tsare." Suka kusan haɗa baki wajen faɗin hakan. Bin sa da kallo Janan ta yi, wasu hawaye na taruwa a cikin idanunta. Ba don da glass a fuskarta ba, da dukkansu sai sun gan shi. Me Yah Farouk ɗin yake nufi da ita? Yau tsawon sati biyu kenan fa tana jira ta ji ya yi mata magana a kan Khaleed amma shiru. Tun tana shiru har sai da ta gaji ta ɗan tuntuɓe shi amma sai ya ce da ita ta bari za su yi magana. Har yanzu jira take yi su yi maganar amma ya ƙi ba ta dama, ya ma ƙi yi mata maganar gabaɗaya. Babban abin da ke damun ta shi ne raba ta da Fa'iza da ya yi. In da tana tare da Fa'iza da tuni ta san halin da Khaleed ɗin ke ciki. Da tuni ta ji muryarsa, kai da tuni ma ta gan shi. To ita kam ya yake so ta yi ne da ranta? Allah kaɗai Ya san irin abin da ke damun ta a cikin zuciyarta, ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta ke ciki na rashin ji daga Khaleed. Duk wani iya ƙoƙarinta take yi don kar iyayen nata su gane ballantana su damu. Sai dai abin ya kusa fin ƙarfinta. Sai dai inda Allah Ya taimake ta, yadda Ummee har ma da Abeen babu mai yini a gida a yanzun. Kowanne ayyuka sun yi masa yawa, wanda ya saka ba sa samun lokacin zama a gida ballantana har su fahimci damuwar da shalelen tasu ke ciki. Sai dai akwai ranar da Ummee ta sake zaunar da ita a kan lallai dole sai ta faɗa mata ko akwai wani abu da ke damun ta. Ta riga ta yi wa Farouk alƙawarin ba za ta sanar wa da kowa maganar Khaleed ba, hakan ne ya sa ta ce mata babu komai, kamar kullum dai ta ɗora da cewar kewar ta ce dai take damun ta.
A hankali ta ɗauki ɗankwalinta ta ƙarasa gaban mudubi ta zauna ta shiga ɗaurawa. A nutse ta sauke idanunta ta cikin mudubin, a kan Janan da ke kwance a kan gadonta kanta ɗore a kan pillow tana kallon Ummeen. Shiru Ummee ta yi tana nazarin yarinyar na tsawon sakanni, kafin zuwa can ta miƙe ta ƙarasa kan gadon.
"Tashi Aysha." Ta faɗa bayan ta nemi waje ta zauna. Da sauri Janan ta kawar da ƙwallar idanunta sannan ta miƙe zaunen kamar yadda Ummee ta buƙata.
"Kar ki sake ki ce mini wai kewa ta ce ta saka kika canja haka. Buɗe baki ki sanar da ni duk wani abu da ke faruwa. Akwai wani abu ne da ya kamata na sani amma ba ki faɗa mini ba? Maza ki sanar da ni Janan." Da sauri Janan ta wanzar da murmushi a kan fuskarta sannan ta ce
"Da gaske Ummee babu abin da ke damu na. Kawai ba na so kullum ki dinga fita kina bari na a gida. Ba na so ko kaɗan Ummee, ina so kodayaushe in dinga kasancewa tare da ke." Ta ƙare maganar kukan da dama take ji kamar ta yi na ƙwace mata. Jan ta jikinta Ummee ta yi tana jin ko kaɗan babu daɗi. Ta san ɗiyar tata ba ta saba ƙarya ba, don haka ɗari bisa ɗari ta yarda da abin da ta faɗa ɗin. Duk da ta ɓangaren Janan ɗin abin da ta faɗa ɗin da gaske ne. Har kuma gobe ta kasa mantawa da abin da ya faru a daren nan. Ga shi kuma ta san aikin Ummeen ba na ƙare ba ne, ballantana ta ce watarana daina zaman Ummee da dare zai ƙare. Ta yarda da Yah Farouk, ta kuma san yana ɗaya daga cikin mutane masu fahimtar ta a kowanne irin hali ne, shi ya sa ta gwammace idan dai har ya ce ta yi abu, ko ta bari to za ta yi ko kuma ta bari ɗin. Don idan dai har ta bi abin da ya faɗa mata ɗin, cikin ikon Allah daga ƙarshe sai dai ta ji daɗi.
"Ki yi haƙuri Baby girl. Kin san yanayin aikinmu, babu yadda zan yi ne idan ba haka ba ni ma ba a son raina nake barin ki ke ɗaya cikin gidan nan ba, bayan dukka 'yan gidan ficewa za su yi su tafi aiki. Ba a son raina ba ne Aysha, amma ki kwantar da hankalinki, in sha Allah komai zai zo ƙarshe. Yanzun ma abin da ya sa abubuwan suka ƙara yin tsamari saboda shirye-shiryen sabon shirin da muka fara ne ya cakuɗe mini. Amma yanzu mun gama komai mun fara, in sha Allah zan san yadda zan yi in samu in dinga dawowa ko da bayan magrib ne." Jinjina kai kawai Janan ta yi, don yanzun dama ta samu wadda za ta yi kukanta son ranta. Kukan da ba na iya rashin dawowar Ummee gida ne da wuri ba, har da na rashin ji daga Khaleed kwanaki masu yawa. Ji take yi kamar ta bijire wa Yah Farouk. Ji take yi kamar ta ci gaba da kula Fa'iza ko ta san halin da masoyinta ke ciki. Ji take kamar ta nemi ko ma wacce irin hanya ce wadda za ta san halin da Khaleed ke ciki. Ya za ta yi? Shin ina za ta tsoma ranta ta ji daɗi?
Daidai lokacin da wayar Ummee ta shiga ruri. Hannunta ta yi amfani da shi wajen janyo wayar tana kara wa a kunnenta bayan ta amsa.
"In sha Allah ina hanya." Shi ne abin da ta faɗa bayan shuɗewar wasu sakanni. Daga haka ta ce
"Shalele, ki kwanta ki yi bacci ki huta. Kin ga har an fara kira na, yau na ɗan so na makara. Amma in sha Allah da wuri zan dawo. Ki cire damuwar komai a ranki uhmm?" Ta ƙare maganar da sigar tambaya tana kallon Janan ɗin. Sai ta jinjina kanta kawai.
"Dats my Baby girl." Ummee ta faɗa tana ƙarasawa gaban mudubin ta ƙarasa ɗaura ɗankwalinta sannan ta yafa mayafinta, ta ɗauki jakarta kana ta ƙaraso ta ba wa ɗiyar tata side hug sannan ta fice.
"Allah Ya tsare." Janan ta yi ƙarfin halin faɗa tana lumshe idanunta.
"Ameen Aysha." In ji Ummee lokacin da ta riga ta fice daga ɗakin. Komawa Janan ta yi a hankali ta kwantar da kanta idanunta a lumshe. Gabaɗaya ta rasa me ke yi mata daɗi.
Tana zaune a kan kujerar ɗakin sanye cikin atamfa riga da zani da ɗauri. Hankalinta na kan wata tasha da suke nuna wani Hausa film da ya ɗauki hankalinta, wannan ne dalilin da ya sa ta ba da hankalinta sosai tana kalla. Kamar daga sama ta ji ana knocking ƙofar sashen nata. Cike da mamaki ta ɗan sake kasa kunnuwanta don tabbatarwa. Da gaske ɗin kuwa knocking ɗin ake yi. Ba don ta so ba, don ba ta so ko ina ya wuce ta a film ɗin ta miƙe. Kai tsaye ta ƙarasa don ganin wane ne.
"Mai gidan ne ya aiko ni." Ta ji an faɗa bayan ta amsa sallamar da aka yi mata.
"Mai gidan kuma?" Ta faɗa cike da mamaki.
"Eh shi ne ya aiko ni." Ya sake faɗa. Ɗan ɗaga kafaɗarta ta yi, zai iya yiwuwa mantuwa Baban ya yi, don ko rabin awa ba a rufa da fitar tasa ba.
"To me ya faru?"
"Wai ya ajiye wani envelope a kan side drawer. Shi ne ya ce in zo in ce ki ɗakko masa." Tsayawa Hajiya Turai ta yi tana nazarin maganar mutumin. Anya kuwa? Baban ne zai aiko wani daban ya karɓar masa saƙo.
"Ikon Allah! To ina zuwa." Ta faɗa tana koma wa cikin ɗakin. Kai tsaye number Baban ta lalubo ta danna masa kira. Sai dai kira har wajen huɗu ba ta shiga. Ta sauke ajiyar zuciya tana koma wa wajen matashin.
"Ka ga na duba gaskiya ban gan ta ba. Ga shi na kira wayarsa ba ta shiga. Ƙila ko a wani wajen ya ajiye ya manta. Ni kuma ga shi ban gani ba. Ko za ka koma ka faɗa masa idan ya so ko Muhammad ne sai ya turo ya duba masa."
"Ikon Allah!" Matashin ya faɗa yana fito da wayarsa. Danne-dannen wayarsa ya yi na tsawon sakanni kafin ya kara a kunnensa.
"Kuma fa yanzun nan muka gama waya da shi. Ina ga ko matsalar network ne. Amma tabbas a kan drawer ya ce ya ajiye. Ga shi kuma duk wasu alamomi sun nuna yana buƙatar su ne da sauri. Amma bari na je na sanar da shi ba a gan su ba." Ya yi maganar yana ƙoƙarin juyawa.
"A'ah tsaya! Bari na sake dubawa." Hajiya Turai ta faɗa a sanyaye. Ita yanzu gabaɗaya tana tsoron abubuwan gidan ne. Maganar gaskiya ba ta shigo gidan nan da niyyar fita ba, don duk wani abu da take buƙata ta same shi. Da farko ta so ta bi Maman Al-ameen da ta ce mata ta bi duk abin da za ta ɗora ta a kai su ci arziƙi su bar shi a wajen. To amma tun da Muhammad ya kama ta tana ƙoƙarin bincike a wayar Baban jikinta ya yi sanyi. Wallahi ba ta shirya sake yin zawarci ba. Zawarcin ma bayan fita daga gidan Alhaji Abbas Shettima. Me ya kai ta? Shi ya sa take bin komai cike da takatsantsan.
Ɗakin Baban ta nufa kai tsaye. Kamar yadda matashin ya faɗa kuwa envelope ɗin na kan side drawer, hakan ne ya sa hankalinta ya sake kwanciya. Kuma ma mene ne na ɗaga hankali? Tun da har aka bar shi ya shigo gidan, har ya ƙaraso sashen ba tare da wata fargaba ba ai kuma shi kenan. Ɗauka ta yi kai tsaye ta je ta miƙa masa.
"Ka ga ga shi na gan shi."
"To madallah, bari na je." Ya faɗa yana yin gaba. Sauke ajiyar zuciya ta yi tana komawa don ci gaba da kallon ta, wanda ta san waje da dama sun wuce ta.
Bayan wajen mintina goma ta sake ji ana knocking. Tsaki ta ja a wannan karon tana ji kamar kar ta miƙe. Sai kuma dai ta tashi ta ƙarasa tana tambayar waye.
"Hajiya ni ne. Ashe saƙon nan ba wannan sashen aka turo ni ba. Ashe ɗayan sashen ne ni kuma kawai na taho nan. Sai da Alhajin ya gaji da jira ya biyo ni. Bayan ya ga takardun da na karɓo ya tambaye ni a inda na karɓo shi ne na nuno masa nan. To sai yake ce mini ai ba nan ne sashensa ba. Ga envelope ɗin."
"To ya yi." Ta yi maganar tana karɓa, a ranta tana jin ai gwara ma haka. Da ma kuma sai da ta yi mamakin turo wani da Baban ya yi ya zo ya karɓar masa saƙo. Ashe matsala aka samu. Sai da ta mayar da envelope ɗin inda ta ɗauke shi sannan ta dawo ta ci gaba da kallon da ta ji ya ɗan soma sire mata, saboda wajen da suka wuce ta.
A cikin makarantar Abee ya sauke ta. Tare suka sauka, saboda sanar da shi da aka yi mai makarantar na son ganin shi.
"Abee a dawo lafiya." Janan ta faɗa tana ɗaga masa hannu.
"A yi karatu da kyau." Ya faɗa lokacin da ya wuce office ɗin mai makarantar. Bayan kamar mintina biyar ya fito, sakawa ya yi aka kira masa Janan.
"Abee ashe ba ka tafi ba." Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso inda yake.
"Eh, mun yi magana da mai makarantar taku ne. Ashe mahaifiyar classmate naku ne ta rasu, makaranta za ta ɗauke ku ta kai ku can gidan bayan an tashi, za kuma su mayar da kowaccenku gida. Da na ji kamar in zo in kai ki da kaina, amma da na ji sun ce har da malamai a tafiyar, hankalina ya ɗan kwanta. Saboda haka ki kula, ki kula. Kin ji ko?"
"To Abee. Allah Ya tsare." Ta yi maganar lokaci guda.
"Ameen Ya Rabbi." Ya faɗa, daga haka ya wuce motarsa.
Yau ɗin ma dai ko da aka fita break suna tare da Ammeey.
"Janan." Ta jiyo muryar Fa'iza. Kamar ba za ta juya ba, don kar ta je idan ta juya ɗin zuciyarta ta kasa haƙuri har sai ta tambaye ta ina Khaleed.
"Fa'iza don Allah ki rabu da ni. Ki fita a harkata, ki daina kula ni. Don Allah ki ƙyale ni." Ta yi ƙarfin halin faɗin hakan cikin raunanniyar muryarta.
"Janan wai anya kuwa kina cikin hayyacinki? Kin manta wace ce ni a wajenki? Ko kuwa ba kya so ki ji daga Khaleed?" Khaleed ɗin da ta ambata, shi ne abin da ya sa ta ɗaga idanunta ta yi saurin kallon ta. Fa'iza ta jinjina mata kai ba tare da ta ce komai ba. Miƙewa Janan ta yi, kafin ta kai ga takawa, Ammeey ta yi azamar riƙo tsintsiyar hannunta sannan ta ce
"Aysha wuce mu tafi. Ba za ki je wajen Fa'iza ba." Ta faɗa tana kallon tsakiyar idanun Janan ɗin da suka ɗan risina. Haɗiyar wani yawu Janan ta yi cikin rashin sanin abin yi. Sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta, hakan ne ya sa ta bi Ammeey da ta ja hannunta suka bar Fa'iza a inda take a tsaye. Wani irin ɓacin rai ne ke nuƙurƙusar Fa'iza, lokaci ɗaya tana jin wani irin haushi, wanda ta rasa ma ita kam haushin wa ya kamata ta ji? Ta dai san daina kula ta da Janan ta yi hakan ba ya rasa nasaba da Farouk. Ta san shi kaɗai ne zai kitsa mata hakan ta zauna daram a kai. Tun da iyayen Janan ɗin babu wanda ya san AyshaJanan ɗin na soyayya ba tare da sanin su ba, sai shi Farouk ɗin shi kaɗai.
Yau ma kamar yadda Ummee ta yi wa Janan alƙawari da wuri ta dawo kamar kwana biyun nan da take samu ta dawo da wuri. Cike da mamaki ta kalli agogon da ke manne a bangon ɗakin, wanda yake nuna ƙarfe 4:20. Ɗakin Janan ɗin ta ƙarasa ta duba, don tun da ta shigo ba ta jiyo motsinta ba, ko wata alama da za ta nuna mata cewar tana gidan ba. Daidai lokacin da ta fito daga ɗaki Farouk ya shigo cikin ɗakin.
"Ummee yau ma ke ce da wuri haka?" Ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa. Ita ma murmushin ta yi wanda gabaɗaya bai fi na sakan biyu ba sannan ta ce
"Ina ƙanwarka ne? Ba ta cikin gidan nan. Ƙarfe 4:20, kuma yau babu islamiyya."
"Janan?" Ya ambaci sunan cike da mamaki.
"Oh! Abee ya ce makarantar za su kawo su. To amma har bayan la'asar?" Ya yi maganar duka a lokaci ɗaya.
"Oh ajiye wannan a gefe, la'asar fa ake magana. Me zai saka su ɗauki 'ya'yan mutane har bayan la'asar? Shin sun san halin da iyaye irina za su shiga? Farouk maza kira mini wani daga makarantar." Da ma tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya shiga danna wayarsa. Number ɗin mai makarantar ya kamo kai tsaye ya danna mata kira. Kira wajen uku wayar ba ta shiga ba, ya ja tsaki yana jin yadda ransa ke ɓaci.
"Farouk mu je ka kai ni makarantar tasu, ba zan iya zama ba. Hankalina ya kasa kwanciya."
"A'ah Ummee, ki zauna zan je na ji duk abin da ke faruwa. Ba wani abu ba ne in sha Allah, saboda haka ki kwnatar da hankalinki zan je in ɗakko miki ɗiyarki." Ya yi maganar cikin kwantar da murya, don so yake Ummeen ta fahimce shi.
"A'ah Farouk ba zan iya zama ba. Mu je kawai." Ta yi maganar tun kafin ta ji me
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 24