Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na biyu da suke zuwa ya taya Baba aikin da ya kawo shi, kuma su ƙare babu farinciki. Don idan dai har ya fahimta da kyau, yau ɗin ma an samu asara ne, kuma asara ba wai ta ƙananun kuɗi ba. To amma a ina gizo ke saƙar? "An sake yin asara kenan?" Daddy ya faɗa shi ma dai cikin mamakin. Ajiyar zuciya Baba ya sauke a karo na barkatai kafin ya ce "Ƙwarai." Ya faɗa a taƙaice, ya kuma kai ƙarshen hakan yana tura wa Daddy takardun. Babu musu ya ɗauka, wajen mintina goma yana nazari kafin ya ajiye su. Sai da ya soma sauke numfashi sannan ya ce "Ban san me ya sa kake son jawo bare jikinka ba. Ba tun yau ba, nake ce maka ka ɗora ni ko Abban Al-ameen a kan harkar kuɗaɗen nan, ban sani ba ko wani abu muka yi maka da ya saka ka ga ba mu cancanci wannan matsayi ba." Girgiza kai Baba ya shiga yi, cikin rashin jin daɗin maganganun Daddyn. "Ko kaɗan, har yanzu ka kasa fahimta ta Aminu. Mutanen nan tun kafin na zama wani nake tare da su, ban kuma taɓa samun wata matsala daga gare su ba. Ina ganin ƙwace wannan matsayi da suke kai cikin ƙanƙanin lokaci kamar butulci ne a gare su. Tun da tun kafin ku zo nan muke tare da su, idan dai har na juya musu baya, na nuna musu 'yan'uwana sun fi su kamar ban kyauta musu ba. Duk da abin a bayyane yake 'yan'uwana na gabansu fiye da tunani, amma tun bayan dawowar ku nan idan na ce zan maye gurbinsu da ku kamar za a kira ni ne na butulu. Mutane kuma za su kalle ni ne a matsayin wanda na more su a lokacin da 'yan'uwana ba sa tare da ni, bayan kuma sun kasance tare da ni sai na watsar da su. Ka ga ko don saboda haka aƙalla ya dace na yi bincike, shi ya sa na sake ba su dama a karo na biyu don tabbatar da abin da nake zargi. Ka ga yanzu da na sake kama su da laifi makamancin wancan ai ina da damar ɗaukar mataki. In kuma cijge su daga kan matsayin da suke kai in canja su da wasu." Da ma inda yake so a zo kenan, wannan dalilin ne ya sanya shi sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa. Wato wannan shi ake kira da, daga ƙarshe dai.. A kan Muhammad idanunsa suka sauka bayan ya buɗe su, Muhammad ɗin da ya kafe shi da waɗannan idanun nasa masu shegen kwarjini. Sai ya ji yana shirin ruɗewa, sai dai cikin ƙarfin hali, da kuma basarwa ya juya ya kalli Baba ya ce "Kar ka yi saurin yanke hukunci, ka sake bincikawa." Ya yi ƙarfin halin faɗar hakan ba tare da ya sake bari sun haɗa ido da Muhammad ɗin ba. Jinjina kai Baba ya yi, don bai ƙi ta ɗan'uwan nasa ba, zai sake bincikawa a karo na uku. Tsananin mamaki ne ya sanyaya masa jiki, don ko kaɗan bai taɓa kawo yaudara ko cuta daga wajen mutanen da ya matuƙar amince musu ba. Ya sakar musu duk wani abu da ya dace shi ko 'yan'uwansa ne suke yi, wanda yake ganin hakan a matsayin saka musu da irin ɗimbin alkairansu a gare shi. Don tun kafin ya zama wani suke tare da shi, suka kuma kasance a ƙarƙashinsa har yanzu. Suka kuma kasance mutane masu amana da a kaf kasuwa ba shi da waɗanda ya yarda da su kamar su. Sai ga shi lokaci guda suna neman cin amanar sa, wanda har hakan ya janyo masa asarar kuɗaɗe masu yawan gaske. In sha Allah ba zai bari hakan ta sake faruwa ba, zai yi maganin abun tun kafin gabaɗaya harkokinsa su durƙushe ƙasa, domin kuwa take-taken abubuwan da ya gani, hakan suke durfafa. A ɓangaren Janan kuwa ko da aka tashi daga islamiyya, Allah-Allah take ta fito kafin maghrib ta yi don haɗuwa da Khaleed kamar yadda suka yi alƙawari. Fa'iza ce ta jagorance ta har zuwa inda za su haɗu kafin ta jire mata hanya saboda tsaro. Tun da suka hangi juna suka fara sakar wa junansu murmushi. Da gaske kowa ya yi kewar ɗan'uwansa. "Ranki ya daɗe yallaɓiya." Shi ne abin da ya faɗa yana kafe ta da idanunsa da ke sake rikita ta, suna kuma sake nutsar da ita cikin ƙaunar Khaleed ɗin. Hira sosai suka sha, duk da tsoro na hana Janan ɗin sakewa. Don ita kam har yanzu ta kasa sabawa, sai take ji kamar Ummee, Abee ko Yah Farouk wani zai iya ganin ta tsaye da shi. Sai dai kuma Khaleed ɗin na neman kashe ta ba tare da ta shirya ba. Ya masifar iya soyayya, wanda hakan ya sa har ta shiririce, ta manta da cewar ƙayyadaddun mintuna gare ta, waɗanda suke dab da gabatowar maghrib. "Ga tsaraba na kawo miki. A wannan karon don Allah kar ki ce a'ah." Ya yi maganar yana miƙa mata wata ƙatuwar leda. Kallon ledar ta yi kafin ta shiga girgiza kanta. "A'ah ka tafi da ita, idan na je gida ban san wa zan ce ya ba ni ba. Kuma idan Yah Farouk ya gani zai yi faɗa." Ta ƙare maganar tana matsar da ledar daga kusa da ita. Ko kaɗan ba ta ankara ba, don ba ta taɓa kawo hakan ba, lokacin da ta ji hannun Khaleed a kan hannunta yana ƙoƙarin saka mata ledar a cikin hannunta. Ba ta san lokacin da ta yi wani irin baya ba bayan ta saki ledar da ƙarfi ba, ba kuma ta san lokacin da ta yi azamar zube ƙwayar idanunta a cikin tasa ba, sai dai tsananin yadda cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya soma rawa ya sanya ta gaza cewa komai. Sai a lokacin ya fahimci katoɓarar da ya yi. Shin wacce wauta ce ta kai shi ga aikata hakan? Wanne irin shirme ne ya kai shi, bayan tun farko ya san halin abar ƙaunar tasa? Shin me ya shiga kansa? Ko kuwa duk giyar soyayya ce? Tun kafin ma ta kai ga furta komai, ya yi azamar zubewa a kan ƙafafunsa ya shiga furta "Ki yi haƙuri masoyiyata, wallahi ba haka nake ba. Tsananin ƙaunar ki ce ke neman zautar da ni. Ba na so ki ƙi karɓar abubuwan da na siyo miki shi ya sa na kasa riƙe kaina. Don Allah ki yi haƙuri ki yafe mini. Kin san dai ko Allah ma muna yi masa laifi, kuma mu roƙi yafiya ya yafe mana. Ki taimaka mini." Ba ta taɓa tunani ba, sai dai ga ɗimbin mamakinta sai ta ji cikin ƙanƙanin lokaci ta yi na'am da maganganunsa, haushin da ta ji lokaci ƙanƙani ya bijiro mata, a take ta ji ya yi nasa wajen. "Ka tashi na haƙura." Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke, wadda har sai da ta fito fili, wanda hakan ya tilasta wa Janan yin dariya. Sai a lokacin ya sake samun sukuni ya ce "Ayshatou ba za ki gane irin tsananin fargabar da na shiga ba, saboda irin kallon da na ga kina yi mini." "To ni dai tafiya zan yi." Ta faɗa bayan da hankalinta ya dawo jikinta, ta kuma lura da yanayin gari kansa ya sauya ya soma duhu. Bai sake bi ta kan kayan ba, saboda kar a sake samun matsala, ya ce "To ki kula mini da kanki. Ki kula mini da kanki don Allah. Ko me za ki yi ki din ga tuna ba ke kaɗai ke da kanki ba, ga wani marayan Allah na gefe, wanda kika kasance mallakinsa." Yanzu kam dariya sosai Janan ta yi, don da gaske ya ba ta dariya. Sallama suka yi suna ji tamkar kar su rabu, bai yi tsammani ba lokacin da ya ga ta saka hannu ta ɗauki ledar sannan ta ce "Na gode." Cikin tsananin farinciki ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai, don ya ma kasa furta komai. Fa'iza ta ba wa ajiyar kayan a gidansu kafin cikin sauri ta durfafi gida, zuciyarta fall farinciki da kuma tunanin masoyin nata. Sai dai ta wani ɓangaren ta kasa mantawa da abin da ya faru a daren jiya. Shin ta yarda da abin da Yah Farouk ya ce cewar ƙila mafarki ta yi, ko kuwa ya ya? Ita dai gabaɗaya ɗakin nata ma ji ta yi ya sire mata. Daga zarar kuma ta yi yunƙurin sanar da Ummee sai ta tuna Yah Farouk ya ce kar ta faɗa musu saboda kar ta tayar musu da hankali. Ta kuma yarda ɗari bisa ɗari da abin da ya faɗa ɗin. Don ita shaida ce a kan sanin halin iyayen nata in dai a kan abin da ya shafe ta ne. Haka nan kawai ta ji zuciyarta ta wani irin harbawa lokacin da ta hangi Yah Farouk zaune a kan kujerar parlour idanunsa a kan ƙofar shigowa, yana ɗan karkaɗa ƙafarsa lokaci zuwa lokaci. Kyakykyawar fuskar nan tasa a ɗinke tsaff. Wanda hakan ba kasafai ya fiya faruwa ba, za ta iya cewa rabon da ta ga fushin Yah Farouk ɗin har ta manta. Dalili kenan da ya sanya ta dakatawa cikin wani irin bugun zuciya. Shi kenan, ta tabbata ya gan ta tsaye da Khaleed. Shi kenan ita kuma tata ta ƙare. Ta raya hakan cikin zuciyarta. Miƙewa Farouk ya yi, cikin nutsuwa ya shiga takowa inda Janan ɗin ke a tsaye, wadda duk wasu alamomi suka gama bayyana cewar ba ta da gaskiya. Da gaske kuma da alama abin da aka faɗa masa a makaranta ya faru. Duk wani takun da Yah Farouk ɗin zai yi, yana yi ne da fitowar bugun zuciyarta. Don rage tasirin hakan, ya sanya ta runtse idanunta don ta riga ta saddaƙar yau ita kam sai dai buzunta. Ba ta san lokacin da ya ƙaraso inda take ba, sai dai amon sautin muryarsa da ya cika dodon kunnenta, wanda ya fita da wani irin fushi da za ta ce tun da take a rayuwarta ba ta taɓa ganin wannan fushin a kan fuskar Yah Farouk ɗin ba. "Daga ina kike?" Shi ne tambayar da ya watso mata cikin tsare gida, shi kansa ba don yana da tabbacin yana da ƙwarin gwuiwar da zai iya yi wa Janan ɗin irin wannan tsawar ba. Sai a lokacin sannan ta iya buɗe idanunta da cikin ƙanƙanin lokaci hawaye suka cika shi taff. "Kar ki bari na sake maimaitawa, daga ina kike?" Ya ƙara faɗa yanzun ma dai a tsawace. A wannan karon har sai da jikinta ya nuna alamar tsoratar da ta yi, lokaci guda kuma hawaye suka soma sintiri a kan kuncinta. Cike da tsoron Yah Farouk ɗin da ya cika mata zuciya a karon farko ta buɗe baki da niyyar yin magana ta sake jiyo muryarsa. "Riƙe wannan, don na san tabbas yana da alaƙa da fitar ki daga makaranta. Wanda har sai da mai makarantar ta kira ni ta sanar da ni. Ina kika je? Me ya fitar da ke daga makaranta? Yanzu kuma me ya sa ba ki dawo gida ba tun da aka tashi? Ina kika tsaya?" Wani irin mahaukacin bugu zuciyar Janan ɗin ke yi. Ba ta taɓa tunani ba, ba ta taɓa zaton lokacin tonuwar asirinta zai zo a nan kusa ba. Tun yanzu? Yanzun da ta fara sanin daɗi da kuma garɗin soyayya? Yanzun da Khaleed ya shayar da ita ƙaunar da ba ta iya tunanin za ta iya rabuwa da shi? Yanzun da ta yarda da maganganun Fa'iza na cewar sai ta fara soyayya za ta san wace ce ita? "Salamu alai...." Muryar Fa'iza ta doso cikin parlourn, wadda ganin Farouk da AyshaJanan ɗin tsaye cirko-cirko ya sanya ta dakatawa cikin wani irin sauri. Take ita ma ta ji zuciyarta ta buga, don ko ba a faɗa ba, ta fahimci tabbas yau wani abu ya faru a gidan nan. Duk wasu alamomi kuma sun nuna dubun Janan da ƙyar idan ba tana dab da cika ba ne. Cikin azama ta yi amfani da ɗayan hannunta wajen rufe abin da ke a hannunta na hagu. Sarai Farouk ya lura da abin da ta yi, don haka a nutse ya kewaye Janan da ke tsaye ya ƙarasa inda Fa'iza take. Janan ban da girgiza kai da kuka babu abin da take yi. Shin me ya kawo Fa'iza cikin gidansu? Me ya sa za ta yi mata haka? "Mene ne a hannunki?" Ya tambaya kai tsaye yana kallon Fa'izar. Yadda ya yi magana ya sanya ta ji jikinta ya sake ɗaukar rawa. Sai dai kafin ta gama tunanin abin da za ta ce ta sake jiyo muryarsa a karo na biyu ya ce "Ba ni." Gabaɗaya sai ta kasa yi masa musu, don haka hannunta na rawa ta miƙa masa. Bin abin da ta miƙo masa ɗin ya yi da kallo kafin a nutse ya kai hannunsa ya karɓa. Idan dai har ba idanunsa ke nuna masa ba daidai ba waya ce yake gani. To amma wayar wace? Me ya sa Fa'izan ta ɓoye saboda ganin sa da ta yi a ɗakin? Kafin ya gama tunanin wayar ta soma ringing, sai da ya kalli Fa'izan da ta kasa kallon sa sannan ya kalli number da ke ci gaba da yawo a kan wayar. Haka nan kawai sai ya ji shi ma tsoro ya kama shi, amma bai bari hakan ya nuna ba, ya ɗaga wayar, ya kuma saka ta a handsfree. "Fa'iza duk yadda ake ciki ki samu ki kai wa Aysha wayar nan. Yau na saka ran sake jin muryarta kafin na yi bacci. Wallahi na kasa sukuni tun bayan da muka rabu da ita." Shi dai Farouk ba zai ce ga lokaci ba, amma tabbas ya ji hannunsa ya soma karkarwa. Shin me kunnuwansa ke jiye masa? Me yake shirin faruwa? Shin ta ina suka gaza wajen ba wa Janan ɗin tarbiyya? Wacce kalar ƙauna ce ba su nuna wa Janan ba? Da gaske Janan ɗin ce ke kula wani a waje? Har da fita daga makaranta don haɗuwa da shi? Don ko ba ta ba shi amsa ba, yanzu ya fahimci dalilin fitar ta daga makaranta. Cikin tsananin zafin zuciya ya ɗaga wayar da niyyar buga ta da ƙasa, bai tsammata ba, bai kuma san lokacin da Janan ɗin ta zube a kan ƙafafunta ba, hannayenta riƙe da ƙafafunsa take faɗin "Yah Farouk don girman Allah ka yi haƙuri kar ka fasa wayar nan. Ba laifin Fa'iza ba ne, don Allah kar ka ga laifinta. Gabaɗaya laifina ne, tun da ni na ji na amince da Khaleed. A shirye kuma nake na karɓi duk irin hukuncin da za ka yi mini. Na kuma san Khaleed ne ya aiko ta, idan ka fasa wayar nan, tamkar ka fasa zuciyata ne, domin hakan na nufin ba zan din ga jin muryarsa ba, har sai mun haɗu da shi. Kuma wallahi ina son shi Yah Farouk, ina son shi." Cikin ƙanƙanin lokaci gumi ya soma tsatstsafowa Farouk, jijiyoyin kansa da tulin sumar kansa ta yi nasarar rufe yadda suka fito, yanzu na kan goshinsa suka yi nasarar fitowa raɗa-raɗa. Kyawawan idanunsa da suka kasance farare ƙall babu sirkin ja ko kaɗan, cikin lokaci kaɗan suka soma rinewa zuwa jar kala. Sai ya zube su gabaɗaya a kan Janan ɗin yana jin yadda kalamanta ke ci gaba da yi masa amsa-kuwwa cikin kunnuwansa duka biyun, kamar yanzun ne take faɗar su, lokaci guda yana saurarar yadda bugun zuciyarsa ke tafiya da maganganun nata. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 07 Ba ƙaramin gigita Fa'iza kalaman Janan suka yi ba. Don ba ta taɓa kawo ko da da wasa makamantan kalaman nan za su iya fitowa daga bakin Janan ɗin ba. Dalili kenan da ya sanya ta kafe ta da idanunta, wai ko hakan zai sa ta tabbatar da abubuwan da kunnuwanta suke jiye mata. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwarta ta tunasar da ita cikin tarkon da take, wanda wannan ne lokaci na daidai da za ta samfe ba tare da hukuncin Janan ɗin ya shafe ta ba. Ta lura gabaɗaya idanun Yah Farouk na kan Janan, kuma duk wasu alamomi sun nuna hatta hankalinsa yana kanta. Dalili kenan da ya sanya ta kalli ƙofar ɗakin, kafin a sukwane ta sake kallon Yah Farouk ɗin, cikin azama ta yi wuff ta fice daga ɗakin. Bayan shuɗewar wajen mintina biyar, zuwa lokacin kukan da Janan ke yi ya ɗauke ɗiff. Ba ka jin sautin komai sai na ajiyar zuciyar da take saukewa lokaci zuwa lokaci. A nutse Farouk ya zagaye ta, ba tare da ya ce ko uffan ba, ya fice daga ɗakin, cikin yanayin da ita kanta ba za ta ce wanne iri ba ne. Sai dai abin da bai sani ba, har gwara ya hukunta ta ko da da duka ne ballantana kuma da fatar baki, a kan dai shirun nan da ya yi mata. Shin ita kuwa ina za ta saka kanta? Ta shafe fiye da rabin awa a wajen, har bayan an idar da sallahr maghrib ta kasa tashi. Sai daga ƙarshe dai da ta ga babu haza ta miƙe ta shige ɗakinta. Gabaɗaya tsoron ɗakin ma da ta ji tana yi sai ya tafi nasa wajen. A ciki ta yi sallah ta zauna a kan dadduma cikin rashin sani abin yi. Sai bayan isha'i sannan Ummee ta dawo. Zuwa lokacin ta yi iya ƙoƙarinta don kada Ummeen ta gane akwai wani abun. Duk kuma wani ƙoƙarinta na son ganin Yah Farouk ya shigo ɗakin amma shiru. Har bayan dawowar Ummee ma bai shigo ba. "Farouk shiru, ko ba ya cikin gidan ne?" Ummee ta jefa wa Janan da ke wasa da hannunta tambayar lokaci guda tana nazarinta. Kafin ta kai ga cewa komai Ummeen ta rufe system ɗin ta ce "Ke zo nan." Sai a lokacin sannan Janan ta ɗaga idanunta ta kalli Ummeen. Ta yi azamar runtse su don mayar da ƙwallar da ta taho mata, lokaci guda tana amfani da hannunta wajen gyara zaman glass ɗin idanunta. Ba ta musa ba ta miƙe ta nemi waje gefen Ummeen ta zauna. "Anya kuwa ba kya ɓoye mini wani abu? Me yake damun ki? Akwai wata matsala ne da ban sani ba? Rashin zamana a gida kwana biyu na damun ki ne? Ko kuwa dai wani abu ne daban?" A jere Ummee ta yi mata duka waɗannan tambayoyin, waɗanda lokaci guda suka so diririta Janan. Sai ta haɗiyi yawun da ya tsaya mata a maƙogwaro tana ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta sannan ta yi ƙarfin faɗin "Ba fa komai Ummee, kawai kewar ki ce." Ta ƙare maganar tana kwaɓe fuska. "Na sani Baby girl, amma kar ki damu nan ba da daɗewa ba in sha Allah zan din ga yini a gida tare da ke." Ta ƙare tana jan Janan ɗin jikinta. "Ina son haka Ummeena." Ta ƙare tana murmushi. Sai da ta tabbatar Ummee ta daɗe da yin bacci. Gidan kuma ya sake yin shiru alamar dare ya sake tsalawa sosai sannan ta ɗauki hijab ɗinta ta zura. A nutse ta tura ƙofar ɗakinta ta fito tana kallon cikin parlourn. Sai da ta sake tabbatarwa babu kowa sannan ta fito. Kai tsaye harabar gidan ta nufa, duk da yadda zuciyarta ke bugawa, amma ba ta bari hakan ya yi tasiri a kanta ba ta ƙarasa zuwa ɗakin da ke gefen gidan, ɗan nesa kaɗan da gate. A nutse ta tura ƙofar ɗakin, kamar yadda ta tsammata kuwa a buɗe take. Sai ta saka kanta cikin ɗakin cike da fata iri-iri. Babu kowa cikin parlourn, sai dai a kintse yake ƙal-ƙal. Kamar yadda mamallakin ɗakin ya kasance mai tsafta, haka ɗakinsa ma ya kasance. Kamar kuma ɗakin mace, ban da sassanyan ƙamshi babu abin da ke tashi a ciki. Ajiyar zuciya ta sauke idanunta a kan bedroom ɗinsa. Tana da tabbacin yana ciki, ko da ya yi bacci ne to za ta iya jiran shi har ya tashi don ta ba shi haƙuri. Hannu ta ɗora a kan ƙofar ɗakin nasa cike da fatan a buɗe take. Addu'ar tata kuwa ta karɓu don kuwa tana turawa ƙofar ta tafi. Sai da ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta sannan ta buɗe kai tsaye ta saka ƙafafunta cikin ɗakin. Ta tabbatar dai a wannan lokacin ya yi bacci, sai dai ga ɗimbin mamakinta yana zaune a kan kujerar da ke gefen gadonsa. Hannunsa ɗauke da waya, wadda haskenta ya bayyana a kan fuskarsa da idanunsa ke a lumshe, ya jinginar da kansa kaɗan ta baya, sai ka ɗauka ko bacci yake yi. A nutse ta shiga takawa idanunta a kan wayar da take iya ganin haskenta duk da akwai ƙwan fitila a ɗakin, sai dai ba irin mai hasken nan ba ne saboda dare. A hankali ta sauke idanunta a kan rubutun da ya bayyana a kan wayar, da alama rubutu yake yi bacci ya ɗauke shi. Don haka ba tare da ta damu da ganin abin da ke cikin wayar ba, ta saka hannunta da niyyar ɗaukar wayar. Kamar wanda miciji ya sara haka ya buɗe idanunsa da sauri yana janye wayar da saurin gaske. Fess ya zube idanunsa a kan Janan cike da mamakin ganin ta. Sai ta bi shi da kallo lokaci ɗaya tana sauke idanunta a kan wayar tasa. Har ya buɗe baki da niyyar yin magana sai kuma kamar wanda ya tuna wani abu ya miƙe tsaye bayan ya ɗan lumshe idanunsa. Bayan shuɗewar wajen mintina biyu babu wanda ya ce komai, Farouk ya ce lokacin da yake ƙoƙarin gyara kan gadonsa. "Me ya fito da ke cikin daren nan?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya kalle ta ba. Sai a lokacin sannan ta ji hankalinta ya ɗan kwanta, don ba ƙaramin tsorata ta yi da shirun da Yah Farouk ɗin ya yi mata ba, ba ta taɓa tunanin fushin ya yi zurfin haka ba. "Yah Farouk don Allah ka yi haƙuri." Shi ne abin da ta faɗa muryarta na rawa. Dakatawa da abin da yake yi ya yi, ya juya ya kalle ta sannan ya ce "Ni na ce kin yi mini wani abu?" Ya tambaya cikin tsare gida. "Ni dai don Allah Yah Farouk kar ka nuna kamar ban yi laifi ba kuma ka ci gaba da fushi da ni. Don Allah ka yi haƙuri ba zan ƙara ba." A nutse Yah Farouk ya taka har inda Janan ɗin take, ya ɗora ƙafarsa a kan kujerar da ta zauna bayan tashinsa ya ce "Janan ke fa kika ce in bar ki kar in fasa miki zuciya." "Ka yi haƙuri Yah Farouk." Ta faɗa a wannan karon hawayen na soma gangarowa a kan kuncinta. Iska ya fesar daga bakinsa kafin ya miƙe tsaye sosai. "Shi kenan Aysha ya wuce. Kar ki sake wannan kuskuren na haɗuwa da wani a waje ba tare da sanin gida ba. Fita daga makaranta hakan na nuna tasirin tarbiyyar da aka yi maka kenan. Kina so ne mu tuhumi kanmu a bisa sakaci da muka yi da kuma gazawa wajen ba ki tarbiyya? Me ya sa Janan? Kar ki sake." "Ba zan sake ba in sha Allah Yah Farouk. Ka yi haƙuri don Allah." Ta sake faɗa a karo na barkatai. Jinjina kansa ya yi lokaci guda yana tafiya, can ya ce "Ba na buƙatar na sake jin ban haƙurin. Ga wayarki nan." Ya faɗa yana miƙa mata wayar da ɗazun da hannunsa yake ƙoƙarin fasa ta. Cike da mamaki ta ɗaga idanunta ta kalle shi, jinjina mata kai ya yi don tabbatar mata da abin da take gani. Sai ta yi saurin ture wayar gefe tana girgiza kai. "Ni ba na so, ba na so wlh." Ɗan cije leɓensa na ƙasa ya yi, kafin ya ce "Wayar masoyin naki?" "Kai Yah Farouk." Ta yi maganar tana ɗan bubbuga ƙafarta. "Shi kenan. Kin san me nake so da ke?" Ya tambaya yana kallon ta. Sai ta girgiza kai ba tare da ta ce komai ba. "Ki faɗa mini gaskiya a kan wanda ya aiko miki da wannan wayar. Me kike ji a kansa? Kar ki sake ki yi mini ƙarya." Shiru Janan ta yi tana tunanin ta ina za ta fara. Shin ta buɗe baki ta zayyano

Chapter 5 of 24