ƙaraso yake lura da yanayinta, kafin da ya ji ba ta ce komai ba har lokacin ya sanya ya ce
"Ummee, lafiya?" Kamar da ma jira take yi, sai ta shiga girgiza kanta tana jin yadda faɗuwar gaba ke ziyartar ta.
"Me ya yi zafi ne Abee? Ba ka ji zuciyata yadda take bugawa ba. Duk mene ne ya sa sai an kai ga haka?" Kallon ta kawai Abee yake yi, cikin rashin fahimtar maganar da take yi. Hakan ne ya sanya shi ajiye wayar gabaɗaya ya miƙe tsaye ya ƙarasa inda take tsaye ya ce
"Kin ga nutsu ki sanar da ni me yake faruwa." Sai da ta sauke numfashi sannan ta ce
"Su Yaya Amina ne wai za su shigo garin, kuma wai a nan za su sauka. Ka san duk lokacin da suka zo ba alkairi ke kawo su ba. Ya zama dole hankalina ya tashi, don a wannan karon kuma ban san da wacce suka zo ba. Ba na so su zama silar rugujewar farincikin gidana." Girgiza kai Abee ya yi kafin ya ce
"Kina da saka wa kanki damuwa Ummee. Duk me ya kawo waɗannan maganganun? Babu abin da zai faru in sha Allah. Ki kwantar da hankalinki, ki bar su su zo, ai dai ba dawwama za su yi a nan ɗin ba ko?" Girgiza kai Ummee ta shiga yi.
"A'ah, ko dai in hana su zuwa in ci gaba da zama cikin gidan nan. Ko kuma in bar su su zo, amma tabbas daga ni har 'ya'yana babu wanda za su samu cikin gidan nan." Ajiyar zuciya Abee ya sauke. Don ya fahimci Ummee ɗin sarai, ya kuma san yanzu tun da ta ce hakan tana nufin haka ɗin ne. Amma zai gwada tausar ta ko za ta sauko. Idan kuma ya yi nazari ya ga hakan ce mafita, to tabbas shi ma zai goyi bayanta, don shi kansa yana iya hasashen abin da zai iya faruwa a wannan karon idan dai har mutanen nan suka zo.
"Ina wuni?" Ya faɗa lokacin da yake ƙoƙarin neman waje ya zauna. Sai ta yi murmushi sannan ta ce
"Lafiya ƙalau Muhammad, barka da zuwa. Abu Muhammad ya sanar da ni da ma za ka zo ka ci abinci. Na shirya maka komai ga shi nan. A ci daɗi lafiya." Jinjina kai kawai ya yi yana ƙaƙalo murmushi a kan fuskarsa. Shi gabaɗaya ba a son ransa ya zo sashen Hajiya Turai ɗin ba, don dai Baba ya matsa masa ne, saboda shirya musu abinci kala-kala da ta yi, shi kuma bai samu ya ci ba, don kar ta ji babu daɗi ya saka shi turo Muhammad ɗin ya ci a madadinsa. Ta ji daɗin hakan sosai, don a yadda Muhammad ɗin yake a wajen mahaifinsa, turo shi da ya yi don ya wakilce shi, hakan ya nuna ya mutunta ta.
Ya shafe wajen mintina ashirin cikin ɗakin, yana ɗan tsakurar abincin hankalinsa gabaɗaya a kan wayarsa. Zuwa can ya danna kiran wani layi da a yau ɗin an kira shi ya fi sau uku da shi. Kira 1 aka ɗaga, tun kafin ya kai ga cewa komai daga can ɓangaren aka ce
"MuhammadAali na ɗauka mahaifinka a wajenmu ma mahaifi ne. Na ɗauka duk abin da zai same ka ko mahaifinka ya shafe mu ne. Mun kasa sukuni, daga mu har Oga a kan abin da ya faru. Ta yaya za mu zuba ido duniya na ci gaba da kallon Faaza a matsayin da aka kwatanta shi? Ta yaya za mu zuba ido bayan duniya na nan tana yi maka kallon mutumin banza? Rayuwar da muka yi ai ta fi ƙarfin hakan ta faru mu kawar da idonmu. Ko da yake mun daina aiki tare, ai hakan ba shi ke kuna alaƙarmu ta yanke gabaɗaya ba. Idan kai kana gaba da mu, mu har yanzu muna son ka, ba a yi ranar da za ta zo mu manta rayuwar da muka yi tare ba." Lumshe idanunsa MuhammadAali ya yi bayan gama saurarar wannan dogon bayanin. Kamar wanda aka yi wa dole haka ya buɗe baki da ƙyar ya ce
"Me kake so a yi?"
"Yawwah." Wancan ɗin ya faɗa yana gyara zamansa, sannan ya ɗora da faɗin
"Ka zo ka same mu, sai a san abin da za a yi. Dole ne a wanke Faaza da kai kanka ta kowacce hanya ce." Da sauri MuhammadAali ya ce
"Ta kowacce hanya?" Shi ma wancan ɗin cikin son gyara kalamansa ya ce
"Ka san bakin ne ya saba, ina nufin za a wanke Faaza da kai kanka, ta hanyar da sai ka amince ta yi, a bi ta." Sai a lokacin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin zillo. Haƙiƙa yadda suka nuna damuwa a kan Baba hakan ba ƙaramin burge shi ya yi ba. Tun yana watsa musu ƙasa a ido, yanzu kam yana ji yana da kyau ya saurare su, ko babu komai a kan rayuwarsa da ta mahaifinsa ne ake magana. A yau, a kuma wannan karon yana jin lokaci na ƙarshe in sha Allah da zai sake saɓa wa Baban, zai yi aiki tare da mutanen da Baban ya hana shi hulɗa da su a kan wannan al'amari. Daga zarar abin da suke buƙata ya faru, zai tsame hannunsa daga cikinsu kamar yadda ya yi a da. Don yanzun ma zai amince musu ne saboda ana magana ne a kan mahaifinsa, ɗaya tamkar da dubu, wanda kaff duniyar nan ba shi da wanda ya kai shi, ba shi kuma da wanda ya fi ƙauna sama da shi.
"Ba ku za ku zaɓar mini inda zan zo ba. Zan sanar da kai inda za ka zo sai mu haɗu mu yi magana."
"Duk yadda ka faɗa haka za a yi MuhammadAali." Daga haka bai sake cewa komai ba ya katse wayar. Daga ɗaya ɓangaren murmushi mutumin ya yi, ya kalli Ogan nasu da tun da ya fara wayar yake kallon sa cike da fata kala-kala. Sai da ya sake sakin wani sabon murmushin sannan ya ce
"Yallaɓai ya amince." Lumshe idanunsa wanda aka kira da Yallaɓan ya yi lokaci guda yana sauke ajiyar zuciya, fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi mai ma'anoni da dama.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 20
Kamar yadda ya faɗa kuwa, shi ɗin ne ya sanar da su inda za su haɗu. Bayan isha'i ya fice daga gidan bayan ya sanar wa da Baba za su ɗan fita shi da Saleem. Yana sake, tun zuwan Saleem ɗin yake yawan ambatar sunansa idan zai je wani wajen, saboda sanin hankalin Baban ya fi kwanciya da fitar su tare.
Haɗaɗɗen waje ne, babu mutane sosai ciki sai jifa-jifa. A nutse kiɗa ke tashi, irin kiɗan nan mai shiga jiki, mai sanya wanda ke saurarar sa cikin shauƙi. Tun kafin ya ƙarasa idanunsa ke nuna masa waɗanda ke zaune a kan kujerun da aka tanada saboda haɗuwar da suka shirya za su yi. Kasancewar babu haske wajen, sai irin colours ɗin nan da suke taimakawa wajen haska waje, ya sanya sai da ya ƙarasa dab da wajen sannan ya shaida fuskar. Dakatawa ya yi da sauri yana jin ɓacin rai na ziyartar sa. Me ya sa Zaki zai yi masa haka? Me ya sa zai zo tare da babban Ogan nasu?
"Kada ka ce za ka koma MuhammadAali." Ogan ya faɗa har lokacin idanunsa na kan waya. Bai nuna alamar ya ji ba, ya juya. Daidai lokacin da Zaki ya miƙe ya yi azamar shan gaban MuhammadAali yana faɗin
"Me ya sa haka ne Muhammad? Ka san irin damuwar da Yallaɓai ke ciki a kan al'amarin nan? Ina roƙon ka kar ka watsa masa ƙasa a ido. Ka tsaya ka saurare shi ko da na mintina kaɗan ne." Shiru Muhammad ya yi kamar mai nazari, kafin zuwa can ba tare da ya ce komai ba ya juya. Ya ja kujera cikin kujerun kusa da Yallaɓan ya zauna. Sai a lokacin sannan Zaki ya sauke ajiyar zuciya, kana ya nemi waje shi ma ya zauna, don sarai ya san taurin kai irin na MuhammadAalin, shi ya sa yake bin sa a hankali. Shiru ne ya wanzu na tsawon mintina biyu, babu wanda ya ce uffan. Ta ɓangaren Muhammad kuwa, jira yake lokacin da ya ɗiba ya cika ya tashi ya bar musu wajen. Duk da a kansa za a yi maganar, amma ai ba shi ya nemi taimakonsu ba ballantana su ce za su gara shi yadda suke so.
"Muhammad." Yallaɓan ya faɗa hannunsa riƙe da wani zagayayyen abu yana amfani da shi kan kujerar gabansa. Sai a lokacin sannan MuhammadAali ya ce
"Uhmm." Bai damu da yadda ya amsa ba, kai bai damu da ko da magana ce Muhammad ɗin zai faɗa masa ba. Don haka ya ci gaba da faɗin
"Dukka muna zaune nan ne a dalilinka. Na ji duk abin da ya faru, za kuma mu haɗa hannu mu yi aiki tare a kanka." Da mamaki Muhammad ya kalle shi, ya ce
"Aiki? Ni na ce ina buƙatar a yi wani aiki da ni saboda abin da ya faru?" Ƙasa da murya Yallaɓai ya yi ya ce
"Wannan fusatar taka ta fi komai burge ni." Da gaske maganganun nasa sake fusata shi suke yi, don haka abin da ya faɗa yanzun ba ƙaramin ƙona masa zuciya ya yi ba. A fusace ya miƙe har yana dukan kujerar gabansu, da sauri Zaki ya miƙe, shi sam ya ma manta wane ne a gabansa, don hakan da Muhammad ɗin ya yi, kamar rashin girmamawa ne wa Yallaɓan nasu. Da sauri Yallaɓan ya ɗaga wa Zaki hannu alamar ya dakata. Babu musu kuwa ya dakata ɗin. Sai ya tsiyayo ruwa mai sanyi a tambulan ya miƙa gaban Muhammad ɗin, ya ce cikin kwantar da murya.
"Kwantar da hankalinka, ba na nufin abin da ƙwaƙwalwarka ke hasaso maka. Zauna mu yi magana ta fahimta." Sai a lokacin sannan Muhammad ya runtse idanunsa, yana fatan wannan ɓacin ran ya tafi nasa wajen.
"Ina jin ka." Ya yi maganar kamar wanda aka yi wa dole bayan ya nemi waje ya zauna. Kafin Yallaɓan ya kai ga cewa komai, ya ɗora da
"Idan har ka kira ni nan ne, don ku taya ni nemo gaskiyar al'amari don nan gaba in biya ka, ka daina tunanin hakan mai yiwuwa ne." Girgiza kansa ya shiga yi. Ya ɗan kurɓi ruwa sannan ya yi murmushi ya ce
"Ko kaɗan, shi ya sa na ce maka ba na nufin abin da ƙwaƙwalwarka ke hasaso maka." Iska kawai Muhammad ya fesar ba tare da ya ce komai ba. Hakan ne ya ba wa Yallaɓan damar ɗorawa da faɗin
"Ka gode wa Allah mutane da dama ba su san fuskarka ba, idan ba don haka ba, ba ka isa ka shigo wajen nan ba tare da wani abu ya faru ba. Abin jin shi ne Faaza, wanda duniya ta riga da ta san fuskarsa. Allah kaɗai Ya san halin da yake ciki, musamman saboda kallon da mutane ke yi masa."
"Yana cikin yanayi mai kyau, cikin kuma kwanciyar hankali." MuhammadAali ya yi saurin katse shi da faɗin hakan.
"Ka tona zuciyarsa ne ka kalla?" Ya jefa masa tambayar kai tsaye yana kallon sa. Cikin basar da tambayar MuhammadAali ya ce
"Mu je kai tsaye zuwa abin da kake so ka ce." Shiru ya yi na tsawon minti ɗaya, kafin daga bisani ya ce
"Idan har ka amince zan saka a binciko ko ma wace ce matar. Ya zama dole a wanke Faaza a idon duniya, ko da hakan na nufin shi ne wani abu mai kyau da za mu yi wa Faaza, wanda zai saka ya ji daɗi, ya ga farin mu, ya kuma yabe mu. Mu kuma wanke kanmu a wajensa, ya kuma daina kallon mu matsayin waɗanda suka zamo sanadiyyar lalacewar ɗansa." Numfashi MuhammadAali ya sauke bayan gama jin maganganun Yallaɓan. Sai yanzu ya fahimci dalilin yin hakan, don da ma ya san babu yadda za a yi su yi hakan babu wani dalili. To amma ko ma dai mene ne, dalili ne mai kyau, shi ma kuma zai so hakan, ko da hakan ba ya nufin zai ci gaba da aiki da su.
"Na gode." Ya faɗa bayan ya jinjina kansa. Hannu Yallaɓai ya miƙa wa MuhammadAali yana murmushi, bin hannun ya yi da kallo kamar mai tunanin wani abu, kafin a hankali ya miƙa nasa, suka gaisa lokaci guda suna kallon juna kowa da abin da yake saƙa wa cikin zuciyarsa.
"Ina so a nemo mini wanda ya fara ɗora shirin a gidan radio." Shi ne abin da Yallaɓai ya faɗa yana kallon Zaki.
"An gama ranka ya daɗe." In ji Zaki.
Tana zaune cikin parlourn, hannunta ɗauke da wani hadith tana maimaita ƙarin da aka yi musu jiya. Ummee tana ɗakinta, ya yin da mazan gidan duk ba sa nan. Wayar Ummee da ke ajiye a kan kujera ce ta shiga ƙara. Sai da ta ɗaga murya sannan ta ce
"Ummee ana kira." Daga haka sai ta ci gaba da maimaita karatunta. Shiru Ummeen ba ta fito ba, har kiran ya katse wani ya sake shigowa. Sai ta miƙe, bayan ta ajiye hadith ɗin ta ƙarasa inda wayar take ta ɗauka kai tsaye ta soma takawa zuwa ɗakin Ummeen. Kamar wadda aka ce ta duba, sai idanunta suka sauka a kan number da ke yawo kan wayar. 'Adam Ibrahim' Sunan da ya bayyana a kan wayar kenan. Sai kawai ta dakata cikin zuciyarta tana tuna sunan mutumin nan, idan dai har ba ta manta ba wannan shi ne sunansa, kuma number ɗin ma ita ce. Sai kawai ta tsinci kanta da son ɗaga wayar, ta leƙa ɗakin Ummeen, sai ta ga bacci take yi. Don haka cikin sauri ta dawo parlourn wayar na dab da katsewa ta yi azamar ɗagawa.
"Hello." Ta faɗa bayan ta ɗaga. Muryarta da ta doki dodon kunnensa ya sanya shi lumshe idanunsa, ya ji mugun daɗi, da ya kasance ba Ummeen ce ta ɗaga ba, an sauƙaƙa masa.
"Kyakykyawa." Ya faɗa a nutse. Sai ta yi saurin rufe fuskarta cike da kunya.
"Eh mana, buɗe fuskar." Ya faɗa. Saurin buɗewa fuskar tata ta yi kuwa, tana zaro idanunta. To ta ya aka yi ya san ta rufe fuskarta? Ta tambayi kanta.
"Ya aka yi ka san na rufe fuskata?" Ta tambaya cike da mamaki. Dariya ya yi kana ya ce
"Kina tunanin muna waya ki yi wani abun in kasa ganewa? Ƙaunar ki ta zarce hakan." Ya faɗa cikin kwantar da murya. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji zuciyarta ta soma bugawa. 'Ƙauna?' Ta ambaci hakan cikin zuciyarta. Ta yaya za ta gane da gaske shi ma son nata yake yi ba yaudara ba irin wadda Khaleed ya yi mata? Duk kanta take ta yi wa tambayar, cike da fatan ta samu mai ba ta amsa.
"Na ji kin yi shiru." Ya faɗa a hankali. Sai ta yi saurin girgiza kai kana ta ce
"Babu komai." Ta faɗi hakan, don yadda take ji a ranta ko da yaudarar ta Adam ɗin zai yi ya riga ya gama sace mata zuciya. Tun bayan da suka yi wayar farko ta kasa sukuni, duk wani motsi da ta yi sai kalamansa sun faɗo mata. Yanayin maganarsa, nutsuwa a magana, da yanayin sanyin muryarsa da take iya fuskanta. Sun shafe wajen rabin awa suna wayar, sannan suka soma ƙoƙarin yin sallama, saboda islamiyya da Janan ɗin za ta tafi.
"Ina neman wata alfarma a wajenki." Adam ya faɗa, cike da fatan wannan alfarmar ya same ta. Sai da ta yi shiru, kafin ta ce
"Tam."
"Ki mini alfarmar kira na da daddare in sake jin muryarki. Wallahi ina masifar ƙaunar ki, zuciyata har wani zillo take yi mini idan muna waya. Ki taimaka wa rayuwata. Na san idan muka yi waya yau, babu lallai in sake samun damar yin magana da ke a cikin kwana biyun da za su biyo baya." Ba tare da ta san ta yadda hakan za ta kasance ba kawai ta amsa da "To" Don ita ma har ga Allah ba ta gaji da jin muryarsa ba. Ita abin har mamaki yake ba ta, ba ta taɓa tunanin za ta iya mantawa da Khaleed haka ba, ballantana har ta samu wani da zai maye mata gurbinsa ba. Sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci Allah Ya kawo mata wani, wanda take ji a jikinta kamar ma har yana ƙoƙarin fiye mata Khaleed ɗin.
Kai tsaye shiryawa ta yi cikin uniform ɗin islamiyya. Wannan rashin fara'ar da take ta fama da shi kwana biyu, tuni ta neme shi ta rasa. Ban da maganganun Adam babu abin da take iya tunawa. Ita kanta wallahi abin har mamaki yake ba ta. Sai ka ce wadda aka saka wa hannu? Ko da ta je makaranta ma kasa sukuni ta yi, karatun ma da ƙyar ta iya yi saboda tunanin mafitar da za ta samu da dare, wadda za ta samu damar yin waya da Adam ɗin da take mutuwar son jin muryarsa duk kuwa da ɗazun suka gama waya.
Da daddare kamar kodayaushe, dukkansu suna parlourn Ummeen, suna hira. A yau kam Janan na gefe ba ta cewa ko uffan, ɗaukar wayar Ummee ba halinta ba ne, musamman da ya kasance kusan kodayaushe Ummeen na aiki a kanta ko dai wani abun makamancinsa. Don haka idan ta ce za ta tsiri hakan, sai take ji kamar za a yi saurin gano ta. Don haka ta ci gaba da zama cikin ɗakin cikin rashin sanin abin yi. Har zuwa lokacin da Ummeen ta ɗauki wayarta ta shiga dannawa. Tun tana jira ta gama har ta fara jin bacci. Kamar wadda aka tsikara, ba ta bari kowa ya ankara da ita ba, ta faɗa ɗakinsu Ummeen. Kai tsaye inda sockets ɗin ɗakin suke ta nufa. Ta tsaya tana kalla na tsawon sakanni, kafin zuwa can ta ƙarasa cikin ɗakin, ta samo wani abu da ya fi kama da katako ta ƙarasa wajen sockets ɗin. Iya ƙarfinta ta saka ta dinga duka, ba ta tsaya ba har sai da ta san ta illata shi. Babu kuma tsoro, ta saka hannunta ta raba wayar da ta tabbatar ita ke saka socket ɗin ya yi amfani. Haka ta bi ɗayan ma ta yi masa, sannan ta mayar da su yadda ba za a fahimci an yi musu wani abu ba. Sai ta dawo parlourn ta ci gaba da zama. Har lokacin Ummee na zaune tana danna wayarta, su ma mazan suna danna tasu. Bayan shuɗewar wasu mintina Farouk ya miƙe.
"Ummee, Abee, sai da safe."
"Har za ka tafi?" Abee ya faɗa yana kallon sa.
"Eh Abee, kamar ina jin bacci ne." Jinjina kai Abee ya yi kafin ya ce
"To Allah Ya ba mu alkairi."
"Ameen." Ya amsa har addu'ar da Ummee ke yi masa.
"Yah Farouk sai da safe." Janan ta faɗa tana kallon sa.
"Sai da safe Aysha." Ya faɗa a nutse bayan ya kalle ta. Daga haka bai sake cewa komai ba ya fice daga ɗakin.
"Aysha ke ba kya jin baccin ne?" Abee ya faɗa yana murmushi. Sai ta girgiza kai sannan ta ce
"A'ah Abee, ai ɗazu na yi bacci ne shi ya sa." Jinjina kai ya yi, cike da gamsuwa da abin da ta ce ɗin kana ya ci gaba da abin da yake yi. Har zuwa lokacin da ya miƙe shi ma don shigewa nasu ɗakin. Ita ma Ummeen miƙewa ta yi tana kallon Janan ta ce
"Shalele je ki kwanta, dare ya yi, kar ki kasa tashi." Sai ta jinjina kai lokaci guda tana miƙewa jiki a matuƙar sanyaye. Kenan duk wannan aikin da ta yi a banza? Sallama ta yi wa iyayen nata, lokacin da suke dab da shige wa ɗakinsu. Sai da suka shiga sannan ta tsaya cike da fata kala-kala cikin zuciyarta. Kai tsaye sockets ɗin parlourn da ta san ana saka charge jikinsu ta nufa su ma duk ta lalata su, a wannan karon har sai da wata waya ta ja ta, amma saboda taurin zuciya da kuma saka kai, toshe bakinta ta yi wasu hawaye na sakkowa kan fuskarta. Ba ta haƙura ba, har sai da ta kammala abin da ta fara sannan hankalinta ya kwanta.
"Janan." Ta ji muryar Ummee na kiran ta. Sai ta yi azamar barin wajen tana amsa kiran Ummeen.
"Jona mini wayar nan a parlour, sockets ɗin nan sun lalace." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke, wadda cikin rashin sani sautinta ya fito fili. Sai ta yi saurin buɗe idanunta da ta lumshe ta kalli Ummee, daidai lokacin da take faɗin
"Lafiya?" Sai ta yi azamar ƙaƙalo murmushi a kan fuskarta sannan ta ce
"Eh fa Ummee." Ba tare da wani tunani ba Ummeen ta miƙa mata wayar. Kai tsaye ta dawo cikin parlourn ta shiga jonawa, irin ba ta san ya lalace ɗin nan ba. Zuwa can ta ce
"Ummee su ma waɗannan fa kamar sun lalace."
"Ikon Allah!" Ummee ta faɗa tana soma takowa cikin parlourn. Da sauri Janan ta katse ta da faɗin
"Ummee ki je ki kwanta, zan je na gwada a ɗakina, Allah Ya sa shi bai lalace ba. Idan ya yi za ki ji ni shiru, idan kuma bai yi ba zan dawo miki da wayar."
"To! Allah Ya sa dai ba wutar da suka kawo jiya ce ta lalata sockets ɗin ba." Ummee ta faɗa.
"Ameen." Janan ta amsa da hakan tana jin zuciyarta na wani irin bugawa. Ita kanta abubuwan da take yi ji take kamar ba ita ba. 'Yaushe ta ƙware wajen zuga ƙarya irin haka?' Ta tambayi kanta, lokacin da ta soma takawa zuwa ɗakinta. Kai tsaye rufe ɗakin ta yi tana sauke ajiyar zuciya wayar rungume a ƙirjinta. Wato daga ƙarshe dai, ta samu damar da za ta yi waya da Adam ɗin kamar yadda ya buƙata. Sai da ta watsa ruwa, ta fito ta shirya cikin doguwar rigar baccinta da hula mai taushi ta haye gado, sannan ta jawo wayar fuskarta ɗauke da maɗaukakin murmushi. Sai da ta kishingiɗa sannan ta danna wa number ɗinsa kira. A lokacin yana zaune cikin ɗakinsa bayan ya sanar wa da Nafisa aiki zai yi don Allah kar ta dame shi. Sai da ta tabbatar babu waya a wajensa sannan ta tafi ɗakinta. Ta yarda da shi a wannan karon, don tun safe ta lura da yadda aiki ya yi masa yawa.
"Barka da wannan lokacin abar ƙaunar Adam." Ya yi maganar bayan ya sauke ajiyar zuciyar jin daɗi. Don da farko har ya fara cire rai a kan ganin kiran Janan ɗin, sai kawai ga shi kiran ya shigo. Murmushi ta yi, tana jin wani sabon al'amari na shiga cikin zuciyarta.
"Ina wuni?" Ta faɗa a hankali kamar mai tsoron kar a ji ta.
Sun shafe fiye da awa ɗaya suna waya. Ba tare da Janan ta tsammata ba, sai ji ta yi ana buga ƙofar ɗakin nata. Cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta buga, ta yi azamar faɗin
"Sai da safe." Ta faɗa muryarta na karkarwa a kuma hankali kamar mai yin raɗa. Ba tare da ta jira abin da zai ce ba ta katse wayar, ta yi saurin dirgowa daga kan gadon tana ƙarasawa ta jona wayar. Kafe ƙofar ta yi ta kallo tana jin yadda har lokacin ake buga ƙofar.
"Waye?" Ta ambata jikinta ban da ɓari babu abin da yake yi, hakazalika muryarta.
"Ni ne Janan." Muryar Yah Farouk ta doki kunnuwanta. Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta ƙarasa jikinta a matuƙar sanyaye ta buɗe, cike da fatan kar ya ramfo ta.
"Janan." Ya ambaci sunanta bayan ta ida buɗe ƙofar.
"Na'am Yah Farouk." Ta amsa ba tare da ta kalle shi ba.
"Na shigo parlour ɗaukar abu, kamar na so in ji magana daga cikin ɗakin nan." Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa. Bugawar da zuciyarta ta yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin runtse idanunta.
"A nan ɗakin Yah Farouk?" Ta yi ƙarfin halin tambaya. Sai ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta haɗiyi wani yawu da ya maƙale mata a maƙogwaro sannan ta ce
"A'ah fa, bacci nake yi, bugun da ka yi ne ya farkar da ni."
"Kin tabbatar?" Ya tambaya har lokacin yana kallon ta, yana kuma nazarin yanayinta. Sai ta jinjina kai kawai, don zuwa lokacin ba ta da ƙwarin gwuiwar cewa wani abu.
"Ohk, asuba ta gari." Ya faɗa, ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 24