yi knocking ƙofar. Muhammad da ke zaune a parlourn ya miƙe da sauri, don yana ji a jikinsa Baban ne. Yadda kuwa ya tsammata Baban yana tsaye.
"Baba." Ya faɗa bayan ya wanzar da murmushi a kan fuskarsa.
"Ka dawo ashe ba ka neme ni ba?" Da sauri ya girgiza kansa ya ce
"A'ah Baba na kira wayarka ta ƙi shiga. Na zo sashenka na tarar da shi a kulle, na buga sosai amma ba a buɗe ba. Na yi tunanin kun yi bacci ne shi ya sa sa na dawo." Jinjina kai Baba ya yi kafin ya ce
"Ina Saleem?"
"Yanzu ya kwanta, ya kwaso gajiya ne."
"To Allah Ya ba mu alkairi." Baba ya yi maganar yana juyawa. Da sauri MuhammadAali ya fito daga cikin ɗakin, ya yi azamar faɗin
"Baba me yake faruwa? Ba ka da lafiya ne?" Da mamaki Baban ya kalli MuhammadAali ya ce
"Lafiya kuma Muhammad? Ina cikin ƙoshin lafiya." Girgiza kansa ya yi bayan jin abin da Baban ya faɗa kana ya ce, lokacin da bugun zuciyarsa ke ƙaruwa. Idan har da akwai abin da ya tsana a duniyar nan, to ya ga mahaifinsa cikin damuwa.
"Baba don Allah kar ka ɓoye mini. Ko dai har yanzu a kan abin da ya faru ne?" Murmushi Baba ya yi, a nutse ya dafa kafaɗar ɗan nasa sannan ya ce
"Babu wannan a zuciyata. Kwantar da hankalinka ka je ka kwanta uhmm?" Shiru kawai MuhammadAali ya yi yana ci gaba da nazarin yanayin Baban. Bai musa ba, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Sai da safe Baba."
"Allah Ya ba mu alkairi Son." Daga haka Baban ya juya ya bar wajen. Bin sa da kallo MuhammadAali ya yi har ya ɓacewa ganinsa, zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane kala-kala. Abu ɗaya ya san zuciyarsa ta fi yin na'am da shi, shi ne abin da ya faru ɗin nan ne har yanzun yake nuƙurƙusar zuciyar Baban ba tare da ya bari an gane ba. To idan kuwa haka ne, ya zama dole ya miƙe tsaye, ya kuma ba da himma a kan binciken da suke yi. Kafin ma ya kai ga shiga ɗakinsu, wayarsa ya fito da ita ya kira Zaki. Tsayin mintina biyar suna magana kafin ya katse ya shige ciki jikinsa a matuƙar sanyaye, sai dai zuciyarsa cike take ta tarin takaici, tana kuma ci gaba da yi masa wani irin zafi duk a dalilin halin da mahaifin nasa ke ciki.
Tare suka fito break ita da Ammeeyn, Ammeeyn da ke jin ta yau kamar ta taka rawa saboda dawowar aminiyar tata. A karo na barkatai ta kalli Janan ɗin da ke ta murmushi lokaci zuwa lokaci.
"Wai Aysha mene ne? Sai fa murmushi kike yi tun muna aji." Wani murmushin ne ya sake wanzuwa a kan fuskarta sannan ta ce
"Ammeey kin taɓa yin soyayya?" Da mamaki Ammeeyn ke kallon ta ta ce
"Soyayya kuma? Rufa ni ki saya ni. Ni wallahi babu ruwana. Kuma ma ai ke ma ɗin kin shiryu kin daina."
"In ji wa? To wallahi na sake afkawa." Janan ta faɗa ba tare da wata damuwa ba. Dakawatawa Ammeey ta yi cike da mamaki take kallon Janan ɗin, ji take kamar wasa kawai take yi. To amma kuma yanayinta sam bai nuna hakan ba. Don haka ta yi saurin riƙo hannun Janan ɗin da ke ci gaba da tafiya ta ce
"Aysha. Me kike cewa ne?" Dakatawar ta yi, kamar yadda Ammeeyn ta buƙata ta ce
"Da gaske nake Amina." Daga nan ta sanar da ita wane ne Adam, da yadda yanzun take ji a kan shi za ta iya yin ko ma mene ne. Shiru ta yi na tsawon sakanni tana jinjina maganganun Janan ɗin.
"Amma kuma idan shi ma ya yi miki abin da Khaleed ya yi fa?" Da sauri Janan ta shiga girgiza kanta.
"Adam ba irin Khaleed ba ne. Adam mutumin kirki ne Amina. Har gida ya zo na faɗa miki, kuma ma ai na ce miki da wayar Ummee muke waya."
"Amma kuma ba da saninta ba ko?"
"Amma kuma ta san da zamansa." Janan ta ba ta amsa kai tsaye. Kafin Ammeey ta kai ga cewa komai Fa'iza ta ƙaraso wajen.
"Aysha tun ɗazu nake son magana da ke kina share ni. Kwana biyu ba kya zuwa, ko damuwa da damuwar da na yi ba ki yi ba, kin dawo kuma kina ta yarfa ni a gaban jama'a."
"Amina mu tafi." Janan ta faɗa bayan ta ɗauke kanta daga kan Fa'izar, ta kuma yi maganar tana jan hannun Ammeey. A wajen suka bar Fa'iza da ta bi su da kallo kawai kamar wata saƙago. Sai da suka yi nisa sannan Ammeey ta dakata, ta ce tana kallon Janan.
"Me ya sa kika daina kula Fa'iza?" Da mamaki Janan ta ɗaga idanunta da ke lulluɓe cikin glass ta ce
"Kina tambaya kamar ba ki sani ba. Yah Farouk ne ai ya ce babu ni babu ita." Murmushin takaici Ammeey ta yi kafin ta ce
"Ai ga shi kin rabu da Fa'iza saboda Yah Farouk ya ce ki rabu da ita. Amma ki kasa daina abin da Yah Farouk, Ummee da Abee ba sa so? Aysha me ya sa?" Ammeey ta ƙare maganar a sanyaye. Shiru kawai Janan ta yi, don ba ta san me kuma za ta cewa Ammeeyn ba. Ta wani ɓangaren a hankali ta ji maganganun Ammeeyn na ƙoƙarin yin tasiri a ƙwaƙwalwarta, sai kuma ta yi azamar yin watsi da ita, daidai lokacin da ƙwalla ta cika narkakkun idanunta. Sai ta yi gaba tana faɗin
"Kar mu sake yin maganar nan." Bin ta da kallo Ammeey ta yi cike da mamaki. Ita ba ta san lokacin da ƙawar tata ta sauya haka ba. Ƙawar tata da idan ta yi ba daidai ba ita ke gyara mata, sai ga shi yau ɗin ta yi ba daidai ba ta nusar da ita amma tana ƙoƙarin nuna mata ba ta ma ɗauki hakan ba. Anya kuwa ba a canja mata Ayshar tata ba?
Tun daga nesa take hangen mutumin da ke knocking ƙofar gidansu. Har zuwa lokacin da ta ƙaraso yana tsaye. Ganin ta ya sanya shi faɗin
"Yawwa, kin ga taimaka ki shiga gidan nan ki ce mai aiki ne." Da "To." ta amsa tana ƙoƙarin shigewa cikin gida, sai kuma kamar wadda ta tuna wani abu sai ta dawo da baya ta ce
"Wai gyaran mene ne?"
"Wanda aka ce ya zo ya gyara sockets ne." Ya ba ta amsar kai tsaye, ba kuma tare da tunanin komai ba. Kawai sai ta ji zuciyarta ta ɗan buga, ta haɗiye yawu da ƙyar sannan ta ce
"Ba nan ba ne." Sai a lokacin sannan ya ɗaga idanunsa ya kalle ta da kyau.
"Kamar yaya?" Sai ta ƙaƙalo wani murmushi kafin ta ce
"Eh ba nan ba ne gaskiya. Ina ga ko maƙotanmu ne, da ma na ji kamar suna neman mai gyaran sockets."
"To babu mamaki." Ya faɗa yana ɗaukar kayan aikinsa ya yi gaba. Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya. Idan dai har mutumin nan ya gyara sockets ɗin gidan ai ita kam ta shiga uku. Kenan hakan na nufin ba za ta ji muryar Adam ba kenan fa? Tun da dai komai nacinta babu yadda za a yi wayar Ummeen ta kwana a ɗakinta babu ƙwaƙƙwaran dalili. Daga haka ta shige cikin gidan tana ƙoƙari wajen ganin bugun zuciyarta ya saitu.
Haka ranar ta kusa ƙarewa, a wajen Janan gani take kamar ranar ta yi tsayi. Shi kansa Adam ɗin ya san idan ya cika kiran Ummee, damar da aka ba shi ma za ta iya yiwuwa a soke ta. Dalili kenan da ya sanya yau ɗin ma ya roƙi alfarmar idan dai har Janan ɗin ta samu dama ta kira shi ya ji muryarta. Ba ta musa masa ba, don ita ma tana masifar son kasancewa da shi ta wayar, yadda yake kashe lokacinsa wajen shanye yarintarta da duk wani abu da za ta yi ba tare da gajiyawa ba, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen saurin sace zuciyarta. Kamar yadda ta faru jiya, sai da Ummee za ta kwanta sannan ta fito daga ɗakinta a karo na barkatai tana sakin tsaki.
"Fisabilillahi wane kalar rashin sanin makamar aiki ne wannan? A ce a kira mutum gyara amma har ga shi dare bai zo ba." Janan da ke zaune a kan kujera tana karatu a littafinta shiru ta yi kamar ba ta ji me Ummeen ke faɗa ba, don lokaci guda ta ji ta fara tsarguwa, kamar kuma idan ba ta yi da gaske ba, Ummeen ka iya gano ta. Tana daga zaune tana ganin Ummeen na sake gwagwgwada caji cikin ɗakin, amma ba sa yi kamar dai jiya. Hakan ne ya sanya ta kai tsaye, ta wuce ɗakin Janan ɗin. Wani irin farinciki ne ya ziyarce ta, fahimtar da ƙyar idan ba caji Ummeen za ta jona ba. Karatun da ta kasa ci gaba kenan. Ta ci gaba da kallon ƙofar ɗakin nata cike da fata kala-kala. Zuwa can kuwa sai ga Ummee ta fito ta kalle ta ta ce
"Wai ni Aysha karatun kike yi ko kuwa tunani?" Haɗiye yawun da ta ji lokaci guda ya maƙale mata a maƙogwaro ta yi kafin ta yi saurin wanzar da murmushi a kan fuskarta ta ce
"E Ummee karatu nake yi fa."
"Ba ki gama ba?" Ta yi tambayar tana karɓar littafin ta shiga dubawa. Sai ta yi azamar miƙewa tana sakin hamma lokaci guda hannunta a kan bakinta ta ce
"A'ah na gama, kuma da ma bacci nake ji."
"To ma sha Allah. Allah Ya taimaka, Ya sa komai ya zauna." Murmushi ta yi kafin ta ce
"Ameen Ummeena."
"Na saka caji a ɗakinki. Zuwa an jima zan zo in cire zan yi amfani da ita." Kawai kuma sai ta ji jikinta ya yi wani mugun sanyi. Da ƙyar ta iya lalubo "To Ummee." Daga haka ta ba wa Ummeen side hug sannan ta wuce ɗakinta jiki a matuƙar sanyaye. Haka nan kawai take jin fargaba tun da Ummeen ta ce mata za ta dawo ta ɗauki wayarta. Kar ta je ta yi wasarere tana waya kuma Ummeen ta zo ta kama ta. Ta daɗe cikin ɗakin, zuwa lokacin kalaman Ammeey sun soma dawo mata cikin ƙwaƙwalwa, ta yadda har ta soma jin kamar ta rabu da Adam ɗin, idan dai har ba kiran da aka amince masa ya yi mata a gida ne ya yi ba. Kar ta sake zama sanadiyyar ɓacin ran iyayenta. Kar ta zama butulu, mara biyayya, wadda ta kasa bin umarnin iyayenta. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci, wata masifaffiyar ƙaunar Adam ɗin ta ji tana yawo a cikin ko'ina na jikinta. Tasirinta, ya sanya cikin ƙanƙanin lokaci ta yi watsi da maganganun Ammeeyn, ta miƙe duk da haka dai jikinta a sanyaye ta ƙarasa wajen wayarta. Kai tsaye number ɗin Adam ɗin ta lalubo ta danna masa kira, sai dai har lokacin akwai wannan fargabar da kuma tunanin maganganun Ammeeyn da suka kasa rabuwa da ƙwaƙwalwarta. Haka ta saka ƙafa ta yi fatali da su ta biye wa abin da zuciyarta ke saƙa mata ta aikata.
Yau ma sun shafe lokaci mai tsayi suna waya, sai dai ba karamar jiyan ba, saboda yadda hankalinta ke can wajen Ummee da ta san a kowane lokaci za ta iya ganin ta cikin ɗakin.
"Sai da safe." Ta faɗa a hankali jikinta a sanyaye, ba don ta gaji da wayar ba. Bai musa mata ba, ya san ƙila ko bacci take ji, idan ya tsayar da ita kuma kamar bai yi mata adalci ba. Don haka ya ce
"To Aysha Allah Ya tashe mu lafiya. Ki yi bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, tare da sanin a kowanne yanayi Adam na tare da ke, zai kuma kasance har abada tare da ke in sha Allah." Lumshe idanunta ta yi tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. Sam ba ta san me za ta ce ba, don haka sai sauke numfashi kawai da ta yi. Daga haka ta katse wayar murmushi na suɓuce mata. Ta kai wajen minti 1 a wajen tana ta murmushi tuna kalaman Adam, waɗanda idan ta yi tunanin ta gwada haɗa su da na Khaleed sai ta ga sam ba su yi kamanceceniya ba. Duk da dai sau da dama takan tuna Khaleed ɗin idan suna hira, wanda cikin lokaci kaɗan take ƙoƙarin watsar da shi. A jikinta take jin ta fi son Adam ɗin a yanzu a kan irin son da ta yi wa Khaleed. Musamman da ya kasance Adam lokaci guda ya sace mata zuciya, ya kuma yi nasara a kanta. Sai kuma kamar wadda aka tsikara ta miƙe ta saka cajin ta koma ta kwanta cike da fatan kar Ummee ta shigo har sai wayar ta ɗauka da yawa.
Wajen ƙarfe 7 ya fito daga ɗakinsa, kai tsaye ɗakin da Inna ta kwana ya durfafa don gaishe da ita. Gabaɗaya idan ka gan shi kuma ka san shi farin sani, to lallai za ka fahimci akwai abin da ke damun sa. Abubuwa biyu ne suka haɗar masa, waɗanda har suka zamo sanadiyyar hana shi bacci. Gabaɗaya bai ma san ta ina zai ɓullo wa al'amarin nan ba. Shin ya amince da ƙudurin Innar, hakan na nufin shi nashi ƙudirin na shekara da shekaru ya tarwatse? To a ajiye wannan ma a gefe, ta yaya zai iya yi wa ɗan nasa bayanin ya auri Hamida? Ya san halin ɗansa, idan har ya ce ya auri Hamida, tabbas zai aure ta, to amma idan ya yi masa haka, anya kuwa ya yi masa adalci? Ta gefe guda kuma ga abin da Maimuna ta yi musu. Ya yi tunanin, ya yi hasashen, ya kasa gano dalilin da ya saka Maimunan ta yi musu haka. Shi dai ya san a gabaɗaya rayuwar da suka gabatar da ita, babu inda ya taba tauye mata haƙƙi, face ma sun rabu ne saboda baƙin halinta da ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen sauya ta amma ta boƙare. Shin me ya sa za ta nemi ta saka musu da wannan? Me ya sa za ta nemi ta ɓata musu suna a idon duniya?
"Abbas." Ya jiyo muryar Innar ba tare da ya tsammata ba. Sai ya juyo da sauri yana kallon ta, tana zaune a kan kujerar parlourn. Sai ya juyo da baya cike da mamakin dai yana faɗin
"A'ah, Inna kin fito ma kenan."
"Wallahi kuwa ka gan ni a nan, ai na ɗan daɗe ma a wajen nan. Na ɗauka zan iske ka lokacin da kake dawowa daga masallaci, ashe na makara." Ba tare da ya ba wa abin da take faɗa ɗin muhimmanci ba ya ƙarasa cikin girmamawa ya ce
"Barka da safiya Inna, fatan an tashi lafiya."
"Barka dai Yayansu. Ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah." Ya faɗa yana gyara zamansa. Fata yake da kuma addu'a Allah Ya sa ta sarara kar ta yi masa wannan maganar. Sai dai tun kafin tunanin nasa ma ya ƙare ya tsinto muryarta lokacin da take faɗin
"Ka san da zafi-zafi ta fi, zaman da ka ga na yi a nan so nake mu ƙare maganarmu kafin kowa ma ya ankara. Saboda haka ya ake ciki? Ya maganar da muka yi jiya?" Shiru Baba ya yi jin wannan tambaya ta Inna. Shi kam me zai ce ne ma kam? Me ya kamata ya faɗa wa Innar? Ya buɗe baki ya ce ya amince ko kuma bai amince ba?
"Ina jin ka." Ta sake katse masa tunanin. Sai a lokacin sannan ya sauke ajiyar zuciya kana ya ce
"Wato Inna, abin da kika faɗa ya yi daidai. Ni ma kuma a iya tunanina na ga auren Muhammad shi ne mafita. To amma wani hanzari ba gudu ba." Ya ƙare maganar yana sake gyara zama.
"Tooooo, ina jin ka."
"Inna wato ba tun yau ba, na riga da na ƙudurcewa kaina haɗa aure tsakanin Ammeey da Muhammad. Wannan abu da shi na tashi tun suna yara har zuwa wannan lokacin da nake dabb da cika shi in sha Allah. Shi ya sa na ce to bari na ba ki haƙuri don Allah."
"Zancen banza kenan! Wacce irin magana ce wannan? Don ka ƙudiri hakan a ranka an riga an ɗaura ne? To ko an ɗaura ma ai shi ɗin mijin mata huɗu ne. Don haka wannan ba uzuri ba ne, ka ajiye ma maganar wata Ammeey a gefe, a soma shirye-shiryen bikin yaron nan da Hamida." Lumshe idanunsa Baba ya yi bayan gama saurarar maganganun Innar.
"Inna ina so ki dubi girman Allah ki bar maganar nan, ki bari in haɗa Muhammad da Ammeey. Ki yi haƙuri Inna." Cikin ƙanƙanin lokaci Inna ta ji ranta ya ɓaci, kamar yaya? Me yaron nan yake ƙoƙarin nuna mata? Kenan bai ɗauke ta a matsayin uwa ba ko me?
"Haɗin aure tsakanin Muhammad da Ammeey shi ke nuna zumuncinmu zai ɗore har gaba. Idan ba ta hanyar auren ba ai murus zumuncin zai rabe. Don haka kawai ka amince a yi auren nan."
"Shi kenan Inna in sha Allah." Baba ya faɗi hakan bayan ya miƙe. Ta fahimci kamar kawai ya faɗi hakan ne don yana so a bar maganar. Don haka duk ƙoƙarin kokawa da take yi da kalaman da ke ta kai-kawo cikin ƙwaƙwalwarta a wannan karon sai ta kasa, don haka kafin ya kai ga tafiya ta ce
"Ka sani, amincewarka na nufin ci gaba da ɓoyuwar ɓoyayyen sirrin nan. Rashin amincewarka ka iya jawo tarwatsewar farincikinka, domin kuwa..."
"Innaa....!!!" Ya faɗa da ƙarfi ba tare da ya sani ba, ban da bugawa babu abin da zuciyarsa ke yi. Sai kuma a lokacin ya tuna da wa yake tare. Don haka ya kalli Innar cikin kwantar da murya ya ce
"Ki yi haƙuri Inna."
"A'ah ci gaba mana Abbas. Ni da ma ai ba mahaifiyarka ba ce. Ashe ba a sama yaron nan ya ɗakko shegiyar zuciya ba. Yau ga shi na ga a inda ya ɗakko ta." Numfashi Baba ya sauke har lokacin bugun zuciyarsa bai saitu ba.
"Ki yi haƙuri Inna, ba na nufin na ɓata miki rai." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya fice daga ɗakin. Bin sa ta yi da kallo har ya fice daga ɗakin sannan ta dawo da dubanta cikin ɗakin tana taɓe baki.
"Amincewa da auren Hamida ya zama dole." Ta faɗa tana miƙewa ta wuce ɗakin da aka sauke su.
"Muhammad." Saleem ya faɗa yana kallon MuhammadAali.
"Uhmm." Ya amsa idanunsa a kan wayarsa.
"Malam ka ajiye wayar nan ka kalle ni magana za mu yi mai muhimmanci." Jin yadda ya yi maganar ya sanya shi ɗaga idanunsa ya kalle shi. Sai ya kashe wayar tasa ya ajiye ta sannan ya sake kallon shi.
"Uhmm?" Numfashi Saleem ya sauke kafin ya ce
"Maganar gaskiya na kasa jurewa. Tabbas ina son Ammeey, kuma auren ta nake son yi. Ina so na je mu yi magana da Baba ko Abba. To amma ya fi kyautuwa in nemi shawararka. Don Allah kar ka ɗauki abun a wasa, da gasken gaske nake son Ammeey har cikin ɓargona." Kallon sa kawai Muhammad yake yi, sai yake jin abun wani banbarakwai, wai har cikin ɓargo. 'Hakan mai yiwuwa ne kuwa?' Ya tambayi kansa ba don yana neman amsar hakan ba.
"Ka yi shiru." Saleem ya faɗa yana kallon MuhammadAali. Kafaɗarsa ya ɗaga lokaci guda ya ɗan taɓe bakinsa kafin ya ce
"Na ji, na kuma yarda. Ka kwantar da hankalinka, zan je na samu Baba na yi masa magana in sha Allah. Kar ka ɗaga hankalinka tun da kana da ni." Ya ƙare maganar cike da shaƙiyanci kamar ba shi ba. Hannu Saleem ya miƙa wa Muhammad ɗin yana faɗin
"Ni na san ba ni da damuwa, shi ya sa na neme ka." Ya ƙare yana murmushi. Daidai lokacin da wayar MuhammadAali ta soma ruri. Ganin mai kiran nasa ya sanya shi saurin ɗagawa yana kara wa a kunnensa.
"Zaki." Ya ambata duk wani hankalinsa na koma wa kan wayar.
"Yallaɓai kamar yadda muka yi komai tare da kai, yanzun ma dai haka abun yake, mun sake yin iya bakin ƙoƙarinmu wajen gano inda matar nan take amma abun ya citira. Ina ganin tserewa ta yi saboda sanin hakan na iya faruwa. Wannan dalilin ne ya sanya muka binciko ita matar da take ɗora labarin a gidan radio. Na tabbatar idan dai har muka yi ramm da ita, to duk inda matar nan take za mu samu. Don ita kanta mai gabatar da shirin ina zargin tana da hannu a ƙoƙarin ɓata wa Faaza suna. Mun nemo wace ce ita, sunanta, hotonta, address na gidanta, da ma komai da ya shafe ta wanda zai yi mana amfani."
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 23
Lumshe idanunsa MuhammadAali ya yi na tsawon sakanni biyar kafin ya buɗe, har lokacin wayar na kare a kunnensa.
"Kana ina?" Ya tambaya kai tsaye. Sanar da shi inda yake Zaki ya yi, ba tare da ya ce komai ba ya miƙe.
"A'ah.. ina kuma za ka je?" Saleem ya tambaya cike da mamaki yana kallon sa. Iska ya fesar daga bakinsa, kamar wanda ba shi da niyyar cewa komai, sai kuma ya ce
"Wani abu mai muhimmanci zai fitar da ni."
"Ko zan iya sanin mene ne?" Ba don Saleem ɗin ba ne, da babu abin da zai saka ya ci gaba da ɓata lokacinsa. Amma kasancewar ba zai iya watsa wa Saleem ɗin ƙasa a ido ba, ko kuma ya dizga shi ya sanya ya ce
"Idan na dawo zan yi maka bayanin komai." Daga haka ya yi gaba. Bin sa da kallo Saleem ya yi cike da mamaki, fata yake Allah Ya sa lafiya. Bai kuma nemi ya raka shi ba, don da yana da buƙatar rakiyar shi da kansa zai neme shi.
Sanye cikin zanin atamfa da kuma wata riga mara hannu, irin mara nauyin nan take. Zaune a kan stool ɗin gaban mudubi tana gyara fuskarta da kayan kwalliyar da Umma ta kawo mata. Ta shafe fiye da mintina ashirin tana ƙyalƙyale fuskar, fuskar kuwa ta yi rabajau da hoda da uwar jagira.
"Wai ni kam Hamida har yanzu ba ki gama ba ne?" Inna ta faɗa tana kallon yadda take ci gaba da zizare a kan laɓɓanta da jagirar hannunta. Sai da ta yi fari sannan ta ce
"E Inna, bar ni na zana bati." Ta yi maganar tana ci gaba da abin da take yi. Ba ta ce komai ba Innar sai miƙewa da ta yi ta shige banɗaki. Bayan wajen mintina biyar ta fito. Ta yi tsammanin za ta ga Hamida a cikin ɗakin amma sai ba ta gan ta ba. Ba ta ga alamar ta fita ba, don daga mayafinta har takalmin babu abin da ta ɗauka. 'To kenan ina ta je?' Ta tambayi kanta tana sake duba cikin ɗakin. Ficewa daga ɗakin Inna ta yi, don ta tabbatar da wuya idan ba parlour ta fita ba. Sai dai ga mamakinta, cikin parlourn ma ba ta nan.
"Wannan gantalalliyar yarinyar. Gidan uwar wa kuma ta tafi?" Ta yi maganar a fili tana ci gaba da dubawa. Kai tsaye ficewa ta yi daga ɗakin zuwa harabar gidan. Tun daga nesa take iya jiyo muryar Hamidar tana sheƙa uwar dariya. Sai ta ci gaba da tafiya har zuwa inda take. Tana zaune a kan kujerar da mazan masu aikin gidan ke zama idan suna hutawa. Ta yi nashe-nashe a tsakiya, sanye cikin zanin nan dai wanda ta ɗan yaye shi zuwa sama saboda ta samu ta zauna da kyau, da kuma farar riga mara hannun. Rigar da rashin kaurinta da kuma ksancewarta fara ya saka har shatar halittun jikinta ana iya gani.
"Wallahi ni da kin ƙarasa ba mu labarin da kika fara na farko. Ai gwara a kai ƙarshe kafin a fara sabo." Ɗaya daga cikin waɗanda ke zaunen ya faɗa yana dariya cikin kallon Hamidar.
"To ai kai ka tsaya ka ji wannan ya fi daɗi." Hamidar ta faɗa tana sake gyara zamanta. Daidai lokacin da muryar Inna ta doki dodon kunnenta.
"Hamida." Ta kira sunan nata cikin ɗaga murya. Da sauri ta ɗaga ido ta kalli Innar ba tare da ta tsammaci ganin ta ba.
"Tashi don ubanki ki wuce mu tafi." Ta yi maganar tana nuni da abin da ta faɗa. Zunkuɗo bakinta da ya ji uwar jagira da janbaki ta yi tana magana ƙasa-ƙasa.
"Gaskiya ni dai Inna ki bar ni wallahi."
"Za ki tashi ko sai na saɓa miki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 24