Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har iyayenta ta bijirewa saboda shi? Me ya sa ma kuma ya shirya rabuwa da ita ta hanyar da Khaleed ya rabu da ita! Shin bai san yadda hakan zai yi mata zafi ba ne? Bai san yadda hakan zai tuna mata da abin da ya faru a baya ba? Me ya sa Adam ɗin zai yi haka. Kuka take yi kamar ranta zai fita, a haka ta silale zuwa ƙasa ta ci gaba da rera kukanta cikin rashin sanin abin yi. Domin kuwa ko kusa ko alama ƙwaƙwalwarta ta ma kasa tunanin komai. Ta rasa abin da ya kamata ta yi tunani, ballantana ta san abin da ya dace da rayuwarta. A hankali Farouk ya ƙarasa zuwa inda take, ya sanya hannunsa ya riƙo kafaɗarta ta miƙe tsaye, har lokacin kukan take yi, kukan da ke sake sosa zuciyar Farouk ainun. A niyyarsa ya ajiye ta a kan gado su samu su yi magana. Sai dai a yanayin da take ciki tana buƙatar kafaɗar da za ta ɗora kanta ta yi kuka ko za ta samu sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta. Don haka ba tare da ya tsammata ba, sai ji ya yi ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani sabon kukan. Ba don a wannan yanayin take ciki ba da tabbas sai ya hana ta. Sai dai jin yadda take kuka kamar ranta zai fita, jikinta kuma na wani irin karkarwa ya sanya shi barin ta. Ta kai wajen mintina biyu tana kukan, shi dai yana tsaye ya yi ƙwam cikin rashin abin yi. Ba zai iya kwatanta halin da ta tsinci kanta a ciki ba, sai dai ya san dole tana cikin wani yanayi da ba zai kwatantu ba. Don haka kukan zai rage mata kaso mai yawa daga cikin damuwarta. Don haka ya bar ta ta yi kukanta son ranta, zuwa can dai da ya ga ba mai ƙarewa ba ne, ya sanya ya buɗe bakinsa a nutse ya ce "Ya isa haka Aysha." Ba ta fasa ba, sai dai ta rage sautin kukan. Hakan ne ya sanya Farouk ya yi amfani da hannunsa wajen jan ta zuwa kan gadon, ya janye ta daga jikinsa ya zaunar da ita a kan gadon, sannan ya nemi waje ya zauna yana kallon ta. "Janan." Ya kira sunan ta a hankali. Ba ta iya amsawa ba, sai ci gaba da kukan da yanzun ta rage sautin sa sosai. Zuwa can dai don kanta da ta gaji da kukan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Idanun nan nata sun sake yin jajir, da ma ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo? Sai da ya tabbatar ta daina kukan sannan ya ce "Ya isa haka Janan. Ki kwantar da hankalinki, ki yi shiru. Ina so ki fawwala Allah komai. Shin kin manta wasu abubuwan muna rasa su ne idan suka kasance ba alkairi ba ne a gare mu? Na san kina son Adam, to ga abin da ya faru, maimakon kukan, ba sai ki yi addu'a Allah Ya sa haka ne mafi alkairi ba? Na san akwai zafi, ni kaina kuma abin ya yi mini zafi, shi ya sa ma ban hana ki kuka ba. To amma yana ƙoƙarin ya yi yawa, kar ki ja wa kanki matsala kuma. Don Adam ya rabu da ke ba shi ke nuna rayuwarki ta tsaya ba. Aysha ke yarinya ce, kada a kan soyayya ki zo ki illata zuciyarki. Daga Khaleed har Adam, babu wanda ya dace da ke, kawai ƙuruciya ce da ƙaddara suka kai ki faɗa wa soyayya da mutanen da ko kaɗan ba su san darajarki ba. Ke ɗin mai tsada ce Janan, irin macen da kowanne namiji zai so kasancewar ki a matsayin matarsa. Hukuncin da iyayenmu suka yanke wa rayuwarki sun yanke ne don suna son ki, don suna so ki zama wata, abar alfahari ga kowa. Babban dalili ne ya sanya su aikata hakan, to amma Allah Ya ƙaddara sai kin haɗu da waɗannan mazan guda biyu. To amma da yake su ɗin duk babu mijinki cikinsu, ai ga shi kun rabu ko? To ki saka a ranki da ma can Adam ba mijinki ba ne. Ki manta da shi ki ci gaba da rayuwarki, sai dai abu guda ɗaya, kar ki sake ki sake sakin jiki har ki yi kane-kane cikin soyayya da wanda bai gama sanin darajar ki ba. Wanda rabuwa da ke a wajensa ba wani abu ba ne. Janan sauƙin zuciyarki har ya so ya yi yawa. Dududu yaushe kika rabu da Khaleed, har kika faɗa ƙaunar Adam, ga shi shi ma kin rabu da shi? Ki yi wa kanki faɗa, ta ɓangare guda kuma ki daina wasa da addu'a. Don da kina yi, tun farko ma babu lallai ki ci gaba da kasancewa da su, ba tare da kin ji a zuciyarki ba su kwanta miki ba. Ki yi haƙuri ki daina kuka uhmm?" Ya ƙare maganar yana kallon ta. Da sauri-sauri take sauke numfashinta saboda kukan da ta sha. Da ƙyar ta iya jinjina kanta ba tare da ta san abin da ya kamata ta furta ba. Duk kuwa da tana da abubuwan faɗa da yawa. To amma bakinta ya yi mata nauyi, ta ma rasa ina za ta fara? Farouk ya daɗe cikin ɗakin, har dai da ya tabbatar hankalin Janan ɗin ya ɗan kwanta sannan ya miƙe. "Na san Ummee na dab da dawowa, Abee kuma babu lallai ya dawo gidan a yau. Saboda haka ina so ki kwanta ki samu ki yi bacci, zuwa safiya zan sanar da su duk abin da ya faru." "Tam." A karo na farko kenan ta buɗe baki da ƙyar ta faɗa da muryarta da ta dishashe. Cike da tausayi ya ɗaga idanunsa ya kalli ƙanwar tasa, kafin ba tare da ya sake cewa komai ba ya fice daga ɗakin, lokaci guda yana kullo mata ƙofar ɗakin. Kafin ya kai ga ficewa daga parlourn kiran Abee ya shigo wayarsa. Ya dakata yana ɗagawa. Daga can ɓangaren Abee ya ce "Zan dawo gida in sha Allah. Tafiyar ba za ta yiwu ba dole sai dai in ɗaga." Shi sai a lokacin ma sannan ya tuna abin da ya fitar da Abee ɗin. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa sannan ya ce "Abee da ma akwai wani abu ma da ya faru. Amma in sha Allah idan ka dawo sai na sanar da kai." "To Allah Ya sa lafiya." "In sha Allah." Shi ne abin da ya faɗa kawai. Daga haka suka yi sallama da Abee ɗin ya katse wayar. Jikinsa a matuƙar sanyaye ya fice daga ɗakin. A ɓangaren Janan, ranar ko daidai da minti ɗaya ba ta samu ta rintsa ba. Kuka kam har sai da hawaye suka gaji don kansu suka daina sauka. Tun tana takurawa zuciyarta wajen tunanin dalilin da ya sanya Adam ɗin ya rabu da ita, har ta gaji ta haƙura. Ba ta tunanin zuciyarta za ta iya jure rashin Adam ɗin. Shin me ya sa ya zaɓi ya yaudare ta? Me ya sa ya zaɓi hakan? Shi ɗin da ya zo mata a lokacin da ta fi buƙatarsa? Yanzu kuma shi ne zai tafi ya bar ta bayan ta gama yin kane-kane cikin masifaffiyar ƙaunar sa? Ashe da ma haka maza suke? Ashe da ma haka soyayyar take? Me ya sa Fa'iza ta dinga kwaɗaita mata ita? Ashe babu komai cikinta sai ɓacin rai da takaici? A yadda Fa'iza ta kwaɗaita mata ita, ta ɗauka za ta same ta ne fiye da hakan. Sai ga shi ita babu abin da ta tsinta a cikinta sai wani dunƙulallen ciwo da ba ta tunanin zai taɓa warkewa a cikin zuciyarta. A hankali ta ji ana taɓa ƙofar ɗakin nata, ba ta damu da hakan ba, don ta san ƙila Ummee ce. Don ta shigo ɗazu ta same ta kamar tana bacci. Sai dai ba baccin take yi ba, kawai ta yi haka ne don bin umarnin Yah Farouk. Abin da ya daɗe bai faru ba, wanda ya saka har ta saki jiki tana ganin kamar hakan ya daina faruwa ne. Wato shigo mata ɗaki da ake yi da niyyar keta mata haddi. A wannan karon ma, kai tsaye kanta aka nufa. Sai dai saɓanin wancan karon, wannan karon da ƙarfi aka shiga ƙoƙarin zare kayan da ke jikinta. Cikin azama ta miƙe tana fasa wani irin ihu cikin tsananin tashin hankali. Jikinta na sake yin wata mahaukaciyar karkarwa. Wadda ta haɗu da yanayin jikinta da babu ƙwari tun kukan da ta yi ɗazu, da kuma tsoron da take ji na yanzun. Hannunsa ya yi amfani da shi wajen toshe mata bakinta. Cikin muryarsa da ta fi kama da wanda ya yi maye ya shiga faɗin "Dare ɗaya, ki bar ni na cika burina a kanki na tsayin shekaru. Ki taimaka mini, idan ba so kike na zauce ba." Ya yi maganar shi kansa gangar jikinsa wani irin karkarwa take yi. Sam ba ta ma san me yake cewa ba. Don gabaɗaya hankalinta ya tafi ta yadda za ta ƙwaci kanta ne. A karo na biyu ta sake saka duk wani ƙarfinta ta sake sakin wata ƙarar, cike da fatan iyayenta su jiyo ta su kawo mata ɗauki. Kamar daga sama, Ummee ta jiyo wani sauti daga cikin parlourn da ta fito. Wanda haka nan kawai ita dai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya, wanda ta rasa gane dalilin hakan. Hakan ne ya sanya ta fitowa parlourn don ta samu ta sha ruwa, ta kuma duba ɗiyarta. Sai ga shi ta ji sautin da ya fi kama da ƙara. Har ba ta san lokacin da kofin hannunta ya faɗi ba. Ta yi saurin ƙarasawa ɗakin Janan ɗin ta shiga murɗa hannun ƙofar cikin tsananin tashin hankali, tana jin zuciyarta na wani irin bugawa. Sai dai cikin rashin sa'a, ƙofar a kulle take da mukulli. Wani irin tashin hankali da ya sake ziyartar ta, shi ne ya janyo silar rikicewar ta. Cikin rashin sanin abin yi ta yi hanyar ɗakinta da niyyar taso Abee da bai daɗe da samun bacci ba. Sai kuma kafin ta ƙarasa hankalinta ya dawo jikinta, inda suka saba ajiye spare keys ta nufa ta ɗauki duka keys ɗin ta koma ɗakin Janan ɗin. I zuwa wannan lokacin tana iya jiyo sautin muryar Janan ɗin da ke ci gaba da kiran sunan "Ummee! Abee! Yah Farouk!." Duka cikin dashashshiyar muryarta da ita kanta ba ta da tabbacin ko za a samu wanda zai ji ta. Wani irin karkarwa jikin Ummee ke yi, lokacin da take gwada keys ɗin jikin ƙofar. Yadda take a rikice ya saka ta ɗauki lokaci tana buɗe ƙofar. Zuwa lokacin ƙarin faɗuwar gabar da take ji ya ƙaru, don ba ta san takamaimai me yake faruwa da ɗiyar tata ba. Daga ƙarshe dai, ƙofar ta buɗu, ta yi azamar danna kanta cikin ɗakin cikin tsananin tashin hankali. Duhu ne ya mamaye mata idanu, don haka ba ta iya ganin abin da ke faruwa cikin ɗakin, sai muryar Janan ɗin da ke faɗin "Don girman Allah ka ƙyale ni..." Abin da take faɗa kenan, don ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen kiran ɗaya daga cikin mutanen gidan, amma babu alamar wani ya ji ta. Tun tana da ƙwarin ture mutumin ba tare da ya samu damar yi mata wani abu ba, har ƙarfin nata ya ƙare. Sai dai duk da haka ba ta daina yunƙurin ƙwatar kanta ba. Amma yadda mutumun yake tamkar mayunwacin zakin da ya fito farautar abin da zai ci, ya saka har ya yi nasarar kai ta kan gadon. Kamar kuma yadda take kuka, haka shi ma yake kuka yana roƙar ta ta taimaka wa rayuwarsa ta bari ya kasance da ita kafin ya kai ga zaucewa. Ita kuwa saboda tsananin tashin hankali, ko kaɗan ba ta sanin abin da yake faɗa. Don yau ɗin ta tabbatar da abin da yake faruwa gaskiya ne. Kuma idan dai har ta kuɓuta a yau ɗin, ko za a kashe ta ba za ta sake kwana cikin ɗakin ba. Daga ita har shi, babu wanda ya san da shigowar Ummee, sai kawai ganin haske suka yi ya mamaye ɗakin. Cikin tsananin farinciki Janan ta buɗe idanunta tarr a cikin ɗakin don tabbatar da abin da idanunta ke nuna mata. Kansa na kan wuyanta da ƙamshin da ke tashi daga jikinta ke sake kiɗima shi. Ya rasa inda zai tsoma kansa ya ji daɗi. Ya yin da lokaci guda hannunsa ke kan zip ɗin rigarta, yana ƙoƙarin yage shi gabaɗaya ma don ya samu damar aikata abin da zuciyarsa ke ci gaba da ingiza shi ya aikata. Sai dai abin da bai taɓa tsammata ba, shi ne hasken da bayyana cikin ɗakin. Kamar wanda aka danna wa remote, cakk ya tsaya da abin da yake ƙoƙarin aikatawa, duk kuwa da har lokacin shi kaɗai ya san yanayin da yake jin kansa a ciki. Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya runtse idanunsa cikin rashin sanin abin yi. Tabbas yau ɗin rana ce mafi muni a gare shi. Bai kai ga ƙarasa tunanin ba, Janan da ke a ƙasa, ta yi azamar ture shi ta miƙe a guje cikin tsananin tashin hankali ta faɗa jikin Ummee tana fashewa da wani irin sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Shi kam kamar wani saƙago sai ya kifa kansa a kan gadon cikin rashin sanin abin yi, ban da bugawa babu abin da ƙirjinsa ke yi. Rungume ta Ummee ta yi ita ma tana fashewa da kukan. Sai dai gabaɗaya hankalinta na kan mutumin da kansa ke kife a kan gadon. Yadda zuciyarta ta buga, shi ne dalilin da ya sanya ta ɗan takawa zuwa cikin ɗakin. Sai da ta je tsakiyar ɗakin sannan ta kafe shi da idanunta zuciyarta na wani irin harbawa. Cike da ƙarfin hali, tana kuma kokawa da abin da zuciyarta ke kitsa mata ta ce "Wane ne kai?" Ta faɗa muryarta har wani karkarwa take yi. Girgiza kansa ya shiga yi har lokacin ya kasa ɗaga idanunsa ballantana ya kalle su. To da wanne idon zai kalle su? Ta yaya zai yi musu bayani? A halin yanzu haka shi kaɗai ya san abin da yake ji. Ji yake kamar ana sake rura masa wuta ne na son kasancewa da Janan. To amma me ya kamata ya yi? Shin ya ɗaga idanu ya kalle su su ga wane ne shi, ko kuwa ya ci gaba da zama a nan ɗin. To har tsayin wanne lokaci zai zauna a nan ɗin? Ai da ma an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. "Ka ɗago idanunka ka kalle ni." Ummee ta sake faɗa haka nan kawai cike da tsoro. A hankali ya shiga ɗaga fuskarsa, kafin ya sauke ta a kan Ummee, idanunsa cike shaɓe-shaɓe da hawaye kamar wani ƙaramin yaro. Cakk numfashin Ummee ya tsaya lokacin da idanunta suka sauka a kansa, wani irin karkarwa jikinta ya shiga yi tafarar ɗaya, kamar wadda zazzaɓi ya yi mata kamun kuku. Da sauri ta runtse idanunta tana fatan Allah Ya farkar da ita daga wannan mummunan mafarkin da take yi. Ta tabbatar mafarki ne wannan ɗin take yi, don ta san hakan ba zai taɓa faruwa ba. Janan fa? A'ah hakan ba zai taɓa faruwa ba. Ta raya hakan cikin zuciyarta daidai lokacin da ta sake buɗe idanunta a kansa, cike da fatan ta ga wani ne zaune a wajen ba shi ba. Ita Janan ma sai a lokacin sannan ta tashi daga jikin Ummee, ta sauke jajayen idanunta a kan inda Ummeen ke kalla. To yaushe ya shigo ɗakin? Ko kuwa me idanunta ke ƙoƙarin nuna mata? Cikin wani irin tashin hankalin da tun da uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba, ta zare glass ɗin idanunta ta goge shi sannan ta sake mayarwa cike da fatan ta ga idanunta ke yi mata gizo. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka sauka a kansa, daidai lokacin da yake furta "Ku tsaya.. ina fatan ku tsaya ku saurare ni don girman Allah." Ai sai ta ji jinta da ganinta gabaɗaya sun ɗauke na wucin-gadi. Wani dumm ta ji kunnuwanta sun yi mata tun bayan da suka ji muryar tasa, wadda ta sake tabbatar mata da wanda take gani a zaune. Idanunta kuwa da ma ta san ƙiris suke jira su makance, to tabbas yau ɗin burinsu ya cika sun makance don kansu. Ita kamar ma gwara da hakan ya faru, don ba ta san da wanne ido za ta ci gaba da kallon wannan mummunan al-amarin ba. Shin da gaske ne ko kuwa dai wani mummunan mafarki ne take yi? Kenan da gaske ne da Yah Farouk ke ce mata mafarki ne take yi? Lallai yau ta yarda ta kuma tabbatar da cewa mafarkin ne take yi. Idan dai har ba haka ba, ta yaya haka za ta faru? Hannunta Ummee ta yi amfani da shi wajen dakatar da shi lokacin da yake ƙoƙarin isowa gare ta. Idanunta tuni hawaye sun cika su taff, sai dai sun kasa sauka ƙasa. Har zuwa wannan lokacin ta kasa tabbatarwa, kawai dai gani take yi kamar dai mafarkin ne. Da hannunta ta ci gaba da nuna shi tana ci gaba da kallon sa cikin tsananin mamaki, kafin da ƙyar ta iya buɗe bakinta don ta samu damar ambatar wani abu. "Ab... Ab...." Shi ne kawai abin da take iya furtawa, kamar wadda ake riƙewa sai ta kasa ƙarasawa. I zuwa lokacin hankalin Janan ya ida tashi, ashe ba ita ɗaya ta gan shi ba. Shin ina za ta saka zuciyarta ta ji daɗi? Wani irin sarawa da kanta ya yi, shi ne ya saka ta kai hannunta ta dafe shi, lokaci guda ta tafi da wani irin ƙarfi. Sai ji kake yifff! Ta faɗi a wajen sumammiya. Alhamdulillah! A nan na kawo ƙarshen littafin BIYU BABU Book 1. Mai son ci gaba da karanta BIYU BABU Book 2 har ma da Book 3, zai tura ₦500 ne ta... 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay Shaidar biya ta 08124818273. Ko kuma kai tsaye a tuntuɓe ni ta 08124818273. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 24 of 24