Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ɓata ransa, wai irin don ya fahimci da gaske yake ba wasa ba, sannan ya ce "Wasa kuma? Da ma muna irin wannan wasan ne da kai? Idan ni na san wasa ai kai ba ka san shi ba, don haka ma ba zan fara yi maka shi ba." Tsaki MuhammadAali ya ja kana ya taɓe baki "Wannan abar? Ita kake so? Kana da abin dariya." Ya ƙare maganar yana koma wa kan wayarsa ya ci gaba da dannawa. "Ko ma dai mene ne sai dai ka faɗa, amma ni dai na ga waje. Ammeey ta tafi da ni gaskiya a wannan karon. Ji yadda ta ƙara kyau, ta zama 'yan mata." Daidai wannan lokacin wayar Al-ameen da ke ajje a gefe ta shiga ruri. Babu wanda ya damu da ya ɗaga, don sun san Al-ameen ɗin na daf da dawowa. Aikuwa ko minti 1 ba a ƙara ba sai ga shi ya zo. "Afuwan guys." Ya yi maganar yana tayar da motarsa. Sun yi tafiyar wajen mintina biyu sannan wayarsa ta sake soma ruri. Gudu yake sosai, don ya riga ya saba da wannan gudun, sai dai idan wani daga cikin iyayensa ya ɗakko sannan ne yake rage gudun. Bai duba mai kiran ba, kai tsaye ya yi amfani da hannunsa wajen ɗaga kiran. "Hello Babe." Aka faɗa daga cikin wayar. Hannunsa ya yi amfani da shi a yanzu ma wajen katse kiran ba tare da kowa ya lura ba. Ya mai da wayar inda ya ɗakko ta ya ci gaba da driving ɗin. Bayan kamar shuɗewar mintina uku ƙarar shigowar gajeren saƙo ya shigo cikin wayar. Bai ji lokacin ba, saboda hankalinsa da yake kan driving ɗin da yake. Daidai lokacin da idanun Muhammad suka kai kan wayar, har yana shirin ɗauke kansa, sai kuma kamar wanda aka fizge shi, sai ya sake dawo da dubansa kan wayar da ƙaramin saƙon ya bayyana a kan allon wayar. "Babe please ina ta jiran ka ka dawo. Na kasa manta daren jiya. And i just can't wait mu sake kasancewa tare." Ya karanta message ɗin a kan laɓɓansa. Kafin ya kai ga ida fassara abin da saƙon yake nufi, Al-ameen ya juyo ya kalle shi. Shi ma shi ɗin yake kalla, sai dai a zahirin gaskiya bai riga ya ma fahimci abin da saƙon ke nufi ba. Ganin irin kallon da Muhammad ɗin ke yi masa ne ya sanya shi ci gaba da kallon sa cike da mamaki, sai kuma ya saukar da idanunsa a kan wayarsa da har lokacin haskenta bai ɗauke ba. Ai tun bai kai ga karanta saƙon ba ya ji zuciyarsa ta wani irin bugawa. Kawai sai ya ja wani mahaukacin burki yana gangarawa gefen titi. Hakan ya ba wa Saleem damar sauka daga cikin motar don dama so yake ya yi waya, kuma network ya hana shi. Hannunsa ya saka ya ɗauki wayar, ya shiga saƙon da tun ganin wadda ta turo shi ya san da wuya idan asirinsa bai tonu ba. Ilai kuwa, sai ya ga abin da saƙon ya ƙunsa. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Bro kar ka yi tunanin haka nake. Wallahi sharrin shaiɗan ne, ban taɓa aikata wani abu makamancin hakan ba sai jiya. Jiyan ma tsautsayi ne da shaiɗan da ya saka na kasa riƙe kaina. Ina roƙon ka, wannan ya zama sirri a tsakanin mu." Runtse idanunsa MuhammadAali ya yi yana jin yadda bugun zuciyarsa ke fita da wani irin mahaukacin bugu. Bai zata ba, bai taɓa tsammani ba. Kai idan da ace wani ne ya ce masa hakan ta faru ba zai taɓa yarda ba, zai ƙaryata ne don ya san halin ɗan'uwansa, ɗan'uwan nasa da ko taba ba ya sha ballantana har ya yi tunanin zai iya aikata zina. Sai ga shi da kansa ba tare da ya tambaye shi ba yana sanar da shi. Ajiyar zuciya Muhammad ya sauke, wato a wannan lokacin babu wanda ya faɗo masa sai Baba. Tun suna yara Baba yake kula da tarbiyyarsu. Ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya inganta rayuwarsu ta hanyar ba su ilimin boko da na addini. Ya kula da su da kuɗinsa da jikinsa, a kodayaushe ba ya ƙosawa da duk wata buƙatarsu. A kullum kuma yana yi wa 'ya'yan nasa addu'a a kan Allah Ya shirya masa su bisa tafarki madaidaici. Ya kasance mai saka idanu a kan 'ya'yan nasa. To amma kowanne bawa da irin ƙaddarar da Allah Yake jarabtar da ita. Yau ɗaya Muhammad ya ji nadamar kasancewarsa yana shan kayan da za su kawar masa da hankali ko su shafe masa wata damuwa da yake ciki. Shin me ya sa suka zama butulu masu butulcewa irin ɗimbin alfarmar da Ubangiji ya yi musu? Me ya sa suka zama butulu ta hanyar butulcewa kula da tarin gudummawar da Faaza ya taka a rayuwarsu? Me ya sa suke nema su ɓata masa suna? Bai taɓa tunanin haka daga wajen Al-ameen ɗin ba. Don kowa ya san shi mutum ne shi mai hankali babu laifi. Ba shi da matsala ko kaɗan, don hatta Baba ba ya ƙorafi a kansa. Sai dai ga shi yau ɗin saƙo ɗaya ya fallasa wane ne Al-ameen. Saƙo ɗaya ya saka ya ji ya tsani kansa da halayensa. Tausayin Baba ne ya cika masa zuciya fall, tabbas ba su yi wa Baba adalci ba. Ba su saka masa irin kulawar da ya ba su ba. Ba su saka masa irin ƙoƙarin da ya yi wajen ganin ya kula da tarbiyyarsu ba. Idan haka ne shi ɗin me yake jira da ba zai share wa Baban hawayen zucin da ya tabbatar da yana yinsa ba? Me ya sa ba zai kasance yadda Baban yake so ya zama ba, duk irin tsananin ƙaunar sa da yake yi? Me ya sa ba zai rungumi duk wani abu da Baban yake so ba, ya kuma watsar da duk wani abu da ba ya so ba, kamar yadda ya ƙarar da rayuwarsa wajen kula da su ba, ya shafe tsayin rayuwarsa wajen nuna masa ƙauna mara algus, ƙaunar da za a iya cewa ta fi ƙarfin a kira ta da ƙaunar uba kawai, sai dai wani zunzurutun ƙauna da Allah ne kaɗai ke dasa ta a cikin zuciyar bawa. Lokacin da MuhammadAali ya isa kasuwa, gabaɗaya jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Yana sanye cikin ƙananan kaya kamar koyaushe, hannayensa duka biyun zube a cikin aljihunsa. In dai ka yi masa farin sani, to tabbas za ka fahimci akwai abin da ke damun sa. Sai dai idan ba ka san shi ba ne sosai, za ka iya cewa da ma shi kullum a haka yake. A nutse ya ƙarasa ya zauna a kusa da kujerar da Baba ke zaune bayan ya gaisa da Abban Al-ameen da kuma Daddyn Ammeey, sai kuma wasu mutane biyu da ke zaune a wajen. Tun da ya shigo wajen Baba ke lura da yanayinsa. Ya riga ya san halin ɗansa, shi ne mutum na farko da yake fara fahimta idan yana cikin matsala ko kuma wani abu na damun sa. Musamman da ya kasance ba ya iya ɓoye masa komai. Ko mene ne ya faru in dai matsalar ta shafe shi, yana sanar da mahaifin nasa ne domin su haɗu su yi maganin matsalar. Takardun da ke kan kujerar gabansu, Baba ya ɗauka ya miƙa wa mutane biyun da ke zaune kusa da Daddy ya ce "Kamar yadda na faɗa muku. Ina so ku duba takardar nan a nutse, don so nake ku tabbatar da ban yanke hukunci ba sai da na yi bincike. Don haka ina mai baƙincikin sanar da ku na sallame ku. A cikin tsayin shekarun da muka yi da ku idan har na yi muku wani abu, ina neman ku yafe mini. Ni dai na yafe muku, amma tun da na gano abin da ke faruwa na ji ba zan iya ci gaba da aiki da ku ba, don ban taɓa tunanin haka daga gare ku ba. A shekarun da muka ɗauka tare da ku na ɗauka mun daɗe da zama ɗaya, kai ko da wani abu na cutarwa kuka gani za ku iya yin maganin hakan ba tare da na sani ba, sai dai ashe ba haka ba ne. Shi ya sa na yanke shawarar sallamar ku, ba kuma sama ta ka ba, sai da na yi bincike mai zurfi. Don haka, ƙannena za su maye gurbin da kuka bari." Cikin tsananin tashin hankali duka suka miƙe a tare. Ɗayan ne ya yi ƙarfin halin ɗaukar takardun ya shiga dubawa idanu a waje. "Yallaɓai da ba ka yi saurin yanke hukunci ba." Ya faɗa har lokacin yana jin wani irin tashin hankali. Sun shafe shekaru masu yawa suna tare da Baban, sun kasance su ke kula da duk wani shige da ficen kuɗin kowanne shago na Baba. Sai dai a kwanakin baya, sai ya zamana ana ta asara, asarar da ta kasance ba ta wasa ba. Wadda idan har ba a yi maganin abun ba, to gabaɗaya harkokin Baban ka iya durƙushewa. Wannan dalilin ne ya saka Baba ya yi bincike, bayan dogon binciken da ya yi, ya tabbatar da kuɗaɗen na salwanta ne sanadiyyar tura kuɗin da suke yi zuwa asusunsu a wasu lokutan. Kuma kuɗaɗen ba na wasa ba, wannan ne ya saka aka dinga asara. Wanda da Baba ya gano su ne suka dinga kwasar kuɗaɗen bai ji ya gamsu ba, har sai da ya sake yin wani binciken da ya tabbatar masa da zarginsa. Shi ya sa ya yanke shawarar ɗora 'yan'uwansa a kan duk wata harka ta kuɗi, tun da baren da ya riƙe su fiye da 'yan'uwansa ga shi sun ci amanarsa. Bayan shi ɗin ya riƙe su ne da amana, har yana ganin ba zai iya barinsu ba, ya ƙi jawo 'yan'uwansa dumu-dumu cikin kasuwancinsa saboda yadda suke tare da shi tun kafin ya zama wani. Yau ɗin ga shi ya tabbatar da abin da yake zargi. "Kai ai taurin kai ne da kai. Ga komai nan kana gani buge a jikin takarda. Ni kaina kun ba ni mamaki. Dalilinku ya saka Yaya ya ƙi sakar mana akalar kasuwancinsa saboda kar a ce ya yi muku butulci. Yanzun ma bai yarda da ku ɗin ne ba, har sai da bugaggun shaidu suka fito ya tabbatar. Ba ku kyauta ba, kun ci amanar mutum mai gaskiya kamar Yaya. Irin ku ne ke sakawa mutane suke ƙin yarda da bare." Daddy ya faɗa bayan ya miƙe tsaye. Kallon sa kawai mutumin yake yi ya ma kasa cewa komai. Zuwa can ɗayan ya ce "Yallaɓai ka sake bincikawa, hakan ba za ta taɓa faruwa ba. Babu ta yadda za a yi mu butulcewa alkairinka gare mu." "Kun ga don Allah mu je ko?" Daddy ya faɗa a fusace, don sun soma isar shi. Ya za a yi su cuci mutumin kirki kamar Baba su zo kuma suna marairaice fuska, salon kyakykyawar zuciyarsa ta saka ya sake yarda da su su zo su sake cin amanarsa? Hakan ba zai faru ba in dai yana raye. Ai kuwa ilai, Baban na neman ba su dama ta ƙarshe su sake yin magana, Daddy ya kaɗa su waje kamar wasu karnuka suna tafiya yana yin amfani da hannunsa wajen kaɗa su. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 15 Lumshe idanunsa Baba ya yi yana jin har cikin zuciyarsa bai ji daɗi ba. Bai so ba, sai dai babu yadda zai yi, tun da ba haka nan kawai ya sallame su ba, sai da ya yi bincike. Bai ce komai ba har zuwa lokacin da Abba da Daddy suka fice. Shiru ya wanzu a wajen na tsawon mintina biyu, sai zuwa can sannan Muhammad ya gyara zamansa ya ce "Baba."  Sai a lokacin sannan Baba ya ɗaga kansa ya kalle shi ba tare da ya ce komai ba. Ganin alamar yana sauraron sa ya sanya shi faɗin "Baba kamar hankalinka bai kwanta da sallamar nan ba." Ɗan murmushi kaɗan Baba ya yi kafin ya ce "Ban da abin ka Muhammad, in kama su da laifin cin amana ta, sannan kuma in yi nadamar sallamar su? Babu wani abu in sha Allah. Allah Ya ƙara tsarewa." Sai da Muhammad ya ɗan ja wajen sakanni talatin kafin ya ce "Ameen." Daga haka shiru ya sake wanzuwa a wajen, har zuwa lokacin da don kansa ya ce "Baba zuwa na yi na ba ka haƙuri." Da sauri Baba ya ɗaga idanunsa ya kalle shi cike da mamakin abin da yake faɗa. "Haƙuri Muhammad?" Ya faɗa haka nan kawai yana jin faɗuwar gaba na ziyarta sa. Sai ya jinjina kai sannan ya ce bayan ya sauke ajiyar zuciya. "Eh Baba, a kan laifin dai da na daɗe ina aikatawa ne. Baba ka yafe mini, in sha Allah ba zan sake shan wani abu ba. Don Allah ka ci gaba da taya ni da addu'a, amma in sha Allah wannan alƙawarina ne ba zan sake ba in sha Allah. A wannan karon da gaske nake, zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ban sake saɓa maka ba har zuwa ƙarshen numfashina." Ya faɗa idanunsa a rusune, sun ɗan janye kaɗan. Lumshe idanunsa Baba ya yi, ba tare da ya san abin da ya kamata ya ce ba. Wani irin farinciki yake ji tun daga can ƙasan ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Shin shi kuwa da wanne baki zai iya buɗewa ya yi godiya ga Allah? Ya san halin ɗansa, ko kuma ma ya ce ya fi kowa sanin halin ɗansa, don haka tun da ya ce a wannan karon da gaske yake, ya daina ɗin ne. Kenan addu'arsa ta karɓu? Lallai Allah buwaya gagara misali ne. "Muhammad?" Ya ambaci sunansa da sigar tambaya. Sai ya shiga jinjina kansa don ya sake tabbatar masa da abin da ya faɗa. Kawai sai ya yi amfani da hannunsa wajen yi masa alamar ya zo. Babu musu ya ƙarasa ya rungume mahaifin nasa, gabaɗayansu suna jin wani irin farinciki na ratsa su. Wannan annurin da ya gani a fuskar mahaifinsa, ba ƙaramin faranta masa yaw, yi ba. Ya tabbatar Allah ne kaɗai Ya san halin da zuciyar Baban ke ciki a wannan lokacin. Cikin uniform ɗinta ta shirya, gabaɗaya idan ka gan ta sai ka ɗauka ta tashi daga wata rashin lafiya ne. Ta yi zuru-zuru, ko kaɗan kuma ba ta da walwala. Kai tsaye ƙasa ta sauko, a nan ta samu Abee da ke shirin fita. Duk yadda ta so ta saki jiki sai ta ji ta kasa. Gabaɗaya ta kasa sukuni, cike da ƙwarin gwuiwa ta ce "Abee na shirya." Kallon ta Abee ya yi cike da mamaki ya ce "Shiryawa zuwa ina fa Ayshatou?" Ya tambaya yana kallon ta, duk da ya ga uniform ne a jikinta, amma so yake ya ji daga bakinta. Sai da ta lumshe idanunta da suka yi rau-rau, sannan ta ce "Abee makaranta." Girgiza kai Abee ya yi sannan ya ce "Aysha kin manta alƙawarinmu da ke. Ai maganar makaranta kuma ta ƙare. Ni da mahaifiyarki muna so mu ga kin zama wata, wadda za mu yi alfahari da ke. Ke ba ma mu kaɗai ba, wadda kowa zai yi alfahari da ita. Abin da ya sa muka dage ki yi karatu kafin aure, ba kowanne miji ne za ki aura da zai yarda ki ci gaba da karatun ba. Ko da kuwa ya amince kafin ya aure ki, bayan auren zai iya canja shawara, lokacin da ba ki da yadda za ki yi. Idan kuwa da karatunki ya same ki, wannan ya rage nasa barin ki ki yi aiki ko kuwa a'ah, saboda ƙaruwarsa ce. Shi ya sa na so ko da zan aurar da ke to sai kin fara karatun jami'a. Kin kasa fahimta Aysha, ban san da me muka rage ki ba, da har ta kai ga kina fita ki haɗu da wani a waje. To dududu ma nawa kike ne Aysha? Fahimtar da na yi kin yi hakan ne saboda alƙawarinmu, ya sa yanzu na janye shi. Ki turo mini duk wanda kike so na aura miki, zan aura miki shi in sha Allah, amma babu zancen karatu." Ƙasa ta zube bayan ta ƙarasa inda yake ta shiga faɗin "Abee don Allah ka yi haƙuri, wallahi ina son karatuna. Ina so na zama kamar Ummee, don Allah Abba ka yi haƙuri ba zan sake abin da na aikata ba. Wallahi ba zan sake ba, don Allah ka yi haƙuri. Wallahi na zaɓi karatuna Abee." "Ummee bari na tafi." Abee ya faɗa yana kallon Ummee da tun da suka fara magana take gefe tana kallon su. Ta san Abee ɗin ya matuƙar damuwa, don ta lura da sauyawar sa tun da abin nan ya faru. Ta kuma san yana yin duk wannan abin ne saboda goben Ayshar. Yana kuma yin abin da yake yi ne yanzu saboda ta gane laifin da ta aikata, ta kuma guji aikata shi a nan gaba. Da mamaki Abee ke kallon mutumin da yake ƙarasowa inda motarsa take bayan ya yi masa alamar wajensa ya zo, hakan ya sanya shi dakatawa. Cike da nutsuwa Adam ya ƙaraso ta saitin da Abee ke zaune ya ce "Barka da wannan lokacin Baba." "Yawwah barka dai." Ganin kallon da Abee ke yi masa ya sanya shi faɗin "Da ma wajenka na zo Baba." Cike da mamaki Abee ya ce "Wajena?" Sai ya jinjina kai kansa a ƙasa don tun da ya ga Abee ɗin ya ji ya yi masa kwarjinin da ya kai yana jin kunyar haɗa ido da shi. Jin bai ce komai ba yana ta wani sissinne kai ya sanya shi faɗin "To shigo ko?" Ya yi maganar yana yin amfani da hannunsa wajen buɗe wajen mai zama banza. Babu musu Adam ya ƙarasa cike da farinciki. Da gaske wannan ne mahaifin Ayshar tasa. Don ya gane shi lokacin da ya je duba ta a asibiti. Sai yanzu ya ji hankalinsa ya kwanta, bayan ya tabbatar da ga shi ga mahaifin Janan ɗin, bayan uban gararin da ya sha a jiya. Daga ƙarshe dai.. Tunanin nasa ya katse lokacin da Abee ya ce "Yawwah ina jin ka ko?" Sai ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Da ma magana ce a kan Aysha. Ni ne wanda ya kai ta asibiti bayan na same ta ita da ƙawarta. Na zo ne don na kawo ƙoƙon barata a kan ganin ta da na yi, ina so a ba ni dama in fara zuwa wajenta. Shi ne na ga dacewar na fara zuwa na same ka. Wannan shi ne dalilin zuwana, wato dai a taƙaice, na ga Aysha ina son ta, kuma da aure nake son ta." Tun da ya fara maganar Abee ke kallon sa har ya kai ƙarshe. Anya kuwa ba zai haƙura ba, ya bar Janan ɗin ta yi aure? Shi kawai gani yake yi wani auren yana iya hana karatu. Shi ne dalilin da ya sa yake so ta yi karatunta, ta sake sanin wace ce ita, ta kuma san me ma duniyar take ciki kafin auren. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci ma ƙwaƙwalwarsa ta fara tuno masa yadda suka yi da ita yanzu kafin ya fito. Kamar ta ce ta zaɓi karatunta ne a kan auren ita ma. Don haka tun kafin ma abin ya yi nisa gwara ya san abin yi. Sai da ya gyara zamansa sannan ya ce "Wato hankalinka ya burge ni ƙwarai. Na kuma ji daɗi da ya kasance ba ka yi gaban kanka wajen soma tunkarar yarinyar ba. Hakan ya nuna mini ka san abin da kake yi, kana kuma da hankali. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Aysha yarinya ce ƙarama, wadda kwata-kwata ma ko secondary school ba ta gama ba. Idan na ce zan sake ta sakaka ta soma kule-kule kamar ban yi wa rayuwarta adalci ba. Ka san dai yadda duniyar take ciki yanzu. Ina son inganta rayuwarta, wannan dalilin ne ya sa nake so sai ta shiga jami'a sannan zan aurar da ita. Idan za ka iya jira ta gama ɗin, zan ce maka muna maraba da kai, don ni dai na yaba da hankalinka. Idan kuma ba za ka iya jira ba, zan ce maka Allah Ya zaɓa maka wadda ta fi ta alkairi." Tuni gumi ya soma tsatstsafo wa Adam, ya ma rasa me zai ce kwata-kwata. Shin ina wannan dattijon yake so ya tsoma rayuwarsa ne ma gabaɗaya? Daga haɗuwa da Janan fa har ya soma hango irin rayuwar da za su gabatar, da yadda in sha Allah hankalinsa zai kwanta ya huta da jarabar Nafisa ta kullum da ba ta ƙarewa. An kai wajen minti ɗaya sannan ya iya buɗe baki da ƙyar ya ce "To Baba na gode sosai Allah Ya saka da alkairi. Ko ma yaushe ne zan iya jiran ta, to amma don Allah ina neman alfarmar a dinga bari na ko da sau ɗaya ne cikin sati biyu in dinga zuwa muna gaisawa, saboda ta san da zamana." Girgiza kai Abee ya yi kafin ya ce "Ni na san sakamakon da hakan zai haifar, saboda haka ka yi haƙuri ka jira ta ɗin dai. Babu wata damuwa in sha Allah. Kai na sani, kuma zan ba ka auren Aysha in dai har ka cika duk wasu ƙa'idojin da ake so ɗa namiji ya cika su. Ta gefe guda kuma idan dai har ba ka janye ba, kana nan kana biɗar auren ta, kuma ta ce tana son ka." "Ba zan taɓa janyewa ba Abee, ina son Aysha ne tsakanina da Allah, saboda haka zan iya jiran ta na ɗan wannan lokacin, matuƙar dai za a ba ni auren ta." Ya ƙare maganar a sanyaye, don sai yanzu ya tuna ashe fa da sirikinsa na gobe yake tare, shi ne ya saki jiki yana waɗannan maganganun. "Shi kenan, ina yi maka fatan alkairi." Abee ya faɗa. "Na gode sosai Baba, Allah Ya saka da alkairi." Adam ya faɗa yana jin wani irin farinciki na ratsa shi. Ko babu komai ya san ya kama dahir, ba shi da wani shakku yanzu haka, tun da har an san da zamansa, ai shi kenan burinsa ya cika. Abu ɗaya zai sake nema, shi ne ba shi damar zuwa wajen Ayshar ne ko da sau ɗaya ne a wata. Sosai idanunta ke yi mata zafi, saboda kukan da ta sha wanda hatta idanun sai da suka gaji. Har lokacin kumburin da suka yi bai baje ba, jan ma da suka yi bai baje ba. Shi ne ma dalilin da ya sa take ta mazewa don kar wani cikin gidan ya fahimta, ta san yanzun nan hankalinsu zai tashi. Ita kuma abin da ba ta so kenan, don ta san ba wata matsala ba ce, kukan kawai da ta yi ne ke neman tayar mata da kwantaccen ciwon idanun nata. Har wajen ƙarfe 12 idanunta biyu, tana tunanin da ya kasa fita daga zuciyarta, wato tunanin Khaleed. Duk da a yanzu ba wai soyayyarsa ce ke damun ta ba, ko kaɗan ba ta jin ƙaunar sa, gabaɗaya ya sire mata, ban da wata irin tsanar sa babu abin da take ji. Abu ɗaya ne ya tsaya mata a rai, shi ne yadda aka yi Khaleed ɗin ya ci amanar ta, ya juya mata baya cikin ƙanƙanin lokaci, a lokacin da take matuƙar buƙatarsa, take kuma jin za ta iya yin komai a kansa. Tuntuni ta cire glass ɗin, saboda ji take kamar yana takurawa idanunta a yau ɗin. Tun da kuma babu wani abu da za ta yi amfani da idanun wajen kallo ya sanya ta zauna a hakan tsayin awanni, zuciyarta gabaɗaya a cunkushe. Mafita kawai take nema, mafitar da za ta sanya biyu babun da take ƙoƙarin yi ya tarwatse. Burinta ɗaya, kar ta rasa Khaleed, ta kuma zo ta rasa karatun ma. Sai dai gabaɗaya ƙwaƙwalwarta ma a cunkushe take, ballantana har ta iya wani tunani mai ma'ana. Abu ɗaya ta sanu, ya zama dole ta je ta sami Yah Farouk, Yah Farouk shi ne kaɗai fatanta na ƙarshe, wanda ta san zai tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da karatunta. Kamar daga sama ta ji an turo ƙofar ɗakin, ba ta yi yunƙurin tashi don ganin wace ba, don ta san Ummee ce,

Chapter 11 of 24