Janan ta ce
"Au, Ummee na manta jiya kaina ya ɗan yi mini ciwo." Ta faɗa da sauri don ba ta so ko kaɗan Ummeen ta rafko ta, har ta saka ta kasa yin shiru sai ta sanar da ita abin da ke faruwa.
"Subhanallahi! Amma dai idonki ba ya ciwo ko?" Ummee ta yi maganar tana ƙarasawa kusa da Janan ɗin sosai, lokaci guda tana taɓa gefen fuskarta, ta wajen idanunta. Sai ta yi murmushi tana sauke gilashin idanunta ta ce
"A'ah fa Ummee, kin gani babu abin da nake ji a cikinsu." Ta ƙare maganar tana ɗan lumshe kyawawan fararen idanunta lokaci guda tana buɗe su. Kyakykyawa ce irin kyan nan na ajin farko, idanunta dara-dara da suka kasance mara sa lafiya suna ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara wa fuskarta kyau. Duk da a wasu lokutan suna janyewa musamman idan ciwon ya motsa mata. Sai dai hakan ba ya taɓa munanta ta, sai dai ma ya ƙara wa fuskarta armashi. Fara ce irin farin nan mai matuƙar kyau, tana da dogon hanci irin na Ummeenta, da jajayen laɓɓa masu matuƙar kyau da ɗaukar idanu. Glass ɗin da take amfani da shi, ba ƙaramin ƙawata fuskarta yake ba. Sai dai ita ba kasafai ta fiya son amfani da shi ba, sai don ya zame mata dole. Kuma Ummee, Abee har ma da ɗan'uwanta Farouk suna saka mata ido a kan ganin ta yi amfani da shi yadda likita ya umarce ta ta yi.
Furzar da iska Ummee ta yi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
"Na gode Allah. Maza wuce mu tafi, ina shirin makara." Ta faɗa tana kama hannun ɗiyar tata suka fice daga ɗakin.
A cikin motarta ta kai Janan ɗin har ƙofar makaranta duk da ba su da nisa, suka yi sallama kafin Ummee ta ja motarta, Janan kuma ta shige cikin makaranta gabaɗaya jikinta a sanyaye. Don za ta iya cewa wannan ne karo na farko da ta fara ɓoye wa Ummeen tata wani abu, har kuma aka kai ga ta yi mata ƙarya. Gabaɗaya ranar haka ta wuni a makaranta cikin rashin sukuni. Daga zarar ta kalli Fa'iza sai ta ji gabanta ya faɗi saboda tuna abin da suke ƙoƙarin aikatawa. Har yanzu ji take kamar kar ta amince da abin da zuciyarta ke tunzura ta ta aikata. To amma burinta fa? Mafarkinta fa? Wannan tunanin shi ne ke sake sanyaya jikinta.
Fa'iza ƙawarta ce a islamiyya, hakan kuma ya samo asali ne kasancewar unguwarsu ɗaya. Sai daga baya sannan aka saka Fa'izan a makarantarsu Janan ta boko.
Da wuri aka tashi 'yan ajinsu saboda za a je gaisuwa wa wata 'yar ajin nasu da mahaifinta ya rasu. Fa'iza ji ta yi kamar an tsoma ta a aljanna, don ta san idan dai har ba wannan damar aka samu ba, babu lallai AyshaJanan ɗin ta biyo ta, ta san za ta kawo mata ƙorafin cewar lokacin tashi ya yi, kar a gida a ga ba ta dawo ba. Ita burinta ɗaya ita ma Janan ɗin ta samu ta waye, ta shiga sahun 'yanmatan da suke tasowa suke kuma ji da 'yammataci. Ita ba ta ga wani abun damuwa ba don Janan ta tsaya tana kula wani namiji ba, saboda ita tun tana J.S.S 3 take kula samari, kuma hakan bai taɓa shafar karatun ba, kuma ko a gida ma an sani, babu wanda ya taɓa nuna mata hakan wani abu ne. Sai Janan? Yarinya 'yar gata mai ji da kyau da kuɗi da gata? Mene ne zai sa ta ƙi morar ƙuruciyarta bayan tana da damar yin hakan? Ita a matsayinta na ƙawarta mai son ta, tabbas za ta taimaka mata.
"Aysha mu je ko?" Fa'iza ta faɗa tana kallon ta. Dogon numfashi Janan ta ja tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu, ita a karan kanta ta san abin da take ƙoƙarin aikatawa ba daidai ba ne. To amma maganar gaskiya ba za ta iya jurewa rashin cikar burinta ba, don haka kawai gwara ta yi shahada ta bi Fa'izan.
"Mu je." Ta faɗa tana yin gaba ba tare da ta kalli Fa'izan ba.
"Yesss." Fa'iza ta faɗa tana ɗakko wayarta daga cikin jaka, wayar tata da ta kasance ƙirar android da wani saurayinta ya siya mata.
Babu daɗewa suka isa gidansu Fa'iza, a harabar gidansu suka nemi wasu kujeru suka zauna.
"Ki saki jikinki su Umma duk ba sa nan, na kuma san sai an jima za su dawo." Fa'iza ta faɗa.
"Uhmm." Shi ne abin da Janan ta iya faɗa kawai.
Sun shafe wajen mintina biyar a wajen kafin Janan ta ce
"Fa'iza zan tafi gida, lokaci yana tafiya." Ta yi maganar tana kallon Fa'iza da ke danna waya.
"Wallahi yanzun nan za ki gan shi ya shigo. Ki yi haƙu.." Maganar tata ta katse lokacin da sallama ta ratso kunnensu. Kusan a tare suka juya don ganin mai sallamar. Yana sanye cikin ƙananan kaya riga da wando, ƙafarsa na saye cikin takalmi sau ciki. Tun da ya shigo idanunsa ke a kan Janan da take iya kallon shi ta cikin glass ɗinta. Haka nan kawai ta ji zuciyarta ta fara bugawa, ta yi saurin runtse idanunta tana ambatar sunan Allah.
"Shi ne." Fa'iza ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi. Ta tabbatar ko Janan ta ƙi, dole Khaleed ya tafi da imaninta, saboda in dai kyau ne daidai gwargwado Allah Ya ba shi, ɗaukar wanka kuwa ba a magana, uwa uba kuma duk wasu alamu sun nuna shi ɗin ƙwararre ne wajen iya soyayya, idan ta yi duba da yadda koyaushe cikin tura wa Janan saƙon soyayya yake, yana bayyana mata irin ƙaunar da yake mata. Flowers kuwa Allah kaɗai Ya san yawan waɗanda ya aiko mata da shi. Amma ko ɗaya ba ta taɓa karɓa ba, gabaɗaya suna wajen Fa'izan.
"Bari na ba ku waje, don ba ku da lokaci mai tsayi." Fa'iza ta faɗa lokacin da Khaleed ya ƙaraso inda suke. Bai iya amsawa ba, sai jinjina kansa kawai da ya yi. Gabaɗaya ji yake kamar ya rungume Janan ɗin saboda tsananin son ta da yake ji yana ratsa kowacce gaɓa ta jikinsa.
"Barka da wannan lokacin Masoyiyata." Ya faɗa bayan ya nemi waje ya zauna har lokacin idanunsa a kan Janan ɗin. Duk da yadda take jin ta a takure, don har ga Allah ta tsani kallo, saboda yadda nan da nan take rikicewa. Ko wani abu za ta yi idan ya kasance akwai idanu a kanta, to nan da nan za ta ji ta kasa sukuni. Sai dai ga mamakinta, sai ta ji ta kasa banzantar da maganar da ya yi mata. Kamar mai koyon magana haka ta buɗe baki tana ƙoƙarin guje wa kallon da yake mata, ta ce
"Barka dai."
Lumshe idanunsa Khaleed ya yi yana kai hannu saitin zuciyarsa ya dafe, da gasken gaske shi kaɗai ya san abin da ya ji saboda muryar Janan ɗin da ya ji. Jin ya yi shiru har bayan wajen minti 1 ya sanya Janan gyara zamanta ta ce
"Don Allah, ina sauri zan koma gida." Yadda ta yi maganar kamar za ta yi kuka, hakan ba ƙaramin kashe Khaleed ya yi a zaune ba. Wato yarinyar komai nata burge shi yake yi.
Ba ta ankara ba, sai ganin Khaleed ɗin ta yi a ƙasa a kan ƙafafunsa. Ta ɗaga idanunta da sauri ta kalle shi cike da mamaki ta ce
"Mene ne hak.." Tun kafin ta ƙarasa tambayar ya ce
"Son ki ne. Komai kika ga ina yi wallahi saboda son ki ne. Babu kuma abin da ba zan iya ba saboda son ki. Don Allah ki tausaya wa rayuwata ki amshi soyayyata. Wallahi duk abin da kika ce mini ni mai bin umarninki ne, ba kuma zan sake yi miki maganar zuwa gidanku ba idan dai har hakan zai iya jawo miki matsala, har sai lokacin da da kanki kika buƙaci in zo gidan naku. Ina son ki, ina matuƙar ƙaunar ki. Ki daure ki amshi soyayyata ko da ba za ki yi mini kwatankwacin son da nake yi miki ba."
Dogon numfashi Janan ta ja, tana ƙoƙarin ganin ta saita numfashinta da tuni fitar sa ta sauya. Jin kalaman nasa take yi suna dukan dodon kunnenta kamar yana sake maimaita mata. Sai dai ta ɓangarensa shiru ya yi yana jira ya ji amsar da za ta fito daga bakin Janan ɗin. Yana fata kuma amsar ta kasance amincewa ce ga soyayyar da yake mata, duk da ya san da wuya. Sai dai ga mamakinsa, sai tsinto muryarta ya yi lokacin da take faɗin
"Tam ni dai don Allah ka bari zan yi tunani."
"Har tsawon wani lokaci za ki ɗauka love?" Ya yi saurin tambaya.
"Gobe." Ta ba shi amsar kai tsaye, ba tare da ita kanta ta san ta faɗa ba.
Kamar an tsoma shi a aljanna haka ya ji, cikin farinciki ya shiga faɗin
"Na gode ƙwarai da gaske, na gode na gode." Gabaɗaya ma sai ya rasa bayan godiya kuma me zai ce mata? Tun da har ta nuna za ta yi tunani a kansa zuwa gobe, hakan na nuna masa akwai ƙamshin nasara. Zai kuma jira zuwan goben, don cikar burinsa. Kafin ta ce komai ya ce
"Yanzu mu je in kai ki gida kenan?" Da wani irin sauri ta dube shi, sai ya yi saurin faɗin
"Afwan love, mu je na taka miki zuwa ƙofar gida." Girgiza kai Janan ta yi ta ce
"A'ah don Allah ka bar shi." Ganin yadda ta yi maganar kamar a dame ya sanya shi faɗin
"Shi kenan. Allah Ya tsare mini ke." Ita dai ba ta iya amsawa ba sai miƙewa da ta yi.
A nutse ya gangara da motarsa gefen titi ya yi parking. Ya ɗauki wayarsa da ke ajje a kan kujera ya yi danne-danne sannan ya kara wayar a kunnensa.
"Ummee Janan ta dawo?" Ya tambaya cikin nutsatsiyar muryarsa bayan ya gaishe da ita. Daga can ɓangaren Ummee ta ce
"A'ah amma dai tana dab da dawowa na san yanzu haka." Da sauri ya ce
"Shi kenan Ummee bari kai tsaye na wuce makarantar tasu na ɗakko ta, idan kuma ta dawo sai ki kira ni."
"To.." Bai jira Ummeen ta ƙarasa maganar ba ya katse wayar. A nutse ya tayar da motar cike da ƙwarewa ya soma tafiya. A ƙofar makarantar ya ajiye motarsa, cikin takunsa na nutsuwa ya fito daga cikin motar, sanye yake cikin shadda riga da wando, waɗanda suka matuƙar amsar jikinsa. Yana da ɗan haske ba can ba, yana da kyau irin sosai ɗin nan. Hannayensa duka biyu ya zuba cikin aljihun wandonsa lokacin da ya soma takawa zuwa cikin makarantar. Daidai lokacin da malaminsu Janan ɗin ke fitowa daga ciki. Kasancewar ya shaida fuskarsa ya sanya shi ƙarasawa ya miƙa masa hannu suka gaisa, kafin a nutse ya furta
"Ba dai har kun tashi ba."
"Aff! Ai mun daɗe da tashi ne, dayake yau ɗin sun je gaisuwar mahaifin wata ɗalibarmu da ya rasu ne."
"Ya Salaam. Ubangiji Allah Ya gafarta masa." Farouk ya faɗa har cikin zuciyarsa yana jin babu daɗi, to amma ya za a yi? Dukkanmu abin da muke jira kenan.
"Ameen-ameen."
Daga haka suka yi sallama, Malamin ya yi inda zai yi, ya yin da Farouk ya koma cikin motarsa. Iska ya ɗan fesar daga bakinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya. Da gaske ya so samun ƙanwar tasa, ya so ya wanke kansa a wajenta yau ɗin. Shi ya sa yake ta Allah-Allah ya zo ya ɗauke ta, su sasanta ma tun kafin su koma gida. Bayan wajen minti 1 ya tashi motar kai tsaye don wuce wa gida. Kafin ya ƙarasa gidan, ya hangi wata 'yar'ajinsu Janan ɗin, wadda ta kasance ƙanwar abokinsa, shi ya sa ma ya gane ta. Tuni ƙwaƙwalwarsa ta tunasar da shi ya cewa Ummee idan Janan ta dawo ta kira shi, amma kuma ba ta kira ɗin ba. Hakan na nufin Janan ɗin ba ta kai ga ƙarasawa gida ba kenan. Don haka sai ya sake tsayar da motarsa ya zuge glass ɗin motar. Da yake inda yake take kalla, ya saka ta hange shi, ta kuma gane ita yake yi wa magana. Don haka ta ƙarasa ta gaishe shi.
"Amm Aysha fa, ko kun rabu?"
Ɗan karkarar da kanta gefe ta yi kafin ta ce
"Aysha..? Gaskiya ba ma tare tun ɗazu. Tun bayan da aka tashi muka rabu, amma dai yanzu na gan su a ƙofar gidansu Fa'iza."
Ba tare da ya gama fahimtar me ta ce ba ya ɗan yi shiru don sake yin nazarin maganar tata. Sai kuma can ya ce
"Ba kwa tare tun ɗazu ke..." Kamar kuma wanda aka kwaɓa, sai ya datse maganar tasa. Ji yake kamar ya tambaye ta tana nufin ba tare suka je gaisuwar ba? Sai dai ta gefe guda ko kaɗan, ko alama ba ya son barin wata alama da za ta janyo zargi wa ƙanwar tasa. Ya ƙaƙalo murmushi ya wanzar a kan kyakykyawar fuskarsa sannan ya ce
"Na gode."
Daga haka ta yi masa sallama ta tafi. Shiru ne ya biyo bayan tafiyar tata. Ya ƙara wajen mintuna 5 yana jira ya ga ko zai ga kiran Ummee amma shiru. Kenan me hakan ke nufi? Yarinyar nan ta sanar da shi tun bayan da aka tashi ba sa tare da Janan, hakan na nufin ba ta je gaisuwar ba? Lallai ya san wani babban uzurin ne ya taso mata ta je gabatar da shi. Don ba shi da shakku a kan ƙanwar tasa, ya san halinta. To amma dai ko ma mene ne, shi gabaɗaya bai fiya son alaƙarsu da Fa'iza ba. Ba ya son ko kaɗan ya gan su tare tun da ya fahimci rawar kan yarinyar. Don haka don kore wa zuciyarsa shakku ya sanya ta tashi motarsa, cikin driving ɗinsa na nutsuwa, musamman da ya kasance ba a kan babban titi yake ba ya soma tafiya, kai tsaye ya wuce zuwa gidansu Fa'izan.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 03
Daidai lokacin da ya isa ƙofar gidansu Fa'iza, wayarsa ta soma ringing. Sai ya dakata yana ɗaukar wayar, ganin Ummee ke kira ya sanya shi saurin ɗagawa.
"Farouk yanzun nan Janan ta shigo gida." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
"Yawwah." Cike da mamakin yadda Ummee ta jiyo sautin ajiyar zuciyarsa ta ce
"Akwai wani abu ne?" Da sauri ya girgiza kai kamar yana gaban Ummeen ya ce
"No, babu komai Ummee, ga ni nan."
Daga haka ya sauke wayar. Haka nan kawai, sai ya samu kansa da kallon gidansu Fa'izan. A hankali ya ɗan kalmashe leɓensa na ƙasa cikin bakinsa, ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya kana ya tashi motar kai tsaye ya wuce gida.
A ɗaya ɓangaren kuwa, tun da Janan ta ji Yah Farouk ya dawo ta kasa sukuni, sai leƙe take don ganin ta inda zai shigo. Ummee na lura da duk wani motsinta. Sai kuma ta ci gaba da aikin da ke gabanta, wanda shi ne ya sanya ta dawo gidan da wuri. Tun da ta ji motsin shigowar motarsa ta fice harabar gidan da gudu fuskarta ɗauke da annuri.
"Oyoyo Yah Farouk ɗina." Shi ne abin da ta fara faɗa tun kafin ya sauko daga motar. Annurin fuskarsa ne ya ƙaru lokacin da ya hango ƙanwar tasa, ya ƙarasa ya yi parking, kana cikin nutsuwa ya sauko. Ko kaɗan bai ankara ba, lokacin da Janan ɗin ta taho da gudu ta rungume shi. Da sauri ya buɗe baki yana jin yadda ta ruƙunƙume shi tana faɗin
"Na yi kewar ka sosai Yah Farouk."
"Oh Baby girl, ni dai ban san lokacin da za ki girma ba." Ya yi maganar a nutse bayan ya saka hannu ya janye ta daga jikinsa a hankali. Cuno ƙaramin bakinta ta yi, ba ta ce komai ba ta yi gaba tana ɗan bubbuga ƙafa. Ɗan lumshe kyawawan idanunsa ya yi, kafin ya buɗe su lokaci guda yana shafa kwantacciyar sumar kansa.
"Afwan Aysha." Ya yi maganar bayan ya fara takawa shi ma.
"To ba kai ba ne ba." Ta faɗa tana jefa masa harara. Murmushi ya yi, kana ya ce
"To shi kenan ba zan ƙara ba. Yanzu dai ki saki fuska kar Ummee ta gan mu a rana." Yanayin yadda ya yi maganar ya sanya ta dole ta yi dariya.
"To ko ke fa." Ya faɗa yana jera wa da ita suka ƙarasa cikin ɗakin Ummee.
Cike da farincikin ganin ɗan nata ta tarbe shi, duk da ba wani daɗewa ya yi a tafiyar ba, amma babu ƙarya ta yi kewar sa. Don haka aikin da take yi ma ajiye shi ta yi don ba shi muhimmanci.
"Amma Janan na je ɗauko ki ashe kun je gaisuwa." Farouk ya katse hirar da suke yi da faɗin hakan, don so yake ya ji abin da Janan ɗin za ta faɗa. Ba don komai ba, sai don hakan nauyi ne a kansa wajen ganin ƙanwar tasa ba ta bi hanyar da ba ta daidai ba. Da sauri ta kalle shi ta ce
"Don Allah ka je?" Jinjina mata kai ya yi don tabbatar mata da abin da ya faɗa ba tare da furta komai ba. Hakan ne ya sa ta ɗan haɗiyi yawun da ya tsaya mata a maƙogwaro tana jin yadda lokaci guda zuciyarta ta ɗan soma bugu. Sai ta yi saurin basarwa sanin halin yayan nata da ke saurin fahimtar ta, ta ce
"Ai Fa'iza ce ba ta da lafiya, shi ne na raka ta gida. Kafin kuma na dawo ashe har 'yan ajinmu sun tafi gaisuwar da za a je." Bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba. Ambatar gaisuwar da ta yi shi ne abu na farko da ya soma kore masa duk wani shakku da yake ji a kan ƙanwar tasa. Abu na biyu kuma sanin halinta da ya yi, ƙarya ba halinta ba ne, ya tambaya ne da ma kawai don dai ya sake tabbatarwa. Kiraye-kirayen sallah da aka fara yi shi ne abin da ya fitar da Farouk daga ɗakin da niyyar ko ya dawo nan ɗin zai dawo ya ci abinci, su kuma yi hira da Ummee da kuma Janan. Don idan ya ce bai yi kewar su ba ya yi ƙarya. Don ba a iya baki ba, hatta da gaɓoɓin jikinsa sun shaida da ya yi kewar gida na tsayin sati biyu.
"Abu Muhammad kawo sai na ƙarasa shigo maka da ita." Hajiya Turai ta faɗa tana kallon Baba lokacin da ya shigo ɗakin, hannunsa ɗauke da jaka da wayarsa. Kallon jakar hannun nasa ya yi kafin ya kalli Hajiya Turai. Kallon da ta ga yana yi mata ya sa ta ɗan tsargu. Ga ɗimbin mamakinta, sai ta ga ya saki murmushi kafin ya ajiye jakar da wayar da ke a hannunsa a kan kujerar kusa da shi. Don kar ya zargi komai, sai ita ma ta mayar masa da martanin murmushin kafin ta ce
"Kafin ka shiga ciki, bari na kawo maka sassanyan lemo ka jiƙa maƙoshinka."
"Ina godiya." Ya ƙarasa maganar yana neman waje ya zauna. Da sauri Turai ta ƙarasa kitchen. Da gaske lemon da ta yi masa ya yi matuƙar sanyi, don har wani naso yake yi. Ta kuma san Baban yana son abu mai sanyi. Har ƙasa ta ƙarasa ta ajiye masa lemon, ba ta tsaya iya nan ba, har sai da ta tsiyaya masa cikin tambulan, sannan ta miƙa masa. Da gaske idan ya ce yau ɗin ba ta burge shi ba ya yi ƙarya. Kai ba ma tun yau ba, tun kafin ta daɗe a gidan ya fahimci kamar halayenta sun sha bam-bam da na mata biyun da ya taɓa aura a rayuwarsa, waɗanda yanzu haka ba sa tare. Sai dai bai sani ba, ba kuma zai yi saurin yanke hukunci ba saboda ruwan mamakin da waɗancan ɗin suka shayar da shi. Zai jira ya sake ba ta lokaci ya ga iya gudun ruwanta, ya kuma sake fahimtar halayenta gabaɗaya.
Sosai ya sha lemon, don babu ƙarya ya yi masa daɗi.
"Sannun ki da ƙoƙari." Ya faɗa yana sake yin murmushi. Murmushin ita ma Hajiya Turai ta yi tana ƙasa da kai irin na kunyar nan. Sai kuma ta buɗe baki ta ce
"Haba haba Abban Muhammad godiyar kuma ta mene ne."
A kaf duniya, yana bala'in ya ji Turai ɗin ta kira shi da Abban Muhammad, kai ba ma ita kaɗai ba, duk wanda ya san shi, to tabbas ya san shalelen ɗansa Muhammad. Ko zaman yini ɗaya ka yi da shi, zai yi wuya ba ka ji sunan Muhammad a bakinsa ba. A kaff rayuwarsa, Allah Bai taɓa jarabtar sa da wani abu ba, kamar yadda yake son ɗansa Muhammad. A gabaɗaya abin da zai yi to Muhammad ne a gaba. Ta inda kuma abin ya zo masa daidai, kamar yadda take a wajensa, hakan take a wajen ɗansa. Ba shi da wani abin so a duniya sama da mahaifinsa. Ko ya ya yake da mutum to sai dai ya biyo bayan babansa. Komai kuma muhimmancin abu, idan dai har mahaifinsa ya nuna ba ya so to in Allah Ya yarda ya bar shi kenan har abada. Abu guda ne har yanzun ya san zai iya cewa ya saɓa wa mahaifin nasa, wanda har yau har gobe idan ya tuna da hakan yana jin ɓacin rai.
Sau biyu Baba na rabuwa da matansa a kan Muhammad ɗin. Saboda duk ya aure su ne ko kaɗan ba sa son Muhammad. Ta farko ɓaro-ɓaro take fitowa ta nuna ko da kaɗan ne ba ta ƙaunar Muhammad, kuma Baban sai dai ya zaɓa ko ita ko ɗansa. Azabar da take gana wa Muhammad ta yau daban ta gobe daban, amma bai taɓa buɗe baki ya sanar wa da mahaifinsa ba, sai da Allah Ya yi zai sani sannan ya sani. Wannan dalilin ya saka suka rabu da ita. Ta biyu ma kusan abin da ya raba su kenan. Duk lokacin da Baba ba ya nan to Muhammad ya shiga uku. Daga ƙarshe dai dole ita ma ya rabu da ita. Fahimtar da ya yi duk Baban na rabuwa da matansa ne saboda shi ya sanya ya ƙuduri aniyar ko me matar da Baban ya aura za ta yi masa, ba zai taɓa bari Baba ya gane ba. Yana gudun ɓacin sunansa kasancewarsa sanannen mutum da duniya ta san shi a harkar kasuwanci. Mutane kuma ba bincike za su tsaya yi ba, kawai za a ce yana da auri saki ne. Don haka ko da Baba ya auro Hajiya Turai, ba kasafai ma yake shigowa sashen ba don gudun faruwar wani abun.
"To shi kenan, mu je in samu in watsa wa jikina ruwa." Baba ya yi maganar yana miƙewa. Ya ɗauki jakar da ya ajiye sannan ya yi gaba. Har tana shirin bin bayansa, sai idanunta suka sauka a kan wayarsa da da alama ya manta da ya ajiye ta a wajen. Birki ta ci kamar wadda ke shirin yin tuntuɓe. Ta sake kallon inda wayar take a ajiye kafin ta ce
"Bari na kai jug ɗin kitchen." Ta faɗi hakan tana ɗan ƙaƙalo murmushi. Ba tare da ya juyo ba ya ce
"Ohk." Daga haka ta juya. Har tana ƙoƙarin yin tuntuɓe lokacin da ta ƙarasa wajen kujerar. Ta yi azamar kai hannunta ta ɗauki wayar cike da fata iri-iri. Kamar yadda ta tsammata da ma babu password. Ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba. Hannunta har karkarwa yake yi lokacin da ta soma danna wayar. Gabaɗaya ma ta rikice ta rasa ta ina za ta fara? Ta san dai tabbas dole za ta samu wani abu a cikin wayar, tun da da ita yake amfani wajen yin kira. A nan ne kuma za ta gano abin da yake ɓoyewa wanda ba ya so kowa ya sani. Ciki kuma har da ƙannensa, kamar yadda Maman Al-ameen ke sanar da ita. Wannan wanne kalar baƙin hali ne? Wanne kalar abu ne yake yi da bai so 'yan'uwansa har ma da matarsa su sani?
Kamar daga sama, ta soma jiyo takun da ya gigita ilahirin jikinta. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya soma karkarwa, hatta ƙafarta sai ta ji tana ƙoƙarin kasa ɗaukar gangar jikinta, wanda hakan ya zamo silar faɗuwar wayar a dandagaryar ƙasa. Cike da tsoro ta ɗaga idanunta ta sauke su a kan mamallakin takun nan. I zuwa lokacin ya dakata daga inda yake, don haka ta yi nasarar sauke idanunta a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 24