Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai ce ta yi gaba. Sai ya furzar da zazzafar iska daga cikin bakinsa sannan ya bi bayan Ummeen. Lokacin da yake ƙoƙarin tayar da motar, kiran Abee ya shigo wayarsa. Ya kalli wayar sannan ya kalli Ummee. Da sauri ta girgiza masa kai. "Kar ka sake ka sanar da shi. In sha Allah ba wani abu ba ne. Kuma yanzu ka sanar da shi hankalinsa zai tashi. Maza ɗaga." Babu musu ya ɗaga wayar yana saka ta a handsfree. "Farouk." Abee ya faɗa bayan ya amsa sallamar Farouk ɗin. "Na'am Abee." "Aysha ta dawo kuwa? Tun ɗazu nake jiran ganin kiran ka na ji ka ce za ka koma gida da wuri." Ɗan gyara muryarsa ya yi yana ɗan lumshe kyawawan idanunsa sannan ya ce "Abee ban riga na koma gida ba tukunna, amma na san ta dawo in sha Allah. Ina komawa zan kira ka." "To babu damuwa. Ko don saboda haka zan ajiye wa Aysha waya a gida saboda kasancewar ku ba mazauna ba." "Ai kam." Shi ne abin da Farouk ya iya faɗa kawai. Daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar. Tayar da motar ya yi a gurguje, kai tsaye suka wuce makarantar. Tun daga nesa suke hangen gate ɗin school ɗin kamar a kulle. Cikin ƙanƙanin lokaci zuciyar Ummee ta soma bugu tana sake watsa idanunta don tabbatar da abin da take gani. A bakin gate ɗin ya tsayar da motar, inda sai da suka zo dab, sannan suka fahimci ɗan sakaya shi aka yi, amma akwai inda mutum zai iya shiga, amma ba wajen mota ba. Daidai lokacin da wata motar ma ta tsaya a bakin gate ɗin. Hannu Ummee ta kai za ta buɗe ƙofar don ficewa daga cikin motar, Farouk ya yi saurin faɗin "Ummee ki yi haƙuri ki zauna cikin mota, bari na je na tambayi mai gadin ko da mutane a ciki. Da alama ma yanzu ake shirin kai ɗaliban gidansu." Ya faɗi hakan don so yake ya ba ta ƙarfin guiwa, duk da shi ma nasa ɗin kaɗan ne. Saboda haka nan kawai yake jin faɗuwar gaba. Daidai wannan lokacin Muhammad ya sauko daga cikin motarsa sanye cikin wasu shaggun ƙananan ƙaya, kansa ya ƙara yin wani azababben kyau, saboda tsadadden gyaran da ya sha. Hakan ya sa yake ta sheƙi, ya kuma kwanta luff-luff a kan farar fatarsa. Hannunsa ɗauke da wayarsa kare a kunnensa yana amsa waya. "Eh ina can." Shi ne abin da ya faɗa lokacin da ya ƙarasa ciki inda maigadin yake. Wayarsa ya mayar cikin aljihu sannan ya miƙa wa mutumin hannu. Sai da suka gaisa sannan ya ce "Akwai ɗalibai ne a cikin makarantar nan yanzu haka?" Da mamaki mai gadin ya ce "Ɗalibai kuma? Ai tun ɗazu aka riga aka tashi. Waɗanda ma suka je gaisuwa tuni an mayar da kowa gidansu, ga motar da ta kai su can ma ajiye. Hajiya ce kawai a cikin makarantar." Shi ne abin da maigadin ya faɗa yana kallon Muhammad. Farouk da bai ma kai ga tambayar maigadin ba, gabaɗaya maganganun sun sauka a cikin kunnuwansa. Sai dai sam bai ma fahimci abin da yake ƙoƙarin cewa ba, duk da wani ɓangare na zuciyarsa na ƙoƙarin tunasar da shi ma'anar abubuwan da mutumin ya faɗa. Amma don ya sake tabbatarwa, sai ya shiga takawa ya ƙarasa zuwa inda maigadin yake don shi ma ya yi masa tambayar da ya zo da niyyar yi. Don haka kawai yake jin kamar ba shi da alaƙa da tambaya da kuma amsar da aka ba wa Muhammad. To ma sha Allah! Ga shi dai na cika alƙawarin da na ɗauka. In sha Allah mun ɗora kenan babu kama hannun yaro. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 11 Sallama ya yi a sanyaye, lokaci guda yana miƙa wa mai gadin hannunsa. Babu musu ya miƙa masa bayan ya amsa sallamar. "Na ji kamar kana magana a kan ɗaliban da suka je gaisuwa ko?" Ya faɗa bayan ya gyara tsayuwarsa. Jinjina kai mai gadin ya yi kafin ya ce "Eh wannan ma da ya shige ciki yanzu na gama yi masa bayani. Babu kowa cikin makarantar sai Hajiya, babu daɗewa motar da ta kai su gaisuwar ta shigo gidan nan." Ya faɗa yana nuna cikin makarantar. Bin bayan Muhammad Farouk ya yi da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya, haka nan kawai ya ɗan ji faɗuwar gaba na ziyartar sa. Bai bari hakan ya yi tasiri ba, ya jinjina kansa sannan ya ce "Bari na shiga ciki." Daga haka bai jira amsar mai gadin ba ya shige ciki zuciyarsa gabaɗaya a cunkushe. Kusan a tare suka isa office ɗin mai makarantar. Sai dai lokacin da Farouk ya isa Muhammad waya yake yi. Don haka ya riga shi shiga, amma kafin ya kai ga zama sai ga shi ya shigo bayan an yi masa iso. Cikin girmamawa suka gaisa, don matar ta san ta kan girmama iyaye ko dai wakilan students nata. Shi Farouk ba ta wani gaisawa yake ba, kawai so yake ya ji me yake faruwa? Ina 'yar'uwarsa take? Don haka ya yi saurin faɗin "Amm, students da aka ce za a mayar da su gida. Har yanzu ba a gama kai su ba ne?" Shi ne abin da ya faɗa kawai, don har zuwa lokacin bai gama gasgata maganar mai gadin ba. Cike da mamaki principal ɗin take kallon sa, sai ta yi ƙarfin halin wanzar da murmushi a kan fuskarta sannan ta ce "Ayyah ina ga ba ka koma gida ba. Ai tuntuni sun koma gida. Sai da aka kai kowa gidansu sannan ya dawo cikin makarantar nan, bai ma daɗe da tafiya ba." Wani zazzafan numfashi Yah Farouk ya sauke sannan ya ce "Daga gidan nake yanzu haka. Aysha ba ta koma gida ba har zuwa wannan lokacin." "Me? Ba ta koma ba?" Principal ta faɗa tashin hankali na bayyana a kan fuskarta. Ɗan numfashi kaɗan MuhammadAali ya ja sannan ya ce "Abin da ya kawo ni kenan. Amina Aminu Shettima ba ta dawo gida ba har zuwa wannan lokacin." A wannan lokacin Hajiya na iya cewa tashin hankalinta ya fi na ɗazun. Don ko kaɗan ba ta shaida fuskar MuhammadAalin ba, saboda duk wani abu na Ammeeyn a kan makaranta ba ya ciki. Da ma Baba, Daddy sai Abba ko Al-ameen su ne suka fi zuwa makarantar, musamman ma dai Baba da yake matuƙar ƙaunar Ammeeyn kamar shi ya haife ta. "Amina ma?" Ta tambaya cikin tsananin tashin hankali tana kallon MuhammadAali. Sai ya jinjina kai kawai ba tare da ya ce komai ba. Wani dogon numfashi principal ta sauke sannan ta janyo wayarta kai tsaye ta shiga dannawa, wajen sakanni biyar ta kara a kunnenta hannunta har wani rawa yake yi. "Hello Abdullahi." Shi ne abin da ta faɗa tana ji an ɗaga wayar. Amsawar da ya yi shi ne abin da ya ba ta damar saka wayar a handsfree sannan ta ce "Ɗaliban da ka tafi da su, duk ka kai su gida?" Cike da mamaki ya sake duba mai kiran nasa, sai ya ga kamar yanzu ya bar makarantar kuma sun gama magana da Hajiyar. To amma tun da dai tambayar tasa take yi, ƙila akwai dalilinta na yin hakan. Don haka ya ce "Ƙwarai kuwa Hajiya. Babu yaron da ban kai gida ba. Gabaɗaya sai da na kai su sannan na dawo da motar." Zuwa lokacin har gumi ya soma tsatstsafo wa principal. Shin me yake faruwa ne? Idan har ya kai su gida to ina suke? Ba mutum ɗaya ba ma ballantana a ce ko ta biya wani waje, har mutane biyu? To kenan ina suke? Shin wani abu ne ya faru da su? A wanne hali suke ciki yanzu haka? "Dole mu san abin yi." Shi ne abin da principal ta faɗa tana miƙewa cikin rashin sanin abin yi. Ta san dai dole su san abin yi ɗin da gaske kamar yadda ta faɗa, to amma ta yaya? Me ya kamata su fara yi? Ina za su fara dosa kai tsaye? Tun kafin ta yi wani yunƙuri na takawa Farouk ya miƙe tsaye yana jin yadda bugun zuciyarsa ke fita da sauri-sauri. Ya san halinsa, zuciyarsa na da matuƙar rauni a kan Janan ɗin. Yana mugun ƙaunar 'yar'uwarsa, ta yadda ba zai iya misaltawa ba. Tabbas idan har wani abu ya same ta, bai san a wanne yanayi zai tsinci kansa ba. Shin da wanne baki zai koma ya sanar wa da Ummee abin da ke faruwa? Shin da wanne ido zai kalli Abee ya sanar da shi Janan ba ta dawo gida ba bayan an tabbatar da an je an ajiye kowaccensu a gida? Shin shi kansa ma me ya kamata ya yi? Cike da mamaki take kallon Hajiya Zainab (Maman Al-ameen) ɗin da ta shigo cikin ɗakin. Duk da da ma dai tana shigowa, amma ganin ta kwana biyu ba ta shigo ba ya sanya ta mamakin shigowar ta yau ɗin. Dukkansu neman waje suka yi suka zauna. "Sannu da zuwa." Hajiya Turai ta faɗa. "Yawwah sannun mu dai. Fatan na same ku lafiya." "Alhamdulillah, ina Al-ameen?" Sai da ta ɗan taɓe baki sannan ta ce "Yana sashensu ko kuma wani wajen dai." "Ma sha Allah." Hajiya Turai ta faɗa. Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru. Zuwa can ta miƙe ta ce "Bari na ɗan je kitchen." "A'ah, kin ga dawo ki zauna. Wani abu ne ya kawo ni fa. Ko kuma bari kawai na ce wani abu mai muhimmanci ne ya kawo ni." Komawa Hajiya Turai ta yi, ta riga ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, ita kuma ta yi alƙawarin Hajiya Zainab ɗin ba ta isa ta yi mata maƙarƙashiya daga ƙarshe ta zo ta kife da ita ba. Ko ma mene ne take shiryawa ta yi ita kaɗai, ba za ta kai ta ta baro ta ba. Idan da ta so biye mata to ban da yanzu. "To ina jin ki." Ta faɗa tana neman waje ta zauna. "A kan maganar nan ne dai...." "Ya Hayyu Ya Ƙayyum, jira ni Muhammad, ga ni nan." Maganar Baban ta ratso cikin parlourn lokacin da yake sakkowa daga kan bene. Kusan duk a tare suka juya suka kalle shi jin yadda ya yi maganar kamar hankali ba a kwance ba. "Ba zan iya zama gida bayan ban san me yake faruwa ba. Ka bar wayarka a kusa, zan fito yanzu." Baba ya sake faɗa lokacin da ya ida ƙarasowa tsakiyar ɗakin. "Me yake faruwa Abu Muhammad?" Hajiya Turai ta yi saurin faɗa tana kallon shi, bayan ta miƙe tsaye. "Ammeey.. Ammeey ba ta dawo cikin gidan nan ba tun bayan da aka tashi daga makaranta. Yanzu Muhammad ya kira ni daga makarantarsu, sun ce sun daɗe da dawo da kowa gida amma ga ta shiru. Hankalina ya kasa kwanciya." "Baba ka kwantar da hankalinka don Allah ko don lafiyarka. Kar ka ɗaga hankalinka kuma a zo a samu matsala. In sha Allah babu wani abu da zai faru. Ba sai ka fito ba." Muhammad da ke jin duk abubuwan da ke faruwa ta cikin wayar ya faɗa cikin kwantar da murya. Don da gaske ba ya so Baban ya fito ko kaɗan, ba kuma ya so ya ɗaga hankalinsa saboda lafiyarsa. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu ina za ka je?" Turai ta faɗa tana kallon Baban. "Zan je ko ma ina ne in san abin da za a yi. Ban ga amfanin zamana cikin gidan ba, tun da har yanzu ba mu san inda take ba." Ya faɗa daga haka ya yi gaba. "Allah Ya tsare." Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan tana jinjina kai. Abin akwai ɗaurewar kai. 'To yanzu kai tsaye ina za su tunkara?' Ta tambayi kanta duk da ta san babu wanda zai ba ta amsa. "Ikon Allah! Ita kuwa yarinyar nan ina ta kai kanta?" In ji Hajiya Zainab cike da mamaki. Ita dai Hajiya Turai ba ta ce komai ba, don yanzu takatsantsan take yi a kan alaƙarta da Hajiya Zainab ɗin, haka kurum a banza ta kashe mata aure, ko ta saka ya soma girgiɗi. "Zauna mu yi maganar da ta kawo ni ko? Allah Ya kyauta." Ta faɗa tana neman waje ta zauna, don ita ma tun fitowar Baban ta miƙe. Girgiza kai Hajiya Turai ta yi tana kallon Hajiya Zainab "Magana kuma? Shin ba ki ji abin da ke faruwa cikin gidan ba ne? In zauna mu yi wacce magana? Mu da ya kamata a ce yanzu haka an shiga fafutukar abin da ya kamata mu yi a cikin gidan nan? Da kuma tunanin halin da Umman Ameeyn ke ciki? Ya ci a ce yanzu haka muna sashenta." "Ke dakata mini uwar iyayi da kiɗifiri! Ki zo ki same ni cikin gidan da na yi tsayin shekaru masu yawa ki ce za ki tsara mini abin da ya kamata? Ki yi takunki a sannu, don wallahi yadda matan da ke shigowa ɗaya bayan ɗaya suna ficewa daga gidan nan, ke ma haka za ki fice ki bar gidan. Arziƙin da kike kwaɗayi ba za ki same shi ba komai nacinki." Hajiya Zainab ta faɗa cike da ɓacin rai. Kallon ta kawai Turai take yi, ita har ga Allah ta wani ɓangaren ba ta ga alaƙar maganar da ta yi da maganganun Hajiya Zainab ɗin ba. Me ya yi zafi? Me ya kawo duk waɗannan maganganu? Me kuma ya kawo zancen dukiya? Ita wai gabaɗaya me yake damun matar nan ne? Gabaɗaya maganarta ba ta wuce ta dukiya da wani abu da ya shafe ta? Shin mene ne matsalarta ne ita kam? Ba ta kai ga cewa uffan ba Hajiya Zainab ɗin ta ja tsaki tana ficewa daga ɗakin. Da ma kuma ba ta yi niyyar cewa komai ba, don haka ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai. Cike da basarwa ya buɗe murfin motar ya shiga. Tun kafin ya gama zama Ummee ta ce "Farouk ina ɗiyata? Ina Aysha take?" Sai da ya zauna sosai sannan ya furzar da iska zazzafa daga bakinsa ya ce "Ummee ki kwantar da hankalinki. In sha Allah babu wani da ya faru." Daga nan ya sanar da ita yadda suka yi da principal ɗin. "Ta yaya zan kwantar da hankalina Farouk? Ta yaya zan samu nutsuwa bayan Janan ba ta tare da ni, ban kuma san halin da take ciki ba. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Ummee ta ƙare kuka na ƙwace mata. Shin ina 'yarta take? Me ya same ta ba ta dawo ba? Shin tana cikin ƙoshin lafiya ko akasin haka? Shiru ya yi ya bar Ummeen ta gama kukan, don shi kansa bai san da waɗanne kalamai zai yi amfani ya kwantar mata da hankali ba. To amma ko ma dai mene ne, dole ya ba ta baki ko ta samu sassauci. Daidai lokacin da wayar Ummeen ta soma ruri. Sai da ta yi amfani da hannunta wajen goge hawayen fuskarta sannan ta kalli wayar, sai kuma ta kalli Farouk. "Ummee ina ganin kawai ki ɗaga ki sanar da shi abin da ke faruwa, ko da akwai wani taimakon da zai iya yi mana." Ita ma a karan kanta ta amince da abin da Farouk ɗin ya faɗa. "Ummee amma ki fara yin haƙuri don Allah, ko za ki samu ƙwarin gwuiwar sanar da shi abin da yake faruwa." Dogon numfashi Ummee ta ja sannan ta kira number Abee ɗin da kiran da ya yi ya katse. "Wai lafiya kuwa Ummee ina ta kiran ki babu amsa? Me yake faruwa ne?" Babu ɓata lokaci ta shiga sanar da shi abin da ke faruwa cike da tashin hankali. Daga inda yake zaune ya miƙe cike da mamakin jin abubuwan da Ummeen ke faɗa. Janan ɗin? "Wannan shi ne dalilin da ya sa ba na buƙatar kowa ya ce zai kai ko ɗakko Janan makaranta. Yanzu me gari ya waya? Wanne irin sakaci ne da zai saka a ce ba a ga har yara biyu ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Abee ya faɗa cikin tsananin tashin hankali. Ita dai Ummee shiru ta yi, don ta san da ma dole Abeen ya yi faɗa. To amma gwara da aka sanar da shi ɗin, faɗan zai fi zuwa da sauƙi a kan idan suka yi shiru sai ya dawo ya ji abin da ya faru. Gabaɗaya ranar haka ta ƙare wannan iyalai biyun suna cikin tashin hankali. Kowa ya duƙufa yana neman inda 'yarsu take. Sai dai har dare babu wani cigaba da aka samu. Ita kanta principal hankalinta a tashe take, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ita ta so ta fara sanar wa da police a kan lamarin, sai MuhammadAali ya dakatar da ita. Don tuni har sun saka an fara bincike a kan lamarin. Duk da haka dai ita hankalinta a tashe yake, don gani take duk wani abu da ya faru dalilinta ne. Idan kuma wani abu mara daɗi ya faru ita za a fara tuhuma. To amma Allah Na gani, tana iya bakin ƙoƙarinta, kulawar da take ba wa students ɗinta sai ta ce ko 'ya'yanta ba sa samun shi. Saboda su ɗin tana ɗaukar su ne a matsayin waɗanda ke kawo mata kuɗi. Shi ya sa ko kaɗan ba ta wasa da abin da zai sa ta rasa wasu hanyoyin shigowar kuɗi. A hankali ya sauke numfashi lokacin da ya tsinci kansa a cikin ɗakinsa. Ƙarfe 12am agogon da ke manne a bangon ɗakin ya nuna. Idanunsa gabaɗaya sun yi jajir saboda tsananin tashin hankali. Shi kansa ma a hargitse yake, don tun fitar da suka yi ɗazun sai yanzu ya samu ya shigo gidan. Ƙarasawa ya yi kan gadonsa a nutse ya zauna, shin ina Janan? A wanne hali take ciki? Tun ɗazu zuciyarsa ke hango masa wani abu, sai dai ya kasa amincewa da zuciyarsa saboda irin yardar da ya yi wa 'yar'uwar tasa. Ina Khaleed? Ina kuma Janan? Zuciyarsa so take ta ƙunsa masa cewar ko dai ta je wajensa ne? To amma sai kwaɓar ta yake yi, saboda ba zai taɓa gasgata hakan ba in dai ba tabbatarwa ya yi ba. Kai ba ma ya tunanin Janan ɗin za ta aikata hakan. Idan ma har hakan ne me ya sa har yanzu ba ta dawo ba? Kuma abu na biyu ma da zai saka ba zai gasgata hakan ba, kasancewar su biyu ne suka ɓace ba a gan su ba. Hannayensa duka biyun ya cusa cikin sumar kansa cikin rashin sanin abin yi. Yanzu haka za su kwana cikin gidan ba tare da Janan ba? Shin a wanne hali take ciki ita a yanzu haka? Ajiyar zuciya ya sauke yana miƙewa, ruwa ya watsa wa jikinsa ya fito ya shirya cikin doguwar rigar bacci, babu abin da ya tsaya ya saka wa kansa kai tsaye ya fice daga ɗakin. Kamar yadda ya tsammata kuwa, a parlour ya samu Ummee tana kukan dai da ya tafi ya bar ta. Ya sauke ajiyar zuciya yana tunanin ta ina zai fara? Shi kansa ƙarfin hali kawai yake yi, don ya sake ba wa Ummeen ƙwarin gwuiwa. Neman waje ya yi ya zauna ba tare da ya ce komai ba. Abee yana cikin ɗakin a tsaye yana amsa waya. Bayan wajen mintina biyu Abee ya kalli Ummee ya ce "Ki yi haƙuri ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo." Ya yi maganar bayan ya nemi waje ya zauna. "Na kasa daina kukan ne Abee, ko na yi shiru sai hawaye sun sakko. Ban san inda Janan take ba, ban san me ya faru da ita ba, ya zama dole hankalina ya kasance a tashe." "Ummee ki yi haƙuri don Allah, in sha Allah komai zai zo da sauƙi. Babu kuma abin da ya samu 'yarki in sha Allah." Farouk ya faɗa a nutse. "Haka nake fata." Ummee ta faɗa tana jinjina kai. Kamar ba zai duba mai kiran nasa ba, lokacin da ya wayarsa ta soma ruri. To amma kuma ganin bayan ƙarfe 12 ne, haka nan dai lafiya ƙalau ya san ba za a kira shi a irin wannan lokacin ba. Saboda haka ya ɗauki wayar ya kara a kunnensa. Shiru ya yi yana saurarar abin da yake ji cikin wayar kafin kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye da sauri har lokacin wayar na kare a kunnensa. Abee da Ummee da ke ankare da shi tun da ya fara wayar su ma miƙewar suka yi kusan a tare suna ci gaba da kallon sa. "Me ya faru?" Ummee ta faɗa bayan ta ƙarasa kusa da Farouk ɗin sosai tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa. "Ummee wai suna asibiti yanzu haka." Shi ne abin da ya iya faɗa kawai ganin gabaɗaya jiran ƙarin bayaninsa suke yi. Maimakon gabaɗayansu su ji farinciki da samun ɗiyar tasu, sai kuma hankali ya ƙara tashi. "Ni kam me ya samu ɗiyata? Ya Allah Ka rufa mini asiri, Ka taƙaita, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ummee ta faɗa tana jin wani sabon kukan na taho mata. "Ku wuce mu je." Abee ya faɗa bayan ya zari key ɗin motarsa. Babu musu suka rufa masa baya zuwa compound ɗin gidan. Farouk na gefen Ummee yana sake ba ta baki a kan ta yi haƙuri, don duk ta fi su ruɗewa. Sai dai in da za a tona zuciyar Farouk, Allah kaɗai Ya san irin yanayin da take ciki. Don dai kawai ya saba da shanye abubuwa ne, ya kuma saba da ajiye abubuwa cikinta, komai zafinsu kuma ta riƙe ba tare da sun bayyana a fuskarsa ba. Hakan ce ta faru yau ma, don kuwa cikin zuciyarsa shi kaɗai ya san abin da yake ji. Lokacin da suka isa asibitin, ya yi daidai da lokacin da iyalan gidan Shettima suka iso a nasu motocin har guda biyu. Kusan a tare suka wuce inda aka umarce su da su je. Tun daga nesa Farouk, Abee da kuma Ummee ke hangen ganin Janan, duk da an ce musu suna asibiti, amma idan dai har ba idanun Farouk ke ƙarya ba, ya hango wata zaune a bakin wani ɗaki sanye cikin uniform ɗin makarantarsu Janan ɗin. Ita ɗaya ce, babu wata ballantana ya ce Janan ce. 'To ina Janan ɗin kenan?' Ya tambayi kansa cike da mamaki. Cike da farinciki Umman Ammeey da tun daga nesa take hango kamar ɗiyarta ta tafi da sauri zuwa inda Ammeeyn ke zaune ta rungume ta. Lokaci guda ita da Ammeeyn suka fashe da kuka. Kukan da ya ankarar da su Ummee wanzuwar halittar da ke cikin irin uniform ɗinsu Janan. Wanda ba sai an tsaya yin bayani ba, hakan ya nuna ita ɗin ita ce wadda suka ɓata da Janan. To amma ina Janan ɗin take? Me ya sa ba su gan su tare ba? Me ya sa ita ɗaya ke zaune a wajen? Ina shalelen tasu? Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 12 A hankali Baba ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya hango Ammeeyn da ya yi jikin Umma tana ta kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa. Duk da yadda ya ji farincikin ganin ɗiyar tasa, to amma kukan da ya ga tana yi ya sa ya ɗan ji tashin hankali na neman ziyartar sa. Shin me yake faruwa? Mene ne ya sa Ammeeyn ke kuka? Mene ne kuma ya kawo ta asibiti? A hankali Baba ya ƙarasa inda suke ya ce "Kin ga ku yi shiru haka nan tun da Allah Ya sa ga ta a gabanmu. Ammeey." Ya ƙarasa maganar yana kallon Ammeeyn. "Na'am Baba." Ta amsa lokaci guda tana amfani da hannunta wajen share hawayen fuskarta. "Ki yi shiru kin ji?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin neman waje ya zauna. Da sauri mutumin da suka tarar tare da Ammeeyn ya ce "Haba Yallaɓai, ai bai kamata ka zauna a nan ba. Akwai wajen da za ku iya zama sai ku yi magana." Murmushi Baba ya yi kafin ya ce "Babu komai, nan ɗin ma ya wadatar." Ya ƙare maganar yana zama kusa da Ammeeyn. Abba da Daddy kowannensu kallon ta yake yi cike da farincikin dawowar ta, ta ɓangare guda kuma jira duk suke su ji me za ta ce. Ta ɓangaren Daddy yanayin yadda Baba ya tayar da hankalinsa bayan ɓatan Ammeeyn, hakan ba ƙaramin yi masa daɗi ya yi ba. Kodayake da ma ya san irin ɗimbin ƙaunar da yake yi wa Ammeeyn, shi ya sa

Chapter 8 of 24