asuba kai tsaye asibitin suka nufo. Lokacin da suka iso, sun samu kyakkyawan labarin cewar Janan ɗin ta farfaɗo tun cikin dare. Likita kuma ya ce a bar ta ta huta zuwa safiya kafin a gan ta. Don haka lokacin da suka iso, ya yi daidai da lokacin da za su iya shiga su gan ta.
A tare suka shiga, kowannensu idanunsa a kan gadon da Janan ɗin ke a kwance.
"Alhamdulillah." Ummee ta faɗa tana lumshe idanunta lokacin da ta hango idanun Janan ɗin da ba sa ɗauke da glass a buɗe tarr.
"Aysha." Ummee ta faɗa lokacin da ta ƙarasa kusa da Janan ɗin sosai. Ba ta san da shigowar su ba, kasancewar sama take kalla. Don haka tana jin muryar Ummee ta yi azamar tashi zaune tana yin amfani da hannunta wajen lalubo gilashinta. Runtse idanunta Ummee ta yi, a kullum a kodayaushe idan ta kalli idanun Janan ɗin, ko ta kalli yadda wani lokacin Janan ɗin ke wasu abubuwan kamar makauniya, tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Tana ji kamar ta zauna ta yi ta wa ɗiyar tata kuka. Tana ji tamkar akwai wata mafita da ta rage musu, ko da a ce idanun Janan ba za su dawo daidai ba, a ƙalla zuciyarta za ta samu salama. Ɗaukar glass ɗin da ke ajiye a gefe ta yi ta saka wa Janan ɗin. Daidai lokacin da ta faɗa jikin Ummeen ta fashe da kuka.
"Ummeena." Shi ne abin da kawai ta iya faɗa tana ci gaba da kukan. Rungume ta ita ma Ummeen ta yi ba tare da ta furta komai ba, don ba ta san me za ta ce ba. Ta kasa ganewa, shin fushi ya kamata ta yi da ɗiyar tata ko kuwa farinciki za ta yi da Allah Ya ƙwato mata ita tun kafin a yi nisa? Sun kai wajen mintina uku a haka kafin suka saki juna. Ummee ta nemi waje ta zauna. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta da suka sake ƙanƙancewa, suka kuma yi luhu-luhu ta kalli Abeenta da har zuwa lokacin bai ce da ita uffan ba. Da dashashshiyar muryarta da ta dashe ta buɗe baki da ƙyar ta ce
"Abee."
"Aysha." Ya faɗa yana iya ƙoƙarinsa don kar ya nuna ɓacin ransa. Don haƙiƙa idan ya ce ransa bai ɓaci ba ya yi ƙarya. Ya yi matuƙar mamakin yadda aka yi hakan ta faru, duk kuwa da irin killace ta da suke yi.
Ko Abeen bai faɗa ba, ta riga ta karanto fushin da yake yi da ita. Ita sai yanzu ma ta tuna da cewar ƙilan duk sun ji abubuwan da suka faru. Sun san komai, sun kuma san alaƙarta da Khaleed. To ita kam ina za ta tsoma kanta.
"Abee don Allah ka yi haƙuri, ka yi haƙuri ka yafe mini. Na yi laifi, na yi laifi. Ni me laifi ce, amma don Allah ka yi haƙuri Abee, kar ka yi fushi da ni." Girgiza kansa kawai Abee ya yi, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma can ya ce
"Wannan ita ce tarbiyyar da muka ba ki ko Ayshatou? Haɗuwa da namiji a wani waje ba tare da saninmu ba." Cikin tsananin tashin hankali take girgiza kanta hawayen da dama ƙiris suke jira suka soma sintiri a kan kuncinta.
"A'ah Abee don Allah ka yi haƙuri. Wallahi ba ita kuka ba ni ba, ban san yadda aka yi haka ta faru ba. Abee kar ka yi fushi da ni don Allah, idan ba haka ba zuciyata ba za ta iya jurewa ba. Abee don Allah ka ce ka yafe mini, ni kuma ba zan sake aikata abin da ba ka so ba. Abee na tuba na bi Allah.. Yah Farouk don Allah ka saka baki." Ta ƙare maganar tana kamo hannun Farouk da tun da aka fara magana bai ce komai ba. Bin hannun nasu ya yi da kallo, kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. To ta ina ma zai fara shi kam? Da wanne baki zai yi amfani wajen tausar su Abeen?
"Ki yi shiru ki daina kukan. Ran Abee a ɓace yake, idan ya soma hucewa sai ki sake ba shi haƙuri." Ya yi maganar bayan fitar da Abee ya yi, Ummee ma kuma ta bi bayansa. Sai ya miƙe shi ma da niyyar ficewa. Yau tabbas idan ba a yi wasa ba, za a iya tsintar gawarta, mene ne haka take gani? Shi ma Yah Farouk ɗin fushi yake yi da ita? To ina ta ga zuciyar da za ta iya jurewa? Ina ta ga ƙwarin gwuiwar da za ta iya ɗaukar duk waɗannan? Ko za ta iya jure fushin kowa ai ba ta tunanin har da na Yah Farouk.
"Yah Farouk." Ta ambaci sunansa a hankali jajayen laɓɓanta da suka sake yin jajir har wani karkarwa suke yi. A hankali ya juyo ya kalle ta bai ce komai ba.
"Kai ma fushin kake da ni ko?" Ta yi tambayar da take cike da jin tsoron jin amsarta. Murmushi Farouk ya yi kafin ya dawo kusa da gadon nata, cikin kwantar da murya ya ce
"Ya za a yi na yi fushi da ke? Ki kwantar da hankalinki ki samu nutsuwa uhmm? Abee da Ummee duk za su yafe miki, kawai sun ji babu daɗi ne a kan abin da kika aikata. Ni da kuma ke duk mun san ba ki kyauta ba. Amma za mu taushe su har su haƙura, amma sai kin yi alƙawarin wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba." Da sauri ta shiga kaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa.
"Eh Yah Farouk na yi wallahi." Numfashi ya sauke sannan ya ce
"Shi kenan.." Sai ya nemi waje ya zauna. Kifa kanta a kan cinyarta Janan ta yi, ta ci gaba da kukan da bai ishe ta ba. Ta rasa da wanne za ta ji. Da rashin Khaleed ko kuma fushin da iyayen nata ke yi da ita?
Wajen ƙarfe 8 aka turo ƙofar ɗakin. Farouk da bai daɗe da dawowa cikin ɗakin ba ya ɗaga idanunsa ya kalli mai shigowar. Amsa sallamarsa ya yi lokaci guda yana so ya ga ko ya san shi. Matashi ne dogo mai ɗan murjajjen jiki. Yana sanye cikin manyan kaya na shadda da ta karɓi jikinsa, da wata ƙatuwar leda a hannunsa.
"Sannu Aysha." Ya faɗa bayan ya ƙarasa inda take zaune. Sai kuma a sannan ya miƙa wa Farouk hannunsa yana mayar da dubansa kan Janan da ke kallon sa ita ma ba tare da ta shaida fuskarsa ba. Irin kallon da take yi masa shi ya tunasar da shi ba ta san fuskarsa ba. Don haka ya yi murmushinsa mai kyau kana ya ce
"Afuwan, na manta ba ki shaida fuskata ba. Ni ne wanda na kawo ku asibiti. Na koma gida jiya saboda wani kiran gaggawa da aka yi mini. Sai dai na kasa samun sukuni, shi ya sa na ga ya dace na sake dawowa na ga jikinki." Ya ƙare maganar idanunsa a kan Janan. Sai a lokacin sannan ta ƙaƙalo murmushi ta wanzar a kan fuskarta ta ce
"Na gode."
"Haba!!" Ya faɗa yana murmushi. Hannu Farouk ya miƙa masa yana murmushi shi ma ya ce
"Muna godiya sosai. Allah Ya saka da alkairi."
"Haba kai kuwa, idan kuna haka sai na dinga jin wani daban. Babu wani abu fa." Adam ya faɗa har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Komawa Farouk ya yi ya zauna bayan ya gyara masa kujerar da ke gefe. Babu musu ya nemi waje ya zauna. Bayan wajen shuɗewar mintina uku babu wanda ya ce uffan. Har zuwa lokacin da Janan da ke ta mutsu-mutsu a kan gado ta zuro ƙafarta ƙasa. Ba ta lura ba, lokacin da ta ida sakkowa ƙafarta ta ɗan gurɗe saboda jikinta da ya ɗan yi rauni. Adam da ke kusa da ita shi ya yi saurin miƙewa da niyyar taro ta don kar ta faɗi lokaci guda yana faɗin
"Yi a hankali kar ki ji ciwo."
"Heyy." Muryar Farouk ta doki dodon kunnensa, daidai lokacin da Janan ta tsaya a kan ƙafafunta. Idanunsa ya sauke a kan Yah Farouk ɗin da bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba, bayan da ya dakata daga ƙoƙarin taro tan da yake yi. Bai gane ba, bai kuma fahimci irin kallon da yake yi masa ba, sai dai ta ɓangare guda, kamar ya so ya yi kama da kallon nan irin na gargaɗi. Daga shi har Farouk ɗin babu wanda ya ce ko uffan, har zuwa lokacin da ya ƙarasa kusa da Janan ɗin sannan ya dubi Adam ya ce
"Ɗan matsa mu ga." Ya yi maganar yana kafe shi da idanunsa. Shi ma kafe shi ya yi da nasa idanun sai kuma ya aikata abin da Farouk ɗin ya umarce da yi, lokaci guda yana sauke ajiyar zuciya. Duk da yanayin mutumin ya nuna yana da nutsuwa, babu kuma alamar yana da hayaniya ko wata damuwa, amma shi dai Farouk haka nan kawai ya ji ya kasa sukuni da zuwan mutumin. Yana lura da yadda yake ta satar kallon Janan, musamman lokacin da suka yi shiru. Yana kuma lura da yadda yake ta wani rawar jiki tun bayan shigowarsa ɗakin. Ko kaɗan sai ya ji bai yi masa ba. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa lokaci ɗaya yana cizar laɓensa na ƙasa.
"Ummee an sanar wa da makaranta ko?" Janan ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin zama cikin motar da za su tafi gida bayan sallamar ta da aka yi.
"Wacce makarantar?" Ummee ta tambaya ba tare da ta kalle ta ba. Cike da mamaki Janan ke kallon Ummee. Wacce makaranta kuma? Da ma akwai wata makarantar da take zuwa ne wadda Ummee ba ta sani ba? To saboda ta kawar da shakkun da ta shiga sai ta ce
"Duka Ummee, har da islamiyya." Shiru Ummee ta yi na tsawon sakanni ba tare da ta ce komai ba, ita kuma Janan ta kafe ta da idanu tana jira ta ji abin da za ta ce.
"An sanar a islamiyya, ita kuma makarantar da kike magana a kai, ci gaba da zuwa za ki yi ne? Ko kin manta alƙawarinku da Abee? Aysha kin yi matuƙar wasa da damarki, har ta kai ga kin manta da irin alƙawarin da kika yi mana. Saboda haka, zancen makaranta kuma ya ƙare." Ummee ta yi maganar ko kaɗan ba tare da ta bari ta kalli ɗiyar tata ba. Don ita kanta shaida ce a kan irin tsananin son karatun da Janan ke yi. Tana matuƙar ƙaunar karatunta yadda babu wanda zai yi tunani. Tana so ta gaje ta, ita ma kuma tana yi mata fatan har ma ta fi ta. To amma yanzu da kanta ta saka ƙafa ta yi fatali da wannan damar. Shiru Janan ta yi tana kallon Ummeen cikin rashin fahimta. Anya kuwa ta fahimci abin da Ummeen ke faɗa? Ko kuwa wani banzan tunani ne ke son ɗarsuwa a ƙwaƙwalwarta har ya kai ga tana yi wa maganganun Ummeen wata fassara daban? Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci maganganun Ummeen suka ci gaba da dukan dodon kunnenta, wanda hakan ya tilasta mata runtse idanunta lokaci guda ƙwaƙwalwarta na tabbatar mata da cewar abin da kunnuwanta ke jiye mata, su Ummee take faɗa. To kenan me ake so a ce mata tana ƙoƙarin yi? Khaleed ɗin da ta yi wasa da karatunsa don kar ta rasa shi ya guje ta. Shi ma kuma karatun da ta yi sakaci da Khaleed a kansa ana nema a ce mata ta rasa shi? Kenan me ta yi? Ina ake so ta tsoma rayuwarta ta ji daɗi? Ta yaya ma za ta iya rashin abu biyun nan lokaci guda? Babu Khaleed babu karatun? Ai zuciyarta ba ta da wannan ƙwarin. Ba za ta iya jurewa ba, tana da tabbacin da gasken gaske za ta iya yin bindiga. Ya ma take ji ne lokacin da ta fahimci Khaleed ya guje ta, ballantana yanzun da take ganin ta rasa har karatun nata ma da take matuƙar ƙauna? Ina.. ba za ta iya ba.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 14
Har suka ƙarasa gida babu wanda ya sake cewa komai. Ita dai Janan tana gefe a takure, hawaye ne kawai ke sauka a kan kuncinta. Don tuni muryarta ta yi dashewar da sautin kukan ya daina fita. Ban da wani irin zafi babu abin da zuciyarta ke yi. Ita ta san tabbas yau za a iya wayar gari a gan ta a mace.
Ko da suka isa gida ma kai tsaye Abee ɗakinsa ya wuce, dukkansu bin sa suka yi da kallo kafin Farouk da Ummee suka dawo da dubansu kan Janan da ta kife kanta a jikin kujera tana jin wani sabon na taho mata. To ita kam ina za ta sanya kanta ta ji daɗi?
"Aysha, ki je ki watsa ruwa ki kwanta ki huta. Zuwa an jima za mu yi magana, za kuma ki je ki ba wa Abee haƙuri, ko a samu ya sakko. Don ko bai faɗa ba, dukkanmu mun san ya yi fushi."
"To Ummee." Ta faɗa bayan ta ɗaga idanunta lokaci guda tana jinjina kanta.
Parking ɗin motarsa ya yi a inda aka tanada don ajiye motoci. Numfashi ya sauke kamar wanda ke a gajiye. Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi lokacin da ya tuna bai san me zai je ya tarar a gidan ba. Tun rana ya kasa sukuni, ya rasa inda zai tsoma kansa ya ji daɗi. Tun bayan da ya tafi wajen aiki daga asibiti wajen Janan, sai ya kasa sukuni. Gabaɗaya ya rasa me ke masa daɗi. Komai yake yi sai ta faɗo masa, fuskarta, muryarta da komai nata. Daga ƙarshe da ya ga yana ƙoƙarin yin shirme sai ya ajiye aikin gabaɗaya.
"Aysha." Ya ambaci sunan a kan laɓɓansa cikin rashin sanin abin yi. Daga ƙarshe dai da ya ga abin na neman fin ƙarfinsa, sai kawai ya saɓi jiki ya tafi asibitin, cike da burin ko da na mintina kaɗan ne ya samu ya yi magana da Janan ɗin. Ya ji muryarta, ya sake ganin fuskarta sosai ba a cikin takura ba. Don tarar da Farouk da ya yi a ɗakin ba ƙaramin taka muhimmiyar rawa ya yi ba wajen ƙin sakin jiki ya kalli fuskar tata da zuciyarsa ke ta muradi. Tun bayan da ya ɗauke ta ya kai ta asibiti sai ya rasa sukuni. Zuciyarsa har wani zillo take yi. Ba don ya so ba, sai don ya zama dole, ya tafi ya bar ta cikin asibitin. Sai dai ko daidai da minti ɗaya bai samu ya rintsa ba. Ba zai iya jure rashin wannan halittar ba. Ba zai iya yi wa zuciyarsa rashin adalci a karo na barkatai ba. Dole ya samar wa kansa mafita. Ya gan ta, ya ji yana son ta. Ba kuma da niyyar komai ba sai don ya aure ta. Ya kuma shirya karɓar kowanne irin ƙalubale ne da zai tunkaro shi a bisa neman aurenta da zai yi. Ko ma mene ne zai karɓa, shi dai kawai yana son Aysha, yana kuma so ya aure ta. Lokacin da ya isa asibitin ya samu su Janan ɗin sun tafi gida. Cike da tashin hankali da fatan kar ya rasa muradin zuciyar tasa da cikin ƙanƙanin lokaci ta tafi da shi, take kuma nema ta hana masa sukuni. Ya nemi da a sanar da shi inda suke, amma bai samu ba. Ya shafe fiye da awa a asibitin amma bai samu takamaimai inda zai same ta ba. Daga ƙarshe abin da ya fahimta, kamar akwai wani abu da ya sa ba sa so su faɗa masa inda zai samu Janan ɗin. Amma bai san mene ne ba, don haka ya kuɗuri aniyar dole zai sake dawowa don ya kuma neman inda zai same ta, ko da hakan zai sa zuciyarsa ta samu sukuni. Sai dai duk wannan uban alwashi da ya ci sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci yana nema ya tashi a banza. Don kuwa yana tsintar kansa cikin gidan, ya ji faɗuwar gaba ta ziyarce shi kamar kullum kamar kuma kodayaushe. A nutse ya saukar da ƙafarsa daga cikin motar yana kiran sunan Allah, kai tsaye ya wuce cikin gidan nasa.
Matashiyar mace ce tsaye sanye cikin riga da wando palazzo, kanta sanye cikin hula, wadda ta ɗan zame ta, hakan ya ba wa gashin kanta damar fitowa, wanda ya ƙawatu da ƙananan kitso irin sosai ɗin nan. Tun da ya shigo ɗakin take kallon sa, ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba. Bai damu da hakan ba ba kuma tare da ya kalle ta ba ya soma ƙoƙarin shige ta, tun da bai samu ko darajar amsa sallama ba ne, ballantana ta kai ga an yi masa sannu da zuwa.
"Ina za ka je Adam?" Ta yi azamar faɗin hakan kamar a tsawace, kai sai ka ɗauka irin uwar nan tasa ce. Kamar ba zai tsaya ba, kamar kuma ba zai tanka ba, sai ya juyo shi ma fuskarsa a ɗinke kamar yadda tata take ya ce bayan ya kafe ta da idanunsa.
"Inda kika aike ni." Cike da mamaki ta taka ta sake matsawa inda yake ta ce
"Ba zai yiwu ka zo ka gan ni a nan ka wuce ni ba. Ka tsaya ka yi mini bayanin inda ka je jiya ka daɗe, sannan kuma yau da sassafe ka fice daga gidan nan ba tare da ko karyawa ka yi ba. Wallahi ba zan ɗauki wannan cin kashin ba, dole ka yi mini bayani ko kana so ko ba ka so."
Murmushin gefen baki Adam ya yi, shi da ma ya san dole sai wani abu ya faru. Nafisa ta kasance wata irin mace ce mara kan gado, wadda ko kaɗan ba ta san yadda za ta yi ta tarairayi mijinta ba. Akwai wani abu guda ɗaya da ya kasance kullum sai ya ji shi, wato faɗuwar gaba. Duk lokacin da zai tunkaro gidan sai ya ji hakan ya ziyarce shi, don bai san idan ya shiga gidan me zai tarar ba. Duk da wasu lotukan da dama maganganun Nafisan na tasiri a kansa har ta kai ga yana ɗan jin shakkarta a kan wasu abubuwan. Ta gefe guda kuma da ya kasance Nafisan ba ta da sirri ko kaɗan. Tun bayan aurensu, burinta wani abu kaɗan ya haɗa ta da shi ta ɗauki waya ta kira mahaifiyarsa ta sanar da ita, komai kuma ƙanƙantar abu ba ta gajiya. Jiya ma daɗewar da ya yi a asibiti wajen Janan, ita ta kira Umman ta shi ta sanar da ita, shi ne ita kuma ta kira shi a kan tana son ganin sa cikin gaggawa.
"Haka kika ce?" Ya faɗa har lokacin idanunsa cikin nata.
"Eh." Ta faɗa ba tare da ta ji ɗarr ba har kuma lokacin ba ta janye idanunta daga cikin nasa ba.
"Ya yi.." Ya faɗa yana ɗaga kafaɗarsa, daga haka ya yi gaba.
"Adam! Adam! Adam!" Ta shiga faɗa cikin ɗaga murya. Sai dai ko kaɗan bai nuna ma ya ji tana kiran nasa ba ballantana ya juyo. Shin me yake faruwa da ita ne? Anya kuwa Adam ɗin ne wannan? Wai me ya sa ita kodayaushe abubuwa ke zuwa mata a bai-bai. Daga zarar ta fara cin karenta babu babbaka sai kuma abu ya zo ya juye? Yanzu me take gani haka? Tana masa magana yana mayar mata ba tare da ya ji ko ɗarr ba? 'Lallai akwai matsala' Ta raya hakan cikin zuciyarta tana bin inda ya bi da kallo. Kamar wadda za ta tashi sama haka ta ɗaga ƙafa ta bi bayansa. Lokacin da ta shiga ɗakin ya shiga banɗaki, don haka kai tsaye inda wayarsa take ta nufa zuciyarta na ci gaba da wani irin tafarfasa. Kai tsaye jerin kiraye-kirayen da ya yi ta shiga ta soma dubawa. Cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta soma bugawa, don tsoro take yi kar ta ga abin da zai iya zama barazana ga lafiyarta. Cike da takatsantsan take ci gaba da dubawa. Sai dai ba ta ga wata sabuwar number ba. Duk jerin waɗanda suka yi waya ta san su. Don ba ta taɓa barin sabuwar number a wayar Adam ɗin ba tare da ta san me ita ba. Ko da da wani sunan ya yi saving, zuciyarta ba ta taɓa amincewa, hankalinta kuma ba ya taɓa kwanciya har sai ta ɗauka a wayarta ta duba don tabbatarwa. Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya tana neman waje ta zauna. Kai ko kaɗan fa ita ba ta yarda da Adam ba. Ina ya je jiya ya kai irin wannan daren? Ya dawo kuma har safiya bai rintsa ba ko da na minti ɗaya ne. Safiya kuma na yi ya fice daga gidan ba tare da ya karya ba. Dole ma akwai wani abu da yake ɓoyewa. 'To ko dai ya faɗa soyayya ne da wata?' Ta tuhumi kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta shiga girgiza kanta, babu wata mace da za ta shiga rayuwar Adam ɗinta. Adam nata ne ita ɗaya, babu wata mace da za ta iya rabawa da shi. Tana masifar son Adam, tana matuƙar ƙaunar Adam, irin mahaukaciyar ƙaunar nan da komai za ta iya yi a kansa. Shi ne dalilin da ya sa take bibiyar duk wani takunsa, komai take idanunta na kansa, tana sane da abin da yake yi, don ba ta so ta yi sake ko da na second ɗaya ne wata ta zo ta ƙwace mata shi. Don idan dai har hakan ta faru, ta yi wa kanta alƙawarin ko ta halin yaya ne sai ta zamo sanadiyyar lalata rayuwar duk wadda ta shiga sha'anin mijinta. Duk wata mace da ta ce za ta shiga gonar Adam ɗin, ko kuma shi da kansa ya jawo ta cikin rayuwarsa, to tabbas ba za ta bar ta ba. Sai ta saka an nemo mata duk inda take ta lalata rayuwarta.
Tana zaune riƙe da wayar a hannunta ya fito. Ba ta damu da ya gan ta ko bai gan ta ba. Ta miƙe haka nan kawai tana jin ɓacin rai ta ajiye wayar tana ficewa daga ɗakin ba tare da ta kalle shi ba. Bin ta ya yi da kallo, bayan ya sauke towel ɗin da yake goge fuskarsa. Sai ya dawo da dubansa kan wayarsa da ke yashe a wajen ya saka hannu ya ɗauka. Ko ba a faɗa ba, ya san bincike ta yi masa, don ya riga ya san halin Nafisa in dai wajen bincike ne. Kuma ko ɗarr ba ta ji, ba ta damu da ya gan ta ba. Sai dai komai rashin kunyarta sai ba ya wajen sannan take yi. Ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa yana jin ya zama dole ya ɗauki matakin da ya dace a kan Nafisar saboda wannan binciken da take yi masa. To amma kullum haka yake ji, sai dai ba ya wani iya taɓuka abin arziƙi sai faɗar. Don haka ya ajiye wayarsa kai tsaye ya tafi ɗaukar kaya cike da tunanin yadda za a yi ya samu Janan.
Har ya shiga cikin motar yana ƙoƙarin tada ita, Ammeey ta fito daga sashensu Al-ameen ta ƙaraso tana faɗin
"Yah Al-ameen, Mama na kiran ka." Iska ya fesar daga bakinsa sannan ya ce
"Kai! Mama." Sai kuma ya ajiye wayarsa sannan ya kalli MuhammadAali ya ce
"Minti biyu please." Jinjina kai kawai Muhammad ya yi yana ɗaga kafaɗarsa. Daga haka ya wuce da sauri.
"MuhammadAali." Saleem ya faɗa daga inda yake zaune a bayan motar shi ɗaya. Shiru Muhammad ya yi kamar ba a kira sunan wata halitta ba. Saleem ya yi murmushi sannan ya
"Muhammad."
"Uhmm." Ya amsa ba tare da ya kalle shi ba.
"Ina ganin fa kamar na faɗa ƙaunar Ammeey." Ya yi maganar yana ɗan sosa gashin kansa. Da sauri Muhammad ya juya ya kalli abokin nasa, abokin da saboda tsananin ƙauna da shaƙuwa har ta kai ga wasu suna zaton 'yan gida ɗaya ne, don an ce har wata kama suke yi.
"Wait? What did you just say?" Numfashi Saleem ya sauke sannan ya ce
"Na san ka ji.. Da gaske kamar ina son Ammeey ne." Bai san lokacin da dariya ta ƙwace masa ba.
"So? Wasa kake amma?" Muhammad ya faɗa da iya gaskiyarsa yana kallon Saleem ɗin. Sai da Saleem
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 24