wa Yah Farouk ɗin yadda take jin Khaleed ko kuwa? Anya kuwa idan ta yi hakan ba ta yi rashin kunya ba? To amma ya za ta yi? Wannan ce kuma damar da take da ita da za ta fitar da sirrin zuciyarta ga wanda take da tabbacin zai iya samar mata mafita. Sai da ta ciza, ta ɗame ranta, ta yi futu-futu da zuciyarta sannan ta ce
"Yah Farouk ina son zama babbar 'yar jarida, shi ne dalilin da ya sa nake son karatuna. To kuma Abee ya ce sai na gama karatu ko da zai yi mini..." Sai ta ɗan dakata a nan tana cuna bakinta kafin ta ɗora da
"Aure.. Ba kuma ya so in kula kowa da sunan soyayya. Idan dai har ya ga saɓanin hakan, to tabbas ƙarshen karatuna ne ya zo. Ni kuma ba na so hakan ta faru. Shi ne ma dalilin da ya sa na zaɓi haɗuwa da Khaleed a wani waje ba tare da sanin ku ba. Amma wallahi Yah Farouk ina son Khaleed, ina son shi sosai. Ba zan iya rabuwa da shi ba, kuma ina matuƙar ƙaunar karatuna, shi ya sa na rasa me ke yi mini daɗi."
Duk da ta ida maganar, ta kuma kai gaɓar da ya dace Yah Farouk ya ce wani abu, amma sai ta ji shiru bai ce komai ba har bayan wajen minti ɗaya. Dalili kenan da ya sanya ta kallon shi ta kira sunansa a nutse. Sai a lokacin sannan ya sauke gajeren numfashi kafin ya ce
"Na fahimce ki Janan, abu ɗaya nake so da ke, ki ba shi numberta ya kira ni. Ina so za mu yi magana."
Cike da tantamar wannan ɗin muryar Yah Farouk ce ta kalle shi, don sosai ta yi mamakin yadda muryarsa ta sauya. Sai dai abin da ya faɗa ɗin ya yi nasarar danne kaso tamanin na mamakin da ta yi. Cikin tsananin farinciki ta shiga faɗin
"Na gode sosai Yah Farouk ɗina. Allah Ya bar mini kai." Ta faɗa tana ji kamar ta taka rawa. Ba don ya ce ta girma ba, da babu abin da zai hana ta rungume shi a yanzun.
Murmushi kawai ya yi mata yana jinjina mata kai. Ba ta damu da ya ce wani abu ba, ta fice daga ɗakin cikin tsananin farincikin da ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarta har ma da motsinta.
Washegari.. Tun da ta shigo yake lura da yanayinta. Duk da kasancewar yau ɗin ya shigo gari, hakan bai sa Ummee ta dawo gida da wuri ba, ballantana kuma wannan kazar-kazar ɗin nata musamman idan ya dawo daga tafiya.
"Kin ga Nafisa nemi waje ki zauna." Ya faɗa lokacin da take ƙoƙarin serving nasa abinci cikin wani plate. Kallon Abee Ummee ta yi cike da mamakin abin da ya ce. Sai ya jinjina mata kai alamar tabbatar da abin da ya faɗa. Hakan ne ya sa ba ta sake cewa komai ba ta nemi waje ta zauna.
"Me yake damun ki?" Ya tambaya kai tsaye. Bai ba ta damar yin musu ba lokacin da ta ɗaga idanunta ta zuba masa su. Hakan ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
"Daga wajen aiki ne."
Numfashi Abee ya sauke, da ma ya san za a rina, ya kuma tabbatar daga wajen aiki ne.
"To wai ni kuwa Nafisa anya kuwa ba ajiye aikin nan za ki yi ba?" Ya faɗa babu wasa ko kaɗan cikin maganarsa. Da sauri ta sake ɗaga kanta ta kalle shi.
"Abee ajiye aiki kuma? Me ya yi zafi?"
"In dai har za ki ci gaba da dawowa a irin yanayin nan, to tabbas za a wayi gari in bijire har sai kin ajiye musu aikinsu." Ya ba ta amsa kai tsaye. Zazzafan numfashi ta fesar daga bakinta tana sauke hannunta da ke ɗore a kan goshinta ta ce
"Ba wai a kan aikin ne gabaɗaya ba. A'ah, wani program ne aka yi mini magana a kansa wai zan fara gabatarwa. Babban abin da ya shigar da ni cikin damuwa, shirin na ɗauke da ƙalubale. Amma fa ba dole aka yi mini ba, tayi aka yi mini. Idan har zan iya ana jiran amsata gobe. Idan kuma ba zan iya ba shi ma in sanar da su."
Jinjina kansa Abee ya yi bayan gama jin maganganun Ummeen. Sai kuma ya yi murmushi kafin ya ce
"Yanzu wannan ne silar shigar ki damuwa?"
"Abee ambatar ƙalubalen da suka yi shi ya jefa ni a damuwa. Ta ɓangare guda kuma kamar wannan ɗin dama ce a gare ni, domin ni aka fara tuntuɓa saboda yadda da aikina."
A nutse Abee ya kamo hannun Ummee cikin nasa, ya soma faɗin
"Kamar ko don hakan ya dace ki karɓi shirin. Da ma ku ai koyaushe cikin ƙalubale kuke. Kenan wannan ma sai ki saka hannu bibbiyu ki tarbe shi kamar yadda aka saba. Ke da kike da Allah." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana jin yadda ta gamsu da abin da ya faɗa ɗin, sai dai har zuwa lokacin ƙwaƙwalwarta ta kasa hutawa da daina tunasar da ita ƙalubalen da suka ambata.
A yi maneji da wannan 🤧
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 08
"Kana ganin zan iya?" Ta tambaya kai tsaye tana kallon sa.
"Ƙwarai kuwa, na yarda da ke in sha Allah za ki iya. Kar ki karaya tun yanzun." Hakan da ya sake faɗa shi ne abin da ya sa ta ji hankalinta ya ɗan kwanta. Sai ta yi ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta lokaci guda tana furta
"In sha Allah."
Ko da Farouk ya shigo ɗakin, ya tarar da su ne suna ci gaba da tattaunawa a kan wannan maganar. Tashin farko shi ma goyon baya ya ba wa Ummeen yana sake jaddada mata cewar za ta iya.
"Ummee idan dai har ba shiri ne da ya saɓa wa addini ba na san za ki iya. Kawai ki ce kin amince, don wannan ɗin kamar dama ce Allah Ya sake ba ki. Muna miki fatan Allah Ya ba da sa'a, Ya sa a fara a sa'a Ya kaɗe fitina."
Ba ƙaramin kwanciya hankalinta ya yi ba, Abee da kuma Farouk sun matuƙar ƙara mata ƙwarin gwuiwa. Don haka gabaɗaya sai ta saki jiki, ta daina jin ɗar-ɗar ɗin da take ji. Hakan ba ƙaramin faranta wa Abee ya yi ba, suka ci gaba da hira.
Washegari Farouk da wuri ya gama shiri, don ya san tun da Abee na nan shi zai kai Janan makaranta. Sai dai kuma yana so ya kai ta da kansa, ya kuma sake jaddada mata magana a kan Khaleed da kuma Fa'iza. A parlour ya samu Ummee, Janan har ma da Abee suna karyawa. A nutse ya ƙarasa hannunsa ɗauke da key ɗin motarsa ya nemi waje ya zauna. Cikin girmamawa ya gaishe da iyayen nasa sannan ya ɗan saci kallon Janan da ke ci gaba da cin abincinta.
"Good morning Janan." Ya faɗa cikin basarwa. Dariya ce ta ƙwace mata bayan ta kalle shi, sai kuma ta dakata da cin abincin da take yi ta ce
"Barka da safiya Yah Farouk."
"Barka dai.. Ci abincinki ki gama kar na makara." Ya yi maganar yana juya hannunsa ya kalli agogon da ke ɗaure a kan tsintsiyar hannunsa.
"Abee ka sake hutawa yau ma, zan ajiye maka shalelen taka a makaranta." Girgiza kai Abee ya yi kafin ya ce
"Wato kai so kake ka ƙwace wannan nauyin nawa na kai Janan makaranta bayan aikina ne ko? Zan jira Ayshatou har ta gama abin da za ta yi mu je in kai ta." Dariya dukkansu suka yi saboda yadda Abeen ya yi maganar ya ba su dariya. Ɗan shafa sumar kansa Farouk ya yi kafin ya ce
"Abee daga abin arziƙi?" Ya yi maganar har da langaɓar da kai. Nan ma dai dariyar suka yi dukansu. Zuwa can Janan ta ce
"Abee na gama." Ta faɗa bayan ta miƙe. A nutse Farouk ya ɗaga idanunsa ya sauke su a kanta jin abin da ta ce. Wato shi za ta gwasale ko?
"Oh..ya yi" Ya faɗi hakan yana taɓe baki. Sai kuma ya miƙe ya kalli Ummee ya ce
"Ummee bari na je. Abin arziƙi bai karɓe ni ba." Dariya Ummee ta yi kafin ta ce
"Yau kuma ganin ku za a yi a rana? Kar ka saka in yi muku dariya mana."
"Ke maza bi yayanki ya sauke ki a makaranta." In ji Abee.
"Ai kuma Abee na fasa. Sai dai ta nemi mai kai ta." Ya faɗa yana watsa mata harara. To ita ba ma sai yanzu ta tuna ya yi maganar zai kai ta makaranta ba, kuma da ta gama ta cewa Abee ta gama. Ita shaff ta manta.
"To Abee ka ji fa zai wulaƙanta ni."
"Ni kuma ba zan yarda a wulaƙanta mini shalele ba. Bari na tashi na ci gaba da aikina." Abee ya yi maganar yana murmushi lokaci guda yana ƙoƙarin miƙewa. Hannunsa Farouk ya yi amfani da shi wajen nuna alamar zauna kafin ya ce
"A'ah, tun da ka matsa dai bari na taimaka na ajiye ta." Ya yi maganar cikin basarwa, shi a lallai dole yana nufin abin da ya faɗa. A wannan karon dariya sosai Ummee ta yi, Abee na taya ta. Ƙarasawa Janan ta yi ta ɗauki jakarta ta saka sannan ta dawo tana faɗin
"Ummee na tafi.. Abee na tafi.." Daga haka ta yi gaba Farouk na gabanta. Sai da suka kusa fita daga ɗakin sannan ya ce
"Ke ɗaya ce ne da za ki wani ce kin tafi?" Turo bakinta ta yi, don ta lura yau ɗin kamar Yah Farouk ɗin da rigima ya tashi. Don haka da kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce
"Kai Yah Farouk na fa ba ka haƙuri." Bai san san da murmushi ya suɓuce masa a kan laɓbansa ba, don ya fahimci abin da take nufi. Ya girgiza kai kawai daidai lokacin da yake shiga motarsa.
Sai da suka fara tafiya sannan ya ce
"Aysha." Kallon sa ta yi kafin ta ce
"Na'am Yah Farouk."
"Ina so na ba ki wani umarni." Cikin azama ta ɗaga idanunta ta kalle shi, ya jinjina kai kafin bai ce komai ba ya ci gaba da driving.
"To Yaya." Ta ba shi amsar tana ɗan ƙiƙƙifta idanunta cikin glass.
"Daga rana irin ta yau, ba na so na sake ganin ki tare da Fa'iza." Ba ta san lokacin da ta sake kallon sa ba, tashin hankali na bayyana a kan fuskarta. Bai ce da ita komai ba, bai kuma kalle ta ba duk da ya san kallon sa take yi. Har zuwa bayan shuɗewar wajen mintina biyu ya jiyo muryarta can ƙasa
"Yah Farouk ka ce kuma in ba shi number ɗinka ya kira ka. Idan ba na tare da Fa'iza ba zan samu wannan damar ba." Ajiyar zuciya ya sauke, ko a nan tunaninsa ya zama gaskiya. Lallai da gaske Fa'iza giɓi ce a cikin rayuwar 'yar'uwarsa.
"Shi ya sa na ce daga rana irin ta yau." Tana ƙoƙarin yin magana ya yi saurin katse ta da faɗin
"Idan dai har ba to za ki ce ba, ba na son jin kowacce magana daga bakinki."
Komawa ta yi ta kwantar da jikinta a kan kujerar da take kai. A hankali ta ɗan zare glass ɗinta ta goge ƙananan hawayen da suka maƙale a cikin idanun nata sannan ta yi ƙarfin halin faɗin
"To Yah Farouk."
Bai ce da ita komai ba, ya ci gaba da abin da yake yi. Zai gani idan har tana jin maganarsa za ta ɗauki hakan, idan kuma ba ta ɗauka ba, to tabbas zai ɗauki mataki.
A ɗaya ɓangaren kuwa tsaki ya ja a karo na barkatai lokacin da ya ga wani kiran ya sake shigowa cikin wayarsa. Sai ya saka hannunsa ya janyo wayar lokaci guda yana kallon fuskar wayar. Da sauri ya tashi zaune, ganin sunan amininsa ya bayyana a kan wayar. Kara ta ya yi a kunnensa lokaci guda yana miƙewa tsaye.
"Hello." Daga can ɓangaren aka faɗa.
"Sorry Man.. Gabaɗaya na manta za ka kira ni."
"Ba don na san waye kai ba da sai in ce don ba ka ɗauke ni da muhimmanci ba ne." Leɓensa na ƙasa MuhammadAali ya ɗan ciza lokaci guda wani miskilin murmushi na suɓuce masa ya ce
"Saleem."
"Kar ka wani kira sunana malam. Za ka zo to ko in hau adaidaita?"
"Je ka hau." Ya yi saurin faɗin hakan yana katse wayarsa lokaci guda yana girgiza kansa. Sauri ya yi ya ƙarasa shiryawa kamar koyaushe cikin shigar ƙananan kaya da suka matuƙar amsar jikinsa. Da ma shirin fitar yake yi, sai kuma wani abu ya ɗauke masa hankali. So yake ya taya mahaifinsa bincike, don ko kaɗan zuciyarsa ta kasa sukuni da abubuwan da ke faruwa. Sai yake ganin kamar akwai wani abun a ƙasa, don haka ta ɓangarensa ma zai taya Baban bincike. Tsaf ya fito ya yi kyau matuƙa. MuhammadAali fari ne, irin farin nan mara hayaniya mai kyau. Yana da tsayi da jiki irin na ƙarfi, wanda ɗaga ƙarfe ya sake murɗe masa jiki. Abubuwa masu matuƙar jan hankali a fuskarsa su ne idanunsa, ba wani girma gare su ba, sai dai tsananin kyawunsu ya girmama. Dogon hanci gare shi wanda ke saman jajayen ƙananan laɓɓansa. Kai tsaye motarsa ya nufa don zuwa ɗauko abokinsa da yau ya sauka a garin, ya kuma saba duk lokacin da ya sauka, a gidansu yake zama, kasancewarsa amininsa na ƙut da ƙut wanda jinin wani ɗan adam bare bai taɓa zuwa ɗaya da na MuhammadAali kamar yadda ya zo da nasa da Saleem ba. Hakazalika hatta Baba yana son alaƙar Saleem da Muhammad, saboda ya yarda da tarbiyyar yaron matuƙa. Shi kuma ya nemi ya dinga zama a gidan duk lokacin da ya shigo garin nasu.
A ɓangaren Janan kuwa, duk yadda ta yi ƙoƙari wajen ganin ba ta haɗu da Khaleed ba ta sanar da shi saƙon Yah Farouk a waya hakan ya gagara. Da Allah da Annabi haka ya dinga haɗa ta da shi, har sai da ya ci galaba a kanta ta amince za su haɗu yau ɗin bayan an tashi daga islamiyya.
Cike da marmarin ganin sa take takawa zuwa inda ta san yana jiran ta, wato inda suka saba haɗuwa. Tun yanzu har ta fara jin kewa, don tabbas za ta bi umarnin Yah Farouk, kamar kuma yadda ta yi masa alƙawari, ba za ta sake haɗuwa da shi a wani waje ba, za ta cika wannan alƙawarin. Kamar yadda suka saba gaisawa, haka suka gaisa yau ma cike da marmarin ganin juna. Sai dai kamar koyaushe zumuɗin Khaleed ya fi nata yawa.
"Da ma wani abu zan faɗa maka, shi ya sa ma na kira ka a waya."
"Ai tun da kika ce mini muhimmiyar magana ce na kasa sukuni, shi ya sa na ga gwara mu haɗu mu yi maganar sai ya fi hankali kwance." Khaleed ya ba ta amsa yana murmushi.
"Da ma Yah Farouk ne ya ce in ba ka number ɗinsa ka kira shi ku yi magana."
"What? Me ya faru? Ko ya gano muna haɗuwa ne?" Ya faɗa idanunsa a warwaje. Dariya ya ba ta ganin yadda ya tsorata. Don haka ta yi kayarta sannan ta ce
"Kai don Allah! Kawai fa a kan maganarmu ne, zai samar mana mafita ne. Kai dai ka kira shi a waya, na san tabbas zai gayyace ka zuwa gida." Ta ƙare maganar kanta a ƙasa cike da kunya. Shirun da ta ji Khaleed ya yi, shi ne abin da ya sanya ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Sai ya sakar mata murmushi kafin ya ce
"Tsananin farinciki ne ya hana ni yin magana. Tabbas zan kira shi, zan kira shi.. Ba ni number.." Ya yi maganar yana miƙa mata hannunsa. Wayarsa ta karɓa ta rubuta masa number sannan ta miƙa masa.
"Mene ne?" Ta yi maganar a shagwaɓe tana kallon sa kamar za ta yi kuka. Murmushin dai ya sake sakar mata kafin ya ce
"Babu komai fa. Kawai dai da yake na baro Umma ne a gida babu lafiya. Ina ganin zan koma ma saboda tsaro."
"Wayyo sannu, Allah Ya ƙara sauƙi." Ta faɗa tana ji kamar a jikinta ne rashin lafiyar yake.
"Ameen Abar ƙauna." Ya faɗa yana murmushi. Daga haka suka yi sallama ya tafi, ya yin da ita ma ta wuce gidansu ba tare da ta nemi Fa'iza ba. Don a ranta ta raya wannan ɗin ita ce alaƙarsu ta ƙarshe tsakaninta da Fa'izan. Kamar yadda ta yi wa Yah Farouk alƙawari, to hakan ya fara ne daga yanzu.
Ƙaton parlour ne, wanda girmansa kaɗai abin kallo ne. Cikin parlourn kansa ɓangare biyu ne. Wannan ɓangaren maƙare da furniture masu masifaffen kyau. Ya yin da ɗayan ɓangaren ma yake a haɗe cike da kaya masu mugun kyau.
Yana tsaye a tsakiyar parlourn hannayensa biyu saƙale da juna a bayansa, yana zagaye ɗakin. Gaba-daya fuskarsa a tamke take babu alamar annuri ko kaɗan. Idan yau ka fara ganin sa, sai ka ɗauka bai taɓa murmushi a rayuwarsa ba. Abin ne kuma ya sake haɗar masa, kasancewarsa mutum irin mai duhun nan sosai, idanunsa ba jajaye ba ne, sai dai ba farare ba ne. Wanda tasirin ɓacin ran da yake ciki ya sanya suka yi ja kamar wanda ya sha wani abu. Da mutane wajen biyar a ɗakin, amma saboda yadda ɗakin ya ɗauki shiru sai ka ɗauka bayan shi babu wanda ya wanzu cikin ɗakin. Bayan shuɗewar wajen mintina goma, wasu mazan su biyu suka sake shigowa. Kai tsaye neman waje suka yi suka zauna.
"Tashi don Allah." A karon farko babban mutumin ya yi magana yana kallon su, lokaci guda yana yin amfani da hannunsa wajen nuni da abin da ya faɗa. Sai ya shiga takawa kamar mai jin tsoron ƙasa yana ƙarasowa inda suke a tsaye. Wajen minti ɗaya ya kafe su da ido yana kallon su kamar wanda zai karanto abin da ke tafe da su a kan fuskarsu. Bai kuma bari sun ce komai ba ya ce
"Duk wasu alamu sun nuna babu cigaba. Me ya sa? Ashe ba ku da amfani? Ashe ina zaune ne da ku kawai ba don za ku yi mini amfani ba?" Ya ƙare maganar yana fidda wani huci daga bakinsa.
"Ka yi mana afuwa Ranka ya daɗe. Ka fi kowa sanin wane ne MuhammadAali, kai za ka fi kowa bayar da shedar wane ne shi da kuma halayensa." Girgiza kai mutumin yake yi, don da ya san yadda waɗannan kalaman ke sake ɓata masa rai da ya daina faɗa.
"Duk cikinku ba ku da amfani a wajena. Aikin da mutum ɗaya zai iya yi mini shi cikin ruwan sanyi, amma gabaɗaya kun kasa. Tabbas ina buƙatar MuhammadAali. Ina buƙatar sa ko ta halin ya ya ne."
"Yallaɓai ta kowanne yanayi?" Da sauri ya kalli wanda ya yi maganar, sai ya shiga takawa har zuwa inda yake ya tsaya yana kallon sa.
"Mamaki kake yi?" Ya tambaya duk da ba ya buƙatar jin amsar da za ta fito daga bakinsa.
"Ban damu da duk hanyar da za a bi ba, ban damu da duk wani abu da zai faru ba. Ni dai kawai MuhammadAali ya dawo tafiyata."
In sha Allah a sati za ku dinga samun update sau biyar. Kenan zan dinga hutun kwana biyu. Ba zan ce ga ranakun da zan dinga hutun ba, saboda tasowar uzuri. Idan uzuri ya taso mini to za ta zama ita ce ranar da babu update. Idan kuma babu wani uzuri in sha Allah za ku samu update.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 09
A cikin motarsa ya ɗakko Saleem, suna tafe jefi-jefi suna 'yar hira, wadda kusan duk Saleem ɗin ne ke yin ta. Shi dai MuhammadAali amsarsa ba ta wuce 'Eh, A'ah' ko ya yi murmushi. Har zuwa lokacin da ya gaji don kansa ya ce
"Malam na ga kana ta babbasar da ni. Ko dai ba ka ji daɗin gani na ba ne?" Ya faɗa yana jefa masa harara, don duk da ya san halin abokin nasa, amma yau ɗin kamar ya so ya fahimci canjawarsa. Sai da Muhammad ya ɗan sauke numfashi sannan ya ce
"Man, akwai wani abu.. Na kuma ji daɗin zuwan ka, amma kafin nan mu je ka huta."
Ba don Muhammad ɗin ba ne da tun yanzu zai tambaye shi abin da ya faru, amma ya san halin abokin nasa, tun da ya ce haka, yana nufin hakan. Don haka sai ya jinjina kai kawai kafin ya ce
"Ina fatan Allah Ya sa lafiya, ameen."
A ƙofar gidan suka samu Abban Al-ameen da kuma Daddy, da wasu baƙi guda biyu. Ganin su ya sanya Muhammad dakatawa, suka sauka tare da Saleem suka gaishe da su gabaɗaya.
"Ku wuce ciki ko?" Daddy ya faɗa yana ɗan murmushi. Kallon sa Abba ya yi cike da mamakin yadda ya yi maganar kamar yana korar su. Su ma kamar sun so su fahimci hakan, Saleem ya yi musu sallama suka ƙarasa suka hau motar sannan ya shige da su cikin gidan.
Kallon baƙin Daddy ya yi kafin ya ce
"Kun ga wannan da suka wuce yanzu? To shi ne mijin Ammeey. Kamar yadda na sanar da ku na yi mata miji, to kun gan shi da idanunku. Ina mai ba ku haƙuri, tabbas da ina da wata ɗiyar da na ba ku aurenta, saboda yaba wa da hankalin yaron da na yi."
"To mun gode, mun gode Allah Ya saka da alkairi. Muna godiya ma da irin karamcin da aka yi mana, Allah Ya sanya alkairi." Ɗaya daga cikin mutanen ya faɗa. Daga haka suka yi sallama da su Daddy cikin mutuntawa suka tafi. Sai a lokacin sannan Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa. Har ya soma shirin tafiya, sai ya sake jin tasirin kallon sa da ake yi a jikinsa. Ya juya ya kalli Abba da ya kafe shi da idanunsa.
"Mene ne kuma?" Ya tambaya cike da gajiyawa, don ya san tabbas zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi.
"Yanzu Aminu me kake shirin aikatawa fisabilillahi?" In ji Abba cike da mamaki. Girgiza kai Daddy ya shiga yi kafin ya ce
"Yanzu don Allah Abban Al-ameen sau nawa zan yi maka bayani? Me kake so in ce? Komai fa a bayyane yake. Na ba su haƙuri ne a kan neman izini da suka zo nemar wa ɗansu a kan Ammeey, na kuma sanar da su na yi mata miji. Ko hakan laifi ne?"
"Muhammad ya taɓa ce maka yana son Ammeey? Ko kuwa ita Ammeeyn ta taɓa ce maka tana son Muhammad? Me kake ƙoƙarin aikatawa ne? Kada fa don wani ra'ayi naka na banza ya sa ka zo ka yi abin da za ka zo kana nadama."
"Tuff! Ka tofar da wannan mugun yawun. Babu abin da zai faru in sha Allah. Aure ne kuma tsakanin Ammeey da Muhammad kamar an yi a gama, lokaci kawai nake jira ya zo kowa ma ya sani. Amma ka yi haƙuri ba wai don ba ka isa da ni ko 'yata ba ne." Murmushin takaici Abba ya yi yana girgiza kansa.
"Ni kuma? Mene ne na ba ni haƙuri Aminu? Ai ka yi abin da ka yi niyya. Amma ka sani, yanzu zamani ya canja da za a zauna ana auren haɗi, bayan kowannensu na da wayon da zai iya samo abokin zama."
"To a dai yi musu addu'a Allah Ya tabbatar da alkairi kawai."
"Ina fatan hakan." Abba ya faɗa, daga haka ya yi gaba ya shige cikin gida. Shi ma Daddyn cikin gida ya nufa, daidai lokacin da wayarsa ta yi ƙara. Tsaki ya ja ganin mai kiran nasa, lokaci guda gabansa na ɗan faɗuwa. Don abin kamar a rubuce yake, ba ya taɓa ganin kiran mutumin sai idan matsala ce ta faru. Kamar ba zai ɗaga ba, sai kuma dai ya ɗaga ɗin lokaci guda yana takawa zuwa cikin gidan.
A parlour ya samu Ammeey zaune tana game a wayar Ummanta, sanye cikin doguwar rigar wani material mai matuƙar kyau, ta ɗaura ɗankwalinsa, gashinta ya sauka a kan kafaɗarta.
"Ammeey." Ya kira sunanta don ya lura gabaɗaya hankalinta na kan wayar, saboda har sallama ya yi amma ba ta ji shi ba. Da sauri ta ajiye wayar tana gyara zamanta ta ce
"Na'am Daddy."
"Ana ta aikin?" Ya faɗa yana murmushi. Ta gane aikin da yake nufi, hakan ya sanya ta ɗan yin murmushi ba tare da ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 24