hankali, don ya fahimci yadda ya shiga ruɗani.
"Baba aure fa kake magana? Aure kuma Baba?"
"E ƙwarai Muhammad, kwantar da hankalinka ka sanar da ni, shin za ka iya auren ɗaya daga cikinsu?" Baban ya sake jefa masa tambayar kai tsaye. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin bugawa kamar za ta faso kirjinsa.
"A'ah Baba, idan har izinina ake nema ba zan taɓa amincewa ba. Sai dai idan umarni ne kake ba ni, to tabbas zan amince da duk wani hukunci da ka yanke wa rayuwata." Shiru ne ya wanzu a wajen bayan hakan da Muhammad ya faɗa. Baba ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa. Shin idan har ya tursasa wa ɗan nasa anya ya yi masa adalci kuwa? Gabaɗaya kansa ya kulle ya ma rasa abin da ya kamata ya yi tunani. Yana iya jiyo sautin numfashin da Muhammad ɗin ke ajiyewa, wanda ya tabbatar na ɓacin rai ne da rashin sanin mafita.
Kallon Baban kawai take daga inda take a laɓe tana so ta ji me zai faɗa. Burinta ɗaya, ta ji ya furta umarni ne yake ba shi a kan ya aure ta, sai dai kuma ba ta sake ji ya ce komai ba. Baya ta yi tana jan tsaki haɗi da hararar inda take tsaye kamar shi ne ya yi mata laifi. Ita gabaɗaya haushin Baban take ji, me ya sa ba zai ce ya ba shi umarnin auren ta ba? To tun farko ma mene ne na haɗa ta da wata Ammeey? Ai wallahi ba a isa su auri miji ɗaya ita da yarinyar ba. Muhammad nata ne ita ɗaya. Babu kuma yadda ya iya dole ya aure ta. Sai dai abin da ya dame ta, yadda ba ta ga alamar Baban zai tilasta wa Muhammad ɗin ya aure ta ba, idan hakan ta faru kenan ita ina ta kama? Ai ya zama dole ta nema wa kanta mafita. Aure a irin gidan nan ba ta taɓa ko da mafarkin rabin rabinsa ba ne, sai ga shi tana ganin dama amma ana ƙoƙarin a hana ta cimma ta? Tabbas sai ta auri Muhammad ko ta halin yaya ne. To amma me za ta yi wanda zai saka Baban ya ba shi umarni kai tsaye a kan ya ya aure ta? Don ta fahimci ko za ta daki taɓarya ba zai yadda a ƙashin kansa ya aure ta ba. Don tun zuwanta gidan ma idan ta ce ya taɓa yi mata kallo ɗaya ma to ta yi ƙarya. Babu lallai ma ya iya shaida fuskarta. Shiru ta yi tana ba wa zuciyarta damar ƙarasa tunanin da ta ji lokaci guda ta ɗarsa mata. Ta kai wajen mintina biyu tana nazari. Zuwa can ta saki dariya tana juyi a cikin ɗakin. Tabbas mafita ɗaya gare ta wadda za ta saka Muhammad ya aure ta. Ta san yadda za ta yi wani abu ya shiga tsakanin ta da Muhammad ɗin ko ma ta wanne hali ne za ta san yadda hakan za ta kasance, idan hakan ta faru, ko da ba a karan kansa ba, tana da tabbacin ba ma Baba ba, kowa na gidan sai ya ba shi umarnin auren ta saboda rufa wa kansu asiri. Ta kuma san shi mai amincewa ne idan dai har Baban ya saka shi. Wani miskilin murmushi ne ya suɓuce mata, ta ja gefen mayafin jikinta da Inna ta tilasta mata sakawa ta tauna gefensa lokaci guda tana ci gaba da murmushi, jin yadda cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta ƙissima mata abin da take da tabbacin shi ne daidai ga rayuwarta. Ita da ma ta san ba za ta wahalar da kanta wajen samun mafitar ba, musamman yadda ta san kaifin ƙwaƙwalwarta. Don kuwa hatta a ƙauyensu an san ta da wannan kaifin ƙwaƙwalwar da shegen wayo. Wanda mutane da dama ke kiran ta da 'Hamida barazana' domin kuwa idan dai har ta shiga rayuwarka ko ta wani naka, da wuya idan ba ta zama barazana ga tarbiyyarsa ba ko wani abu makamancin haka. Ta ƙware wajen shuka tsiya iri-iri a ƙauyen, inda kuma ta fi ƙwarewa, shi ne inda za ta samu kuɗi. Shi ya sa ba ta jin komai don ta bari a lalube ta a ba ta kuɗi. Sau da dama takan ja ra'ayin samarin ƙauyen nasu ta hanyar 'yar'iskar shigar da take yi. Ba iya samari ba, hatta ga mazan aure masu mummunar zuciya irin tata, tana sane take abin da za ta ja hankalinsu. Musamman idan ya kasance ta ga mace tana cika baki a kan mijinta, to a nan take tashi tsaye don ta nuna mata ita ɗin ba kowa ba ce idan tana wajen. Wannan ya sake ɗabbaka sunan 'Barazana' ga Hamida.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 26
Gabaɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa inda za ta tsoma kanta ta ji daɗi. Ta gefe guda kuma ta rasa wanne ɓangare ya kamata ta fi ba wa muhimmanci. Zuciyarta da ke mata wani irin zafi, ko kuwa idanunta da ke azabar raɗaɗi? Numfashi kawai take saukewa da sauri-sauri cikin rashin sanin abin yi. Ta je wajen Ummee don ta saurare ta kar ta biye ta abin da Yah Farouk ya ce, amma ta ƙi saurarar ta. Ta je wajen Abee, shi ma ya nuna amincewarsa a kan abin da Yah Farouk ɗin ya faɗa ɗari bisa ɗari. To ita kam ina ake so ta jefa rayuwarta ta ji daɗi? Ta yi kukan ta yi kukan, tun tana ji kamar zai yi nasarar wanke mata ko da kaɗan daga cikin damuwarta ne har ta haƙura ta daina. Tun tana yin mai hawaye har ta koma na zuci. A nutse ta miƙe tsaye tana jin yadda hatta gangar jikinta karkarwa take yi, ta ƙarasa jikin tagar ɗakin da take iya hango harabar gidan. Tun ɗazun ta hangi Farouk a wajen, har kuma zuwa wannan lokacin yana tsaye a wajen. Ta runtse idanunta, ta ɗauka za ta ga gabaɗaya 'yan gidan ne cikin rashin damuwa, tun da suna ƙoƙarin yanke wa rayuwarta abin da suke ganin shi ne ya dace da ita. Sai dai ko kaɗan ba ta ga alamun hakan ba, ta kasa gane dalilin da ya saka su ma kansu mutanen gidan yanayinsu ya canja. Gabaɗaya kamar dai ita tun bayan hakan, dukkansu ba su da sukuni musamman ma Yah Farouk. Kodayake hakan ba ya rasa nasaba da sun yanke ne kawai ba don hakan ya kasance zaɓin ransu ba. Hannu ta kai ta zare glass ɗin idanunta, sannan ta goge idanun da suke cike taff da hawaye. Sai ta mayar da glass ɗin sannan ta taka ta fice daga ɗakin. Ko ma mene ne yake faruwa ita ta san abin da ke damun ta, duka kuma 'yan gidan sun sani. To amma su ba ta san abin da ke damun su ba, don haka ya zama dole ta san mene ne yake damun su. Musamman ma ɗan'uwanta da ko kaɗan ba ta son ganin sa cikin damuwa, kamar yadda shi ma ba ya son ganin ta ciki. A nutse ta ƙarasa tana ci gaba da kallon Yah Farouk ɗin da ke a juye ba ta iya ganin fuskarsa.
"Yah Farouk." Kamar wanda ya tsorata, haka ya juyo ya kalle ta, sai kuma ya kafe ta da idanunsa kamar wanda ya ga baƙuwar halitta.
"Yah Farouk." Ta sake ambatar sunansa a karo na biyu. Da sauri ya gyara tsayuwarsa yana yin azamar ɗauke idanunsa daga kallon da yake yi mata ɗin. Ita kanta a yau ɗin sai da ta ji wani banbarakwai da irin kallon Yah Farouk ɗin, amma sai ta basar kafin ta kai ga cewa komai ya ce
"Me ya fito da ke?" Sai ta lumshe idanunta sannan ta ce
"Na hango ka ne a nan tun ɗazu Yah Farouk, ban san me yake damun ka ba. Amma na san za ka faɗa mini abin da yake damun ka ko?" Ta yi maganar a marairaice duk don ya sanar da ita abin da ke damun nasa.
"Ke ba ki ga halin da kike ciki ba?" Ya yi mata maganar kai tsaye bayan ya sake zube ƙwayar idanunsa a kan fuskarta. Sai da ta fesar da numfashi a hankali sannan ta ce cikin basarwa.
"A'ah Yah Farouk kar ka damu da ni, ka faɗa mini me yake damun ka?" Ta ƙare, tana yin kokawa da hawayen da ke ƙoƙarin sakkowa a kan kuncinta, don dannewa kawai take yi, amma ba don ta gan shi cikin yanayin nan ba, sai dai ta yi masa magana a kan matsalarta. Murmushin yaƙe Farouk ya yi kana ya gyara tsayuwarsa.
"Kina fushi da ni ko?" Ya jefa mata tambayar da ba ta tsammata ba. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi cike da mamaki. Sai ya jinjina mata kai don ya tabbatar mata da abin da ya faɗa. Babu shiri ta shiga girgiza kanta lokaci guda tana janye idanunta zuwa ƙasa, sannan ta ce
"A'ah Yah Farouk, ta yaya ma za a yi na yi fushi da ɗan'uwana?" Bai san dalili ba, kawai dai ya ji zuciyarsa ta wani irin harbawa wanda har bai san lokacin da ya yi azamar runtse idanunsa ba. Shiru ya wanzu a wajen na tsawon sakanni babu wanda ya sake cewa komai, har zuwa lokacin da Janan ta ce
"Ka faɗa mini Yah Farouk, me yake damun ka." Ta yi maganar cikin raunanniyar muryarta da ta sake yin rauni saboda halin da zuciyarta ke ciki. A hankali Farouk ya shiga takawa zuwa kujerun da suke a wajen, yana ƙarasawa ya nemi waje ya zauna. Ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta ƙarasa kamar wadda ba ta da laka ta nemi waje ta zauna, cike da fatan Yah Farouk ɗin ya sanar da ita abin da ke damun sa ko ta samu wata daga cikin damuwar da take ciki ya ragu.
"Babu abin da ke damu na Aysha." Ya yi ƙarfin halin faɗar hakan yana kafe ta da idanunsa. Ba ta san dalili ba, yau ɗin gabaɗaya sai take jin nauyin haɗa idanu da Farouk ɗin, ta janye idanunta kafin ta ce
"Don Allah ka faɗa mini ka ji?" Gyara zamansa ya yi bayan ya yi murmushi, ba tare da ya ba wa maganarta muhimmanci ba ya ce
"Zan tambaye ki, ina so ki faɗa mini gaskiya." Haka nan kawai ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi, sai kawai ta jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba. Ya ja ajiyar zuciya sannan ya ce
"Abin da na yanke wa rayuwarki ba shi ne daidai ba Aysha? Kina ganin ɗan'uwa zai zaɓar wa 'yar'uwarsa abin da zai zama cutarwa a gare ta bayan yana sane? Hakan ba za ta taɓa faruwa ba." Daga nan ya yi shiru. Ita ma ba ta iya furta komai ba, don ya taɓo inda yake mata ƙaiƙayi ne. Ta runtse idanunta kawai tana ci gaba da saurarar sa. A karo na barkatai ya sake sauke ajiyar zuciya kana ya ce
"Aysha idan aka ba ki zaɓi, shin za ki iya zaɓar tsakanin wani da Adam?" Cikin rashin fahimta Janan ta ɗaga idanunta ta kalli Farouk, shi ma ita yake kalla. Sai dai da gaske ko kaɗan ba ta gane kan tambayar tasa ba. Ya ɗauka ko tunanin amsar tambayar da ya yi mata ɗin take yi, sai dai yanayin yadda take kallon sa ya tabbatar masa da ba ta gane ba. Don haka ya ce
"A ba ki zaɓi tsakanin wani da yake neman auren ki, ga kuma Adam a gefe, a matsayin waɗanda za su aure ki. Shin za ki iya zaɓar wanin ki bar Adam?" Da sauri ta soma girgiza kanta, ko kaɗan abin da ba zai taɓa yiwuwa ba kenan. Ta zaɓi wanin Adam? Kenan ta zama butulu? A'ah, ko ba za a kira ta da butulu ba ma ba za ta iya ba.
"Faɗa mini da bakinki Janan." Lumshe idanunta ta yi, tana tunanin amsar da ya kamata ta ba wa Farouk.
"Ba zan iya ba Yah Farouk."
"Ko wane ne shi? Kina nufin komai ingancinsa?" Ya sake jefa mata tambayar zuciyarsa na wani irin bugawa. Sai ta jinjina kanta a wnanan karon ma da sauri, don ta tabbatar masa da abin da take nufi sai ta buɗe baki ta ce
"Ba zan taɓa iyawa ba Yah Farouk, matuƙar akwai Adam a waje, zan kwana in tashi ina zaɓar shi ne. Wallahi Yah Farouk ina son shi, ina son shi sosai Yah Farouk." Kansa Farouk ya ɗora a kan kujerar da yake kai ta baya, idanunsa a wani irin runtse kamar zai cizge su. Idan ka kafa idanunka a kan ƙirjinsa za ka iya ganin yadda ƙirjin nasa ke wani irin ɗagawa yana sauka.
Ta kai wajen minti ɗaya a wajen kafin hankalinta ya ƙarasa dawowa jikinta. Ta kalli Farouk ɗin da har lokacin idanunsa ke a rufe ta ce
"Yah Farouk." Da sauri ya buɗe idanunsa da suka sauya kala daga fari zuwa ja.
"Yah Farouk ba ka da lafiya ne? Kai ma ciwon idon kake yi?" Ta yi azamar jefa masa tambayar lokaci guda tana matsa wa kusa da shi sosai, tana kuma kai hannunta jikinsa. Da sauri ya miƙe yana faɗin
"Bari na shiga ciki, za mu yi magana zuwa an jima." Ya yi ƙarfin halin faɗin hakan. Daga haka ba tare da ya jira amsarta ba ya juya ya ya yi hanyar ɗakinsa. Bin sa ta yi da kallo cike da tausayin yayan nata. Da alama ba shi da lafiya, ita kuma ko kaɗan ba ta son ganin sa a irin yanayin nan, yanzu hankalinta zai tashi.
Sai da ta bari ya shiga banɗaki sannan ta ƙarasa ta ɗauki kayan da ya cire. Dubawa ta shiga yi cike da takatsantsan, ko da za ta ga wani abu da zai ɗarsa mata zargin da take yi. Sai dai iya bincikenta ba ta ga komai ba. Don haka ta koma kan wayarsa da har lokacin ta kasa gano mene ne sabon password ɗin da ya sauya. Ta kai wajen minti 1 tana ta gwadawa amma shiru, har zuwa lokacin da ya fito daga toilet ɗin, ɗaure da towel, hannunsa ɗauke da wani ƙarami yana goge sumar kansa. Turus ya yi, lokacin da idanunsa suka sauka a kan Nafisa da ko tsoro ba ta ji, don ita ko shakkar ya ga tana duba masa waya ba ta yi, kodayake shi kansa ai ya san halin kayarsa in dai a wannan fannin ne. A nutse ya ƙarasa yana ci gaba da kallon ta, zuwa lokacin ta sake fusata ta yi kici-kicin da fuska kamar wadda aka aiko wa da mutuwa.
"Nafisa, yau ma?" Ya faɗa a nutse yana ci gaba da kallon ta. Ba ta ce komai ba, sai ya nemi waje ya zauna a gefen gado sannan cikin nutsuwa ya ce
"Me ya sa kullum ba kya yarda da ni? Me ya sa kike so ki ƙare rayuwarki kullum cikin fargaba? Ba kya fatan a ce kin rayu ba tare da kina ɗaga wa kanki hankali ba? Shin ni ba abin yarda ne a gare ki ba?"
"Adam kai ba abin yarda ba ne." Ta faɗa da ƙarfi lokaci guda hawaye na taruwa cikin idanunta. Hannu ya saka ya karɓi wayarsa da ke hannunta, bai ce komai ba ya buɗe password ɗin sannan ya miƙa mata.
"Ba dai wannan ne ba? Ga shi nan ki je ki yi duk abin da kike so ki yi da ita. Amma dai ki dinga tunawa da abu ɗaya, kowa ya yi na gari don kansa." Kallon wayar ta yi cike da mamaki sannan ta kalle shi, a karo na biyu ta sake kallon wayar. Sai kuma ta saka hannu ta ɗauka ta jefa masa ta ce
"Ni za ka mayar 'yar'iska? Da ka gama goge-gogen naka shi ne za ka miƙo mini, ga shashasha mara hankali wadda ba ta san me take yi ba ko?" Zazzafar iska Adam ya fesar daga bakinsa. Sau da dama yakan rasa da waɗanne kalmomi ya kamata ya rarrashi Nafisa. Ita a kodayaushe shi ɗin abin zargi ne a wajenta. Ko me zai yi ba ta yarda da shi, a kullum cikin zargin sa take yi. Sai dai yau ɗin da gaske so yake ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen rarrashin ta, don ta ba shi haɗin kai ko da kaɗan ne, ko hankalinsa zai kwanta.
"Nafisa." Ya kira sunanta a nutse. Ba ta amsa ba, sai share ƙwallar da ta ci gaba da yi, hakan ya ba shi damar ci gaba da faɗin
"Kin san dai ina son ki, ina matuƙar ƙaunar ki. Aure da na ce miki zan yi ba wai don ba na son ki ba ne, ke kin sani ba a na ƙara aure ne don an gaji da ta gida ba, hasalima Allahn da Ya ɗora mini ƙaunar ki, Shi Ya ɗora mini ƙaunar ta. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, wallahi babu abin da zai faru sai alkairi in sha Allah, kuma.."
"Adam ka ƙyale ni, ka ƙyale ni kafin na illata kaina na kuma illata ka. Kar ka sake yi mini maganar wata mata wadda kake ƙoƙarin cewa za ka haɗa ni da ita. Ba zan taɓa amincewa ba, wallahi ba a haifi matar da zan yi kishi da ita ba. Adam kai nawa ne, don ni kaɗai aka halicce ka. Ka daina zancen kowacce mace Adam, Adam kai nawa ne ni kaɗai." Ta ƙare maganar cikin ɗaga dashashshiyar muryarta. Daga haka ta fice daga kamar za ta tashi sama. Bin ta da kallo Adam ya yi yana lumshe idanunsa. Gabaɗaya ya rasa inda ya kamata ya tsoma kansa a rayuwa ya ji daɗi. Wani lokacin yana jin shakkar Nafisar, to amma a kan auren nan dai kam, ba ya ji ko kashe shi Nafisan za ta yi zai haƙura da auren Aysha ne. Ayshar da yake jin ta cikin ƙashi, ɓargo har ma da gangar jikinsa.
Kai tsaye ɗakinta ta faɗa ta fashe da kuka. Kukan da ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarta mai cike da raɗaɗi. Ita kam kodayaushe zuciyarta a cunkushe take, cike da tunanin Adam ɗin, kar ta je yana can yana cin amanar ta. Sai ga shi da bakinsa ma yake sanar da ita wai zai yi aure ta kwantar da hankalinta. To aka faɗa masa mahaukaciya ce ta yaye ta, da za ta yarda da kalamansa, ko kuwa manta wace ce ita ya yi? Wayarta ta janyo ta kira Yayarta, tana ɗagawa ta fashe da kuka mai cin rai. Ta kai wajen minti 1 tana rairawa sannan ta ce
"Yaya wai ya na ji shiru ne? Ni kawai ki bar ni a koma wajen malamin nan zai yi mana maganin abin da ke faruwa." Tsaki Yayar ta ja sannan ta ce
"Ke daɗina da ke gajen haƙuri. To yanzun nan nake ƙoƙarin kiran wanda zai yi mana aikin shi ne kiranki ya shigo. Me ya sa ba ki da haƙuri ne? Wanne kalar Malam kuma? Ai ba kodayaushe ake zuwa ba idan kina son ayyukanki su dinga yin kyau. Ya zamana ana caccanjawa, don ba na so ko daga ƙarshe kar ya zo ya ruguje, don haka wannan da hannunmu za mu yi aikin, wanda nake da tabbacin har abada ba zai rushe ba tun da ba aikin wani gardin ba ne." Shiru ta yi tana nazarin maganganun yayar tata, kuma ta yarda da abin da ta faɗa ɗin. Don da ma ita ma yanzu a tsorace take da aikin malam, tun da aiki ne da idan ya ɗauki lokaci zai iya rushewa, ita kuma wanda ba zai rushe ba shi take buƙata.
"Ka yi haƙuri da marin da na yi maka, tun da na koma gida na kasa sukuni, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, har sai da na nemo ka na zo don na ba ka haƙuri. Ka yi haƙuri ka yafe mini. Sannan kuma in roƙi alfarma a wajenka." Sai ta dakata a nan tana yin ƙasa da fuskarta cike da kunya.
"Ina son ka, ina matuƙar ƙaunar ka. Za ka aure ni?" Ta tambaya bayan ta ɗaga kanta ta dube shi tana murmushi. Wani irin murmushi ne ya suɓuce masa a kan fuskarsa, ya lumshe idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ta yi wani irin sanyi. Cikin tsananin farinciki ya buɗe baki da niyyar yin magana, kamar daga sama ya wani irin firgita ya tashi zaune kawai sai ya buɗe idanunsa. Cike da mamaki yake kallon ɗakin da yake ciki, sai kuma ya dawo da dubansa jikinsa. Da sauri ya runtse idanunsa yana jin wani irin ɓacin rai na ziyartar sa. Shin me yake damun ƙwaƙwalwarsa ne? Wanne kalar datti ke ƙoƙarin shiga ruhi, ƙwaƙwalwa, zuciya har ma da gangar jikinsa? Me ya sa ya kasa manta ta? Me ya sa ya kasa manta fuskarta? Me ya sa ya kasa daina jiyo sautin muryarta cikin kunnuwansa? Me ya sa ya yi mafarkinta? Shin akwai wani haɗi da yake da ita ne da har zai saka ya yi mafarkin ta? Shin mene ne yake damun sa ne? Me ya sa ƙwaƙwalwarsa ke masa haka ne? Hannunsa guda ɗaya ya cusa cikin sumar kansa yana sake runtse idanunsa. Daidai lokacin da Al-ameen ya shigo ɗakin, da sauri ya ƙarasa ya buɗe wardrobe ya ɗauki abin da zai ɗauka sannan ya juya ya kalli MuhammadAali da har lokacin ke zaune a kan gadon cikin rashin sanin abin yi, sai dai cikin ɓacin rai.
"Tun ɗazu na ga kana bacci. Zan fita ne, akwai wani kira da aka yi mini." Ya faɗa saboda sun yi da Muhammad ɗin za su fita. Ba tare da ya amsa ba, kawai ya jinjina kansa. Daga haka ya fice daga ɗakin, a karon farko Muhammad ya ja tsaki, sai kuma a hankali kamar mai jin tsoro ya taune leɓensa na ƙasa yana sauke numfashi.
Sai da ya isa inda ta nemi su haɗu sannan ya kira ta. Ta sanar da shi inda take sannan ya ƙarasa.
"Al-ameen." Ta ambata tana murmushi.
"Hajjaju." Ya faɗa shi ma yana murmushi. Gaisawa suka yi cike da sabon da ke tsakaninsu sannan ta ce
"Na san za ka yi mamakin kiran da na yi maka, duk da dai na riga na fara yi maka bayani a waya." Jinjina kansa Al-ameen ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce
"Na san ka san ƙanwata Nafisa."
"Ƙwarai kuwa." Ya faɗa yana jinjina kansa.
"To wannan aikin zan ce kusan a kanta ne. Ita za ka taimakawa." Cike da mamaki ya ce
"Ina jin ki Hajjaju." A karo na biyu ta sake sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
"Akwai wata 'yar'iskar yarinya da take ƙoƙarin shiga tsakanin ta da mijinta, bayan kuma sun kasance tsayin shekaru tare ba tare da wani abu na tashin hankali ya taɓa haɗa su ba, sai bayan da ta shiga rayuwarsa. Gabaɗaya ta hana Nafisa kwanciyar hankali, ta hana ta sukuni, ta raba ta da farincikinta, ta kuma raba ta da zaman lafiyar da ke a tsakanin ta da mijinta. Nafisa a shirye take ta biya ko nawa ne, kai ba ta ƙi ta ba ka cheque ka rubuta ko nawa kake buƙata ba. Kai ita mai iya mallaka maka duk wani abu da ta mallaka ne don a ɓata wa yarinyar suna ko ma gabaɗaya rayuwarta, ta yadda ba iya mijin Nafisa ba, kowanne namiji mai tarbiyya zai guji haɗa zuri'a da ita."
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 27
Shiru Al-ameen ya yi na tsawon sakanni ba tare da ya ce komai ba, yana nazarin maganganun Yayar. Kafin zuwa can a hankali ya shiga jinjina kansa tuna irin kuɗaɗen da ta ambata. Sai ya yi murmushi sannan ya ce
"A samo hoton yarinyar, sai na gan ta sannan zan san wane irin aiki za a yi a kanta."
"Shi ya sa nake son ka Al-ameen, don Allah kar a yi wasa. Ni na san ka a kan kuɗi shi ya sa ba na jin ka. Da farko ma da har na ɗan ji nauyin samun ka da maganar, amma da na tuna wane ne kai, ya saka na daina jin shakka." Murmushi ya yi yana shafa sumar kansa sannan ya ɗage kafaɗarsa ba tare da ya ce komai ba. Don ta gefe guda abin da ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 24