Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
parlourn ya yi babu wanda ya sake cewa ko uffan. Da ma shi Oga da ke zaune a gefe ko yunƙurin magana bai yi ba tun ɗazun. Shi kaɗai ya san me yake ji duk lokacin da ake maganar MuhammadAalin. Ya kasa gane dalilin da ya saka Alhaji Mauden ya kasa yadda shi mai iya maye masa gurbin Muhammad ne. Shin mene ne dalili? Mene ne Muhammad ɗin yake da shi wanda shi ba shi da shi? Mene ne Muhammad ɗin ke taƙama da shi wanda shi ba shi da shi? Shin akwai wani abu da zai nuna masa ne, bayan duk irin ƙoƙarin da yake yi wa Alhaji Mauden? Lallai tabbas ko ma mene ne ba zai taɓa ɓarin Muhammad ba. Ba zai taɓa barin sa ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali ba, kamar yadda shi ma ya hana shi, kullum cikin tunanin yadda zai yi wata bajinta da zai saka ya burge Yallaɓan nasu yake. Sai dai a kullum a kodayaushe ko me ya yi, abin da ke biyo baya shi ne "Ka yi ƙoƙari, amma tabbas da MuhammadAali na nan zai yi fiye da hakan. Ka sake dagewa." Waɗannan kalaman ba ƙaramin yi wa zuciyarsa illa suke yi ba. Yana matuƙar kishi da Muhammad ɗin, wanda hakan ya janyo ko daidai da ƙwayar zarra ba ya ƙaunar Muhammad ɗin, ya tsane shi, don yana ganin shi ne sanadin da ya saka har yanzu bai kai inda yake son kai wa a rayuwarsa ba. "Wace ce yarinyar? A nemo mini ko wace ce ita. Zaki na ba ka damar aikata abin da ya dace. Ba a haifi macen da za ta tozarta MuhammadAali ina raye ba. Ga mari ga tsinka jaka? Ko yaya ne ta san ta taɓa MuhammadAali, kar ta sake ta ci bulus." "Yallaɓai gargaɗi ma kaɗai ya ishe ta, za kuma ta shiga taitayinta." Wanda suka shigo da Zakin ya faɗa. Shi kam Zaki tuni hankalinsa ya tafi wani waje daban. Shi kaɗai ya san me zai yi wanda zai rama wa MuhammadAali wulaƙancin da yarinyar ta yi masa. A hankali ya saki wani shu'umin murmushi yana shafa haɓarsa idanunsa na hasaso masa yadda yarinyar za ta kasance. A inda ya saba parking ɗin motarsa ya yi, sai a lokacin sannan ya samu damar ɗaga hannunsa ya shafa inda Janan ta mare shi. Har zuwa lokacin yana iya jin sautin saukar marin a kunnensa, kamar yadda kalaman nan da ta faɗa masa suka kasa barin kunnuwansa. Wanda suke ta maimaita kansu tamkar a lokacin take faɗa masa. Hannunsa ya buga a kan steering motar cikin tsananin ɓacin rai, yadda zuciyarsa ke bugu hatta ƙirjinsa ɗagawa yake yi, kamar wadda zuciyar ke ƙoƙarin faso ƙirjinsa ta fito. Buɗe motar ya yi ya fita, cike da sassarfa yake ƙoƙarin shiga sashensu, daidai lokacin da Hamida da ta ci kwalliya ta ƙaraso tana faɗin "Ina kwana Yaya Muhammad." Ko da da wasa bai ma lura da ita ba, ballantana kuma ya san abin da take faɗa. Don haka ya ci gaba da tafiya har zuwa lokacin zuciyarsa a cunkushe cike da ɓacin rai. "Muhammad." Baba ya kira sunansa cike da mamakin yanayin da ya ga ɗan nasa a ciki. A karo na biyu kenan da Baban ya faɗa, don duk wasu alamu sun nuna bai ji na farkon ba. "Na'am Baba." Ya ambata da muryarsa da ta ɗan shige ciki, cike da basarwa don kada Baba ya lura da shatin marin da Janan ta yi masa. Don ko ba a faɗa ba, ya san tabbas shatin marin ya fito. "Me ya faru?" Baba ya tambaya kai tsaye. Shiru MuhammadAali ya yi yana tunanin ta ina zai fara. A wannan lokacin ba shi da ra'ayin yin magana, to amma Baba ne fa. Sai dai da gaske bai san ta inda zai fara ba, ya faɗa masa ga abin da ya faru, daga ƙarshe ya gane ya bijire masa cewa da ya yi kar ya yi yunƙurin yin wani abu? Ko kuwa daga ƙarshe ya gane ya haɗa hannu da su Alhaju Maude? Sam bai iya yi wa Baban ƙarya ba, don haka da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yana shirin fara magana, Baba ya katse shi da faɗin "Je ka Muhammad. An jima za mu yi magana. Da ma kuma akwai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi da kai." Ya faɗa a nutse, don ya lura da yanayin ɗan nasa. Lumshe idanunsa ya yi, yana jin hukuncin da Baban ya yanke ya yi masa daɗi. Don haka sai ya jinjina kai kawai ba tare da ya furta komai ba. Daga haka ya wuce. Bin sa da kallo Baba ya yi, fata yake a ce lafiya ce. Abu ɗaya ne ya saka bai takura masa ba, saboda duk wasu alamu sun nuna ba wani abu ya sha ba, shi ya sa har ya iya barin Muhammad ɗin ya bar wajen ba tare da ya ji dalilin da ya sauya masa yanayi ba. Don haka yana fatan ko ma mene ne, mai sauƙi ne in sha Allah. "Ka yi haƙuri don Allah..." Saƙon da ta fara rubutawa kenan, wanda ba ta kai ga ci gaba ba, Ummee ta fizge wayarta. Da sauri ta ɗaga jajayen idanunta ta zube su a kan Ummeen. "Janan?" Ummee ta kira sunanta, a yau ɗin kam ta sare da al'amarin Janan ɗin gabaɗaya ba kuma ta san abin da ya kamata ta yi ba a wannan lokacin. Ba ta san Janan ɗin ta fi ƙarfin tunaninta ba sai a yau ɗin. "Ummee don Allah ki ba ni na tura masa saƙo, daga yanzu kar ki sake ba ni. Don Allah Ummee ki taimaka mini." Tun ɗazu ya shigo ɗakin, yana jin duk abin da yake faruwa. Sai a wannan lokacin sannan ya ƙarasa jikinsa a matuƙar sanyaye. "Farouk." Ummee da ta lura da shigowarsa ta kira sunansa. Sai ya ƙarasa har inda suke, yana kallon yadda Janan ke kuka kamar wadda aka yi wa dukan tsiya. "Ummee don Allah ki yi haƙuri ki ba ni kin ji?" "Za ki yi mini shiru ko sai na karya ki a wajen nan Janan? Farouk kana kallon abin da ke faruwa ko? Farouk anya kuwa yaron nan haka ya bar mini yarinya bai asirce ta ba?" Ta ƙare maganar hawaye na sauka a kan fuskarta idanunta a kan Farouk. Girgiza kansa ya yi, shi kansa lamarin Janan ɗin ya fara ba shi tsoro. To amma me ya sa har yanzu su Ummeen suka kasa gano abin da ya dace da rayuwarta? "Ummee babu wani asiri fa, ba ki ga yadda ya faru tsakanin ta da wancan ba? Wata irin zuciya gare ta, da ke saurin narkewa a kan abu, ban da wannan babu komai Ummee." Ya ƙare maganar a hankali kamar wanda ba shi da lafiya. Neman waje Ummee ta yi ta zauna tana barin hawayen na ci gaba da sauka a kan fuskarta. Ita kuka Janan ma kuka, gabaɗaya sai ya rasa abin ma da ya kamata ya yi. Kawai sai ya runtse idanunsa lokaci guda zuciyarsa na wani irin bugawa. "Ummee, ki yi haƙuri ki daina kuka ta dalilina don Allah. Ki yi haƙuri Ummeena na yi nadama wallahi." Janan ta faɗa bayan ta ƙarasa inda Ummee ke zaune. A hankali ya buɗe idanunsa ya zube su a kan Janan ɗin. Kamar ba wannan ne karo na farko da ta fara faɗar hakan ba, to amma me ya sa ba ta cikawa. Me ya sa take biye wa zuciyarta wajen saɓa wa iyayen nata? Ya aka yi ƙanwar tasa ta zama haka? Yaushe? "Ummee." Farouk ya kira sunan Ummee a nutse bayan ya ja wani dogon numfashi ya kuma lumshe idanunsa ya buɗe su lokaci guda. Ba ta iya amsawa ba, sai kallon Farouk ɗin kawai da ta yi. Don ita abubuwan sun yi mata yawa, ga halin da ɗiyar tata ke ciki, ga kuma abin da ya faru tsakanin Janan ɗin da ɗan gidan Shettiman. Ba ta san me zai faru ba. Ga shi ba ta san inda za ta nemo Maimuna ba, ba kuma ta san me zai biyo baya ba, sanadiyyar marin da Janan ta yi wa mutumin da daga ita har Janan ɗin ba su ga alamar zai yi shiru ba ne. Shin ina za ta jefa zuciyarta ta ji daɗi? Ina za ta saka kanta ta ji daɗi? "Ummee dukkan wannan abu da yake faruwa yana faruwa ne saboda kun zaɓa wa rayuwar Aysha yin karatu kafin aure. Me zai hana ku ajiye maganar karatun a gefe, ku aura mata wanda take so, ko da hakan na nufin secondary school ɗin ma za ta ƙare ta ne a ɗakin aurenta." Ya ƙare maganar yana jan wani irin numfashi da sauri wanda ya maƙale masa a maƙogwaro. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 25 Kafe shi da idanunta Ummee ta yi tun da ya soma maganar har ya ƙare. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji jikinta ya sake yin wani irin sanyi. Shin abin da Farouk ɗin ke faɗa shi ne mafita, ko kuwa akwai wata hanyar da za su bi ta a matsayin mafita ban da wannan ɗin? Sai dai kuma ta gefe guda, yanayin yadda ta kasa furta komai hakan ya nuna mata kamar ita ma tana ƙoƙarin yin na'am da zancen nasa. Tabbas a yanayin Janan, a abubuwan da take aikatawa, ya kamata su ajiye duk wani makamin yaƙi nasu su yi mata aure. Ko ba ta faɗa ba, a wannan karon kamar ba sai sun tambaye ta ba, don duk wasu alamomi sun nuna ta fi son aure a kan karatu. Kawai tana zaɓar karatu ne wataƙila don ta faranta musu. Shin me ya sa suka kasa ankara har sai da Farouk ya ankarar da su? Me ya sa tuntuni ba su yi tunanin hakan ba? Tunanin nata ya katse lokacin da ta jiyo sabon kukan da Janan ta fashe da shi kamar wadda ake duka. "A'ah Ummee, ba na so wallahi, wallahi ba na so Ummee, ni karatuna nake so. Ki cewa Yah Farouk ya daina wannan maganar Ummee, don Allah ya bari." Iya abin da ta iya faɗa kenan lokaci guda tana runtse idanunta. Ita kam yau ji take kamar idanunta za su faɗo ko kuma su tsiyaye, saboda azabar raɗaɗin da suke yi mata, ga kuma yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa wanda ita kanta ta san ya wuce ƙa'ida. Shin me Yah Farouk ke faɗa? Me ya sa yake so ya ruguza mata mafarki? Me ya sa yake so ya tarwatsa wa iyayenta mafarkin da suka daɗe suna yi a kanta? Me ya sa yake ganin kamar wannan ce mafita a kan al'amarinta? Ita ko kaɗan ba ta son aure, kamar yaya ma aure ana zaune ƙalau. Ita gabaɗaya rayuwarta ma ba ta taɓa kawowa kanta zancen auren ba, kodayaushe mantawa ma take yi da shi. Kuma soyayya da ta fizge ta ba tare da ta shirya hakan ta faru ba, kawai shammatar ta ta yi ta faɗa, har ta kai an zo wajen da ba ta tunanin za ta iya haƙura da soyayyar, sai dai kuma ba aure ne a ranta ba. Ba ta fatan a ce su Ummee su ɗauki shawarar Yah Farouk ɗin. Ita ko kaɗan ba haka ne a ranta ba, idan kuma ba har so suke su illata mata zuciya ba. Ba ta fata ta zama sanadiyyar rushewar burin iyayenta, da kuma nata burin kansa. Don kuwa ba za ta taɓa yafewa kanta ba har abada. "Je ka Farouk zan samu mahaifinku na yi masa magana." "A'ah Ummee ki rufa mini asiri don Allah, ki yi haƙuri Ummee kar ki yi haka. Don Allah Yah Farouk ka tsaya ka roƙi Ummee kar ta faɗa wa Abee, ko kuma ka ce wasa ne kake yi ka ji Yah Farouk ɗina?" Ta ƙare maganar muryarta kanta da ƙyar take fita. Sam Farouk ba ya ma fahimtar abin da take faɗa, don tuni hankalinsa ya yi gaba, tun lokacin da kunnuwansa suka tsinci maganar Ummee. Ya runtse idanunsa lokaci guda yana miƙewa ya fice daga ɗakin cike da sassarfa. Ranar dai gabaɗaya haka suka wuni cikin gidan babu wanda ke a daɗin rai. Ita Ummee gabaɗaya tunaninta ya tafi yadda za ta samu Abee da maganar, lokaci guda kuma ta kasa daina mamakin yadda aka yi ɗiyar tata ta zama haka. Ya yin da ta ɓangaren Janan gabaɗaya zuciyarta a cunkushe take. Duk kuma irin ciwon da idanunta ke yi ta kasa daina kuka, hakazalika zuciyarta ta ƙi daina zafi. Gabaɗaya ilahirin jikinta a matuƙar sanyaye yake, ta kasa daina tunanin abin da ya faru. Shin ita kuwa wace irin rayuwa ta zaɓa wa kanta? Saɓa wa iyayenta, wanda har hakan ke shirin jawowa su aurar da ita? Me ya sa ta zama haka ne? Me ya sa ta kasa amincewa da zaɓin da suka yi mata. Zaɓin da kowacce ɗiyar da ke da biyayya ba za ta yi jayayya da shi ba? Ya yin da ta ɓangaren Farouk, abin ba a cewa komai. Shi kawai yana cikin ɗakinsa a zaune cikin rashin sanin abin yi. Ya ma rasa me zai yi, kawai dai abu ɗaya ya sani, fargaba ce take damun sa. Ban da bugawa babu abin da zuciyarsa ke yi. Sai da daddare sannan Abee ya zo gidan, don da ma sai da Ummee ta fara neman shawararsa a kan zuwa gidan nan ya amince mata kafin suka zo. Don haka kai tsaye nan ɗin ya taho. Sai da ta bari ya gama cin abinci ya huta sannan ta nemi waje ta zauna. Da ma tun ɗazu yake lura da yanayinta, wanda har tambayar ta ya yi ta ce ya gama cin abincin. Don haka yana ganin ta zauna ya ce "Sanar da ni me yake faruwa? Ko sun biyo ki har nan ɗin ne?" Ya tambaya cike da damuwa. Sai ta girgiza kanta sannan ta ce "A'ah Abee, wannan wani abu ne na daban. Kuma ina fata za ka dube shi cikin fahimta." Daga haka ta sanar da shi abin da ya faru, har zuwa shawarar da Farouk ya bayar. Ta ƙare da faɗin "Ka yi haƙuri da ba wa Adam damar kiran ta da na yi. Na yi duba ne da irin son da na ga yana yi mata. Amma idan na ɓata maka rai ka yi haƙuri, don tabbas na san ni ma na taka muhimmiyar rawa a wannan karon, ka yi haƙuri." Shiru Abee ya yi na tsawon mintina uku ba tare da ya ce komai ba. Har sai da Ummee ta cire ran zai ba ta amsa, sai kuma can ya buɗe baki ya ce "Janan." Ya ambata yana jijjiga kansa. Gabaɗaya lamarin yarinyar ya fara ba shi tsoro. Abubuwan da Ummeen ta faɗa sun matuƙar ba shi mamaki, bai taɓa kawowa ko kaɗan a ransa Janan ɗin ka iya yin haka ba, ko kuma za ta sauya ta zama mai saɓa wa umarninsu ba. Shin yanzu duk maganar da suka yi da Janan ɗin kafin ta koma makaranta ashe a banza? Ashe kawai ta faɗa ne don jin daɗin bakinta, har Abeen ya bar ta koma makaranta? Shin duk a ina ta koyo waɗannan halayen? Ƙarya da bijire musu? A hankali Abee ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Wato Janan ta matuƙar ba ni mamaki. Sai dai abin da ya ba ni mamaki, yadda aka yi Farouk ya ga wannan shi ne hanyar da ta dace, ga shi kuma mu ba mu taɓa tunanin hakan ba. Kodayake dukkanmu idanunmu sun rufe a kan karatunta. To amma me ya sa muka fifita karatun a kan farincikin ɗiyarmu? Na amince da abin da Farouk ya faɗa. Kuma in sha Allah zan nemi Adam ɗin, kai tsaye zan umarce shi ya turo iyayensa. Ko da nan da yaushe ne a ɗaura musu aure. Hankalin kowa ma zai fi kwanciya." Ya ƙare maganar a sanyaye. Lumshe idanunta Ummee ta yi tana sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya. Gabaɗaya jikinta a matuƙar sanyaye yake, kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce "Duk abin da ya fi zama alkairi a rayuwar Janan Allah Ya zaɓa mata shi." Shi ne kaɗai abin da ta iya furtawa. "Ameen." Abee ya amsa da hakan, daga haka duk suka ja bakinsu suka yi shiru, kowa da abin da yake saƙawa cikin zuciyarsa. A karo na barkatai ya sake jin wayarsa ta yi ƙara. Da wani irin zafin nama ya janyo wayar yana ji kamar ya rotsa ta da ƙasa saboda damun sa da ake ta yi. Sai idanunsa suka sauka a kan saƙon da ya shigo daga Alhaji Maude, bayan uban kiran da ya jera masa ya ƙi ɗauka. "Wai me kake ɗaukar kanka ne Muhammad? Me ya sa kake yin haka? Shin kana mantawa ne duk muna yin abin da muke yi ne saboda mahaifinka? Me ya sa kake ƙoƙarin watsa mana ƙasa a ido? Yanzu duk shirin da muka yi ka saka ya tashi a banza? Idan haka ne me ya sa ka je neman bayanin da kanka? Ina Maimuna? Ita ce tambayarmu, na kuma tabbatar ba ka samo amsar ba haka ka baro wajen. Ashe haka ka canja da yawa ban sani ba? Me ya sa Muhammad? Ina wancan MuhammadAalin? Ina Muhammad nawa da kowa ya sani, mai zafi, izza da rashin son wasa. Me cika duk wani abu da ya saka wa kansa ran sai ya cika shi. Me aikata duk abin da na saka shi ya aikata cikin ruwan sanyi babu hayaniya? Wanda ke iya aiki ba tare da ya yi amfani da makami ba? Shin ina wannan Muhammad ɗin ya tafi?" A wannan karon jifa ya yi da wayar yana komawa ya cusa dukka hannayensa cikin sumar kansa da ke a hargitse yana ajiye zazzafan numfashi cikin tsanann fushi. Me ya sa kodayaushe burinsa ya dinga tuna masa wane ne shi a baya? Me yake nufi da hakan? Me yake kuma so da shi? Me ya sa yake so ya dinga ɓata masa rai ta hanyar tunasar da shi abin da ya riga da ya shafe shi daga tarihin rayuwarsa, saboda faranta wa mahaifinsa? Zazzafan numfashi yake saukewa idanunsa a runtse gam kamar mai shirin cizge su daga fuskarsa. Kamar ɗazun, yanzun ma fuskar nan ce ta dawo masa cikin idanunsa, lokaci guda kuma waɗannan maganganun nata na ci gaba da maimaita kansu cikin kunnuwansa. Da sauri ya buɗe idanunsa yana sauke numfashi da sauri-sauri kamar wanda ya yi tsere. Cikin tsananin mamakin da har yanzun ya kasa sakin shi yake sake saurarar yadda kalaman ke maimaita kansu sai ka rantse yanzu take faɗa masa su. Abu ɗaya ya tsaya masa a rai, yake kuma sake hasala shi, shi ne yadda ƙwaƙwalwarsa ta kasa daina zana masa fuskar wadda ta sharara masa mari. Haka zalika yadda ƙwaƙwalwarsa ta riƙe kalaman zam ba tare da ta manta da ko kalma ɗaya ba ne, sai ka ce wanda ya yi hadda. Da ƙyar ya iya tashi ya shirya cikin ƙananan kaya saboda kiran da Baba ya yi masa. Har zuwa lokacin idan ka gan shi ka san akwai wani abu a ƙasa. Kai tsaye inda Baba ya saba zama ya huta a harabar gidan ya nufa, yana zaune shi ɗaya hannunsa ɗauke da wasu takardu yana dubawa. A nutse ya ƙarasa ya zauna bayan ya yi sallamar da babu lallai Baban ya ji ta. A nutse Baban ya ajiye takardun hannun nasa a gefensa, cikin mamaki yake ci gaba da kallon ɗan nasa da ya sake tabbatar wa da kansa lallai akwai matsala. "Muhammad." Ya kira sunansa har lokacin yana kallon sa. A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli Baba sannan ya ce "Na'am." "Sanar da ni, me yake faruwa?" Baba ya faɗa kai tsaye yana nazarin ɗan nasa. Shiru Muhammad ya yi na tsawon sakanni ba tare da ya ce komai ba. Zuwa can ya lumshe idanunsa sannan ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa ya ce "Baba.." Baban bai iya amsawa ba, don ya ƙagu ya ji abin da zai fito daga bakin ɗan nasa. Bai ɓata lokaci ba ya shiga sanar da shi abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Daga haka ya ja bakinsa ya yi shiru. Gyara zamansa Baba ya yi, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya soma faɗin "Na ji. Ka kuma yi ƙoƙari, duk kuwa da na ce maka ka bar Maimuna da Allah, in sha Allah za ta ga sakayya tun a nan duniya." "Faaza na kasa haƙuri ne, amma ka yi haƙuri." Ya faɗa kai tsaye bayan ya ɗaga idanunsa da suka janye ya kalli Baban. "Idan aka ajiye wannan a gefe, na kasa gane abin da ya saka ka cikin yanayin da kake ciki. Akwai wani abu da ya kamata na sani?" A wannan karon ma iska ya fesar mai zafi, kafin ya ɗan yi luu da idanunsa kamar zai rufe su, sai kuma ya buɗe. Ji yake kamar ya rasa ta ina ma zai fara, me kuma ma ya kamata ya ce. "Baba." Ya sake ambata a cunkushe. "Na'am." Baba ya amsa kai tsaye yana kallon ɗan nasa. "Ina ji kamar in yi me don takaici. Ba ni da niyyar in ɗauki wani mataki ko wani abu, to amma na kasa mantawa da fuskar yarinyar, na kasa mantawa da kowacce kalma da ta faɗa mini. Ɗaya bayan ɗaya ƙwaƙwalwata ke ci gaba da bitar su, da kuma bitar fuskar da ta kasa barin idanuna a duk lokacin da na rufe su. Me ya sa haka Baba? Na yi ƙoƙari na yakice abin amma ya ƙi yiwuwa, me ya sa ƙwaƙwalwata ta zama ba ta saurin manta abu?" Shiru Baba ya yi yana nazarin kowacce kalma da Muhammad ɗin ke faɗa. Ɗaya bayan ɗaya yake sake bitar abin da ya faɗa ɗin, yana kuma ci gaba da kallon ɗan nasa. Kamar ya so ya fahimci inda zancen yake. Kamar ya so ya fahimci inda zuciya har ma da gangar jikin Muhammad ɗin ke ƙoƙarin kai shi. Amma da alama sam bai fahimta ba, bai sani ba ko don bai taɓa tsintar kansa cikin yanayin ba ne. Zai sanar da shi hakan, amma ba yanzu ba, har sai ya fara gabatar masa da ƙudurinsa. Ƙudurin da idan dai har ya amince zai bar shi, idan kuma bai amince ba zai yi masa bayani dalla-dalla a kan abin da ya faɗa masa ɗin. Don haka tun kafin ɗan nasa ma ya fahimci yanayin da yake ciki gwara ya sanar da shi batun aurensa. Don haka ya gyara zamansa kafin ya soma faɗin "Muhammad, ka buɗe kunnenka da kyau ka ji ni. Da ma na sanar da kai akwai muhimmiyar da nake so mu yi da kai. Kafin nan ina so ka manta da abin da ya faru, kamar yadda na faɗa maka ba na so na sake jin tashin zancen Maimuna. Abu na gaba, ina so na tambaye ka Muhammad, shin za ka iya aurar Hamida ko Ammeey?" Cikin rashin fahimta Muhammad ke kallon Baban kamar wanda ya yi saɓo. Idan ya ce bai gane abin da ya faɗa ba to ba ƙarya yake ba. Don shi dai ya san babu yadda za a yi maganar aure ta haɗa shi da sunayen da Baban ya ambata. A karo na biyu Baba ya sake jefa masa tambayar da ta sanya shi saurin runtse idanunsa. Zuwa can ya buɗe su har lokacin mamaki bai bar kan fuskarsa ba ya ce "Baba su wane ne hakan?" Ya san halin ɗansa sarai, sai dai ya san dole ne ya shiga mamakin wannan lamari. Don haka ya ce "Hamida dai da Inna ta zo da ita gidan nan, Ammeey kuma ɗaya muke da ita, kuma ita ce ta cikin gidan nan." Da gaske bai san lokacin da ya yi dariya ba, sai dai dariyar nan ce da ake cewa ta fi kuka ciwo. Ya girgiza kansa, bai san lokacin da suka fara irin wasan nan da Baba ba. Suna yin wasa da Baban, amma ban da irin wannan, shi ya sa ya yi mamakin yau ɗin me ya sa Baban ke ƙoƙarin farawa da irin wannan abu? "Babu wasa ko kaɗan a cikin maganar nan Muhammad, ka nutsu ka ba ni amsa ka ji?" Baba ya faɗa cikin kwantar da murya, da son kwantar wa da ɗan nasa

Chapter 19 of 24