An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 01
بسم الله الرحمن الرحيم.
Ƙarfe 8:00 agogon da ke ɗaure a kan tsintsiyar hannunsa ya buga. Ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke ƙwayar idanunsa daga kan agogon ya mayar kan titin da motoci ƙalilan ke shawagi a kansa, kasancewar safiya ce. Hannayensa duka biyu ya sarƙafe cikin juna a hankali yana kaɗa babban ɗan yatsansa da ɗan'uwansa. Bayan shuɗewar wajen minti uku, wayarsa ta shiga ruri. Sai da ya ɗan fesar da iska daga bakinsa kafin ba tare da ya dubi mai kiran nasa ba, ya kara wayar a kunnensa. Cikin kamilalliyar muryarsa ya ce
"Ina fata ban ɓata maka lokaci ba." Da sauri wanda ke can ɓangaren ya ce
"A'ah.. a'ah Yallaɓai ko kaɗan.. A yi mini afuwa ma kiran da na yi, ina so ne da ma na tabbatar da zuwanka."
"Ina hanya in sha Allah." Ya sake faɗa a nutse. Numfashi ya sake ajiyewa bayan ya sauke wayar, cikin nutsuwa ya juya ya kalli matar da ke zaune a gidan baya ya ce
"Zainab ko za mu sauke ki a nan, kamar yadda na sanar da ke ina sauri ne. Sai ki samu ki ƙarasa."
Wadda ya kira da Zainab ɗin ce ta ɗaga kanta ta kalle shi, ji take ina ma a ce tana da ƙwarin gwuiwar da za ta iya kallon cikin idanunsa ta faɗa masa ba suga, amma ba za ta iya ba, saboda wani irin kwarjini da Allah Ya zuba masa. Muryarta har wani shaƙewa take yi lokacin da ta furta
"To."
Daga haka ya juya ya ba wa driver umarnin ya tsaya. Babu musu ya tsaya. Hajiya Zainab ta buɗe ƙofar ta fice ba tare da ta sake bin inda mutumin yake da kallo ba. Buga ƙofar ta yi kamar wata ƙaramar yarinya, ya yin da ita a wajenta wannan ce kaɗai hanyar da za ta nuna masa ta ji zafin sauke tan da ya yi a tsakiyar titi.
Gefe da gefe ta kalla kafin ta ja tsaki. Sai kuma ta saka hannu cikin jakar da ke rataye a hannunta ta lalubo wayarta ta yi danne-danne kana ta kara a kunne.
"Al-ameen." Ta faɗa tun kafin ya ce komai
"Na'am." Aka amsa daga can ɓangaren
"Kana ina ne? Ka yi maza ka zo ka ɗauke ni wan ubanka ya ajiye ni a tsakiyar titi kamar wata shara."
Cike da mamaki ya ce
"Me? Baban? Me ya sa?" Ya yi tambayar duka lokaci ɗaya.
"Ta wuce ba ya so a san munafurcin da yake ƙullawa. Wallahi tabbas ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba akwai abin da yake aikatawa ba ya so a sani. Duk a ƙoƙarin gano hakan ne fa ya sanya ni shiga motarsa, ashe da rabon ya wulaƙanta ni a titi."
"Haba Mama, Baban ne ke munafurci?"
"Za ka zo ka ɗauke ni ne ko za ka tsaya kana ci gaba da tuhuma ta ne?" Ta tambaya a kufule kamar yana gabanta.
"Ki tura mini address." Ya faɗa a taƙaice.
A karo na barkatai ta sake buɗe labulen tagar da ke a sake ta leƙa. Da dai ta ga ba ta ga abin da take nema ba sai ta saki ta dawo cikin ƙaton ɗakin da ke ɗauke da furniture masu kyau, tana safa da marwa.
Sanye cikin riga da wando na kanti masu kyau ya fito, hannunsa ɗauke da cup ɗin tea yana sipping lokaci zuwa lokaci. Tun kafin ya ƙaraso yake kallon Hajiya Zainab ɗin. Ya san halinta sarai, ya san halin mahaifiyar tasa na sanya wa kanta damuwar abin da ya shafe ta, har ma da wanda bai shafe ta ba. Sai da ya nemi waje ya zauna kafin ya ce
"Mama, me ya faru?" Ya tambaya lokaci ɗaya yana ajiye cup ɗin da ke hannunsa. Kyakkyawa ne, fatarsa tana da ɗan duhu amma can ba, irin duhun nan mai kyau. Kansa cike yake da tarin suma da take a ɗan hargitse, sai dai kasancewar sumar tasa mai kyau ce ya sa ba ta yi muni ba.
"Je ka tambaye su." Ta faɗa tana nuna masa ƙofa. Murmushi ya yi don ya fahimci abin da take nufi, kafin ya ce
"Abin ne ya ɗaure mini kai Mama. Na ga Abba da Daddy duka zaune a haraba, alamu sun nuna akwai abin da suke jira."
Yanayin yadda ya yi tambayar ne ya kufula ta don haka da kamar ba za ta tanka ba, sai kuma can ta ce
"Suna jiran Babanku ya dawo su tuhume shi inda ya je tun safe."
Dariya Al-ameen ya sheƙe da ita ba tare da ya shirya ba. Da gasken gaske maganar Maman ta ba shi dariya.
"A tuhume shi?" Ya tambaya cike da mamaki bayan ya gama dariyar. Ba ta ce da shi komai ba, sai sake leƙa wa da ta yi ta taga don ganin abin da ke wakana a ƙatuwar harabar gidan, da ta lamushe motoci masu yawa, amma ko kaɗan ba za ka hango su ba ma idan ba wajen ka nufa ba, saboda girmanta.
"Da gaske Mama, tuhuma kamar ya ya kenan? Ta ya ya za su tuhumi Baba, bayan shi ne gaba da su?"
"Ko shi ya haife su, idan ya yi abin da ba daidai ba dole ne su nemi mafita, ko da ta hanyar tuhumar tasa ne."
Taɓe baki Al-ameen ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba, don da gaske abin ya ba shi mamaki ƙwarai. Shi dai bai san yadda aka ƙare ba, bayan ya gama abin da zai yi a sashen Maman ya tafi ɗakinsu don kwanciya.
Washegari, ƙarfe 7:00 Baba ya fito daga ɗakinsa hannunsa ɗauke da brief case. Kyakykyawan dattijon da aƙalla ya ba wa shekaru 60 baya. Amma wata irin halitta da Allah Ya yi masa, ba za ka taɓa cewa ya kai shekarunsa ba. Yana da matuƙar kyawun jiki, wanda jin daɗi da kwanciyar hankali su ne kusan kaso hamsin da suka samar da hakan. Yana sanye cikin manyan kayan da suka matuƙar amsar jikinsa, da hula zanna-bukar da ta dace da kalar shaddar jikinsa.
Da sauri Hajiya Turai ta ƙaraso da fara'a kan fuskarta tana ƙoƙarin karɓar brief case ɗin hannunsa ta ce
"Bari na taimaka maka." Sai da ya kalli fuskarta sannan ya mayar mata da martanin murmushin ya ce
"Babu damuwa, zan riƙe da kaina." Kamar ta ce wani abu, sai kuma ta basar ta ce
"To mu je ka yi break." A nutse ya girgiza kai kana ya ce
"No, i'm in such a hurry, idan na dawo zan ci."
"Amma Abban Muhammad ka san jiya ma fa haka ka fita ba tare da ka karya ba. Fisabilillahi idan ka yi mini haka yau ma zan ji daɗi? Wannan wanne irin aiki ne da ke ƙoƙarin shiga tsakanina da Abu Muhammad." Ta ƙare a shagwaɓe kamar wata ƙaramar yarinya. Tilas maganar da ta yi, da kuma sunan da ta kira shi da shi ya sanya shi yin murmushi. Ta san da irin salon da take cin galaba a kansa, don haka ba don ya so ba, ya yi murmushi kafin ya ce
"Mu je."
"Yawwah." Ta faɗa tana yin gaba.
A gurguje ya ci abincin, ba don yana jin daɗinsa ba, sai don kar ta ji babu daɗi. Amma duk hankalinsa ba ya wajen. Tana lura da duk wani motsinsa ba tun yanzu ba, gabaɗaya satin ma tana ankare da duk wani take-takensa. Tabbas akwai wani abu da yake ɓoyewa. To amma mene ne abun? Ta san halinsa sarai, ba a iya bugar cikinsa, kai gabaɗaya ma a iya zaman da ta yi da shi ta fahimci ba a iya jin cikinsa. Mutum ɗaya ne ta san ya san shi, ya san komai nasa, yana kuma jin komai na cikinsa, wato ɗansa.
Agogo ya kalla, ganin lokaci ya tafi ya sanya shi jan kujerar da yake kai baya ya miƙe yana faɗin
"Bari na tafi, I'm almost late."
Saboda mamaki ma ita kasa furta komai ta yi. To ina mutumin nan yake ta gaggawar zuwa? Me yake fitar da shi daga gida kullum da safe haka? Kuma koyaushe kusan a gaggauce? Me yake ɓoyewa? Mutumin da a da sai ya ga dama ma yake fita daga gidan, tun da yara ke masa aikin komai a kasuwa? Tabbas akwai lauje cikin naɗi. Amma ba za ta yi gaggawa ba, za ta bi komai a sannu ta gano ko ma mene ne cikin ruwan sanyi.
A harabar gidan Baba ya haɗu da ƙannensa biyu, Abba da Daddy. Suka gaisa cike da ƙaunar juna da tambayar lafiyar iyalansu.
"Yaya, jiya kuma mun yi ta jiran ka ba ka dawo ba." Daddy da ya kasa haƙuri ya tambaya.
"Oh jiya ko? Gaskiya duk kun yi bacci lokacin da na dawo. Akwai inda na je ne, so ban gama abin da ya kai ni wajen ba, shi ya sa na yi dare." Ya faɗa a nutse yana kallon Daddyn, don so yake ya fahimce shi, ya tambaye shi haka ɗin ne don kulawa ko kuwa ya ya? Tunanin nasa ya katse, lokacin da Abba ya ce
"Za ka fita kenan, to Allah Ya tsare."
"Ameen Ya Rabbi." Ya amsa kafin ya ɗora da
"Kira mini Ammeey in sauke ta a makaranta."
Kamar an tsoma shi a aljanna, haka Daddy ya ji, don haka da sauri ya amsa da "Toh." Yana wucewa sashensa. Ko babu komai ƙila Ammeeyn ta gano musu inda yake zuwa da safiyar Allah ba tare da ya sanar da su ba, a matsayinsu na 'yan'uwansa da ba shi da tamkar su a gabaɗaya rayuwarsa.
Sanye cikin doguwar rigar uniform ta fito, ba ta kai ƙasa ba, sai dai farar socks ɗin da ta saka ta rufe ƙafarta. Hijab ɗin da ke jikinta ƙarami ne daidai ƙirji, bayanta sanye da jakar goyo. Hannunta na saƙale a kan jakar goyon nata, tana tafiya kamar wadda ba ta da laka, fuskar nan kamar tana jira ne a ce ƙiris ta fashe. Lokacin da ta fito, Baba ya shiga cikin motarsa, don haka tana zuwa kamar ta fasa ihu ta buɗe murfin motar ta shiga. Ba tare da ta dubi wanda ke zaune a mazaunin driver ba kawai ta rufe ƙofar. A nutse Baba ya tayar da motar suka fice daga gidan.
"Ammeey." Baba ya faɗa bayan sun yi nisa da fara tafiya, ganin har lokacin ba ta ce komai ba, sai kuma cika take yi tana batsewa. Da sauri ta ɗaga idanunta masu kyau cike da mamaki ta kalli Baban, don ba ta taɓa tsammanin shi za ta gani ba, saboda ita dai kafin ta ga Baban yana tuƙi za ta iya cewa har ta manta.
"Baba!" Ta faɗa cike da mamaki, lokacin da murmushi ya suɓuce mata. Sai da ya kalle ta shi ma yana mamakin yadda ta yi maganar sannan ya mayar da hankalinsa kan titi, kafin ya ce komai ta ce
"Baba wallahi ban gan ka ba, ni fa ban ɗauka kai ba ne ba ma wallahi. Good morning Papa" Ta faɗa tana gyara zamanta. Murmushi ya yi, don ya fahimci hakan
"Da wa kike tunani to?" Sai da ta ɗan turo bakinta sannan ta ce
"Babu kowa fa."
Shiru Baba ya yi yana ɗan nazarin abin da ta ce ɗin. Har cikin makaranta ya kai ta. Ta sauka ta yi masa sallama bayan ya ba ta kuɗin break.
A bakin class ɗinsu ta hango ƙawarta Aysha, kamar yadda ta tsammata kuwa Fa'iza tana kusa da ita suna hira. Ita har ga Allah haushi take ji, kwata-kwata ba ta ma so aka kawo Fa'iza makarantar ba. Ga shi tana shirin ƙwace mata ƙawa. Su ma duk suna sanye cikin uniform ɗin kalar na Ammeey.
"Aysha." Ta faɗa bayan ta miƙa mata hannu. Murmushi ne ya suɓuce wa wadda aka kira da Ayshan, ta ba ta hannunta tana faɗin
"Dallah can, yau nutsuwa ce ta zo miki." Hakan da ta faɗa ya sanya Ammeeyn yin dariya tana neman waje ta zauna. Suka yi magana da Fa'iza da ke kusa da Aysha kafin suka shiga aji, don 8 na dab da yi.
"Aysha kin san me?" Fa'iza ta faɗa tana kallon Ayshar da ke zaune kusa da Ammeey. Idanunta da ke saye cikin wani farin siririn glass mai kyau ta ɗaga ta kalli Fa'izan. A haka idan ka kalle shi za ka iya tunanin tana saka wa ne kawai don ado, saboda yadda ya yi wa fuskarta bala'in kyau. Manyan idanunta kuma ko kaɗan ba su nuna alamar akwai wata nakasa a tare da su ba ballantana ta kai ga saka medicated glass, kafin ba tare da ta ce komai ba, ta girgiza kai kawai.
"Bari na je na dawo." Ammeey ta faɗa tana ficewa daga ajin kasancewar lokacin break ne. Hakan ya ba wa Fa'iza damar zama inda ta tashi.
"Kin san mene ne?" Yadda take ta maimaita tambaya ɗaya ne ya sanya ta gyara zamanta sannan ta ce
"A'ah ki faɗa mini to mana." Ta ƙare a ɗan dame.
"Wannan mutumin fa ya sake turo saƙo."
Har ga Allah ba ta san lokacin da ta dafe ƙirjinta ba tana runtse idanunta.
"Hmmm." Fa'iza ta faɗa kafin ta ɗora da
"A kan dai zuwa gidanku ne, ai wallahi ba ki so nema wa kanki zaman lafiya ba, ta ya ya ma ga hanya sassauƙa ki din ga damun kanki?"
"Fa'iza don Allah ki bari kin ji? Ni ban san yadda zan yi ba, na ce ya ƙyale ni ya fita a rayuwata amma ya ƙi bari. So yake Abba ya saɓa mini." Ta ƙare kamar za ta fashe da ihu.
Tsaki Fa'iza ta ja ta ce
"Ai kin ji tsiyarki. Wallahi a wannan karon ya ce idan har ba ki bari kun haɗu ba, tabbas sai ya je gidanku." Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin nazartar kyakykyawar fuskar Ayshan da ta yi shiru kamar mai nazari
"Kina ji? Idan a wani wajen ne ba kya so ku haɗu, kawai gobe ki zo gidanmu sai ku samu ku haɗu a nan."
"Ke Fa'iza wai mene ne haka? In haɗu da shi ya ce mini mene ne? Wallahi a'ah, ni dai ki ƙyale ni ba zan je ba."
"Ai dai kina so ki ci gaba da makaranta bayan mun gama secondary ko?" Ba ta jira amsar Ayshan ba, don ta san amsar hakan, don haka ta ɗora da
"Ai dai ke da bakinki kika ce Abba ba zai aurar da ke yanzu ba, kuma idan ya san kina kula wani to karatunki ya zo ƙarshe. Ni fa mafita nake nema miki, idan kuka haɗu a gidanmu babu wanda zai san an yi haka. Ku sha hirar ku idan kun gama ku tafi." Ta ƙarashe maganar tana riƙo hannunta. Hannunta Aysha ta ƙwace tana miƙewa ta fice daga ajin. Manyan fararen idanunta tuni kalarsu ta sauya, musamman da ma da suka kasance ba lafiyayyu ba. Shirin kukan da take yi ya sanya suka yi ja. Ba ta san me za ta cewa Fa'izan ba. Ba ta san me ya kamata ta yi ba, ta amince ta bar mutumin ya je gidansu karatun da take masifar so ya zo ƙarshe? Burin da take da shi tun yarinta na zama babbar 'yar jarida kamar mahaifiyarta ya tarwatse? Ko kuwa ta amince su din ga haɗuwa da shi a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba? Gabaɗaya ƙwaƙwalwarta a cunkushe take. Ko da ta fito break ɗin ma ba ta nemi Ammeey ba, don ta san dole ta tambaye ta dalilin sauyawarta. Ita kuma gabaɗaya ma ba ta son ta faɗa mata halin da ake ciki, ita ma Fa'izan don komai yana biyo wa ta wajenta ne shi ya sa ta sani.
Kasancewar ranar Juma'a ce ya sa da wuri aka tashi. Da wuri aka zo aka ɗauki Ammeey, don haka ko sallama da Aysha ba su samu sun yi ba.
Kamar kullum, ita ma Ayshan ba ta daɗe ba, Abeenta ya zo ɗaukar ta. Tun kafin ta shigo motar yake lura da yanayinta. Kamar mara laka haka take tafiya, hannunta ɗauke da wani littafi, ya yin da ta saƙala jakar goyo a kafaɗarta guda ɗaya.
"Good afternoon Abee." Ta faɗa lokacin da ta nemi waje ta zauna a wajen mai zaman banza.
"Afternoon my baby, wa ya taɓa Janan?" Ya tambaya yana kallon ta. Da sauri ta ƙaƙalo murmushi ta ce
"Babu kowa fa Abee."
"Na kusa daina zuwa ɗaukar Ayshatou, in dai har za ta riƙa dawowa a haka." Ya yi maganar lokacin da ya fara ƙoƙarin tayar da motar. Murmushi ta yi don ta san Abeen kawai ya faɗa ne, kafin ta ce
"Ka yi haƙuri Abee, kawai yau gabaɗaya mun gaji ne, ga yunwa kuma nake ji."
Da gaske shi ma faɗa ɗin kawai, don ya san ba abu ne mai yiwuwa ba. Don tun AyshaJanan ɗin ba ta san wace ce ita ba, yake wannan jigilar. A kullum, a kuma kodayaushe, ba ya gajiya. Duk rintsi, duk wuya, ruwa ko iska, babu wanda ke ɗaukar wannan sai shi ɗin. Daga kai ta, har ɗakko ta, sai dai idan wani babban uzurin ne sannan yake wakilta wani ya je ya ɗakko ta.
Da gudu ta ƙarasa ta rungume Ummeenta da ke zaune a kan kujera da laptop a gabanta tana dannawa.
"Welcome my baby." Ummeen ta faɗa bayan ta rungume ta ita ma.
"Ummee aikin ne?" Ta faɗa tana kallon abin da Ummeen ke yi a cikin laptop. Sai da ta yi murmushi kafin ta ce
"Shi ne kam. Maza je ki yi wanka ki ci abinci ki zo ki taya ni." Ta faɗa don ta san halin ɗiyar tata, idan dai har za ta yi aiki kuma Janan ɗin na gida, to kodayaushe tana gefenta ne tana kallon duk wani abu da take yi.
"To Ummee." Ta faɗa tana miƙewa da sauri ta shige ɗakinta. Da gaske Allah Ya zuba mata ƙaunar aikin jaridar a cikin jininta. Tana masifar so ta ga ta girma ta zama kamar Ummeen tata. A kaf duniya wannan ne babban burinta, kuma tana fata a ce watarana ta wayi gari Allah Ya cika mata shi.
Sai bayan isha'i sannan Ummee ta samu kanta. Don haka ta shiga gyara wa ɗiyarta kanta bayan ta wanke mata shi. Don ita ma kamar mahaifinta, duk wani abu da ya danganci ɗiyar tata in dai bai fi ƙarfinta ba ita take yi mata shi. Ko da aiki zai yi mata yawa, za ta gwammaci ta takure kanta ta yi mata duk wani abu da take so.
"Ummee da alama Yah Farouk ya koma can da zama." Janan ta faɗa bayan ta gyara kwanciyarta a kan cinyar Ummee. Murmushi Ummee ta yi kafin ta ce
"Ke dai kawai ki ce kin yi kewar sa."
"Eh wallahi Ummee, gidan ma gabaɗaya babu daɗi." Ta faɗa tana ɗan taɓe baki.
"To zuwa gobe zai dawo."
"Shi ne bai faɗa mini ba amma." Ta yi maganar tana tashi zaune tana kallon Ummee.
"Wannan kuma kun fi kusa. Ki tuhume shi idan ya dawo." Ba ta ce komai ba ta koma ta kwantar da kanta kan cinyar Ummeen tana jijjiga kai.
Sun shafe lokaci mai tsayi zaune a parlourn suna ta hira har bayan dawowar Abee, kafin suka yi sallama, Janan ta tafi ɗakinta ya yin da iyayen nata ma suka yi nasu ɗakin.
Kai tsaye ruwa mai ɗan ɗumi ta watsa wa jikinta, kafin ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar bacci, wadda da kaɗan ta wuce guiwa. Ta saka hula mai taushi a kanta da Ummee ta gyara mata shi ya yi kyau matuƙa.
A nutse ta cire glass ɗin da ke fuskarta ta saka shi a ma'ajiyarsa sannan ta ja bargo ta lulluɓe har wajen ƙirjinta. Sai a lokacin maganar da suka yi da Fa'iza ta dawo mata kanta. Ta runtse idanunta da ba ta iya gani sosai idan babu glass, tana jin yadda zuciyarta ke ɗan bugawa. Ita har yanzu ta rasa ɓangaren da za ta ɗauka. Amma idan dai har za ta bi inda zuciyarta ta fi karkarta, to za ta zaɓi mafarkinta ne, kuma burinta, ta bi shawarar da Fa'iza ta ba ta. Za ta yarda su din ga haɗuwa da mutumin a duk inda ya zaɓa musu su haɗu, idan dai har hakan ba zai zama sanadiyyar rugujewar burinta ba.
Toh Alhamdulillah!
Cikin ikon Allah, ga ni yau ma cikin wata sabuwar tafiyar mai ƙarko. Ina fatan za ku ba ni haɗin kai kamar yadda aka saba, mu tsunduma cikin wannan tafiyar mai tsaya wa a zuci.
Ba zan ce tafiyar ta fi sauran ba, amma na san mai ƙarko ce mai kuma taɓa zuciya. Ina kuma da tabbacin za ku ce na faɗi hakan.
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 02
Sanye cikin uniform ɗin islamiyya, riga da wando da dogon hijabi wanda da kaɗan ne bai ƙarasa ƙasa ba ta fito daga ɗakinta. Daidai lokacin da Ummi ma ta fito daga nata ɗakin, sanye cikin doguwar rigar atamfa da wadataccen mayafinta da ya dace da kalar atamfar. Ta kalli Janan da ke ƙarasawa inda take ta ce
"Kin fito?"
"Eh Ummee, ina shirin zuwa ne ma in faɗa miki." Ta faɗa a nutse. Ba tare da Ummee ta ba wa abin da take faɗa ɗin muhimmanci ba ta kafe ta da idanunta, lokaci guda tana nazarin ta. Ta riga ta san halin ɗiyarta, a kuma kowanne yanayi take, tana ɗaya daga cikin mutanen da ke saurin gano akwai wani abun. Don haka cikin kafe ta da idanun dai ta ce
"Aysha, lafiya kuwa? Akwai wani abu da ke damun ki?" Ta tambaya kamar a ɗan ruɗe. Da sauri Janan ta girgiza kanta kafin ta wanzar da murmushi a kan fuskarta ta ce
"Eh fa Ummee me kika gani?"
"No, dole akwai wani abu.." Kafin ta ida abin da ta fara faɗa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 24