Ya fi dacewa mu matsa mu ba su wajen".
"Ai kuwa na ga alama". Na yi maganar yayin da nake bin bayansa muka matsa gefe, mun ɗan yi hira jifa-jifa kafin Amira suka yi sallama da Mansur. Da ya buɗe bayan boot ɗin motarsa ya fara sauƙe mata manyan ledodi sai da abin ya ba ni tsoro aƙalla sun kai bakwai a ƙidayen da na yi kuma dukkannisu shaƙe suke da kaya. Har da kukanta da Mansur zai tafi shi ma duk yanayinsa ya sauya haka ya shiga mota ya tafi bayan ya yi mata alƙawarin ƙiran ta da zaran ya isa garin da zai je.
Muka kwashi ledodin wanda za mu iya muka shiga da su ragowar kuma muka saka yara suka shigo mana da shi. Ina cikin lallashina Amira a ɗakinsu Umma ta aiko ƙira na na tashi da hanzari na je.
[7/19, 7:42 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1️⃣2️⃣
Tana zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanunta kamar mai bacci. Gaban ta wani baƙin leda ne a ajiye. Sai da na nema waje na zauna kafin na ce"sannu da dawowa". Ba tare da ta buɗe idanunta ba ta amsa mini tana ci gaba da cewa"ki haɗa wuta ki ɗaura min ruwan kunu". Na ɗan jim kafin na ce"Umma lokacin islamiyya fa ya yi". Sai a sa'ilin ta buɗe idonta tana kallona"ai tun da ba ki da safe ba to tabbas sai kin fita na rana".
"Ranan nan ma fa ban sama zuwa, da kin yi haƙuri yau ɗin na je ko da yamma inna dawo sai na fita da kunun". Ba ta ce da ni komai ba ta ta shi ta ɗauki ledar ta shige cikin ɗaki ba ni da zaɓi dole na tashi na fito na huta wuta na ɗaura ruwan da ta umarce ni na zauna na zabga tagumi sai da ruwa ya tafasa na je na sanar da ita ta fito ta dama kunun yayin da na shiga ciki na gabatar da sallan zuhr. Na fito na yi wanka na fara shirin fita idona ya raina fata lokacin da ta miƙo mini kwallin ta ce na saka a idona bayan ta gama turare bokatin kunun da hayaƙi.
Zuciyata kamar za ta tsago ƙirjina ta bayyano waje tsabar bugawan da take yi duk kuka da magiyar da nake yi wa Umma hakan bai yi tasiri ba, dole ƙanwar naƙi na karɓa kwalli na saka a idona. Na ɗaura bokatin a kaina na fita ina tafe ne kawai amma ban san inda nake cilla ƙafafuna ba mussamman da na ga duk layin da na wulga sai jama'ar wajen su bi ni da kallo. Gabaɗaya sai na ji ni duk a takure na kasa sakewa.
"Amatullah Mannir".
Na tsinkayo amon muryar Malam Suleiman Malamin ajinmu a islamiyya kamar daga sama, a hanzarce na waiga ina kallonsa yayin da shi ma ɗin ni yake kallo kallo irin na mamaki.
"Ina wuni Malam".
Na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa sai ya ƙara dawo mini da wata tambayar.
"Ina za ki je haka bayan lokacin islamiyya ya yi?".
"Yau ba zan sama zuwa ba ne".
"Me yasa?".
"Zan je talla ne".
Ya yi shuru na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya furta"waye ya sa ki tallan?".
Muryata tana rawa na ce"Ummata".
"To mu je islamiyya sai ki ajiye tallan a staff a wajena ki wuce aji, wataƙila a can sai ya ƙare".
"Malaman ba kayan islamiyya ba ne a jikina da kuma na baro jakata a gida". Ya ɗaure fuskarsa tamau"wuce mu je kafin na sassaɓa miki". Ban kuma cewa komai ba ya wuce gaba ina bin sa a baya har muka isa islamiyyan na ajiye kunun a staff kamar yadda ya ce. Ya ɗauko ƙur'ani ya ba ni ya ce da ni na wuce ajinmu. Haka na wuce ajin na je na zauna muka fara kara karatu, ko da muka fito sallan asr ban yarda mun haɗu da Ammi da Rauda ba don na san zan sha tambayoyi a wajen su, ina yin salla na koma aji na yi zamana ba mu tashi ba sai ƙarfe biyar muna yin addu'a na fito da saurina zan tafi Rauda ta dakatar da ni.
"Don Allah Amatullah ki tsaya".
Sanin girman wanda ta haɗa ni da shi ya sani tsayawa har ta iso gabana hannunta saƙale cikin na Ammi.
"Wai me ye yake faruwa ne kwana biyu ba kya zuwa? Yanzu kuma kin zo amma sam ƙi yarda ki haɗa inuwa ɗaya da mu". Ammi ta ci zancen cikin damuwar da ya bayyana har a cikin kalamanta, kafin na ba ta amsa Rauda ta karɓe zancen"kin san Allah yau muka ce idan ba ki zo ba daman za mu ke gidanku mu duba ko lafiya".
Cikin ƙosawa da sauraran zantukansu na furta"lafiyata ƙalau kamar yadda kuke gani ai babu alamar jinya a tattare da ni".
"Amma ai akwai alamar damuwa a tattare da ke".
"Don Allah Rauda mu bar maganar nan. Tun da yanzu kam na zo ai shikenan ko". Ina dasa aya na sa kai zan wuce wajen Malam Suleiman suka ƙara tsayar da ni.
"Wallahi Amatullah akwai wani abu da yake faruwa ko ma ya riga ya faruwa don ba haka kika saba zuwa ba. Kuma yaya Musbahu ya ce min ya gan ki kina talla a filin taurari, inda duk wata mai tarbiyya da kamun kai ba ta sanya ƙafarta cikin wannan filin. Me yake faruwa Amatullah?".
Ban yi aune ba na ji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniyata sai dai na yi jarumta da ƙarfin hali ban bari sun tsiyaya ba. Na ja dogon numfashi kafin na sama sararin faɗin"zan yi muku bayanin komai amma ba yanzu ba".
"Sai yaushe kenan?".
Na toshe kunnuwana"don Allah ku yi haƙuri ku bar ni haka. Na ce zan faɗa muku idan lokaci ya yi". Ina gama faɗin haka na bar wajen da matuƙar sauri na nufi staff wajen Malam Suleiman, shi kaɗai na samu duk ragowar malaman sun watse kasancewar lokaci ya fara ƙurewa. Sai da na yi sallama ya amsa kafin na shigo na tsuguna raina ya yi wani sanyi kamar an ɗaura mini ƙanƙara ganin bokitin kunun saura kaɗan.
"Amatullah".
Sautinsa ya dawo da ni cikin duniyar zahiri, na gyara tsugununan da na yi a nutse na ce"na'am Malam".
"Me yasa ba kya zuwa makaranta kwana biyu da suka wuce?".
"Malam ba na samun dama ne. Idan na fita talla ba na dawowa da wuri kuma idan na dawo da ragowa Umma za ta yi mini faɗa".
"Me yasa ba kya fita da wuri?". Na yi shuru don ba ni da amsar tambayar.
"Ban hana ki talla ba Amatullah kuma ba ina nufi kar ki yi abin da mahaifiyarki ta sa ki ba. Amma ina mai ba ki shawara da kar ki sake ki yi wasa da damarki, a wannan shekarun ne kawai ki ke da damar yin karatu sosai kafin abubuwa su sauya. Ke mace ce rayuwarki gabaɗaya ƙanƙanuwa ce saura ƙiris ku haɗa hadda ki dage duk runtsi ki na zuwa".
"In sha Allah zan daure ina zuwa". Na amsa a raunane.
"Ga kuɗinki an saya na ɗari bakwai da saba'in". Na sa hannu na amsa kuɗin ina yi masa godiya maimakon na tashi na tafi sai na koma na zauna, hakan ya sa shi zuba mini ido cike da zallar mamakin dalilin da ya sani share waje na zauna.
"Lafiya kuma kika koma kika zauna?".
Cike da tsoro na ce"Malam wata alfarma nake nema daga wajenka". Ya tattaro dukkan hankali da nutsuwarsa gare ni"to ina sauraronki".
"Malam so nake yi a yi wa mahaifiyata nasiha da kuma tsoritarwa akan wani aikin saɓon Allah da take aikatawa wanda ba zan iya faɗawa kowa ba. Sannan alfarma ta biyu tambaya ce da ni da na daɗe ina buƙatar amsarta na rasa wanda zan tunkara da lamarin. Malam mahaifiyata ta kasance mai kaifin harshe irin mutanen da komai ya fito daga bakinta za ta furzar da shi ga ko waye ba tare da tunanin abin da kan je ya dawo ba. Tun kafin na yi wayo take jefa da mungayen kalamai tsinanniya, shegiya wani lokacin har ta suffata ni da ƴar zina. Kuma ni kaɗai ce ƴarta a duniya balle na yi tunanin son da take yi wa sauran ƴaƴanta ne ya rinjayi wanda take yi mini. Yayin haihuwata ta sama matsala har sai da aka cire mata mahaifa wanda hakan yake nuni da ba za ta sake haihuwa ba bayan ni. Tun abin baya mini ciwo har an kai munzalin da nake kasa bacci saboda damuwa".
Na tsagaita saboda kukan da ya taso mini a lokaci guda na yi na yi son raina ba tare da ya lallashe ni ba kana na ɗaura daga inda na ka burki.
"Malam ba yabon kai na sama tarbiyya daidai gwargwado daga wajen mahaifina, ina da kamun kai da nutsuwa. Duk layinmu da ni ake buga misali wajen kyakykyawan hali da ɗabi'un ƙwarai. Amma tsorona ɗaya kar bakin da mahaifiyata take yi mini ya yi tasiri a kaina, ya wargaza duk shiri da tanadin da na yi wa rayuwata. Mahaifina ya sha nusar da ita da fahimtar da ita illar abin da take aikatawa amma kamar ana watsa ruwa a bayan ƙwarya".
Jikina ya soma rawa saboda kukan da ya gama galaitar da ni duk da bai ce da ni komai har lokacin amma na ji sanyi a cikin raina. Ko ba komai yau na fitar da damuwar da ta daɗe tana yi mini kai kawo a cikin ƙalbina.
Sai da aka shafa wasu mintuna kafin Malam Suleiman ya ja dogon numfashi ya fesar daga bakinsa da har da na ji sautin fitarsa. Kana ya soma magana cikin jimami da tarin damuwa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Amatullah ko wani bawa kika ga cikin wannan duniyar yana da tashi irin damuwar. Da za a ba ki tahirin rayuwar wasu mutane sai babu shakka da sai kin yi mamakin yadda aka yi har yanzu suke dariya, rayuwa ce lokaci shi yake warkar da komai. Yanzu kin ga lokaci ya ƙure ki tashi ki je gida gobe idan kin zo sai mu ƙarisa maganar".
Cike da girmamawa na ce"na gode sosai Malam na gode da lokacinka da ka ba ni ka saurare ni". Ina gama maganar na tashi na ɗauki bokitin na ɗaura a kaina zan fita ya tsayar da ni.
"Ki cire damuwar komai a cikin zuciyarki. Sannan a duk lokacin da za ki fita talla ki dinga saka hijabi mai girma da zai rufe miki jikinki".
"To in sha Allah, na gode Malam". Na amsa cike da kunya ina sadda kaina ƙasa. Lokaci da na fito kowa ya watse daga islamiyyan kafin na iso gida har an ƙira salla, bayan cinikin da Malam Suleiman ya yi mini a hanya na ƙara yin cinikin naira ɗari uku jimillan kuɗin gabaɗaya ya kama dubu ɗaya da naira saba'in haka na koma gida a gajiye ina ajiye bokitin kunun, na yi alwala na yi sallan magrib na fito na haɗa wuta na ɗaura mana abinci kana na koma ɗaki na kai wa Umma cinikin da na yi.
Ban ga damuwa ko tashin jin daɗi a fuskarta ba duk da kuwa ban sayar da kunun gabaɗaya ba. Ki irgawa su ba ta yi ta ajiye su a ƙasan matashi har na tashi zan fita ta ce na koma na zauna na koma na zauna ina sauraronta.
"Mun yi magana da Sahura akan za ki dinga tafiya talla tare da Amira don na ga ta fi ki wayewa da sanin harkan. Da zaran kin kammala haɗa haddarki sai na fara yi miki soyayyar doya da ƙwai kina fita da shi bayan sallan isha'i'.
Na ɗaura hannu a ka"na shiga uku Umma. Amira kuma?". Ta gallo mini wata banzar harara"ita ta ko tana da wani aibu wanda ni ban sa ni ba? Da za ki kafa hujja da shi".
"Wallahi inda take kai talla duk maza ne a wajen marasa ɗa'a. Umma kin gan su kuwa? Duk ba su da kamun kai kuma ba sa kunyar haɗa jiki da mace, ko ita Amirar ma ki tambaya za ta faɗa miki". Ta yi sauri katse mini numfashi.
"Inna fahimce ki kina so ki ce ita ma kanta Amirar ba ta da kamun kai kenan ko? Idan da kuwa haka take to ina tabbatar miki ke ce ta farko wacce za ta fara gurɓatawa tun da ba ki da wata ƙawa ta kusa sama da ita kullum kuna tare da ita".
Na zube ina yi mata rantsuwa"wallahi tallahi Umma kullum muka zauna da ita sai na yi mata nasiha akan abin da take yi ba daidai ba ne".
"Amatullah na gama yanke shawarar dole ki fara bin Amira kuna fita tare har izuwa lokacin da ke ma kanki zai waye".
Wani irin zafi da tafasa zuciyata take yi mini na cire leɓena hawaye suna zuba daga idona da ƙyar na iya furta"Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi". Ban jira abin da za ta ce ba na tashi na fita, har na gama girkin hawayen idona bai tsaya ba.
Yanayin da nake ciki ya sani sallamar yaran da nake yi wa karatu don babu abin da zai iya aiwatarwa a halin da nake ciki. Ina yin sallan isha'i na kwanta raina gabaɗaya babu daɗi.
Kamar a cikin mafarki na soma jiyo wani tashin sauti da ya sani buɗe idanuna da ƙyar saboda ciwon kan da ya addabe ni. Na laluma gefena ban ji alamar Umma tana kwance a gefe na, na yi zumbur na tashi na jawo tocilan da yake ƙasan matashi na kunna na haska ɗakin ban ga Umma ba. Kuma har lokacin ban daina jin tashin sautin ba.
Haka ya sa na fito falo na haska tocilin daidai inda kunnuwana suke jiyo mini sautin. Babu shiri na yi zaman ƴan bori saboda munin abun da na yi tozali da shi.
Umma ce tsaye tana kewaye Abba riƙe da kw turaren wuta tana yi mass hayaƙi, ɗaurin ƙirji ne a jikinta yayin da ta ware kitson kanta ta bar gashin haka ba tare da kallabi ba. Tana wani irin suturai da yaren da tun da na zo duniya ban taɓa jin sa ba balle na san nau'in sa.
[7/20, 1:53 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 1️⃣3️⃣
Ƙarar faɗuwar tocilan daga hannuna shi ya fizgo hankalinta zuwa gare ni take na ga ta rikice irin rikicewar da tun da ta haiho ni ban taɓa ganin ta cikin makamancin sa ba. Jikinta gabaɗaya ya soma rawa zan iya rantsuwa da Sarkin da ba shi da abokin tarayya ban taɓa ganin ta cikin wannan halin ba, sai dai bushashshiyar zuciyar da take ta shi ya hana ta sa fasa abin da ta yi niyya ba ta dakata da abin da take yi ba har sai da ta gama, wani ƙarin abun mamakin da ya hana ni tashi daga zubewan da na yi shi ne har lokacin Abba bai tashi ba yana nan kwance kamar gawa.
Sai da ta ƙara zagaye shi sau uku tana ƙiran sunanta tare da busa masa hayaƙin kafin ta ajiye kwasko a gefe ta nufo ni tamkar kububuwa. Cak ta ɗago ni ta dige ni akan dugadugaina ta finciki hannu kamar za ta raba ta da gangar jikina ta ja ni zuwa cikin ɗaki muna shiga ta cilla ni kam gado ta rufe ƙofar ɗakin kiruf.
"Me ya fito da ke cikin wannan daren?".
Ta watsa mini tambayar babu alamar wasa a tattare da ita yayin da ta dalle mini idona da tocilan da ta ɗauko kafin ta rufe ƙofar ɗakin.
Ruɗu da riɗimewar da na yi ya sani kasa cewa komai illa numfashin da nake sauƙewa a wahala. Ta zo dab da ni ta zauna kafin na yi aune na ji ta damƙo gashin kaina da na tufke ta bayan wuyana ta riƙe gam tana gindaya mini sharaɗi.
"To billahillazi bari na ja miki kunne, ki manta da duk abin da kika gani ki ɗauka tamkar mafarki kike yi kuma har yanzu ba ki tashi daga baccin da kike yi ba. Idan kika sake na ji labarin nan a wani wajen sai kin yi mamakin abin da zan aikata gare ki, ki burne duk abin da kika gani a yanzu don na tabbatar da cewar sai kin fi kowa amfanar abin da na aikata a nan gaba kaɗan".
Na buɗe baki zan yi magana ta katse mini numfashi.
"Ba na so ki tambaye komai ki dai kawai ki yi abin da na ce da ke". Cikin wani irin yanayi da ya zarce a ƙira sa da tashin hankali ko firgici na ce"in sha Allah". Na ja bargo zan kwanta duk da na san ko da na kwantan ba zan iya baccin ba.
"Amatullah idan har kika fallasa wannan sirrin babu shakka sai na tsine miki kuma sai kin biya ni ɗawaniyyar da na yi dake". Zumbur na miƙe tsaye jikina yana wani irin matsanancin rawa duk yanda na so na yi magana amma hakan ya gagara, babu shiri na zube ƙasa sakamakon gazawar ƙafafuna na kifa kaina jikin gadon ina rera wani irin kuka marar sauti.
Ko gizau Umma ba ta yi ta haye gado ta yi kwanciyarta ba tare da ta damu da nake ciki ba, babu abin da yake sanya zuciyata tafasa da hana ruhina samun sallama da nutsuwa kamar idan na tuna ban san turaren me ye Umma take yi wa Abba ba.
Tsorona guda kar ta cutar da shi don na tabbatar idan wani abun ya faru da shi ba zan taɓa rayuwa ba ni ma. Ko motsawa ban yi ba har aka yi ƙiran assalatul farko bayan mintuna ƙadan na ji ana bubbuga ƙofar ɗakin na tashi jikina gabaɗaya babu ƙwari ina dafe jiri yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa na isa na buɗe ƙofar.
Ganin Abba tsaye yana ƙoƙarin saka hularsa ya sani yin mutuwar tsaye hasken tocilar wayarsa da ya kunna a falon shi ya ba ni damar ƙarewa fuskarsa kallo.
"Ku tashi asuba ta yi kar lokaci ya ƙure, ni ma masallaci zan tafi yanzu".
Kar ya juya ya fita na kasa cewa komai tsabar giyar mamakin da yake ɗawainiyya da ni. Na ja dogon numfashi na fesar da shi ta bakina ina jeranta hamdala da godiya ga Allah a cikin ruhina. Alwala na fito na yi kana na koma ciki na yi salla na zauna akan sallayan ta zabga tagumi duk damuwar da take kai kawo a cikin ruhina amma bakina ya kasa cewa komai sai dai ina da yaƙinin Ubangijina masanin abin da yake cikin zuƙatana ne kuma babu shakka yana sauraron yaren zuciyata.
Har gari ya fara haske Umma ba ta tashi ba balle ta yi sallan asubahi, kuma na yi mini kashedin kar na ƙara tashinta daga bacci kowa za ta kwana da wuni. Don na taɓa yi karon mu da ita a sa'ilin bai yi mini daɗi ba.
Yanayin da nake cikin bai hana ni tashi na haɗa wuta na ɗaura mana ɗumame ba, na zubowa Abba na shi na kawo masa na ajiye a gabansa ina gaishe shi, cike da kulawa ya amsa mini yana bi na da kallo. Zan tashi ya ce na koma na zauna.
"Kamar akwai abin da yake damunki ko?".
Na jijjiga kaina"babu komai".
"Amma kin san dai a duniya gabaɗaya babu wanda ya san halinki ya kuma karanci dukkan motsinki sama da ni ko?".
A sanyaye na furta"haka ne Abba".
"To sanar da ni me ye yake damunki Amatullah?".
Kafin na kai ga ba shi amsa Umma ta fito daga ɗaki tsam na ga Abba ya tashi tsaye yana faɗin"kin tashi kenan? Ai daman yanzu nake son in mun magana da Amatullah na shiga na tashe ki sai kuma kika fito".
Ba ta amsa ba har sai ta zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana jijjigawa ta ce"Allah ya yi na tashi ko ba ka ji daɗin hakan ba ne?".
"Ni na isa na faɗi haka Hafsatu ni waye? A'a wallahi kawai dai na ga shurun ya yi yawa ne".
Banza ta yi da shi hakan ya ba ni damar gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ba tare da ta kalle inda nake ba.
"Kai kuma za ka zaune ne ko za ka ci gaba da yi min tsayeye a ka, kamar ka haɗiye taɓarya".
Da rawar jiki na ga Abba ya koma mazauninsa ya zauna ko abincin da yake gabansa ya kasa buɗe wa balle ya ci. Hakan ya sa Umma sakin wani ƙayataccen murmushin da har sai haƙwaranta suka bayyana.
"Amatullah tashi ki je ɗaki ki fara haɗa mana kaya, tun da Ubanki ya dage akan sai mun tashi daga gidan nan gwara mu fara shirin tun yanzu".
Abba ya yi wuf ya karɓe zancen"ranki ya daɗe uwar gida ran gida ai tun lokacin da kika nuna ba kya so na janye maganar tashin. Babu inda za mu je tun da har kika nuna ba kya son hakan".
"Manniru ban isa ka watsa min tsaba kaji su bi ni ba, salon ƴan uwanka sun kwanko ƙafa su zo har cikin falon nan su yi min ɗiban albarka su ce na hana ka sauƙe aiwatar da abin da ka yi niyya. Ai tun da ka furta za mu tashi to babu makawa sai mun bar gidan nan".
"Wallahi babu wani daga cikin ƴan uwana da ya iso ya zo ya gaya miki magana ahalin ina ji ina gani. Babu inda za mu har sai lokacin da kika ji zuciyarki ta sama nutsuwa da lamarin". Abba ya ƙare zancen cikin tsatsar biyayya kamar zai yi mata sujjada.
Umma ta gyara zama tana duban sa da wutsiyar idonta"tashi ka zauna a kujerar mana. Ko ka manta ikararin da ka yi na cewar kai ne mai gidan". Da mamaki gami da al'ajabina sai na ga Abba ya tashi ya zauna akan kujerar, zuciyata ta harɓa da wani ƙarfin bala'i take na faɗa tunani. Kenan da Umma ba ta ce ya kau kujera ba a ƙasa zai ci gaba da zama?.
"Tashi ki ba mu waje za mu yi magana". Muryar Umma ta dawo ni duniyar zahiri daga tunanin da na yi nisan kiwo a cikinta, na tashi na fita waje ba na jin zan iya cin komai shi yasa ban zuba abincin ba na zauna na zuba tagumi yanayin da na sama Umma daren jiya da abun da ya faru yanzu ya dinga yi mini safa da marwa a cikin kwanyata. Tabbas akwai wani surkulle a cikin hayaƙin da Umma ta yi wa Abba jiya da ya juya masa kafatalin tunaninsa.
"Ke kuma lafiyarki da sanyin safiyar nan kika zagba tagumi?". Muryar Amatullah ya fizgo tunanina da ya yi nisa da gangar jikina, na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya ina miƙa mata kujera ta zauna. Maimakon na amsa mata tambayar da ta yi mini sai na sako wani maganar na daban.
"Umma ta ce za mu na tafiya talla tare da ke, ban san ko kin san da maganar ba".
Ta ɗan murmusa kafin ta ce"tun jiya Ummata ta sanar da ni. Kuma na ji daɗin haka sosai fiye da zatonki".
"Amma kin san ni fa ba zan na daɗewa ba saboda zuwa islamiyya".
"To na ji ustaziya".
Tana rufe bakinta Abba tana fitowa ta gaishe shi ya amsa yana saka takalmarsa ya fita da sauri, sai da na bi shi da ɗayar takalminsa don haɗin gambiza ya yi ba tare da ya sani ba. Na tsaya a zaure na goge hawayen da ya zubo mini kafin na dawo wajen Amira, duk yadda ta so jan hankali da hira ta kasa samun kaina. Haka har Umma ta kammala kunun ta ce da ni na je na saka kwallin kafin ta shigo kasancewar kwallin yana wajena ina ajiye da shi.
Ban sa ka ba amma ko da ta shigo ta tambaye ni na ce da ita na saka. Don har cikin raina nake jin ba zan iya yin abin da take so na yi ba. Akan idona ta yi wa bokitin kunun turare har da gammo da zan naɗa bai
tsira ba, sai da ta gama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 24