ita a ɗaura mata talla tana yawon layi-layi, kororo-kororo, lungu-lungu da sunan neman kuɗi. Wanda ina da tabbacin ba ku rasa ci da sha ba balle suturar da za ku rufe tsiraicinku, ya kamata ka farka daga baccin da kake yi kai ne na miji a gidanka kuma kai kake da alhakin gyara shi da daidaita shi. Ka sani fa akwai ranar Allah zai tambaye ka amanar da ya ba ka a ranar da babu lauyan da zai kare ka".
Numfashi mai zafi Abba ya furzar daga bakinsa sai da ya musguta kafin ya ce"wallahi ni ma har cikin zuciyata ba na son wannan tallan da Amatullah take yi......".
"Kar ka wani rantse min Manniru. Kai ne fa namiji a cikin gidanka kuma da Amatullah da uwarta duk a ƙarƙashin ikonka suke, idan suka lalace sai Allah ya tambaye ka don haka zaɓi ya rage gare ka".
"Ba shakka Maman Umar dole ka sa shi a gaba kina yi masa huɗubar banza. Ke ki fara gyara naki gidan auren mana kafin ki wa gidan wasu katsalandan".
"Ke Hafsatu ki iya bakinki idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri. Zan jure komai akaina amma ba zan juri cin mutumci ga ƴan uwana ba. Maman Umar kamar uwa ce a gare ni zan iya ƙarya duk hannun da ya nuna mata ƴatsa".
"Dole na furzar da abin da yake cikin raina Manniru, ko yaushe ƴan uwanka gani suke yi kana ɗaukar duk ɗawainiyyarmu bacin ba haka ba ne. Talla dole na ɗaurawa ƴata don na rufawa kaina asiri ina da yaƙinin ko aurenta ne ya tashi babu wanda zai tsinana mana komai daga kai har dangin nakan". A matuƙar fusace Abba ya soma magana kamar zai yi aron baki.
"Ya ishe ki haka kar ki wuce gona da iri. Ki ɓace min daga gani kafin na yi miki abin da zuƙata da yawa za su raunana". Tanadin kallo ta ƙare masa tas kafin ta buga tsaki ta wuce cikin ɗakin bayan ta ba ni umarnin tashi daga wajen a cewarta a daga wajen su nake koyan baƙin hali da gardama. Muna shiga ɗaki ta tsare da ido tamkar mai son gano wani gaskiya a tattare da ni.
"Kar ki ba ri kalamansu su sama matsuguni a cikin kanki balle har zuciyarki ta amshe su. Ke ganau ce ba jiyau ba cikinsu gabaɗaya waye yake taimaka mana da ko da tsinke ne? Ko yaushe gani suke yi kamar duk duniya babu namijin da yake ƙoƙarin sauƙe haƙƙoƙin iyalinsa da wadata su da komai na rayuwa kamar ɗan uwansu don zuzurutun son kai. Dole na yi sana'a haka zalika dole ki je min talla don mu rufawa kanmu asiri".
Tun da ta fara zancen kaina yake ƙasa har ta gama kana a hankali na furta"in sha Allah Umma zan ci gaba da zuwa matuƙar ba Abba ba ne da kansa ya dakatar da ni". Ba amsa mini ba illa ɗauke kanta da ta yi gefe guda, na fito na yi alwala na koma na yi sallan zuhur a ƙuraran lokaci babu jimawa aka yi ƙiran asr na yi su gabaɗaya. Na janyo jiki na zauna a ƙasa kusa da ƙafafunta.
"Umma kin ga ikon Allah ko? Ga shi yau na sayar da duk kunun ba tare da ko sisi ya yi ciwon kai ba. Daman na gaya miki idan Allah ya so kuma ya datar da mu ko ana so ko akasin haka zan sayar da kunun, Umma shi Allah mai nuna iko da isarsa ne akan komai kamar yadda ya nuna mana a yau ko da laƙanin nan ko babu idan ya nufa wallahi ko a cikin gidan nan ne sai kin ga an saye kunun, ina roƙonki da mu haƙura da wannan abun ki watsar da duk zantukan da Malamin bogin nan ya zuba miki a cikin kanki, ni kuma na yi miki alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina na ganin ban dawo da kwantan kunun ba".
Tun da na soma maganar take bi na da wani irin kallo da na gaza gane ma'ana da maƙasudin yin sa. Ta taɓe baki kafin ta ce"ki daina ɓata bakinki don babu abin da za ki ce min na fasa aiwatar da abin da na yi niyya musamman yanzu da hassadan Sahura ya fito ƙiri-ƙiri akan mu. Dole ne na tashi na tsaya akan ƙafafuna don na san ba za ta taɓa bari na haka banzan ba".
"Don Allah ki yi haƙuri ki tura mata mungun nufinta".
"Ke Amatullah". Ta doka mini tsawan da ya tursasa mini yi wa bakina linzami nan take.
"Kar ki ƙara yi min wannan maganar don na riga da na gama yanke shawara". Haƙuri na ba ta na ja bakina na gimtse har izuwa lokacin Anty Sawwama ta soma shirin tafiya a sa'ilin Abba ya tafi masallaci bai dawo ba.
Fuskata ɗauke da annuri nake faɗin"Anty har tafiya za ki yi ga shi ko abinci ba ki ci ba". Kafin ta yi magana Umma ta yi caraf ta amshe zancen kamar jira take yi na ce kule ta ce da ni cas.
"Ai dole ta tsaya jiran abinci tun da shi ɗan uwan natan ya kawo ya ajiye. A kan idonta ya dawo ai haka ya shigo siƙau hannu na dukan cinya, don haka ba abin da za mu ɗaura balle har ta sa tsammanin ci".
Sosai kalaman suka daki zuciya na ji wani ɗaci a bisa maƙoƙarona yana tasowa har izuwa cikin bakina. Satan kallon Anty Sawwama na yi na ga gabaɗaya jikinta ya yi sanyi da alama ita ma zancen ya baƙanta mata ruhi sai dai ba ta bayyana shi a fuskarta ba.
"Ba komai Uwata zan tafi, daman na gama abin da ya kawo ni kuma mun yi sallama da shi kafin ya fita masallaci. Kin ga kuwa ai babu abin da ya rage". Ta yi zancen yayin da take miƙewa tsaye kafin na ce wani abu har ta fice daga falon na yi wuf na rufa mata baya muka fito daga gidan tare, har ƙarshen layinmu na yi mata rakiya kasancewar ranar babu islamiyya kana muka yi sallama a dawo gida.
Ganin har lokacin Umma ba ta ce da ni na haɗa wuta ko kuma ga abin da za a girka ba, ya sani shimfiɗa tabarma a ƙofar ɗakinmu na ɗauka jakar islamiyyata na soma tilawa. Kamar faɗuwar aradu haka abin da ya faru da ni ɗazu a wajen talla ya faɗu mini a rai na ja dogon numfashi na fesar ina lumshe idanuna.
Na sha jin ana cewa ƴan talla ba su da kunya kuma ba sa tsoron ta mutuwa balle ta yi rayu wanda wasu suke amfani da wannan dalilan suke yi wa duk wata mai talla kuɗin goro. Ban taɓa yarda kalaman da ake faɗa akan su ba sai yau da na ga zahiri ya kuma faru a kaina. Tabbas akwai babbar matsala matuƙar aka ci gaba da tafiya, zuciyata ta harba yayin da na tuno irin musayan kalaman da Zaina da Mai aska suka yi da irin ikirarin da alwashin da ta yi a kaina. Gabaɗaya sai na yi gwiwoyina sun sake zuciyata ta karaya yayin da raunina ya bayyana.
"Amatullah".
Sautin ƙiran sunana da Amira ta yi ya fizgo tunanina da ya yi ƙaura daga gare ni izuwa gangar jikina. Na gyara zamana a ƙoƙarin daidaita nutsuwata.
"Amira yaushe kika zo kika zauna a nan?".
"Lokacin da kika yi nisa cikin kogin tunanin da kika faɗa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ba tare da na tanka mata ba.
"Wai me ye yake damunki ne? Tun da kika shigo na fahimci akwai tsoro da firgici a tattare da ke".
"Ina Ummanki?".
Ta murmusa kafin ta ce"tana cikin ɗaki tana bacci ki kwantar da hankalinki na san abin da kike tsoro. Kafin ta kwanta sai na tabbatar ta manta komai, kuma ina da tabbatar ko musayar alburushi suka yi da Ummanki Ummata ba za ta taɓa hana ni zuwa inda kike ko mu'amala da ke ba, a wajenta laifin wani ba ya shafan wani, don haka ki sanar da ni kawai me yake faruwa?". Tiryan-tiryan na kwashe komai na faɗa mata da ita kaɗai na ji zuciyata ta nutsuwa da ita, ta ƙura mini ido kafin can ta soma maganar da ya ƙara sanya hankali tashin gauron zabuwa.
"Don ɗan wannan abun shi ne duk kika bi kika tashi hankalinki? Indai har wannan abun zai ɗaga miki hankali to ai ba ki shirya yin talla ba ne Amatullah. Wannan su ne abubuwan da suke faruwa yau da kullum kuma duk wacce ta amsa sunan cikakkiyar ƴar talla ya kamata ta san da su ta kuma tanadar wa kanta mafita".
"Kin ga haukan da ta yi kuwa Amira? Ni wallahi ta ba ni tsoro har na yanke shawarar ba zan ƙara zuwa wajen talla ba". Ta hanzarin katse ni"ai kuwa yanzu ma aka fara ɗaura ɗamarar yaƙi da su za ki yi, ki nuna musu duk abin da suke taƙama da shi kin dama su kin shaye. Ki fito a cikakkiyar ƴar tasha ki yi musu hauka da naɗe-naɗanta, hatta shi mai gidan nasun ki yi duk yadda za ki yi ki dawo da hankalinsa gare ki ta yarda za ki gasa musu aya a tafin hannunsu".
Sakeke na yi ina bin ta da kallo har ta kai aya kafin na iya magana.
"Wallahi Allah ma ya sani ni kam ba zan iya ba".
"Za ki iya kuma in har kika gwada ina da yaƙinin ke ce da riba. Ai ko a addini ma an ce ka kare kanka daga wanda zai cutar da kai, kuma ai raba cuta ga macuci ibada ne".
[7/13, 1:19 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 0️⃣9️⃣
Wuri-wuri na yi ido ina bin ta da kallo tamkar na sama majigi raina cike fal da mamakin zantukanta tsoron da yake cikin zuciyata ya bayyana ƙarara a bisa fuskana.
"Ki nutsu ki nazarce abubuwan da na faɗa miki. Don matuƙar tallan za ki yi da gaske to sai kin shafawa idanunki toka kin rikiɗa kin koma ƴar tasha ko ma na ce ƴar bariki. In ya so in kika dawo gida duk ustazancin da za ki yi sai ki yi".
"Ba na ma fatan na ɗau tsawon lokaci ina wannan tallan Amira. Allah ya sani ba zan iya yin waɗannan abubuwan ba". Dariya ta bushe da shi mai matuƙar sauti sai da ta tsagaita kana ta ce"lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan Amatullah amma ina da yaƙinin sanda za ki fara ma ba za ki sani ba".
"Ke Amira a uban waye kike yi wa dariya?".
Muka tsinkayo muryar Ummi kamar daga sama duk mu biyun muka miƙe muna kallon juna. Amira ce ta yi magana don ni kam bakina ya rufu kiruf.
"Da uban wanda ya tsarku nake yi. Inda abun da za ki yi kuma to bismillah".
"Billahillazi ki fita daga idona Amira ba ni da daɗi, yanzu zan yi wasan kura da ke hakan ba damuwata ba ne".
"Don girman Allah Ummi ki yi min abin da Allah bai yi min ba yanzu-yanzun nan. Idan kin cika ƴan halak kar ki bar ni da numfashi". Amira tana rufe bakinta Ummi ta cakumo ta da kokuwa suka kaure da faɗa kamar ba za su bar junansu da rai ba.
Duk yadda na so raba su hakan ya gagara sai da Baban Adnan ya fito daga ɗaki ya raba su, duk da hakan Ummi ba ta lafa sai sura take kai wa Amira.
"Malam ka matsa ka ba ni waje yau sai na koyawa yarinyar nan hankali. Sai na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan mahako ba ne kuma wallahi na gaba ya yi gaba na baya sai dai labari".
"Ke mahaukaciya ce wai? Ana raba ku har kina wani cewa a bar ki. To ka ga ki kashe ta in kin ga dama". Baban Adnan ya yi maganar cikin tsananin fusatan da ta bayyana har a kalmominsa.
Duk suka yi shuru sun yi zuru-zuru da ido, lokacin har an ca a kan su kowacce mata ta fito daga ɗakinta don ba wa idanunta abinci.
"Na lura da ke yarinyar nan Ummi sam ba ki da kunya, har za ki kalla tsabar idona ki ce wai na matsa na ba ki waje ki koya mata hankali?. Ko kin manta wane ne ni? To a matsayina na ɗan sanda ba zai yiyuwa na zuba ido ayi ɓarna akan idona ba".
"Da yake Ummi ce marainiyar wayonka dole ka ce ita ce ba ta da kunya. In shari'ar gaskiya za ka yi ai kamata ya yi ka bar su su fitar da raini a tsakaninsu, ina kuma adalci za ka yi kamata ya yi la fara da tambayar abin da ya haɗa su". Furucin mahaifiyar Ummi kenan yayin da take isowa wajen ta riƙo Ummi kana ta zarce da faɗin"ba fa zai yiyuwa ace duk gidan nan an sawa ɗiyata ido ba. Babu uban da ya isa ya takura mata tun da kuɗi muke biya muna haka muke biya. Daga yau na ba ka damar ki ƙwaci ƴancinki duk wanda ya taka ki kema ki taka shi komai girma, shekaru ko furfurarsa".
"Ai kuwa da kin ba ta lasisin aikata kuskure mafi girma a cikin rayuwata. Don duk ranar da tsautsayi ya sa ta yi wa Baban Adnan tashin kunya ko kallon banza, sai na yi mata raunin da har ta koma ga mahaliccinta rabonsa bai bar jikinta ba".
Maman Adnan ta yi zancen daidai sanda take fitowa daga banɗaki. Ummi ta mayar mata da martani daidai da zancenta.
"Billahillazi ko iyayenki ne suka zo gidan nan suka shiga karkata sai na ba su amsa daidai da su, balle kuma wani banza".
"Banza? Ummi mijin nawan kike da ƙira da banza akan idona? To yanzu ni zan koya miki hankalin da ke kika gaza koyawa Amira". Tana rufe bakinta ta tunkaru Ummi kafin ta yi aune tunin ta rotsa mata bokitin ƙarfen da ta fito daga wanka riƙe da shi a hannunta. Kan ka ce kwabo jini ya ce sallama alaikum jini kamar an yanka saniya sai zuba yake yi daga gashin Ummi da ta zube a ƙasa tana burburko tare da rausa ihu.
"Wayyo Allah! Jama'a ku kawo min ɗauki za ta kashe min ɗiya. Shikenan ta tsiyayar mata da ƙwayan idonta".Mahaifiyar Ummi ta yi zancen tana fasa ƙara ta riƙo Ummi suka fice daga cikin gidan ko mayafi babu balle takalmi. Nan kuma wani faɗan ya kaure tsakanin Baban Adnan da matarsa. Ta hau masifa tana ikirarin duk abin da ake mata a cikin gidan shi yake ja mata, saboda shishshiginsa da tsoma baki a cikin abin da babu ruwansa a ciki sai ya yi wanka tsarki ya faɗa, sai da ya gaggaura mata mari kafin ta yi shuru.
Don shi a gare sa dukan mace akan abin da bai taka kara ya karya ba shi ne abu mafi sauƙi a wajensa wajen aikatawa.
Sai da ƙuran ya lafa kafin na sama damar ba wa Amira haƙuri tana buƙarewa akan za ta jira Ummi ta dawo su ɗora daga inda suka tsaya. Da ƙyar da suɗin goshi na shawo kanta ta haƙura. Sai da aka magarib kafin Umma ta ce na tafasa tafiyar murji kamar yanda ta ce haka na yi na ci nawa na kai mata nata ɗaki na zuba na Abba a kula na ajiye masa. Na yi sallan isha'i na kwaso littattafain da nake koyar da yara da su na fito gidan ya haɗe da gurmi. Don mahaifiyar Ummi ta lashi takori akan sai an bi wa ɗiyarta haƙƙin zubar mata da jini da aka yi ba gaira ba dalili. Ta ƙira Mahaifin Ummi da yake legas a waya tana shaida masa abun da ya faru ya fi sau shurin masaƙi.
Tunin na tarar da yaran da nake koyar da su a zaure suna jirana babu ɓata lokaci muka fara karatu har mun yi nisa Abba ya dawo na miƙe tsaye da fara'ata ina yi masa sannu da zuwa sai kafin ya kai ga amsawa wani yaro ya shigo.
"Wai ana sallama da Amatullah a waje".
Daga ni har shi duk muka yi mutuwar tsaye kafin ya tsayar da idanunsa a kaina tamkar yau ce rana ta farko da ya fara ganina. Cikina sai ƙugi yake yi haƙwana suka datse harshena lokacin da Abba yake tambayar yaron da har yanzu yana tsaye bai gusa ba.
"Waye yake sallama da ita?".
"Wani ne ya zo akan babur ya ce a ƙira ta".
"Ke waye ya zo neman ki?". Tambayar da ya watsa mini ta sanya hanjin cikina kaɗawa jikina ya soma rawa kamar mazari.
"Ba magana nake yi miki ba? Waye ya zo neman ki a daidai wannan lokacin?". Ya kuma maimaitawa a karo na biyu cikin tsantsan buƙatuwar sn jin amsar tambayarsa.
"Ka yi haƙuri Abba ni ake nema ba Amatullah ba. Wani ne muka haɗu da shi kuma ya ce min zai zo gidanmu, yanzu ma muka gama waya da shi, ni ce na ce masa sunana Amatullah saboda ya takura min a lokacin".
Da wani irin hanzarin na waigo ina ƙarewa Amira da ta yi maganar cikin takewa da ƙwarin gwiwa kallo haka nan ma Abba shi ma kallon natan yake yi.
"Ita ba ta da bakin kare kanta sai ke?". Cikin girmamawa Amira ta amsa da faɗin"Abba ba ta san komai ba ne shi yasa ta kasa cewa wani abu. Amma ina mai ƙara ba ka haƙuri na san yadda kake taka tsantsan da tarbiyyan Amatullah. Ka yafe min akan kuskuren da na yi na ba ta sunanta a matsayin nawa".
Sai da ya yi ɗan jim kamar mai tunani ko nazarin wani abun kafin ya ce"ba komai amma dai a dinga kiyayewa. Ke ma bai dace kina tara samari a ƙofan gidanku ba ki nutsu ki fitar da wanda kike so a cikinsu, don haka ne daraja da kimarki a matsayinki ta ɗiya mace".
"In sha Allah Abba kwana nan zan fita da guda daga cikin su. Ku dai ci gaba da yi mana addu'a Allah ya ba mu na gari". Cike da jin daɗi Abba ya ce"Amin amin ya hayyu. Kuma in kin je kar ki daɗe Amira, ni sai na rasa ma me ye kuke tattaunawa su yi awanni suna zance".
"Ba zan wuce mintin talatin ba ina sha Allah". Kansa kawai Abba ya jinjina ya wuce ciki sai da na tabbatar ya gama wucewa kafin na fizgo hannun Amira.
"Waye kika kika ba shi sunana har yanzu gida nema na?". Ta fizge hannunta"dalla! Ki nutsu mu yi magana. Malama ni babu wanda na ba wa sunanki balle har ya zo gida ne nemanki, na yi haka ne kawai don na ƙwace ki daga tuhumar Abba. Yanzu dai ki zo mu je mu ga ko wane ne kuma da me ye ya zo".
"A'a Amira ni gaskiya babu inda zan je tsoro nake ji". Ta watsa mini harara kafin ta finciko ni muka yi waje muna fitowa muka hango mutum zaune a bisa babur yana latsa wayarsa.
"Amira na shiga uku! Idan Abba ya fito ya kalle ni fa?". Na furta muryata tana rawa.
"Ki nutsu mu yi abin da ya kamata mu koma gida akan lokaci. Ban da abin ki me ye zai fito da Abba yanzu kuma, ke dai kawai ki nutsu". Tana dasa aya anan ta ja hannuna muka ci gaba da tafiya duk ɗaga ƙafar da zan yi sai ƙirjina ya buga har muka isa wajen mutumin.
Sunan da ya ƙira ni da shi ya ƙara jefa ni cikin firgici.
"Tauraruwa Amatullah ba ki tsammanin gani na a ƙofar gidanku ba ko?". Jikina ya soma rawa tamkar wacce ake jonawa wutan lantarki. Da ƙyar na daidai nutsuwata.
"Mai-mai-mai aska kai ne?".
"Ƙwarai kuwa ni ne haka kawai zuciyata ta kasa nutsuwa. Na ji ko runtsawa ba zan iya yi ba idan har ban yi kwalli da kyakykyawar fuskarki ba".
"Amatullah wane shi? A ina kika san shi?". Amira ta yi magana a karo na farko.
"Amira shi ne wanda na ba ki labarin wanda muka haɗu a inda na kai talla yau". Ban jira amsarta ba na juya ina fuskantarsa da kyau na ci gaba da maganata.
"Na roƙe ka da girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara kar ka ƙara sako ƙafarka cikin layin nan, me ye kake so da ni? Don Allah kar ka ja mini masifa da bala'in da kaina ba zai iya ɗauka ba".
"Amatullah ba na nufin da masifa ko bala'in face alkhairin Allah".
"Wani irin alkhairi?".
"Ƙauna ce tafe da ni kuma ina fatan za ki amshe ƙoƙon barana".
Takaici ya mamaye zuciyata"ba na soyayya kuma ba zan fara akan ba don haka ka yi haƙuri Abbana bai ba ni damar tsayawa da ko wani ɗan namiji ba a hali yanzu". Ina gama faɗin haka na ja hannun Amira muka bar wajen muka shiga zaure ɗalibaina suka zuro mana ido. Nan take na sallame su duk suka watse muka zauna ni da Amira.
"Shi ne za ki tursasa mini fita kuma ki kasa cewa komai a gabansa. Kika bar ni ni kaɗai ina ta magana". Ta ɗan murmusa kafin ta ce"na ga ai ba cutar da ke ya zo yi ba shi yasa na yi shuru. Soyayya ce ta kawo sa kin ga kuma babu yanda za a yi na farraƙa tsakanin masoya".
Babu shiri na kai mata duka ta kauce tana ƙara ƙyalƙyale wa da dariya. Na miƙe tsaye ita ma ta miƙe na naɗe tabarma ina cewa"zan shiga ciki kar Abba ya ce na daɗe. Idan Allah ya kai mu gobe za mu tattaunawa".
"Cab! Ni kuwa kin ga yanzu ma zan je na ƙarbo awarata a fita tuya". Na taɓe baki"Allah ya ganar da ke". Ba ta amsa ba illa dariyar da ta yi muka shigo ciki tare ta yi ɗakinsu na yi namu.
[7/17, 1:21 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 1️⃣0️⃣
Kamar ƙadangaruwar bayan murhu haka na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka ko kuma wacce ta yi wa Sarki ƙarya, na nema waje na zauna a falo kasancewar na jiyo Umma da Abba suna tattaunawa a cikin uwar ɗaka. Kamar ko yaushe muryar Umma ya ɗara na Abba sai hayagaga take yi kamar za ta yi aron baki.
"Manniru ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ka tisa ni a gaba ka yi min wannan zancen banza da na wofin. Da yake ni ce karkatacciyar bishiyar kuka mai daɗin hawa shi yasa kowa ya ɗebo shararsa sai ya watso min, kai da danginka kun uzura min kun sako ni a gaban akan yarinyar da babu wanda ya taya ni goyan cikinta na tsawon watanni tara balle a kawo min tallafi yayin da nake nishin naƙudanta. Kowa ya ɗebo warin bakinsa zai nufo wai ina ƙoƙarin lalata tarbiyyar yarinyar nan".
"Ni kike kallon tsabar idona ki gaya min wannan zancen?". A kaurare na tsinkayo muryarta tana mayar masa da martani kamar wacce take jira ya ce kule ta ce cas.
"An gaya maka ɗin na ce an gaya maka. Manniru ka yi duk abin da ka ga dama ga fili ga mai doki, babu wanda zai dakatar da kai balle ya hana ka wanzar da abin da zuciyarka ta yi niyyar aikatawa, ko ce maka aka yi ina tsoro ko shakkanka ne? Ai wallahi an sha ni na warke kan mage ya daɗe da wayewa".
"Ba zan taɓa iya aikata abin da zuciyata ta saƙa min akan ki ba. Allah ya sani kuma shi ne masanin abin da yake taskace a cikin tsokar zuciya kina da girma da matsayi a wajena ta yadda duk abin da kika yi zan jure shi, kuma na yi miki uzuri. Amma kin ga wannan harshen naki Hafsatu ina jiye miki zuwan ranar da zai yi silar fadawarki cikin halaka, DAFIN HARSHE ya fi dafin maciji illa da saurin nakasa sassan jikin ɗan adam".
Gama maganar da fitowarsa sun yi daidai da lokacin da ƙwallan da suka wadaci koramar idanuna samun hanyar kwaranya. Ya kafe ni da ido da hakan ya sani yin ƙasa da idanuna.
Sai da ya zauna kafin ya ba ni umarnin zama, na nema waje na zaune kusa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 24