Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da wanzuwar nutsuwar ruhi. Ji nake yi kamar gari ba zai waye ba balle har mu taro a filin walimar, ranar mitsitsi na kafe akan ba zan je gidan Hajiya Tasalla ba saboda shirye-shiryen walimar man gobe. Abba ya kawo wake kwano biyu da wasu kayan miyan ya ce a yi alala na sauƙan, sannan ya ba ni naira dubu biyu ya ce na yi zoɓo. Duk yadda na so hana Amira sanar da Mansur labarin walimar sai da ta zagaya ta sanar da shi. A daren ranar ya zo shi ya yi mana siyayya sosai sannan ya ce zai halacci walimar da iznin Allah. Haka muka surfa wanken muka shanya sa muka je muka sayo kayan haɗin zoɓon, ba mu kwanta ba sai ƙarfe sha ɗaya saura na yi wanka na ɗauro alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu, na dinga zagba godiya ga mahaliccina a cikin sujjadata na ƙarshe. Ina ɗagowa na ɗauko alƙur'anina na buɗe na soma karanta ban dakata ba har ƙarfe biyun dare kana na rufe alƙur'anin. Duk yadda na so na runtsa bacci ya gagari idanuna haka na yi juyi har aka ƙira sallan assalatu, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan na yi zumbur na tashi na zauna. Na fito na yi alwala ina ƙoƙarin koma ciki Amira ta fito ta dalle mini idanuna da hasken tocilan wayarta tana yi mini tsiya. "Hafiza Amatullahi". Na murmusa ina kare hannuna daga hasken tocilan haɗe da faɗin"in za ki yi sallan dai ki yi ki fito mu zo mu yi aiki". "An gama ranki ya daɗe" Ta amsa da shi ban tanka mata ba na koma ciki na yi sallan sai da na ƙara tilawar karatun da zan gabatar a wajen taron kana na fito, muka wanke waken tare da Amira muka kai niƙa muka dawo muka soma ƙulƙulawa kafin garin ya yi haske tunin ya dahu, muka ɗauko lemukan da Mansur ya kawo muka sassaka a leda muka alalen bibbiyu, sai da muka sama leda hamshin da uku. Muka ƙula zoɓon ma, Amira ta ce tun da mun saka lemo a ledan na bar wannan na ba wa baƙina. Zoɓon kuma nawa da na ƙawayena na yarda da hakan, muna cikin aikin zoɓon Baban Adnan ya fito cikin shigar kayan aikinsa yana karkaɗe hularsa yayin da matarsa take biye da shi tamkar jela. Amira ta taɓo ni"ga mutanan fa. Wallahi sai na ya masa magana ko don na ƙular da ita da safiyar nan". "Ki rufawa kanki asiri dai". Ba ta ji abin da na ce da ita ba don sai da ta aikata abin da ta yi niyya. Ta lanƙwashe murya tana faɗin"Barka da fitowa Baban Adnan, har an fito ke nan? Allah dai ya saka muku da alkhairi don wannan aikin nakun ba kowa ba ne zai iya yin sa". Take ya washe baki kamar gonar auguda" barka dai Amiratuwa ku na ta aiki ke nan da safen, biki kuke da shi ne ko suna?". "Au! Wai daman ba ka sani ba? Amatullah ce za ta yi sauƙa yau". "Sauƙa dai irin wacce na sani na izu sittin ko kuwa?". Ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa shi fa". Zai yi magana Maman Adnan ta amshe zancen"ya dai kamata ka wuce ka tafi aikin gabanka". Ya juyo ya wurga mata wani mungun kallon da ya sanya ta saurin yi wa bakinta limzami. Ya zaro wasu kuɗi daga cikin aljihunsa ya irgo guda biyar ya miƙawa Amira"ga wannan to ku ƙara ayi hidima, don ina da aiki da yawa ne ma da zan halatta amma yanzu ma dai bai ɓaci ba sai a yi hotuna a kawo mana mu kashe ƙwarƙwatan idonmu". Kafin Amira ta kai ga amsar kuɗin Maman Adnan ta yi wuf ta kai hannu ta wafce. "Wallahi ba za ku yi amfani da kuɗi nan ba, me ye haɗin kifi da kaska da har za ta ɗauki kuɗi ka ba su...". Tana rufe bakinta ya wanke ta da mari. "Ba ta kuɗin nan tun kafin na tattaka ki a nan wajen". Babu girma babu azurki ta miƙawa Amira kuɗin ta koma ɗaki tana kuka da faɗin magauta sun shiga tsakanin ta da mijinta. Tun da aka fara dramar har aka ƙare ta ban tsoma bakina a ciki ba har sai da Baban Adnan ya fita kana na ce"yanzu me ye amfanin abin da kika yi kenan? Suna zaman zamansu ki haddasa musu rigima". Ta sheƙe da dariya kafin ta ce"ko banza dai mun sama dubu biyar a ɓagas kuma ta yi asarar hawayenta a banza". Na jinjina kaina cikin takaici ba tare da na ce da ita komai ba. Haka Ustazu Abdulwahab ya fito ya same mu muka gaishe sa Amira ta shelanta masa cewar yau za mu yi walimar sauƙan alƙur'ani, ai kuwa ya nema waje ya zauna ya soma zubo mini ruwan addu'o'i da yi mini fatan alkhairi. Ya kuma nema da na yi masa kwantacen islamiyyar in Sha Allah amaryarsa za ta je na yi masa. Kafin ƙarfe takwas mun kama komai har na yi wanka na kimtsa cikin sabuwar atamfa da hijabina da ya amshe ni sosai. Abba ma sai da ya yaba da shigar da na yi na ɗauko niƙab na ɗaura a kai, tare muka tafi da Amira abincin kuma su Umma za su taho da shi idan za su zo. Muna isa cikin islamiyyar Malam Suleiman ya aika aka ƙira mu ni da Al'amin da Aliyu da suka suka sha ankon faran shadda da rawani sai sheƙi da ƙamshi suke bazawa. Sai da muka yi bitan karatun da za mu yi a wajen su, suka gyagygyara mana inda ya kamata kana muka fito lokacin waje har ya ɗau harama. Filin makarantar ya sha ado an kafa rumfuna da kujeru babban taro aka shiyar mana kasancewar an haɗe murnar waliman namun har da na bikin murnan cikar islamiyyar shekaru goma da kafuwa. Muka zazzauna a inda aka tanada domin su masu ɗaukan hoto sai hasko muke yi, na ji kaina ya sara jikina ya ɗauki zafi tsabar zumuɗi ko abincin ban tsaya ci ba haka na taho. Lokaci guda na ji wajen ya ɗauki kabbara ana faɗin isowan Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe tare da shaƙiƙin ɗansa na miji ɗaya tilo. Duk yadda na so ganinsa cincirindon mutanen da suka kewaye sa sun hana ni ganinsa. Sai da Malam Aminu ya yi magana cikin lasifika kana wajen ya nutsu, ya ƙira Rauda Salisu a matsayin ɗalibar da za ta buɗe taro da addu'a. Sai a lokacin idanuna suka sauƙa akan Sheikh Dawood take ƙirjina ya buga na ƙura masa idanuna, tabbas shi ne wanda na ga ni a tasha har ya yi mini maganar banza da ƙoƙarin taɓa jikina. Haka zalika yanzu ma shi ne zaune cikin kamala da nutsuwa, duk wanda zai gaishe shi sai ya durƙusa har ƙasa. "Ga can Anty Sawwama da su Yaya Alhassan sun iso, Abba ma ya iso tun ɗazu. Umma ma su a hanya tare da Ummanta mun yi waya da ita ta ce sun kusa isowa". Na tsinkayo amon Amira ta yi zancen a daidai saitin kunnena, na yi kamar zan tashi na je wajen su Malam Suleiman ya yi mini ido akan na koma na zauna, babu yadda na iya haka na koma na zauna. Sai aka gabatar da jawabi sosai sarakuna da ƴan siyasa suka tashi suka yi nasu jawabin kana Malam Aminu ya fara ƙiran Aliyu a matsayin wanda zai fara gabatar da karatu. Ya tashi ya yi karatun cikin tsantsan nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harrafi, wajen ya ɗauki kabbara aka ayyana shi a matsayin wanda ya zo na uku kuma ya kasance ɗaliba mafi ƙwarzo na shekara. Aka ƙira wani basarake ya ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada masa sannan shi ma ya ƙara masa da kyautar zunzurutun kuɗi har naira dubu ɗari tare da fatan alkhairi da addu'o'in da ya dinga yi masa. Har na yi shiri don na sa a raina cewar ni za a ƙira a matsayin ta biyu, haka nan ma sauran ɗaliban don duk sai waigowa suke yi suna kallona. Kwatsam muka yi an ƙira sunan Al'amin jikin kowa ya yi sanyi, hatta shi Al'amin ɗin da kansa don bai fito ba har sai da aka ƙara maimata sunan a karo na biyu kana na tashi. Ya je ya yi karatun jikinsa gabaɗaya babu ƙwari, shi aka ayyana a matsayin wanda ya yi na biyu aka ƙira dan takaran kansilan yakinmu da ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada domin shi aka yi musu hoto. Daga haka ya dawo ya zauna gabaɗaya yanayinsa ya sauya. "Amatullah Munnir". Malam Aminu ya ƙwala ƙiran sunana a cikin lasifika take zuffa ya keto mini ina ɗago kaina muka haɗa ido da Abbana. Fuskarsa a washe cikin tsantsan farin cikin da har sai da na hawaye a idanunsa. Na tashi na isa kan munbarin ina karantu auziya da bismillah wajen ta kaure da kabbara na ci gaba da karatun suratul Maryam cikin sanyin murya wajen ya yi shuru ina cikin karanton na hango shigowar Umma da Umman Amira. Sai da na karance suran tas kana aka yi kabbara da alama hatta su Malam Suleiman sun ji daɗin karatun da na yi fiye da na sauran. Aka bayyana ni a matsayin wacce ta yi na ɗaya. Aka ƙira wani basarake ya ba ni kyautata ya kuma ba ni wasu kuɗaɗen da ban san adadin yawansu, zan tafi aka ce na tsaya aka kara ayyana ni a mashin gwarzuwan shekara kuma ɗaliba mace ta farko ta yi sama iri wannan nasarar cikin shekaru goma da kafa islamiyyar. Sannan aka ayyana ni a matsayin ɗaliba mafi hazaƙa a cikin ajinmu. Malam Aminu ya ɗauko kyautar da za a ba ni ya ƙira sunan Sheikh Dawood a matsayin wanda zai karrama ni da kyauta ya taso cikin shirgar alfarma, tun da ya taso nake bin sa da kallo har ya iso wajen. Ya karɓa lasifikan ya soma jawabi. "Yau na cika da murna da farin ciki ganin yadda aka yaye ɗalibai masu yawan gaske kuma duk sun haddace littafi mai tsarki. Ina jinjinawa malamanku ƙwarai da gaske da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da sun sama ilmi mai inganci. Wannan ɗalibar da ta yi na ɗaya kuma ina yi mata fatan alkhairi da addu'ar dacewa a cikin rayuwarta. Sannan idan mahaifi ko mahaifiyarta yana wajen wannan taron ina so a taso ya hau kan munbari domin na yi masa wani albishir". Aka dinga kwarara kabbara har Abba ya iso wajen suka yi musaba kana Sheikh Dawood ya ci gaba da jawabinsa. "Bawan Allah da farko ina taya ka murna domin Allah ya yi maka arzikin da ba kowa ne yake dacewa da irin sa. Wannan ɗiya taka zinariya ce a cikin zinaru, idan akwai wani karatun da take yi ko kuma za ta fara to na ɗauki ɗawainiyyarta daga yanzu har ta gama shi, idan kuma daga nan aure za ta yi to na ɗauki nauyin yi mata kayan ɗaki da duk wani abun da ake yi mace yayin bikinta. Zan karrama ta cikin alkyabba mafi daraja da tsada". Wajen gabaɗaya ya ruɗe ya sa aka ɗauko wata alkyabba mai tsananin sheƙi da ƙyalle wanda ko da daga kallo guda ka san cewa mai tsada ce balle kuma ace ka murza jikinta. Ya ɗaura mini ita a kaina idanumu suka sarƙafe cikin na juna, take na ji raina yana tafasa sakamakon wani irin kallon da yake yi mini da na kasa gano ma'anarsa. Abbana sai godiya yake zuba wa yana yi yana ƙarawa, ɗan takarar kansila da sarakuna duk suka gaisa da shi tare da yi mini kyaututtuka masu tsoka. "Ina taya ki murna matuƙa kuma ina addu'ar Allah ya sanya albarka a karatunki". Da sauri na ɗago kaina don tabbatar da mamallakin wannan muryar da ta kasa gogewa daga cikin kaina. Caraf idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye a gabana fuskar ɗauke da maɗaukaki murmushi. Hannunsa riƙe da alƙur'ani da aka yi ado da wasu irin zare masu jan hankali. Ya miƙo sai dai mamaki ya hana ni karɓa balle na ce da shi wani abu. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"Muhammad Taufik ko?". Ya sakar mini da murmushin yana faɗin"karɓi mana kin tsaya ki na ta kallo na". Jikina a sanyaye tamkar kazar da aka kwararawa ruwan zafi na kai hannu na amsa alƙur'anin. "Ina taya ki murna Allah ya albarkacin karatun da aka yi. Kafin ku tafi zan neme ki". Kaina kawai na girgiza masa kafin na ce wani abu Malam Aminu ya iso wajen ya ƙira gefe. "Amatullah mu je Sheikh yana son magana da ke". Take na ji ƙirjina ya buga ya yi gaba ina bin shi a baya har gaban Sheikh na durƙusa a ƙasa, ya ƙura mini idanu kamar zai cinye ni ɗanya ya ɗauko wasu littattafai ya miƙo mini na miƙa hannu zan karɓa caraf na ji ya riƙe hannuna gam. Babu shiri na ɗago idona ina kallonsa sai dai ko a jikinsa sai murza mini hannuwa da yake, sai da na sa ƙarfi kafin na kwace hannuna. Na yi zumbur zan tashi wani jiri ya ɗauke ni duk yadda na so tsayiwa akan ƙafata lamarin ya ci tura, Malam Aminu da yake kusa da ni ya yi saurin karɓan alƙur'anin da yake hannunsa da sauran kyaututtukan. Luu na yi baya na faɗi a ƙasa ina jin kaina yana juyawa jikina gaba ya sake, mutane suka cika a kaina ina ganin su dishi-dishi. "Amatullah lafiya kike kuwa?". Muryar Yaya Alhassan kenan da ya kasance abu na ƙarshe da na ji kafin hankalina ya gushe, aka ɗauke ni ridi-ridi sai asibiti. A hankali na soma buɗe idanuna da na ji sun yi mini matuƙar nauyi ina ƙarewa ɗakin da nake cikinsa kallo. Sai da na ƙarewa ɗakin kallo na tabbatar da cewar asibiti ne. Ummata, Umma Amira, Anty Sawwama da kuma Amira, Anty Zulaihatu su kenan a cikin ɗakin. Suka fara jeranta mini sannu wani na bin wani kafin na kai ga amsawa Abba, Yaya Alhassan, Umar da Malam Suleiman suka shigo cikin ɗakin cikin wani irin matsanancin firgici da tashin hankali, na lura idon Abba har da hawaye ya kafe ni da idanuna kamar ya ga wata sabuwar halitta. Kafin na yi aune ko na ce wani abu tunin Abba ya wanke ni da mari, ina ɗagowa ya ƙara wanka mini wani marin. Su Umma duk suka tattaso suna tambayar ko lafiya. [10/25, 8:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 3️⃣6️⃣ "Munniru lafiya kuwa? Za ka ɗauke yarinya da mari alhalin tana gadon asibiti cikin jinya". Ta juya tana duban Yaya Alhassan da tun da suka shiga kansa yake ƙasa ya gaza ɗago ido balle ya kalli kowa. "Alhassan wai me ye likitan ya shaida muku ne? Me yake faruwa da Amatullah ɗin?". Bai ɗago kansa ya kalle ta ba kamar yadda bai amsa mata ba. "Ba fa zai yiyuwa a tisa min ɗiya a gaba da duka ba akan wani dalilin? Tana cikin jinya idan ba a lallashe ta ba ai ba za tada mata da hankali ba, wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa". "Hafsatu ki rufe min baki tun kafin na yi sassaɓa miki a nan wajen nan. Kin cuce ni kin cuci rayuwar ƴarki. Hafsatu kin wargaza min duk tanadi da shirin da na yi wa rayuwar Amatullah, kin jefa ni cikin kunya da tsoron haɗuwa da mutane balle har na shiga cikin su na yi mu'amala da su, tsakani na da ke Allah ya isa ban yafe miki". Gabaɗaya wajen ya ɗauki salati da sallallami Umma ta hau hayagaga ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, sai da Umman Amira ta taso ta riƙe ta tana ba ta haƙuri da tunatar da ita cewar a asibiti fa muke. Kuka nake yi da dukkan ƙarfina jikina gabaɗaya yana rawa tamkar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna kamar jinriran kazar da ruwa ya yi wa ɗan banzan duka. "Don Allah ku ba mu waje ina son ganawa da Amatullah ita kaɗai". Abba ya yi zancen cikin tsantsan tashin hankali da ruɗewan da ya bayyana har a cikin muryarsa. "Ai ba kai kaɗai ka haifa yarinyar ba Manniru don haka babu inda zan je, komai a gaba na za ku tattaunawa. Ai ni ma ina da iko akanta kamar yadda kake jin kai ma kana da cikakken iko akan ta". Umma ta yi zancen cikin isa da izgilanci da ƙyar Umman Amira ta shawo kanta ta yarda ta fita daga cikin ɗakin, ya rage daga ni sai Abba a cikin ɗakin har zuwa lokacin kuka nake yi duk da ban san abin da yake faruwa ba amma na yi imanin duk abin da zai sanya Abba shiga makamancin irin wannan tashin gami da furta zafafan kalamai ba ƙaramin abu ba ne. Ya zauna a kusa da ƙafafuna ya kafe ni da ido lamarin da ya ƙara sanya jikina yin sanyi ƙalau don bai taɓa yi mini irin wannan dogo kallon ba. "Amatullah". "Na'am Abba". Na amsa muryata a kashe tamkar wacce aka sanya igiyar kirtani aka shaƙewa wuya tamau. "Amatullah ki na ɗaya daga cikin jerin matan da na yarda da su a cikin rayuwata kuma na yi imanin ba za su taɓa cin amanata ko su kunyata ni ba. Tun ranar da kika zo duniya aka cirewa mahaifiyarki mahaifa sakamakon irin wahala da azabar da ta sha tun daga rainon cikinki har izuwa lokacin haihuwarki. Ya tabbatar ba za ta sake haihuwa ba a duniya haka ni ma inda ba wata macen na aura to ba zan sake haihuwa ba tun da an raba ta da mahaifa, tun daga lokacin na yuƙurce a raina cewar zan tarbiyyartar da ke na ba ki kula na ba ki ilmin addini ta yadda za ki zame mini madadin ƴaƴa goma a gare ni, kuma alhamdulillah haƙiƙa na cika da farin cikin a yau ganin kin haddace littafin alƙur'ani akan ki babu abin da zan ce Allah sai dai godiya. Amma me yasa kika zaɓi ki jirkita min wannan ranar ta farin ciki zuwa ta baƙi ciki da kasance rana mafi muni a gare ni?". Bai ba ni daman cewa wani abu ba ya ci gaba da cewa"Allah ne shaidana domin ba ya bacci yana ganin duk abin da yake na zahiri da na baɗili. Ya san na kula da amanarki da ya ba ni daidai da rana guda ban taɓa barin ki kin sauƙa daga tafarkin addinin da Manzon ya zo mana da shi ba. Amma Amatullah me yasa kika zaɓa ki saka min ta wannan hanyar? Me yasa kika zaɓa ki shayar da zuciyata raɗaɗin baƙin cikin da ba zai taɓa bari na yi rayuwa cikin farin ciki da walwala ba?". Na tuntsire da wani irin kuka mai ƙarfi numfashina har ɗaukewa yake yi. "Amatullah likita ya tabbatar mana da cewar ki na ɗauke da ciki a jikinki na tsawon sati biyu, Uwata wa ya yi miki ciki?". Mutuwa zaune na yi don cak numfashina ya ɗauke na wucen gadi na dawo da ni da gawa ba mu da maraba. Na ji duniyar gabaɗaya tana juya mini ban dawo daidai ba sai na ji sauƙan wani abu mai zafi a fuska da ya ratsa dukkan sassan jikina wanda ina da tabbacin ruwa Abba ya watsa mini a fuska. Na ci gaba da wani irin kuka wanda ya yanayin da irin zafin da nake cikin a ƙirjina ba na jin akwai kalmomi da za su wadatar wajen fassaruwansa. Duk yadda na so na yu magana baki ya ƙi ba ni haɗin kaina furta abin da yake yi mini ƙaiƙayi a cikin raina. Hankalina ya kai ƙololuwan tashin ganin hawaye suna zuba daga idanun Abba ya sukunyar da kansa ƙasa ba tare da ya ƙara cewa da ni komai ba. Tun ina yin kukan idanuna suna zubar da ƙwalla har sai na da idanuna suka kafe tsiyayar da komai. "Abba". Na furta cikin wani iriyar muryar mai cike da rauni haɗi da maɗaukakin tashin hankalin da ya jirkice da rashin nutsuwa, shuru bai tanka mini na ƙara ƙira a karo na biyu nan ma shuru ina jijjiga shi na ga ya faɗi a ƙasa idanunsa sun kakkafe bakinsa ya koma gefe guda. Na ɗaura hannu aka na fasa ihun da ya sanya su Umma faɗowa cikin ɗakin tamkar an jefo shi. "Innalillahi wa inna ilahirin alaihir raji'un! Me ya same shi?". Anty Sawwama ta jefa mini tambayar da na gaza amsa wa illa kukan da nake ji jikina yana rawa. Yaya Alhassan da Malam Aminu suka ɗaga shi suka kwantar da shi akan gadon da na tashi, Umman Amira ta fita ta ƙira likita ya shigo ya umarce mu da duk mu fita. Sai dai ni kam na kasa motsa ƙafafuna daga inda nake tsaye duk da jan hannuna da Amira take yi kamar za ta fincike shi daga gangar jikina. Ganin halin da nake ciki ya san likitan da kansa cewa a ƙyale ni haka suka fita suka bar ni a wajen, na ja saƙararran gangar jikina na isa na durƙusa gaban gadon da Abba yake kwance na riƙe hannunsa ina murzawa a hankali. Likitoci suka rufu akan sa suna ta ƙoƙarin ceto rayuwarsa domin har jijjiga ya fara aka ɗauko wani abu kamar dutsin guga ana danna masa a ƙirjinsa. Sun ɗau lokaci a haka har sai da komai ya daidaita aka maƙala masa roban numfashi. "Ki yi haƙuri ki tashi ki fita waje, in sha Allah zai sama lafiya kamar yadda kike gani ma ai yanzu da sauƙi". Likitan ya furta cikin sanyin harshe da sassauta amonsa. Na cira kai ina kallonsa"don Allah zai tashi kuwa?". "Me zai hana shi tashi? In sha Allah zai tashi ya sama lafiya ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa tamkar babu wani abun da ya taɓa faruwa". Ban ce da shi komai ba na kuma fashewa da wani kukan ina murza hannun Abba da yake cikin nawa. Lokacin guda har fuskarsa ta faɗa tafin hannunsa ya yi sanyi ƙalau kamar wanda aka ɗaurawa ƙanƙara. Aka bankaɗo ƙofar ɗakin na waigo ina ganin Umma da ta faɗo cikin ɗakin a fusace tamkar kububuwa tsoro ya mamaye mini ƙalbina, kafin na yi wani yunƙuri na ji ta rufe ni da duka da ko'ina ana ƙoƙarin raba ni da numfashina. Ta buga kaina a jikin ƙarfe gadon take jini ya ce sallama Alaikum ya fara malala kamar da bakin ƙwarya. Da ƙyar likitotin suka ɓanɓare ta daga jikina duk da hakan bakinta bai fasa furta mini mungayen kalmomi ba. "Allah ya isa tsakanina da ke Amatullah. Da haihuwarki irin ki gwara na rayu har na koma ga mahaliccina ba tare da na yi ko ɓatan wata ba, da na san haka za ki zame min annoba da tun ranar da kika zo duniya na murɗe miki wuya kin mutu kowa ya huta, na tsane ki na tsani kallon ki. Da wannan abun kunyar da kika ɗauko mana gwara a kawo min gawarki a gaba na hankalina sai ya fi kwanciya". Na rarrafo na zo na riƙe ƙafafunta"don girman zatin Allah Umma ki yi haƙuri kar ki furta mini kalmar da za su jirkita tunanina. Umma ki ba ni dama na yi miki bayani wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini...". Tun kafin na ƙarisa ta sa ƙafa ta yi bol da ni na faɗi gefe guda, babu shiri na saki ihu saboda zafin da na ji ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina. "Ke ba ki da hankali ne? Idan kika ji mata ciwo fa? Ko me ta yi ai kamata ya yi ki bari sai kun je gida ko kin manta cewa nan asibiti kuma a cikin ɗakin majinyaci kuke kike wannan hayaniyan. Ku tattara ku fita waje don ba ma buƙatar hayaniya da ɗaga murya a nan". Likitan ya yi zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai da takaicin abin da Umma ta aikata, Umman Amira da Anty Sawwama suka shigo suka fitar da Umma Amira ta ɗago ni likitan ya ce na fito a bar Abba ya huta muka je wani waje a cikin asibitin aka yi mini dressing ɗin goshina da yake zubar da jini.

Chapter 21 of 24