cikinsa. Kafin ka ce kwabo mutane sun cika a wajen kamar kai ka ce kisan kai aka yi a wajen ko kuma wani babban laifi.
Girmamawa da mutuntawan da duk wanda ya zo wajen yake yi wa mutumin shi ya fi komai ɗaure mini kai da jefa ni cikin kokonto. Wasu har tsunguwana suke yi har ƙasa kafin su gaishe shi ko ya miƙo musu hannu don su yi musabaha ba sa miƙa nasu.
"Wai me ye yake faruwa ne ya Sheik? Me ye ya haɗa ka da wannan yarinyar?". Ɗaga daga cikin mutanen da suka cika a wajen ya jefawa mutumin tambaya kafin ya amsa masa wani ya amshe zanen ya soma furzar da zancen da yake cikinsa cikin tsananin fusata, tamkar zai kai mini bugu.
"Allah dai wadaran naka ya lalace. Yanzu ke don fitsara da rashin kunya ki dubi tsabar idanun wannan mutumin da ya yi kusan jika da ke kina yi masa rashin kunya irin na ku na ƴaƴan zamani. Ke kam alla wadaran halinki hakan ya nuna ba ki sama kyakykyawan tarbiyya ba a gida".
"Alhaji Mamman ka yi haƙuri mana mu ji ta bakinta. Kafin mu yanke hukunci".
Ɗaya daga cikin mutanen wajen ya furta kafin ya juyo yana dubana tare da faɗin"ke yarinya me ye haɗinki da wannan mutumin kar kika nema ki yi masa raini da rashin kunya". Duk yadda na so na yi magana lamarin ya gagara hawaye ne kawai suke gudun famfalaƙi akan kuncina na kasa furta ko da kalma guda.
Ana cikin haka Amira ta dawo ta tambayi me ke faru aka mayar mata da ba'asi ita ta yi ta masu haƙuri, amma da farko tsayawa suka yi tsayin dakan akan sai sun lakaɗa mini na jakuna. Yayin da manyan wajen suke ta ba wa mutumin haƙuri kamar wanda aka yi mata wani gagarumin zunubi. Da ƙyar Amira ta shawo kansu shi ma sai da taimakon samarinta na wajen da suka sanya baki.
Ƙurar tana lafawa na fara harhaɗa kayan tallana, Amira ta riƙe ni tana jijjiga ni"wai Amatullah me ye yake damunki ne? Hauka kika yi ko kuma aljanu ne suka shafe ki?".
Na kawar da hawayen idanuna kafin na sama lasisin faɗin"babu ko ɗaya kawai tafiya zan yi ne".
"To ki tsaya mu nema almajirai su ɗeba mana kayan mana". Ban kula ta ba na ci gaba da tattare tattaren da nake yi. Ta nema almajirai suka ɗeba mana kayan muka bar wajen har yanzu hawaye ba su daina kwaranya daga idanuna ba.
"Don girman Allah ki nutsu ki daina wannan kukan haka ya isa mana. Ki bari mu je gida mu zauna sai mu tattauna akan lamarin".
Na shece majinan kukan da ya zo mini kafin na ce"Amira ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai na san wane ne wannan mutumin, da ya ƙware a munafurci da launa zance". Kafin na gama ta yi saurin kai tafin hannunta ta rufe mini baki.
Kamar mai raɗa ta soma cewa"ke Amatullah ki rufa mana asiri, kar wani ya ji ki kina wannan maganar. Kin san waye wannan mutumin kuwa? To idan ba ki sani ba ki saurara ki ji wannan mutumin sunansa Sheik Dawood Nasarawa babban malamin addini ne a jihar nan da ma kewayenta, ya yi shura sosai a fannin ilimin addini da sanin hukunce-hukuncensa. Sannan kuma malamin jami'a ne a babban jami'in jihar na koyar da kimiyya da fasaha kuma na ji an ce ma ba a iya wannan jahar yake koyarwa ba. Kin gan sa nan babu wani abun duniyar da za a ba shi ta ruɗe sa haka nan babu adadin kuɗaɗen da za a ba shi a rinjayi hankalinsa, kin gan sa nan ko motar kansa bai da shi. Duk wani shugaban da ya yi ba daidai ba ga al'ummarsa ba ya ragar masa fitowa yake ya tsigale shi ba tare da fargaba ko tsoron abin da kan je ko ya dawo ba. Da yawan mutanen suna yi maka kirari da murucin kan dutse ba ka fito ba sai da ka shirya wasu kuma su ce da shi gaskiya dokin ƙarfe".
Ba kaɗan ba kalaman Amira suka daki ƙwaƙwalwata tare da munana ƙalbina. Take yanke zuffa ya soma tsatstsafo wa daga jikina. Na yi maza na cafko hannunta na riƙe gam saboda rawar da ƙafafuna suke yi.
"Ki na nufin wannan mutumin shi ne Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe?". Na galla mini harara"ƙwarai kuwa shi ne".
Na dafe kaina ina karanto auzila kafin na ci gaba da magana cikin tsananin kaɗuwa da ruɗewa.
"Na daɗe da sanin muryarsa babu wani malamin da nake bibiyar wa'azinsa kamar sa. Hatta Abba yana son wa'azinsa saboda yadda yake feɗe gaskiya komai ɗacinta".
Ta zame hannunta daga cikin nawa kafin ta furta"kowa ya san wannan. Don kwanakin baya duk inda kika shiga a garin nan maganarsa ake yi. Mai girma gwamna da kansa ya ba yi masa tayi wani gwagwgwaɓan matsayi a gwamnatance da alƙawarin buɗe jami'a mai zaman kanta a damƙa masa ragamarta kuma a sanya mats sunansa. Ban da alƙawarurrukan zunzurutun kuɗin da abubuwan more rayuwa da ya yi masa, amma duk da haka ya ƙi karɓa".
"Na rantse da girman wanda rayuwata take hannunsa ban san fuskarsa a zahiri ba. Kuma shi ya fara tara ta da maganan banza".
Ta yi hanzarin katse ni"ki rufa mana asiri Amatullah. Ko a mafarki mutumin ba zai taɓa tarar wata mace da maganar banza ba saboda dattakunsa yana ƙoƙarin kiyaye duk wani abun da zai taɓa martaban kimarsa. Ke dai kawai ki tsori ta ne da kalaman Bashir suna yi miki amsa-kuwwa a kunnenki". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"wallahi babu kuskure cikin abin da na faɗa miki Amira".
"Ki yi shuru haka ya isa". Tana rufe bakinta ta ja hannuna muka ci gaba da tafiya, har muka isa gida na kasa magana kamar gunki tafiyar kawai nake yi ba tare da na san inda nake ajiya ƙafana ba.
[8/4, 7:11 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 1️⃣8️⃣
Muna isa na wuce ɗakinmu na yada zango a falo ina mayar da nurfarfashi kamar wacce ta yi gudun ceton rai. Sai Amira ce ta shigo mini da kayan tallan ta juya ta fita bayan ta gama jeranta mini maganar da ban ba ta amsar ko guda daga ciki ba. Yadda na ji falon ya yi shuru ya tabbatar miji da cewar Umma ba ta cikin gidan amma na fi zargin cewar ba ta yi nisa ba tun da ga shi ba ta rufe ƙofa ba.
Ina zaune a wajen Abba ya fito daga ɗaki yana saka hula akansa, na maza na tashi na gyara zamana ina yi masa sannu da fitowa. Ya amsa mini yana neman waje ya zauna, mamaki ya hana ni yin wani motsin kirki na shiga duniyar tunanin dalili da ya hana Abba fita wajen aiki, a iya sanina da shi baya fashin zuwa wajen aiki in ba tare da wani ƙauƙauran dalili ba.
"Har kun dawo kenan?".
Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi zarafin ci gaba da maganar da ya sani daskarewa a wajen, na sha jinin jikina ainun.
"Ummanki ce ta fita tun ɗazu ita nake ta jira ni ma shi yasa ban fita ba". Na ɗaga ido ina kallonsa"Abba da ka yi tafiyar ka ai, wataƙila ba nisa ta yi ba".
Ya jijjiga kansa kafin ta ce da ni"A'a Amatullah ko na fita hankalina ba zai kwanta ba. Zan fi samun nutsuwa idan na ga ta dawo cikin ƙoshin lafiya". Na yi shuru na kasa yin magana don na ga lamarin ya fi ƙarfin kwanyata, tausayin Abba ya cika mini sashin ruhina har ƙwalla suka ciko mini kurmin idaniyata.
"Ya islamiyyarta kun kuwa? Ya batun sauƙanku yaushe ne?".
Na musguta kafin na ce"islamiyya alhamdulillah, Abba nan da sati huɗu ne sauƙar in sha Allah". Ya jinjina kansa"Allah ya nuna mana lokacin, za mu yi magana da Ummanki sai mu ga abin da ya dace ayi".
"Ina godiya Allah ya ƙara girma. Bari na sa maka ruwa a buta an yi ƙiran salla". Na ƙare zancen ina miƙewa na fita waje na sa masa ruwan alwala a buta kana ni ma na yi nawa. Na shiga cikin ɗaki bayan na sanar da shi na saka ruwan.
Ko da na iddar da sallan na daɗe a zaune na gaza gane me ye yake yi mini daɗi. Ƙur'anin da na ɗauko zan yi muraja'a ma na gaza karanta ko aya guda, ganin wankin hula yana son kai ni dare ya tursasa mini tashi na fara shirin tafiya islamiyya, sauran kunun da na dawo da shi na sha kafin na fito har lokacin Abba bai dawo ba. Don haka na shiga ɗakin su Amira na sanar da ita idan Abba bai dawo ba ta ja mana ƙofar falon.
Ina fitowa daga cikin gida na hango Abba yana dawowa na tsaya har ya iso wajen.
"Har kin fito za ki tafi?". Na ɗaga masa kaina.
"Kin cin abinci ne?".
"Na sha kunu". Cike da kulawa ya ce"kunu ai ba abinci ba ne Uwata, ga wannan naira darin ki sayi ko awara ce ki ci in kin isa". Cikin girmamawa na amsa ina yi masa godiyar da yake amsawa cikin daɗin rai, muna tsaye a wajen muka hango Umma tafe, jikina ya yi matuƙar sanyi ganin yadda Abba gabaɗaya ya gigice daga ganin ta tun kafin ta iso wajen ya ɗauki hanyar zuwa gare ta da rawar jiki ya amshi jakar da yake maƙale a kafadarta.
Yana ta yi masa sannu ta yi biris da shi har suka iso inda nake, na yi mata sannu ta amsa mini a daƙile tamkar an yi mata dole.
"Ai ke na tsaya jira ki dawo kafin na fita".
Ta gantsalo masa harara kamar ta yi arba da kashi"ko yanzu da na dawo ɗin uban me ye zan tsinana maka?. Yanzu kam ga ni ai sai ka dafa ni ka cinye, babu dama na motsa ko wani wajen sai ka titsiye ni da tambayoyin babu gaira babu dalili". Ya yi shuru tare da sadda kansa ƙasa ba tare da ya ce komai ba. Ta kuma jan wani uban tsaki kafin ta zarce da faɗin"wuce mu shiga ciki yanzu ko". Ta yi zancen lokacin da yaran gidan da iyayensu maza da suka je masallaci suka nufo inda muke tsaye.
Tamkar raƙumi da akala haka Abba ya bi bayanta suka shiga cikin gida, na yi maza na goge hawayen da suka zubo mini ba tare da na shirya musu kafin na ɗauki hanyar bari wajen. A hankali nake tafiya tamkar wacce aka zarewa laka na shawo layin da zai sada ni da islamiyyar kenan na ji an danna mini horn ɗin mota har sai da na riɗime na rasa inda zan yi na tsaya kawai cak na ɗaura hannuna aka na lumshe idanuna ina jiran na ji da inda motar za ta buge ni.
"Ƴan matan buɗe idonki mana".
A hankali na soma buɗe idanuna kafin har na buɗe su tar akan sai da gabana ya faɗi, saboda kwarjinin da ya yi mini a ganin farko da na yi masa. Na yi saurin ja da baya ina dafe ƙirjina dole na yi ƙasa da idona.
"Na razana ki ko? Ki yi haƙora tuba nake yi. Ban lura da ke ba sai na zo dab dake". Shuru na yi ban amsa masa ba sai dai hakan bai hana sa ci gaba da furzar da zancen da ke cikinsa ba.
"Ko sai na durƙusa akan gwiwoyina ne sannan za ki haƙura".
"To ai ni babu abin da ka yi mini ba". Na yi maganar ina ƙoƙarin wucewa ya yi saurin shan gabana.
"Na razana ki mana baiwar Allah. Kuma kin san an ce tsorita musulumi haramu ne. Don Allah ki furta ki yafe min raina zai fi samun nutsuwa, don akan hanyar nake zan yi tafiya mai nisa. Ki taimaka min kar na tafi da haƙƙin wani a kaina".
Na cira kai na yi masa kallo guda kafin na janye idanuna"kamar yadda na gaya maka ba ka yi mini komai ba, amma tun da ka matsa na haƙura Allah ya kiyaye hanya ya kai ka lafiya". Ina gama maganar na wuce na soma tafiya cikin sauri saboda lokaci ya riga ya ƙure kafin na iso har Malam Suleiman ya shigo ajinmu ana karɓan hadda na shiga na zauna na buɗe ƙur'anina, duk yadda na so biya karatun lamarin ya gagara wai cire wando ta kai, ji na yi kamar ba a taɓa karanta mini wajen ba a kaf cikin rayuwata. Ina ta ƙoƙari haɗa kalmomin amma ya ci tura har aka iso kaina na tashi na isa gaban Malam Suleiman, sai dai na gaza karanta ko aya guda sai faman kame-kame nake yi.
"Amatullah anya ki biya karatun nan a gida kuwa?".
Na yi ƙasa da kaina don ni kaina na san duk abin da zai fito daga bakina a lokacin ƙarya ne.
"Malam na yi amma......". Kafin na ƙarisa ya dakatar da ni"koma ki zauna idan an fito salla ki zo ki same ni".
"To Malam". Na amsa da shi ina tashi daga wajen na koma mazaunina na zauna, na kwantar da kaina akan desk ban ɗago ba har sai da aka fita sallan asr Rauda ta taɓo ni na tashi muka fito muka yi alwala, muna iddar da sallan na wuce wajen Malam Suleiman.
Yana zaune a cikin staff room na shigo na zauna, sai da ya gama rubutun da yake yi kafin ya gyara zamansa yana fuskanta na da kyau ya soma magana.
"Amatullah mene ne yake damunki? Me ye ya yi miki zafi a cikin rayuwar nan?".
Kalamansa suka daki ƙwaƙwalwata tare da raunana zuciyata, na ɗau tsawon lokacin wani bai yi mini irin wannan tambayar ba.
"Babu abin da yake damuna Malam".
"Kar ki yi ƙarya don fuskarki ta riga da ta bayyanar da labarin zuciyarki. Amatullah dole akwai wani abun, tun da ga shi har ya fara taɓa karatunki, duk wanda ya sanki a makarantar nan ya san ki ne saboda dalilai guda biyu na farko ƙoƙari da mayar da hankalin da kike da shi akan karatu na biyu kuma ladabi da biyayyarki".
"Babu komai akwai dai matsalolin rayuwa ne na yau da kullum, kuma yanzu a rayuwar nan kowa da irin na shi kalan damuwar".
Ya yi ɗan jim kafin can ya yi magana cikin taushin harshe"na fahimta kuma ina fatan haka ɗin ne. Kar ki saka komai a ranki ki miƙa wa Allah dukkan lamuranki don shi kaɗai ne zai iya magance miki matsalolinki, kin ga rayuwar nan kowa da na shi matsalar idan kika ji na wani sai ki ji na ki ko kashi ɗaya bai kai cikin kashi ɗarin nasa ba. Kar ki bari ki ɓata shekarun da kika yi a baya kuma karatu mussamman yanzu da aski ya zo gaban goshi".
Cike da gamsuwa da zantukansa na ce"in sha Allah Malam ina godiya sosai". Haka na tashi na baro cikin staff ɗin jikina duk a sake, na koma aji har aka tashi ban dawo daidai ban tsaya jiran su Rauda ba na yi tahowa ta, ina tafe kaina a ƙasa
na ji ana yi mini sallama. Da farko ban amsa ba sai da aka ƙara yi a karo na biyu kafin na amsa tare da waigawa bayana.
Na yi turus na tsaya ganin mutumin da muka haɗu da shi ɗazu da zan taho ne kafin na yi magana ya riga ni.
"Na ƙara tsorita ki ko?"
Na jijjiga kaina na juya zan ci gaba da tafiyata ya kuma tsayar da ni.
"Har kun tashi daga islamiyyar kenan? Ai tun ɗazu nake tsaye a nan ina jiran dawowanki".
"Don Allah bawan Allah kar bar ni haka nan".
"Zan bar ki ne kawai idan har na tabbatar da cewar kin isa gida cikin ƙoshin lafiya, ba tare da wani ya ƙara firgita ko tsoritar da ke ba".
Na ɗaga kai ina kallonsa ganin ya bar motar ya soma bi na da ƙafa.
"Ba ka tsoron a ɗauke motan ka baro ta a can?". Ya murmusa kafin ya ce"na bar ta a hannun Allah, na yarda kuma duk abin da ya zartar babu kuskure a cikinsa".
"To ka koma kawai na gode da rakiyar". Ya ɗan ranƙwafo da kansa ya rage tsayinsa ya ce"don Allah kar ki hana ni aikin lada. Ni ma fa ina da ƙanne mata kuma na san yanayin rarurarsu, yanzu haka a gajiye kike".
Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi kafin na furta"babu alamar gajiya ni kam".
"Kar ki faɗa abin da ba shi ne a cikin zuciyarki ba don fuskarki ta riga da ta bayyana gaskiyar da kike ɓoyewa".
"Wai me yasa mutane da yawa suke cewa fuskana yana bayyanar da labarin zuciyata ne?".
Ya ɗage girarsa guda"wataƙila zuciyar ce ba ta son a zarge ta da kasancewa daga cikin maƙaryata". Babu shiri na ji dariya mai sauti ya ƙwace mini na sake ina yi babu ƙauƙƙautawa. Sai da na tsagaita don kaina kafin na ce"kai dai da abin dariya kake".
"Ɗabi'ata ce son ganin wani yana farin ciki a sanadina. Yanzu dai mu je na raka ki ko". Ban ce da shi komai ba muka fara tafiya yana ta ja na da hira ina amsa masa har muka isa farkon layinmu na dakata a nan.
"To rakiyar ta isa haka kar na ja ka da nisa. Kuma ka ce tafiya ce a gabanka".
"Tafiya ce kam a gabana mai nisa amma na zaɓi na tsaya na fara sauƙe haƙƙin da yake kaina".
Na ɗage masa ido ɗaya alamar ban fahimci zancen ba haka ya ba shi damar ci gaba da zancen"haƙƙin tabbatar da cewar wani bai sake razana ki ba mana".
"Da ba ka fasa tafiyarka ni kam babu wani matsala, ni da ko sani na ma ba ka yi ba".
"Ina ji a jiki zuwa gaba zan zama ɗaya daga cikin mutanen da suka fi kowa saninki, yanzu dai mun iso ne kika tsaya a nan?".
"Ba mu iso ba amma ga can gidan mu daga nan ma ina hango sa". Na ƙare zancen ina nuna masa gidanmu da ƴar manuniyar ƴatsata.
"To tun da kin hana ni aikin lada bari na tsaya daga nan, sai dai har za mu rabu ba ki tambayi sunana ba alhalin ni kuma na san naki". Na ware idanuna"a ina ka san sunana bawan Allah?".
"Zuciyata ce ta sanar da ni".
"To me ye ta sanar da kai?".
Ya juya manyan fararen idanun"Safiyya". Na jijjiga kaina"tun da na ɗan ji tausayinka bari na sanar da kai. Sunana Amatullah".
"Ni kuma sunana Muhammad Taukeeq".
Na jinjina kaina"ina godiya, Allah ya kiyaye hanya". Cike da jin daɗi ya ce"Amin na gode, ki fara wuce wa tukunnan". Murmushi kawai na yi na wuce izuwa gida har na isa annuri bai gushe daga fuskana ba.
[8/4, 8:52 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 1️⃣9️⃣
Kai tsaye na wuce ɗakinmu ba tare da na mayar da hankali akan tunkoson jama'ar da suke tsaye cirko-cirko a cikin gidan ba. Sauya kayan jikina na yi na fito na soma haɗa wuta saboda wani irin masifaffan yunwan da take ƙwaƙulan hancin cikina da tun suna kukan yunwan har sun saduda. A wajen na tsinci kan zancen wai sata aka shiga ɗakin Maman victor aka yi mata na turamen zannuna da kuɗi. Sosai aka yi dambarwa kamar ba za su bar juna da rai ba, sai da wasu biyu daga cikin manyan dattijan unguwa suka shigo suka tsawatar saboda hayaniyar ya ƙai ƙololuwar yawa. Taliya na tafasa fara na ci na zuba mata mai da yaci na ci nawa na bar wa Umma da Abba na su a kula, ina gamawa na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan kasancewar yau ba mu da karatu da yaran da nake koyar da su, hakan ya sa ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai na haɗa izu biyu cif-cif. Na yi sallan isha'i na fito falo na zauna don har yanzu Umma ba ta dawo ba haka nan ma Abba tun da na shigo ban shi ba, kuma a sanin da na yi masa tun runtsi ba ya wuce ƙarfe taran dare a waje.
Kamar an jefo ta haka Amira ta faɗo cikin ɗakin ta manna mini waya kunne, na bi ta da kallo.
"Mansur ne za ku gaisa".
Na riƙe wayar ina yi masa sallama ya amsa, haka muka gaisa cikin girmamawa da mutunta juna kafin na miƙa mata wayar, ba su yi wani dogon magana ba ita suka yi sallama. Ta ajiye wayar tana kallona.
"Ba ni labari mana?". Na ɗage mata gira"ban gane ba wani irin labari kenan?".
"Kar ki raina min hankali mana Amatullah. Wane ne wannan mutumin da ɗazu kuka tsaya da shi a bakin layin nan, kuna ta hira kamar kun daɗe da sanin juna".
Fuskana ɗauke da mamaki ƙarara na furta"waye ya sanar da ke wannan labarin?". Ta sheƙe da dariya kafin can ta soma cewa"da idona fa na ganki, na so na je na tutsiye ki a wajen sai kuma na sauya shawara". Na yalwata fuskana da yalwataccen annurin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata.
"Wallahi ni ma ban san ba ban taɓa ganin sa sai yau ɗin nan. A hanya muka haɗu shi ne ya tsaya jirana har muka taso daga islamiyya, ya dage wai sai ya rako ni gida saboda kar wani ya ƙara tsorita ni kamar yadda ya tsorita ni da horn ɗin motarsa". Na ƙare zancen ina baza murmushi kamar wacce aka yi wa alƙawarin kujerar makka na bana.
Sake da baki Amira take kallo na har na gama zancen kafin ta musguta tana faɗin"amma ai ba shi ne mutum na farko da ya taɓa nuna buƙatar yi miki rakiya ba, kika watsa musu ƙasa a idanunsu. Shi wannan me yasa kika amince masa har kika sake masa fuska".
"Wannan ya bambamta da duk wanda na taɓa haɗuwa da su akan hanya". Ta katse ni"me ye ya bambamta shi da sauran?".
"Saboda har muka rabu da shi bai yabi sura ko halittan jikina ba. Saɓanin sauran samarin da nake cin karo da su maganar farko da yake fara fitowa daga bakinsu shi ne yabon surana".
"Ki na da gaskiya da wannan fannin. To ba ni labari me ye kuka tattauna?". Na galla mata harara"ban sani ba uwar son gulma da bin ƙwaƙwƙwafi".
"Shikenan in ta yi tsami ai za mu ji".
Na gyara zamana na kawar da zancen ta hanyar sauya akalar maganar"wai ina Umma ta je ne ga Abba ma har yanzu bai dawo ba?".
"Umma ta dawo ta ƙara fita. Shi kuma Abba bai fita ba ma sai da aka yi ƙiran asr".
Na ɓoye mamakina na ce"Abban?". Ta gyaɗa mini kai alamar e tana ci gaba da cewa"me ye wani abin mamaki?".
"Babu daman ina so mu yi magana akan wannan malamin da muka haɗu da shi a tasha.......". Ta ɗaga mini hannun na dakata haka.
"Ki rufa mana asiri Amatullah kar wani ya ji ki kina maimaita wannan maganar, ki manta da wannan mutumin ki sa a ranki kamar babu wani abun da ya faru. Wallahi idan kika kuskure wani ya ji ki kina irin wannan maganar sai ɗan buzunki".
"Ki saurare ni ki ji abin da zan faɗa mana".
"Ina jin ki". Ta amsa mini a daƙile.
"Sheikh Dawood Nasarawa yana daga cikin manyan baƙin malaman da za a gayyata a lokacin yaye mu daga islamiyya, saboda ya sama halatta babu irin faɗi tashin da Malam Suleiman bai yi ba. Zuciyata ta cika da wasi-wasi akan sanin da mutanen gari suka yi masa da kuma fuskar da yau nuna mini a tasha". Tun kafin na gama zancen na ga ta haɗe giran sama da na ƙasa ta zuba mini na jiyamunta. A kufule ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa masa a cikin ranta.
"Ki yi maza ki cire wannan gurɓataccen tunanin daga cikin ranki kafin ki jefa kanki cikin wata masifar da ba za ki iya cire kanki ba. Kin san fa yanzu duniya ta sauya abu ƙiris za ka yi ko'ina ya ɗauka, yadda malamin nan ya yake kan lokacinsa idan kika ce diddiginsa za ki bi sai kin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 24