Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ana gamawa Anty Sawwama ta ce mu tafi gida Yaya Alhassan zai zauna a wajen Abba kafin a ga abin da hali zai yi. "Anty don Allah ku yi haƙuri ku bar ni a nan...". Kafin na rufe bakina ta katse ni"kar ki yi gardama da ni Amatullah ki wuce mu tafi". Ban ƙara cewa komai don ban ga fuskar hakan daga gare ta ba. Malam Aminu da Yaya Alhassan da Muhammad Taukif suka iso wajen a tare duk su ukun suka jefo mini wani matsanancin kallo. Ba kamar Malam Aminu da har cije baki yake yi, shi ya fara tafiya bayan Anty Sawwama ta zabga masa godiyar ɗawainiyyar da ya yi. "Anty na ga kamar ku ma tafiya za ku yi ko zan sauƙo a gida. Daga nan ni ma sai na wuce". Muhammad Taufik ya yi zancen idanunsa akan Anty Sawwama. "A'a ɗan nan tun da lamarin nan ya faru kake ɗawainiyya da mu, kai ka kawo mu asibitin nan mai tsada a cikin motarka sannan ka biya kuɗin komai da komai, ɗawainiyyar ai sai ta yi yawa ka yi tafiyarka kawai za mu hau motar hanya". "Mahaifina ya umarce ni da na tsaya akan lamarin wannan baiwar Allahn nan har sai na tabbatar da cewar komai ya warware. Don haka ina roƙonki da ki taimaka mini wajen cika umarnin mahaifina". Shuru Anty Sawwama ta yi kawai tana jijjiga kanta kana ta ce"shikenan to mun gode". Suka yi sallama da Yaya Alhassan bayan sun yi musayar lambar wayan juna ya yi gaba muna biye da shi a bayan, a Umma da Umman Amira tunin sun tafi gida. Kamar motar gawa tun da muka shiga babu wanda ko tari har muka isa gidan, Anty Sawwama da Amira suka yi masa godiya ni kam na kasa cewa komai illa kallon juna da muke yi ni da shi. Muna sanya ƙafarmu a cikin filin tsakar gidan Umma ta tare mu tamkar daman jiran shigowarmu take yi. "Kar ki sake ki nufo ɗakin nan shegiya tsinanniya kawai. Amatullah kin ja min abin magana da yamaɗiɗi a cikin gari ki jawo min abin kunya, kar ki matso inda don babu makawa matuƙar muka haɗa wajen zama da ke zuciya za ta iya ɗiba na na murɗe miki wuya". "Subhanallahi! Haba Hafsatu idan hankali ya gushe ai hankali ake sawa a nemo shi. Ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi sai a zauna a nemo yadda za a ɗinke wannan ɓarakar da ta same mu gabaɗaya". Kalaman Anty Sawwama kamar aka fusata Umma suka yi ta cika ta yi fam. "Maman Umar ki fitar da yarinyar nan daga cikin gidan duk kafin na biye zuciyata na aikata abin da daga ni har ke za mu zo muna cizon ɗan tsaya daga baya". Anty Sawwama ta dafe kai"innalillahi wa inna ilahirin raji'un". Idanuna suka daina gano mini komai illa gilmawar baƙin duhu duk da haka na ja jiki na isa gaban Umma na riƙe ƙafafunta. "Umma idan ba ki rufa mini asiri ba waye zai rufa mini asiri a cikin duniyar nan. Umma ki ba ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta Ubangiji ta faɗa mini". Ta sanya kafa ta yi kutufol da ni sai da na yi tanbulin goshina da aka yi wa dressing ya bugu da ƙasa, jini ya soma zuba da goshi da hancina. Anty Sawwama ta yi saurin ɗago ni sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna sai da ta riƙe ni kam. Duk rashin tausayin mutanen gidanmu a ranar sai da na tausayina kwance a fuskarsu. Matar Uszatu ta ce na je ɗakinta na zauna Umma ta daka tsalle ta dire a duk wanda ya ba ni wajen rakaɓewa sai ta yi masa ɗiban albarka mai wasali, haka Anty Sawwama ta riƙo ni ina kuka ita ma tana yi haka nan ma Amira da ƙyar aka ɓanbare ta daga jikina muna kuka wiwi muka fito daga cikin gidan. Muna fitowa idanuna suka sauƙa akan Muhammad Taukif ya na ganin mu ya yi saurin fitowa daga cikin motarsa ya fito. "Hajiya lafiya na ga kun shiga kun fito?". Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa wata tambayar"kana nan ba ka tafi ba?". "Yanzu nake son tafiya sai kuma na ga fitowarku. Lafiya kuwa?". "Lafiya ƙalau yanayin jikin natan ne ƙawa babu daɗi, shi ne za mu je gidana da ita". "To ku shiga na kai ku mana". "A'a kar ka damu za mu nema abin hawa". Da hanzari ya katse ta"Hajiya umarnin mahaifina nake cikawa, don yana girmamawa da mutunta duk wanda ya haddace littafin mai tsarki yana musu hidima da ƙarfinsa da kuma aljihunsa. Don Allah ku shiga na kai ku". Ba ta musu ba ta ja hannuna muka shiga cikin motar har muka isa kuka nake yi, mu fito za mu shiga cikin gidan nan na ji ya ƙira sunana na tsaya cak. "Amatullah". Na waigo muna kallon juna"Allah ya ba ki lafiya". Na kasa amsawa da kalmomin baka sai a cikin zuciyata na amsa. Na muka ƙarisa shiga cikin gidan ina shiga cikin ɗakin na zube akan katifanta ina ta kuka. Anty Zulaihatu ta shigo ta yi mini dukkanin lallashin duniya amma na kasa daina kukan, Anty Sawwama ita ma ta shigo. "Amatullah tashi ki zauna mu yi magana". "Anty ba zan iya tashi ba". Cikin kakkauran murya ta furta"Amatullah waye ya yi miki ciki?". Numfashina ya tsaya na lokaci guda saboda cakwakiyar da yake cikin tambayar da ta yi mini. Wanda ni ma kaina ban san wanda ya aikata mini hakan balle na sama kalaman kare kaina. Abu na sani kuma na yarda da shi shi ne ƙaddarata ta zo a haka babu yadda zan yi na guje mata. [10/26, 3:09 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 3️⃣7️⃣ Numfashi nake ta sauƙewa wani na bin wani ga jinin da yake sauƙowa daga goshina yana wanke mini fuskana, cikin taushin murya na ji ta ƙara faɗin"Amatullah ki taimaka ki sanar mu wanda ya yi miki ciki. Ki dubi halin da mahaifinki yake ciki, a cikin rayuwarsa kina ɗaga daga cikin abin da yake matuƙar alfahari da su tun da kika zo duniya ya kalle ki har kika girma farin cikinsa ya ninku. A lokuta da yawa darajarki mahaifiyarki take ci yake ɗaga mata ƙafa akan dukkan abubuwan da take yi, domin a cewarsa ita ma ta taka rawar gani ta haifa mata ɗiya sannan a dalilin hakan aka cire mata mahaifa yana ganin inya rabu da ita bai yi mata adalci ba. Amatullah iyayenki sun yi ɗawainiyya da ke irin ɗawainiyyar da fi ƙarfin baki ya suffanta shi cikin kalmomi, mahaifiyarki ta sha wahalar rainon cikinki lokacin haihuwarki ta yi dogon naƙudan da har sai da muka cire rai da cewar za ta rayu. Mahaifinki ya yi wahala da ke tun ki na ciki har kawo girmanki ya yi duk mai yiyuwa wajen ganin ya tanada miki more rayuwa daidai ƙarfin aljihunsa, ya ba ki ilmi har sai da yau aka wayi gari kin kammala haddan alƙur'ani. Amma ki rasa da me ye za ki saka musu sai da wannan abun shin sun cancanci hakan ne daga gare ki?". "Wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini ba da son raina ba, Anty ki yarda da ni ba zan taɓa wofantar da tarbiyyan da kuka har ni ko na sauƙa daga kan gwadaben da kuka ɗaura ni akai ba". Ta katse ni"waye ya yi miki ciki?". "Ban san shi ba ban taɓa ganin sa hasalima shi ma bai sanni ba, bai taɓa ganin fuskata ba". A fusace ta miƙe irin fusatar da tun da uwata ta kawo ni duniya na girma na yi hankali ban taɓa ganin ta cikin makamancinsa ba. "Wani irin magana ce haka wanda hankali ba zai ɗauke shi ba? Kamar ya ya ba ki san shi ba?". "Wallahi tallahi ban san shi ba ba mu taɓa ganin juna ba ni da shi". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta furta cike da damuwa tana dafe kanta, Anty Zulaihatu ta tashi ta riƙe ta don tana ƙoƙarin faɗuwa. Ta zaunar da ita tana faɗin"don Allah Umma ki yi haƙuri a bi komai a sannu. Son samu ma a bar ta kar kowa ya ƙara yi mata maganar har sai ta dawo cikin hayyacinta nutsuwarta ta daidaita lamuran sun dawo daidai". Numfashinta ne ya soma sama da ƙasa na fita waje da sauri na ɗebo mata ruwa zan kai mata muka yi kiciɓus da Umar ya shigo gidan. Ya sha gabana"ina za ki je?". Cikin rawan jiki da na murya na ce"ruwa zan kai wa Anty numfashinta sai sama-sama yake yi". Ya kwace kofin ruwan yana jifa na da wani matsiyacin kallo na bi bayan sa da sauri, muka shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta karɓa kofin ruwan ta yi tofin addu'o'i ta ba ta sha ragowar kuma ta shafa mata a jikinta take ta koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Anty Zulaihatu ta gyara mata zamanta ta kwantar da ita cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta. Duk muka sauƙe ajiyan zuciya muna hamdala da lamarin ya zo da sauƙi haka don tana da hawan jini mai sarƙarƙiya gefe guda kuma tana cutar numfashi. "Anty wai me ye wannan take yi a cikin gidan nan ne?". Umar ya yi zancen cikin haɗe rai da zafin zuciya. "Amatullah ce fa ko ba ka gane ta ba ne? Nan kamar gida ne a gare ta ai, tana da ikon zuwa a duk sanda take so kuma ta yi niyya". "Anty a da kenan ba yanzu za ta watsa mana ƙasa a idanunmu ba. Cikin shege fa Amatullah waye ya yi miki ciki? Me ya sa za ki yi mana haka?". Fayau Anty Sawwama ta ɗauke shi da mari ta nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsarsa"Umar ba ka yi hauka ne ko kuma shaye-shaye ka fara yi ba mu sani ba?. Ashe ba za ka iya rufawa ƴar uwarka asiri a bisa ƙaddarar da ta same ta ba". Ya dafe gefen kuncinsa da ta watsa masa marin"Anty ƙaddara? Ƙaddara fa kika ce? Amatullah ba yarinya ba ce ta ba wa shekaru goma sha biyar baya. In ma ƙaddarar ce me yasa tun lokacin da abin ya faru ba ta sanar ba har sai da ciki ya ɓullu a jikinta?". Tana ada aya a nan tashi ya fice daga cikin ɗakin fu cikin saurin kamar mai tafiyan akan iska. Anty Zulaihatu ta dafe kanta"innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musifati". Kasa motsa na yi daga inda nake zauna izuwa yanzu kam ma kukan ma na daina illa kukan zucin da nake yi mai matuƙar ƙuna da raɗaɗi. Ina nan zaune har Anty Zulaihatu ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta zauna a kusa da ni. "Ki tashi ki je ki yi wanka, ki gyara jikinki. Ki sauya kaya sannan ki zo ki ci abinci sai ki kwanta ki huta". Na ɗago rinannun idanuna ina kallon ta da shi sai dai bakin ya kasa furta komai. Ta dafa kafaɗata" Amatullah ki yi haƙuri na san ba zan iya kwatanta girman damuwar da kike ciki ba, amma tabbas ni ma ina cikin damuwa domin duk abin da ya same ki haƙiƙa kai tsaye ni ma ya shafe ni. Ki miƙa lmauranki ga Allah ki daidaita nutsuwarki sannan ki tanadi bayanan da za ki yi wa iyayenmu". Da taimakon ta na miƙe tsaye ta riƙo ni ta kai ni har ƙofar banɗakin na shiga. Na durƙushe a gaban bokatin ruwan da ta kai mini ina kukan zuci kaina har wani ciwo yake yi mini idanuna suka kumbura tsumtim. "Allah na tuba ka yafe mini. Allah ya kawo mini ɗauki da mafita. Ya Allah na yarda babu kuskure a cikin hukuncinka kuma ba ka ɗaurawa Bawa abin da ba zai iya ba, Ya Ubangijin sammai da ƙassai bakwai ya Ubangijin talikai da dukkan wasu halittu ina roƙon da ka tashi kafaɗun Abbana ka ba shi lafiya, kar ka bari baƙin ciki ya yi silar faɗawarsa cikin wani irin yanayi". A raunane na ƙare zancen cikin dushashewar murya, da ƙyar na miƙe akan ƙafafuna saboda rawar da suke yi na yi wanka na fito sai da na yi alwala kana na shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta ba ni zani da riga t-shirt na saka kasancewar gidan babu ɗiya mace wannan ma a cikin kayan Anty Sawwama ta binciko mini. A zaune na yi sallan saboda ba zan iya tsayiwa ba, na daɗe a sujjadata ta ƙarshe ina kuka kafin na ɗago na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa cewa ko kanzil. Ko buɗe abincin da Anty Zulaihatu ta kawo mini ban iya ba na kifa kaina da gwiwa ina ta sauƙe ajiyan numfashi. Haka na wuni cikin wani irin mungun yanayin da ban taɓa tsintar kaina a cikinsa ba tun da na zo duniya sai bayan sallan la'asar Anty Sawwama ta farka. Anty Zulaihatu ta kai mata ruwa ta yi wanka ta zo ta gabatar da salla ita ma ta kasa cin abincin sai cewa ta yi a ƙira mata Alhassan, Anty Zulaihatu ta ƙira shi ta miƙa mata wayar bayan ta sanya ta a amsa-kuwwa. "Alhassan ya mai jikin?". "Da sauƙi dai kawai za a ce Umma, amma tabbas Kawu yana jin jiki wallahi. Bayan tafiyarku ma sun mayar da shi emergency sannan sun hana kowa ya shiga ya gan sa, sun ce zuwa safiya idan babu wani ci gaba dole za su tura mu asibitin dake maƙwabciyar jihar nan, wanda su daman masu irin laluransa kawai suke dubawa". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wai me ye suka ce yana damunsa ne haka?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"Umma gefensa ɗaya ne ya shanye sannan zuciyarsa ta kumbura. Dole akwai buƙatar a yi masa gashin ƙashi da aiki a zuciya". Tun kafin ya ƙarisa zancen muka saka salati wani kuka marar control ya ƙwace mini na so ma yin sa da dukkan ƙarfina. Anty Zulaihatu ta karɓa wayan" in mun zo za mu sama ganin sa ne?". "Babu wanda ake bari ya gansa likitotin ne kawai suke shiga, kuma sun dawowa za mu yi don sun ce su a tsarin su ba a kwana a tare da majinyancin da aka kai emergency. Suna da ƙwararrun ma'aikata da kuma masu kula da majinyanta". A rikice Anty Sawwama ta furta"ku kuka shi da waye za a bar shi?". "Umma ki kwantar da hankalinki fa babu wani abun da zai same shi. Idan na dawo sai mu gama maganan". Da aka suka yi sallama duk muka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa. Sai bayan sallan isha'i Yaya Alhassan da Amir suka dawo suka ƙara yi mana bayanin halin da Abba yake ciki, ni dai ina rakuɓe a gefe guda ina jin na wanin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Anty Sawwama ta umarce mu da mu tashi mu je mu alwala kowa ya karanta alƙur'ani iya yadda ya sawwaƙa mu yi tawassali da hakan wajen nemawa Abba lafiya a wajen wanda babu abin da ya gagari ƙarfin ikonsa. Hakan muka yi ba mu kwanta ba sai ƙarfe ɗayan dare, daga Yaya Alhassan har Amir tun da suka shigo cikin su wanda ya ce mini ko kanzil haka nan ba su buƙacin jin dalilin kasancewata a gidan ba. Yadda nake jin jikina a wannan daren ban taɓa zaton za a wayi gari da ni cikin rayayyu ba, gaba ɗaya na cire tsammani da rayuwa na saddaƙar da komai na miƙa wuya ina jiran yadda Ubangiji zai yi da ni. Don na yadda duk abin da ya zartar hakan shi ne daidai kuma babu kuskure a cikin sa. Yadda na ga rana haka na ga ban runtsa ko na sakon guda ba. Daga masallacin sallan asubahi Yaya Alhassan da Amir suka wuce asibiti wajen Abba. Wajajen ƙarfe goma Anty Sawwama da Umar suka shirya za su tafi asibitin na dage akan zan biso na je na ga Abba amma ta hana ni babu yadda na iya dole na haƙura muka zauna da Anty Zulaihatu zaman jiran tsammani. Ba su daɗe da tafiya ba Amira ta zo ta ina jin sallamarta na zabura da sauri na fito filin tsakar gidan, muka rumgume juna muna wani irin kuka mai ban tausayi da ƙyar Anty Zulaihatu ta lallashe mu muka tashi muka cikin ɗakin. "Amira kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Ni kuma tawa salon ƙaddarar kenan". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata cike da tausayi ta soma cewa" komai yana da lokaci Amatullah komai watarana zai zo ƙarshe zai zama labari har ya shuɗe. Don Allah ki cire damuwar komai a ranki". "Ta ya ya kike tunanin zan iya cire damuwa daga cikin raina? Ba ni da wannan ikon Amira, ba ni da wani buri yanzu da ya wuce na ga Abba ko da kuwa shi ne abu na ƙarshe da idanuna da su yi tozali da shi kafin rai ya yi bankwana da gangar jikina". Ta kai tafin hannunta ta rufe mini bakina ruf. "In sha Allah ma babu wanda zai mutu. Kuma komai zai zo ƙarshe". Na kasa cewa da ita komai illa kukan da na fashe da shi ina yi ita ma tana yi babu mai lallashin wani a tsakaninmu. Duk ƙarfin halin Anty Zulaihatu ma sai ta yi kukan haka muka sha kukan har muka gaji. Na ɗago idona ina kallon Amira da ita duk damuwa ya bayyana a fuskarta. "Umma ba ta neme ni ba ko Amira?". Ta ɗan yi jim ba tare da ta ba ni amsa ba. Shurunta ya sani cewa"ba ta neme ni ba ko? Na kan ji ana cewa uwa ita ce majingina kuma mafaka a wajen ƴaƴanta, na sha jin a cikin labarun hikayoyi cewar uwa ce kaɗai ba ta juyawa ƴaƴanta baya ita ce kaɗai take rufawa ƴaƴanta asira komai munin abin da suka aikata. Amma me yasa tawa uwar ta bambamta da sauran?". "Umma ta na son ki Amatullah ke ma shaida don ta yi abubuwa da yawa da bayyanar da hakan. Ki yi mata uzuri akan abin da ta aikata ki ba ta lokaci ta huci sannan ku yi magana". Amira ta yi kalaman cikin sigar son kwantar mini da hankali. Haka muka zauna har sai bayan sallan asr Anty Sawwama da Umar suka dawo cikin wani irin yanayi na sanyin jiki. Nan suke shaida mana cewar an tafi da Abba asibitin ƙwararru dake maƙwabtaka da jiharmu ta kuma ƙara bayyana mana cewar yana buƙatar addu'armu, lamarin da ya ƙara gigita nutsuwar da ta yi saura akan jikina kuka nake yi tuburan jikina yana rawa tamkar mai shafan iskokai sai Anty Zulaihatu da Amira suka rirriƙe ni suna yi mini tofi kafin na lafa na kwanta na yi lamau. Sai dab da magrib Amira ta tafi mijin Anty Zulaihatu ma ya zo ya ɗauke akan gobe da safe za ta dawo ta ƙara duba jikin nawan. Haka na ƙara kwana cikin wannan yanayin kafin gari ya waye zazzaɓi ya rufe ni ko idona ba na iya buɗewa, na firgita na ruɗe bisa mummunan mafarkin da na yi da Abba, wai na je wajen sa a asibiti ya ce kar a bar ni na shiga wajensa ba ya son ganina. Wajajen ƙarfe takwas Yaya Alhassan ya ƙira waya ya shaida mana cewar ga su a hanya suna dawowa. Tsam Anty Sawwama ta miƙe"alhamdulillah! Lafiya ta samu kenan? Ina shi Mannirun haɗa da shi". "Umma ba zai iya magana ba, sai dai mun iso ɗin kawai". Yanayin da ya ƙare zancen da kashe wayar da ya yi ba tare da an gama maganar ba, ya samu ɗaura ayar tambaya akan sa. Haka muka dinga ƙiran wayar amma baya ɗauka daga ƙarshe ma ya kashe ta, daga shi har Amir muka daina samun wayoyinsu. [10/27, 5:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 3️⃣8️⃣ Haka muka kasa tsaye balle zaune duk muka yi jigum-jigum da mu cikin mu babu mai walwala. A zaune na yi sallan zuhr saboda yadda ƙafafuna suke rawa ji nake yi tamkar ba sa cikin gangar jikina, ina zaune a wajen na zagba uban tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda komai ya sauya mini cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. "Abba ka yafe mini Allah ya tashi kafaɗunta. Na san kai kaɗai ne za ka fahimce ni a kaf cikin faɗin duniyar nan. Abba kai ɗaya ne kake fahimtar shuru na kuma ina da yaƙinin kai kaɗai ne za ka yi mini uzuri akan abin da ya faru. Na yi kewarka ina son ganinka sai dai ba zan iya jure ganinka cikin yanayin da na yi silar jefa ka a ciki ba. Abba ka yafe mini ka yafe mini". Na yi zancen cikin karyarwan zuciya wasu hawaye suna rige-rigen fitowa daga cikin rinannun idanuna. Na ji wani abu ya tokare mini ƙirjina numfashi ma da ƙyar nake fitarwa tamkar mai lalurar cutar numfashi. Kamar daga sama na tsinkayo sallamar su Yaya Alhassan take na ji fada na ya yanke ya faɗi zuciyata ta buga irin bugun da har sai da ya tilasta mini runtse idanuna. Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka miƙe a tare suka fita amma ni kam ko gizau na gaza motsawa daga inda nake zaune, sai dai ina zaune ina jiyo abin da suke tattaunawa. "Alhassan ya ya na gan ku haka? Ina shi Mannirun? An sallama ku ne daga asibitin?". Duk jerin tambayoyin da Anty Sawwama ta jefa masa bai amsa ko guda ba. "Wai kurame kuka zama ne ko kuwa? Cikinku babu wanda zai amsa min tambayoyina". Anty Sawwama ta ƙara buga musu wani tambayar muryarta har ta na harɗewa waje guda. "Umma ku shiga ciki za a shigo da shi". Ina yin wannan furucin na Yaya Alhassan na zabura tamkar wacce aka tsigarawa alluran doki. Na miƙe har ina ƙoƙarin faɗuwa na fito waje daidai lokacin da wasu maza biyu suka shigo da mutum cikin lulluɓi farin ƙyale, Amir ya ɗauko tabarma ya shimfiɗa suka kwantar da shi, mazan suka fita ya rage daga m sai ya mu. "Wane ne wannan Alhassan? Alhassan kar ka ce min gawan Manniru ne kwance a nan. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Daman da kuke cewa za ga ku nan za ku dawo ɗin gawarsa za ku dawo da shi". Anty Sawwama ta yi kalaman cikin tsananin ruɗani da kaɗuwa, Anty Zulaihatu kam ta kasa magana sai kukan da nake yi, ganin yadda na tsaya a waje ɗaya na kasa gaba balle baya ya sa ta iso gare ni ta riƙo ni. "Amatullah sai dai mu yi haƙuri". Tun kafin ta gama maganar na fizge jikina daga riƙon da ta yi mini kamar mai aljanu ko iskokai haka na ƙanƙame ta ƙam ta gaza motsawa balle ta yi wani yunƙurin ƙwacewa. "Abba bai rasu ba, ba shi ba ne bari na buɗe miki ki gani ba shi ba ne fa Anty Sawwama ku daina wannan kukan". Na kai aya ina jan ƙafafuna da nake ɗagawa da ƙyar na je zan buɗe gawan Yaya Alhassan ya riƙe hannuna jikina har wani jijjiga yake yi tamkar mazari. "Kar ka hana ta Alhassan ka bar ta ta buɗe". Anty Sawwama ta furta dole yaya Alhassan ya cika ni na je na durƙushe a gaban gawar haka kawai tun kafin na buɗe na ji ƙirjina yana tsananta bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya bayyano waje ya daka rawar disko. Duk yadda hawaye suka wadai kurmin idanuna ƙarfi hali da bushewar da zuciyata ta yi ya hana sa zuba, don ba na son na gaskata abun da su Anty Sawwama suke yi wa kuka. Jikina gabaɗaya yana rawa na kai hannu na buɗe dirsham na zame na yi zaman ƴan bori hawayen da nake riƙewa suka zama lasisin yin gudun famfalaƙi a bisa fuskata. "Abba don girman Allah ka tashi kar ka tafi ka bar ni a cikin wannan yanayin. Abba kar ka yi mini haka ni kuwa ina zan tsoma kaina idan na waiga ban ganka a kusa da ni ba, don Allah ka buɗe idanunka ka tashi kar ka tafi". Na

Chapter 22 of 24