Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mu tafi ba sai da Umma ta dawo muka yi mata sallama muka tafi. Sai da muka tsaya a wajen Halilu mai chemist ya mini alluran kana muka tafi. Ko kallon azurki ban yi wa Hajiya Tasalla ba duk da kuwa kulawar da take ba ni don tun da muke je ta kasa zaune ta kasa tsaye sai hidima take yi da mu har sauya mana ɗaki ta yi. "Hajiya ina ita Ramlatun ta dawo?". Na yi tambayar fuskata a ɗaure kamar hadarin gabas. Ta soma inda-inda"ki yi haƙuri an yi rasuwa ne a can ƙauyen shi yasa. Ni ma saboda na san za ku zo ne shi yasa ban je ba. Amma in Sha Allah da zaran an yi sadakan bakwai za ta dawo ku yi haƙuri". Ban ce da ita komai ba na tashi da sauri na har ina harɗewa na shige ciki ina tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mini daga idanuna. Amira tana shigowa muka rufe ɗaki na ciki na amsa wayarta na buɗe application ɗin alƙur'ani ina karantawa tun Amira tana zaune har sai da ta kwanta bacci ya soma fizgan ta don daren jiya ba mu runtsa ba. Na daɗe ina karatu kafin na ɗaga hannuna sama sai dai na kasa cewa komai illa kukan da ya kubce mini. Na kifa kai da gwiwa ina rero shi. Yadda na ga rana haka na ga dare don ko ya ya na rufe idanuna sai na ga kamar abin da ni jiya ne zai ƙara maimata kansa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana shuɗe wa tun ina kwana na tashi cikin fargaba da zulumin abin da zai je ya dawo har tunanin hakan ya fara raguwa, daidai da rana guda Umma ba ta taɓa fahimtar halin da nake ciki ba balle ta lura sauyawar yanayin jikina. Haka har sati cif ya cika lokacin ya rage saura sati biyu sauƙarmu komai ya kankama, tun ina saka rai da dawowar Ramlatu kamar yadda Hajiya Tasalla take faɗa har na miƙa lamarin ga Allah na kuma yi yaƙinin dukkan abin da ya zartar a kaina shi ne daidai. Cikin ƙanƙanin lokacin na rame na zabge na yi baƙi kowa ya ganni sai ya ce na rame. Duk wanda ya tambaye me ke faruwa na kan ce da shi karatun sauƙanmu ne kawai na sa a gaba shi yasa. Na yi duk yadda zan yi na haɗu da Ramlatu ko shi Mus'bahun amma lamarin ya ci tura duk da kuwa irin naci da bibiyar lamarin da nake yi daki-daki. Komai nawa ya sauya hatta a karatun islamiyya ƙoƙari na ya ja baya. Har gida Anty Zulaihatu ta aiko mini kayan da Yaya Alhassan ya saya mini kasancewar ban sama nutsuwar zuwa gidan ba balle na amsa, Umma ta daka tsalle ta dire ta ce ba zan yi amfani da kayan ba. Babu yadda muka iya daga ni har Abba, haka muna ji muna gani aka mayar da kayan, na ci kuka har na godewa rabbana. Ana saura kwana uku sauƙan mu a wani yammaci Malam Suleiman ya zo gidan mu ya yi sallama da Abbana, tun da na ji sunan wanda ya zo neman Abba na tsinci kaina cikin faɗuwar gaba. [10/22, 7:02 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 3️⃣4️⃣ Tun da Abba ya fita ganawa da Malam Suleiman na kasa zaune balle tsaye, haka kawai na tsinci kaina cikin tsananin faɗuwar gaba da kuma tsinkewar zuciya. Amir ya bankaɗo labulen ƙofar falon da hakan ya sani miƙewa zumbur na miƙe akan ƙafafuna ina sauraren abin da yake faɗi cikin tsiwa. "Wai ki zo in ji Abbanki suna zaune". "Ni kuma?". Na jefa masa tambayar cikin ruɗewa. Ya taɓe baki kafin ya ce"e ke ɗin fa malama". Yana dasa aya anan ya saki labulen ya juya ya fice yana wasu ƙananun magana. Jikina a sanyaye na fito ina tafi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na iso cikin zauren bakina ɗauke da sallamar da ta sama amsawar Abba da Malam Suleiman. "Abba ga ni an ce kana nema na". Ya yi ɗan jim kafin can ya furta"Uwata wai me yake faruwa ne? Ga malaminku nan ya kawo min ƙorafin cewar yanzu ba kya mayar da hankali akan karatunki". Na rusunar da kaina ƙasa ina faɗin"Abba babu komai". Ya yi saurin datsen numfashina"Uwata akwai wani abun mana ai da ba haka kike ba". "Abba kawai jinyar da na ɗan yin nan ne cikin kwanakin nan shi yasa". Malam Suleiman ya but caraf ya karɓe zancen"Amatullah akwai abin da yake damunki duk yanayinki ya sauya, kin daina mayar da hankali akan karatunki bayan kin san cewar kina ɗaya daga cikin ɗaliban da za su yi karatu a ranar taronmu. Ki cije damuwar da ke cikin ranki ki fuskanci abin da yake tunkaro rayuwarki". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar wacce aka zarewa laka, hawaye suka ciko mini koramar idanuna hakan ya sa na yi hanzarin rutsunar da idanuna ƙasa da hakan ya ba wa hawayen da ke cikin idanuna kwaranyowa. Cikin sanyin murya Abba ya ce"Amatullah me yake faruwa ne?". "Babu komai Abba". "Kar ka matsa mata Malam Munnir, amma zan so ki ƙara mayar da hankalinki akan karatunki sosai. Don ba zan ɓoye miki ba ke ce hope ɗinmu gabaɗaya Amatullah, duk ƙoƙarin da za ki yi ba iya kanki zai tsaya ba har mu malamanku da makaranta abin zai shafa". "In Sha Allah Malam na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da amin, suka ba ni iznin tafiya na tashi na koma ciki ɗakin su Amira na nufa na iske ta tana waya da Mansur na zauna a gefenta na buga uban tagumi tamkar mai takaba. "Ke kuma fa lafiya?". "Amira wai ya ya zan yi na dawo yadda nake ne a baya? Ni kaina na san na sauya irin sauyawar da ba zan taɓa dawowa daidai ba". Ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya da har sai da na ji sautinsa kafin ta sama zarafin cewa"komai fa sai a hankali zai dawo daidai ba zai yiyuwa a lokaci guda ba. Yanzu kuma me ya faru sanar da ni". Na kwashe duk yadda muka yi da su Abba na sanar da ita ta yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin can ta ce"sai ki mayar da hankali kan karatunki tun kafin su fara zargin wani abun. Na san abin da nauyi Amatullah amma ya ya muka iya da ƙaddara". Na fashe da kuka kamar wata ƙaramar yarinya har jikina yana rawa tamkar mazari. Ta riƙo hannuna na kwantar da kaina a bisa cinyarta. "Amatullah wai me kike so ki mayar da kanki ne? Ko so kike yi ki jawa kanki wani ciwon na daban?. Tun ranar da abin nan ya faru kullum sai kin yi kuka fiye da sau biyar a yini guda, Haba Amatullah abin da ya faru fa ya riga da ya faru damuwa da wannan kukan ba shi zai gyara abin da ya wuce ba". "Allah na tuba ka yafe mini kar ka hukunta ni akan laifin da na aikata a bisa rashin sani....". Ban ƙarisa ba Amira ta rufe mini baki"kar ki ɗaura wa kanki laifin abin da ba ki da ikon sauyawa shi ko hana faruwar sa, kowa fa da kika gani a cikin duniyar nan da irin na shi salon ƙaddaran. Kuma yarda da ƙaddara tana daga cikin cikar imanin mumini". Ban ce da ita komai ba har lokacin da wayarta ta soma ruri ta ɗaga suka yi magana da Mansur sai da suka yi sallama kana ta ce"tashi mu je ga can Mansur a ƙofar gida". "Ki je kawai". Na furta a taƙaice numfashina yana cushewa waje guda. "Kar ma mu fara gardama da ke Amatullah, ki tashi kawai mu tafi don na tabbatar da zaran na gusa daga nan wajen kukan dai za ki ci gaba da shi". Ban tanka mata na tashi gabaɗaya jikina babu ƙwari muka fita tare da ita muka tarar da Auwal da Ummi a zaure suna hira, ta banko mana harara Amira ba ta yi wata-wata ba ta maida mata. Muka iso wajen Mansur da yake tsaye a jikin motarsa kamar ko yaushe yana latsa wayarsa tare da jijjiga makullin motarsa. "Barka da fitowa Tauraruwar birnin zuciyata, hasken da yake haska ƙalbina ta yadda zan yi tafiya ko babu sandan jagora". Lumshe idanunta Amira ta yi cike da jin daɗin zantukansa ta soma cewa"maraba da zuwa Sarki mai sarautar dukkan zuciyata. Ban san da wasu kalmomi zan yi amfani da su wajen nuna maka yadda na yi kewarka ba Ya masoyin raina". Wani murmushi mai laushi suka soma sakarwa junansu mai ɗauke da wani ɓoyayyan saƙonni. "Ni kam bari na koma ciki kafin kun gama". Na yi zancen da ya yi silar dawo da su cikin duniyar zahiri tare da figzo hankali da nutsuwarsu zuwa ga gangunan jikkunansu. Mansur ya haɗe hannayensa wajen guda alamar roƙo yana faɗin"afuwan ranki ya daɗe babban ƙawa, sam ban lura da ke ba ne ayi min aikin gafara". Na taɓe baki"idan ina da zuciya ni ma dai ya kamata na daina rako ta. Kullum sai an ce da ni ba a lura da kasancewata ba a wajen". Duk suka saka dariya kafin Mansur ya ci gaba da magana. "Tuba muke yi a yi mana afuwa. Kuma mussamman zuwan don ke aka yi ta ba na zo duba ki don ta ce da ni ba ki daɗi tsawon kwanaki". Na jinjina kaina"ai na ga ana ƙoƙarin yi mini kora da hali ne". "To yanzu dai ya ya jikin?". "Da sauƙi alhamdulillah". "Sai dai sauƙin musulunci aminiyarmu, amma ban ga alamar sauƙi a tattare da ke ba. Ga shi duk kin faɗa kamar kin yi shekara kina jinya". Na yi ƙarfi hali na murmusa kafin na ce"kuma fa da sauƙi sosai fiye da lokacin baya ne, ka san ciwo ne yake shiga lokacin guda amma warkewa ko samun sauƙi sai a hankali-hankali". Ya jinjina kansa alamar gamsuwa da furucina kana ya ɗaura da cewa"haka ne kam. Allah ya ƙara sauƙi da lafiya mai amfani". "Amin ya Allah". Muka haɗe ni da Amira waje amsawa, mun ɗan taɓa hira kafin Mansur ya ce mu shiga mu fito ya sauƙe mu a gidan Hajiya Tasalla. Muka shiga ciki muka yi wa Ummana da Umman Amira sallama muka fito, ba don raina ya so ba muka shiga motar Mansur ya kai mu gidan. Ya fito da wasu manyan ledodi guda biyu ya ajiye su a gabana da bi ledan da ido kafin na sauƙe idona akan sa alamar son ƙarin bayani. "Wannan naki ne ranki ya daɗe, Allah ya ƙaro sauƙi". Zan yi magana ya katse ni"don Allah kar ki ce komai kuma kar ki hana ni aikin alkhairin da na yi niyyan aikatawa. Ke fa Malama ce kin san cewa ba kyau mayar da hannun kyauta baya". "Gaya mata dai wataƙila ta ji nakan". Amira ta yi zancen tana ƙunshe dariyar da yake ƙoƙarin kwace mata. Na galla mata harara kafin na yi wa Mansur godiya suka yi sallama da Mansur na ɗauki ledar muka shiga ciki. Muna shiga cikin gidan na ji gabana ya yanke ya faɗi lamarin da ya tilasta mini runtse idanuna ina karanto duk addu'ar da ta zo bakina. Sharau muka tarar da gidan don masu kwana ba su fara zuwa ba a wannan lokacin, sai sun gamo sharholiyar su kafin suke dawowa cikin gidan idan dare ya tsala. Muka tarar da Hajiya Tasalla tare da wata matashiyar budurwar da fatarta ta sha bleaching har ta gaji ta yi jajir da ita duk fatan fuskar ya taƙushe waje guda tamkar an yi ɓarin garwashin wuta. Tun da na ɗaura idona akan ta na yi bugun zuciyata ya tssnanta. Har muka iso muka zauna ban ɗauke idona daga kan ta ba, muka gaisar da Hajiya ta amsa ta yi mana tayin abinci muka ce mun ƙoshi, haka nan kawai na ji zuciyata ta kasa nutusuwa don haka na tashi zan shige ciki. "Hajiya ko wannan ce wacce tsautsayin ya faɗa mata?". Cak na tsaya bisa sauƙar furucin a na'urar naɗan sautina. Kafin na waigo na ji Hajiya ta ba da amsa da faɗin"uhmm! Ke dai ki bari kawai ita ce ina gaya miki". "Hajiya ita ce Ramlatun?". Na watsa mata tambayar hawaye suna ciki mini koramar idanuna. "Ita ce, ita ma tun da tazo take tambayar ki". Take na ji jikina ya soma rawa duk yadda naso na furzo da zancen da yake ci min rai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan. Jikina ya ci gaba da rawa ƙafafuna suka nuna gazawar su wajen ɗaukar nauyina sai da Amira ta taso ta riƙe ni, na fizge jikina na shiga ɗaki da gudu. Shirij na zube akan katifa ina kuka tamkar raina zai bar gangar jikina. Na ji an dafo kafaɗuna haɗe da cewa"Amatullah kike ko wace ce?". Na ya banza da ita ba tare da na ce da ita komai ba, hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Hajiya ta sanar da ni duk abin da ya faru kuma na ji baƙin ciki matuƙa musamman da ta sanar da irin kamun kanki da ƙoƙarin ki wajen ganin kin killace mutumcin kanki da kiyaye kima da martaban gidanku. Ki ɗaga hannu ma ki godewa Allah da ya kasance ba ke kika kai kanki ba ƙaddara ce ta faɗa miki wacce ba ta wuce ranar ta. Ko kin zo gidan nan ko ba ki zo idan Allah ya nufa faruwan hakan babu makawa sai ya faru a gare ki, Mus'bahu cikakken namiji ne na tabbatar ke ma kin ji daɗin kasance da shi...". Kalamanta na ƙarshe suka daki zuciyata tare da baƙa mini ruhina. Na yi zumbur na tashi na zauna tare da buge hannunta daga jikina. "Ki na matsayin mace kike furta wannan maganar? Shin ko kaɗan ba ki ji tausayina ya ɗarsu a cikin ranki ba? Wallahi don babu yadda na iya ne ba ni kuma da wani zaɓi balle mafita amma da tunin na daina zuwa gidan nan. Ba zan ce da ke komai kuma ba zan nema jin wani abu daga gare ki na yarda ƙaddarata ce ta zo a haka kuma ina neman sauƙi a wajen wanda yake da ikon sausauta lamurana". Tun da na soma maganar take kallona har na akai aya, ta yi dariya ta ce"ba nufi na baƙanta miki rai ba ne baiwar Allah. Sai dai zan so na yi miki wata tambaya guda, a yadda kike da diri da kyawun suran nan ki na nufi babu wani na mijin da ya taɓa kusantark....". "Ki tashi ki fita tun kafin na idanuna su rufe na illata ki ko kuma na yi miki raunin da har ki koma ga mahaliccinki ba zai bar jikinki ba". Ya miƙe tsaye ta riƙe ƙugu tana ƙare mini kallo kafin can ta ce"zan fita kamar yadda kika buƙata, amma kafin na tafi zan ba ki wani shawarar da nake da yaƙinin cewar za ta amfane ki. Na ji an ce kina neman Mus'bahu to ba za ki taɓa samun sa don na tabbatar tun ranar da ya aikata wannan abun ya haɗa jakarsa ya bar garin nan wataƙila yanzu ba ya ƙasan nan". Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ta bar ni da sakin wani gigitaccen kuka mai raunana zuciyar mai saurare. Ban gushe ina yi ba Amira ta shigo ta dinga rarrashi na, na amshi wayarta na soma karatun aƙur'ani da shi sai da dare ta raba kana na ajiye wayar na yi dogon addu'a na shafa a nan wajen bacci ya yi nasarar ɗauka ta sai dai ban yi nisa ba na farka a zabure. "Lafiya kuwa?". Amira ta jefa mini tambayar cikin damuwar da ya bayyana har a cikin furucinta, maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kuka. "Amira an ya ba haukacewa zan yi ba kuwa ni kam?". Cikin sanyin murya ta soma cewa"babu abin da zai faru da ke in Sha Allah". Ta jawo ledar kayan da Mansur ya kawo ta fito da kayan ciki kayan marmari ne sai kuma wasu manyan cakuleti masu sanyi sa'annan lemonka gora har kala biyar. Ta matsa mini akan sai na ci wani abu ba don raina ya so ba na sha lemon da wasu daga cikin kayan marmarin. Washe garin ranar a islamiyya Malam Suleiman ya aiko aka ƙira ni ya zaunar da ni ya dinga yi mini nasiha tare da ba ni wasu shawarwari, ban iya daurewa ba har sai da na zubar da ƙwalla. Ko da a fito daga wajen Malam Suleiman lokacin har an tashi ban ga su Rauda da Ammi don daman sun ce daga islamiyyar wajen ɗinki suka nufa za su je su karɓo ɗinkin ankon waliman. A hankali nake tafiyar tamkar wacce take jin tsoron taka ƙasa na fito daga cikin islamiyyar, zan tsallaka titi na ji an ƙira sunana na waiga da sauri. "Yaya Alhassan". Na furta kalmar cikin mamaki don ban yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba. [10/24, 10:06 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 3️⃣5️⃣ Da saurina na iso inda yake tsaye a jikin mashinsa ɗin tare da wani abokinsa da tun ina tahowa idanunsa yake kaina har na iso wajen bakina ɗauke da sallama. Suka haɗe baki wajen amsawa kana na gaishe su suka amsa. "Kun tashi kenan?". Na gyaɗa masa kaina ina zarcewa da faɗin"daman ma ina so na je gida wajenka na ba ka haƙuri akan abin da ya faru game da waɗannan kaya...". Ya yi saurin ɗaga mini hannu alamar ba ya son sauraren ragowar zancen. "Abin da ya faru ai ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye faruwarsa a gaba, na ji wai ba ki da lafiya tun lokacin nake so na zo na duba ki amma ina gudun abin da zai je ya dawo shi yasa ma ban zo ba, shi ne na zo islamiyya. Me yake damunki ne haka Amatullah? Duk kin rame kin faɗa tamkar ba ke ba, me ya yi zafi haka?". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na sama zarafin faɗin"zazzaɓi ne kawai sai kuma yanayin karatu". "Amatullah kar ki faɗi saɓanin abin da yanayin fuskarki ya riga ya nuna. Tabbas akwai wani abun da yake faruwa ko in ce akwai abin da yake damunki". Na yi shuru ba tare da na ce komai tare rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. "Alhassan don Allah kar ka yi sanadin zubar hawaye daga fuskar wannan kyakykyawar halittan". Furucin abokinsa kenan ya ƙara sausauta amon muryarsa ya ci gaba da cewa"ƙanwata me yake damun ki?". Na ɗaga idona na yi masa kallo guda na janye a hankali na ce"babu komai". Yaya Alhassan ya amshe zancen"shikenan ba zan matsa miki amma ko ma mene ne ina miki fatan samun mafita cikin gaggawa, ranar yaushe ne walimar takun". Na yi murmushin ƙarfin hali"gobe ne da ƙarfe tara na safe". Ya jinjina kansa"me kike so na taho miki da shi, tun da Umma ta hana ni yin wancan aikin alkhairin da na yi niyya". "Zuwanka ma kaɗai ya wadatar da ni ba sai ka zo mini da komai ba". Ya tsuke fuskarsa"idan ba za ki faɗa ma ba ai kuwa duk abin da na yi niyya shi zan saya na kawo miki, in ya so in kin ga dama inna ba ki ki watsar ko ki kyautar wannan kuma ra'ayinki ne". Na saki taƙaitaccen murmushi"to shikenan na bar maka zaɓi duk abin ka taho mini da shi ina maraba da shi". "Ni ma da za a yi na'am da nawa kyautar da na yi " Furucin abokinsa kenan da ya sani ɗaga idona na yi masa kallo guda na mayar da idanuna. Na kawar da maganar ta hanya cewa"yaya Alhassan don Allah ka sanar da Anty Zulaihatu ma don ban sanar da ita ba". Ya riƙe haɓa"ai duk dangi babu inda ban shelanta cewar ƙawata ɗaya tilo za ta yi sauƙa ba. Don haka ki kwantar da hankalinki gayya guda za ki gan ma ranar, yanzu dai ga wannan ki wuce ki hau abin hawa ki wuce gidan na ga magriba tana kawo kai". Ya ƙare zancen yana miƙo mini naira ɗari biyar ɗin da ya zaro daga cikin aljihunsa, na amsa tare da yi masa godiya sai da na tsallaka titi na shiga napep kana na ga sun tafi. Ina sauƙa a layinmu na hango Amira tsaye da Bashir a ƙofar gida duk suka zubo mini na jiyamunsu, na sa kai zan shige cikin gida tamkar ban gan su ba Amira ta dakatar da ni. "Amatullah ba ki ga kin yi baƙo ba ne?". "Amira don Allah na gaji don Allah ki bar ni". Ina ƙare zancen na shige ciki ta rufa mini baya tare da shan gabana. "Me yasa kike haka ne Amatullah? Ai ko ba za ki ce da shi wani abu ba ya dace ki saurare shi ki ji da abin da yake tafe. Wanda ya damu da ke da halin da kake ciki da ai a tunanin ya wuce wulaƙanci a gare ka". "Wai da wani yare kike so na yi miki bayani ki fahimta ne? Na gaya miki ba na son ganin wani alaƙa ta ƙara haɗa da wani ɗa na miji ko da kuwa ta gaisawa ce matuƙar shi ɗin ba wai ya kasance muharramina ba ne". Na yi zancen ina ƙoƙarin wuce ta riƙo hannuna gam ta riƙe. "Kar ki manta fa ke kika ba shi dama. Kar ki zama mai ƙarya alƙawari mana". Na ɓanɓare hannunta daga jikina"ki je ki ba shi haƙuri don ba zan iya sauraren sa, ina ji a jikina ma kamar wannan ce haɗuwar mu ta ƙarshe da shi". Ban jira abin da za ta ce ba na ya wucewa ta ciki kai tsaye na nufi ɗakinmu bakina ɗauke da siririyar sallamar. Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Umma da na iske zaune a falon tana irga wasu kuɗaɗen masu yawa, ba ta amsa mini na har na gaji da tsayiwar na tashi zan shiga ɗaki kana ta yi magana a gajarce. "In kin shiga ɗaki akwai saƙon ki akan katifa". "To". Na amsa dashi duk da kuwa ina buƙatan ƙarin bayani sai dai sam ban ga fuskar yin hakan ba. Na wuce cikin ɗakin ina shiga fige hijabina na ajiye na suri ledar da na gani akan gado na buɗe. Hijabi ne a ciki sai kuma ɗinkin doguwar rigan da aka watsawa stone ya fito ya yi ɗasar da shi, wani ihun daɗi da farin ciki na saka a lokaci guda ina faɗawa kan gadon ina tsalla tsabar murnar da na tsinci kaina a cikin sa. Na rumgume hijabin ina ta washe haƙwara tamkar wacce aka biyawa kujerar hajji, tabbas Umma ta faranta mini don na daɗe da cire tsammanin cewa zan yi ankon hijabi da atamfar walimarmu tun bayan abin da ya faru lokacin da Yaya Alhassan ya kawo mini waɗannan kayan. Sai da na ƙarishe murnata na fito na yi wa Umma godiya bakina har kunne, rabon da na tsinci kaina cikin makamamcin irin wannan farin cikin tun kafin wannan iftila'in ya faru da ni. Sai dai kalaman da ta tare ni da su suka sanyaya mini jikina matuƙa. "Ki dai maida hankali akan karatunki sosai da sosai. Daga ni har mahaifinki mun yarda da ke ne shi yasa muka tura ki wanga islamiyyar, Amatullah...". Kafin ta ce wani abu na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta yi sakake tana kallona kamar ba ta taɓa ganina ba. "Kukan kuma na me ye ne? Ki tashi ki ba ni wani waje idan ba za ki rufe min baki ba". Haka na ci gaba da kukan har aka yi ƙiran sallan magriba tun Umma tana mamakina har ta tashi ta bar ni wajen. Na tashi da ƙyar na je na yi alwala na dawo na gabatar da salla tun kafin na yi iddar nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin riƙe ni. Ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cike da shauƙin abin da nake karanta haɗe da sanin fassaransa, haka kawai ranar na tsinci kaina cikin wani irin matsanancin kwanciyar hankali

Chapter 20 of 24