Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta juya ta fita hakan ya ba wa Amira daman faɗin"yanzu dai ki tashi ki je ki cire kayanki ki zo mu yi wa Mansur girki, don ya kusa isowa". Ban iya amsa mata da kalmomin baki ba illa gyaɗa mata kai da na yi na tashi na fita. [9/29, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 2️⃣3️⃣ Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka nake ɗaga ƙafafuna da ƙyar tamkar wacce ke tsoron taka ƙasa, kamar daga sama na ji an jawo hijabina ta bayana ya zarge mini wuya har sai da tari mai ƙarfi ya sarƙafe ni. Babu shiri na waiga don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni bayan na yi kici- kicin fizge hijabina da aka damƙe. Na yi turus ganin Ummi tsaye a bayana ta sha ɗamara a ƙudunta tana cika tana batsewa kamar saniya za ta kai bugu, sai da na yi ƙoƙarin daidai nutsuwa da numfashi da yak tsaya mini a ƙirji kafin na iya harhaɗo kalmomin da bakina ya furta cikin tsananin takaicin da ta yi sanadiyar cusa mini. "Ummi lafiya? Me ye na yu miki haka?". Ta galla mini wata uwar harara kafin ta furta"aw! Wai har kin manta kenan? To ba ri na yi miki tuni wallahil azim duk wanda ya ci tuwo da ni sai na tabbatar masa da cewar miya ya sha, tun da har kika yi kuskuren shiga cikin gonata sai kin yi kuka da idanunki". Raina ya harzuƙa zuciyata ta soma tafasa take jikina ya soma rawa saboda tsabar ɓacin rai da kalamanta suke jefa ni, idanuna suka soma cikowa da ƙwalla. "Ummi magana ta riga da ta mutu a tsakaninmu, don haka ki bar ni haka na sarara. Babu ni babu ke babu ruwan biri da gada". Ta tafa hannu gami da tsarin shewa kafin ta ce"ai kuwa magana tana nan daram har sai zuwa lokacin da na rama irin ɗiban albarkan da kika yi min a cikin gidan". Na buga tsaki na juya zan tafi ta koma cakumo ni daga lokacin da Abbanmu da Baba Habu suka shigo cikin gidan suka buga salati kafin Abba ya nema jin ba'asin abin da ya afku, na kwashe komai na sanar da shi. "Yanzu ke Ummi tun da an gama magana me ye amfanin tayar da shi yanzu?". Tambayar da Baba Habu ya jefa mata kenan kafin ta amsa Ummanta ta yi caraf ta amshe zancen. "Ko sama da ƙasa za ta haɗe sau Ummi ta ɗauki fansar abin da Amatullah ta yi mata". Kansa kawai Abba ya yi kafin ya furta"Uwata wuce ɗaki, ga salla ma yanzu ake ƙira". "To Abba". Na amsa da shi a taƙaice ina jin wani takaicin a cikin raina da ta tokare mini ƙirjina. Ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba yayin da nake shigewa ɗaki kai tsaye na wuce na je na sauya kayana, na fito na ɗau alwala na zo na yi salla. Sai a lokacin na lura da cewa Umma ba ta cikin gidan don haka na wuce wajen Amira ta ɗauke fuskana na yi mur don ba na so ma ta tare ni da wani zancen, tare muka fara aikin abincin da ita fried rice muka yi da soyayyar kazar da muka yi mata miya ta sha kayan lambu. Haka muka yi muka gama duk jikina babu ƙwari kuma na ƙi ba wa Amira fuskar da za ta yi mini wata tamnayar. Ina zaune a ɗakinsu ina latsa wayarta ta shigo ta dire plate ɗin abincin da ta shigo da shi a gabana, tare da fizge wayar tana faɗin"to Madam Bismillah mu ci abinci". Na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na sama zarafin cewa"wallahi kin ga ni kam ko yunwar ma ba na ji". Ta watsa mini harara"saboda me ye?". Kafin na ba ta amsa ta ɗaura da faɗin"kin ga Amatullah in zan ba ki shawara ki ɗauka to tun wuri ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Kar ki je ki ja wa kanki wani matsalar na daban akan wasu mutane can daban, yanzu dai ki daure ki ci abincin sai mu yi magana daga baya". Ban ce da ita uffan ba na saka hannu muka soma cin abincin har muka gama ban yi magana ba, duk da yadda take ta ja na da ita, da uhm ko umm kawai nake amsa mata wani sa'ilin kuma na saki taƙaitaccen murmushin da iyakar sa leɓena. Haka muka gama cin abincin na baro ta akan za ta shiga wanka don sun yi waya da Mansur ya ce ya ma shigo garin, wajenta kawai zai nufa. Sakakken ajiyar zuciya na sauƙe lokacin da na shigo ɗakinmu na iske har yanzu Umma ba ta dawo ba wanda ban san inda ta je ba, alwala na fito na yi na koma na yi salla ko da na iddar na gaza tashi daga inda na yi sallan na zaune na zagba tagumi da hannu bibbiyu tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta. "Uwata lafiya kuwa ina ta sallama ki zauna kin yi tagumi, ko amsawa ba ki yi ba?". Tamkar a cikin mafarki na tsinkayo amon Abba a tsakiyar kaina, da hakan ya tilasta mini cira kaina ina dubansa na miƙe na amsa baƙar ledar da ya shigo da ita ina yi masa sannu da zuwa. Na kawo masa ruwa ya sha kana na ce"ba ri na ɗaura maka girki kafin Umman ta dawo". Ya yi saurin faɗin"ba na jin yunwa sai dai ki dafa iya cikinki, Ummanki kuma na san ko ta dawo ba lalle ba ne ta ci wani abu". Tsimi-tsimi na koma na zauna kusa da ƙafafunsa tare da sadda kaina ƙasa, shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin Abba ya kawar da shi ta hanyar faɗin"walimar sauƙanku tana ta gabatowa ko?". "E akwai ƴan kwanaki ma yanzu kam suka rage". Ya yi ɗan jim kafin ya ce"kuma za ku yi wasu hidimomi ko?". "Hijabi ne kawai sai ankon da za mu yi. Kuma Umma ta ce za ta yi mini hijabin". "In Sha Allah kafin lokacin ma zan yi iya ƙoƙarin na ga na yi miki ankon, su makarantar takun me ye suke shirya muku na ga ana gayyato mutanen". Sai da na haɗiye wani miyau mai kauri daga bushashshen maƙoshina kafin na sama lasisin faɗin"Sheikh Dawood za a gayyato". Tun kafin na gama maganar ya tari numfashina"kai! Ai kuwa ya zama dole na halacci wannan taron nakun ko don na yi ido huɗu da Sheikh Dawood. Amma gaskiya sun yi ƙoƙari da suka gayyato shi don a malaman yanzu da wuya a sama kamarsa, mai ƙoƙarin hidimtawa addini da ziyartar duk wani wajen taron addini". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na yi shuru kamar wacce ruwa ya cinye ta. Ban ƙara cewa komai don na gaza samun abin da harshena zai sarrafa. Sallamar Amira shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga duniyar tunanin da na yi nisan ciwo a cikinsa, na amsa mata kana ta shigo ta durƙusa har ƙasa ta gaida Abba tare da yi masa bayanin zan raka ta ƙofar gida ta amsa saƙo. "To kar dai ku daɗe kuma ku lura, ni ba na son wannan hirar daren nakun wallahi". Amira ta fashe dariya har da rufe fuskarta saboda kunya kafin ta ce"Abba saƙo ne kawai za mu karɓa". Ya murmusa tare da cewa"to na ji, Allah ya kiyaye sai kun dawo". "Amin mun gode". Muka haɗe baki wajen amsawa kana muka tashi muka fita a zaure muka dakata ina ƙarewa Amira da ta sha doguwar rigar shuɗin kamfala an mata wani masifaffen ɗinkin da ya fito da duk wani suran jikinta. Ta kashe ɗaurin ture ka ga tsiya yayin da ta watsa sumarta zuwa bayan wuyanta. "Ma sha Allah! Wallahi kin yi kyau kamar a sace a gudu. Anya kuwa in Mansur ya ganki zai iya motsawa". Cike da matuƙar jin daɗi ta yi fari da idanunta gami da buga tsalle. "Na gode ta kusa da ran". Ta amsa da shi tana jan hannuna muka fita wajensa, yana tsaye a inda ya saba tsayuwa inda ya zo a jikin motarsa da duk da duhun dare hakan bai hana sheƙin da take yi ɗaukar ido ba. Da sallama muka isa wajen bai amsa ba illa kafe ta da idanu da ya yi wanda ita ma ɗin shi take kallo. "Barka da fitowa tauraruwata hasken idaniyata, filitar dake haskaka birnin zuciyata da kewaye. Na yi kewarki yadda ba ki ba zai iya misaltawa ba, wasu lokutan har ji nake yi kamar na yi tsuntsuwa na zo don kawai na gan ki sai dai hakan ba mai yiyuwa ba ne". "Ni ma nan kullum da kewarka nake kwana kuma nake tashi a cikin raina Masoyi". Na naɗe hannayena tsam a ƙirjina ina kallon su"to masoya tun da ba a gani ba babu amfanin tsayiwata a wajen. Don na ga alama iya junanku kawai kuke gani". Murmushi Mansur ya yi yana haɗe hannayensa waje guda alamar ban haƙuri. "Afuwan ranki ya daɗe, mun yi kewar juna ne irin sosai ɗin yadda baki ba zai iya furta wa ba". Na taɓe baki ina cewa"to har shekara dubu nawa kuka yi ba ku ga juna ba?". "Ai duk kwana guda jin sa muke yi tamkar shekara muka yi ba mu ga juna ba". Amira ta yi furucin fuskarta tamkar gonar auduga. "To sannu masoya yanzu kam ai ga ki ga shi. In kun ga dama ma ku cinye juna ƙarshen soyayya". Dukkan su suka tuntsire da dariya kamar waɗanda aka ba su wankan gardi, sai a lokacin muka sama damar gaisawa da Mansur na yi masa sannu da dawowa mun ɗan taɓa hira na wani lokaci kafin na ce zan shiga ciki, Amira ta yi tsalle ta dige akan babu inda za ni. Dole na tsaya ba don raina yana so ba jifa-jifa nake soma baki a cikin hirar tasun kafin can na hango Umma ta doso gida. Da alama ba ta gan mu ba don kai tsaye ta wuce cikin gidan ba tare da waiwaye ba. "Amira kin ga Umma ta dawo bari na wuce gida". Ta galla mini harara"babu inda za ki je yadda muka fito tare to haka za mu koma. Sai ka ce cizon naman jikinki ake yi a nan ɗin". Ban ce komai ba illa murmusawan da na yi, ba su ja hirar da yawa ba don hatta shi kansa Mansur ɗin ya fahimci cewar na ƙosa na bar wajen, ya zagaya ya buɗe bayan motarsa ya fito da wasu manyan ledodi biyu ya zo ya dire su a gabanmu. "To Babe ga tsarabarki". "Ranka ya daɗe ba na so ka na wahalar min da ajihunka". Amira ta yi zancen cikin karya harshe da sausauta amonta. "Rufe idonki ki miƙo min hannunki". Mansur ya furta a dake don kar ma ta kawo masa wargi. Kamar yadda ya buƙata hakan ta yi, ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali. Ya ciro wani kyakykyawan agogo daga ajihunsa ya ɗaura mata a hannunta kana ya ce ta buɗe idonta. Ta cika da farin ciki da murna yayin da ta ya tozali da agogon ta dinga jeranta masa godiya wani na bin wani ni ma ina taya ta. Haka suka yi sallama ya tafi mu kuma muka shigo gida kai tsaye na wuce dakinmu don haka kawai na ji ƙirjina yana bugawa fiye da kima a kimiyance. Babu kowa a falon don haka na wuce uwar ɗaka na yi turus bisa tozali da mummunan ganin da na yi, take ƙafafuna suka soma rawa suffa ta soma keto mini daga dukkan mafitan gashin dake jikina. [9/30, 7:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 2️⃣4️⃣ Tabbas indai ba idanuna ne suka sama matsala ba ko kuma suka daina aikin su yadda ya dace, to babu shakka Umma na ga ni tana tsaye a kan Abba da yake kwance a bisa gado yana bacci huce gajiyar da ya kwaso, ƙaramin almakashi ne a hannunta tana yadda gashin gemunsa tana zubawa a cikin wani kwalba. Ban yadda ta ganni ba na yi wuf na koma don da farko ban ya ma tunanin cewa Abba yana cikin ɗakin ba da ba zan shigo ba, zama na yi a ƙasa dirshan na tallafe kuncina yayin da numfashina yake sarƙafe mini a ƙirjina, zuffa ya soma jiƙa miji jiki lajaf tamkar wacce aka juyewa bokatin ruwa a kanta. Na dulmiye cikin kogin tunanin dalilin abin da Umma take yi, sannan me ye za ta yi da gashin gemun Abba da take yadda take sanyawa cikin wannan kwalban?. "Amatullah". Na tsinkayo muryar Umma a tsakiyar kaina, na yi figigi na miƙe tsaye ina goge ƙwallan da ya ɓata mini fuska wanda ban san lokacin da suka zubo ba. "Ki samo min garwashi". "Umma ai ba a hura wuta ba ma. Amma me ye za ki yi da garwashi a daren nan?". Kallon da ta tsare ni da shi ya sanya ni rusunar da idanuna ƙasa jikina a sanyaye tamkar jinjiran kazar da ruwan sama ya yi wa ɗan banzan duka. "Ba na son yawan tambayoyi ki wuce kawai ki nemo min abin da na buƙata". Ban kuma cewa komai ba na fice jikina gabaɗaya babu kuzari kamar wacce aka zarewa laka. Ko da na fito na gaza assala komai na tisa munkubarin a gabana na zagba tagumi tunani kala-kala babu wanda bai kawo wa ƙwaƙwalwata ziyara ba. "Ƴar uwa lafiya kika zauna kika zagba tagumi haka?". Babu shiri na ɗago kaina saboda ba kaɗan ba sauƙar furucin a ƙofofin kunnuwana ya razana ni, Anty Amarya ce matar ustazu Abdulwahab ta yi maganar tana tsaye kusa da ni. Ganin ban amsa mata ba ya sanya jan kujera ta zauna kusa da ni tana ƙara faɗin"ko dai akwai wata matsalar ne wanda kike ganin bai dace kowa ya sani ba, ba zan matsa miki sai kin faɗa min sirrin zuciyarki ba amma in Sha Allah zan taya ki addu'a. Allah ya kawo miki mafita ta inda ba ki taɓa zato ba balle tsammani". "Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice kasancewar tun da suka shigo gidan ba mu taɓa wani dogon magana da ita da ya wuce gaisuwa ba. Har ta tashi za ta tafi na yi hanzarin dakatar da ita ta hanyar faɗin"don Allah na ga kamar girki kike yi ko?". "E girki nake yi yau na yi dare ban gama ba". "Don Allah garwashin wuta nake so ko guda biyu ma. Za mu sa turaren wuta". Ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kafin ta ce"ba damuwa ina kaskon na zuba miki". Na ji kamar an sauƙe mini wani ƙaton dutse daga kaina, na tashi da sauri na shiga na ɗauko mata kaskon na ba ta. Ta karɓa ta je ta ciko mini shi na karɓar ina ta zuba mata godiya kafin na yi mata sai da safe na shiga ciki. A falo na iske Umma na ajiye kaskon a gabanta. "Umma ga garwashin". Ba ta tanka mini ta ɗauka ta shiga cikin uwar ɗaka, babu jimawa ta fito mini da abun shimfiɗi ta ce na yi shimfiɗi na kwanta a falon na amsa tare da yi mata sai da safe wanda ba ta ko amsa ba ta yi shigewarta ciki. Shimfiɗi na yi na ɗauko alƙur'ani da tocila a kusa da ni na zauna, sosai na mayar da hankalina kacokam ga karatun don so nake yi na hana kaina faɗa cikin tunanin da yake addaban kwanyata. Na daɗe ina karatun don aƙalla na yi awa guda ina yi ban gushe ina yi ba har sai da na yi wani sanyi ya soma ratsa sashin ruhina kana na rufe alƙur'anin. Na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zamo shamaki tsakanin ganina da sararin samaniya, ajiyar numfashi na koma sauƙewa wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai tunanin abun da na ga Umma ta yi shi ya tsaya mini a rai kwatankwacin yadda ƙayan kifi yake tsayiwar ƙiƙam a maƙoƙaro. A bayyane na furta"Ya Allah ina roƙonka tare da tawassali da sunayenka tsarkaka guda ɗari ba ɗari da ka shirya mini Ummata ka dawo da ita kan hanya madaidaiciya mai ɓulewa. Ka kuɓutar da Abbana daga dukkan abin da take shiryawa ka kuma tsaretar da shi daga dukkan ƙullin da take ƙullewa". Cikin wani irin yanayi na mutuwar jiki na ƙare zancen ina jin wasu tsiraran hawaye masu ɗumi suna bin gefe da gefen fuskana. Haka na ƙarar da kusa rabin daren ban runtsa ba abubuwa da dama sun taron sun yi mini yawa sai da na yi sallan asubahi kana na sama runtsawa. Hayaniyar da nake ji kamar a cikin mafarki shi ya yi silar farkawa na ba don baccin ya ishe ni ba. Na soma buɗe idona a hankali kafin na buɗe sa tar ina ƙarewa ɗakin kallo, tashi na yi na zauna ina murtsike idanuna tare da ambaton addu'ar tashi daga bacci kamar yadda addinina ya tanada. Ƙananun maganganu nake yi suna tashi daga ɗakin wanda ina da tabbacin Abba da Umma ne suke magana, numfashi na sauƙe mai karfi kafin na tashi na soma tattare shimfiɗana. Don na yi wa kaina alƙawarin indai ba bisa kuskure ba ba zan taɓa sauraron zancen da suke tattaunawa a tsakaninsu ba, ko da kuwa ya shafe ni. Tattare falon na yi tsaf na yi shara na kimtsa ko'ina na fito na haɗa wuta na ɗaura farar shinkafa, ina girkin ina duba alƙur'anina ina ƙara tisa karatun da aka yi mana jiya. A haka Amira ta zo ta same ni ba ta katse ni ba har sai da na kai ƙarshen ayan da nake karantawa na rufe ƙur'anin, kana muka gaisa da jin lafiyar juna. "Wannan ledar fa?". Na jefa mata tambayar ina jawo ledar da ta ajiye a gabanta na soma buɗewa, atamfa ne guda biyu da sarƙa da ɗan kunne. "Wai har kin manta kenan? Tsarabar da Mansur ya kawo ne". Na yi mata kallo guda ina fiddo da atamfar ina ƙare musu kallo. "Ai kuwa ga su ma sha Allah! Allah ya saka masa da alkhairi ya ƙara buɗi. Amma dai wannan ɗawainiyyar ta yi yawa kar ki manta fa ko gabatar da kansa bai yi a gaban magabatanki ba". "Amin! Matsalata da ke kenan ba a yi miki gwaninta ko kaɗan. Bawan Allahn duk ƙoƙarin da yake yi a kaina in ba a sa masa albarka ba ai bai dace a kushe sa ba, ke yau da safen nan ma da muka yi waya cewa ya yi na kusa na daina fita wannan tallar sai ɗauka dukkan ɗawaniyyata da ta mahaifiyata". Babu shiri na ware dukkan girman idanuna a kanta tare da sake leɓɓe ina bin ta da kallon mamaki, kafin na yi magana muka jiyo sallamar Anty Sawwama da hakan ya tursasa mini haɗiye zancen da na yunƙuro da nufin furtawa. Muka haɗe baki da Amira wajen amsa sallamar muna yi mata martaba da zuwa, falo muka shiga muka zauna kana muka gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da yalwataccen annurin da ya ƙara taimaka wajen fito da tsatsar kaman jinin da suke yi da Abbana. " Na yi muku sammako ko?". Na yi murmushi tare da girgiza kaina alamar a'a hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Ina son na yi magana da Abbanki ne shi yasa na yi wannan sammako don kwana biyun nan da damuwar nan nake kwana nake tashi a cikin raina. Ina dai suna ciki ko?". "Ga mu me ye muka yi ake nemanmu da wannan farar safiyar?". Martanin da Umma ta mayar mata kenan cikin kakkauran murya tana isowa cikin falon ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya. "Hafsatu kenan kun tashi lafiya, Mannirun yana ciki kuwa?". "Da ba mu lafiya ba ai ba za ki zo ki tadda mu haka ba. Manniru kuwa yana ciki amma na yanzu zai fito ba sai ki jira shi". Gabaɗaya ji na yi jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin zafin furucin da Umma ta yaɓawa Anty Sawwama. Fitowar Abba ya sani ɗago kaina ina bin sa da kallo har ya zauna haka kawai na ji tausayinsa ya cika mini raina ba tare da na san dalili ba. "Maman Umar ke ce tafe da safiyar nan? To ya gidan ya kuma yaran?". "Wallahi ni ce tafe gida da yara kuma duk lafiya lau. Daman na zo mu tattaunawa wata magana ne da kai shi yasa na yi sammako kar na zo na iske ka fita wajen aiki". Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta ce"su aiki manya, yo wannan aikin har wani abun ne? Aikin da ba ya tsinana masa komai shi kansa balle kuma wanda suke kewaye da shi". Ƙwalla suka ciko mini kurmin idaniyata cikin rauni na ce"don Allah Umma ki yi haƙuri mana". Amira ta riƙo hannuna tana faɗin"Amatullah mu je daga waje mu ba su waje su tattaunawa". Ban yi mata musu na tashi muka fita muna fita wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini na kifa kaina a bisa gwiwa ina rero sa cikin durshashewar murya. Duk ƙoƙarin da Amira ta yi na ba ni haƙuri da lallashina na gaza sarrafa kaina kukan ne kawai nake jin yana yi gaban kansa yana fitowa. Har sai da Ummanta ta fito ta nema jin ba'asin me yake faruwa Amira ta yi mata bayani ita ma ta lallashe ni sosai ganin ba ni da niyyar tsagaita kukan hakan ya sanya ta jan hannuna zuwa ɗakinsu, ta umarci Amira da ta ƙarisa girkin da na aza bisa wuta. Ko anan ɗin ma hawayen sun kasa tsayawa da ƙyar Umman Amira ta lallashe ni ta zubo mini wainar da take toyawa sai dai na kasa kai ko da loma guda cikin bakina. Haka har Amira ta zo ta iske ni . "Don Allah ki kwantar da hankalinki babu komai fa,Anty Sawwaman ma fa yanzu na ga ta fito za ta tafi". Na zabura na miƙe zan fice Amira ta riƙo hannuna ta riƙe gam" ina kuma za ki je?". "Zan je wajen ta ne kafin ta tafi mana". Ta gizgiza mini kanta"bai kamata ki je yanzu ba Amatullah. Idan maganar da suka tattauna ta shafe ki to ko ba ki je ba za a ƙira ki, amma tun da kika ga ba a neme ki to maganar ba ta shafe ki ba ne ta kowacce fuska". Cikin sanyin jiki na koma na zauna tare da buga wani uban tagumi, ganin yadda Amira ta dage ita da Ummanta wajen kwantar mini da hankali hakan ya sani dole na saki fuskata ba don na daina jin raɗaɗi da zogi a cikin raina ba. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya ishe ni har yunƙurin ƙiran Anty Sawwama na so yi da wayar Amira sai dai ban haddace lambarta a kaina ba haka dole ina ji ina gani na haƙura. Umma ta soma ƙwala mini ƙira tana shelanta mini na fito na gama dama kunnun, sai da na yi wanka na shirya kana na ɗauki tallan muka fito tare da Amira yayin da almajirin da yake tafiya mana da kayan ya yi gaba. Inda muka saba zama kamar kullum yau a nan muka yada zango, ba mu yi awa guda cikakken ba muka sayar da komai. "Bari na yi sauri na je na kai wa Naziru masarsa kar ki gaji da zaman". Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, taɓe baki na yi ina faɗin"ni yau gabaɗaya ma wallahi ba na sha'awar komawa cikin gidan nan. Don tashin hankalin cikinsa ya fi komai yawa". "To Amatullah ya ya za mu? Tun da ƙaddara ta jefo nan kam ai haka za mu yi haƙuri". Haka kawai na ji wani sanyi a raina da na hango Bashir yana nufo wajen har sai da na kasa haƙuri na fito da abin da yake raina, wanda ni ma kaina ban taɓa zato da tsammanin bakina zai iya furta makamancin irin wannan kalamin ba. "Yauwa! Ga can Bashir ma yana tahowa, za mu yi hira da shi kafin ki dawo don na lura mutumin akwai shi

Chapter 13 of 24