Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wulaƙanci ko ka ga alamar yunwa ko ƙishi a tattare da ita?. Ƴar iska mai baƙin hali ke kuma har da wani zama ki sadda kai ƙasa kina sauraronsa shegiya munafuka kawai". Tsam! Abba ya miƙe akan ƙafafunsa ya yi taku uku ya isa dab da Umma ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa yana cewa"Hafsatu kar ki ƙara cewa yarinyar nan ƴar iska balle har ki yi gangancin sheganta ta. Ki kiyaye ranar da za ki kai ni bango, na fara gajiya da halinki fa". "Manniru ban ga dalilin da za ka zaunar da ƴarta kana aibata ni a gabanta ba kuma na zuba ido na yi shuru. Wallahi ka yi tsararo". Cike da takaici Abba yake jinjina kansa"Hafsatu ki kiyaye harshenki Manzon Allah ya ce"kuffa alaika haza" ku kiyaye wannan a gare ku. Ki dinga tauna magana kafin kin furta ta domin masu iya magana sun ce magana zaran bunu ce in har ta fita ba a mayar da ita". Ya sausauta amon muryarsa kafin ya ci gaba da magana"na roƙi ki zubar da waɗannan halayen ki zo mu zauna mu ba wa ƴarmu ɗaya tilo tarbiyyar da ta dace. Na yi muku alƙawarin ba ku kula daidai ƙarfina samun aljihuna". Dariyar da Umma ta ba she shi ya sanya Abba dakata wa ba don ya gama bayyanar da takaicin da yake cikin ransa ba. "Alamar ƙarfi ai tana ga mai ƙiba Manniru. Na tabbatar ko zuciyar da take dashe a cikin ƙirjinka ba ta yarda da zancen bakinka ya furta ba. Yanzu kai ko wani ne ga tare ka a hanya ya ce kai Manniru za ka iya ɗaukar ɗawaniyyar iyalinka sai ka yarda?. A aikinka na maluntan ne za ka ɗauki nauyinmu?Shekarunmu nawa tare amma har yanzu ko gidan kanka ba ka mallaka ba ban da keke mai kake da shi a duniya?". "Ni kuwa nake da abubuwa da yawa tun da na rayu da imani da kuma ƙaunar ma'aikinmu. Ina da lafiyar da zan fita na nema halal ɗina ban taɓa aika wani abun alfasha ba. Ba na so muna musayan yawo da ke a gaban Amatullah don haka wani mataki ne na lalata mata tarbiyanta". Tsaki ta buga ta koma ɗaki ta bar shi tsaye a wajen. Hularsa Abba ya ɗauka zai fita na yi saurin cewa"Abba abincin fa?". Ba tare da ya kalle ni ba ya furta"lokaci ya riga ya ƙure zan tafi kar na yi latti". Yana dure zancen ya fice ya bar ni zaune cikin tarin damuwar da ya yi wa zuciyata katutu. "To ke kuma munafuka sai ki tashi ki tattare ɗakin kafin na gama dama kunnun nan ki fita da shi. Yarinya kamar ƴar gaba da fatiha tun da na haife ki ban huta ba har yanzu, oh! Ni kam ina ganin takaicin haihuwa". Ta yi maganar tana ficewa daga ɗakin. Dole na tashi na tattare falon kana na koma na gyara ɗaki cikin tashin kuzari, wanka kawai na yi na kora kokon da na damawa Abba wanda bai sha ba ya fita. Na fito waje na tarar da Umma zaune ta kammala komai na kunun. "Umma na fito". Ta ɗago kai ta ƙare mini kallo kafin ta miƙe ta ja hannuna muka koma falo ta shige ɗaki ta fito. Ta miƙa mini kwalli. "Ga shi kar ɓi ki saka sa a idanunki. Sannan ga can garwashi wuta ki ɗauko ki turare da shi". [7/12, 1:06 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 0️⃣7️⃣ Ban san lokacin da ƙwalla suka wadaci koramar idanuna ba sai jin ɗuminsu na yi suna shawagi a bisa kuncina. Ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba. Na haɗe hannayena wajen guda alamar roƙo kafin na sa magana cikin rawar murya da sarƙafewar harshe. "Umma don girman ki rufa mana asiri kar mu garin neman gira mu rasa ido, garin neman duniya mu faɗa cikin fushin Ubangiji, wannan abun fa kamar shirka ne. Don yana nuni da cewar ba mu yarda cewar Allah ne mai yi ba, ba mu yarda shi yake kawo kasuwa kuma ya buɗe wa bawa ƙofofin samunsa a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama ba. Umma na yi miki alƙawarin ko zan wuni ba zan dawo ba sai na sayar da wannan kunun". Tun da na fara maganar ta kafe ni da idanu tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta taɓe baki kafin ta soma faɗa a fusace. "Lalle wuyanki ya yi kauri ya isa yanka Amatullah, har ni za ki kalla tsabar idona ki ce zan jefa mu cikin fushin Ubangiji?. In don islamiyyar da kike zuwa ne ko kuma kina ganin kina dab da haddace alƙur'ani ya saki faɗa min waɗannan kalaman, to sai na hana ki zuwa ko'ina. Ko Allah ma ai ya ce tashi na taimake ka ba zai taɓa yiyuwa kana daga kwance ka ga kuɗi suna zubowa daga rufin ɗakinka ba dole sai ka tashi ka neme su. Da ke gwara ƴar zina sam ba kya tausayina balle mu haɗa kai mu samarwa kanmu mafita. Ni kam ina ganin takaicin haihuwa". Haƙiƙa kauraran kalamanta sun yi nasarar narkar mini da zuciya har su yi sanyaya mini dukkan gaɓoɓin jikina. Kaina ya ɗauki zafi kamar garwashin dake ƙasan tukuban tsire. Kafin na yi magana na tsinkayo amon muryar Anty Sawwama babbar ƴar Abba da take kusa da mu. Na waiga ina kallonta daga yanayin fuskarta na fahimci ta ji abin da Umma take faɗi. "Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Yanzu Hafsatu haka abin nakin ya girmama har ta kai ta kawo ki titsiye ƴar cikinki kina jifan ta da irin waɗannan mummunan kalaman? Kar ki manta ke ba uwa ce DAFIN HARSHEnki yana da matuƙar tasiri akan ta kamar yadda duk addu'ar da kika yi mata Allah zai amsa ta don babu hijabi tsakanin addu'ar uwa da Ubangiji". Ta gyara ɗaurin zaninta kafin ta ci gaba da faɗin"tabbas sai yau na ƙara yarda da cewar babu butulu kamar ɗan Adam shi ne mai manta alkhairi cikin ƙiftawan ido. Ashe Hafsatu kin manta tsawon shekarun da kuka shafe da Manniru a matsayin ma'aurata kafin Allah ya azurta ku da samun Amatullah?. Kin manta wahalhalun da kika sha a yayin goyon cikinta har zuwa lokacin haihuwarta wanda dalilin hakan aka cire miki mahaifa gabaɗaya?. Waɗannan dalilai guda biyu ba su isa su sanya zuciyarki karaya ba ba su isa su dasa so da ƙaunar Amatullah a cikin ƙirjinki ba tun da kin sani na sani daga ita ba za ki ƙara haihuwa ba a duniya, amma don kin cika cikakkiyar butulu mai mance ni'imar da Ubangiji ya lulluɓe ta da shi har kike buɗe baki ki ƙira da ita gwara ƴar zina. Hafsatu ina guje miki ranar ƙin dillanci ranar da ido za ta raina fata. Wannan harshen da muke rainawa wallahi yana da tasiri akan ƴaƴanmu". "Maman Umar ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ki wanko ƙafa ki zo har cikin gidana kina gaya min abin da ya dace na yi ko wanda zan bari ba. Ke fa bakinki kika furta na sha wahala a lokacin rainon cikinta har zuwa haihuwarta don haka kuwa kin ga duk wanda zai nuna mata wata soyayya a bayana yake". "Hafsatu nusarwa ce na yi miki, ke ɗin fa uwa ce duk abin da kika furta akan ta wallahil azim zai bibiyi rayuwarta ne. Kuma ko ba daɗe ko ba ji ma watarana sai abin da kika shuka ya yi tsuro kin girbe sa". Kallon uku saura kwata Umma ta watsa mata kafin ta juyo kaina"fita ki je ki ɗauki kunun nan ki wuce, idan Allah ya kaimu gobe za mu aiwatar da shirin mu". Tana dure zancen ta shige ɗaki ta bar mu a wajen, na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin na tsugunawa har ƙasa ina gaishe da Anty Sawwama. Ta yalwata annuri fuskarta kafin ta amsa da faɗin"lafiya ƙalau uwarmu maganin kukanmu. Baya goya marayu Allah ya sa ki yi gadon halin mahaifiyarmu wanda tun yanzu ma alamomin hakan sun bayyana. Kina da haƙuri da ɓiyayya Allah ya yi miki albarka". "Amin". Na amsa da shi ina sadda kaina ƙasa a ƙoƙarin tare hawayen idona kwaranya. "Ki je ki ɗauki kunun kar ta fito tun da kin fi kowa sanin halinta". Duk yadda na so tare hawayen idona zuba lamarin ya faskara ba tare da na yi aune ba suka fara gudun famfalaƙi a tsakanin kuncina da saman haɓata. "Anty zan dawo na same ki ko tafiya za ki yi?". Ta matso kusa da ni ta riƙo hannuna da hannunta ɗaya, yayin da ɗayan kuma ta soma share mini hawayen fuskana da su. "Za ki dawo ki same ni, don zan jira har mahaifinki sai ya dawo akwai maganar da za mu yi da shi". Kaina kawai na gyaɗa mata na zare hannuna na fita na ɗauki bokitin kunun da ragowar robobin na fita. Ina fitowa na tsaya a ƙofar gida ina kallon gabar da yamma kudu da kuma arewa. Na rasa wani hanya zan bi da sai sada ni nasara a safiyar yau. So nake yi na goge tunanin da yake cikin kan Umma na nuna mata cewar ko da laƙani ko babu idan Allah ya tsara zan sayar da kunun nan babu makawa sai na sayar ko da kuwa a ƙofar gida ne. Ganin tsayuwar da nake yi ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sani soma tafiya ƙirjina yana tsananta bugu. Sai da na fice daga unguwar gabaɗaya na fito bakin titin da ya rabu kashi biyu kudu da kuma arewa. Can na hango tawagar wasu masu talla sun haɗo kansu za su wuce na bi su a baya har muka isa wani babban fili da yake a bakin hanya kusa da wani sabon gidan mai. Suka zauna ni ma na nema waje na zauna bayan na ajiye tallana a gabana, duk suka zubo mini idanu kamar sun ga wata baƙuwar halittar da ta zo daga wata duniyar da ba namu ba. Tabbas wajen fuskar jama'a ne don tun da muka zaune ake ta sayan kayan mussamman awara da wainar fulawa su suka fi ciniki. Raina ya yi fari ƙal nauyin da yake zuciya a hankali na ji ya fara sauƙa kamar an jefa dutsin a cikin ruwa. Farin ciki ya mamaye ni ganin a ƙasa da mintuna talatin na yi cinikin dubu da ɗari biyu. Farin cikin da yake fuskana ya soma dushashewa ganin sauran masu tallan sun yi cirko-cirko a gabana duk sun riƙe ƙugu fuskokinsu kamar a murtuƙe kamar hadarin da ya taso daga gabas. "Bayin Allah lafiya?". Na jefa musu tambayar bayan na haɗo jarumta na yafawa kaina, ɗaya daga cikinsu ta wurga mini wani mungun kallo har da tsirta da miyau kamar ta yi tozali da kashi. "Uban waye ya ba ki iznin kawo talla nan wajen?". Na ɗaya iso na yi mata kallo guda kafin na mayar mata da amsa"har sai an ba da izni kafin a kawo tallan? Na yi zaton fili ne kawai dajin Allah kowa ya kawo tallansa in ya sayar ya koma gida....". Kafin na rufe bakina ɗaya daga cikin da ta fi su fusata ta ɗauke da mari da ya sani jin hajijiya na ƙoƙarin buga ni da ƙasa duk da a zaune nake. Kafin igiyar firgicin marin ya gama sake ni sautinta ya dira a ƙofofin kunnuwana kamar sauƙar ungulu. "Ke har kin isa Zaina tana magana kina mayar mata, wane ne ubanki a cikin garin nan? Kuma waye ya tsaya miki a nan wajen?". Na dafe kuncina kafin na ce"laifina ne don ta tambaye ni na ba ta amsa?". Ta ƙara fusata ta nufo ni wata ta dakatar da ita. Cikin isa take faɗin"ƙyale ta Zulfa'u akwai buƙatar sai mun yi mata komai a aikace". "Zaina don Allah ki bar ni na koyawa wannan kucakar yarinyar hankali. Na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne". Wacce ta ƙira da Zainan na bi da kallo da ta yi musu alama da hannu akan a kawo mata kujera cikin sauri aka kawo mata ta zauna tana fuakanta na sosai. Tsawon wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba sai can ta soma magana a gadarance. "Ni ce shugaban masu kawo talla a wannan wajen kuma duk wacce kika gani a nan tana ƙarƙashin iko da isata ne. Ko kara na ajiye babu wacce za ta tsallake shi sannan kafin ki kawo talla nan wajen sai kin zo wajena na yi miki regista sannan a kowacce rana dole ki biya haraji ko kuma ki fuskanci hukunci mai tsauri". Ta dakata kafin ta doka mini tsawa"me ye kike sayarwa?". "Kamar yadda kike gani kunu nake sayarwa. Kuma duk waɗannan ƙa'idodin da kika gindaya ba za su aiki a kaina ba don daga yau ba za ki ƙara ganina a nan ba. An yi na farko kuma na ƙarshe". "Kunu? Wannan ne kunun?". Ta ƙarƙare zancen tana saka ƙafa ta yi kutubol da bokitin kununa. Sam na miƙe Zulfa'u ta doka mini wata tsawar, cikin ba da umarni ta ce"koma ki zauna ƙasƙantacciya, ke har kin isa Zaina tana zaune ki tashi tsaye ki tsaya mata akai". Na cire leɓena raina cike da takaici na bi su da kallon ɗaɗɗaya kafin na ce"ita ɗin wace ce da in zan tashi ko zan zauna sai na nema izninta, ko ba ki ga ɓarnar da ta yi mini ba ne? In ce dai talla ta zo kuma ni ma shi ya kawo ni don haka ba mu da wani bambanci. Kayana kuma sai an biya ni". Suka tashi gabaɗaya suka yi kaina suka cakumo ni kokuwa ya kaure a tsakaninmu. Kafin wani mutum ya zo wajen ya shiga tsakaninmu. Ya janye Zaina gefe guda tana tambayata abin da ya faru. "Allah ya ja zamaninka wannan yarinyar ce ta zo ta zauna ba tare da ta cike ƙa'idodi ba". Ya juyo yana kallona sosai"ke me yasa kika zo ba tare da kin bi ƙa'ida ba?". "Ni baƙuwa ce a nan wajen ban taɓa zuwa ba. Shi yasa ban da dokokin ba, maimaikon ta kawo hankali cikin fahimta sai ta sa ƙafa ta zubar mini da kununa". Na kai aya ina yi masa nuni da inda gabaɗaya kunun ya malale. Ya jinjina kansa yana ƙara kusanto ni har yanzu idanunsa suna kaina ya furta"ba a kyauta miki ba kam, ke Zaina me yasa da ta zo ba ki kawo ta wajena ba?". Sai da ta wurga masa harara kafin ta ce"na ga zan iya shawo kan matsalar da kaina ne, ba tare da mun je teburinka ba". "To yanzun kin shawo kan matsalar ne na zo na tarar da ku haka?". Ta waro idanu waje"Mai aska ni nake maidawa magana haka a gaban kowa? Ko ka manta waye ce a gaban ka?. Zaina ce fa tauraruwarka". "Zaina na gane ki mana akwai ina sanar da ke kuskuren da kika yi ne. Na sha gaya miki idan irin hakan ya faru ki dinga zuwa kina sanar da ni amma sam na fahimci ba kya jin abin da nake faɗa miki ba". Ta zabura ta kurma wani uban ihu kamar wacce aka watsawa garwashi ta yi kukan kura za ta cakumo ni ya tare ta ya riƙe ta gam. Amma duk da haka ba ta fasa kai mini duka ba. Ganin ba za ta tsaya ba ya sanya shi ɗauke ta marin da ya sanya kowa shan jinin jikinsa duk suka yi tsam kamar ruwa ya cinye su. "Ke Zaina ke wata iriyar mahaukaciya ce jaka kawai marar lissafi. Ana tare ki har kina wani ƙara dagewa sai kin yi, to ga ta ki duke ta na gani. Wallahi in har kika yi kuskuren ɗaura hannunki a jikinta sai na tabbatar da hakan ya zamo kuskure mafi girma da za ki yi a cikin rayuwarki". "Wayyo jama'a ku taimake ni ga annoba ta zo. Mai aska yau ni kake gayawa haka?". "Na gaya miki ɗin uwa ta ce ke? Na ce uwa ta ce ke da ba zan gaya miki magana ba?. Na baki mintuna goma ki tattara kayan tallanki ki bar nan wajen, kuma idan ba ki wasa ba har matsayin da na ba ki sai na ƙwace sa". Za ta yi wani maganar Zulfa ta hana ta, sai da suka rirriƙe ta saboda yadda jikinta yake karma kafin suka bar wajen. Maganar da ya soma yi shi ya dawo da ni duniyar zahiri. "Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke kyakykyawa da kyawun zubi gami da tsari. Mene ne sunanki?". "Sunana Amatullah". "Sunan ya dace da ke matuƙa. Shin ko zan iya sanin adadin kuɗin kunun da Zaina ta zubar miki, ina so na biya don na san hatta su kuɗaɗan za su yi farin ciki idan suka shiga hannun kyakykyawar mace kamar ki". Na ɗan yi jim don na fara tsorita da irin kallon da yake yi mini. "Ina fatan ba za ki hana ni aikata wannan aikin alkhairin ba. Ya ke tauraruwa mai haske duniya". Tuna jarfan da zan tarar da gidan idan na koma a haka babu kuɗin kunu babu kunu a wajen Ummata, ya tursasa mini jam dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama sararin cewa"dukka dubu uku ne amma na yi dubu da ɗari biyu". Babu musu ya zaro kuɗin ya irga su ya miƙo mini yawansu ya tsorita ni don na tabbatar da sun zarce dubu ukun da na faɗa masa. "Ka yi haƙuri ba na buƙatar kuɗinka, iya kuɗin ɓarnar da aka yi mini kawai nake buƙata". Bai yi musu ba ya irga su ya ba ni na karɓa sai na miƙa masa dubu daya da ɗari biyun da na yi amma ya ƙi karɓa, na ajiye masa su a wajen na fara tattare kayan tallana. Na kimtsa komai na soma ƙoƙarin barin wajen ya dakatar da ni. "Zan so ki ba ni damar ki yi miki rakiya har gida. Don na tabbatar da tsaronki saboda na san Zaina kamar yunwar cikina ba ta da daɗi ko na misƙalla zarratin za ta iya bin bayanki". Ambatan sunan Zaina da ya yi shi ya tursasa mini amince ya yi mini rakiya, sai dai ban yi zaton rakiyan zai yi tsayi ba. Har bakin layinmu ya yi mini rakiya kuma bakinsa bai fasa magana da yabon girin jikina ba duk da ba na tanka masa, shi yake kiɗansa yake rawarsa. [7/13, 7:23 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 0️⃣8️⃣ "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya tsara halittarki ya kuma busa miki numfashi. Bai bar ki haka ba ya kuma yi miki tagomashin iya magana da iya taku". Cak na tsaya jin kalamanta da suka sauƙa a na'urar naɗar sautina, na juya ina kallonsa don tunin na yi gaba na bar sa sai dai ban yi tunanin tazarar ta kai haka ba. Hijabina da iska ya ɗaga mini shi ta baya na yi saurin gyarawa ina ɗauke kaina daga gare shi. "Rakiyar ta isa haka na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Ya biya maka buƙatunka". "Amin tauraruwa, amma zan so na kai ki har ƙofar gidanku don na sauƙe nauyin tsaronki da yake kaina". Cikin ƙosawa da sauraronsa na ce"Malam na ce maka ya isa na gode, to kuma me ye kake so da ni? Don Allah ka bar ni ka koma wajen sana'arka". Ya yi wani irin shu'umin murmushi yana takuwa a hankali ya zo gabana. "Ai tun da na yi tozali da ke zuciyata take wajabta min ya zama dole na ba ki kariya da kuma kulawa ta mussamman. Babu wani aikin da ya sha gaban hakan a yanzu". Taɓe baki na yi na ƙara yi masa godiya na ci gaba da tafiya ganin har yanzu yana bi na ya sani ɗaga ƙafa kamar wacce aka jefo haka na faɗa cikin gida ina waige-waige. Saura ƙiris na yi karo da Ummi da Auwal da suke zaune a zaure suna hira, cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil na yi wucewa ta cikin gidan. Duk matan gidan suna waje yayin da Sahura mahaifiyar Amira take baza shewa ta baje a ƙofar ɗakinsu tana irga cinikin da Amira ta yi yau na waina fuskarta kamar gonar auguda. Kamar wacce aka tsigarawa matsilli haka Umma ta yi wani wawan zabura ta miƙe sa'ilin da ta ganin. Ta iso wajena tana bi na da wani irin kallo kafin ta ce"Amatullah yaya haka nake ganin ƙasa a jikin bokitin?". "Umma na sayar da shi gabaɗaya, a hanyar dawowa ne bokitin ya faɗa shi ne kika ga haka". Na ƙare zance ina miƙa mata kuɗin ta amsa tana lalle su ɗaya bayan ɗaya, tsakanin mamaki, al'ajabi da farin ciki na gaza bambance takamanmen wanda ya hana Umma yin magana a lokacin sai juya kuɗin take yi a hannunta kafin daga bisani ta ja ni zuwa ƙofar ɗakinmu muka zauna. Tsakin da manaifiyar Amira ta buga shi ya hana ta maganar da ta yunƙuro za ta yi ta kallo ta. "Ke kuma tsakin na me ye Sahura?". "Sai kuma aka ce miki da ke nake yi Hafsatu? Lissafi ne ya ɓarce min kin ga kuwa dole na yi abin da ya ci uwar tsaki ma. Babu uban da ya isa ya hana ni don daidai nake da uban kowa a cikin gidan nan yadda ake biyan kuɗin haya haka ni ma nake biya babu raran ko ficika". Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta furta"Allah na gode maka. Daman an ce makashinka yana tare da kai kuma hassada dai aka ce mungun ciwo ce a zuciyar mai ƙula shi. Mu zuba ni da ke Sahura tsakanin ni da ke ɗan halak ka fasa". "Tun da haka kika ce to mu zuba ɗin wallahi sai na tabbatar da in kika zuba ba ki kwashe ba Hafsatu". Sahura ta yi zancen tana miƙe wa tsaye Amira ta riƙe ta tana ba ta haƙuri suka shiga ɗaki, nan Umma ma ta ƙarishi banbamin ta ta gama. Jikina a saɓule na tashi na shiga ciki a falo na tarar da Abba da Anty Sawwama duk su biyun sun yi shuru alamar duk abin da yake wakana a filin tsakar gidan suna saurara, na durƙusa na gaishe su Anty Sawwama ce ta amsa Abba kuma maimako ya amsa sai ya jefo mini tambaya. "Yau ma kin je tallan ne?". Kafin na amsa masa Anty Sawwama ta tari numfashina"kunun ma yana tafiya kenan? Daga fitarki har kin dawo ko awa biyu masu kyau ba ki yi ba". Ƙirjina ya harba ɓat! Kamar yadda alburushi yake fita daga cikin bindiga, gabaɗaya na riɗime na daburce na soma kame-kame har izuwa lokacin da na ƙara tsinkayo amon Abba a karo na biyu. "Ina kika kai tallan ya yi saurin ƙarewa haka?". "Bakin titi ne Abba, masu tafiya makaranta da gona ne duk suka saye". Shurun da ya yi ya tabbatar mini da hashashen zuciyata na cewar bai yarda da abin da na faɗa ba. Zancen da Anty Sawwama ta yi ya ƙara jefa ni cikin kogin firgici har na kasa magana da motsi na tsawon wasu mintuna. "Ya kamar shatin ƴatsu ne a fuskarki Amatullah? Ko dai dambatuwa kuka yi a wajen tallan?". "Ba-ba-ba- ba abin da ya faru, shatin kwanciya ne kawai. Don jiya ban kwanta ana matashi ba". Ta gyara zamanta tana fuskantar Abba da kyau kafin ta sa furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan ranta"Allah ya jiƙan iyayenmu ya sabunta rahama a gare su, tabbas bango Ya faɗi don na tabbatar da ɗaya daga cikin iyayenmu suna raye ba za su taɓa zura ido jikarsu ta yi talla ba komai talauci da matsin rayuwar da muke ciki. Don an shaide su da wadatar zuciya da kuma kare mutunci da martaɓan ƴaƴansu mussamman ɗiyoyinsu mata, har muka girma iyayenmu mata ba za fita ko'ina iyayenmu da yayun maza suke fita domin samar mana da abin da za mu gudanar da rayuwa da shi. Amma yanzu kai Manniru ka ga dacewar wannan tallan da Amatullah take yi? Zankaɗeɗiyar budurwa da

Chapter 4 of 24