Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kifa kaina a saman ƙirjinsa ina kuka ji nake yi numfashi yana cushewa tamkar an ɗaure mini wuyana da ya kasance hanyar shiga da fitan numfashina. "Amatullah haƙuri za mu yi Kawu kuma lokaci ya yi wanda ya fi mu sonsa ya karɓe rayuwarsa. Sai dai mu yi masa addu'ar Allah ya kyautata makwancinsa idan lokacin mu ya yi mu kuma Allah ya ba sa mu cika da imani". Raɗau na ji maganar a na'urar naɗan sautina sai dai na kasa tantance waye mamallakin murya. Kukan kawai nake yi duk da hawaye ba sa fita daga idanuna amma ina jin zafi a cikin ƙirjina tamkar ana watsa mini garwashin wuta, na ji an ɗago ni sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna ana ɗago ni nake faɗuwa, aka Anty Zulaihatu ta riƙe ni muka shiga cikin ɗaki take numrashina ya soma ɗauke wa. Jikina ya soma jijjiga sai da ta dafa kaina tana karanto karatun suratul baƙara tana tofa mini a hankali na soma yi kamar an warware mini tirniƙin da ya zarge mini maƙoshina. Na koma kamar gunki babu wani gaɓa a jikina da yake motsawa face idanuna da suka kafe babu ɗigon baƙi a kaɗan a cikinsa ya juya zuwa launin fari fat. Sai da ta nem ruwa ta yi tofi a ciki ta shafa mini a jikina da ya sake ba shi da maraba da bishiyar da ta baza jijiyoyinta a ƙarƙashin ƙasa. Ba ta gushe ta na yi mini har sai da na ji nauyin da ƙirjina ya yi mini ya taguwa har na iya tashi da kaina na zauna. Na kasa kuka da hawaye illa na zuci da nake yi. Anty Sawwama ta shiga tararradin yadda za a sanarwa Ummata labarin rasuwar Abba, daga ƙarshen dai aka yanke shawarar aika Umar ya je ya ƙira ta. Babu jimawa suka dawo tare Anty Sawwama ta zaunar da ita ta yi mata dukkan nasiha cikin sigar mai jan hankali kafin daga ƙarshe ta sanar da ita labarin rasuwar. Ban ga tsananin kaɗuwa a fuskarta ba illa miƙe wa da ta yi ta nufo ni, na yi zaton runguma na za ta yi na ji ɗumin jikinta ko zan ji sauƙi yanayin da nake ciki sai dai na ci karo da saɓanin tunani da hashashena. Ta wanke ni da wani mahaukacin marin da har sai da ɗan kunnena ya faɗi ƙasa na dafe kuncina. "Amatullah shikenan hankalinki ya kwanta kin yi silar mutuwarsa. Ya tafi ya bar miki duniyar sai ki yi yadda kike so....". Na riƙe ƙafarta ina kuka mai haɗe da magiya. "Don Allah ki taimake ni ki taimaki rayuwata kar ki yi silar rugujewan ta gabaɗaya". Ban ta ce da ni komai ba ta zare ƙafarta daga riƙon da na yi mata ta juya tana fuskantar Anty Sawwama. "Ku yi zaman makokinku anan ni ma zan je na yi nawa a can." "Haba Hafsatu me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?. Me zai hana duk mu zauna a nan tunda nan ɗin ma ya fi fili". A zafafe Umma ta mayar mata da martani"in kun ga dama ku tafi bangon duniya ku yi na ku zaman makokin amma ni a ɗakina zan yi. Babu dalilin da zai sa na zo na tare a gidanku tun da wanda ya haɗa ya raba". "Haba! Anty Hafsatu ki yi haƙuri mana da nan da can ɗin ai duk ɗaya ne. Kar ki manta fa ga Kawu can a kwance ko kai sa ba ayi ba kike wannan maganar". Amir ya yi zancen hawaye suna ciko masa kurmin idaniya, tsaki Umma ta buga bayan ta gama jifan mu da harara ta sa kai za ta fice, Yaya Alhassan ya dakatar da ita ta hanyar faɗin" za ki tsaya dai ku yi bankwana da shi ki yi masa kallon ƙarshe tare da addu'o'i". "Zan iya masa addu'a daga duk inda nake kuma ta iske shi har cikin kushewarsa". Tana dasa aya a nan ta yi ficewar. Kalmar innalillahi wa inna ilahirin raji'un kawai Anty Sawwama take ta maimata jiri ya ɗebe ta za ta faɗi Amir ya riƙe ya zaunar da ita. "Umma a ina za a yi jana'izar kenan?". "Amir ya ya muka iya dole mu yi yadda take so, tun da a wancan unguwan aka san shi kuma a can yake zaune aje can kawai a yi masa salla a ƙofan gidan. Allah ya jiƙanka Manniru Allah ya kyautata makwancinka halinka na gari ya fita". "Amin ya Allah" . Duk muka haɗe baki wajen furta, Yaya Alhassan da Amir suka fita suka nemo mota aka tafi da gawar can unguwanmu Umar ya sanar da dangi labarin rasuwar, muka bi bayan su mu ma zuwa can unguwanmu. Muna karyo kwanar gidan na ga an kafa rumfuna har guda uku a ƙofar gidanmu ga mutane maƙil a wajen wasu suna zaune, wasu suna alwala wasu kuma su na tsaye jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau. Ban taɓa zaton haka mutuwa take da zafi ba sai yau da ta raba ni da jigon rayuwata. Muna shiga cikin gidan muka tarar da taron mata, yau ne rana ɗaya tal da na ga nutsuwa a tattare da matan gidan kowacce tana zaune a ƙofar ɗakinta cikin jimami har da masu kuka wiwi da hawaye don a tsawon shekarun da muka yi a gidan Abba ya zauna da kowa lafiya cikin aminci da girmamawa. Amira ta taso muka rungume juna muna kuka kowa sai da ya tausaya mana, aka ce mu shiga cikin muka shiga ɗakin Ummanta don ɗakinmu ya cika da mutane babu masaka tsinke. Mun daɗe muna kukan har sai da na kasa buɗe idanuna saboda yadda suka kumbura ji nake yi tamkar ni ma ba zan kai zuwa yamma a raye ba. Umman Amira ta shigo ta ce mu zo mu yi wa Abba addu'a za a tafi da shi, ko da na fita na kasa taɓuka komai illa kwantar da kaina da na yi a jikin makaran, bakina ya kasa cewa komai addu'ar ma a cikin zuciyata na dinga yi masa. Da ƙyar aka ɓaɓɓare ni daga jikin makarar, ina da ilmin cewar mamaci ba a nuna masa ƙauna da hanyar yi masa kuka. Wannan dalilin ya sanya yi ƙarfafa zuciyata na dinga karatun duk wani addu'ar da ya zo bakina a lokacin ina yi. Ban yi aune ba na ji an rufe ni da duka ta ko'ina tun ina kare kaina har na sadadu na baje a ƙasa. Idanuna suka soma gano mini Umma da ta kau saman ruwan cikina tana ta jibga duk da yadda mutane suka yi tururuwa suna janye ta amma ba ta fasa abin da ta yi niyya ba. "Ku bar ni na kashe matsiyaciya wacce ba ta yi gadon abin azirki ba. Ku bar ni na kashe ta don babu amfani rayuwarta gwara na kawar da ita". Da ƙyar mutane suka taru suka janye Umma daga kaina, lokacin har na fita daga cikin hayyacina na ji ɗumin wani abu mai ruwa yana bin tsakanin cinyoyina yana sauƙar har izuwa dugadugaina. Aka ɗaga ni na kasa tsayiwa na lu na faɗi. Tun daga sa'ilin nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni a gadon asibiti da Anty Zulaihatu da Amira a kusa da ni, ina buɗe ido suka soma yi mini sannu wani bin wani kana Amira ta je ta ƙira likita ya zo ya ƙara duba ya kuma tabbatar da cewar babu wani damuwan. "Amira me ye ya faru da ni ne ki sanar da ni. Ganin komai na ke yi tamkar a cikin mafarki, don idan mafarki nake yi ki taimaka ku tashe ni tun kafin na zauce". "Babu abin da ya faru da ke Amatullah faɗuwa kika yi aka kawo ki asibiti kuma yanzu kin ji ai da kunnenki cewar babu wata matsala. Sai dai kuma wani abu....". Ta yi shuru ba tare da ƙarisa ba suka haɗa ido da Anty Zulaihatu take na ga duk su biyun sun fashe da kuka, hakan ya ba ni tabbacin cewar akwai wani abun da suke ɓoye mini. "Don Allah Anty Zulaihatu kar ku ɓoye mini komai ku sanar da ni abin da ya faru da ni komai munin sa, babu abin da zai same ni yanzu babu wani labarin da zai tayar mini da hankali fiye da rasuwar Abba. Don Allah ku sanar da ni". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya. Sai da suka ɓata wasu mintuna kafin Anty Zulaihatu ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali ta ke faɗin. "Amatullah kin shiga cikin jarabawa da yawa wanda sai mai ƙarfin imani ne kawai zai iya jure su ba tare da ya rasa tauhidinsa ba. A yanzu ma ina so ki yi haƙuri da abin da za ki ji daga gare ni". Na gyaɗa mata kaina alamar ina sauraran duk abin da take faɗa da hakan ya ba ta damar ci gaba daga inda ta tsaya. "Sakamakon dukan da Ummanki ta yi miki cikin da ke jikinki ya bi rariya". Na ware dukkan girman ƙwayan idona"ya zube kenan?". "Babu yadda za mu yi Amatullah haka Allah ya ƙaddara". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya na rasa a tsakanin farin ciki ko baƙin ciki wanne ya fi dacewa da ni a yanayin da nake ciki. Yaya Alhassan yana zuwa asibitin aka sallame mu sai dai maimakon mu wuce can gidanmu sai na ga sun wuce gidan Anty Sawwama. Na yi kuka iya kuka har sai da idanuna suka kafe, na ji gabaɗaya duniyar ta ishe ni babu abin da yake yi mini daɗi a cikinta. Wai ace mahaifina ya rasu amma ba ni da ikon zuwa wajen makokinsa ni kam ba san abin da ya fi wannan ciwo da raɗaɗi ba. [10/29, 10:08 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 3️⃣9️⃣ Haka na kwana na tashi da zazzaɓi a jikina garau kamar garwashin wuta ake watsa mini a cikin jikina. Ji nake yi tamkar a mafarki wai yau Abba ba ya raye cikin duniya ya rasu ba tare da na sanar da na kore masa kokonton da share masa zargin na aikata abin da ake zargina da shi. Ban taɓa sanin haka mutuwa take da matuƙar zafi da ciwo ba sai yanzu da ya juyo kaina, ji nake yi kamar ni ma ba zan yi tsawon rai a duniya ba ko da kuwa na yi to haƙiƙa zan zauce ne na fita daga cikin hayyacina. Tun ina yin kukan da hawaye har suka daina zuba ƙirjina ya yi miji nauyin gaske tamkar an yi mini ajiyan dutsin dala ta Kano a saman ƙirjina, idanuna har sai da suka daina buɗuwa saboda tsabar kumburan da suka yi. Kafin gari ya waye ko magana ba na iya yi haka nan ba na gane wanda yake tsaye a kaina sai dai kawai na tantance muryan. Ina kwance tamkar ruwa don ko ƴatsan hannuna ba na iya motsawa jikina ya yi lamus ko kaina ban iya ɗagawa, ranar da aka yi sadakan ukun Abba yayin da Anty Sawwama ya ce a haɗa har na bakwai kowa ya watse aka kuwa yi hakan. Aka bar mu daga mu sai ya mu sai kuma halinmu, har zuwa wannan lokacin Umma ta Antyaihatu ta shigo cikin ɗakin ta zauna a kusa da ni ta ɗaura hannunta a bisa goshina da ya ɗau zafi gau. "Ya subhanallahi! Amatullah jikin ne haka? Don Allah ki tashi ki ci wani abun ko kaɗan ne sai ki sha magani". "Anty Zulaihatu mutuwa zan yi ni kam ba zan rayu ba mutuwa ni ma zan yi". Na zaro maganar da ƙyar saboda yadda numfashina yake cukurkuɗewa waje guda kamat mai lalurar cutar numfashi. "Amatullah duk wanda kika ga ya mutu ai lokacinsa ne ya yi. In sha Allah ba za ki mutu ba sai lokacinki ya yi, za ki ci gaba da rayuwa har ma ki yi dariya ki yi mu'amala kamar kowa. Don Allah ki kwantar da hankalinki komai ya faru da Bawa muƙaddari ne daga Allah ne kuma Bawa baya wucewa ƙaddararsa balle ya guje mata". Na ɗaya kaina ina ganin ta dishi-dishi ga numfashina yana sama yana ƙasa na yi ƙarfin halin faɗin"Anty Zulaihatu rayuwata ta zo ƙarshe ni kam". Ban ƙarisa ba ta rufe miji bakina da tafukan hannayenta. "Don Allah ki daina faɗin irin wannan maganar babu wanda ya san gobe sai Allah". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai ɗumi ina lumshe kumburarrun idanuna da kamar za su faɗo ƙasa. Sama-sama na soma jiyo amon Yaya Alhassan a masarrafan naɗan sautina, kafin na ji muryar dab da ni. "Amatullahi". "Na'am". Na amsa a taƙaice da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganan da yake yi. "Wannan damuwar duk na mene ne haka ƙanwata? Abin da ya faru ai riga da ya zama tarihi sai dai ayi ƙoƙarin gyar gaba. Kawu yanzu addu'armu yake buƙata ba wannan koke-koken ba, na san abin da ciwo amma ina so ki daure ki yi ƙoƙarin cire komai daga cikin ranki ki fuskanci rayuwarki ta gaba ka shagala wajen ingantata". "Yaya Alhassan ni kuma me ye ya rage mini a duniya ai rayuwata kam ta gama rushewa ta rugurguje". "Har yanzu ki na da sauran daman da za ki ɗinke ɓarakar da ya ɓullo a cikin rayuwarki. Amatullah rayuwa jarabawa ce mai girman gaske, duk munin halin da kike ciki idan kika ga wani ko kika ji halin da wani yake ciki sai kin ji tamkar ke ɗin ki na cikin gidan aljanna ne". Na yi lamau na kasa cewa da shi komai zuciyata tana turara kamar talgen masarar da aka aza bisa murhu. "Tashi mu yi magana". "Ba zan iya tashi ba". Muryarsa babu alamar wasa ya furta"tashi ki zauna magana za mu yi da ke". Na cije leɓe na tashin na zauna saboda duk inda na motsa a gaɓoɓina ciwo yake yi mini. Shruu ya ratsa ɗakin kafin ya kawar da shurun ta hanyar faɗin"Amatullah da waye kika keɓe har ciki ya shiga cikinki?". Zuffa ya jiƙa mini jikina tsam jikina ya soma rawa sai da na fizgo numfashina da ƙarfi kafin na iya faɗin"Yaya Alhassan wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini...... ....". Na irge masa komai duk abin da ya faru tun daga faru har ƙarshe. Ya zabga mini wani gigitaccen marin da ban san lokacin da na sake ihu ba. Ya tashi tsaye yana cije leɓansa tare da kai wa iska naushi. "Amatullah me yasa kike ɓoye faruwar wannan abun? Shin ba kya kishin kanki da har wannan abun zai faru amma duk da haka ki zaɓi ki ɓoyewa kowa hatta iyayenki da ƴan uwanki. Wanda kika san cewa duk wuya duk tsinki suka rufa miki asiri. Ina ma kin sanar tun a lokacin da lamarin ya afku da duk abin da ya faru bai faru ba". Ya ƙarishe zancen cikin matuƙar takaici daidai lokacin da Anty Sawwama take shigowa ɗakin cikin tsananin damuwa da alamar ta saurari duk abin da na muka faɗa. "Allah ba ka jarabtan Bawa da abin da ba zai iya yi. Ya Allah don ƙarfin zari da ikonka ka ba mu juriya da haƙurin jure wannan jarabawan da ka jarabce mu da shi". "Amin ya Allah". Duk suka haɗe baki wajen furtawa amma ni kam sai a zuciyata na amsa don bakina ya kasa motsawa. "Umma yanzu ya ya za a yi?". Anty Zulaihatu ta tambaya muryarta tattare da tarin damuwa. "Dole mu je mu yi magana da mahaifiyarta don yadda ta yi watsi da Amatullah a wannan yanayin da take ciki abin yana damuna matuƙa. Zuwa yamma in sha Allah za mu je gabaɗayanmu mu same ta". Duk suka yi na'am da abin da Anty Sawwama ta furta ni kam na yi shuru tamkar wacce ruwa ya cinye ta. Zuwa bayan sallan asr suka sauƙa daga napep a ƙofar gidanmu. Na waiga na hango masallacin da Abba yake salla kuma yake yawan zama a bakin wajen, na ga tarin dattawa zaune a wajen sai dai duk cikin su babu Abba, mutuwa kenan mai raba zumuci da daɗaɗɗan alaƙa. Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna kafin na ja ƙafafuna muka shiga cikin gidan, yara da manya suka taru suna ganina kamar ba su taɓa ganina ba kaina a ƙasa tun da muka shigo amma hakan bai hana su magana ba. "Wannan ce annobar kenan? Ni kam da haihuwar irin wannan ai gwara ka zo duniya har ka gama rayuwarka ba tare da ka haihu ba". Cak na tsaya bisa sauƙan furucin da na ji a kunnuwana da ya damalmala mini dukkan lissafina ya farraƙa nutsuwa da gangar jikina. "Amatullah ke ce haka duk kika lalace kamar mai cutar ƙanjamau?". Maman Adnan ta yi zancen tana iso ta tsaya a gabana kafin na ba ta amsa ta ci gaba da zancen tana taɓe baki. "Ai daman ƙarya fure take yi ba ta ƴaƴa kuma komai nisan daren dole gari zai waye haske ya mamaye ko'ina, ashe duk sintirin da kike yi da sunan da zuwa islamiyya fakewa ake yi da guzuma a harɓi karsana to an yi walƙiya mun gan ku". "Malama idan har kin san cewa bakinki ba zai furta alkhairi ba, to zai fi dace ki yi shuru". Anty Zulaihatu ta mayar mata da martani a zafafe tana jan hannuna muka shige cikin ɗakinmu, muka tarar da Umma tare da wasu mata biyu muka yi sallama sai dai cikinsu babu wanda ya amsa mana muka shigo muka zauna, ina satan kallon Umma sai dai ko kaɗan ban ga ta yadda na yi tsammanin ganin ta ba. Na yi zaton kamar yadda mutuwar Abba ta girgiza ni haka ita ma lamarin zai taɓa zuciyarta sai dai kash! Ashe kallon kitse nake yi wa ruwa hange dala nake yi wanda ya ke ba shiga cikin birni ba ne. "Hafsatu ya muka ji da haƙuri?". "Alhamdulillah". Ta amsa da shi tana yatsina fuska. "Na zo mu yi magana da ke ne amma na ga ki na da baƙi, na ce ko za mu shiga cikin uwar ɗaka?". "Babu inda zan motsa daga idan kuka riske don haka duk abin da za ki faɗa ki faɗe ta a nan. In ba za ki iya ba kuma ki wanke ƙafafunki ki koma inda kika fito ba lalle ba dole ai". Lamarin ya ƙullar da Anty Zulaihatu har sai da ta tanka"Maman Amatullah izuwa yanzu kam ai na yi tunanin komai ya wuce, ya kamata mu bayar da hankali mu fuskanci abin da yake gabanmu. Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen nemawa yarinyar nan nutsuwa da farin cikin ko don daidaituwar rayuwarta". Umma ta gyara zamanta tana fuskantar Anty Sawwama da kyau tare da faɗin. "Ku yanzu har ku na tunanin cewa a cikinku akwai wanda ya fi ni son Amatullah ne, na fi kowa son ganin rayuwarta ta gyaru shi yasa nake yi duk waɗannan abubuwan. Wallahi duk daren duniya ba na iya runtsawa saboda baƙin cikin abin da wannan yarinyar ta aikata, ni kaɗai na sa irin son da nake yi wa Amatullah ko har kun manta irin wahalar da sha yayin raino da haihuwarta". Kalamanta ya sanya idanuna kwaranyowa da hawayen da na daɗe ban tsiyayar ba, na ja gwiwoyina na gurfana a gaban Umma na ɗaura kaina a bisa kan cinyoyinta. "Umma na tuba ki yafe mini wallahi ni ma shaida ce na san cewa ki na yi mini irin soyayyar da babu wanda zai yi mini kwantan-kwacinta a cikin duniyar nan. Amma zan so ki zauna ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini Umma kin san da hankali da tunanina ba zan aikata wannan abun ba, don Allah ki sassauta mini ki ba ni mafaka na sama sassauci a wajenki". "Amatullah na riga da na cire ki daga cikin raina, tun ranar da abin kunyar da kika aikata ya bayyana na sallamar da ke a duniya......". Da hanzari Anty Sawwama ta katse ta"kar ki yi mata baki Hafsatu ki saurare abin da za ta ce da ke don Allah". "Babu wani abun da ya yi saura wanda za ta sanar da ni da ban ji shi a bakin al'umman gari ba. Amatullah na sallamar da ke ga duniya daga yau ni Hafsatu ba ni da wata ɗiya a duniya, don haka ki tashi ki bi su kar ki ƙara zuwa inda nake balle ni ma baƙin cikinki ya kashe ni kamar yadda ya yi silar mutuwar ubanki". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahumma ajirni fi musibati. Ya Allah ka kawo mana sauƙi wannan lamarin". Wani irin kuka nake yi mai raunana zuciyar mai saurare babu shiri na ɗago kaina sakamakon dukan da na ji kalaman Umma sun yi mini. Duk yadda na so na yi magana na kasa yin haka sai ma tashi da na yi da sauri har ina haɗawa da gudu-gudu na bar cikin ɗakin kai tsaye ɗakin su Amira na nufa na zube akan kujera ina ci gaba da kukan. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me ya faru kuma? Tun ɗazu nake so na je ɗakin nakun sai kuma Ummata ta ce ai da baƙi a ciki shi yasa na dakata". Na tsinkayo muryar Amira cike da kulawa yayin da take zama kusa da ni tare da ɗago kaina. Ta soma goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana. "Amira me yasa munanan abubuwan suke faruwa da ni? Da farko an yi mini fyaɗe ciki ya bayyana a jikina, Abba ya mutu da baƙin cikin da na yi silar cusa masa sannan yanzu Umma uwar da ta haife ni ta furta cewar ta sallamar da ni ga duniya ba ta buƙatar gani na a kusa da ita. Amira ya ya ake so na yi rayuwata? Allah ma fa da kansa mu na yi masa laifi ya yafe mana to me ya sa Umma ta kasa fahimta na akan wannan lamarin balle har ta dube ni da idon rahama, jin ƙai tare da tausayi. Wallahi zuciyata ta soma saƙa mini wani mungun tunani, duk abin da na aikata kar ku ga laifina wallahi na rasa mafita ne". Na yi zancen cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa cikin kalmomin baki, Amira ma kanta sai da hawaye suka zubo mata daga idanunta. Ta kasa lallashina illan kukan da muka haɗu ni da ita mu na yi. "Duk laifina ne Amatullah ni na fara kawo shawaran zuwa gidan Tasalla. Kuma bayan abin da ya faru ya faru na goyi bayan a ɓoye lamarin. Komai ya faru ni ce sila ina ma a kaina wannan abun ya faru ba ke ba Amatullah ina ma....". Ba ta ƙarisa ba sakamakon kukan da ya ƙwace mata mai ƙarfin gaske muka haɗu duk mu biyun muna yin sa. Ummanta ta shigo ta tsaya a kanmu na tsawon lokaci kafin ta yi magana. "Haƙuri za ku yi don duk abin da ya faru kuka ko shiga tsananin damuwa ba ya gyara shi. Ƙaddara ce da ta riga fata cikin mu babu wanda zai iya guje mata". Ta dafa kaina kana ta ci gaba"Amatullah ki yi haƙuri na san cewa ke mai haƙuri ce da juriya da kuma tawakkali. Duk layin nan da ke ake buga misali da kwatance idan za yi maganar tarbiyya, kamun kai, hankali da kuma nutsuwa kuma ina da tabbacin kowa zai shaide ki cewar hakan ba halinki ba ne. Ki tashi ki share hawayenki ki fito ku tafi ga su can suna jiranki a waje". Na kuma fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya ni nake yi zuciyata tana yi mini hura. Muka fito har zaure hannuna saƙale cikin na Amira suna fitowa waje muka ga dandazon mutanen unguwa ƙwansu da ƙwarƙwatansu wai duk su zo kallona. "Dube ta simi-simi kamar na Allah ashe kura ce lulluɓe da fatan akuya. Allah dai wadaranki da kuma mungun halinki, ga shi yanzu ki kashe mahaifinki har lahira Allah sarki! Malam Manniru bawan Allah da ya san irin annobar da zai haifa kenan na tabbatar da ya gwammace ya rayu har ya koma ga Allah babu ɗa babu jika". Kalaman da suka sauƙa a na'urar naɗan sautina kenan da ya gigita ni numfashina ya soma sama da ƙasa, ashe kowa zargina yake yi da

Chapter 23 of 24