Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi hanzari rufe mini baki da tafukan hannayenta na zame hannunta. "Amira Ina kika sama wannan dalleliyar wayar nan? Ko wani ne ya ba ki ajiye? Ko aka aike ki da shi wani wajen?". Ta saki dariya har da riƙe ciki sai da ta yi mai isharta kafin ta tsagaita gami da faɗin"babu ko ɗaya nawa ce, daren jiya ta zo hannuna". Na watsa mata kallon mamaki da al'ajabi. Cike da son tabbatar mini da sahihancin abin da ta furta ta ɗage mini idonta guda tana zarce wa da cewa"wallahi kin dai ji rantsuwa kenan ko, wayata ce". Na katse ta kafin ta ƙarisa zancen. "Ina kika sama kuɗin sayan wannan wayar Amira? Ita wayar nan ce fa ta cikin shirin film ɗin labarina, ta hannun Baban Sumayya. Kuma na san ko riba da jarinki gabaɗaya kika haɗa ba za su sayi wannan wayar ba". Ta kuma fashewa da dariya kafin ta ce. "Ba ko sisina a cikin kuɗin wayan nan Mansur ne ya kawo min ita jiya, tukwuicin amsar tayin soyayyarsa da na yi". Kamar saƙaho haka na saki baki da hanci ina bin ta da kallo tamkar yau na fara tozali da ita. Sai da na tattaro jarumta na yaɓa wa kaina kafin na iya yin motsin kirki har na iya furta wani abun. "Amira anya kuwa kina da hankali? Haka siddan daga haɗuwa da mutum ya ɗauki wannan wayar ya ba ki kuma ki sa hannu ki amsa". Ta galla mini harara tana fizge wayar daga hannu. "Kin ga Amatullah kar ki ɓata min rai da sanyin safiyar nan, sanin kanki ne a kaf cikin gidan nan da ke kaɗai nake hira har na saki jiki na sanar da ke abubuwan da nake yi". Ganin tana ƙoƙarin ficewa ya sani riƙo hannunta. "Kar ki ɗauka da zafi mana ke kuwa. Ki yi haƙuri". "Ke ce ai kike ƙoƙarin ɓata min rai Amatullah". Ta koma mazauninta ta zauna ta murtuƙe fuska. "Haba! Ke kuwa saki fuskar mana ta Mansur". Babu shiri ta ƙyalƙyale da dariya. Ta gyara zama tana zubo mini bayanai"ban san inda yake ba amma dai a gajerin da nake kai tallar waina muka haɗu da shi ya kawo gyaran motarsa, ya saya waina ya buƙaci lambata na ce da shi ban da waya. A haka kusan kullum sai ya zo gajerin don kawai ta ganni har ya yi min tayin soyyarsa bayan na gara shi shekaran jiya na amince. Daren jiya kuwa ya same ni har ƙofar gida ina soyar awara ya ba ni ita, bayan p yi min juye". Ƙwala mata ƙiran da mptessghaifiyarta Sahura ta yi mata shi ya hana ni furta zancen da na yunƙuro da nufin yi. Ta tattare kwalin wayar ta miƙe"bari na je na san yanzu Ummata ta kammala wainar, duk sauran ƙarin bayani inna dawo za ki ji shi". Da kallo na raka ta har ta fice na gaza cewa komai saboda giyan mamakin da ta shayar da ni, haka na zauna ina bitar zantukan Amira tare da yi musu tankaɗe da rairaya. Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ina tallafe kuncina lalle Amira ta kusa ta fi ƙarfina. A kwanakin baya sai da muka daina magana da ita don kawai na gaya mata gaskiya akan irin shigar banzan da take yi in za ta fita talla. Ko da na yi mata magana sai ta kaɗa baki ta ce da ni idan ba ta yi kwalliya waye zai kalle ta balle har ya sayi abin da take sayar wa. Yanzu ga halin biyewa samari da ta tsira. "To maza malalaciya tashi gari ya waye. Ga kunu can ya kammalu". Na tsinkayo amon Ummata da ya yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. DAFIN HARSHE ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 0️⃣5️⃣ Zumbur na miƙe na rarumo hijabina na saka na bayyano waje, tana tsaye a baranda ta cika ta yi him da dukkan alamu ƙiris take jira ta fashe. Na durƙusa a gabanta sai dai tsoron da ya yi mini katutu a cikin ƙalbina ya hana ni furzar da zancen da ya maƙale mini a bakina. "Uban me ye kike jira? Shegiya mai zubin aljanu". Ta doka mini tsawan da ya tilasta mini runtse idanuna ƙirjina yana tsananta bugu. Ta rusunar da kaina ƙasa kafin na soma faɗin"daman tambaya na nawa ne zan yi". Da alama zancen nawa ya yi tasiri wajen ƙara rura wutan da yake huruwa a cikin ƙirjinta, ta yi ƙwafa tsabar takaici. Duk da idanuna suna ƙasa amma a jikina nake jin ni take kallo. "Amatullah kina ƙure ni fa kina tuntsira ni. Ina jiye miki tsoron ranar da zan yi wasan kura da ke a cikin gidan nan. Dan ubanki na dubu ɗaya ne da ɗari biyar, idan kin ga dama ki dawo min da shi yadda na kika fita da shi. Tun da daman ke ba ki gaji abin azurki ba tsinanniya". Babu shiri na ɗago kaina"don Allah Umma ki yi haƙuri in ranki ya ɓaci ki dinga yin shuru. Kullum ana gaya mana a islamiyya cewar ba a son a dinga yi wa ƴaƴa irin waɗannan kalaman".. Kallon da ta tsare ni da shi ya sani yin shuru tare da mayar da kaina ƙasa ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata. Fahimtar abin da shurunta yake nufi ya sani tashi na naɗa gammo na ɗaura bokitin kunun a kaina, numfashi mai zafi na fesar daga bakina ina ƙarewa layin namun kallo. Don ban ma san inda zan nufa na sayar da wannan kunun ba. Amon muryar Auwal da suka yi wa ƙofofin kunnuwana sauƙan bazata. "Amatullah kenan! Ƴan mata adon gari matar manya, irin ta gaban mota". A tsorace na waigo ina bin sa da kallo cike da son ƙarin haske, kamar ya san abin da yake cikin raina ya ci gaba da magana kansa tsaye ba tare da tsoro ko shayin komai ba. "Allah ya yi miki zubi da tsari uwa uba ga diri kamar ke kika zana kanki, wallahi ba namijin da za ki wulga ta gabansa bai ji wani abu a cikin ransa ba. Ni da sai yanzu ma na fahimci na yi zaɓen tumun dare, sam Ummi ba ita ce kalan matan da nake so ba sai dai ance da babu gwara ba daɗi. Amatullah na yi miki alƙawarin matuƙar kika amshi soyyayata a shirye nake da na yi watsi da Ummi daga cikin zuciyata, daman can ba shiga can ciki ta yi ba". Sakeke na tsaya ina kallonsa raina cike fal da mamakin furucinsa da yadda yake ya wani kanne ido guda ana lashe leɓan bakinsa kamar maye. Na gyara tsayiwata kafin na harhaɗo jarumta har na sama ƙarfin gwiwan iya furta"Auwal babu abun da ya haɗa ni da kai saurayin Ummi ne kai kowa ya shaida hakan, na roƙe ka don girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara ka fita daga harkana ko har ka manta abin da ya faru ne? Ba na son na ƙara tsoma kaina cikin wani masifan". Na ƙarisa zancen cikin sigar roƙo da magiya sai da dukkan alamu roƙon nawan bai ɗaɗa sa da ƙasa ba. "Tun ranar da na yi ido huɗu da ke Allah ya ɗaura min sonki a cikin zuciyata, ba yin kaina ba ne ni ma Amatullah. Kuma ina mai ba ki haƙuri akan abun da ya faru, ban yi da wani manufa ba kuma ban yi tunanin lamarin zai yi ƙamari har haka ba, ki yi haƙuri ya ke Sarauniya". Yana rufe bakinsa muka yi ido huɗu da Salmanu ƙanin Ummi ya dawo daga aiken da aka yi masa, ina ganin sa na sha jinin jikina. Don na san na yi shuka ne a idon makarwa tun da ya ganni da Auwal sai ya je ya isarwa Ummi. "Ka ga ni dai babu ruwana. Ina zaman zamana ba za ka ja mini bala'i da masifa ba, ka ga tafiyata". Ina dasa aya a nan na juya na bar ƙofar gidan da sauri har ƙafafuna suna sarƙafewa, sai da na cire daga layin gabaɗaya kana na sauƙe wani wahalallan ajiyar zuciya. Sai da na yi tafiya mai nisa amma ko ciniki naira biyar ban yi ba na nema waje na zauna ina huta gajiyar da na kwaso. Na tallafe kuncina ina bin bokitin kunun da kallo. A ƙalla na yi zaman mintuna ashirin kafin na yi cinikin naira ɗari biyu na kuma yin naira ɗari, har hantsi ya fito ba a ƙara saya ba, hakan ya sa ni tashi na ɗaura a kaina na fara bi gida-gida. Gida guda ne suka saya na hamsin. Cikin fargaba na nufi gida ganin ranar ta fito ta take ta yi ƙwal, da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata saboda gajiyar da na yi lis tun daga nisa idanuna suke gano mini wata shirgegiyar mota a fake a ɗan nisa da gidanmu. Na lumshe idona na buɗe don tabbatar da sahihancin abin da suke gano mini. Sai na yi kusa kafin na gane Amira ce da wani tsaye a jikin motar suna fuskantar juna sun ƙurawa junansu idanu kamar za su cinye juna. Kai tsaye zuciyata ta fassara irin kallon da irin kallon da malamin littafin ahalari ya faɗa mana, kallon da addini ya haramta. Gefe guda kayan tallanta ne a kusa da ita. Jikina ya yi sanyi ƙalau ganin har ta sayar da duk tulin wainar da tun fitowa ta alwalan asubahi Sahura take tuyawa. "Amatullah". Ta ƙira sunana yayin da nake gab da shiga cikin gidan, na juyo jikina a sanyaye. Ta yi mini ishara da hannu akan na zo na isa wajen tare da sallama ɗauke a bakina suka amsa na gaishe shi ya amsa yana kallona. "Masoyi ga aminiyata ko ma na ce ma ƴar uwata sunanta Amatullah". Ya jinjina kansa"ma sha Allah, Amatullah sannu". Kafin na amsa Amira ta riga ni faɗin"Amatullah ga Mansur wanda nake ba ki labarinsa". Na ɗago kaina ina satan kallonsa caraf idanunmu suka sarƙafe na yi hanzarin janye nawa kafin na ce"sannu da zuwa, ai kuwa ta na yi mini labarinka. Allah ya wanzar da alkhairi a cikin alaƙarku". "Amin ya Allah". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da shi kafin ya ce"ya kuma kika dawo kunun nakin bai ƙare ba?". "Na yi mantuwa ne na zo ɗauka". Na ji bakina ya furta ba tare da ya yi shawara da zuciyata ba. "Amatullah kenan ke dai akwai zurfin ciki. Ba kya son kowa ya san halin da kike ciki". Na wurgawa Amira da ta yi zancen harara kafin na zarce da cewa"kin ga ni ba na son dogon magana. Sai kin shigo, Mansur na bar ku lafiya". Ya washe baki har kunne ya zaro wasu kuɗi daga aljihunsa ya miƙa mini"to ƙawarmu ga wannan a sayi kayan kwalliya". "A'a na gode Allah ya ƙara azurki". Na furta ina juyawa na bar wajen don na gaji da kallon da yake mini, na shige gida daidai sanda ake ƙiran sallan zuhur da Umma muka fara yin kato za ta fita gani na ya sa ta komawa da baya tana ƙare mini tanadin kallo. "Me nake gani haka? Amatullah yaya da haka kuma?". Na sauƙe bokitin daga kaina na miƙa maka cinikin da na yi ina ƙara wa da cewa"Umma an saya fa wallahi, kin ga ma cinikin da na yi". Ta firge kuɗin ta na irga su kafin ta yi magana yaro ya yi sallama ya shigo da kayan tallan wainar Amira Umma ta bi robobin da kallo da ina da tabbacin ganin su wayam babu komai a ciki shi ya fi komai jan hankalinta. Sahura ta fito daga ɗaki tana rangaɗa kuɗa"Allah kai ne abun godiya. Maraba da ke ƴar azurki irin albarka har kin sayar ki dawo". Ta yi furcim sa'ilin da Amira take shigowa tana tafiya ɗaɗɗaya tana taunar cigam da yake ba da sautin ƙas ƙas. "Umma ni ce fa ko kin manta alƙawarin da na yi miki ne? Ai waina ko na dubu hamsin za ki yi min sai na sayar da ita". Ta ƙare zancen tana miƙa mata kuɗin ta irge su a filin tsakar gidan cas ta lale su, lamarin da ya baƙanta ran mutane da yawa ciki har da Ummata da take ta faman ciki tana batsewa. Na tabbatar takaicin da ya zo mata har wuya ya yi mata tsayiwar ƙayan kifi a maƙoshi shi ya hana ta furta ko da baƙi ɗaya illa ƙwafan da ta yi, ta fice daga gidan. Na bi ta da kallo har ta fice kafin na ɗauki bokitin na shiga ɗakinmu na cire hijabina na fito na yi alwala na koma na yi salla nan kan sallayar na zauna don na san yau kam babu batun zuwa na islamiyya tun da Umma ta sa ƙafa ta fice. Ban san lokacin da bacci ya sure ni ba sai da na soma jin ana bubbuga ni tare da ƙiran sunana. Na buɗe idanuna a hankali har suka yi tar akan fuskan Amira da take tsaye a gabana. Da ƙarfi ta miƙar da ni tsaye ta ja ni zuwa cikin uwar ɗakanmu, na fizge hannuna ina murtsike idona. "Wani irin wulaƙanci ne haka Amira? Ina baccina za ki zo ki tashe ni ki wani jawo ni ɗaki". "To jarabu ki yi haƙuri mana taimako za ki yi min". Ban amsa mata ba na ja tsaki na zauna na kafe ta ido. Ledan hannunta ta zazzage akan gadon Umma ta ɗago dogayen riguna biyu. "Ta ya ni zaɓan wanda ya fi kyau da tsaruwa za ki yi a cikin waɗannan. Mansur ne zai zo mu fita shan ice cream". Ta ƙarƙare zancen tana wani lumshe idanunta. Ta kufule na ce"akan wannan shi ne za ki tashe ni ina baccina? To ki saka duk wanda ya yi miki". Na miƙe zan fita ta riƙo hannuna. "Ki tsaya mana haushinki fa nake ji ma in ba ki sani ba, amma duk da haka na zo neman shawaranki". Na ware idanuna akan ta"haushin me ye? To ma me ye na yi miki?" Na ƙwace hannuna daga riƙon da ta yi mini. "Mussamman na zaɓo ki kamar tumu, a yaran gidan nan gabaɗaya ke kaɗai na ba wa damar ganin Mansur amma kika zo kika wani haɗe rai. Har ya yi miki kyauta ki ƙi karɓa don wulaƙanci". "To kuma sai aka ce dole in ya mini kyauta zai na amsa? Na ga dai kar addu'a na yi muku da fatan alheri. To me ye kike so bayan hakan?". "A bar maganar nan, ni dai yanzu ki duba min rigar da zan sa". Na wafce rigunan ina jujjuya su kafin na ce"ki sa wannan shuɗin za ta yi miki kyau sosai". Ta daka tsalle"haka Mansur ma ya ce da ya kawo min su". "Kina nufin shi ya saya miki?". Ta ɗaga mini gira guda"ƙwarai kuwa". Kafin na dawo daga mamakin da na faɗa ta kuma cewa"bari na je na saka na dawo". Ba ta jira abin da zan ce ba ta karɓa rigar ta fice cikin zumuɗi da tsantsan farinciki. Mamaki ya hana ni motsawa daga inda nake har sai da na jiyo sallamar Umma na fito ina yi mata sannu da zuwan da ta yi kunnen uwar shegu da ni. Na ɗauki hijabin da ta cire ina ninkewa na furta"Umma ina kika je kuwa da ranan nan?". Kaman ba za ta amsa ba sai kuma can ta ce da ni"gidan Malam mai laƙanin sa'a na je". Na dakata da abin da nake yi"Umma ke kuwa me ye kika je yi?". "Kukana na kai gidan mutuwa, na je na ƙarbo taimakon buɗewar ƙofar nasara akan sana'ata. Don ina da tabbacin Sahura ma a nan ta karɓo na ta laƙanin". [7/7, 10:28 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 0️⃣6️⃣ Sakeke na yi ina kallonta kamar doluwa sai da na ja dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama damar sarrafa harshena da ya cika mini baki ya kuma yi mini nauyin ɗagawa. "Umma wani irin laƙani ke kuwa? Akwai wanda ya isa ya yi abinda Allah bai yi ba ne? Me yasa ba za ki kwantar da hankalinki ba?. Ko ba ki yi sana'ar komai ba ba za mu rasa ci da sha ba haka nan ba za mu tafi tsirara ba, to mene ne na tada hankali har kike ƙoƙarin faɗawa cikin halaka....". Kafin na rufe bakina ta sauƙe mini marin da ya sani ganin gilmawar baƙin dubu a idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi saboda gazawar ƙafafuwa. Sai da na yi sa gaske kafin na iya riƙe kaina na dafe kuncina ruwan ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata. "Ke har kina da bakin magana akan wannan matsalar Amatullah? Bayan ke ce matsalata ke ce sila da tushen shiga ta cikin kowani irin damuwa. Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki zage damtse wajen warkar min da raunin da yake cikin zuciyata ba? Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki kashe wutar da take ƙoƙarin ƙona min zuciyata ba?. Kina ganin yadda Amira take yin komai wajen ganin ta farantawa mahaifiyarta, ba ta taɓa yi mata jaura ta dawo mata da shi ba face ta sai ta sayar da shi tas komai yawansa. Shin ke hakan bai ishe ki ishara ba? Ban da rashin zuciya irin naki ke ko wani abu ba kya ji a zuciyarki game da ita?". Ji nayi kaina ya soma juyawa jiri yana ƙoƙarin kai ni ƙasa. Ban taɓa zato da tsammanin haka Umma ta ɗauki wannan abun azimun ba. Na gaza cewa komai illa hawayen da suka soma gudun famfalaƙi akan kuncina. Da ƙyar na furta"Umma ki yi haƙuri". Na ƙare zancen cikin raunin da ya bayyana har a muryata ina durƙushewa akan gwiwoyina na riƙo ƙafarta. Tsawon wasu mintuna ba ta ce da ni ko kanzil ba sai da na cire tsammani da samun amsa daga gare ta kafin ta furta zancen da ya girgiza ni ainun. "Babu wani zaɓi Amatullah dole ne ki yi amfani da wannan laƙanin. Ga shi nan kamar yadda kike kallo kwalli ne sai kuma turare, a duk san da za ki fita talla za ki saka kwallin a idanunki turaren kuma za ki turara kayan tallan da su. Malam ya ba ni tabbacin matuƙar kika yi hakan ko talla dubu ɗari kika fita da shi sai ya ƙare tas kamar yadda wuta take cinye auguda cikin ƙiftawan ido. Amatullah idan kina da hankali da hangen nisa yadda Amira ta zama cinye du kaɗai ya ishe ki ishara kuma hakan ya isa ya zaburar da ke wanda ke da kanki za ki ce na je na nemo miki wannan laƙanin". Tunani gabaɗaya ya tsaya cak bugun zuciyata ya tsananta. Gaɓoɓin jiki gabaɗaya suka yi sanyi na kasa motsa su. Ina ji ina gani ta zare ƙafarta daga riƙon da na yi mata ta bar ni yashe a wajen. Cikin rashin kuzari na tashi na yi sallan asr na kwanta a inda na yi sallan ina jin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Shiga goma fita goma Umma ba ta ce da ni ko kanzil ba har aka yi ƙiran sallan magrib, a zaune na yi sallan na ci gaba da zama a wajen na kafa kai da gwiwa. Ina karanto karantun al'ƙur'ani a cikin zuciyata. Kamar a mafarki na soma tsinkayo amon Umma a kusa da ni, sautin da kunnena yake tantance mini shi ya tabbatar mini da a kusa da ni take zaune. "Amatullah". Ta ƙira sunana cikin wata iriyar murya na amsa ba tare da na ɗago kaina ba. Hakan bai ɗaɗata da ƙasa ba ta ci gaba da maganarta. "Ki buɗe idanuki ki kalli abubuwan da suke faruwa a duniyar zahiri. Me ye Amira ta fi ki da shi kyau, diri, sura, asali, zaƙin murya ko kuma sa'a ta fi ki? A bayyane yake duk waɗannan abubuwan da na lissafo kin fi Amira su ban da abu ɗaya shi ne sa'a. Kuma shi ma na yi alwashin sai kin fi ta shi". Muryata a dushashe na ɗago kaina ina faɗin"Umma da kin fara nazari akan hanyar da Amira take bi wajen sayar da tallanta domin shi ne gaba da komai. Wallahi kin ji na rantse miki samari ne suke yi mata juye kuma su suke ba ta maƙudan kuɗaɗe har wayan da yake hannunta saurayi ne ya ba ta. Babu wani sa'a da take tare da shi haƙiƙanin gaskiya kamun kai ne ba ta da shi". Kallon da ta kafe ni da shi ya tilasta mini mayar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran abin da yake faɗi a zafafe alamar ta soma fusata ta kuma zo har wuya. "Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi, Amatullah har ke za ki zaunar da ni kina gaya min abin da ya dace na yi?. Ƴar iskan yarinya marar kunya to ko karuwanci za ki yi sai kin kawo min kuɗin tallan kununa babu gara bin zago, wallahi ba zan ƙara ɗaukar asara ba tun da na lura ba mutunci ne da ke ba shegiya mai mataccen zuciya". Duk yadda zuciyata ta so ba ta haƙuri cikin ƙasƙantar da kai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen furta abin da yake kan harshena, haka ta gama ta tashi ta shiga kicin. Na kasa motsawa daga wajen gabaɗaya na gaza gane abin da yake yi mini daɗi cikin duniyar. Ina jin sallamar yaran da nake yi wa darasi a ƙofar ɗakinmu amma na kasa amsawa balle har na tashi na ji da me ye suka zo, har Umma ta fito ta fararraƙe su suka tarwatse a haka Abba ya dawo ya same ni na ji jugum kamar majinyaciya. Babu nau'in tambayar da bai yi mini ba amma na ce da shi babu komai da ya matse na ce kaina ne yake ciwo. A daren ta fita kemis ya karɓo mini magani na sha sannan na kwanta. Haka na yi ta juyi don bacci sam ya yi ƙauracewa idanuna suna nan ƙamas kamar na kifin da aka tsoma a cikin ruwan mai aka tsamo. Haka na yi ta juyi har aka ƙira sallan assalatu na tashi da ƙyar saboda mutuwan da jikina ya yi na gabatar da sallan a zaune. A ɗaki ya na ci gaba da zama saboda ruwan da aka soma yi kamar da bakin ƙwarya bai tsagaita ba har sai ƙarfe takwas saura. A lokacin na yi ƙarfin hali na bayyano waje na haɗa wuta wanda sai da na ci kwakwa kafin ya ruru na ɗaurawa Abba abin kaci. Kunnu na dama na ɗumama sauran tuwon dare ba kai masa har zan tashi ya dakatar da ni na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraronsa. "Amatullah tun daren jiya na lura da yanayin da kike ciki tabbas akwai wani abun da yake faruwa. Shin mene ne ki sanar da ni komai kar ki yi ƙoƙarin ɓoye min". Sai da na sauƙe gwauron ajiyan zuciya kafin na sama zarafin cewa"babu abin da yake faruwa Abba, kamar yadda na sanar da kai jiya kaina ne yake yi mini ciwo. Bayan hakan babu komai". Ya kafe ni da kallon da ya fi kama da na tuhuma duk da idanuna suna ƙasa amma tabbas jikina ya tabbatar mini da irin kallon da yake yi mini, shuru ya ratsa wajen kafin can ya zarce da cewa"ba na son kin sanya kanki a ciki damuwa Amatullah. Ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi kuma na san ki da shi in sha Allah za ki ga riban hakan ko ba daɗe ko ba jima". "Ai dole ka zaunar da ita a nan kana biya mata zancen banza da na wofi har da cewa wai ta ƙara haƙuri. Ai dole ka ce ta yi haƙuri tun da cutar da ita nake yi ko kuma ka ga alamar ina gallaza mata. Ka taɓa shigowa gidan nan ka gan ta a

Chapter 3 of 24