Khadija za ta sama zuwa ba".
Cikin girmamawa na ce"to Malam". Na juya na fita har na yi ɗan nisa na jiyo muryar Aliyu na tsaya har ya iso gabana ya tsaya har da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa.
Na bi sa da kallo tun daga ƙasa har sama, ƙal-ƙal uniform ɗinsa yake ya sha goga ga ƙamshin wani sanyayyan turare da yake tashi daga jikinsa, hularsa taɓa ni ka sha hadisi fara sol sai sheƙi take yi.
"Tunanin me ye kike yi?".
Na yi masa wani kallo guda na ɗauke kaina tare da cewa"tunanin me ye kuwa zan yi?". Ya murmusa kafin ya ce"tunanin yadda za mu fafata da ke mana, tun wuri ki sauƙaƙawa kanki yawan damuwa don ba za ki taɓa cin nasara akan Aliyu Haidar ba, tun shigowata islamiyyar ni nake yi na ɗaya kuma na lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a duk shekara, na yi bajinta a shekarar wasu ma balle shekarar walimarmu. Har na bar Islamiyyar nan babu abin da zai sauya wannan tarihin don haka ma kar ki sa a ranki".
Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na sama zarafin cewa"Aliyu kenan!. Ai kai ya fi dacewa na ba wa shawarar ka cire tunani daga cikin ranka don da dukkan alama kai hakan ya dama. Ina yi maka fatan nasara a ko yaushe ni ka ga tafiyata". Ina ƙare faɗin haka na bar wajen na nufi aji huɗu domin karɓan haddarsu kamar yadda Malam Aminu ya umarce ni, har na yi na gama raina a ƙutume na yi musu ƙari na fito lokacin har an tashi sallan asr don haka kai tsaye na wuce wajen alwala na zauna na zabga tagumi abin duniya duk ya fi ya ishe ni.
"Ke lafiyarki kuwa? Yau ki haɗuwa ba mu yi ba".
Na tsinkayo muryar Rauda a kusa da ni na zame hannayena daga tagumi da na rafza ina saki tagwayen ajiyar zuciya wani na bin wani.
"Wallahi na fara gajiya da abin da Aliyu yake yi mini a ciki islamiyyar nan".
Ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani"wani Aliyu kenan?".
"Aliyu Shehu mana".
Ta taɓe baki kafin ta soma cewa"kin san Allah Amatullah wannan Aliyun sonki yake yi, matuƙar so ma kuwa. Ke in taƙaice miki bayani mazan ajinsu sun taɓa kama sa yana rubuta sunanki jikin ƙur'aninsa". Wani kallo na watsa mata da ya sanya ta haɗiye sauran zancen ba tare da furta su ba.
"Wani irin banzar magana ce haka Rauda? Sanin kanki ne babu wanda ba ya ƙaunar ci gaba na a cikin islamiyyar nan kamar Aliyu. Ko wani abun bajinta na yi sai ya ƙalubalence ni akan hakan ki na nufin wanda ma duk cikin so ne kamar yadda kika yi ikirari?".
"Ko waɗannan ba su kasance alamomin so ba to tabbas akwai soyayyarki mai ƙarfi a cikin zuciyar Aliyu. Shin ke ba ki lura da wani abu, duk yadda ƴan matan islamiyyar nan suke yi masa shishshigi baya kula su amma ke ko kina so ko ba kya so sai ya nema hanyar da zai yi magana da ke ko da kuwa baƙar magana zai faɗa miki".
Na miƙe kafin na furta"Rauda mu bar wannan maganar don hankali ba zai taɓa ɗaukarsa ba". Ban jira abin da za ta kuma cewa ba na tafi na soma yin alwala na zo na yi salla har iddar tana zaune a cewarta tana fashin salla a lokacin tare muka koma aji muka soma muraja'a cike da shauƙi da soyayyar abin da muke karantawa. Har sai da aka tashi ba mu sani ba sai da muka zo daidai inda muke son tsayawa kana muka yi addu'a kowa ya fito domin tafiya gida.
Tsaye a ƙofar fita na hango Al'amin yana tsaye muka sakarwa juna murmushi yayin da muka haɗa ido, na riƙo hannun Ammi ina cewa"raka ni na je na yi wa Bawan Allahn can godiya".
"In kuka daɗe ni kam tafiyata zan yi don yunwa nake ji". Rauda ta yi zancen tana neman waje ta zauna tana jiran mu, ba mu amsa mata ba illa darawa da muka yi dukkanmu. Da sallama muka isa wajen Al'amin ya amsa mana yana ƙara yalwata annurin fuskarsa.
"Na yi tunanin ai ɓacewa kuka yi a cikin makarantar".
Na murmusa tare da cewa"mun tsaya yi karatu ne".
"Na dai lura ajin matan nan kun dade sosai".
Na ƙara murmusawa a karo na biyu kana na ce"daman na zo na yi maka godiya ne. Tabbas ka cece ni daga tuhumar Malam Aminu".
"Ya zama dole ne hakan Amatullah babu wanda bai san tambayoyin titsiye irin na Malam Aminu ba".
"To ni dai ina godiya matuƙa".
Har yanzu fuskarsa ɗauke take da murmushi ya ce"to yanzu dai mu je na raka ku ko?".
Ammi ta amshe zancen"mu muka ce maka muna buƙata".
Ya harare ta"yau dai ba zan kula ki don masifarki sai dai ki ci kanki". Ban tsoma musu baki ba illa murmushin da na yi muka soma tafiya muka isa wajen Rauda sai dariya muke yi mata don duk ta sauya Ammi sai tsiya take ya mata wai kamar ba ta yin azumi yunwar lokaci guda ta jigata ta har haka. Har muka rabu da Ammi da Rauda, Al'amin bai daina ja na da hira ba har farkon layinmu ya raka ni, muka rabu cikin girmamawa da mutunta juna.
Ina doso ƙofar gidanmu na ji gabaɗaya raina yana ɓaci zuciyata tana tafasa sosai. Haka kawai na nema dukkan nutsuwata na rasa ƙirjina ya tsananta bugu. Sai da na tsaya a zaure na ja dogon numfashi na fesar kafin na ƙarisa cikin gidan, har yanzun Umma ba ta dawo ba don haka wanka na yi na sauya kayana na tattare wasu abubuwan kana na ɗaura mama girki tuwo na yi da miyar bushashshen kuɓuewa na juye a kula, na je wajen Amira don ba na son zama shirun.
Babban dalilin ma shi ne ina son jin haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin Asabe da Malam Vector da ya kai su ga raunana juna, kiciɓus na yi da Ummanta za ta fito na matsa na mata hanya ina yi mata addu'ar a dawo lafiya bayan ta shaida mini za ta je wajen Sa'ade uwar adashe ta kai zubinta.
A falo na tarar da Amira tana kallo a wayanta na zauna kusa da ita tare da fizge wayar, ta bi ni da kallo"har kin dawo?".
"Har ne ma? Watau don ba ke kike zuwa ba dole ki faɗi haka. Amira na yi na yi dake mu shiga islamiyyar nan amma kin ƙi, ina guje miki ranar da wannan damar za ta kuɓuce miki".
Ta gyara zamanta tare da cewa"tun da dai na sama na salla ya ishe ni". Kaina kawai na jijjina na kawar da maganar ta hanyar cewa"wai ni kuwa me ye faru tsakanin Asabe da Maman Vector, Umma ba ta nan balle na tambaye ta".
"Kin san Baban Vector ya dawo daga Benue shi ne Maman Vector ta kama shi da Asabe a cikin ɗakinta suna hira, kin sa ta da shegen kishin tsiya tana ganin haka ba ta wata-wata ba ta ɗauko tafasasshen ruwan zafi ta shiga ta juyewa Asabe a jikinta".
Na dafe ƙirji"na shiga uku. Amma kuwa Maman Vector ba ta kyauta ba ai kamata ya yi ta fara jin dalilin shigarsa ɗakin Asabe".
"Ko ni ce fa zan yi fiye da abin da Maman Vector ta yi, wani dalilin ne zai sanya su keɓe da juna bayan su ɗin ba muharraman juna ba ne".
"Amira kenan. To ai in haka ne ma laifin Baban Vector ne tun da shi ya je har cikin ɗakinta". Ta taɓe baki"koma dai mene ne ni kam Maman Vector ta yi min daidai". Ta gyara zamana ina fuskantan da kyau kana na soma cewa"ni zuwa na yi ma na tambaye ki, ko akwai in da za ki je ne yanzu ko zuwa bayan sallan isha'i?".
Ta yi mini wani kallo kana ta ce"yau ko toyar awara ba zan fita ba amma lafiya kike tambaya?". Na yi ɗan jim kafin na ce"wallahi ba za ki gane ba ne ba na son zaman cikin gidan ne, ko Bashir za ki ƙira mini a waya to mu gaisa?". Tun kafin na rufe bakina na ga ta tsare ni da wani irin kallon mamaki da al'ajabi.
[10/4, 12:16 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 2️⃣7️⃣
Sake da baki da hanci take kallona tamkar wacce ta ga wani sabon halitta, mamakinta ya kasa ɓoyiwa har sai ta furzo shi waje.
"Bashir kuma? Yau da bakinki kike cewa na ƙira miki Bashir?". Na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai nauyin gaske kafin na sama zarafin faɗin"Amira ke fa ko yaushe kike nusar da ni cewar wanda ya nuna yana sonka a rayuwar nan ya gama maka komai, to yanzu laifi ne don na buƙaci ki ƙira mini shi kawai mu gaisa". Ta jinjina kanta"ba laifi ba ne kawai ban yi tunanin za ki buƙaci hakan da wuri ba ne, bari na ƙira miki shi". Murmushi kawai na sakar mata ina miƙa mata wayarta da yake hannuna ta karɓa ta soma lalumo lambarsa, haka kawai na tsinci kaina cikin wani irin yanayi wanda ni kaina ba zan iya fasalts ainihin takamammen abin da nake ji ba, na dai don kawai na sauya daga Amatullah ɗin da nake a can baya.
Manna mini wayar da ta yi a kunne da sauƙar sallamar Bashir a cikin kunnuwana su suka yi nasarar dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na afka.
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na amsa sallamar, jin muryata ya sanya sa sakin wani nishaɗantaccen murmushin da har sai da na ji ilahirin gaɓoɓin jikin sun amsa.
"Tabbas na cika cikakken mai sa'a tun da har Sarauniya da kanta ta ƙira ni yau. Da ina da ikon buɗe ƙirjina da na yi hakan don na gwada miki irin farin cikin da nake ciki a yanzu".
"Uhmm! Daman na ƙira ne don mu gaisa. Kuma na ba ka haƙuri akan abin da ya faru ɗazu".
Tun kafin na rufe bakina ya katse ni"babu abin da za ki yi min a cikin duniyar wanda yake buƙatar sai kin ba ni haƙuri Amatullah, ni ɗin bawanki ne mai hidimta miki kuma zan yi alfahari da hakan a ko'ina kuma a gaba ko waye. Ina da tabbacin ba zan taɓa yin dana sanin sonki ba har abada ki ba ni dama don na gwada miki ƙarfin son da nake yi miki".
Gabaɗaya na ji jikina ya mutu murus na gyara zamana kafin na ce"na ba ka dama". Ina faɗin haka na miƙawa Amira wayar ina rufe fuskata da tafukan hannayena saboda kunyar da yi wa raina mamaya.
Babu abin da Amira take yi face dariya a haka dai suka yi sallama da Bashir bayan na ji da kunnena ya na faɗin ya damƙa amanata a hannunta.
"Lalle ikon Allah! Ashe akwai ranar da za ki ba da kai bori ya hau Amatullah?. Haƙiƙa Bashir ya cika mai sa'a kamar yadda yake faɗa".
"Ban san me yasa ba ban san dalilin da ya sa har na ba shi dama ba Amira. Na dai fahimta kawai ina buƙatar wanda zai dinga kwantar mini da hankali ne wanda zai dinga saurara damuwa da matsalolin rayuwarta, wanda a duk lokacin da nake cikin damuwa zan tsaya a tare da ni. Tun da kin ga Umma ko yaushe ba ta zama a gida babu shaƙuwa a tsakaninmu ba ta da lokacin sauraran damuwata". A raunane na ƙare zancen ƙwalla yana ciko mini kurmin idanuna.
Cike da kula ta Amirka take furta" ko ba ki da wata matsala ma yanzu kin kai muzalin da za ki buƙaci wani a kusa da ke, rayuwar nan sai da farin ciki. Farin ciki kuma ba ya samuwa daga wajen masoyi na haƙiƙa". Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na sama sararin cewa"indai har na fahimci yana da ɗabi'un ƙwarai zan buƙaci ya gabatar da kansa a wajen Abba, don ni ba zan tsaya yin dogon soyayya da mutum ba".
"Ina da tabbaci akan son da Bashir yake yi miki gangariya ce".
Ban ce da ita komai illa gyaɗa mata kai da na yi alamar na gamsu da abin da ta furta, na jingina bayana cikin kujerar da nake zaune tare lumshe idanuna ina jin kaina kamar ba ni ba don ban taɓa tsammanin a nan kusa ko nisa zan iya amincewa wani saurayi ba. Shuru ya ratsa wajen kafin na kawar da shi ta hanyar cewa"wai a gida za ki zauna ne yau ba inda za ki je?". Na yi zancen har yanzu ban buɗe lumshashshun idanuna ba.
"Wai lafiyarki kuwa Amatullah? Sai ka ce wacce take zaune akan wuta a cikin gidan".
"Ba za ki gane ba ne Amira wallahi har raina yanzu ba na ƙaunar zaman cikin gidan nan, indai ba ya zama dole ba". Ta yi ɗan jim kafin ta ce"to ki dai yi a hankali". Na zabura tamkar wacce aka tsigarawa matsilli na buɗe idona tare da cewa"to ko dai gidan Ta salla za mu je?".
"Wai ke lafiyarki kuwa?".
Ta yi saurin katse mini hanzari kallon da ta tsare ni da shi ya tursasa mini yin ƙasa da kaina ina jin wani iri a rai da ruhina. Tashi ta yi ta shiga ciki ta ɗauko hijabinta ta dawo.
"Tashi mu je don na fahimci in dai ba fita muka yi hankalinki ba zai kwanta ba".
Zumbur na yi na miƙe har na riga ta fita daga cikin ɗakin, ina sanya ƙafata na fita daga cikin gidan na ji wani sanyin daɗi yana ratsa ruhina. Nauyin da ƙirjina ya yi mini yana warwarewa a hankali-hankali, gidan Ta salla muka nufa wacce take dafawa Amira awara.
Cike muka iske gidan da samari da ƴan mata, gefe guda wasu sun baje hajarsu yayin da Ta salla take zaune akan garduma gabanta da manyan kulolin abincin da take sayarwa a gida, kusa da ita muka zauna ta bi mu da kallo har muka zauna muka gaishe ta ta amsa tana zarcewa da faɗin"Amira wannan fa ina kika samo ta?". Ta kai ƙarshen zancen tana nuna ni da ƴar manuniyar ƴatsarta.
"Au! Wannan ɗin ce ba ki gane ta Hajiya? Amatullah ce fa ta gidanmu".
Ta tafa hannu gami da rafza salati ta riƙe haɓa cikin mamaki ta ce"lalle girman ɗan mutum ba shi da wuya yanzu Amatullah ɗin Hafsatu ce ta girma har haka? Lalle muna da ƴan mata a unguwan zankaɗa-zankaɗa sai mu yi fatan Allah ya baku mazaje na gari".
"Amin ya Allah".
Muka haɗe baki wajen amsawa, sai a lokacin na sama damar ƙarewa tsari da zubi gami da irin mutanen da suke cikin gidan, a ƙalla mutane za su kai ashirin muka iske a gidan kowa yana harkan gabansa daga fahimtar da na yi ma wasu a gidan suke kwana.
"Har yanzu muna gidan nan nakun ashe? Ciki da falo ne kaman ai ko?". Tambayar da Ta salla ta jefo mini kenan da ya dawo da ni daga cikin karatun wasiƙan jakin da na faɗa.
Na sadda kaina ƙasa na ce"e ciki da falo ne kawai, ai duk ɗakunan gidan ma haka ne".
"Ai kuwa wannan akwai takura a ciki yanzu haka kuke cakuɗuwa da iyayen nakun duk a ɗaki ɗaya?". Kunya ta hana ni cewa komai yayin da Amira babu abin da take yi face dariya har da ƙyalƙyalewa.
Tashin samun amsa daga gare ni ya ba ta lasisin ci gaba da cewa"ai kuwa gwara tun wuri ku nemawa kanku mafita. Ga ku ƴan mata da ku amma ace har yanzu kuna raba ɗaki da iyayenku. Ai gwara ku ɗinga zuwa nan kuna kwana".
"Kwana kuma a nan Hajiya?". Na furta babu shiri ina ware girman idona akan fuskarta da ta gaji da jin man bleaching har ya saduda ya daina amsar man, ta yi jajir da ita tamkar ƙosan da ya ji jawa.
"Ƙwarai kuwa ƴan mata nawa ne akan layin nan suke kwana a cikin gidan nan. Kai wasu ma gabaɗaya rayuwarsu a cikin gidan nan suke gudanar da ita".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina satan kallon Amira na ga hankalinta ba ma a kanmu yake ba. Sai da na haɗo jarumta kafin na iya furta"Hajiya haka dai za mu ci gaba da haƙuri har Allah ya kawo mana mafita, ko kuma mazaje mu yi aure mu tafi gidajenmu".
Ta taɓe baki"to Allah ya kyauta".
"Amin".
Na amsa da shi a taƙaitacce, ba ta ƙara cewa da ni komai illa mayar da idonta kan Amira ta yi ta umarce ta da ta tashi ta ɗauko kwana ta zubo mana abinci na ce na ƙoshi da ƙyar ta tilasta mini akan sai na ci na saka hannu na ɗan caccakala abincin sai da muka yi sallan isha'i kafin muka fito za mu tafi. Cike ƙofar gidan yake da masu jaura babu wani nau'in abincin da ba a sayarwa a wajen, ƴan shaye-shaye sun yi bataliya a wajen sai cin karensu suke yi babu babbaka.
Gabaɗaya jikina ya yi sanyi luƙus haka har muka isa gida jikina babu kuzari ba mu iso gida sai kusa ƙarfe tara da wasu mintuna na dare. Muna shiga gidan tun daga zaure na fahimci Abba ya dawo gaba ya soma faɗuwa har muka ƙarisa ciki. A ƙofar ɗakinmu na hango Abba yana tsaye ya naɗe hannayensa a bayansa idanunsa akan hanyar shigowa take na sha jinin jikina na kasa ɗago kaina. Ko gaisuwar da Amira ta yi wa Abba bai amsa ba ya juyo ya shige ciki ya bar ni cikin tarin fargaba.
"Amira na shiga uku, me ye zan cewa Abba?".
Na yi zancen a rikice muryata har yana shaƙewa tsabar rikicewar da na yi. Ta riƙo hannuna saboda gabaɗaya jikina rawa yake yi tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki.
"Ki kwantar da hankalinki mana komai zai zo da sauƙi. Idan ya tambaya ki ce raka yi kika gidan Sa'ade mu kai zubin adashen Ummata".
"Amira ke ma kin san ai dole ne ya tambaya".
"Ki nutsu kawai don in dai kika shiga a wannan yanayin duk abin da za ki faɗa ba zai shiga kansa ba".
Kaina kawai na jinjina mata alamar na ji muka yi wa juna sai da safe kafin na shiga cika. Sai na da na aro jarumta da ƙarfin hali na yafawa kaina kafin na sama ƙwarin gwiwan shiga ciki bakina ɗauke da sallamar da sai na yi baki biyu kana a yunƙuri na uku na ji Abba ya amsa mini tare da ba ni iznin shigowa. Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na shigo cikin falon kaina a ƙasa kamar wacce ta ƙullawa Sarki sharri na zo na zauna ina yi masa sannu da zuwa maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini tambaya.
"Daga ina kuke?".
"Na'am".
"Na ce daga ina kuke a cikin daren nan?". Ya kuma maimata mini tambayar a karo na biyu cikin tsawar da ya haifar mini da runtse idanuna.
"Abba ka yi haƙuri".
Na furta hawaye masu ɗumi suna gangarowa daga kurmin idaniyata.
"Ba abin da na buƙata ba kenan. Amatullah daga ina kuke kuma waye kika tambaya kafin ki yi?". Sosai jikina ya ɗauki kyarma don duk ranar da Abba ya ƙira sunana kai tsaye to tabbas magana ce mai girma zai yi da ni ko kuma ransa ya kai maƙura wajen tunzura.
"Wai me yake faruwa ne nake jin ka na ta ɗaga murya?".
Furucin Umma kenan yayin da take fitowa daga cikin ɗaki ta iso cikin falon ta zauna, Abba ya irge mata komai da ya wakana.
"Don ta fita shi ne kake ta tada jijiyoyin wuya haka Manniru? So kake yi mu garƙame ta a cikin gidan mu dafa ta mu cinye kenan?. Ni fa ba zai yiyuwa ka tisa min ƴa a gaba kana ɗaga mata murya ba ba zai yiyuwa. Kai ba ka bar ni ba ƴan uwanka ma ba su bar ni ba, da wanne kuke so na ji ne?".
"Hafsatu ki bar ni da yi iko da ƴarta don ni Allah ya ɗaurawa nauyin kula da tarbiyanta. Ba zai yiyu na zuba ido ina ji ina gani ta lalace ba, wani abu ne zai fitar da ita da dare wanda ba ta yi sa ba tun ido na ganin ido?. Daga yau sai yau idan na ƙara dawowa ban tarar da Amatullah a cikin gidan nan daga ke har ita sai na saɓa muku saɓawa mafi muni".
Tsam Umma ta miƙe tamkar kububuwa jikinta har wani rawa yake yi ta nuna Abba da ƴatsarta haɗe da cewa"Manniru ba ka isa ba wallahi ka yi tsararo".
"Ai kuwa yau zan nuna miki cewa na isa a gidana". Ya yi zancen shi ma yana miƙewa akan ƙafafunsa cikin tsananin ɓacin rai.
Ta matsa kusa da shi tana nuna kanta"ni kake ɗagawa murya? Ni kake kallon tsabar idona kana furta min duk abin ya fito daga bakinka? Tabbas ka kyauta kuma na gode". Tana dasa aya ta juya ta shige cikin ɗaki tare da turo ƙofar ta murza masa makulli. Cikin wani irin sauri kamar mayan ƙarfe haka Abba ya bi bayanta ya soma dukkan ƙofan yana magana.
"Hafsatu ki yi haƙuri ki buɗe ƙofar nan ki fito mu zauna mu fahimci juna. Kar ki kwanta da baƙin cikina a cikin ranki hakan sai ya fi komai ƙona min rai". Har ya yi ya gama jawabinsa Umma ba ta tanka masa ba balle ta buɗe ƙofar, haka ya yi ya gaji ya komo ya zauna ya zabga tagumi.
Na ja jikina na matso na riƙe ƙafafunsa ina kuka don yadda na so na yi masa jawabi na rasa wannan ƙwarin gwiwan, saboda kukan ya gama cin ƙarfina ainun. Da dukkan ƙarfina nake kuka da take jikina ya ɗauki zafi kaina ya yi mini wani irin nauyi tamkar an ɗaura mini dutsen dala na jihar Kano a tsakiyar kaina.
"Ki daina wannan kukan komai ya wuce ki je ki kwanta. Dare ta yi yanzu".
Ya yi zancen yana zare ƙafarsa daga riƙon da na yi masa. Ya miƙe tsaye na yi wuf na ƙara riƙe sa sai a lokacin na sama damar yin magana.
"Abba to ina za ka je?".
"Zan je masallaci na kwana, kar ki manta ki rufe ƙofar".
Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya jira abin da zan ce ba. Na daɗe zaune a wajen ba tare da na motsa ba ina kuka kafin na tashi na lallaɓa na fito waje na yi alwala na koma ciki na gabatar da salla raka'a biyu. A falon na kwanta bayan na rufe ƙofar na kashe wuta, gabaɗaya na rasa gane mai yake yi mini daɗi idan na tuna Ni ce silar faruwar duk abin da ya faru sai na ji zuciyata ta ƙara karyewa hawaye sun soma ambali a kuncina.
Maganganun Hajiya Ta salla ta soma dawo mini cikin kwanyata tabbas da yanzu ina da wajen kwana da Abba ba zai fita ya kwana a masallaci ba.
[10/6, 3:36 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 2️⃣8️⃣
Haka na ci gaba da juyi na kasa runtsawa har aka yi ƙiran sallan asubahi, da ƙyar na tashi saboda nauyin da gabaɗaya ilahirin jikina ya yi mini na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da zauna. Sosai kaina yake yi mini ciwo tamkar zai faɗo ƙasa ko zai rabu zuwa gida biyu, runtse idanuna na yi ina jin yadda ɗakin yake juya mini ina jin rufin ɗakin tamkar zai rikito a kaina.
Na kifa kaina akan gwiwa ina karato farkon suratul Maryam ban gushe ina yi ba har sai na ji sauƙin lamarin na zame ns kwanta akan sallayan babu jimawa wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.
Tamkar a cikin mafarki na ji ana ƙiran sunana na buɗe idanuna da ƙyar ina jin ciwon kan ma tamkar ƙaruwa ya yi maimakon raguwa. Na tashi na zaune dafe da goshina da jijiyon kaina suka fito suka yi ruɗu-ruɗu ina kallon Umma da take tsaye a kaina dishi-dishi. Na yi ƙarfin halin jefa mata gaisuwa sai dai ko gizau ba ta yi balle ta amsa illa kallo
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 24