Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sama ma su tsigare ki ma daga cikin addinin. Don haka ki rufa mana asiri ki rufawa kanki asiri". Sallamar Umma shi ya sanya ni haɗiye maganar da na yunƙuro da nufin furtawa, ni da Amira muka haɗe baki wajen yi mata sannu da zuwa ta amsa mana a taƙaice tana wucewa cikin ɗakin. "Kin ga ni bari na je na karɓo awarata, na fita soya". Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, na yi banza da ita na ƙi kallonta. Fahimtar abin da nake nufi ya sa ta ci gaba da magana. "Na manta ban sanar da ke ba, ɗazu Bashir ya ƙira ni wai yana son jin muryar sarauniyar mata tauraruwar birnin zuciyarsa....". Ba ta ƙarisa ba na ɗauki pillown kujerar na jefa mata ta fice cikin sauri tana ƙyalƙyala dariya. Tsaki na ja kafin na tashi na shiga ɗaki wajen Umma tana tsaye tana duba cikin kayanta na iske ta da alama wani kayan take nema. Na tsuguna kafin na ce"Umma ga can abinci na gama a kawo miki nan ne, ko za ki fito?". Kamar ba za ta amsa mini ba sai can kuma ta yi magana kamar wacce aka yi wa dole. "Me ye kika dafa?". "Taliya". Na amsa da shi kaina yana ƙasa. "Ba na jin sha'awar cin taliya ki je ki cinye kawai. Idan Manniru ya dawo sai ya je ya sayo min fankasau da miya". "Fankasau kuma Umma? A cikin wannan daren a ina za a samu a nan kusa". Na yi maganar da ban san lokacin da ya fito daga bakina tsabar kaɗuwar da na yi da zancen. Ta bar abin da take yi ta juyo tana kallo na kamar wacce ta yi tozali da wani abun al'ajabi. "Amatullah ba ni da ƴancin cin abin da raina yake so kenan a cikin gidana?". Na jijjiga mata kaina"a'a Umma amma wallahi ba a sayar da irin wannan nau'in abincin a nan kusa. Kuma kin ga Abba idan ya dawo yana buƙatar hutu, don Allah ki yi haƙuri ko awara ce sai na karɓo miki a wajen Amira....". Kafin na rufe bakina na ji sauƙar mari a kuncina da ya gigita ni da na yi zaman dirshan. Cikin kauraran amo ta soma magana tana nuno ni da ƴar manuniyar ƴatsata. "Na yi miki iyaka da shi shiga abin da babu ruwanki mussamman abin da ya shafi tsakanina da mahaifinki. Duk abin da zan yi a cikin gidana na ki ido ne, idan kuwa kin yi kunnen uwar shegu da zancen ai jiki magayi". "Ki yi haƙuri Umma ban yi don na ɓata miki rai ba. Don Allah ki yafe mini". Rufe bakina ya yi daidai da sa'ilin da Abba ya shigo cikin ɗakin idanuna suka sauƙa a kansa, da hakan ba wa hawayen da suka wadaci koramar idanuna damar kwaranya kamar an kunna burɗaɗɗan famfon burtsatse. "Lafiya na gan ku haka duk a hargitse?". Umma ta buga wani uban tsaki tamkar wacce ta yi arba da kashi, ta juya ta ci gaba da abin da take yi. Na tashi ina yi Abba sannu da zuwa na kai hannu zan amshi ledar da yake hannunsa ya dakatar da ni. "A'a wannan saƙon Ummanki ne". Ya juya yana fuskantar inda take kafin ya zarce da cewa"Hafsatu ga abin da kika buƙata na taho miki da shi".Ta ɗaura hannu aka ta buga salati da sallallami. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Ni kam na shiga tara ma ba uku ba, wai a cikin ɗakina ma ba za a bar ni na huta ba. Manniru me ye kake so da ni ne? Kai ƙaramin yaro ne ko mene ne. Don ka sayo min kilishi shi ne sai na amsa da hannu ko me ye kake so da ni? To ba na cin kilisin fankasau da miya raina yake so". "Fankasau kuma Hafsatu?". "Ƙwarai kuwa". Ya yi shuru yana jijjiga kansa bai ce komai ba ta juya ya fita daga ɗakin. Dole ni ma na tashi na fita na yi sauri na cimma Abba a zaure yana ƙoƙarin fita. "Don Allah Abba ka koma ka huta yanzu fa ka dawo cikin gidan, bai dace ka ƙara fita ko'ina ba. Ka ba ni kuɗin ni zan je na nemo mata fankasau ko a ina ne a cikin garin nan". Ya tsaya kawai yana kallo hasken farin watan da ya gauraye ko'ina shi take ba ni damar kallon fuskarsa tar. "Amatullah ni ya dace na fita na nemo mata, don haka ki koma ciki ki zauna. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru da ni". Zan yi magana ya ɗaga mini hannu"ki koma kawai". Muna cikin haka Amira ta shigo ta gaishe da Abba ya amsa mata a taƙaice da ido na yi mata alama akan babu lafiya. Hakan ya sa tambayar Abba ko lafiya. "Lafiya lau Amira zan ɗan fita ne amma yanzu zan dawo". "Abba idan wani abun kake buƙata ka ba mu mana sai mu je mu nemo maka..". Tun kafin ta ƙarisa ya taka mata burki"ku shiga gida kawai na ce". "Ko mun shiga hankalinmu ba zai kwanta ba matuƙar muka bar ka fita yanzu. Abba tun safe fa kake aiki kamata ya yi yanzu ka zauna ka huta, yayin da mu kuma za yi maka hidima". Ya yi ɗan jim yana kallon ta sai dai bai ce ko kanzil ba. "Me ye amfaninmu idan ba za mu iya samar maka da nutsuwa ba. Amfanin haihuwar kenan fa Abbanmu, ka sanar da ni abin da za a sayo maka matuƙar akwai shi a cikin garin nan sai na kawo maka shi gabanka kafin ka kwanta bacci". Ya ja dogon numfashi ta fesar kafin ya ce"to shikenan fankasau da miya nake so, amma kar ku bata lokaci idan ba ku samu ba ku dawo kawai". Ya kai aya yana zaro naira dubu ɗaya daga aljihunsa ya miƙa mata ta ƙarba kana shi kuma ya koma ciki. Tana wucewa ta ja hannuna muka fita waje muka tsaya. "Sanar da ni me ye yake faruwa ne?". "Amira mu fara neman fankasau ɗin tukunna. Yanzu a ina kike ganin za a samu?". Ta yi shuru kamar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"zo mu je akwai inda nake da yaƙinin za mu samu". "To soyar awaran fa?". "Na gama don yau na fita a sa'a. Tun kafin na fara soyawa aka saye ta dukka". Tana kai wa aya ta ja hannuna da ƙarfi muka bar wajen. [8/10, 3:10 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 2️⃣0️⃣ Tafiya muka soma yi bar cikin layin gabaɗaya muka tsaya a bakin kwalta, zan iya rantsuwa akan cewar tun da uwata ta haife ni ban taɓa fitowa wajen a irin wannan lokacin ba sai ga shi yau ƙaddara ta jayo ni inda ƙafafuna ba su taɓa tunanin zuwa ba. Na cika da mamakin ganin yadda ƴan mata da samari suke ta wucewa daga wajen yayin da wasu kuma suke hira har da masu yin hoto. "Amira yau ina za mu je da muka zo nan muka tsaya?". "Fankasau za mu nema mana Amatullah". Na tsayar da idona akan ta"ban ga alamar abin da abin da kika faɗa ba" Ta fito da wayarta ta soma latsawa tana ƙiran wani layi bugun farko aka ɗaga aka fara magana. "Amira zah big girl yaya aka yi". "Babe gani a bakin hanya ka fito in kana kusa". "To ranki ya daɗe". Ya amsa da shi a taƙaice yana kashe wayar, mintuna kaɗan tsakani ya iso waje sosai na tsorita da ganin yanayinsa don babu alamar nutsuwa ko kaɗan a tattare da shi balle a yi zaton samun sanin hukuncin addini a tattare da shi. "Bane ya me ye da akwai ne?". Ta shagwaɓe fuska kafin ta soma cewa"fankasau nake son ci a cikin daren nan". Ya waro idanu waje kafin ya fashe da dariya har da tafa hannun. "Fankasau kuma Babe? Yanzu ina zan sama fankasau a cikin daren nan. Ni tukunnan ma me ye wannan fankasau ɗin nan ne da ya ɗag miki hankali cikin daren nan har kika fito?". "Ni dai wallahi ji nake yi kamar zuciyata za ta fashe idan ban ci fankasau ɗin nan ba". Bai ce komai ba illa dariyar da ya ci gaba da yi yana tafa hannu tare da shafa ƙasuban da ya yi wa fuskarsa ƙawanya. Ta riƙo hannuna ta riƙe gam a cikin nata tana dubansa ta ce"dole ka tisa ni gaba kana yi min dariya ai tun da kana magana da mahaukaciya wacce ba ta san abin da nake yi ba, duk duniya kai ɗaya na zaɓo kamar tumu. Tun ka nuna gazawarka a gare ni na gode Almustapha". Za mu wuce kawai na ga ya riƙo ɗayan hannun natan ya riƙe. Na cika da mamakin ganin ba ta dakatar da shi ba balle ta yi wani yunƙurin tsawatar masa. "Common Babe ai duk inda fankasau yake a cikin garin nan sai na nemo miki shi. Ina zan tsoma raina na ji sanyi ahalin kina fushi da shi, bari na ɗauko mota sai mu je global delight na san babu abin da za a rasa a nan". Ta yi banza da shi ba tare da ta tanka masa ba. Ya wuce ya bar wajen da hakan ya ba ni damar furzar da abin da ya tokare mini ƙirjina. "Ke wai ina zamu je har da mota? Ki rufa mana asiri Amira". "Nan kusa ne fa yanzu za mu dawo ai". Kafin na yi wani magana tunin har ya iso wajen da mota ta ja hannuna muka isa wajen muka shiga gidan bayan saboda akwai abokinsa zaune a kujerar mai zaman banza. Muna shiga cikin motar ya fige ta tamkar zai tashi sama ya cilla motar a bisa titi. "Babe wannan ƙawar takin ba ta magana ne?". Kalamansa suka dawo da ni cikin duniyar zahiri daga na tunanin da na faɗa. "Amatullah ba ta cika magana ba ne shi yasa". Abokin nasan ya amshe zancen"au sunanta Amatullah kenan? Sunan a dace da ita. Kyakkyawan sunan da kyakykyawar halitta ya dace daman". Ban kula su saboda tsoron da ya gama cika ni duk gudun da yake yi ji nake yi kamar ba sauri, ban ce komai ba har sai da na ga ya tsaya ya faka motar a cikin wani babban fili gefe guda ina hango wani babban wajen da aka rubuta sunan wajen da manyan harrufa suna wani walwal da wuta yana sauya kala daga ja zuwa shuɗi. "To Babe mu je ko". Almustapha ya furta yana ɓalle murfin motar ya fita Amira ita ta fita, ya rage daga ni sai abokinsa a cikin motar. Zuciyata sai bugawa take yi haka siddan na gaza gano dalilin harbawanta fiye da kima. "Ƴan matan mu yi amfani da wannan lokacin mana kafin su fito". Saurin ya yi wa ƙofofin kunnuwana dirar mikiyar da ya sani hanzarin kai duba na zuwa ga inda na jiyo sautin. Ban san lokacin da har ya dawo bayan motar ya zauna dab da ni ba har ina iya jiyo fitar numfashinsa ya ƙura mini idanu kamar zan cinye ni ɗanya. "Malam ka fita tun kafin na kurma maka ihu". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya har da ƙyalƙyalewa, takaici ya cika ni na yi fam babu shiri na soma ture sa daga kusa da ni amma ƙarfina ya gaza don ko gizau bai yi ba balle na haƙata ta cimma ruwa. Mutuwar zaune na yi yayin da na cafko dukka hannayena ya haɗe su waje duka ya riƙe, ya fizgo ni na faɗo kan ƙirjinsa. Na runtse idanuna da mungun ƙarfi hawaye suna kwaranya. "To yanzu ki yi ihun na ji, kina tunanin ko kin yi ihu anan akwai mai kawo miki ɗauki ne? Ko an samu ma to duk ire-irena ne nan wajen babu wani mutumin kirki da yake ko wucewa ta hanyar balle har ya faka a nan. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi mu gama a wuce wajen, ni ba baƙon zafi ba ne shafa jikin ma kawai ya isa ya gusar min da ishina akan ki". "Allah ya haramta abin da zake ƙoƙarin aikatawa, ba saduwa ba ce kawai zina akwai hanyoyin aikata zina da dama. Abin da kake ƙoƙarin yi yanzu yana ɗaya daga cikin su, ka cika mini hannayen duk kafin na yi maka mummunan raunin da duk sadda ka gani sai ka tuna da ni". Da alama bazaranar da na yi masa ba su shige ba, ya ci gaba da cewa"ki yi duk abin da za ki yi. Amma ni dai kam sai na aiwatar da ƙudurina". Kafin ya rufe bakinsa tunin na fizge hannayena daga cikin nasan na soma kai masa yakushi da cizo ta ko'ina har sai na kai shi ƙasa ya kwanta akan seat ɗin, na cire takalmina ina kai masa duka da shi cikin tafasar zuciya da ɗacin rai. Ina cikin haka na hango Amira da Almustapha sun dosa wajen hakan ya sani furta"ka tashi ka koma mazauninka tun kafin na tona maka asiri". Tsam ya tashi ya zauna ta tsakanin kujerar direba da na mai zaman banza ya wuce izuwa mazauninsa yayin da na kimtsa kaina na zauna. Har Amira ta shigo ta rufe ƙofar Almustapha ya ja motar ban ko kalle ta balle na ce da ita wani abu, tamkar talgen da aka aza bisa wuta haka zuciyata take tafasa ina jin wani ɗaci yana gauraye mini dukkan wani kusurwan bakina yana bi har ta cikin maƙoƙarona. Na daɗe da yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa ba ta kaina wani ya yi amfani da ni alhalin ina cikin hayyacina ba. Sai dai ya yi amfani da abun da zai gusar mini da hankali kafin ya kai ga cimma burinsa a kaina. Jin motar ta tsaya ya sani dawowa daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa. Na ɓalle murfin motar na fito na tsaya ina jiran Amira. "Ki yi min abin da tun da uwata ta haihu ni ba a taɓa yi min irin sa a cikin duniyar bariki ba. Ina mai tabbatar miki da duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, sai na fanshe abin da kika yi min a lokacin da ba ki da wani abun da za ki kare kanki da shi". Na cira kai ina kallonsa yayin da yake furta zancen cike da ƙwarin gwiwa yana tsaye a gabana, na galla masa harara kafin na soma furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan raina. "Da Allah a dogara kuma na yi imanin duk wanda ya jingina yarda da yaƙininsa zuwa gare shi ba zai taɓa kunyata ba, balle tozarta. Don haka ni kai ɗan halak ka fasa". Na ƙare zancen ina jefa idanuna cikin nasan, na daɗe da yakice wannan tsoron a cikin raina, wannan dalilin ya sanya ko kaɗan kalamansa ba su yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba balle su haifar da tsoro a cikin raina. Kafin ya yi wata maganar Amira ta iso wajen ban tsaya ɓata lokaci ba ya ja hannunta muka bar wajen har sai muka tsallaka titi kafin na sakar mata hannu, daidai lokacin da ta sama sararin jefa mini tambayar lafiya?. Na yi kunnen uwar shegu da ita na ci gaba da tafiya ita ma ta yi banza da ni har muka iso gida cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil. Muna shiga zaure ta riƙo bayan hijabina na juyo a fusace ina kallonta. "Ga shi in kin ga dama ki ɗauka in kin ga dama ki bar shi a wajen. Tun dai ke duk abin da mutum zai yi ba ya yi miki gwaninta". Ta ƙare zancen tana ajiye mini ledar da ke hannunta a gabana, har za ta shige ciki na dakatar da ita. "Ki yi haƙuri Amira wallahi raina ne a ɓace, da ya kai matakin da har na kasa sarrafa fushina". "In ce dai ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni ko? Don haka sai da safe". Na yi wuf na sha gabanta tare da zayyana mata duk abin da ya faru, ita ma kanta na hangi mamaki kwance akan fuskarta. "Amatullah me ye kai sa'in'sa da shi? Irin su fa billahillazi ba a yin ja-in-ja da su yanzu kana zaman zamanka sai su jawo maka wata masifar da babu mai iya fitar da kai. Shin ke ba ki san hanyar da za ki bi ki kuɓuce masa ba sai kin bi wannan hanyar". "Magana ake fa ta kare mutunci da kimata Amira. Shin na yi laifi don na kaina da kimata?". "Ba za ki gane ba Amatullah amma ina fatan nan gaba kaɗan ki gane duk karantun da nake yi miki, ba tare da kin nema fassaran su". Na sauƙe gauron numfashi kafin na furta"ba na fatan na gane wannan karatun har duniya ta naɗe". Ba ta ce da ni komai ba illa jinjina kanta da ta yi ta wuce ciki, nima na rufa mata baya bayan na ɗauki ledar. A ƙofarmu na hango Abba tsaye yana riƙe da tocila a hannunsa kallo guda za ka yi masa ka fahimce nutsuwa da kwanciyar hankali sun yi hijira daga gare sa. Yana ganina ya iso inda nake cikin hanzari. "An samu kuwa Amatullah?". "E an samu". Na amsa da shi yayin da nake miƙa masa ledar dake hannunsa, sai da ya sauƙe numfashi kafin ya duba ya gani ya ce"alhamdulillah! Allah ya miki albarka Uwata, wuce mu je ciki". A raunane na amsa da kalmar amin na wuce gaba yana baya na har muka shiga ciki. Na zauna a falo yayin da shi kuma ya wuce cikin ɗakin wajen Umma. Tun ina lissafin fitowarsa nan kusa har sai na kishingiɗe ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba, sai ji na yi kamar a mafarki ana ƙiran sunana na yi firit na tashi. Kafin na tsinkayo muryar Abba. "Ki tashi ki je ki kwanta dare ta yi". Ban ce komai ba na wuce ciki na kwanta saboda gajiyar da na yi jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, ko sallar asubahi a makare na yi ta bayan na iddar na soma karatun alƙur'ani har lokacin Umma ba ta tashi ba, shigowa huɗu yana tambayar ko ta tashi na ce masa a'a. Har sai da na yi shara na shigo ɗakin na samu a sa'ilin take tashi na tsuguna har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini a daƙile. "Umma me ye za a ɗaura?". Ta yi banza da ni sai can ta ce"ki dafa ko ma mene ne". "To". Na amsa ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin ta tsayar da ni. "Zo ki ɗauki wannan ledar fankasau ɗin ki fitar min daga ɗaki". Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je na ɗauki ledar sai jin ta da nauyi alamar ba a ma buɗe ta ya hana ni fita. "Umma ya kamar ba ki ci ba?". "Ba a kawo min ita a lokacin da nake so ba ne". "Umma da kin yi haƙuri kin ci ko kaɗan ne. Wallahi ba ki ga irin ƙoƙarin da Abba ya yi ba, har kasa kwanciya ya yi sai da ya ga an samu miki fankasau ɗin nan. Ko kaɗan ki ci ai shi ma zai ji daɗi....". Kallon da ta tsare da ni shi ya tursasa mini yin shuru ba tare da na gama furzar da zancen ba. "Ba zan ci ba idan kuma dole ne cin sai kin sani dole na gani". Na sadda kaina ƙasa kafin na ce"ki yi haƙuri". Na fita daga ɗakin na je ƙofanmu na zauna na tisa ledar a gaba na zabga tagumi ina hashasho irin abubuwan da suka faru da ƙoƙarin da muka yi da Amira kafin mu samo fankasau ɗin nan. "Tunanin me ye kike yi kuma?". Muryar Amira ta sauƙa a kunnuwana. Na bi ta da kallo yayin da take ɗauko kujera ta zauna kusa da ni kafin na yi magana da ci gaba da cewa"wannan ba ledar jiya ba ce?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta buɗe ganin ba ci ba ya sa ta kallona tana faɗin"ya haka kuma Amatullah?". "Yadda kika gan shi ni ma haka na gan shi, Umma ta ce ba za ta ci ba wai ba a kawo mata shi a lokacin da take buƙata ba". "To Abba kuma ya ya ya yi?". Na zame hannuna daga tagumin da na zagba kafin na ce"ya ya zai yi kuwa? Dole shi ma ya haƙura ai". Ta saki dariya mai matuƙar sauti da hakan ya sani kafe ta da ido. "Mata masu duniya, lalle Umma ta na sha'aninta. Tana gara Abba kamar ƙwallon tamula wallahi shi yasa wani lokacin har cikin raina take burge ni don mazan yanzu sun zama zuma dole sai da wuta". [9/21, 10:16 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________________ Page 2️⃣1️⃣ Harara na bi Amira da shi da ta yi furucin tana sheƙewa da dariya gami da tafa hannu. "Ke Amira ba na son rainin wayo fa, me ye hakan kuma? Yanzu wannan abun ne ya zama abin dariya a wajenki?. In ce dai da ke muka sha wuyar nemo wannan fankasau ɗin na yi tunanin ai za mu haɗu ne mu taya juna jimami da takaici, amma sai ki bige da dariya". Na ƙare zancen a kulefe don ba ƙaramin cusa mini takaici dariyar tatan ta yi ba. "Ki yi haƙuri ƙawata, me ye laifin maganata fisabillillahi? Ai ni ina ga hakan ma abin alfahari ne gare ki da tunƙaro. Ko a gaban waye za ki tinƙaho ki bigi ƙirji domin mahaifiyarki sarauniya take a cikin a wajen mahaifinki kuma tana iya juya gidan kaman waina a bisa tanda". Na bi ta d irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce kafin na furta"yanzu ke a irin tunaninki wannan abin wayewa ne?". Ba tare da shakkan komai ba ta ce"ƙwarai kuwa, ai duk wacce kika ga mahaifiyarta ta isa da gidansu ta huta gaba da baya kuma ta wuce raini". Na jijjiga kaina tsabar takaicin da ya zarge muni wuya ya haifar nuni da wanzuwar ɗaci a cikin maƙoƙarona. "Wani lokacin idan kina yin magana sai ki jefa ni cikin tunani, na yi ta hashashen anya kina amfani da ilmi da hankalinki kuwa wajen haɗa kalmomin da bakinki zai furta. Amira ina wayewa a cikin wannan lamarin? Yanzu fa in gaya miki gaskiya samari sun waye ko aure za su nema sai sun tabbatar da cewa uban yarinyar ya isa da gidansa, kuma yana da cikakken ikon zartar da ko wani irin hukunci ta yadda ko kara ya ajiye babu bai ƙetare shi". "Wannan kuma ra'ayinki ne. Kin faɗi naki ni ma na faɗi nawa, don haka kowa sai ya riƙe na shi". Tana ƙare zancen ta soma cin fankasau ɗin zallarta ba tare da ta haɗa da miyar ba. Ban ƙara cewa da ita komai ba har izuwa lokacin da Umma ta fito daga cikin ɗaki, Amira ta gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa kafin ta juyo gare ni. "Wai ina mutumin nan ya shiga ne?". Cikin rashin fahimta na ce"Umma waye fa kenan?". "Waye kuwa ban da wannan lalatacceb uban nakin. Ina magana kin wani tsare ni da ido shegiya tanbaɗaɗɗiyar yarinya wacce ba ta yi gadon abin azurki ba". Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau har da na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, muryata a shaƙe na furta"tun safe da ya fita har yanzu bai shigo ba". "Haba! Ke kuwa baiwar Allah ki dinga sasauta harshenki mana akan yarinyar nan. Wallahil azim bakin uwa guba ne ga ƴaƴansa wanda da yawan uwaye ba su san hakan ba". Furucin ustazun gidan kenan wanda bai daɗe da kama hayar ɗakin da yake kusa da na Naman Vector ba, daga shi sai matarsa amarya wanda a cewarta aure su wata huɗu kenan. "To fa! Ɗankari manƙari har da su kaza acin ɗanko?. Wanene kake da suna?". Ya yi hanzarin faɗin"Abdulwahab nake". Umma ta gyara tsayiwarta kafin ta ci gaba da furzar da zantukan dake kan harshenta masu nauyin gaske, wanda kunnuwa ba za su yi mararin ƙara sauraran su ba ko da bisa kuskure ne kuwa. "Zan ɗaga maka ƙafa ne kawai don kai baƙo ne a cikin gidan nan, amma wallahi bacin haka babu abin da zai dakatar da ni daga yaga maka rigar mutumci a tsakar gidan nan a gaban kowa. Don ni

Chapter 11 of 24