riga da ya faru, sai dai a kiyaye gaba". Na galla mata harara kamar idanuna za su faɗo.
"Hajiya an cuce ni a cikin gidanki ai dole ki ce mini haka. Me yasa tun farko ba ki sanar da mu cewar kowa yana da ikon shiga kowani ɗaki ba a kowani lokaci? Me yasa kika bari aka cutar da ni cutarwa mafi muni da raɗaɗi da zai ci gaba da bibiyar rayuwarta har zuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikina?. Hajiya me na yi masa ya aikata hakan a gare ni?". Na ƙare zancen ina sulalewa ƙasa saboda gaza ɗaukana da ƙafafuna suka yi na durƙushe ina kuka da tun sautinsa yana fita har ya dishashe.
"Amatullah ki tambayi kowa a cikin unguwan nan zai faɗa miki cewar gidana akwai tsari da kuma dokoki daki-daki. Na fi zargin kin taka sawun ɓarawo ne kawai domin nan ɗakin Ramlatu ƴar gold ne sai dai in wani jagwal ɗin ta haɗo kai kuma ya faɗi akan ki. Tabbas Ramlatu ƴar hau ce ta bugawa a jarida". Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli.
"Wace ce Ramlatun? Don yanzu haka tana ina?". Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ita ce mai ɗakin nan kuma yanzu haka tana can ƙauye amma bari na ƙira ta a waya". Tana ƙare zancen ta shiga latsa wayarta bugu biyu aka ɗauka ta soma magana.
"Kina ina ne?". Daga ɗayan ɓangaren aka amsa da"ina ƙauye mana. Bashi ko tara kike yi min waɗannan tambayoyin?".
"Ramlatu akwai wanda kuka yi da shi za ku haɗu ne, a cikin ɗakinki?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"babu wanda muka yi da shi, amma na san ko an zo nema na ma ba zai wuce Mus'bahu ba. Kin san shi kaɗai ne yake zuwa har gida ai kuma ba shi da shamaki da ɗakina".
Ta ɗaura hannu a ka"shikenan Musbahu ya cuce mu ya tona mana asiri. Duk abin da kike yi ki bar shi da asussubahin gobe ki dawo, don wata wuta ce ta kunno kai". Daga haka ta datse wayar duk muka zauna jigum-jigum, zaman dirsham na yi kukan ma na gaza samun ƙarfin yin sa balle wani motsi mai ƙarfi ina jin numfashina yana sama yana ƙasa. Take na ji kaina yana juyawa duk da ina zaune ne sai da na yi lu zan faɗi Amira ta yi saurin riƙo ni na faɗo jikinta.
"Hajiya ya kamata fa mu kai ta asibiti. Don wallahi ni kam lamarin nan ya fara ba ni tsoro, kin ga fa jijjiga take yi".
"Ƴar nan ai ba zai yiyuwa a kai ta asibiti a wannan yanayin, da zaran mun saka ƙafa mun fita to asiri fa ya tonu mutumcinta da na iyayenta ya zube. Kin kuma san ance mutumci madara ne in ya zube ba a iya kwashewa, akwai wani likitan da zan ƙira zai zo har gida ya duba ta". Ta ɗaga waya ta yi ƙira babu jimawa ta fits ta je ta shigo da mutumin, lokacin gabaɗaya na cire rai da ci gaba da numfashi a doron duniya, na fidda rai ga rayuwa. Da taimakon Amira na tashi na zauna bayan ta sa mini matashi na zauna a kai likitan ya duba ni kana ya soma jero mini tambayoyi.
"Da alama wannan ne karon farko da kika taɓa saduwa da wani ɗana miji a rayuwarki ko?". Na ji tambayar ta tsaya mini a rai kwatankwacin irin tsayiwar da ƙayan fiki yake yi a maƙoƙaro. Na haɗiye wani miyau mai kauri kafin na sama zarafin gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi daman ci gaba da tambayoyi.
"Hajiya ba wani babban abu ba ne da zarar ta juri shiga cikin ruwan ɗumi kuma tana samun ishashshen huta, za ta dawo daidai. Sannan zan rubuta wasu magunguna sai a daure a neme su tabbas su ma za su taimaka".
"Likita ka tabbata za ta warware?".
Ya gyaɗa kai"za ta warware Hajiya wataƙila ma nan da zuwa safiya duk ciwon jikin da take ji zai yi sauƙi. Ga maganin sai a nemo mata su". Ya ƙare zancen tare da miƙa mata wata takarda ta karɓa jikinta har rawa yake yi, ya fita ta bi shi a baya.
Har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta zo ta durƙusa a gabana. Na runtse idanuna don ba na ƙaunar ko da ganin fuskarta balle sauraren zantukanta.
"Amatullah ina mai ba ki haƙuri na san an cutar da ke, amma babu yadda muka iya ƙaddararki ce ta zo a haka babu yadda za mu yi mu sauya ta. Ina mai roƙon ki da ki rufe wannan maganar a nan inda ta faru kar ki bari kowa ya sani ciki kuwa har da iyayenki". Babu shiri na ware idanuna tar akan ta cike da son ƙarin bayani.
"Ƙwarai kuwa hatta iyayenki kar su ji wannan labarin don in suka ji to har su koma ga Allah wannan tabon ba zai bar cikin zuciyoyinsu ba. Sannan babu wani ɗa na mutunci zai dai fito neman aurenki, ko ya zo ma ƴan gulma za su tsegumta masa abin da ya faru. Ki rufa wa kanki asiri ki rufawa iyayenki".
Wasu tsiraran hawaye suka soma rige-rigen fitowa daga idanuna suna sauƙa har izuwa tudun wuyana. Na ji ta riƙo hannayena na yi saurin zamewa.
"Hajiya wace ce Ramlatu kuma me ye tsakaninta da shi Musbahun? Me ya sa zai aikata wannan abun a zuwan cewa akan ta ya yi?".
Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta soma cewa"Ramlatu ƴar ƙanina ne da iyayenta suka rasu tun tana jaririya, ni ce na raine ta da hannuna har ta girma kuma na ba ta mummunan tarbiyan da yanzu haka take kan gwadabensa. Mus'bahu wani saurayinta ne da ya yi hidima da ita tun zamanin ƙuruciyarta har ta riƙa ta zama cikakkiyar budurwa sun yi soyayya da shi na bugawa a jarida kafin daga bisani masu hannu da shuni suka soma danno gare ta, a lokacin ne hankalinta ya karkata zuwa gare su har ta zaɓo ɗaya daga cikin su ta tura shi can ƙauye ya magantu da manya. Tun daga wannan lokacin ta fara wasan ɓoya da Mus'bahu don ya yi ikirarin cewar idonsa idonta sai ya lahanta ta ko kuma ya gurgunta mata rayuwa, sai dai ban taɓa kawowa a raina cewar yana da wannan mungun nufin a cikin ransa ba. Amatullah ƙaddara Ramlatu ce ta faɗa akan ki". Wani zazzafan kuka mai sauti na fashe da shi tabbas na yarda ƙaddarar bawa ba ta wuce ranarta sai dai ban taɓa tunanin ta wa ƙaddarar za ta zo a irin wannan siffan mai muni ba.
Duk su biyun suka haɗu suna rarrashina amma na kasa tsayar da kukan da nake yi, tausayi da tunanin halin da Abba zai shiga shi yake ta kai kawo a cikin birnin zuciyata yana yi mini yawo a cikin kwanyata.
Haka muka kwana da idanunmu har aka yi ƙiran assalatu Hajiya Tasalla ta ƙara dafa mini ruwan zafi na shiga na yi wanka, tun kafin gari ya gama wayewa na zara hijabi na kallo Amira da ta buga tagumi na ce"ki tashi mu tafi in kuma ba yanzu za ki tafi ba. To ni kin ga tafiyata".
Ta yi sauri ta riƙo ni"don girman Allah ki yi haƙuri ki bari tukunnan mu ƙara ganin yanayin jikin nakin zuwa nan da gari ya yi haske".
"Amira ki bar ni na tafi kawai". Na yi zancen ina fizge jikina daga riƙon da ta yi mini. Na durƙushe a ƙasa ina hawaye tare da sumbatu.
"Amira da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ke ce mutum na farko da za ki fara taimaka mini da hanyar barin cikin gidan nan. Ashe akwai irin wannan baƙar ranar cikin ranakun rayuwata? Ashe duk yadda nake tattali da killace mutumcina wani wanda shari'a ba ta mallaka masa ni ba zai rusa mini dukkan tanadin da na daɗe ina yi a rayuwata. Amira da wani idon zan kalla Abba?".
"Ai ba za su taɓa sanin abin da ya faru ba ma har abada". Na kafe ta da ido don na kasa cewa komai sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na zama zarafin faɗin"ke ma kin goyi bayan abin da Tasalla ta faɗa kenan?".
"Ba wai ina goyan bayan ta ba ne ina dai goyan bayan abin da zai siya miki mutunci ne Amatullah. Haƙiƙa idan maganar nan ta fita ba ke hatta ni ma na kaɗe balle kuma iyayenmu don shiga cikin jama'a ma sai ya gagare su, an dinga yi musu zumɗe kenan ana nuna su da baki tamkar watan Ramadana. Ki yi haƙuri ki karɓa ƙaddarar da ta faɗa miki, na tabbatar ko a wajen Allah ba ki da laifi don ba son ranki hakan ya faru ba. Kowani bawa da irin na sa salon ƙaddara ke ma kuma ta wannan fannin Ubangiji yake son ya gwada ƙarfin imaninki".
"Ko zan ɓoyewa kowa ba zan iya ɓoyewa iyayena ba".
Ta zo dab da ni"za ki iya matuƙar kika sa a ranki cewar za ki yi hakan. Yanzu dai ki bari gari ya ƙara waye wa sai mu tafi". Na gaza cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da ni, a haka Hajiya Tasalla ta shigo ta same mu ta kawo mana abincin karin kumallo sai dai gabaɗayamu mun kasa cin komai, da kanta ta je ta sayi maganin da aka rubuta ta kawo mini, da ƙyar Amira ta lallaɓa ni na sha maganin muka fito za mu tafi, har zaure Hajiya Tasalla tako mu tana jeranta mini sannun da ko kallon arziki ba ta ishe ni ba balle na amsa mata.
Muna shawo kwanar da za ta sada mu da gidanmu muka hango Abba tsaye a ƙofar gidan, sai waige-waige yake yi. Cak na tsaye ina lalumo hannun Amira yayin da hawaye suka ciko mini kurmin idanuna.
[10/21, 5:05 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
____________________________________
Page 3️⃣3️⃣
Amira ta riƙe hannuna gam"don girman Allah Amatullah ki nutsu kar ki tona mana asiri, kar ki bari ya gane da wani abu".
"Na shiga uku kin ga fa Abba ne tsaye".
"To don Abba ne sai me ye? Ki nutsu dai kawai ke kam kar ki yi abin da zai gane cewar wani abu ya faru". Ban kuma cewa da ita komai ba na goge fuskana da hawaye suka ɓata mini shi kana mu ka ci gaba da tafiya har zuwa lokacin hannuna yana cikin nata.
Muna doso wajen muka haɗa ido da Abba ya sauƙe wani ƙatuwar numfashi yana kafe mu da idanu.
"Uwata sai yanzu kuka dawo, a ina kuka tsaya?". Kafin na yi magana Amira ta yi hanzarin karɓe zancen cikin faɗin"Abba ba sa buɗe gidan da wuri ne shi yasa. Don a cewarta babu wanda zai fita sai gari ya yi haske ido na ganin ido". Ya yi ɗan jim tamkar yana nazarin wani abun kafin can ya ce"shikenan tun da kun dawo cikin ƙoshin lafiya alhamdulillah, amma dai ku daina tsayawa a ko'ina. Ku wuce ku shiga ciki".
"To in sha Allah". Muka haɗe baki wajen amsawa, muka soma tafiya ina jan ƙafana a hankali saboda ciwon da gabaɗaya jikina yake yi mini. Cak duk mu biyun muka tsaya bisa zancen da Abba ya furta da ya kusa tarwatsa zuƙatanmu.
"Uwata lafiya na ga ki na tafiya kina ɗingisa ƙafa?". Take gumi ya keto mini jikina ya soma rawa cikin in'inar da ban san ina yin ta na soma cewa"daman-daman-daman Abba...". Ban ƙarisa ba Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin hanzari.
"Abba zamewa ta yi a banɗaki shi ne ta bugu". Cike da tausayi da jin ƙai Abba ya furta"subhanallahi! Sannu ba ki dai ji ciwo ba ko?". Na runtse idanuna a ƙoƙarin hana hawayen da suka ciko mini koramar idanuna samun damar kwaranya.
"Ban ji ciwo ba Abba akwai bugu na yi a ƙuguna". Na yi zancen cikin sanyin jiki da na murya.
"Allah ya kiyaye na gaba. In sha Allah in zan dawo zan taho miki da magani sai ki sha kin ji?". Kaina kawai na sama damar gyaɗa masa na yi masa fatan a dawo lafiya ya tafi yayin da mu kuma muka shige ciki.
Muna shiga zaure na sulale a ƙasa saboda wani ƙarƙarfan kukan da ya yanko mini, Amira ta dafo kafaɗuna haɗe da faɗin"don Allah Amatullah ki yi haƙuri wannan kukan da kike yi fa ba shi zai gyara abin da ya riga ya afku ba. Ki nutsu mu yi tunanin hanyar da za mu ɓullowa lamarin nan".
"Allah in wani laifin na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar, Allah na tuba ka yafe mini".
Na yi furucin cikin ƙanƙan da kai da jingina dukkan lamurrana ga Sarkin da ba shi da abokin tarayya wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Cikin lanƙwasar da murya da rarrashi ta soma yi mini magiya da ban haƙuri.
"Don Allah ya ya kike so na ya miki ne Amatullah? Na ba ki haƙuri na ƙara ba ki haƙuri amma kin ƙi fahimta ta, abin da ya faru fa ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye gaba, yanzu idan wani ya fito daga cikin gidan nan ya gan ki a haka ai shikenan asirin mu ya gama tonuwa".
"Amira kin san yadda nake ji a cikin raina kuwa?". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta katse numfashina ba tare da na dire zancen ba.
"Duk abin da kike ji a cikin ranki ina jin makamancin sa a cikin raina Amatullah. Don Allah ki yi haƙuri ki tashi mu shiga ciki". Tana rufe bakinta muka jiyo sautin muryar Auwal saurayin Ummi ya buga sallama. Zumbur na miƙe ina karkaɗe jikina tare da goge hawayen da suka ɓata mini fuskata.
"Ƴan mata adon gari, Hajiya Amatullahi manyan gari ashe ana ganin ku a cikin duniyar nan?". Ta buga masa harara ina sauƙe numfarfashi na ja hannun Amira muka shige ciki, har muna na ƙoƙarin cin karo da Ummi yayin da take fitowa ta ja gefe ta tsaya tana bin mu da ido tare da riƙe haɓa.
"To ikon Allah! Wai na kwance ya faɗi ku kuma fa lafiyarku?".
Cikin mu babu wanda ya tanka mata har ta yi ta gama. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama ƙarfin gwiwan shiga cikin ɗakin mu bayan Amira ta gama ƙara mini ƙarfin gwiwa da ƙarfafa ni. Da sallama na shiga ɗauke a bakina kaina a ƙasa saboda nauyin haɗa ido nake da Umma ma balle kuma Abba da tausayinsa ya gama ragargaza mini zuciyata. Na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ba ta amsa mini ba illa mayar da hankalinta da ta yi akan ci gaba da irga kuɗin da take yi.
Na tashi zan shiga ciki na je na kwanta don gabaɗaya ba na jin daɗin jikina ga wani azababben zazzaɓin da yake ƙoƙarin rufe ne lokacin guda. Har na fara tafiya zan doshi hanyar ɗakin ta dakatar da ni ta hanyar faɗin abin da ya gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina, hanta cikina ya haɗa yayin da kaina ya juya jikina ya ɗauki rawa tamkar wacce akan jona wa wutan lantarki, haƙwarana suka datse harshena, yawun bakina ya ɗauke cak kamar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe ya tsawon zamani.
"Me ya same ki na ga yanayin tafiyarki ya sauya?".
Take zuffa ya soma tsatstsafo mini daga dukkan mafitan gashin da yake jikina, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na sama damar sarrafa abin harshena da ya cika mini bakina.
"Umma zame wa na yi a banɗaki na faɗi. Shi ne ƙuguna ya bugu". Ta ɗago ido tana ƙare mini tanadin kallo har sai da na tsargu na rusunar da kaina ƙasa.
"A ina kika zame ɗin? Wannan kayan kuma fa na jikinki?".
"A gidan Hajiya Tasalla, kayan kuma ita ta ba ni na sauya don nawa sun jiƙe na shanya su". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin can ta ce"Allah ya sauwaƙe ki je ki kwanta". Ban ce da ita komai ba na wuce cikin ɗakin ina shiga na fire hijabin kaina na yi jifa da shi kamar jaka haka na zube akan gado ina wani irin matsanancin kuka mai matuƙar cin rai da haifar da zogi da ƙaiƙayi a cikin zuciya. Na cire kallabin kaina na tusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan nawan fita, har sai da na ji numfashina yana ƙoƙarin sarƙafewa kana na tashi na zauna na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata, tabbas ɗan Adam baya taɓa gujewa ƙaddararsa amma na yanke hukuncin ba zan ƙara zuwa gidan Tasalla da sunan kwana ba, na gwammace na kwana ko da a soron gidanmu ne don sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi. Take na ji jikina ya ɗauki zafi zazzaɓi ruf-ruf ya rufe ni na koma na kwanta ina ta rawan ɗari.
A cikin wannan yanayin Umma ta shigo ta iske ni, ta kai hannunta saman goshina ta ji zafi gau hakan ya sa ta faɗin"Ke Amatullah lafiyarki kuwa? Mene ne yake damunki haka?".
"Kaina ne yake ciwo".
"To ki tashi ki sha magani mana sai ki kwanta da ciwo haka ba tare da kin sha magani ba". Na tashi ta fito falo inda ake ajiye maganin na duba na ɓalle paracetamol ƙwara biyu na fito waje na ɗebo ruwa na afa ina jefa ƙafana a cikin falon na ji jiri yana ɗeba tare da ƙoƙarin nanayi da ƙasa. Na yi hanzarin dafe kaina da yake juyawa tamkar sitiyarin mota a hannun ɗan koyo. Ban yi aune ba na ji ni shirib na zube a ƙasa na yi warwas, ina jiyo amon Umma ta zo kaina tana tambaya ta ko lafiya amma na gaza samun bakin da zan ba ta amsa. Daidai lokacin Amira ta shigo ɗakin suka haɗu ita da Umma suka ɗago ni suka kwantar da ni a bisa kujera suna yi mini fiffita don fankan da yake aiki a cikin falon bai hana ni fitar da gumi b ya yi mini lajab kamar wacce aka watsawa ruwa.
"Ki tashi ki daure ki ci wani abu sai a kai ki chemist ɗin Halilu ya yi miki allura. Don zazzaɓin bana sai an tare shi tun da wuri in ba haka ba sai ya tsotse mutum tsaf". Furucin Umma kenan da ya sanya hawaye zubowa daga idanuna ina jin a raina ina abin da take tunani ne watau zazzaɓi ba wannan abun ba. Amira ta taimaka mini na tashi na zauna Umma ta dama mini koko da ƙosai kunun kawai na iya zuƙa na koma na kwanta na yi luf, Umma ta ce Amira ta raka ni chemist ɗin Halilu ya yi mini allura. Haka muka fito tare da ita tana riƙe da hannuna muka wuce Ummi da Auwal zaune a zaure suna hira, suka zaro mana idanu lamarin da ya fusata Amira har ta furzar da takaicin da yake cikinta.
"Wannan kallon fa bayin Allah? To sai dai ku ci kanku wallahi mu kam nan gani nan bari ɗumamen mayya".
"To ma me ye za mu gani a jikinku? Har ina abin yake wai maye ya ci jariri?". Ummi ta mayar mata da martani a zafafe. Amira ta yunƙura za ta tanka mata ta kwaɓe ta, sai da muka doso chemist ɗin Halilu na ja na tsaya, Amira ta juyo tana kallo na alamar lafiya.
"Anya kuwa ba a gane abin da ya faru ba? Ni fa duk a tsorace nake".
Ta jijjiga mini kanta"babu wanda zai gane matuƙar ba ke kika faɗa ba". Tana dire zancen ta ja hannuna muka shiga ciki chemist ɗin Amira ce ta yi masa bayanin wai zazzaɓi ne yake damuna da kuma ciwon kai, ya rubuta mini magunguna sannan ya yi mini allura ya ce da dare na dawo a yi mini. Har muka iso gida ban ce da Amira komai ba, duk da kuwa yadda ta dage tana lallashina da roƙona akan kar na faɗa kuma kar na bar kowa ya gane halin da nake ciki.
Koda muka dawo ɗakinmu na shige na kwanta lamau ba tare da na yi aune ba nake jin wasu tsiraran hawaye suna kwance mini fuskata. Ina jin ƙirjina yana yi mini wani zafi tamkar ana watsa mini garwashin wuta. Ban san sa'ilin da wani wahalallen bacci ya yi awun gaba da ni ba.
Kamar daga sama na jiyo muryan Umma tana ƙiran sunana tare da bubbuga matashin da kaina yake kai. Na yi figigi na farka ina sumbatu.
"Don Allah ka yi mini rai ka taimake ni kar ka raba ni da......".
Muɗuk na haɗiye ragowar zancen yayin da idanuna suka washe a bisa fuskar Umma, jikina sharaf da gumi saboda mungun mafarkin da na yi da ya gigita ni ainun.
"Ke lafiyarki kuwa sai ka ce mai shafar aljanu? Ki na bacci kina ta battutuwa".
Sai da na daidaita nutsuwata kafin na yi ƙarfin halin faɗin"lafiya ƙalau Umma, yanzu ƙarfe nawa?". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf kana ta ce da ni a taƙaice.
"Ƙarfe biyu saura".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!".
Na furta ina dirowa daga oan gado na fito waje na yi alwala na koma ciki na yi salla, duk yadda Umma da Amira ta suka matsa mini akan na ci abinci kasa ci na yi, da ƙyar na sha kunu shi ma bai wuce ludayi uku na yi ba. Ranar ko islamiyya ban je ba duk son da nake yi mata kuwa, haka na wuni a ɗaki inna fito waje to alwala zan yi ina kammalawa nake koma na kwanta tun ina hawayen har suka daina tsiyaya. Tun da na kwanta nake ta biya karatun alkur'ani a cikin zuciyata har wani baccin ya kuma ɗauka na, ba ni na tashi ba dab ana ƙiran sallan magrib na fito na shiga banɗaki da nufin yin wanka amma na fi mintuna talatin ina durƙushe ina kuka, da ƙyar na yi wankan na fito na ɗauro alwala na koma ciki na yi salla, ban tashi daga kan sallayan ba har sai da na yi sallan isha'i ina zaune Amira ta shigo lokacin Umma ta fita.
"Ya jikin nakin?".
"Da sauƙi".
Na amsa mata da aa taƙaice da hakan ya ba ta damar ci gaba da magana.
"Ki tashi mu je ayi miki alluran daren daga nan kuma sai mu wuce ko?".
Na ware dukka girman idona akan ta"mu wuce zuwa ina ke nan Amira?".
"Gidan Tasalla mana". Baƙi ciki da takaici ya hana ni cewa komai illa bin ta da kallo da na ci gaba da yi ina cije leɓena. Ta riƙo hannuna na zame.
"Na san abin da kike tunani a cikin ranki Amatullah, amma idan kika ce kin daina zuwa to ina tabbatar miki da cewar kin kafawa kanki alamar zargi kenan. Dole su Abba su bincika dalilin da ya sa kika ce ba za ki koma ba alhalin ke da kanki kika zo masa da buƙatar". Ta sauauta amon muryarta kana ta ci gaba da cewa"ki ɗauri abin da ya faru a matsayin ƙaddara".
"Na yarda da ƙaddara mana Amira na yarda da ƙaddara. Amma ba zan iya komawa gidan nan ba". Na yi zancen cikin raunin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata.
"Ni ma ba wai na ce ki ci gaba da zuwa ba ne, na ɗan wani lokaci kawai saboda mu kawar da zargi. Ki daure ki rufa mana wannan asirin". Na fashe da kuka ina faɗin"Allah na tuba idan laifi na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar. Allah na tuba ka yafe mini".
"Ki yi haƙuri ki daina wannan kukan Amatu ya isa haka. Kar ki ja wa kanki wani ciwon na daban don Allah".
Kafin na amsa mata muka tsinkayo sallamar Abba, na yi zumbur na miƙe ina gyara ɗaurin zanin da yake jikina na goge fuskana da bakin hijabin da yake jikina. Na fito falon Amira tana biye da ni. Muka haɗe baki wajen yi masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayata ya ya jiki na ce da shi da sauƙi.
Ya ba ni wani magani ya ce ma sha na ciwon jiki ne, a take a wajen na ɓalla na sha ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 24