Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
komai ta ce na ɗauka na fita na ɗaura a kaina na fito na iske Amira har ta shirya tana jira na. Ta ci ƙwaras cikin shigar doguwar rigar kamlafa da ya bi jikinta ya fito da surarta a bayyane. Ta yafa mayafi a kafaɗarta bayan ta buga ɗaurin da ake wa take da ture ka ga tsiya a kanta. Har muka fito ban yi mata magana haka nan ma ita ma ba ta ce da ni uffan ba illa latsa wayarta da take yi, kasancewar ita akwai almajirin da yake tura mata kayan tallanta a bairo ya kai mata har inda za ta. Sai da muka yi nisa na ce"wai ina muka nufa ne?". "Tasha mana". "Tasha kuma? Haba Amira duk faɗin garin nan mu rasa inda za mu yada zango sai tasha?". Ta cira kai tana kallona"ke dai ba buƙatarki ki sayar da wannan kunun ba?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"to ke dai kawai ki biyo ni". Daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka isa tashan almajirin ya sauƙe mata kayan ta sallame sa ya juya ya tafi. Kan ka ce kwabo samari sun yi mana rumfa sayar masan suke yi ba ƙaƙƙaurawa. Kafin awa guda ta rufa ta sayar da Masar tas har ana nema, sai dai ta ajiye take away guda biyar ta ƙi sayar wa kowa, ni ma ba laifi na dandani farin jininta na yi ciniki sosai. Ganin ana ta zuwa neman masan tana cewa ya ƙare ya sani yi mata magana"ke kuwa ki sayar musu da wannan ɗin ma tun da ana ta zuwa nema". "Wannan ba na sayar wa ba ne don a riga da an saye su tuntunin. Wannan da kike gani na Naziru ma Zamani ne kuma ko wani take away ɗaya naira dubu biyar yake sayansa, sai dai shi yana da sharaɗi". Na ware idona tar a kanta"wani irin sharaɗi kuma?". "Har inda yake ake kai masa kuma a taya sa hira". "To a ina za ki same shi?". "A ɗakin mana". Na dafe ƙirji ina maimata abin da ta furta"a ɗakinsa kuma?". "Ƙwarai kuwa. To me ye abu tada hankali dududu ba kya wuce awa guda ya ba ki kuɗinki ki dawo". Shuru na yi na kasa motsin arzuki balle na yi furta wani kalma tsabar ruɗun da na shiga. Sai da na fizgo numfashina kafin na ce"yanzu kuma Amira sai ki je ɗakin nasan?" "To sau nawa kuwa. Wani lokacin ma da na fito a can nake tsaya wa ya yi min juye. Ke ma kwanan nan zan nema miki wani na jona ku". Na galla mata harara"Allah Ubangiji ya kiyayi gatari da saran shuka. Ke ma ki yi wa kanki faɗa don ke yanzu ba yarinyar ba ce ko a addini alƙalami ya hau kanki. Ya rage na ki ki yi daidai ko akasin hakan". Dariya kawai ta soma yi ta tashi ta ɗauki take away ɗin ta miƙe tsaye. "Lokacin da za ki fara hakan Amatullah ke ma kanki ba za ki sani ba. Lokaci shi ne sauya komai, mu ma da ba mu tunanin za mu iya ba amma lokaci ya koyar da mu abun da ba mu taɓa tsammanin za mu iya aikata shi ba". Tana dasa aya ta juya ta tafi kai masa take away ɗin. [7/21, 6:16 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 1️⃣4️⃣ Da kallo na raka ta har ta ɓacewa ganina na sauƙe wani gawurtaccen ajiyar zuciya ina zabga tagumi da hannuwa bibiyu. Kafin maganganun da ta yi mini ya soma dawo mini a cikin kwanyata ina yi masa rankaɗe da rairaya. Babu shiri na zame hannuna daga tagumin da na yi ina ji har cikin ƙasan zuicyata ba zan taɓa iya aikata abin da Amira take ikirarin lokaci zai sa na koya ba. "Ƴan mata me ye kike sayarwa ne?". Muryar saurayin ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na cira kai ina ƙare masa kallon tsaf. Shigar ƙananan kaya ne a jikinsa da su da kansu suke bayyanar da tsadan farashin su, komai na shi tsaf-tsaf alamar baya haɗa hanya da ƙazanta ko mai aikata ta. "Ko ba za ki yi min magana ai za ki tashi daga nan wajen kar zafin rana ya yi wannan kyakykyawan fatarta ki illa". Sai da ya yi maganar na ankara da har rana ya iso inda nake zaune na tashi na matsa gefe na zauna shi ma ya matso. "Don Allah ki yi min magana mana ko da kuwa zagina za ki yi ko cin mutunci. Na tabbatar yanda kike da kyawun jiki da na fuska muryarki ma za ta kasance kamar sarewa a kunne". A kufule na ce"me ye kake so daga gare ni? Idanunka dai sun gane maka kuma sun isa su ba ka amsar duk wani tambayar da kake tafe da shi. Ba shashashci ba ne ya kawo ni nan sana'a nake yi". Ya murmusa yana ɓalle murfin ruwan roban da yake hannunsa ya kurɓa kafin ya ce"tsarki ta tabbata da Ubangijin da ya tsagawa bayinsa baki kuma ya ba su ikon yin magana. Tabbas ki na da zaƙin murya mai rikitar da ƙwaƙwalwa tun da na hango ki daga nisa na ji zuciyata tana cewa na zo gare ki". "Don Allah Malam ka yi haƙuri". "A zuba min kunun na dubu biyu". Na ɗaga kai na yi masa kallo guda kafin na kawar da kaina gefe ina faɗin"gabaɗaya sauran kunun bai kai na adadin wannan kuɗin ba". "To yanzu a zuba min na sha sauran kuma sai ki yi yadda kike so da shi". Ban ce da shi uffan ba na zuba masa na ɗari biyu na miƙa masa ya ɗauka ya zauna ya soma sha. "Kin san dai wallahi ita ce ƙarshen rantsuwa ga duk wani ɗan musulmi ko? To wallahi tun da nake ban taɓa shan kunun mai daɗin wannan ba. Don Allah zan roƙi wata alfarma daga gare ki idan ba za ki damu ba". Ba tare da na kalla inda yake ba na ce"don damuwa kam dole na damu. Faɗi na ji wani irin alfarma ce". "So nake yi a duk lokacin da kika kawo tallan kunu tashan nan, na zama mutum na farko da zan fara sha kafin kowa". Na galla masa harara"ba zan iya ɗaukar abun da ba zan iya ba ka yi haƙuri". Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi na kuma watsa masa wani harara ina saki gajeren tsaki. "Wallahi idan kina magana kamar kar ki daina. Yadda kike fassara leɓɓanki shi kaɗai ma abin burgewa ne". Ban ce da shi komai ba har ya gama kiɗansa kuma ya yi rawansa bayan ya gama shan kunun ya miƙe tsaye ya tsaro wasu kudaɗe daga aljihunsa ya raba biyu ya ajiye mini kashi ɗaya akan bokitin kunun yana faɗin. "Ga kuɗin kunun". Ta ƙara ajiye mini ɗayan kashin yana ci gaba da cewa"wannan kuma ni ne na yi niyyan baki saboda gamsuwa da na yi da wannan daddaɗan kunun nakin". "Malam na ɗari biyu ai kawai ka sha. Don haka iya ɗari biyun nake buƙata domin shi ne haƙƙina". Kafin ya yi magana Amira ta iso wajen hakan ya sani miƙewa tsaye ina kallonta sai dai kafin na yi magana ta riga ni. "Tuba nake yi na bar ki ke ɗaya ko? To yanzu dai ga shi na dawo". "Kin ga ni kawai ma mu tafi gida na gaji da wajen nan gabaɗaya". Ta yi sakeke tana kallona"ban gane mu tafi gida ba Amatullah? Ta yaya za mu tafi gida bayan kunun har yanzu akwai saura. Ai kawai haƙuri za ki yi mu zauna har ya ƙare". "Babbar yarinya daman tare kuke da ita? Ai kuwa faɗuwa ta zo daidai da zama da ke zan yi kamun ƙafa". Ta murmusa tana fuskantarsa kafin ta ce"Bash ai ban gane ka ba kai ne haka? Duk ka wani canza ka sama duniya ka manta da mutane. Na ji ma ance wai yanzu babbar mota kake ja. Sai jifa-jifa ake ganinka a cikin tashar". Ya bushe da dariya har da tafa hannu sai da ya tsagaita kafin ya ce"ikon Allah! Ke ma kin sama labari kenan?. Wallahi ina gaya miki yanzu gabaɗaya ba na samun sama". Cike da fara'a Amira ta ce"ma sha Allah ina taya ka murna". "Ina godiya babbar yarinya. Wannan fine girl ɗin fa?". Ta waigo tana kallona. "Au wai Amatullah? Ƙawata ce ko akwai magana ne?". "Sosai ma kuwa sai dai ina ta yi mata magana ba ta tanka min. Kin san ba ni ban cika shiga harkokin mata ba amma ita ɗin ta yi nasarar yin daidai da ra'ayina, da ita za a tafi". Ta saka dariya kafin ta ce"to wannan kuma ai maganarku ce kai da ita sai dai ko na ba ku waje". Na haɗe giran sama da ba ƙasa ina watsa mata harara da wutsiyar idona"Amira kin fi kowa sanin ba na son irin wannan wasan". "Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zoman ba rataya aka ba ni". Daga haka ta nema waje ta zauna ta zaro wayarta tana dandanawa ni ma na koma na zauna. "To babbar yarinya ni dai zan wuce. Ɓarauniyar zuciyata ga kuɗin nan don Allah kar ki ƙi ɗauka". Ya ƙare zancen yana maraicecewa lamarin da ya ƙara tuntsura mini zuciyata ta zo daidai wuya ta yi nuni tsayiwar ƙaryan kifi a maƙoƙaro. "Malam na ri ga da na gaya maka adadin kuɗinan ai ko? Me zan yi da wannan tulin kuɗin da ka ajiye mini?". Kafin ya ba ni amsa Amira ta yi caraf ta cafke zancen. "Kar ka damu Bashir zan shawo maka kan komai". Ya yalwata fuskarsa da yalwataccen annuri kafin ya furta"ina godiya ƴar gari, yanzu dai ki saka min sha ɗayanki tun da na ga kin ƙara da gari yanzu, kin dantsalo babbar waya". Da murmushi a fuskarta ta karɓa ta sanya masa lambarta ya ƙira a take ya ce ta yi saving kafin suka yi sallama ya tafi. Ta watsa kuɗin ta irga su kafin ta soma cewa"kin ga dubu dubu huɗu ne dukka. Yanzu me ye za a yi da su?". Raina ya kai ƙololuwar ɓaci na yi mata wani irin mungun kallo ina furzar da takaicin da ta yi silar cusa mini cikin raina. "Sai ki san yadda za ki yi da shi tun da ke kika ɗauke su". Ganin na ɓata rai ya sanya ta soma faɗin"ki saki ranki Amatullah abun da na yi shi ne daidai. Don idan ba ki karɓa ba ma wata can daban ce za ta ci kuɗin kin ga kuwa ban yi laifi ba don na ɗauka. Su da irin su Bashir kuɗinsu duk a wajen mata yake ƙarewa ba sa tsinanawa kansu komai gwara ma ki kwanki gara ki bar gara a inda kika same shi". Ban ce da ita komai ba na tashi na na ɗaga gammona zan ɗauki bokitin kunun na ɗaura a kaina ta dakatar da ni. "Haba ke kuwa ina za ki da ragowar kunun? Ai almajirai za ki nema ki yi musu sadaka ki nema albarkar kasuwa". Na kasa cewa da ita komai balle na yi wani yunƙurin haka ina ji ina gani ta rabarwar almajirai kunun har da cewa wai su yi mini addu'a Allah ya sa na shigo tashar da ƙafar dama. Ta tattara kayan gabaɗaya tare da na ta almajirai suka ɗauka mana zuwa gida, suna gaba muna biye da su a baya. "Amatullah sai fa kin watsar da waɗannan tsauraran ɗabi'un nakin kafin ki iya zama cikin tashar nan har ki ci riban zaman. Kin ga mutanen sai ka musu abin da suke so kafin kai ma ka sama yadda kake so daga gare su". Na yi hanzarin taka mata burki"ban gane sai ka yi musu abin da suke so ba?". "Kwantar da hankalinki kar ki fassara zancena ta wani hanyar daban. Ki dinga sakar musu fuskar kuna yin ɗan hira nan ko da jifa-jifa ne. Matuƙar za ki yi haka to jauranki ba zai taɓa yin kwantai ba, kuma ina tabbatar miki babu wanda ya isa ya taɓa a tashar nan ya kwana lafiya". Na yi ɗan jim ina nazari da lalumen gurbin da zan aza zantukanta. "Amma ai ce mini kika yi garejin mota kike zuwa kai talla". "Kin manta Mansur baya gari ne? Idan yana gari ne nake zuwa gareji amma idan baya nan tashar nan nake zuwa". "Me yasa?". "Saboda haka kawai na yi ra'ayi". Na ja hannunta muka tsaya muna kallon juna. "Amira ki ji tsoron Allah kin san da cewa Mansur yana sonki sosai kuma yana iya ƙoƙarin sa a kanki na gani ya biya miki duk wata buƙatarki da ta taso ɓangaren ƙudi. Amma me yasa don baya gari za ki nema cin amanarsa ta hanyar kula wasu mazan bayan shi? Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba na san shi ne ya hana ki zuwa wannan tashar saboda baya son ki yi mu'amala da mazan wajen". Ta fizge hannunta ta fara tafiya na bi ta a baya. "Shikenan don ina sonsa sai aka ce ba zan yi mu'amala da kowa bayan shi ba. Aure na ya yi ko kuwa ya zo gidanmu an ba shi ni ne da kike yi min wannan maganganun?. Amatullah idan na ce ba na son Mansur na yi ƙarya amma mu'amala da wasu mazan bayan shi ya zama wajibi". Ta yi tsaki daidai lokacin da muke karya kwanan shiga layinmu kafin ta ci gaba da maganan. "To ma ce miki aka yi su ɗin soyayya muke yi ko me ye? Ko ke za ki ba da shaidar babu wanda nake so a cikin zuciyata sama da Mansur". "Ko ba soyayya kuke yi ba amma ai abin da kuke yi bai dace ba. Me ye zai kai ki ɗakin mutum ku kwashe tsawon mintuna kuna hira don kawai zai sayi abin da kike talle alhalin ku ba muharraman juna ba ne, me yasa ba zai zo ya saya ba kamar yadda kowa yake yi?". "Lokacin da lamarin zai juyo kanki, na tabbatar miki a sa'ilin ko kalmomin kare kai ba za ki same su akan tsinin harshenki ba". Rashin gane inda zancen natan ya dosa ya tursasa mini yin shuru ba don na rasa abin faɗa ba. Haka har muka isa gida cikinmu babu wanda ya kuma cewa uffan almajiran suka shigar mana da kayan har cikin zaure, ta ba su naira ɗari biyu bayan ta ce da su gobe da safe ma su zo su ɗauka mana kayan. Cike muka iske gidan kowa yana tsaye cirko-cirko kamar waɗanda suka haɗiye taɓarya sai da muka ƙarisa shigowa muka gane wa idanunmu abin dake faruwa. Mahaifin Ummi ne a tuɓe a tsakar gidan daga shi sai singilet da gajeren wando tana ta ɓarin zancen da ikirarin sai ya ɗaukar wa ɗiyarsa fansan fitar mata da jini da Maman Adnan ta yi ba gaira ba dalili. Yayin da mahaifiyar Ummin take ƙara rura wutar rikicin. Can ka ce kwabo yaran unguwa da uwayensu sun cika ƙofar gidan har cikin zaure babu masaka tsinke. Muka shige ɗakinmu tare da Amira muka tarar da Umma tana zaune a falo tamkar ba ta san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba. Duk rusuna muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Amira ta yi mata bayyanin mun sayar har mun dawo Umma ta cika da farin cikin mussamman lokacin da ta miƙa mata wannan dubu huɗu ta haɗa mata da bayanin inda muka same su. Lamarin da ya faranta ran Umma har ya kai ta ga rangaɗa guɗa. "Aw ashe fa gidan ba lafiya? Amira ai irin ki ake so ɗiyar azirki irin albarka. Ga Amatullah nan na bar ta a hannunki ki ci gaba da ɗaura ta akan hanya". "Ba ki da damuwa Umma. Yanzu dai bari na je na huta". "To yarinyar kirki ɗiyar fita kunya, na gode sosai ko". Murmushi kawai Amira take ta baza wa ta tashi ta fita. Ta bar ni da ƙuncin rai don ban yi zaton za ta iya faɗawa Umma yadda aka sama kuɗin nan ba sai gashi ta shafe idonta ta aikata. "Umma ga cinikin da aka yi, bari na yi salla na yi shirin islamiyya". Na furta yayin da nake miƙa mata kuɗin cinikin da yake wajena. Ta amsa tana washe baki har kunne, ganin ba ta da niyyar ce mini komai ya sani fallasa abin da yake raina. "Umma ni ma ko sau ɗaya ai sai ki sa mini albarka". "To Allah ya yi albarka. In ce dai shikenan ko?". Babu shiri wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce mini"na gode sosai". Sallan na yi kana na yi wanka na ci abinci na yi shirin islamiyya na tafi. Bayan mun fito sallan Malam Suleiman ya aiko ƙura na na je na same shi a cikin staff room. [7/22, 6:43 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 1️⃣5️⃣ Shuru ya biyo bayan gaisuwar da na yi masa ya amsa. Sai da aka yi nisa kafin ya kawar da shurun ta hanyar soma faɗin"Amatullah na je na yi nazari akan maganganun da muka fara tattaunawa da ke jiya, mataki na farko da za ki ɗauka wanda babu nadama shi ne ki dage da addu'a, ki dinga tashi cikin dare yayin da kowa ya kwanta ki yi alwala ki yi salla ki yi kuka a Allah ki ƙasƙantar da kanki gare sa. Ki yi tawassali da sunanyensa ɗari ba ɗaya tsarkaka ki roƙe sa mafita. Ki nema wa mahaifiyarki shiriya Allah ya sa ta gane illar abin da take aikata. Sannan ɗabar da nake son na ja hankalinki sosai akan sa shi ne kar ki sake shaiɗan ya yi nasara akanki ki wa mahaifiyarki rashin kunya ko ki raina ta ki daina ba ta girma da kimarta a matsayinta na uwa. Allah ya kan jarabci bawansa ta ko wani fage a rayuwa kamar yadda ya zo a tarihin Allah ya jarabci Annabi Ibrahim ta ɓangaren mahaifinsa wanda ya kasance mushiriki. Daidai da rana guda bai taɓa ƙin aikata masa abin da yake so ba, Annabi Ibrahim har tallen gumaka ya yi don jaddada biyayarsa ga mahaifinsa. Don Allah ina mai jan hankalinki da duk runtsi duk wuya da yadda lamura za su sauya kar ki kuskura ki yi wa mahaifiyarki rashin ɗa'a". Na sauƙe ɓoyayyan ajiyar zuciya kafin na ce"in Sha Allah Malam zan yi amfani da duk shawaran da ka ba ni. Ba zan taɓa kauce wa daga wannan turban ba". Cike da jin daɗin kalamaina ya ci gaba da cewa"Allah ya yi miki albarka ya kawo miki sauƙi da mafita a cikin dukkan lamuranki. Zan ba ki wasu addu'ar da Annabi ya yi amfani da su kuma ya umarce mu da mu yi amfani da su, a duk lokacin da muka tashi roƙon wani buƙata a wajen Allah. Babu inkari matuƙar ka yi su Allah da kansa ya ce yana jin kunyar wanda zai roƙo sa da wannan addu'ar ba tare da ya ba shi duk abin da ya roƙo ba". "Na gode sosai Malam Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata". "Amin ya Allah". Ya amsa yana miƙo mini watar farar fefe da ya rubuta mini addu'ar a jiki, na amsa ina ƙara yi masa godiya. Tun kafin a tashi daga islamiyyar na haddace addu'ar kafin na iso gida ta zauna ɗas a kwanya da saman harshena. Ina isowa gida na wuce ɗaki na sauya kayan da ke jikina na fito kasancewar ban tarar da Umma ba. Ɗakin su Amira na nufi don karanta mata dashin dacewar abin da ta aikata mini ɗazu, tana kwance a cikin kujera a falo ta duƙunƙune waje guda yayin da ta lumshe idanunta tana ƙare matse wayar da yake kunnenta. Da hakan ya hana ta jin sallamar da na shigo da ita ɗauke a bakina. Ganin ba ta da niyyar saurara ta ya sani na fizge wayar, ta tashi ta zauna tana kallona bayan ta dafe kanta. "Wallahi na san duk gidan nan babu wanda zai yi min wannan wulaƙanci sai ke Amatullah". Na galla mata harara"kin kyauta abin da kika yi min kenan ko?". Cikin rashin fahimta ta ce"da na yi me ye kenan?". "Ya dace ki je ki sama Umma ki sanar da ita inda aka sama wannan kuɗin? Ni da nasan haka ne ma ba zan bari ki ɗauka ba". Ta tuntsire da dariya har da riƙe ciki lamarin da ya ƙara fusata ni na cika na yi fam na zo har wuya. "Au! Dariya ma maganar ta ba ki kenan?". "To Amatullah idan ban yi dariya kuka kike so na yi? Me ye don na sanar da Ummar hanyar da muka sama kuɗin?. Ince dai ke ce kullum kike jan hankalina da yi min nasiha akan na guji faɗar abin da daidai ba duk runtsi da matsin lambar da za a yi min na faɗi iya gaskiyata a cikin ko wani irin yanayi. Cikin ikon Allah kuma yau na faɗi gaskiya kin zo kin titsiye ni". "Ni ba titsiye ki na yi ba amma ai kin san zancen da ya dace a faɗa da akasin hakan". "Ni dalla ba ni wayata ina shan soyyaya da masoyi kin zo ki katse min jin daɗina". Ta ƙare zancen tana fizge wayarta da yake hannu ta koma ta kwanta ta ci gaba da wayarta, yayin da na nema waje na zauna na yi tagumi. Babu abin da yake yi mini yawo da kai kawo a cikin raina face yanayin da na sama Umma jiya da yadda Abba ya sauya a safiyar yau. Duk da Abba yana da sauƙin kai da hakan yake sa mutane da yawa tunanin ya fiye sanyi, amma tsayayye ne kuma jajirtaccen mutum ne akan iyalinsa da ba ya ɗaukar wargi a wannan fanni ko kaɗan. Kamar daga sama na ji an manna mini ways a kunnuna hakan ya dawo da hankali da tunanina da suka yi nisan kiwo gare ni. Na cira kai ina duban Amira. "Mansur ne za ku gaisa". Na amshi wayar muka gaisa da shi sannan na yi masa ya hanya ya amsa mini da sun sauƙa, kafin mu yi sallama ya dinga jeranta roƙo akan na kula masa da Amira kafin ya dawo ya ba ni amanarta ya bar ta a hannuna da makamantan su. Sai da na dara sosai kafin na amsa da cewar zai dawo ya same amanarsa yadda ya bar ta da iznin Allah. Da haka muka yi sallama na miƙa mata waya ita ma ɗin sallama suka yi ta ajiye wayar. Na gyara zamana ina kallonta haɗe da cewa"Mansur yana matuƙar sonki ta yadda ba iya ɓoye hakan har a cikin kalaman da suke fita daga bakinsa. Don Allah kar ki ba wa kowa irin damar shiga zuciyarki balle har ya kai inda Mansur yake, kar ki ci amanar bawan Allah nan ko da wasa". Numfashi mai ƙarfi ta sauƙe da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta soma magana a hankali alamar na taɓo mata inda yake yi mata ƙaiƙayi. "Ni ma ina jin sa har ƙasan raina, kuma ina sonki fiye da tunaninki. In sha Allah zan yi amfani da duk shawarwarin da kika ba ni". Daga haka na daina fahimtar abin da take faɗa sai dai na ƙura mata idanu ina ganin leɓanta yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da har yanzu ba ta daina maganar ba. Sai da ta taɓo ni kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na afka na figigi na ɗaga kai ina kallonta. "Tunanin me ye kike yi ne haka Amatullah? Tun da safe na fahimci akwai abin da yake damunki, amma kika ce min babu komai. Me ye amfanin muna ƙiran kan mu aminai kuma ƴan uwa amma ba ma iya sanarwa junanmu abin da yake damun mu?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin faɗin"Amira babu abin da yake damuna akwai dai matsaloli ne na yau da kullum, kuma kin san ba'a raba bawa da tunani komai daular da yake cikinta". "Ko kin ɓoye min abin da yake damun ki fuskarki ba zai ƙi bayyanar da labarin zuciyarki ba. Tabbas akwai abin da yake damun

Chapter 8 of 24