akan mutuwar Abba?. Da ƙyar na isa wajen napep ɗin Anty Zulaihatu ta tsayar na shiga na zauna.
"Amatullah don Allah kar ki aikatawa abin da zai cutar da ke ko ya jefa mu gabaɗaya cikin wani ruɗanin. Ki yi ƙoƙari ki cire damuwa a cikin ranki in sha Allah gobe da sassafe ni ma zan zo, kuma Mansur ma ya ce a yi miki gaisuwa kafin ya zo da kansa". Kaina kawai na jinjina mata muka rabu, ko da muka isa gidan Anty Sawwama su Yaya Alhassan sun hi matuƙar baƙin cikin abin da ya faru Umar sai da ya yi kuka tsabar takaici.
A daren ranar sai da aka ƙara mini ruwa leda biyu aka yi mini allurai da sauran magungunan da na sha. Ina kwance a ɗaki kamar gawa Yaya Alhassan ya shigo ya yi mini sannu na amsa can ƙasa maƙoshina.
"Amatullahi ki cire damuwar komai daga cikin ranki in sha Allahu duk wanda ya yi miki wannan abun sai na nemo sa ko ina ya shiga a cikin duniya sai kuma na tabbatar da cewar an hukunta sa, bisa tanadin doka. In sha Allah farin cikinki zai dawo za ki rayu cikin nutsuwa da walwala kamar yadda kike a baya".
"Yaya Alhassan ni da samun farin ciki mun yi hannun riga".
Ya yi hanzarin katse ni"zan dawo miki da farin cikinki zan tabbatar da cewar duk matsalalolinki sun kau. Amatullahi ki ba ni dama in har kin aminta da ni kuma ki na jin za ki iya rayuwar aure da ni to zan iya ki".
Take na wartsake na tashi na zauna ina kallon sa cikin son tabbatar da abin da kunnuwana suka jiyo mini.
"Ƙwarai da gaske ni zan aure ki don ba zan ba ri aure ya kai ki inda za a wulaƙanta ki ko a yi miki gori bisa ƙaddarar da Allah ya ɗaura miki ba".
"Yaya Alhassan rayuwarka tsarkakkiya ce babu wani mummunan abu a cikin tarihinka. Don Allah kar ka gurɓata tarihinka ta hanyar haɗa jini da ni".
"Ko a gidan karuwai kike rayuwa Amatullah zan iya aurenki. Balle kuma ke ɗin ƴar uwata ce ta jini. Sai dai ba zan yi miki dole ba don yanzu farin cikinki shi ne abin da na fi so don haka ki je ki yi tunani da zuciyarki".
Na sunkuyar da kaina ƙasa kafin na ce"Anty Sawwama ta san da wannan zancen?".
"Sai da na fara tinkarar ta da maganar kafin na zo wajen ki". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ban iya cewa wani abun har ya tashi ya fita daga cikin ɗakin, ji nake yi kaina yana juya tamkar ba a cikin duniyar nake ba ga wani jirin da yake ɗeba ta don da kasancewar a zaune nake. Na koma na kwanta hawaye suna tsiyaya ta gefe da gefen idona.
Tabbas Yaya Alhassan mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kame mutuncin kansa da kuma na ahalinsa a ko da yaushe, mutum ne mai nutsuwa da sanin ya kamata me yasa Anty Sawwama za ta amince masa akan auran watsatstsiyar da ta yi cikin shege ta kunyatar da iyayenta da duk wani wanda ya yarda da ita a idon duniya. Hatta mahaifiyarta ta nuna rashin buƙatata a kusa sai ita ce za ta buƙaci ɗanta ya kasance a tare da ni?.
Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina gyara kwanciyata, ba zan zama silar rugujewar rayuwar Yaya Alhassan ba. Don haka na gwammace na tafi can wani wajen da ban san kowa ba ni ma ba sanni ba na je na yi rayuwata. Ko zan sama kwanciyar hankalin da na rasa a yanzu. Gwara na shiga duniya kamar yadda Umma ta yi ikirarin ta sallama ni gare ta.
[10/30, 4:03 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 4️⃣0️⃣
Haka na kwana ina tunani da saƙa da warwara cikin raina, ganin bacci ya ƙi kawo mini ziyara hakan ya sani tashi na fito na ɗaura alawa na koma ciki na gabatar da salla raka'a biyu. Na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa magana rawa kawai jikina yake yi. Na kifa kaina a bisa gwiyoyina ina rero kukan marar sauti. Ban runtsa ba har sai da aka yi ƙiran sallan asubahi Anty Sawwama ta shigo da nufin tashi ta iske ni zaune ta dalle mini idanuna da haske tocila.
"Lafiya na gan ki a zaune kamar ba ki runtsa ba?".
"Na runtsa kawai na tashi ne da na ji ƙiran salla". Ba ta ce da ni komai ba ta juya ta fita na bi bayan ta alwala na yi na zauna na buga tagumi a gaban botan har Yaya Alhassan, Amir da Umar suka fito domin tafiya masallaci.
"Amatullah lafiya kuka zauna kika zagba tagumi?". Na tsinkayo muryar Amir a tsakiyar kaina na yi figigi na dawo cikin hayyacina.
"Lafiya ƙalau ina kwananku". Suka haɗe baki wajen amsawa kana suka fita, na tashi na koma cikin ɗakin na shimfiɗa sallaya a zaune na yi sallan don ji nake yi tamkar ƙafafuna ba za su ɗauke ni ba tun ina raka'an farko nake kuka har na yi sallama na ɗaga hannayena dukka biyu zama ina kirari ga Ubangijina.
"Ya Allah kai mai ikon akan kowa da kuma komai. Ya Allah kai ne masanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciyar dake a ciki ƙirji, Allah ka kawo mini mafitan halin da nake ciki. Zan tafi na je can wani wajen da ba a sanni ba ni ma ban san kowa na je na ci gaba da rayuwa a can, don na fahimci zama a nan shi ma wani matsalan ne. Tun da har Umma ta furta ba ta buƙata ta ta sallamar da ni ga duniya zan tafi can wani wajen na je na yi rayuwata, ba zan zama matsala ga rayuwar wasu ba. Ya Allah ya dubi lamarina ka kawo mini komai da sauƙi ka ba ni ikon cinye wannan jarabawan da ya faɗa mini. Allah kai mai rahama ne Allah ya lulluɓe Abbana da rahamarka, Ya Allah kai mai gafara ne Allah ka gafarta masa".
Na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki wasu hawayen suna gangarowa daga idanuna, na ji ƙarar buɗe ƙofar hakan ya sa na yi saurin komawa na kwanta ba tare da na cire hijabin da na yi sallan ba. Aka shigo aka zauna kusa da ku dab har ina ji sautin ajiyan zuciya da take sauƙewa akai-akai.
Ta dafa goshina tana shafawa har zuwa kaina"Amatullahi Baiwar Allah ina son rayuwarki ta inganta ina don ganin ki cikin farin ciki. A yanzu ba ni da burin da ya wuce na gan nutsuwarki ya daidaita kin sama kwanciyan hankali da walwala ki yi rayuwa kamar kowa cikin sakewa wannan dalilin ya sa nake son Alhassan ya aure ki. Don hankalina ba zai kwanta ba matuƙar kika yi aure a wani wajen kika shiga cikin wasu dangin da wataƙila su goranta miki akan abin da ya faru da ke ko ma su wulaƙanta ki. Amatullah tun ranar da aka kawo mini gawar Manniru a gaba babu rai a tattare da shi na yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa barin abin da ya haifa ta wulaƙanta ba bayan ransa, zan yi tsayiwan tsayin daka wajen tabbatar da cewar rayuwarki ta inganta. Ina da yaƙinin ko bayan babu raina Alhassan ba zai taɓa bari ki wulaƙanta ba".
Ta ƙare zancen tare da gyara mini Kwanciyata ta ja hijabin ta lulluɓe mini ƙafafuna da shi, ta fita rufe ƙofan da ta yi ya yi daidai da bugawan da zuciyata ta yi tamkar za ta ɓalle allon ƙirjina ta fito waje ta daka rawan disko. Tausayin kaina da na ahalina ya mamaye mini ruhina hawaey suka jiƙa mini fuska lajab kaina ya sara ƙirjina ya ci gaba da tsananta bugu.
A bayyane na furta"Anty ki yafe mini wallahi ba zan iya zama ba. Gwara na fi can inda ba a sannin ba kuma ban san kowa ba sai na fi samun kwanciyar hankali". Na ƙarƙare zancen ina tashi na zauna daɓas na leƙa ta taga na ga har gari ya soma yin haske na buɗe ƙofar ɗakin har na saƙalo ƙafata waje na hango su Yaya Alhassan suna shigowa da alama sai yanzu suka dawowa daga masallaci na yi wuf na shanye ƙafata na tura ƙofar ina leƙan su, zuciyata ta harba ganin Yaya Alhassan ya nufo ɗakin yayin da Amir da Umar suka shige ɗakinsu. Ban san abin da ya tuna ba sai kuma na ga juya ta ya bi bayan su Amir, na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ina dafe ƙirjina da yake bugu.
Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu ina tsaye kafin na buɗe ƙofan a hankali na fito, filin gidan wayam babu kowa don ranan Anty Zulaihatu a gidanta ta kwana, na riƙe takalmana a hannu kamar ƙadangaruwan bayan tullu haka nake yin tafiya saɗaf-saɗaf na yi sa'a su Yaya Alhassan da suka shigo ba su rufe ƙofar ba. Na ja na fita waje layin babu kowa da alama daga masallacin sallan asubahi kowa gida ya shiga saboda yanayin hunturu da ake yi, sanyi ya lulluɓe ko'ina ga wani iska mai daɗi da yake haɗawa da hakan yake alamta sauƙar ruwan sama a ko wani irin lokacin.
Sai da na ƙarewa ko'ina kallo gabar da yamma kudu da arewa kafin na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai nauyin kasa na soma lafiya. Sai da na bar cikin layin gabaɗaya kafin hango titi na miƙe, na dinga tafiya har sai da gari ya yi haske sosai mutane suka fara wucewa jifa-jifa domin gudanar da lamuran yau da kullum kamar yadda aka saba. Tun da na soma tafiyar ban tsaya ba sai da na iso babban tasha da ta fi wacce muke kaiwa talla girma da kuma mutane. Na tsaya cak na kasa gaba na kasa baya illa bin mutanen da ido nake yi ina ganin yadda suke ta zirga-zirga.
"Malama ki kauce daga kan hanya kin zo kin tare ma waje".
Na yi an yi zancen a zafafe kafin na matsa aka bangaje ni saura ƙiris na faɗi. Na ja ƙafafuna na je kasan wata itaciya na zauna na zabga uban tagumi.
"Baiwar Allah lafiya kuwa kika zauna kika yi shuru? Ko dai ba lafiya ne?".
A tsorace na ɗago kaina sakamakon furucin da suka yi wa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya. Na firgita sosai da ganin yanayin wanda ya yi zancen, matashi saurayi ne da fuskarsa ta sha ɗinki kamar bayan ƙwarya ya shigan da sam babu tsari a cikinta ga jakan kayan da yake rataye a kafaɗunsa. Ban gama dawowa daidai daga giyan mamakin da ya shayar da ni ba na ƙara jin sautinsa a karo na biyu.
"Baiwar Allah ko dai da kurma nake magana ne?". Na girgiza masa kaina alamar a'a.
"To na ce lafiya kuwa na ga kin saɓe daga cikin al'umma kin zo gefe kin raɓe".
"Lafiya ƙalau".
"Wannan kuma zance ne kawai kike yin sa wataƙila don ki ji daɗin bakinki. Amma duk wanda ya gan ki ya san da cewar akwai damuwa a tattare da ke".
"Babu komai".
Ya ɗage kafaɗunsa alamar babu abin da ya sha masa "to shikenan Allah ya raba mu da babu". Ya sa ya yi wucewansa ya bar ni a wajen haka na ci gaba da zama har rana ta ƙwalle ban gusa daga wajen ba, motocin da aka yi wa lodi suka fara tashi.
"Baiwar Allah zai fi kyautuwa ki sauya wajen zama tun da na ga kamar zaman ne yake yi miki daɗi. Don rana ya fito kuma ya na gasa ki".
Na saci kallonsa da gefen idona kafin na tashi daga wajen kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na sauya wajen zama ya biyo.
"Motar wani gari za ki shiga ne?".
Na soma zazzare idanu kamar shege a rabon gado, kamar daga sama na ji wani karan mota yana shelan sauran mutum uku motar garin jafari. Da sauri na furta "garin jafari zan je".
"Ai kuwa faɗuwa ta zo daidai da zama ni ma garin jafari na nufa sai ka tashi kawai mu shiga mota".
Na sadda kaina ƙasa"kuɗin motan ne ya faɗi a hanya ta ta zuwa nan".
"Ba komai kar ki ji kin damu mu shiga ba zai gagara ba". Ban kuma cewa komai ya yi gaba ina bin sa a gaba kamar raƙumi da akala har cikin motar babu jima aka sama ciko mutum ɗaya motar ta cika. Karan motan ya zo ya karɓan kuɗi riƙe da wani takarda a hannunsa in ba ka da kuɗin sai ya ce ka sanya lambar wayan wani nata ta yadda ko da na Allah ya kasance ba fata ake yi ba za a tuntunɓe sa.
Ko da aka zo kaina na rasa lambar wayan wanda zan saka ƙarshe da tunanina ya ƙore na saka lambar wayar Abbana ina rubutawa hawaye suna jiƙa littafin haka har na gama, na yi saurin goge su don na ga yadda mutumin ya kafe ni da ido kamar majigi.
Tun da motar ta ɗau hanya na ji gabaɗaya hankalina ya tashi nutsuwata ta yi nisa da gangar jikina. Tun da nake a rayuwata ban taɓa jin sunan garin jafari ba balle har na yi tunanin zuwa cikinta, ban san kowa ba amma yau ƙaddarata ta ja ni zuwa gare ta. Tafiya ce mai nisan gaske don a hanya muka sallan zuhur da kuma Asr dab ƙiran sallan magriba muka iso kowa ya fiffito, nan fa idona ya raina fata don ban san inda zan nufa ba. Tsoro da firgicin da nake ciki ya ƙara hauhawa tashin hankalina ya ninƙu.
"Baiwar Allah ke kuma haka ake yi za ki fito ba tare da kin jira ni ba".
Na yi ƙoƙarin ɓoye firgicin da nake cikin kafin na furta"a'a ba haka ba ne ina sauri ne shi yasa". Ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya ce"ina kika nufa daga nan? Kuma ke da za ki yi wannan doguwar tafiyar nan na gan ki ko jakan kaya babu". Na daburce na kasa cewa komai ina ta inda-inda da na kamo bakin zaren maganan sai ya zille.
Ya ƙara taku uku ya matso kusa da ni"tun kallon farko da na yi miki na ga ne akwai damuwa da firgici a tattare da ke amma kika nuna min ba komai. Tun da na gan ki babu ko jaka na dasa alamar tambaya akan ki don na san nisan tafiyar jafari da irin lalacewar hanyarta da wuya mutum ya ce a wuni guda ya dawo a ranar. Kin gan ni nan da kike ji da gani na ga abubuwa da yawa a cikin wannan duniyar, na ga ƴan mata kala daban-daban na yi mu'amala da mutane iri-iri. Tun daga yanayinki na yi zargi biyu wanda ciki dole ɗaya ya tabbata ko dai cikin shege kika yi kika gudu daga gida kike neman mafaka ko kuma iyaye ne suka wofartar da rayuwarki".
Kalamansa suka sanya hawaye suko mini kurmin idaniya da hakan ya ba shi daman ci gaba da maganan.
"Wannan hawayen da kike yi ya ƙara tabbatar min da abin da nake zargi akan ki".
Na haɗe hannayena waje guda"don Allah ka taimaka mini da inda zan zauna. Da zaran na sama inda zan zauna zan kama sana'a ko na aikatau ne na biya ka kuɗinki gidan hatta kuɗin motan da ka biya mini". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya.
"Kowacce yarinya da irin kalaman nan take fatawa ƴan mata. Indai wajen zama ne to kin sama akwai inda zan kai ki ki zauna kuma cikin mata ƴan uwanki".
"Na gode Allah ya saka da alkhairi".
Bai amsa mini ba ya zari jakarsa ya rataya ya kafaɗa ya tari adaidaita muka shiga ba a yi wani tafiya mai nisa ba muka tsaya a ƙofar wani gida ya fito ni ma na fito ya sallami mai adaidaitan. Kana ya yi gaba ina bin sa a baya har cikin gidan.
Tun daga shigar mu na sha jinin jikina, don wasu garke ƴan mata da samari muka iske manne da juna suna ta busa hayaƙin sigari gefe guda kuwa mata ne sun tsuke cikin shigar da bai taimaka da komai wajen rufe tsiraicinsu ba sun zage sai buga caca suke yi. Ya shiga wani ɗaki ya je na jira shi a waje.
Ina tsaye na yi an kwanto a gadon bayana na yi saurin zamewa cike da tsoro.
"Ke Lawisa wai me yasa kike yi min haka ne?". Ya yi zancen cikin maye yana ƙara nufo ni, duk tarin jama'ar da suke zaune a yalwataccen filin tsakar gidan babu wanda ya kawo mini ɗauki. Na kurma ihu yayin da na ga yana ƙoƙarin kai hannunsa saman ƙirjina. Lamarin da ya jawo hankalunsu zuwa gare ni sai dai babu wanda ya taso, mutumin da ya kawo ni ya fito daga cikin ɗakin yana tambayar abin da ya faru na irge masa komai. Bai ce komai ba ya ce mu shiga cikin ɗakin ya yi gaba na bi shi a baya.
Wata dattijuwar mace muka iske a ciki tana zaune da ɗaurin ƙirji a jikinta, duk da ban san giya ba amma ba ni da inkari akan cewa kwalban da take kwankwaɗa giya ne. Na tsuguna har ƙasa na gaishe ta amsa tana kallona kafin ta mayar da idanunta kansa.
"Aminu wanna ita ce baƙuwar takan?".
"Ƙwarai kuwa Hajiya Babban ita ce, to ya ya kika gan ta?".
"Ba laifi komai ya yi akwai kuma yiyuwan da za sama riba akan ta".
Na gaza gane abin da suke faɗa illa rarraba idanun da nake yi, ta ƙira wata ta zo ta ce da ita ta kai ni wannan ɗakin da babu koma a cikin sa, na tashi na bi bayanta. Ta kai ta cikin ɗakin babu komai a ciki face tabarma. Za ta fice na yi saurin cewa"don Allah ko zan sama rufa na yi alwala na yi salla?".
Ta yi sakeke tana kallona kafin ta ce"ruwa? Ai sai dai ki cire kuɗinki ki saya don duk abin da idanunki ya gane miki a cikin gidan nan na sayarwa ne". Tana gama faɗin haka ta fice ta bar ni tsaye cikin matsanancin mamaki na daɗe a tsaye kafin na ja kafafuna na zauna akan tabarma na kifa kaina da gwiwa ina tunanin makomar rayuwata.
Sallamar da na ji an yi ya sanya ni ɗaga kaina, na ga Aminu ne ya shigo da wasu ledodi guda biyu a hannunsa ya ajiye su a gabana ya zauna.
"Ga abinci da wasu kayan amfani na kawo miki, don na san za ki buƙace su".
"Don Allah nan ina ne ka kawo ni?".
Ba tare da shakkan komai ba ya ce"nan da kike ganin gidan masu zaman kansu ne". Babu shiri na miƙe tsaye"gidan ba masu zaman kansu kuma? gaskiya Allah ya sani ba zan iya zama a cikin wannan gidan ba, gwara na fita a cikin daren nan na nema inda zan kwana".
"A cikin garin nan dai ina da tabbacin babu inda za ki samu mafaka da ya wuce gidan nan. Amma idan ki na ganin za ki iya samu ba zan hana ki ga ƙofa nan sai ki bi ta inda muka shigo ki bita. Na san ba ki da ko sisi balle ki je ki kama wani wajen, kuma ma inda za ki kama ma ɗin ki na tabbacin za ki sama tsaro a can? Ki na tabbacin in kin je can ɗin kin tsira?".
Ya miƙe tsaye yana ci gaba da maganar"nan ne ya fi dacewa da ke don haka ki na mai ba ki shawarar za ki guje masa. Ga abinci da sauran kayan amfani in ki na buƙata za ki iya ci. Sauran bayanin kuma sai gobe kafin kin yanke shawarar zama ko tafiya". Yana dasa aya a nan ya fice ya bar ni tsaye kamar gumki.
Shirif! Na zube akan taburman ina kuka na ciro ɗan kwalina na cusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin fita. Rayuwa juyi-juyi wai kwaɗo ya faɗa a cikin ruwan zafi, ban da ƙaddara me ye zai kawo ni gidan masu zaman kansu balle har na yi rayuwa a ciki su?.
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
A nan na kawo ƙarshe littafin DAFIN HARSHE littafi na ɗaya. Shin ya ya rayuwar Amatullah za ta kasance a cikin wannan gidan? Shin za ta tsira da mutumci da tarbiyyan da ta zo da shi? Wani irin rayuwa za ta faɗa? Wani irin tashin hankali Anty Sawwama da iyalanta za su shiga idan aka wayi gari ba su ga Amatullah ba? Ta ina za su fara neman ta? Sannan daga ƙarshe wani irin gwarama za a yi tsakanin Anty Sawwama da Hafsatu idan ta ji labarin ɓacewar ɗiyarta?. Duk amshoshin waɗannan tambayoyin suna cikin littafi na biyu wanda za a posting ɗin sa daga ranar 10 November 2025 in Sha Allah, akan kuɗi naira N500 kacal babu ragi babu ƙari. Ga mai buƙata ƙarin yana iya tuntuɓata ta wannan lambar kamar haka 07038908713
Abin lura: ba complete document ba ne posting za a dinga a paid group daily har mu gama.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 24