Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suna sai kuma ya dace da kyakykyawa mai kyawun sura kamar ki. Gaskiya ki godewa Allah". Rai a jagule na cira kai na yi masa kallo guda tare da cewa"kullum cikin gode masa nake yi Malam". "Ya kamata ki ƙara masa don ba kowacce mace ba ce ta haɗa abubuwan da kika haɗa. Ga kyau ga sura ga kuma cikakken diri". Zumbur na miƙe ina nuna da ƴatsa"Malam ba na son maganar banza, ka ja girmanka in kana son na girmama ka". "Ba Malam nake ba sunana Haruna". Na ja doguwar tsaki ina tattare robina da almajiran suka gama sha na bar wajen zuciyata tana tafasa kamar talgen da ke bisa wuta. Duk da ɓacin ran da nake ciki wani sashin zuciyata yana cike da murna tun da na yi ɗari biyar don a tunanina na yi abun a yana mini har zuciyata tana kwaɗaita mini samun albarka daga bakin Umma abin da tun da na buɗi ido ban taɓa jin ta furta mini ba. A ƙofar zaure na yi kiciɓus da Auwal saurayin Ummi saura ƙiris jikina ya goge shi na yi hanzarin ja da baya . "A'uzubillahi mini shaiɗanir rajim!". Idanunsa ƙar a kaina ya ce"me ye haka? Kamar wacce ta yi karo da aljani?". Ban ba shi amsa ba na raɓa zan wuce ya sha gabana. "Ka matsa na wuce ba na son Ummi ta zo ta same ni a nan". "To ta zo mana ai ita ma kanta ta san kin fi ta diri da sura. Amatullah babu lafiyayyan namijin da zai ganki bai ji wani abu a ransa ba". Yanda ya yi zancen yana lumshe idanu shi ya fi komai ba ni tsoro. Ban ƙara firgita ba sai da na ji hannunsa a bisa ƙuguna. Na juye masa kunun a jikinsa na ɗauke sa da mari a kuncinsa. Jikina gabaɗaya yana rawa na kasa cewa komai kamar yadda na gaza motsawa daga wajen. Sautin marin da na yi masa shi ya ja hankulan mutanen gidan suka cika a zauren. "Amatullah lafiya? Auwal me yake faruwa?". Ummi da zuwan ta kenan ta jefa mana tambayar a haɗe. Na kasa cewa komai don bakina ya ƙi ba ni wannan damar sai Auwal ne ya soma cewa. "Babu abin da ya faru, wai daga ta shigo na ce in ta shiga ciki ta yi min magana da ke ina so na wuce. Shi ne ta fara gaggaya min maganganu da na tsawarta mata ta juye min kunun a jikina". Kowa ya saki salati da sallallami gami da tafa hannu. Sai a lokacin na sama zarafin magana"Auwal ka ji tsoron Allah. Wallahi Ummi ba haka ba ne ya faru, maganar banza ya tare ni da shi....". Kafin na rufe bakina ta ɗauke ni da wani gigitaccen marin da ya sani ganin baƙin duhu yana gilmawa. Za ta ƙara nuni wani Umma ta iso wajen ta riƙe hannunta. "Kar ki sake ki ƙara yin gangancin marinta. Don wallahi sai kin yi dana sani". Ummi ta fizge hannunta"ai kuwa dole na mare ta har ma da abin da ya ci uwar mari, ko ba ki ga abin da ta yi wa Auwal ba ne?". "Na gani shi uban waye ya ce ya aike ta ƙiranki? Ko zamansa take yi a cikin gidan da zai aike ba? Yanzu kuke biya kuɗi fa haka muke lalewa mu ma mu biya don haka muna da damar da za mu sakata mu wala a cikin gidan nan. Ke ma mai naman neman magana haka kike so ai, kullum burinki ki hannu cikin tashin hankali. Ƴar iska dantalalliya marar kishin uwarta". Tana dure zancen ta jawo ni kamar za ta fige mini hannu muka shiga ciki, ɗaki ta wurga ni ta hau huce takaicinta a kaina. [6/12, 6:29 PM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 0️⃣3️⃣ Da ƙyar na ƙwaci kaina na koma gefe guda na takure ina ji wani zazzaɓi yana ƙoƙarin rufe ni. "Ni kam ban san ke wacce iriyar yarinya ba ce mai baƙin jinin tsiya. Yarinya kamar ƴar zina ko wacce take da bakin iyaye komai aka yi miki babu alkarba sai ka ce karfa. Kunu abin banza ma ba za ki iya sayar da shi to ina da wani abun na daman, kina gani ganin idonki yadda Amira ta hucewa uwarta Sahura takaici da tallan wainar da take yi a kowacce rana a ƙalla tana yin dubu goma zuwa sha biyar amma ke kamar wacce aka sawa hannu komai aka yi miki babu sa'a. Oh! Ni Hafsatu ina ganin takaicin duniya". Muryata a raunane na ce"Umma na yi naira ɗari biyar fa". Ta wurga mini watsa uwar harara kafin ta ce"ina ɗari biyar ɗin?". Na soma laluma jikina sai dai wayam babu kuɗi babu alamarsa na yi tsilli-tsilli da idanu iwa kwarton da aka kama a cikin turaka. "Wallahi tallahi billahillazi la iya ha illa huwa Umma na yi naira ɗari biyar sai dai in ya faɗi a zaure". Ba ta ce da ni uffan ba illa kaɗa kanta da ta yi ta juya za ta fice sai da ta kai ƙofar fita kana ta ce"ki yi shirin makaranta". Tana rufe bakinta ta fice ta bar ni da saki sakakken ajiyan zuciya ina ƙara laluma jikina ko zan ga kuɗi. Har zanina na since amma babu kuɗi babu alamarsa na ƙara tabbatarwa kaina ba ya jikina, na zauna na yi shiru ina faman tunani barkatai. "Za ki fito ki tafi makarantar ko sai na shigo". Na tsinkayo muryar Umma kamar daga sama, zumbur na miƙe ina amsa da faɗin"Umma zan sauya kaya ne". Kayana na sauya na saka na islamiyya sai da na fito na yi alwala na koma ciki na yi salla kana na ɗauko jakata da sallaya na fito. Umma tana zaune tana ƙula farar aya a leda. "Na fito zan tafi". Ba tare da kalle ni ba ta ce"ki je ɗaki cikin samira ki ɗauki ɗari ki sayi wani abun ki ci, tun da baƙin hali ya hana ki ki sayar da kunun ". Godiya na yi mata na shiga na ɗauko kuɗin na fito sai a lokacin ta ɗaga kai kalle ni. "Ki maida hankali ki yi abin da ya kai ki sannan kuna tashi ki kamo hanyar gida. Ki zo ki kasa min ayar nan a ƙofar gida". "To in sha Allah". Na amsa da shi yana jin kamar ana yaye nuni wani nauyi daga ƙirjina. Ta inda na sama sauƙi duk zafin Umma da hargaginta gami da son kuɗinta ba ta taɓa gana ni zuwa neman ilmi, a lokuta da yawa ita take kora ni ko da raina baya so. Haka na fice ina zuwa zaure abin da ya faru tsakanina da Auwal ya fara dawo mini sabo a cikin kwanyata sai da na ƙare wa kaina kallon tsaf. Allah ya yi ni mace mai matuƙar diri da kyawun sura wanda ba maza kaɗai ba hatta ƴan uwana mata suna yabon dirin da nake da shi. Duk da ba ni da kyawun fuska amma ina da cikakken zubin diri, shekarata goma sha biyar amma ga wanda bai sani ba zai yi zaton na kai shekaru goma sha tara saboda girman jikin da nake da shi. Sai da na muka fito sallan asr sannan na sayi awarar ɗari na ci na sha ruwa muka koma aji, ƙarfe biyar daidai na yammaci muka tashi. Muka tsaya tattaunawa batun walimar sauƙar da za mu nan da satikai shida sai da aka tsara komai sannan muka watse. Muka kamo hanyar gida ni da ƙawayena biyu Ammi da Rauda. "Don Allah ku raka ni shagon Abbana na amso cefane". Rauda ta yi zancen cikin kwantar da murna. "Ni fa Ummata tana jira na na fitar mata da farar ayan da ta yi. Kin ga kuma yanzu lokaci har ya ja". Ta kuma marairace"don Allah ki yi haƙuri mu je ba za mu daɗe ba, kin ga Ammi yanzu za mu rabu da ita ta iso gida". Na jim ina tunani kafin na ce"mu je amma ba za mu daɗe ba". Muka nufin shagon muna tsallake kwalta muka rabu da Ammi ta shige gidansu. Babu daɗewa muka isa shagon muka duƙa muka gaishe shi ya amsa fuskarsa a washe ya ɗauko ledar ya ba ta ta amsa da godiya. Har muka har ƙofar shagon bai daina sa mana albarka ba. Lamarin da ya yi matuƙar burge ƙalbina sai da ta taɓo ni kafin na dawo daga kogin tunanin da na faɗa. Ta ɗage mini ido guda"tunanin me ye kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru". Na sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya mai sauti kafin na sama zarafin cewa" ba zan miki ƙarya ba Rauda rayuwar gidanku yana burge ni, yadda muke mu'amala da iyayenku abin sha'awa. Babu tsangwama balle hantara uwa uba kullum cikin sa muku albarka suke yi da yi muku addu'ar shiriya. Ku kam kun dace". Sai da ta murmusa kafin ta ce da ni"haka kowa yake cewa amma ke ma ai kin dacen mahaifi Amatullah, kowa ya shaida cewar mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kiyaye halak da haram. Sannan duk layinku da ke ake kwatance wajen kyawawan ɗabi'u da halayen ƙwarai, ga nutsuwa ga ƙur'ani". Duk mu biyun muka fashe da dariya haka muka ci gaba da tattauna har na iso gida kana muka yi sallama na shiga gida ita kuma ta wuce, layin gabanmu inda za ta iske gidansu. "Mun rantse da girman zafin Allah ba za ta taɓa saɓuwa ba wai bingida a ruwa. Dole mu ƙwatawa ƴar uwarmu haƙƙinta. Don ba daga sama ta faɗo ba ita ma ƴa ce kamar kowa mai gata da galihu yau sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi". Kalaman da suka fara sauƙa a ƙofofin kunnuwana kenan yayin da na kutsa kai cikin gidan. Maman Adnan ce tsaye ta sha ɗamara ga kuma wasu jibga-jibgan mata uku masu ƙiran samudawa tsaye a kutsa da ita wanda suka kasance ƴan uwanta ne na jini. Da ƙyar na jan ƙafafuna na ƙariso ƙofar ɗakinmu na rakuɓe jikin Ummata da take zaune tana sauraran rediyo ta yi bakam kamar ba ta san wainar da ake toyawa ba. Na durƙusa kusa da ita ina cewa"Umma wai me yake faruwa ne?". "Safina ce ta ɗebo ƴan tashan ƴan uwantan suka zo cikin nan suke yin tijara. Wai don mijinta ya lakaɗa mata ɗan banzan duka, yo daman wacce ta mai da kanta jaka kam ai dole ta zama abin jibga a wajen miji a ko yaushe". Ɗaya daga cikin matan ta yi kukan kura ta yo kan Umma, kallo kawai Umma ta yi mata ta tsaya cak ta kasa gaba balle baya. Na sha jin ana cewa Umma tana kwarjini da cika ido wannan dalilin ya sanya kowa a gidan yake matuƙar shakka da tsoron shiga gonarta ban gama gaskata hakan ba sai yau ɗin nan. Ƙafarta ta ɗaura ɗaya bisa ɗaya tana ƙare musu kallon ɗaɗɗaya"ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kare ya ja ta. Idan ki na ji da rashin kunya da tashanci ne to gidansa kika zo. Da kin ƙariso ai da na nuna miki yadda ake yin wasan". Maman Adnan ta ɗaura hannu a ka ta fasa ihu tana durƙushewa akan gwiwoyinta"shikenan na shiga uku na lalace wannan matar so take yi ta guntile min igiyoyin aurena. Anti ku taimake so take ta ƙwace min miji, jama'ar gidan nan muna gani kun kasa cewa komai". U Ɗaya daga cikin mata ta ɗago ta tana faɗin"ta yi tsararo ta raba ki da mijinki Safina. Idan taƙamarta sammako da to mu a hanya muka kwana idan ta san wata ai ba ta san wata, sai mun nuna mata faɗa da aljani sai an shirya wallahi kin taɓo tsuliyar dodo". Tana ada aya ta figi hannun Maman Adnan suka wuce ɗakinta raguwar mata biyun suka rufa musu baya. Shewa Umma ta saka har da tafa hannu tana faɗi"ai ni wargi ce daidai ƙugun ko wani ɗan iska, mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa". "Umma don girman Allah ki fita daga harkan mutanen nan ki bar su su zauna lafiya da mijinta..". Kafin na ƙarisa ta sauƙe mini ƴatsunta biyar a fuskana, a kufule take cewa"ke har me ye kika sani da za ki zaunar da ni kina faɗa min abin da ya dace na yi ko kar na yi. Amatullah ki fita daga idona na rufe daman ina cike da ke ƴar iska mai kunnen ƙashi, ban ce da ke ki dawo da wuri ki fita min da farar ayan nan ƙofar gida ba?". Kaina a sunkuye na ce"mun tsaya tsara yadda walimar sauƙar mu za ta kasance ne". Ba ta ce da ni komai ba kamar yadda ba ta ba ni umarnin tashi ba, haka na ci gaba da tsugunawa akan ƙafafuna don na san idan na tashi ni na san abin da na taro. Sai da aka yi ƙiran sallan magrib kafin na tashi daga wajen na je na yi alwala na shiga ɗaki na yi salla na fito na soma ciki-cikin haɗa wutan dare. Sai da na sha baƙar wahala kafin wutan ya kama na aza sanwa na ɗauko kayan miya na soma yankawa. Ganin mutum tsaye a kaina ya sani hanzari ɗaga kaina ina dafe ƙirjina ganin Ummi ce ya tursasa mini sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya. "Ummi lafiya? Kika zo kika yi mini tsaye a tsakiyar kaina?". "Watau har kin manta abin da ya faru ko?". Ta yi ƙwafa kafin ta ɗaura da cewa"ai idan maye ya manta uwar ɗa ba za ta manta ba. Ke har kin mance rashin mutuncin da kika yi wa Auwal ɗazu watau a tunaninki kin ci banza ko?". "Ni kin ga na har na kanta kimai. Kin ga Ummi ki tsaya mu yi magana ta fahimta wallahi Auwal ƙarya ya faɗa ba abin da ya faru ba kenan, shi ne fa ya tare ni da maganar banza". Ta doka mini tsawa"dalla! Rufe min baki, ko da Auwal ya kasance ɗan iska ai ba kuma kai matsayin da zai tunkare ki da maganar banza ba. Amatullah zan miki gargaɗin dab da mari ki fita daga harkan Auwal, don tun ba yau ba ina ankare da ke a duk lokacin da ya zo hira kin ginda shiga da fita kenan kina shawagi a gabansa kina juya manyan mazaunanki don kawai ki ja hankalinsa. To hawainiyarki ta kiyaye rama ta kuma wallahi Auwal dai nan gani nan bari ɗumamen maya na gaba ya yi gaba". Sake da baki da hanci nake kallon ta har ta kammala zancen tsabar mamakin da ta ba ni. "Allah ya ba ku haƙuri ke da shi". Na furta a taƙaice ina mayar da hankalina ga aikin da ke gabana. "Idan ya ba ni ki ƙwace banza shashasha, girman buredi kawai". Ban tanka mata ba har ta ƙarishe tsayiwarta ta gaji ta tafi, tana barin wajen Amira tana isowa ta ja kujera ta zauna. "Wai me ye take faɗa miki ne?". "Gargaɗi ta zo ta yi mini akan saurayinta Auwal". "Cab! Ke kuma kika ce mata me ye?". "Me ye kuwa zancen da ya wuce na ce ta yi haƙuri". Ta tafa hannu kafin ta ce"wallahi in ni ce ba ta isa na ba ta haƙuri ba, akan wani saurayinta mai zubin ƴan daudu ga shegen kallon matan tsiya". Ta ɗago kai na yi mata kallo guda kafin na furta"ki rufawa kanki asiri ki yi shuru kafin ta ji ki wani rigimar ya kaure. Kin san ita ba tsohon ta mutu take yi ba balle ta rayu". Ta tsirtar da tsaki"to sai me ye in ta ji? Ke dai Amatullah Allah ya ƙara miki haƙuri kawai". Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi na amsa da cewa"Amin ya Allah". Mun ɗan taɓa hira kafin ta miƙe tsaye na bi ta da kallo kafin na yi magana ta riga ni. "Bari na yi shiri fita tallan dare kafin lokaci ya ƙure". "Da kin zauna mun yi hirar mu ke da in kika fita sai mutum ya yi bacci kafin ki dawo". Ta bushe da dariya kana ta ce"dududu ƙarfe nawa nake dawowa Amatullah? Karfe sha ɗaya ne fa zuwa da rabi. Ke dai bari na wuce na san yanzu an gama dafa min awarar a gidan Tasalla". Kasa cewa da ita komai na yi har ta wuce saboda mamakinta da nake yi na rashin tsoro komai dare ba ya hana ta fita talla haka kuma za ta ratso ta dawo gida idan ta gama soya awarar. Sai da na kammala girkin na kwashe na tattare wajen, na ɗeba nawa na ci a wajen na kai wa Umma na ta kana na ajiye na Abba. Wanka na yi na yo alwala na yi sallan isha'i na ɗauko littattafaina na fito zaure ina nake ƙara wa yara karatu bayan sallan isha'i. [6/14, 11:31 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 0️⃣4️⃣ Muna tsaka da karatun Abba ya shigo na miƙe zan karɓa ledar dake hannunsa bayan na yi masa sannu da zuwa. "Zauna ku ci gaba da karatunku". Ya furta fuskarsa washe da annuri, hasken ƙwan fitillan aci bal-bal da na kunna a wajen shi yake ba ni damar kallon fuskarsa har na fahimci yanayin da yake ciki. Ƙarfe tara na sallami yaran kowa ya watse kafin na koma cikin gidan. "Hafsatu na gargaɗe ki da ki fita daga harkan Ibrahim da kuma matarsa amma kin yi kunnen uwar shegu da zantukana. Ki sani kin fara kai ni bango fa, me ye haɗinki da mijin wata bayan kasancewarki matar aure? Da ilminki da komai amma kike takewa wane irin rayuwa ce wannan kika ɗaurawa kanki?. Saboda son zuciyarki da masifar son kuɗi ki ja wa baiwar Allah duka daga wajen mijinki kuma tsabar tsaurin ido irin na ki kika yaɓawa ƴan uwanta magana". Zantukan Abba kenan da na fara cin karo da shi yayin da na kutsa kai cikin falon. Jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, shirib na zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin ɗan madaidaicin falon na mu da hakan yake ba ni damar sauraron abin da suke tattaunawa daga cikin uwar ɗaka. "Roƙansa kuɗi na yi ko kuma maula na yi? Da za ka ɗebo tsamin jikinka ka zo kana yi min hayagaga a kaina. Dare ma da ya kasance mahutan Bawa ba za ka taɓa barin mutum ya huta ba". "Hafsatu ni kike cewa ina yi miki hayagaga?". "Kai ɗin fa Munniru. Wani irin masifa ce wannan? Kai komai na yi a idanunka ban fita ba. Ka ƙwammace ka goyi bayan matar wani akan ka goyi bayan matarka ta sunna har kake ƙiran ta da baiwar Allah. Duka kuma ba ni na ce ya sake ta ba tashin hankalinta ne ya jaza mata, ƴan uwanta kuma da ta kwaso ba a haifi shegiyar da za ta zo har inda nake ta gaya min magana na ƙyale ta ba. Kuɗi kuwa ko sau dubu sai ɗauka ya ba ni billahillazi sai na amsa ai ba tursasa masa na yi ba shi ya yi niyya, kai ba ka ba ni ba kuma ban ga dalilin da za ka hana ni karɓa ba". Sai mintuna suka shuɗe kafin Abba ya ce"ki kiyaye harshenki, ki dinga tauna lafazi kafin ki furta shi. Domin da zaran ya fita to ba a iya dawo da shi. Shi yasa Annabinmu da kansa ya ce kuffa alaika haza ma'ana ka kiyaye wannan a gare ka watau harshe, dafinsa ya bi na bakin maciji. Ke komai ya fito daga bakinki za ki yaɓawa mutum ba tare da tunanina ba, Hafsatu ina guje miki ranar da za ki yi dana sani". "Babu dana sanin da zan yi Munniru, bakinka ya sari guntun gashi". Ta yi zancen tana banko labulen ɗakin ta fito falo. Kamar wacce aka tsigara wa matsilli haka na zabura na tashi, kallon da ta tsare ni da shi ya sani saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. "Watau kin na zaune a nan kin kasa kunne kina sauraron abin da muke tattaunawa ko?". Na girgiza kaina"ban daɗe da shigowa ba ma". Ta doka mini tsawan da ya haifar mini da rawar jiki. "Dalla rufe min baki munafukar banza munafukar wofi. Duk ba ke kika ce ummul abasin faruwar komai ba. Shegiya ƴar iska mai jinin tsiya". Kafin na ce wani abu tunin Abba ya fito falon cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa kammalalliyar fuskarsa da farin gashi su ka yi masa ƙwawanya a saman harbarsa. Ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa da hakan yake tabbatar da ya kai ƙololuwan ɓaci rai da faɗa wa cikin tarin takaici. "Na hane ki da jifan Amatullah da waɗannan munanan kalaman amma kin liƙa wa kunnuwanki gayan tuwo. Shin ashe idan wani ya ce da ita shegiya ko ƴar iska abin ba zai yi miki ciwo ba kenan?. Ke uwa ce ki zama mai tausasa lafazinki akan Amatullah. Ba na son mins sa'in sa dake amma ke kike jan komai". "Mtscheew". Umma ta ja dogon tsaki tana yi wa kanta mazauni a kujerar da na tashi daga kanta, jinjina kansa kawai Abba ya yi kafin ya maido da duban sa gare ni yana faɗin"Amatullah ki kai min ruwan wanka". "To Abba". Na amsa da shi yayin da nake fita daga falon na ɗauki bokiti na cika da ruwa na kai masa bayi. Kana na zo na sanar da shi. A uwar ɗaka muke kwana tare da Umma yayin da shi kuma Abba yake kwana a falo, tun da na yi girma na yi wayo muke yin hakan wannan dalilin ya sa kullum sai na yi addu'an Ubangiji ya buɗa wa Abba ya yi gidan kansa ko da kara ya kewaye mana mu koma. Mu huta da wannan baƙin masifan takuran. Kamar a mafarki haka nake jiyo sautin maganar a tsakiyar kaina na mirgina ina murtsike idanuna tare da buɗe su kana na maida su na lumshe. Duk da haka ban daina jin sautin yana tashi ba dole ƙanwar naƙi na tashi ina yin miƙa daidai lokacin limamin masallacin kusa da gidanmu ya rangaɗa ƙiran sallan assalatun cikin zazzaƙan muryarsa mai sanyi. Na tashi zan fita falo na jiyo Abba da Umma ne suke magana na koma na zauna, don ba na ƙaunar sauraron abin da suke tattaunawa wanda ina da tabbacin zai iya zama sirrinsu ne wanda bai dace na ji ba. Ina nan zaune Umma ta shigo tana ta bambamin da ban gane takamanmen akan abin da take yi ba, na tashi na fita domin ɗauro alwalan sallan asubahi na tarar da an haɗa wani rigimar a filin tsakar gidan. Maman Rayyan ce take ta surfa masifa Asabe tana taya ta, a nan na tsinci kan zancen wai a daren jiya ne gandaderen ƙato ya shiga har uwar ɗakinta yana shafa jikinta, kasancewar mijinta ba mazauni ba ne ya kan yi watanni biyar zuwa shida ba ya gida. Har hantsi ya fito masifa da bala'in bai lafa ba abu kamar wasa har ya kai gaban mai unguwa da wasu manyan unguwan, ina kwance a ɗaki ina fitan karatun islamiyya Amira ta shigo sai da na kai ayar ƙarshe da nake karantawa na cikin suratul tagabun kafin na rufe ƙur'anin ina duban ta fuskana cike da murmushi. Kafin na yi magana ta datsi numfashina"karfe goma da rabi na dawo, na san abin da za ki tambaya kenan". Na murmusa kafin na ce"ai ke da kan ki Amira ya kamata ki yi wa kanki faɗa, wannan daren da kike kai wa a waje ba mutuncinki ba ne a matsayinki na ɗiya mace. Ko na miji ne ai duk inda goma zuwa sha ɗaya ta yi daga lokacin ta fara neman hanyar gida balle kuma mace". Ta yatsina fuska kafin ta ce"kin ga ni ba wannan ba ne ya kawo ni. Amshi ki buɗe ki ga". Ta ƙarishe zancen tana ajiye mini wani baƙin leda a bisa cinyata, ta bi ta da kallon mamaki. "Mene ne a ciki?". Na jefa mata tambayar ina juya ledar a hannuna. "Ke kuwa ki buɗe mana idanunki su gane miki". Kamar yadda ta faɗa hakan na yi na soma ciki-cikin buɗe ledar. Kwalin waya ce sabuwa dal da ita ƴar shafai. Na kwasa ihu ta

Chapter 2 of 24