Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kake gani na ɗin nan abun kunya gaba na ba shi ba baya ba. Ka jira tukunnan idan ka sama naka ɗiyar sai ka yi yadda kake so da ita amma ba yanzu ba, Amatullah ƴata ce babu wanda ya fi ni ƙarfin iko akan ta". Cike da takaicin zantukan Umma, Ustaz ya jijjiga kansa tare da sadda kansa ƙasa. "Allah ya kyauta, Allah ta yi mana mai kyau". Ya furta yayin da yake ficewa daga cikin gidan ba tare da ya ɗago kansa ba. "To ku kuma munafukai masu kunnuwan son jin gulma da tsegumi, sai ko wacce ta ja jikinta ta bar nan". Umma ta yi zancen tana wurgawa Maman Adnan da Asabe da suke yi cirko-cirko a ƙofar ɗakunansu harara, kafin ta ja dogon tsaki ta shige ɗaki. Ban san sa'ilin da ƙwalla suka soma tsere a bisa kuncina sai ɗuminsu na ji suna sauƙa a saman haɓarta, daidai lokacin da Amira ta dafo kafaɗuna tana doge mini hawayen da suka ɓata mini fuska. Ta ja hannuna zuwa ɗakin su a nan ta dinga lallashina da kalaman masu kwantar da hankali da haifar da nutsuwa a cikin rai da ruhi. Wayarta ta soma ruri ta ɗaga ta sanya a kunnenta, hankalina baya gare ta hakan ya sa ban ci abin da take faɗa ba har sai lokacin da na ji ta duga ihu gami da tashi tsaye ta daka tsalle. Na fita da kallo ba tare da na ce da ita ko kanzil ba har sai da ta gama wayar kafin ta kallo ni, fuskarta kamar gonar auguda bakinta har kunne ta soma cewa"albishirinki Amatullah". "Goro". "Fari ko ja?". Na juya idanuna kafin na ce"fari ƙal kamar haƙwaranki". "Yau Mansur zai dawo kuma ya yi min alƙawarin yana shigowa garin nan a ƙofar gidan nan zai tsaya. Saboda ya yi wa kansa alƙawarin da ni zai fara tozali da zaran ya dawo". "Allah ya dawo da shi lafiya, Allah kuma ya bar ƙauna". Cike da annuri ta furta"Amin na gode". Ta ƙare maganar tare da rungume ni. Mun ɗau lokaci muna tattaunawa har Ummanta ta gama toya waina ta zubo mana muka ci, na baro ta akan za ta shiga wanka. Na iske Umma har ta kammala dama kunnun na yi mata sannu da aiki ta yi banza da ni, sai da na jira Amira ta fita kana ni ma na shiga na yi wanka muka shirya muka fita muka yada zango a inda muke zama a tasha. Kan ka ce kabo mutane sun yi mana rumfa sanyan waina da kunun ake yi babu ƙauƙautawa, tun daga nisa da na hango Bashir na fara haɗe fuskata ban bar wata ƙofar da zai iya yi mini kowacce iriyar maganar ba. Ya iso ya zauna suka gaisa da Amira suka ɗan taɓa hira ina jin su ban soma baki ba. "Bari na kai wa Naziru masarsa kafin ta yi sanyi". Na tsikayo muryar Amira. Na bi ta da ido don na san da gayya ta yi maganar, na yi tsam na riga ta miƙewa ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani. "E mu je na raka ni, tun da muke tashar nan fa kin san babu inda na taɓa zuwa a cikinta". "Kin san ke ma ai hakan ba zai yiyu ba. Kayan kuma a waye za mu bar wa". Na saurin tarar numfashinta" ba ga Bashir yana zaune a wajen ba, sai mu bar mi shi". "Bashir kuma?". "Ƙwarai kuwa, Bashir ko kana da wani uzurin ne?". Na yi zancen cikin sanyin murya mai cike da taushi gami da jawo hankali mai sauraro. "Kin san ance ai sayon giwa ya take na raƙumi, ko ina da wani uzurin ai ya sama dole na zauna na jire muku kaya tun da Gimbiya da kanta ne ta buƙaci hakan". Ya yi zancen yana washe baki kamar wanda aka yi wa kyautar kujerar hajji da umra. Ta yi masa fari da ido kafin muka bar wajen tafiya ce mai ɗan nisa muka yi kafin muka iso bakin wasu shagona biyu. "Ki jira ni anan bari na shiga na kai masa". Na yi wuf na riƙo hannunta"Amira shiga za ki yi? Kamar ɗaki ne fa?". "Ba ma kama ba ne ɗauki ne, ke dai kawai ki jira ni yanzu zan fito". Ba ta jira abin da zan ce ba ta fizge hannunta ta shige ta bar ni tsaye a wajen ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali. Tun ina tsaye akan ƙafafuna har sai da suka gaji Amira ba ta fito ba, ɗakin da yake kusa da wanda Amira ta shiga aka buɗe ƙofar aka fito, wata mai tallan awara ne ta fito daga ɗaƙin riƙe da roban awaran a hannunta yayin da wani mutum yake bayanta daga shi sai singileti da gajeren wando. Ya miƙo mata kuɗi yana faɗin"yau fa ba irin farashin kullum zan biya ba, don ba ki yi min yadda nake so ba don haka ga wannan ki je ki rage zafi". Ta yi masa wani mungun kallo kafin ta amsa kuɗin" kawo ai an ce raba arne da makami ibada ne". Ta kai aya tana kwafce kuɗin daga hannunsa.Ya ɗaga hannu zai maka duka ta yi hanzarin kaucewa. "Matsalan ƴaƴan matsiyata kenan kana son su da azurki kuna ɓokarewa. Da ni kike zance yarinya". Ya yi zance a kufule yana yin ƙwafa. Daidai sanda zai shige ɗakin muka haɗa ido da shi ya yi mini ɗagowa, da hakan ya sanya ni sauri rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, kafin kakkauran muryarsa suka dira a ƙofofin kunnuwana. "Ke dan ubaki me ye kike yi a nan? Kuma me ye kika tsaya kina kallo?". Na ji maganar ƙarshen a kusa da ni na cira kaina na gan shi tsaye a gabana. Gaba ɗaya na ruɗe hakan ya sani gaza cewa komai. Har Amira ta fito ta same mu a haka. "Amatullah me ye yake faruwa? Me ye ya haɗa ki da shi?". "Babban yarinya daman kin san ta ne?". "Ƙwarai kuwa tare muke da ita". Ya gyara tsayinsa yana kallona tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"ga ta kuwa ƴar ɗas da ita komai na ta cif-cif. Cikakken ƙirji ga kuma faffaɗan ƙugu". Take na ji wani jarumta ya zo mini ruɗewan da na yi lokaci guda na neme shi sama ko ƙasa na rasa shi, na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata idonuna har sun soma ƙanƙancewa don masifa. "Ahir ɗinka ko kai maye ne sai dai ka ci kanka". Ina ada aya anan na figi hannun Amira kamar zan raba shi da gangar jikinta muka bar wajen, ba mu tsaya ko'ina ba sai wajen kayanmu na zauna a mazaunina ina jin zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka ɗaura a bisa wuta. "Har kun dawo kenan?". Bashir ya tambaya. Na yi buga masa wani mungun kallon da bai ƙara yin gigin kallon inda nake ba balle ya yi nuni wata magana. Sai Amira ce ta ba shi haƙuri ta ce gobe ya dawo, muna gama sayar da kayanmu muka haɗa su almajiran da suke kwasar mana suka ɗeba suka yi gaba muna biye da su. "Don Allah ki dunga ɗaukar abubuwa a hankali Amatullah. Rayuwar nan fa sai ana kai zuciya nisa". Na galla mata hararar"babu wanda ya isa ya yi nuni maganar banza ba tare da na mayar masa da martani ba". Ta sheƙe da dariya mai isarta kafin ta ce"ai kuwa duk mazan yanzu haka suke, maganar batsa ya zama ruwan dare a wannan zamani tsakanin samari da ƴan mata. Sai dai in ba za ki yi soyayya ba balle aure don duk maza halinsu ɗaya ne. Musamman ke da Allah ya bai rage ki da komai ba kina da kyawun sura da diri ina yaƙinin babu namijin da zai ganki bai yabi surarki ba, Amatullah surarki jikinki kawai ya isa namiji ya so ki. Shi yasa kowa ya ganki sai ya yabe ki". Na ja dogon numfashi na fesar"Amira akwai na tabbatar akwai. Akwai namijin da muka rabu da shi bai yi mini magana akan kyawun sura na ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi har muka rabu bai yi mini maganar banza ba". "Amatullah ƙarya kike yi in akwai kuma ki faɗa min wanene wannan? Ni kuma zan tabbatar miki da a cikin biyu dole akwai ɗaya, ko dai ba shi da cikakken lafiya ko kuma idanunsa ba sa aikin su yadda ya kamata". Na tsaya cak a inda nake ina kallonta cike da yaƙini na ce da ita"ki yarda da duk abin da zai fito daga bakina, tabbas akwai". [9/28, 9:31 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 2️⃣2️⃣ Tsare ni ta yi da ido tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta jijjiga kanta alamar duk abin da na furta bai sama matsuguni a cikin kwanyata ba. Balle har zuciyarta ta aminta da shi. "Kin ga Amatullah ki zo mu tafi mu bar wannan maganar". Ban ce da ita komai ba ta yi gaba na bi ta a baya babu abin da nake yi illa saƙe-saƙe a cikin raina, kalamanta suna yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata. Har muka kai gida cikinmu babu wanda ya ce ko kanzil muka shigo da kayayyakinmu ciki. Har na nufi hanyar ɗakinmu ta dakatar da ni ta hanyar faɗin"kar ki manta yau Mansur zai dawo kuma komai dare a nan zai fara tsayawa. Don haka akwai shirye-shiryen da zan yi wanda ina buƙatar taimakonki". Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kafin na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna na ce da ita" zan je islamiyya fa amma....". Ta katse ni"idan ba dole ba ne ki haƙura mana da zuwa na yau ne fa kawai". "Ki yi haƙuri Amira ya zama dole ne, kin ga sauƙarmu fa wasa gaske sai ƙara matsowa yake yi. Amma na yi miki alƙawarin zan dawo da wuri". Ta faɗaɗa annurin fuskarta"yauwa to jiran ki". Muka sakarwa juna murmushi kafin kowa ya shige ɗakinsu, Umma na iske a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana sauraron rediyo, na yi sallama ta amsa mini kamar wacce aka yi wa dole na durƙusa na yi mata sannu ba ta kula ni ba, na ajiye mata kuɗin cinikin da na yi. "Umma ga kuɗin na sayar da shi tas ban dawo da ragowa ba". Ba tare da ta kalle ni ba ta ce"kin kyautawa kanki". Daga haka shuru ya cika ɗakin na wani lokaci kafin na gusar da shi ta hanyar faɗin"Umma daman ina ta so na yi miki magana akan bikin sauƙarmu da yake ta matsowa, akwai ankon atamfa da hijabi da zamu yi shi ne nake son idan Allah ya hore miki ki yi mini ko da hijabin ne kaɗai". Sai a sa'ilin ta cira kai ta kalle ni. "Saura kwana nawa ne yanzu sauƙar nakun?". Cike da farin ciki na gyara zama na soma zubo mata bayani daki-daki wani na bin wani. "Yanzu dai saura kwana ashirin da biyar cif sati uku kenan ƴan kai". "Allah ya kaimu lokacin". "Amin ya Allah, me ye za a ɗaura?". "Ki dafa iya abin da za ki ci". "To". Na amsa mata da shi ina jin raina ya yi mini ƙal zuciya ta washe ta yi tas. Taliyar murji na tafasa na ci da manja da yaji. Wanka na shiga tun ina banɗakin nake jiyo hayaniya har ana dukan ƙofar banɗakin hakan ya sani saurin zura zumbuleliyar hijabinta da na shigo da ita, ina gama sawa ana bankaɗo ƙofar tamkar za a karya ta. "Na rantse da Allah sai kin fito don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa". Furucin Ummi kenan da suka sauƙo a ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu ta finciko hannuna ta yi waje da ni. Tsabar ɓacin rai da baƙin ciki da takaicin da suka yi wa raina rakon dangi ban san lokacin da idona ya makance ba na sauƙewa Ummi mari a kuncinta. Marin da ya jawo hankulan sauran mutanen zuwa gare mu. "Ubara uban can! Ni za ki mara Amatullah? Ai kuwa kin taro balbalin bala'in da babu ranar mutuwarsa. Daga nan har yanzu lokacin da mahadi zai bayyana". "Na mare ki ɗin na ce na mare ki Ummi ki yi duk abin da za ki yi. Wani irin wulaƙanci ne wannan ina banɗaki ina wanka za ki buɗe mini ƙofa, shin ba ki yi tunanin a wani irin halin za ki riske ni ba?". Ta yi hanzarin katse mini numfashi"babu ruwa da ko wani irin hayaniya zan same ki, ai kina ganin ruwana a ƙofar banɗakin kika shiga don haka ban ga dalilin da zai hana ni fiddo da ke waje ba ko da kuwa tsirara kike". Baƙin cikin kalamanta ya tursasa mini runtse idanuna ina jin rai da zuciyata yana wani irin tafasa kafin na yi magana Amira ta iso wajen ta nema jin ba'asin me ke faruwa Ummi ta yi caraf ta amshi zancen tamkar jira take yi. "Ruwa na ajiye zan shiga banɗaki tana gani amma don tsaurin ido ta riga ni shiga shi ne ni kuma na shiga na fiddo da ita". Tsabar mamaki Amira ta riƙe ƙungunta"kanbu! Kika shiga kika fito da ita? Ke kuma Amatullah kina tsaye duk aka yi wannan abun?". "Ai in gaya miki Amatullah ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ta ɗauke Ummi da mari in ni ma kaina sai da na ji raɗadinsa balle ita kuma da aka sauƙe shi akan kuncinta". Furucin Maman Vector kenan cikin gurɓatacciyar hausarta da har yanzu ba ta hau hanya ba. "Tabbas kin cika cikakkiyar ƴar halak, Wallahi da ba ki ɗauki wannan hukuncin ba Amatullah takaici da baƙin ciki sai ya hana ni motsawa daga nan wajen". "Na rantse da Sarkin dake dake busa min numfashi ban zan yarda ba. Ko sama da ƙasa za su haɗe sai na rama marin da kika yi min, tun da ni ba jakar uwarki ko ubanki ba ne kuma ba cin azurki na zo yi cikin gidan nan ba. Yadda kuke biyan kuɗin haya haka mu ma muke biya". Ummi ta yi ikirarin tana tankaɓar da ruwan da yake cikin bokatin ƙarfe da za ta shiga wanka da shi ta sure shi ta nufo ni gadan-gadan da nufi rotse mini goshi. Ƙam na tsaya a inda take tsaye kusa da Amira na riga da na ƙudurce a raina cewar duk abin da zai faru sai da ya afku. Ba zan matsa ba balle na yi ƙoƙarin guduwa in ta fasa yin abin da ta yi niyya ma ta raina iyayen da suka yi silar kawo ta duniya. Kafin ta iso gare ni muka ji tas sautin sauƙar mari duk muka jiyo da hakan ya yi daidai sake wani gigitaccen ihun da Ummi ta saka tare da zube a ƙasa tana yin burburku. Duk muka tsayar da idanunmu akan Baban Adnan da yake tsaye a wajen cikin tsananin fusata ya yi cilli da bukatin da ya amshe daga hannun Ummi. "Wannan wani irin fitina ce haka? Babu dama mutum ya yi aikin kwana ya dawo gida ya kwantar da haƙarƙarinsa ya huta sai kun ɗaga sa. Kar ku sake ku kai ni bango a cikin gidan nan don idan har hakan ya faru to kowa ba zai ji daɗi ba daga babba har yaro, ko wani bala'i daga gare ki yake fara ɓullowa Ummi". Ya ƙare zancen tamkar zai kai wa Ummi da take yashe a ƙasa duka. "To wallahil azim yau kam ba zan yarda da wannan cin kashin da ake mana, babu dama abu ya haɗu yaran nan sai ka yi wankan tsarki ka tsunguma ciki ka yi kane-kane ka juya zancen ka ba wa Amatullah gaskiya, don ita ce ta gaban goshi". Furucin Maman Ummi kenan yayin da take ɗaura ɗamara tamkar mai shirin tafiya filin yaƙin duniya na biyu. "Idan ba ki rufe min baki ba yau sai na nuna miki iyakarki a cikin gidan nan, yanzu waya kawai zan ɗaga kawai na ƙira azo a kwashe ku a kai ku bayan kanta". Tsam Maman Ummi ta sha ruwan jikinta ta koma yin wasu ƙananan maganan, ta zo ta ɗaga Ummi suka wuce ɗaki suna cin alwashi akaina. Kaina kawai na jijjiga har yanzu ban sauƙo daga dokin zuciyar da na hau ba na wuce ɗaki, na wuce Umma ba ta ce da ni komai ba shiryawa na yi na fice islamiyya. Kaina a ƙasa tun da na fito daga gida har na isa islamiyya ban ɗago ba, raina cike da takaicin da kuktun abin da Ummi ta yi mini. Babu shiri na saki wata doguwar tsaki mai matuƙar sauri tunawa da na yi zancen Abba na barin mu gidan izuwa yanzu kam ya sha ruwa. Ban yi aune ba na ji dirar wata baƙuwar murya a cikin dodon kunnena da ya tursasa mini tsayawa cak tamkar gunki. "Ke uban waye kike yi wa tsaki?". Na bi mutumin da kallo cike da tsoron da ya yi wa birnin zuciyarta dirar mikiya. Muryata a shaƙe na ce"ba da kai nake yi ba bawan Allah". Ya yi ƙwafa"Allah ya taimake ki". Daga haka ya ja zugan ƙafafunsa ya bar ni cike da tarin mamaki da al'ajabin da ya tsaya mini a rai. Lalle sai yau na ƙara gaskata cewa mafi yawan mutane yanzu a fusace suke ainun. Haka na wuce islamiyyar na samu har Malam Suleiman ya shiga ajinmu, da hanzari na ƙarisa na shiga na zauna na ciro alƙur'anina na soma karatu. Haka muka fito salla muka koma ajinmu har mun fara karatu Malam Suleiman ya aiko ya ce duk ƴan ajin sauƙa su je filin salla yana son ganin su. Duk muka ɗauki jakakkunanmu muka nufi filin kasancewar an kusa tashi ma a lokacin, ba mu daɗe da haɗuwa ba ya zo shi tare da Malam Aminu, Malam Suleiman ya fara yin jawabi mai kama hankali. "Mun tara ku ne a nan akan sauƙarku da kullum yake ƙara gabatowa, akwai abubuwan da makaranta ta shirya yi muku domin taya ɗalibanta murnar haddace littafi mai tsarki. Cikin abin da makaranta ta shirya har gayyato manyan malaman domin su zo su yi muku nasiha da nusar da ku hanyar da za ku yi amfani da ilmin da kuka samu ta hanyar da ta dace, hukumar makaranta ta zauna ta yanke hukuncin turawa Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe a matsayin babban malamin da zai halarci walimar sauƙan ku". Ras! Na ji gabana ya yanke ya yi wani mummunan faɗuwa. Babu shiri na ɗago kaina ina kafe Malam Suleiman da idanu tamkar magiji ko kuma yau ce rana ta farko da na fara yin tozali da shi a cikin rayuwata. "Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe". Na maimaita a cikin raina zuciyata cike da tarin fargaba. Babu shiri na dafe ƙirjina da dukka hannayena saboda tsananin bugun da yake yi, take na ji zuffa ya soma keto mini. Idanuna suna hasko mini zanen hotonsa tar ina gani tare da wassafa kalamansa da ya furzo mini a cikin kwanyata. Maganar da Malam Suleiman ya ɗaura da shi shi ya yi silar fizgo hankalina da ya yi nisa daga gangar jikina zuwa gare ni. "Babban mutum ne a ƙasan nan da ma nahiyar Afrika gabaɗayanta. Mutumin kirki ne ƙwarai da gaske kuma mutunci da dattakunsa sun kai matuƙa ba ya wasa da duk wani lamarin da ya shafa addininsa komai uzurin da yake cikin idan aka yi masa irin wannan gayyatar haƙiƙa yana amsar ta. Ta yadda ko mai sama damar halalta ba ya kan wakilta ɗansa ɗaya tilo namiji ya zo a madadinsa, sai da ku kun yi sa'a shi da kansa zai zo walimar yaye ku ba aike zai yi ba, don haka muna son ranar ku fitar da mu malamanku da kuma makaranta da kanta kunya". Take wajen ya rikice aka soma yin kabbara babu ƙauƙatawa, ni dai ina zaune inda nake rungume da jakata ko motsin kirki na gaza yi balle na bi ayarin masu yi kabbaran. "Za mu ware ɗalibai uku da za su yi karatun littafi mai Tsarki a ranar daga cikinku, wanda kuma suka kasance masu ƙwazo ne da basira haɗi da mayar da hankali akan karatunsu. A cikinsu kawai Al'amin Yakubu, Aliyu Shehu sai kuma Amatullah Munnir". Ras! Na ji gabana ya yi wani mummunan faɗuwa da hakan ya haifar mini da runtse idanuna, wajen ya ɗau shewa abokan karatunmu suna cike da farin ciki don a ganin su wanda aka zaɓa ɗin duk sun cancanta. Na buɗe idanuna a hankali ina kallon maza biyu da suka fito suka tsaya kusa da Malam Suleiman wanda ni ko sanin fuskokinsu ban yi ba, kasancewar ajin maza daban haka nan ma na mata, wajen alwala da salla ma nasu daban da na mu ba ma haɗuwa da su sai in an tashi yayin tafiya gida. "Amatullah ki tashi mana ki je ke ma". Na tsinkayo amon Ammi yayin da take zare jakata daga runguman da na yi mata, tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki haka na tashi duk jikina babu ƙwari na fita na tsaya wanda hakan ya ba wa Malam Aminu ɗaurawa daga inda ya dakata. "Waɗannan su ne ɗalibai uku da za su yi karatu yayin walimar yaye ku, kuma a cikin su muke saka ran samu na ɗaya, na biyu da kuma na uku". Kan ka ce kabo wajen ya ƙara kaurewa da kabbara ni dai ina tsaye ne kawai a wajen amma hankali da nutsuwata ba sa tare da gangar jikina. Kafin a watse Malam Suleiman ya ce gobe yana buƙatar ganin mu da wuri kafin a shiga aji, muka amsa da to. Kafin ta sallame kowa har muka fito daga cikin makarantar babu abin da ake tattaunawa sai batun zuwan Sheikh Dawood. Ko jiran Rauda da Ammi ban tsaya yi ba na yi tafiya don ji nake tamkar ba zan isa gida ba, ina so wa kuwa kai tsaye na wuce ɗakin su Amira na iske Ummata zaune a ƙofar ɗakin na tsuguna har ƙasa na gaishe ta kafin na shiga ciki. "Amira na shiga uku". Na furta a razana cikin rawar murya da take bayyanar da tsoron da ya yi wa ƙalbina naɗin huhun goro. Tsam ta tashi daga inda take zaune ta kamo hannuna muka shiga uwar ɗaka. "Sanar da ni me yake faruwa Amatullah? Rasuwa aka yi?". Na girgiza mata kaina alamar a'a. "To me ye faru?". Tiryan-tiryan na kwashe duk abin da ya wakana na sanar da ita daga farko har ƙarshe, ba tare da tsallake ko da jimla guda ba. Dogon tsaki ta saka kafin ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa mata. "Yanzu akan wannan abun ne kika bi duk kika ɗaga hankalinki?". "Dole hankalina ya tashi Amira ko kin manta yadda muka yi da shi, a tasha ne?". Ta musguta kafin ta furta"ban manta komai ba, amma yadda malamanku suka suffanta muku kirki da mutumcinsa a ido duniya shin hakan kaɗai bai isa ya wanke zargin da zuciyarki ta ɗisa miki akan sa ba?. Ya kamata fa izuwa yanzu ki manta da duk abin da ya faru, babban mutum ne a ƙasan nan kuma yana da girma a idanun mutane, ko zuwan da zai yi walimarku ma ai ya isa ya sa ki ji kin nutsu akan kasancewarsa mutumin kirki". "Amira babu wani zancen da zai sauya abin da na gani da idanuna kuma na ji da kunnuwana. Tabbas akwai wani ɗabi'a da mutumin nan yake aikatawa a ƙarƙashin ƙasa wanda ba ya son duniya ta sani, ko kuma in ce yana amfani da girmamawan da mutanen suke yi masa wajen lulluɓe wannan sirrin". "Wani mutum kuke magana akai? Kuma wani sirri yake ɓoyewa?". Zancen Umman Amira suka yi wa ƙofofin kunnuwanmu dirar mikiya. Duk muka cira kai muna dubanta tana tsaye a ƙofar ɗakin ta kafe mu da ido tana jiran amsan tambayoyinta. "Umma ba fa wani abu ba ne, wai wani malamin islamiyyansu ne fa ta gani tare da wata budurwa anan bayan layin nan suna tsaye. Shi ne fa duk ta bi ta tada hankalinta wai ta ji an ce yarinyar ba ta da halin ƙwarai". Ta ɗan yi jim kafin ta ce"Allah ya kyauta, ki tashi ka ga gawayin an kawo sai ki ɗaura girkin kafin ya iso". "To Umma yanzu zan fito". Ba ta ce komai ba

Chapter 12 of 24