na da ta ci gaba da yi tamkar yau ta soma tozali da ni.
"Ba ki da lafiya ne?".
"Kaina ne yake yi mini ciwo sosai". Na amsa mata da shi cikin dauriya da halin da nake ciki. Ta yi ɗan jim kafin ta furta"ki tashi ki je ki ɗeba kunnu ga shi can na dama, sai ki dawo ki kwanta. Na san yadda zan yi da kunun tun da na ri ga da na dama shi".
Na yi zumbur na ce"A'a Umma ai zan iya zuwa tallan ma". Kallon da ta katse ni da shi ya sani hanzarin haɗiye ragowar zancen ba tare da na gama amayo da shi waje ba.
"Ki fita daga idona na rufe Amatullah, in ba haka ba kuwa yanzun nan zan yi wasan kura dake a cikin gidan nan ƴar iskan yarinya mai halin dangin ubanta". Jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi tamkar naman da yake wuta ake sulala shi.
"Ki tashi ki je ki yi abin da na saka ki".
Ban ce komai ba na tashi na fita na je na wanke bakina kafin na ɗeba kunna na zauna a ƙofar ɗakin ina sha a hankali, da ƙyar yake wucewa ta maƙoshina tamkar wacce take haɗiyar ƙarangiya.
"Amatutun Mama". Na ji yo muryan Amira ta tsakiyar kaina yayin da take jan kujera ta zauna kusa da ni. Ta bi ni da kallo"ya kamar ba kya jin daɗi? Na ga duk yanayinki ya sauya".
Na lumshe idanuna da babu komai a cikin su face bacci da gajiya kafin na buɗe su tar akanta ina faɗin"wallahi kar ki so ki ji yadda kaina yake yi mini wani masifaffen ciwo. Ko juya kaina ban so na yi balle wani motsi mai ƙarfi".
Ta jinjina kanta cikin kulawa kafin ta furta"Ayya! Sannu Allah ya ba ki sauƙi".
"Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina kurɓan kunun da ko kaɗan ba na jin danɗanonsa a bisa harshena.
"Amma yau kam ba za ki sama zuwa tasha ba ko? Don na ga jikin nakin ba ƙwari". Na caraf na mata amsa har ina neman ƙwarewa tsabar sauri.
"Me zai hana ni zuwa kuwa Amira?. Yanzu ma tashi zan yi na je na shirya na fito mu tafi". Ta kafe da wani kallon da ya fi kama da na al'ajabi don ya zarce a misalta shi da kallon mamaki.
"Ke Amatullah kin san komai sai da lafiya ake yin sa. Mene ne don yau kawai kin zauna a gida kin huta? In kin sama lafiya ai za ki je".
Na katse mata hanzari"ni fa babu abin da zai hana ni zuwa, bari ki ga tabbaci". Ina dasa aya na tashi na ɗeba ruwa na shiga banɗaki na yi wanka na fito duk tana zaune a wajen na wuce ta na shige ɗaki na sako kaya, na fito falo inda na wuce Umma tana zaune.
"Umma na fito zan tafi".
"Zuwa ina kenan?".
Na saci kallonta kafin na ce"wajen talla".
"Har kin ji sauƙi kenan haka da wuri?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin na ce"ban ji sauƙi sosai ba amma duk da haka dai zan iya zuwa". Ta jinjina kanta ba ta amsa mini ba har sai da na cire rai da samun amsa daga gare ta kafin ta ce da ni"Allah ya kiyaye".
"Amin sai na dawo".
Na amsa da shi annuri yana wanzuwa a bisa fuskata tsam na tashi na fita na faɗa ɗakin su Amira na iske ta har ta shirya tana ɗaura ɗankwali. Daga ni har ita babu wanda ya yi wa wani magana na jira ta ta gama muka fito tare tunin almajiran da suke ɗauka mana kaya suka yi gaba muka bi su a baya.
"Daga jiya zuwa yau na gaza gane kanki Amatullah".
Na ware idanuna akanta"me ye kuma na yi?"
Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ke ma kanki kin san kin sauya ba kya buƙatar sai an sanar da ke hakan". Na matse yatsun hannuna waje guda na matse su har sai da suka ba da wani ɗan sauti kafin na sama zarafin cewa.
"Amira ba za ki gane ba wallahi ni ma kaina ban san me ye yake damuna ba. Haka kawai nake ji na a matuƙar takure a cikin gidan indai ba fita na yi ba na taɓa samun kwanciya hankali balle nutsuwar zuciya".
"Ina tsoron abin da hakan zai iya jawo miki. Don haka ina mai ba ki shawara tun wuri ki nema wa kanki mafitar da ta dace dake da kuma tsarin rayuwarki".
"Shikenan kuma ni ba ni da ƴancin jin daɗi ko kasancewa da waɗanda za su samar mini da farin ciki a cikin rayuwarta?".
"Amatullah kenan! Lokaci ne kaɗai zai ba ki amsar waɗannan tambayoyin nakin". Ban ce da ita komai daidai lokacin da muka karyo kwanar da za ta sada mu tashar har muka shiga muka zauna a wajen zamanmu ban daina jin ciwon kan ba, sai dai na gwammace da zauna a nan ɗin da na koma gida. Aƙalla mu shafa biye da mintuna arba'in amma ko wulgawar Bashir ban ga ni ba hakan ya sani furta abin da yake ƙunshe cikin raina ga Amira, da hakan ya ƙara jefa ta cikin mamaki.
"Amira kin lura kuwa yau ko wulgawar Bashir babu a cikin tashar nan?".
"To me ye abin mamaki a cikin hakan? Ke ma kanki kin sa direba ne to wataƙila an yi masa lodi ya tafi bai dawo ba". Na jinjina kaina tare da yi wa bakina sakata ba wai don na gamsu da abin da ta ce ba. Haka muka ci gaba da zama duk da azababben ciwon kan da yake ta'azzara na bai gani waige-waige ba ko zan yi tozali da Bashir. Lura da yanayin da na shiga ya sanya Amira soma furucin da ya yi silar jawo hankalina.
"Amatullah ba na buƙatar sai kin faɗa min da kalmomin baki yanayinki kawai ya nuna min cewar kin faɗa cikin soyayyar Bashir, sai dai kin yi zurfi da yawa. Tun yanzu har kin fara irin wannan abu to ina kuma idan soyayyar ta yi ƙarfi a cikin zuciyarki. Ina gudun abin da zai je ya dawo".
Ban san dalili sai kawai na ji na fashe da kuka mai matuƙar ƙarfi na kifa kaina da gwiwana ina rure shi da dukkan ƙarfin iyawana.
"Na shiga uku! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru me ye aka yi miki?".
"Amira ni ma kaina ban san me ye ya faru, kuma zan fi kowa son jin abin da ya faru ɗin. Wallahi ni ma kaina ina ji a jikina cewar na sauya sai dai babu yadda na iya. Zuciyata tana gaya mini cewar ba ni da wani zaɓin da ya wuce na amshi tayin soyayyar Bashir, ko don farin cikina tun da kin ga Umma ba samun lokacinsa take yi ba balle har ta ji damuwar da yake cikin raina".
Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da ta sauƙe kafin cikin sanyin murya ta soma cewa"na fahimce ki amma fa dole sai kin iya sarrafa kanki, kar ki bari zuciyarki ta dinga sarrafa maimakon ƙwaƙwalwarki. Ko da ya ke zan yi miki uzuri guda na cewar wannan ne karo na farko da kika fara soyayya". Ban iya cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da shi jikina har yana rawa tsabar kukan ya gama galaitar da ni ban gushe ba na ji ta furta kalmar da ya sani saurin ɗago kaina babu shiri.
"To ai ga can Bashir ɗin ma yana zuwa".
Na kafe shi da idanuna da suke tsiyayar da ƙwalla har ya iso wajen.
"Subhanallahi!Kuka kuma, me yake faruwa ranki ya daɗe?". Ya watsa mini tambayoyin a rikici yayin da yake ƙoƙarin zama akan bencin da yake kusa da ni.
"Yauwa! Na gode wa Allah da ya kawo ka a wannan lokacin. Tun ɗazu nake yi da ita amma ta ƙi jin lallashi balle lallami, ka ta ga ka kai m sai ka gwada taka sa'ar bari na je na dawo".
"Me ya same ta ne? Za ki tafi ba ki yi min bayani ba".
Ta yarfa hannunta alamar ita ma ba ta sani ba, ta ɗauki masar Nasiru ta tafi kai kai masa.
"Don ki yi haƙuri ki tsagaita da wannan kukan da kike yi billahillazi ba ki ji yadda nake ji wani abu yana tasowa daga ƙasan ƙirjina yana sukan raina ba. Ki taimaka ki sanar da ni abin da yake damunki".
Na kai hannu na share ƙwallar da suka ɓata mini fuska kafin na furta"ba komai". Ya jijjiga kansa alamar bai gamsu ba.
"Kar ki ɓoye duk abin da yake cikin ranki, ni kuma na tabbatar miki da cewa indai bai fi ƙarfina zan magance miki shi". Na kafe da idanuna ko ƙiftawa ba na yi"Bashir ka tabbata inna sanar da kai za ka iya magance mini ita?".
Cike da tabbatarwa ya ce da ni"ƙwarai kuwa matuƙar bai fi ƙarfina ba, indai kuɗi ko ƙarfi suna magani to tabbas zan tsaya miki".
Na cije leɓena kana na ce"kulawa nake so". Ya ranƙwafo da kansa saitin fuskana"kin tabbata shi kaɗai kike buƙata, bayan shi ba kya buƙatar komai Amatullah?".
"Ba na buƙatar komai bayan hakan".
Ya yi gyaran mury kafin ya soma cewa"to na yi miki alƙawari ba za ki taɓa yin kuka alhalin kina tare da ni ba. Kuma zan tabbatar da cewa ba ki yi dana sanin amsar soyayyata, ina so ki ba ni dama na nuna miki tsantsan son da nake gwada miki".
Ya ƙare zancen yana marairaice murya tare da lumshe idanunsa yana yi muni wani irin kallon da na ji dukkan jikina ya amsa, da hakan ya tursasa mini sadda kaina ƙasa.
Ya saki murmushi kafin ya ce"ki ɗauko kanki ko kuma na ɗago shi na goge miki hawayen da suka ɓata wannan kyakykyawar fuskar". Babu shiri na ɗago kaina ya miƙo mini wani ƙyale da ya zaro daga aljihunsa na amsa na goge fuskata.
Kamar ko yaushe na zuba masa kunun a roba na miƙa masa ya miƙo hannu zai ƙarba, kwatsam ya cafko da ƴatsun hannuna ya riƙe. Jikina ya yi wani irin yarfawa na same hannu babu shiri sai dai da mamakina ko gizau ban ga ya yi ba balle ya ji wani iri kamar yadda ni na ji.
Har ya gama shan kunun ya ƙarishe surutunsa na gaza sake jikina, muka yi sallama aka zai je ya dubo ko an gama masa lodi ya dawo. Wani numfashi mai nauyi na fesar daga bakina ina jin ƙirjina ya yi mini wani irin nauyi tamkar an yi min ajiyar dutsi. Kamar daga sama na ji an rumgume ni ta baya tare da faɗin"babbar yarinya, yarinya mai lokaci na yi kewar kasancewa tare da ke". Take jikina ya soma rawa tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki na yi ta maza na ƙwace jikina tare da miƙews tsaye duk da rawar da ƙafafuna suke yi da ya taimaka wajen ƙara dahuwar jikina ina jin zafin har cikin jiki da jijiyata.
"Malam lafiyarka kuwa me ye hakan?".
Na yi maganar har yanzu jikina bai bar rawa ba, shi ma da alama mamaki ne ya hana da motsa balle ya ce wani abun illa kallona da yake yi. Sai da ya dafe goshinsa kafin ya ce"ki yi haƙuri don Allah na yi zaton Amira ce, amma ki yi haƙuri".
"Ba komai".
Na amsa da shi a gajarce ina komawa na zauna, amsar da na ba shi ya ƙara gaskata mini abin da Amira take sanar da ni na ce na sauya. Tabbas da da ne sai na ko farcena ya riƙe bisa kuskure sai na yi masa wankin babban bargo tare da tara masa mutane su yi ca a kansa.
"Don Allah ke ƴar uwar Amiran ce?"
Na tsinkayo muryarsa a karo na biyu na yi masa kallo guda tare da kawar da kaina gefe.
"E".
"Ta yi nisa ne?"
"E za ka iya tafiya in sauri kake yi".
Bai ce da ni komai face murmushin da ya saka wanda na gaza gano manufar yin ta. Ya ja bencin ya zauna tare da fito da wayarsa yana latsawa, babu jimawa Amira ta dawo lokacin har na soma tattara mana kaya ina haɗa su a wajen guda.
"Mafarki nake yi ko kuma a farke nake? Sayyid kai ɗin ne ko kuwa gizo idanuna suke yi min?".
Amira ta yi zancen cikin zallar mamakin da har sai da ya bayyana a cikin kalymanta yayin da take isowa wajen. Ya tashi ya tsaya yana murmushi wanda na lura kamar hakan ɗabi'arsa ce.
"Ni ɗin ne dai babbar yarinya, yau da asuba na doro garin". Ta dafe ƙirjinta"na shiga uku! Kai da aka ce an fashi sun tare motaku sun tafi da ku".
"To yanzu dai ai idanunki sun gane miki gaskiya. Ya wannan cikar ƴar uwarki ce?". Ta kallo ni kafin ta ce"e ga shi kuma ka zo za mu tafi". Ya ɗage kafaɗunta"ba matsala gobe za mu haɗe. Dole mu magantu da ke".
"Sayyid manyan gari, to shikenan sai gobe za mu haɗu". Da haka suka yi sallama almajiran suka yi gaba da kayan yayin da mu ma muka fito. Har mun yi nisa kafin na yi magana.
"Amira me ye haɗin ki da wannan mutum?".
"Wa? Wai Sayyid? Abokina ne da harkan azurki ya haɗa mu da shi".
"Ki dai yi hankali da shi, har ta rumgume ni ya yi cikin rashin sani wai ya yi zaton ke ce. Hakan ya nuna kenan kuna yin irin hakan a tsakanin ku".
Ta ja tsaya"kar ki gaya min Amatullah. Amma lalle Sayyid ya ƙaro wulaƙanci". Daga haka ta fashe da dariyar da ya ƙular da ni har na kasa cewa da ita komai har muka isa gida, cinikin da na yi na damƙawa Umma na yo alwala na gabatar da salla na ci abinci kana na watso ruwa na soma shirin tafiya islamiyya. Ina ta so na tambayi Umma shin ko Abba ya dawo amma ban ga fuskar hakan ba.
Haka na fito duk masallatan unguwan sai da na rage ƙafa inda na iso wajen kon zan ga Abba amma babu shi babu alamarsa. Haka na isa islamiyyar raina duk babu daɗi ina zuwa Malam Aminu ya ce na aji huɗu na yi musu ƙari na je na yi musu na koma ajinmu, sai da muka dawo daga salla kana Malam Suleiman ya shigo ajinmu ya yi mana ƙari tun da muka soma ba mu dakata ba har sai da aka tashi, ya yi mana addu'a kowa ya watse.
Hatta Rauda da Ammi sai da suka fahimci ba na jin daɗi amma na musanta musu na fir na ƙi yarda, haka muka rabu da su kowa ya yi layinsu. Tun da doso ƙofar ɗakinmu nake jiyo tashin muryar Umma har na doso ƙofar ƙirjina bai daina sakan lugudai ba.
[10/15, 11:05 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 2️⃣9️⃣
Gabana ya ci gaba da bugu yana jin wani irin tsananin faɗuwar gaba, sai dai hakan bai hana ni ƙara tunkarar ɗakin ba. Ciki-ciki na yi sallamar da ya tsaya iya kan leɓena yayin da nake zura ƙafafuna cikin falon na tsaya cak yayin da na yi tozali da Abba, Yaya Alhassan da kuma Umar ƴaƴan Anty Sawwama ƴar uwa ɗaya tal ga Abba.
"Da ku har mahaifiyar takun da take ikirarin ɗan uwanta ne uban me ye kuke tsinana min?. Ko yaushe kuna sintikin zuwa gidan nan ba za a bar ni na huta a cikin gidana na sakata na wala ba, wacce iriyar bala'i wannan?". Zafafan kalaman Umma kenan da suka fara dira a kunnuwana da ya tilasta mini yin mutuwar tsaye ina kallon su ɗaya bayan ɗaya.
"Anty Hafsatu mu fa da ki gan mu ba tashin hankali ba ne ya kawo mu ehe. Ziyara muka zo wajen kawunmu kuma dai ba za ki taɓa raba hanta da jini ba. Ko kin ƙi ko ƙin so shi namu ne muma na sa ne". Umar ya yi zancen yana miƙewa tsaye fuskarta ta yi kici-kici, daman duk ƴaƴan Anty Sawwama babu mai zafin zuciyarsa da saurin fushi.
"Lalle Umar wuyanta ya isa yanka, ba shakka uwar taka ce kenan ta kitsa maka ka zo ka yi min wannan ɗiban albarkan. Manniru kana gani wannan yaron da aka haifa akan idona yana kallon tsabar idona yana gaya min abin da ransa ya ke so amma don mutuwar zuciya irin naka ka gaza taɓuka komai. Allah wadaran naka ya lalace".
Cikin sanyin murya Yaya Alhassan ya amshe zancen cikin faɗin"don Allah Anty Hafsatu ki yi haƙuri, ki hukunta Umar akan duk abin da ya yi miki amma na roƙe ki da kar ki jingina wautar da ya yi da mahaifiyarmu......". Kafin ya rufe bakinsa Umma ta katse shi.
"Dalla can rufe min baki kai da shi ɗin me ye bambamcinku? Duk ƙwaryar sama ce take dukan na ƙasa. Don Allah zan ba ku sallahu ku kai wa ita uwar takun ni wargi ce daidai nake da ƙugun ko wani ɗan iska".
"A'a Anty ki dinga sausauta kalamanki don ba za mu jure wani abun ba....". Umar ya yi furucin cin zallar ɓacin ran da ya bayyana har a bisa harshensa, yana rufe bakinsa Yaya Alhassan ya ɗauke sa da mari.
"Umar ka yi hauka ne ko kuma wani abun ka sha? Ko manta wacece a tsaye a gabanka da har take faɗa kake mayar mata ita ɗin tsararka ce? Ko me ye za ta yi ta ci daraja da kimar Kawu mana, maza yanzu ka ba ta haƙuri kafin na sassaɓa maka".
Dafe kuncinsa Umar ya yi yana wani irin huci ba a kufule ya ce"Anty ki yi haƙuri". Yana dasa aya anan ya fice daga falon fu kamar iska ina da tabbacin ɓacin ran da yake ciki ya makantar da idanunsa daga ganina tsaye a kusa da ƙofar. Sai a lokacin muka haɗa ido da Yaya Alhassan sai dai ya ɗauke idonsa ya yi tamkar bai ganni ba ya ci gaba da maganar daga inda ya ja burki.
"Kawu don Allah ka yi haƙuri ba nufin mu kenan mu zo mu tada maka da hankali ba, mun zo ne don mu sada zumunci mu kuma tattaunawa da ƴar uwarmu Amatullah akan batun sauƙanta da yake gabatowa. Amma ba mu sama ganawa da ita ba".
Ya juyo yana kallona kana ya zarce da faɗin"Amatullah don Allah duk wani abun da kike buƙata kar ki yi ƙasa a gwiwa ki garzayo ki sanar da ni, duk wani abun da ake yi wa ko wacce yarinya a irin wannan lokacin zan yi miki shi".
Taɓe baki Umma ta yi tana jan wani dogo tsaki mai dogon zango, Abba kam ƙasa ya yi da kansa ya kasa ɗagowa balle ya ce wani abun har Yaya Alhassan ya juya zai tafi.
"Sai ki ƙariso ai ƴar iska tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba".
Munanan kalaman da Umma ta yaɓa mini kenan da ya tursasa Yaya Alhassan tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya, ya runtse idanunsa cike naman leɓensa alamar ya ji zafi da ɗacin kalaman Umma matuƙa. Ina iya jiyo ajiyar zuciyar da ya saka daidai sa'ilin da yake buɗe idanunsa ya fita na yi wuf na bi bayansa ina ƙiran sunansa cikin kuka da tsananin damuwar da ya sanya ƙirjina yi mini wani irin nauyin gaske.
Bai amsa mini ba kamar haka nan bai waigo ba ya ci gaba da tafiyarsa har sai da muka zo zaure kana na yi nasarar shan gabansa. Na haɗe dukkan hannayena waje guda alamar roƙo ina wani irin kuka mai matuƙar ciwo da cin rai, duk yadda na so ce da shi wani abu na gaza samun wannan damar saboda galabaitar da ni da kukan ya yi jikina har rawa yake yi tamkar ana jona mini lantarki.
Babu shiri na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna ban gushe ba ina yin kukan don a halin da nake ciki shi kaɗai ne abun da nake yi na ji sanyi a raina, bayan ambaton Ubangijina.
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama zarafin faɗin"don Allah kar ka tafi".
Ya tsuguna akan ƙafafunsa a gabana kansa a ƙasa gabaɗaya shi ma jikinsa ya mutu murus. Zan yi magana ya ɗaka mini hannu.
"Ba sai kin ce komai ba Amatullah ba ki da laifi kuma ba ki yi mana komai ba. Anty uwa ce a gare mu baki ɗaya dama su iyaye wani lokacin sai ana haɗawa da haƙuri, ko kaɗan ban ji ciwon abin da Anty ta yi ba kuma ke ma ina so ki cire damuwar hakan daga cikin ranki, ki daina wannan kukan laifinmu ne don mun zo ba tare da mun sanar ba".
Na jijjiga kaina alamar ban gamsu da kalamansa ba"ina mai ba ku haƙuri a madadin Ummata. Don Allah ki yi mata uzuri...". Kafin na gama maganar ya ɗaura yatsansa a saman leɓena alamar na yi shuru.
"Normal ne fa don haka kar ma ki damu. Yanzu dai alfarman da za ki yi min shi ne ki goge fuskarki ki daina wannan kukan har tsakiyan kaina nake jin sa".
Ya ƙarƙare zancen yana zaro handkerchief ɗaga aljihun farin jamfan da yake jikinsa ya soma goge mini fuskana da shi, na koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse.
Tamkar daga sama muka ji an sheƙa mana ruwan sanyi duk muka yi mutuwar zaune na wucen gadin, sanyin ruwan na ji ya ratsa har jini da jijiyoyin jikina na daskare a wajen na kasa motsa gaɓoɓin jikina illa idanuna da nake sarrafa su daga wannan gefen zuwa wani.
Ummi da mahaifiyarta ce tsaye a kanta sun riƙe ƙugu suna jefanmu da wani irin kallo da na gaza gano manufarsa.
"Bayin Allah lafiya? Za ku yi mana wannan aika-aikan?".
Yaya Alhassan ya jefa musu tambayar yayin da yake miƙewa tsaye yana kakkaɓe jikinsa da ruwan ya yi masa lajab.
"Ahayye! Yau ina ganin iskanci da wasalinsa. Ai kamata ma ya yi idan ka dawo cikin hankalinka ka yi mana godiya".
Cikin rashin fahimta ya ce"godiya kuma? Na meye kenan?".
"Aw tambaya ma kake yi? To bari ka gani". Take Umman Ummi ta soma kurma shewa kan ka ce kwabo ta tara mana mutanen gidan manyansu da ƙanana suka cika akan mu suna rige-rigen kallon mu tamkar jinjirin watan Ramadana.
"Wai me ye yake faruwa ne?". Baba Habu ya tambaya, Ummi ta yi caraf ta ce"ga su nan kama su muka yi suna aikata baɗala sun fita daga cikin hayyacinsu. Har sai da muka watsa musu ruwa kana suka dawo cikin hayyacinsu". Take wajen ya ruɗe da salati da sallallami kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake yi ba tare da su ba mu damar cewa komai ba. Cikin tururuwan mutanen ban ga Ummana ba amma Abba kam tun da Ummi ta yi jawabin da ya hargitsa wajen bai ce komai ba, illa dafe kansa da ya yi cikin wani irin yanayin da kalmomin baki sun yi kaɗan wajen siffanta su.
"Me kuke jira? Ba za ku taru ku lakaɗa musu ɗan banzan duka ba".
Na jiyo maganar ta gefen inda nake yashe sai dai na kasa tantance mai muryar, kafin na yi yunƙurin tashi na jiyo muryar Abba a karon farko.
"Ku yi haƙuri su ɗin dukkan su ƴaƴana, a ba ni damar ganawa da su kafin yanke ko wani irin hukunci". Aka wani ƙananun maganganu kafin a hankali-hankali aka fara watsewa daga wajen.
"Kawu wallahi wallahi sharri suke yi mana, ba mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba. Amatullah ƴarka ce ka fi kowa sanin irin tarbiyan da ka yi mata ni ma kuma ka san halina, ka san abin da za mu yi iya aikatawa da akasin hakan. Kawu ka yarda da ni sharri ne kawai.....".
Abba ya ɗaga masa hannu alamar ba ya ƙaunar jin komai daga gare sa.
"Alhassan ka wuce ka tafi, ina roƙanka da ka ɗauke ƙafarka daga zuwa gidan nan har sai wannan ƙurar ta lafa".
"Kawu don Allah ka saurare ni na yi maka bayani...".
"Alhassan ka wuce ka tafi ka tafi na ce, zan zo gidan na same ka". A tsawace Abba ya yi zancen har sai da zauren ya amsa. Cikin sanyin jiki da na murya Yaya Alhassan ya ce"shikenan Kawu na gode mu kwana lafiya".
"Amin".
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 24