bari abubuwa su lafa tukunnan. Ta shawarce ni akan ko zan je to gwara na je wajen aikin Yaya Alhassan na same shi mu yi magana, na amince da hakan.
Kamar yadda na yi zato ban sama Umma a gida ba Amira ta kawo mana abinci muka ci kana na soma shirin tafiya islamiyya, don so nake yi kafin na wuce na tsaya a wajen aikin Yaya Alhassan duk da hanyar ba ɗaya ba ne.
[10/18, 1:53 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 3️⃣1️⃣
Ban ɗau lokaci ba na isa wajen aikin Yaya Alhassan na gyaran shinkafa, na tsaya a waje ina ta hange-hange kafin can na hango wani saurayi yana fitowa daga cikin wajen na yi hanzari na isa gare sa bakina ɗauke da sallama. Ya amsa yana kafe ni da idanuna.
"Don Allah wani taimako nake nema".
"Ina jinki".
"Ina so ayi mini magana da wani ne a ciki, sunansa Alhassan". Ya yi ƙuri yana kallona kafin can ya furta"a wani sashi yake aiki? Kin san akwai ɓangaren masu zuba ita shimkafan a buhu akwai masu ɗinke bugun sannan akwai masu lissafi". Na yi shuru ina cizon ɗan ƴatsa, kafin na kai ga furta wani abun ya katse mini hanzari.
"Mu je ciki sai na saka a duba miki shi. Amma me ye haɗin ki da shi Alhassan ɗin?".
"Yayana ne". Ya jinjina kansa yayin da ya yi gaba ina bin sa a baya muka bi ta wani ƙaramin ƙofa mun ɗan yi tafiya mai nisa kafin na tsaya saboda ganin wajen shuru babu gilmawar mutane.
"Malam wai ina za mu je ne?".
"Ina kike tunani?". Na yi zancen yana riƙo gefen hijabina na fizge ina nuna sa da ƴar manuniyar ƴatsata.
"Kar ka sake ka yi kuskuren taɓa jikina, don ina mai tabbatar maka da cewar hakan da za ka yi shi ne kuskure mafi girma da za ka yi a rayuwarka".
Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya yana ƙara matso ni. Na sa dukkan ƙarfina na hankaɗe sa ya faɗi sai dai kafin na yi wani yunƙuri tunin ya tashi ya finciko ni ya ɗaga hannu da nufin zabga mini mari. Na yi saurin runtse idanuna cike da tsoro ina jira na ji ta wani ɓangare zai sauƙe mini marin, jin shurun da na yi na sanya ni buɗe idona a hankali.
Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe bisa ganin Yaya Alhassan da na yi tsaye a wajen ya riƙe hannun mutumin da ya ɗaga da nufin zuba mini mari.
"Halilu ashe har yanzu ba ka sauya wannan halin nakan ba?. Ina maka nasiha da ka tun kafin lokaci ya ƙure mata ka sauya zuwa mutumin kirki wanda iyaye da al'umma za su yi alfahari da shi".
Yana gama faɗin hakan ya sakar masa hannunsa, cikin rawar jikin da borin kunya mutumin ya bar wajen tana ta muzurai tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya.
"Amatullah me ye ya kawo ki wajen nan?".
"Wajen ka na zo Yaya Alhassan".
Ya murtuƙe fuskarsa tamkar bai taɓa yin dariya ba"me ye kawo ki? Me ye da ba za ki iya zuwa gida ki same ni ba. Yanzu da ya yi galaba akan ki fa, ki wuce ki tafi islamiyyarki in kun tashi zan zo na same ki a can".
"Don Allah Yaya Alhassan ko minti biyu ne ka ba ni, ka saurari abin da na zo da shi".
"Ki wuce ki tafi". Cikin tsare gida ya yi zancen da hakan ya hana ni cewa komai haka na wuce na tafi har na isa islamiyyar ina ji na wani iri, ina shiga aji na kifa kaina akan benci ina kuka marar sauti ban gushe ina yi ba har sai da Malam Suleiman ya shigo ajinmu kana na ɗago kaina fuskana ya kumbura ya ya tsimtim yayin da idanuna suka yi ƙulu-ƙulu tamkar za su faɗo ƙasa.
Har aka fito salla jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki. Ko tambayoyin da Rauda da Ammi suke haɗe suna yi mini ban amsa musu ko guda ba ko da suka matsa mini cewa na yi da su ba ni da lafiya ba, dole suka rabu da ni bayan sun yi mini addu'ar samun sauƙi.
Tun kafin mu fito daga cikin aji na hango Al'amin da alama ni yake jira haka kawai na ji raina yana ɓaci ba tare da wani dalili ba.
Ko da aka shafa fatiha mun tattaunawa sosai akan walimar sauƙarmu da yanzu ya rage saura kwanaki ashirin cif, an tsara komai yadda zai gudana domin abubuwa su tafi yadda ake so a kuma fita kunyar baƙin da aka gayyata.
Muna fitowa daga ajin na yi wa su Rauda sallama na ɗauki hanyar har na yi nisa na ji ana ƙiran sunana. Ya tsaya ina dafe goshina don muryar Aliyu ce, ban motsa ba har iso gabana.
"Saurin me ye kike yi haka? Tun da kuka fito nake ƙiran sunanki amma ba ki waigo ba".
"Aliyu yau ba na jin daɗi ne so nake yi na tafi gida da wuri". Cike da kulawa ya furta"Ayya! Sannu ai ban sani ba da ban tsayar da ke ba. To amma don Allah ina neman alfarma ina son gobe idan kin shigo akwai maganan da za mu yi da ke".
"To ba matsala sai goben". Na furta ina barin wajen ba tare da na jira abin da zai ce ba. Ina shawo kwanan layinmu na hango Yaya Alhassan akan mashin ɗinsa yana zaune yana latsa wayar hannunsa.
Na ƙara sautin da nake yi na isa gare shi bakina ɗauke da sallama sai dai duk jikina ya bi ya yi sanyi ganin yanayin da ya amsa mini sallamar fuskarsa babu walwala balle annuri.
"Sai yanzu aka tashe ku?". Na yi ƙasa da kaina"mun tsaya mun tattaunawa akan walimarmu ne shi yasa na ɗau lokaci". Ya jinjina kansa yana kallo ya furta"gani kin ce za mu yi magana".
Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibayi na yi ƙasa da kaina"daman na je na ba ka haƙuri ne akan abin da ya faru". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. Ya cira kai yana kallo na tare da faɗin"ba ki yi min komai abin da ya faru kuma ai ƙaddara ce wacce ba ta wuce rana da sa'ilin ta. Don haka ki ma manta da abin da ya riga ya faru, damuwata ma shi ne kar hakan ya sa Abba ya yi fushi da mu".
"Abba bai yi fushi ba. Don ya fahimci mu sosai kuma ya yi imanin cewar ba za mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"amma gaskiya mutanen nan sun ba ni matuƙar tsoro. Na sha jin ana cewa ka guji sharrin mace ai ranar na ga zahirinta".
"Yaya Alhassan sharri ai dodo ne mai shi ya kan ci". Ya jinjina kansa cike da gamsuwa"haka ne kam. Yanzu dai ya batun sauƙan nakun me da me ake buƙata".
Na lissafa masa komai da komai da za mu yi. Bai ce komai har sai da na gama lissafin ya ɗago ido ya kalle ni"shikenan ko akwai sauran wasu abubuwan?".
Na waro idanuna"kai! Yaya Alhassan to waɗannan ɗin ma da na lissafo ba dole sai na yi su dukka ba. Hijabi daman Umma ta ce za ta yi mini ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa".
"Ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa". Ya kwaikwayi muryata da hakan ya sani murmusawa ina rufe fuskana.
"Duk abin da kika lissafa da ma wanda ba ki saka su cikin lissafin duk sai na yi miki su Amatullah. Gobe idan kin taso daga islamiyyar ki bi ta wajen Anty Zulaihatu zan ajiye miki a can sai ki karɓa".
Na turo baki ina furta"kar ka ɗaurawa kanka nauyi da yawa fa".
"Ke ɗin ce za ki zama min nauyi? To ashe in haka ne ni ma wataran zan gaji da ɗaukar nauyin kaina da kaina. Amatullah ke ƴar uwata ce kuma ba zan gaji da yi miki ɗawainiyya ba har abada, yanzu dai ki wuce gida magriba ta kusa". Godiya na gabatar masa sosai kana muka yi sallama ya wuce yayin da ni kuma na ƙariso gida, ina shigowa ana ƙiran sallan magriba don haka sai da na yi alwala kana na shiga ciki na yi salla, na sauya kaya na fito na haɗa wuta na ɗaura girki. Ina girkin ina biya karatun da aka yi mana haka Amira ta zo ta iske ni har sai na kai ayan da na ɗauko kana na kallo ta tare da cewa"yau ba za ki ke tallan taren ba ne?".
Ta dafe ƙirji"ni jikar mutum huɗu rufa min asiri. Ai wataƙila in dai ba wani ikon Allahn ba kuma na daina tuya awarar dare".
"Me yasa?".
"Mansur ya ce ba ya so iya na safen da nake zuwa na ya isa. Ya ce na yi masa lissafin abin da nake samu a toyar awarar a kullum zai na ba ni, kin ga kuwa ai kakata ta yanke saƙa".
Na tallafe kuncina ina kallon ta"to Allah ya saka masa. Amma ni kam da wannan kashe miki kuɗin da yake yi ɗin nan ai gwara ya fito ayi maganar aurenku. Tun da dai alhamdulillah yana da rufin aisirinsa daidai gwargwado".
"Yana so sai ya gama gininsa ne kana ya zo gida. Yau ma zai zo mu haɗe a gidan Tasallah za mu fi sakewa a can, kin san gidan nan da tsegumi da sa ido shi yasa duk nacin son zuwa hirar dare irin na Mansur na shata masa layi, ban isa ayi min sakiyar da babu ruwa ba, yadda ƴan matan gidan nan suka ƙware wajen ƙwacen saurayi ban isa ba. Don tabbas idan Mansur ya juya min baya ko ban bar duniya ba sai na zama marar amfani ta yadda ba zan iya amfanin kaina ba balle wani".
"To ya dai kamata iyaye su shiga cikin zancen gaskiya".
"Kar ki damu in Sha Allah ban da wani na mijin da ya wuce Mansur a duniya da lahira". Na bushe da dariya kafin na yi magana Abba ya shigo muka haɗe baki wajen amsa sallamar da ya shigo da ita, muka yi masa sannu da zuwa ya amsa ba tare da ko kalle inda muke ba.
"Wai har an yi isha'i?".
Amira ta tambaya, na gyaɗa kaina"ga shi kuwa tun da kika ga Abba ya shigo".
"Bari na yi je na yi salla kafin kin gama girki sai mu tafi".
"Wallahi Amirka yanzu kuma sai na ji gabaɗaya hankalina bai kwanta da zuwa gidan Tasallan nan ba, ina jin kamar ƙaddarar faruwar wani mummunan abu ne zai kai ni".
Ta dafo kafaɗata cikin son kwanta mini da hankali ta soma cewa". Amatullah ki haƙurƙantar da zuciyarki daga ni har ke ba mu da yadda muka yi iya shi yasa. Kina ganin dai irin rayuwar takurar da muke yi muka iyayenmu duk muna rayuwa ne a ɗaki guda, dole za ta sa mu zuwa ba wai don son ranmu ba". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na furta"haka ne Amira to Allah ya kawo mana mafita cikin sauri".
"Amin ya Allah".
Ta amsa da shi tana tashi ta koma ɗakinsu. Ina gama girkin na zubawa Abba na shi na kai masa ciki na ajiye masa a gabansa na fito na ci na wa a waje, na san Umma yanzu sai ta yi niyya take cin abinci don haka na juye ragowar a cikin kula. Na ɗauro alwala na shigo ciki har yanzu Abba yana nan inda na bar shi da alama ko buɗe abinci bai yi ba balle ya ci.
Na tsuguna a gabansa ina faɗin"Abba lafiya kuwa ka zauna ka yi shuru? Ko dai akwai wani abun ne?".
Ya saki sakakkiyar ajiyar zuciyar da har sai da na ji sautin ta kafin ya soma magana.
"Na daɗe ban shiga cikin matsanancin tashin hankali irin na yau ba, na daɗe ban ga Maman Umar cikin irin yanayin da na gan ta a yau ba. Tun muna yara mace ce mai fara'a da sakin fuska mace ce mai son nata akan komai da kuma son ɗabbaka zumunci. Amma yau a dalilina har hawaye sai ya taro a idanunta Amatullah".
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau" Abba wani abun ne ya faru tsakanin ku?".
Ya goge zuffa da ta taru masa a saman goshi kafin ya ce"na je na sanar da ita saƙon mahaifiyarki na cewa ba ta son ci gaba da ganin ta a cikin gidan nan. Haƙiƙa lamarin ya jijjiga ta amma sai dai ba ta bar ni na fahimta. Ba ta ce da ni komai ba illa fatan ɗaurewan lafiya da ta yi a gare mu, ta kuma ƙara da cewar idan har hakan zai samar mana da kwanciyar hankali babu matsala don tana maraba da duk abin da zai haifar da zaman lafiya a tsakaninmu".
Lokaci guda na daskare a wajen ina jin kamar ana ɗauɗare mini dukkan gaɓoɓina. Ban yi zaton Abba zai iya zuwa ya sanar da Anty Sawwama wannan lamarin kai tsaye haka ba. Ban yi aune ba na ji hawaye sun ciko mini koramar idanuna.
A raunane na ce"Allah ya daidaita tsakanin ku".
Ya amsa da amin yana ɗaurawa da"yau za ka fara tafiya gidan kwanan ko?". Na gyaɗa kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar.
"Nasiha ɗaya zan yi miki shi ne ki ji tsoron Allah Amatullah. Ki sani cewa duk in da kike da duk abin da kike aikatawa Allah yana kallonki ko da kuwa mu kin ɓoye mana, ki kiyaye mutumci da kimarki a duk kika tsinci kanki sannan tarbiyyarki ta bayyana a cikin aikinki, Allah ya kiyaye ki ya kuma tsare ki da tsarewar sa a duk inda kika kasance".
"Amin ya Allah. Abba in Sha Allah ba zan ba ka kunya ba".
"Allah ya miki albarka". Na amsa da amin ina tashi na shiga cikin ɗakin na tarar da Umma tana bacci na yi sakeke ina kallonta don ina da tabbacin ko sallan magrib ba ta yi ba balle isha'i. Kayana na ɗauka na fito na shiga wanka na dawo na tarar a lokacin ta tashi muka yi sallama da ita na fito. Na tarar da Amira ma ni take jira tun da muka fito take waya da Mansur tana yi masa kwantacen gidan Tasallan har muka isa. Kamar yadda na yi zato haka muka iske ƙofar gidan cike da masu jaura muka kutsa kai zuwa cikin gidan, inda muka iske Tasalla zaune a bisa tabarma ta ba za hajarta a gaban ta, muka isa muka zauna a kusa da ita bayan mun gaishe ta Amira ta yi mata bayanin komai.
Ta riƙe haɓa"tirƙashi! Ga shi kuma yanzu babu ɗaki duk da mutane a cikin sa, daman na yi tunanin zuwan nakun zai kai gobe ne hala ko jibi don zuwa lokacin akwai wacce za ta tashi".
"To Hajiya yanzu ya ya za a yi ke nan? Ko za mu je kawai sai goben to?".
"A'a bari na ƙira Ƴar gold na ji ko kwana za ta yi a can inda ta je ɗin, in kwana za ta yi sai ku yi amfani da ɗakin kafin na gyara muku waje zama"
Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta shiga latsawa, ba ma ji abin da ake faɗa daga ɗayan ɓangaren mun dai ji sai amsawa take yi da to to har ta zare wayar daga kunnenta.
"Za ku iya amfani da ɗakinta don ita ta yi nisan zango, dawowanta sai wani sati ta tafi can ƙauyen su saboda batun auren da ya taso. Sai ki tashi mu je ka ga can ɗakin sai na kai ku". Haka kuwa aka yi ta tashi ta kai mu har ɗakin kuma ta sa aka sayo mana maganin sauro ta kunna mana, muna zaune wayar Amira ta yi ruri ta kalle ni"tashi mu je Mansur ne ya iso".
"Sai dai ki je ki don babu inda zan iya zuwa yanzu".
Ba takura mini ba ta tashi ta fita bayan ta buɗe wayarta ta bar mini ita da nufin ta ɗebe mini kewa. Mahanjar shafukan alƙur'ani na shiga na soma karantun. Sai ƙarfe sha ɗaya Amira ta shigo na galla mata harara ina faɗin"na yi tunanin ai a can za ki kwana".
"Har kin fusata kenan? Yanzu dai bari na yi je na yi fitsari na zo na ba ki labari". Ban kula ta ba illa lasje wutar ɗakin da na yi na ja bargo na yi kwanciyata a bisa katifar. Tamkar daga sama na ji an yaye bargo na yi zumbur na tashi ina lalumar inda na ajiye wayar Amira don na kunna haske na ga an dalle mini idanuna da haske tocila.
"Watau aure za ki yi ki bar ni ko? Kin sama wanda ya fi ni shi ne za ki juya min baya. To billahillazi ba ki isa duk gyaran da kika yi sai na buɗe ki sai dai a kai ki gidan nasan a haka".
Take jikina ya soma rawa na fara kuka ina masa magiya, cak numfashina ya tsaya bayan da na jin ƙarar rufe ƙofa da hakan ya yi daidai da lokacin da aka kashe tocilar.
"Wallahi ba ita ba ce don girman Allah ka yi mini rai kar ka cutar da ni....". Ban ƙarisa maganar ba na yi an sa wani abu mai kauri an ƙulle mini bakina da hakan ya hana sautina fita, na sanƙare lokacin da na ji yana ƙoƙarin raba ni da kayan jikina, na so kai masa duka, yakushi da cizo ya falla mini marin da sai da na ji bakina ya cika da ruwa wanda nake kyautata zaton jini ne, ya hankaɗe ni gefe guda kaina ya bugu da ginin ɗakina. Da wani irin ƙarfi na ji ya yage rigar jikina na yi saurin kai hannu na rufe ƙirjina, ina ƙoƙarin tashi ya jawo ni, tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba saboda zafin buguwan da na ji da ya ratsa har tsakiyar ƙoƙon kaina.
[10/19, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 3️⃣2️⃣
Tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba, numfashina ya ɗauke na wucen gadi na gaza motsa ko da ƴatsan hannuna balle sarrafa sauran gaɓoɓin jikina.
A hankali na soma buɗe idona da suka yi mini nauyi wasu hawaye masu zafi da ɗumi suna gangarowa ta gefe da gefen idanuna suna wanke mini fuska da nake jin sauƙar su bisa fatana tamkar tafashashshen ɗanyen ruwan dalma, na yi yunƙurin motsa jiki amma na kasa saboda wani zafin da na ji ya ratsa dukkan ilahirin jikina tun daga ɗan ƴatsan ƙafata har zuwa tsakiyar kaina.
Jin wani abu na bin tsakanin cinyoyi yana gudu zuwa ƙafafuna ya tilasta mini runtse kumburarrun idanuna ina sakin wani irin kuka marar sauri haɗe da cin rai. Na ji an buɗe ƙofar ɗakin an fita babu jimawa na ga an kunna wutar ɗakin haske ya gauraye ko'ina.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Na shiga uku ni Amira me zan gani haka? Me ye ya faru Amatullah?". Na tsinkayo muryar Amira cike da damuwa tana nufo inda nake yashe tamkar gawa ban da idanuna babu abin da nake iya sarrafa a cikin jikina.
"Amira ki taimaka ni ki ɗaga ni na zauna".
Ta kamo kafaɗana da nufin ɗago ni na calla wani uban ƙaran da babu shiri ta maida ni na koma na kwanta. Duk inda ta latsa a jikina ciwo nake ji yana yi mini.
"Amatullah wai me ya faru ne? Waye ya yi miki wannan ɗanyen aikin?".
Na gaza magana illa kukan da ya ɓalle mini na ke yin sa tamkar da bakin ƙwarya. Ji nake yi gabaɗaya duniyar tana juya mini ina ganin rufin ɗakin tamkar zai rikito a bisa kaina, na yi nadama ainun na kuma ƙara yin da na sanin kasancewa ta a raye har zuwa wannan lokacin da wannan ƙaddarar ta afka mini a bisa turban tsautsayi.
"Amira jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, jini zuba yake yi daga jikina. Amira mutu zan yi mutu zan yi". Na furta zancen cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa cikin kalmomin da baki kan iya furtawa, ji nake ji tamkar ba zan iya ƙara ko da sakon ɗaya a raye ba saboda tsananin azaba da masifar azababben ciwon da nake ji a cikin jikina.
"Ba za ki mutu ba Amatullah, bari na je na sanar da Hajiya abin da ya faru". Amira ta yi zancen tana lulluɓa mini mayafi a jikina da ya taimaka wajen ɓoye tsiraicina da ya bayyana. Ta tashi ta fice daga cikin ɗakin cikin hanzari babu jimawa suka dawo tare da Hajiya Tasalla da ta na shigowa ta soma zagba salati da sallallami ganin mungun halin da nake cikinsa.
"Amatullah tashi ki yi min bayanin abin da ya faru? Waye ya yi miki haka? Waye ya shigo cikin ɗakin nan ba tare da sanina ba? Alhalin tun ɗazu ina zaune a filin tsakar gidan nan ban ga shigowar kowa ba balle fitar wani".
"Hajiya ku kai ni asibiti wallahi mutuwa zan yi". Na yi zancen cikin tsananin zafin ciwo da takaicin halin da na tsinci kaina, da kuma sauyawar da rayuwata za ta yi daga wannan lokacin.
Ta dafe ƙirji tare da waro idanunta waje"asibiti kuma Amatullah ai hakan daidai yake da tonuwar asirinki, na iyayenki da kuma ni da kaina. Bari na je na tafasa muka ganyan magarya da lalle ki ci shiga ciki za ki ji daɗin jikinki". Ba ta jira abin da za mu ce ba ta tashi a hanzarce ta fice tamkar za ta kife akan hancinta.
"Na shiga uku ni Amira yanzu da wani idon zan fuskanci Abbanki da wannan zancen, bayan ya damƙa amanarki a hannuna. Ya yarda da ni tare da yaƙinin matuƙar kina tare da ni ba zan taɓa bari wani abun ya cutar da ke ba". Furucin Amira kenan da ya ƙara saka ni kuka daga ni har ita kukan muke yi da dukkan ƙarfinmu, tamkar wanda aka aiko da saƙon mutuwar iyayensu uwa da uba tare da dukkan ahalinsu.
Har Hajiya Tasalla ta dawo ba mu daina kukan ba, ta je ta rufe gidan ruf a cewarta kar wani ko wata ya shigo ya tarar da abin da ya faru asiri ya tonu, ta kuma sallami duk masu kwanan ranan suka tafi. Tare da Amira suka cicciɓe ni zuwa waje na shiga cikin ruwan ɗumin wani azababben zafi na ji ya ratsa ƙoƙon kaina na yi zumbur zan tashi Hajiya Tasalla ta maida ni.
"Ki yi haƙuri ki koma ki zauna a cikin ruwan nan, domin shi ne samun lafiyarki a yanzu".
Haka ina kuka ina cije leɓe na koma na zauna na aƙalla mintuna talatin kafin na fito ta kai mini ruwan ɗumi banɗaki na yi wanka na fito ina ɗingisa ƙasa. Wani kayan ta ba ni na saka na kifa kaina da gwiwa ina ci gaba da kukan tausayin kaina da iyayena da nake yi. Amira ma ta zo ta jona ni muna yi tare.
Cikin durshashewar murya da sarƙafewar harshe na ce"Amira gida zan tafi ba zan iya kwana a nan ba, ki taimaka ki mayar da ni gidan. Ko mutuwar ce ma na fi so ta ɗauke ni a can".
"Amatullah ki yi haƙuri yanzu idan muka koma gida ai asirinmu ya gama tonuwa a idon duniya. Dole mu tsara yadda lamarin zai tafi". Ban tanka ba na miƙe tsaye ina cije leɓe na yunƙura zan fice daga cikin ɗakin ta sha gabana tana yi mini magiya.
"Don girman Allah Amatullah ki yi haƙuri ki rufa mana asiri kar ka fita cikin wannan daren". Runtse idanuna na yi ina jin wasu hawayen da na gaza samun ikon akan su suna kwaranya daga koramar idanuna.
"Ya na ganku duk kuna tsaye cirko-cirko?". Na tsinkayo amon Hajiya Tasalla na buɗe idona ina kallon ta da wutsiyar idanuna, ji nake yi tamkar na yi tsalle na je na shaƙe mata wuya.
Ta dire wannan abinci da kofin da ta shigo da shi kana ta zo ta riƙo hannuna za ta taɓo jikina na zame. Ina ci gaba da kukan da nake yi.
"Ki yi haƙuri mana ke kuwa abin da ya faru ai ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 24