Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [6/9, 6:34 PM] iyammaimuna: Bismillah rahmanir rahim. Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da tagomashin aron rai da numfashi da ya ba ni na rubuta wannan littafin mai suna DAFIN HARSHE bayan kammala littafin KE CE MADADI, wanda har yanzu ana dillancinsa a kasuwar online. Ina rokon Allah da ya tsare mini hannayena daga rubuta abin da zai zama ɓarna ko cutarwa ga al'ummar musulmai tare da tarbiyyansu da kuma al'ada. Ga mai buƙatar litattafaina *MATAN AREWA *SALON ƘADDARATA *UWATA CE SANADI *ƁOYAYYAR MANUFA *KE CE MADADI Zai iya samun su kai tsaye a wajena ko kuma ya tuntunɓi wannan layin 07038908713, ba kya bi na ba shi rantsuwa duk wanda ya karanta tabbas ba zai yi dana sanin sayan guda daga cikin su ba. Page 0️⃣1️⃣ Kamar ko wacce safiya yau ma ba ta sauya zanin ba, kururuwa da ihun ƙiran da Ummata take doka mini shi ya farkar da ni daga baccin da ya sace ni, bayan iddar da sallan asubahi. A firgice na tashi Ina rarumar kallabina na saka na bayyano waje. Inda da yawa daga cikin mutanen gidan sun tashi sun fara aikace-aikacen gabansu a ƙofar ɗakunansu. Kasancewar gidan haya ne da ba mu da wadataccen fili sai yawan ɗakun da take ɗauke da su guda goma reras, hakan ya sa mutanen unguwar suke yi masa laƙani da gidan yawa wasu kuma su ce gida goma. "Za ki iso ki ɗauka tallan kunun nan ko kuma sai na zo na saɓa miki? Oh! Hafsatu ina ganin takaicin rayuwa. Ya tabbata in ban kai zuciya nisa ba baƙin cikinki ke da ubanki sai ya kai ni ƙasa". Zantukan Umma kenan da suka yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga kogin tunanin da na dulmiya, na yi ƙasa da kaina ina sauraron zancen da ta ɗaura da shi. Wanda tun suna yi mini ciwo har sun zame mini jiki duk nusar da ita da Abba yake kamar yana zuba ruwa ne a bayan ƙwarya. "Umma yanzu fa garin ya waye. Kuma ba sayan kunun nan suke yi ba da safe". Ta yi hanzari katse ni tana nuni da ƴar manuniyar ƴatsarta. "Kunun ne aka daina shan sa ko kuma mene ne? Ai kuwa da safe ake cinikin kunu tun da ga masu fita aiki nan suna shiri". Ta ƙare zancen tana yi mini nuni da ido zuwa ga Baban Adnan da yake saka takalmarsa sau ciki cikin shigar jami'an ƴan sanda. Matarsa da take tsaye kusa da shi ta bankowa Umma harara babu wata-wata ita ma ta rama kafin ta juyo kaina a zafafe. "Za ki zo ki ɗauka ko sai ya huce? Ƴar iska mai baƙin hali irin na Ubanta". Tana kai wa aya Abba yana sako kan sa cikin gidan muka yi ido huɗu da shi kafin ya sadda kaina ƙasa. "Mu je ciki mu yi magana Hafsa". Abba ya furta cikin sanyin amon, don mutum ne marar son hayaniya, uwa uba yana son sirri duk dambarwar da za a yi zai yi wuya ya tattauna da Umma akan abin da ya shafe mu a filin gidan. "Daga zuwanka ba za ka kafa min ƙahon zuƙa ba. In naje cikin uwar me ye zan yi maka? Kai ba yaro na goye ba balle ka ce ina mun shiga shayar da kai zan yi". Da hanzari na ɗauko kaina na kafe Umma da idanuna da suka kawo ruwan ƙwalla. Shewar da Maman Adnan ta saka game da tafa hannu ya yi daidai lokacin da hawayen da suka wadaci kurmin idanuna kwaranya a bisa dandamalin fuskana. Takaici ya zo mini a wuya wanda ina da tabbacin shi ne ya tunzura zuciyar Abba har ya soma cewa. "Wani irin magana ne wannan haka Hafsa? Ko za ki furta min wannan furucin zai ki yi a nan". "Mtschew! Ka ji da shi yanzu kam kanka ake ji, wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wanka na nake yi. Ki zo ki ɗauka kunun nan shegiya mai zubin munafukai". "Babu inda za je shin sau nawa zan ce da ke ba na son wannan tallan da kike ɗaura wa Amatullah?". Ba ta amsa masa da baki ba illa tsakin da ta buga tana wurga masa harara tare da yatsina fuska tamkar ta yi tozali da ɗanyen kashi sakin yanzu. Na jayo ƙafafuna da ƙyar na zo na ɗauki gammo na naɗa na ɗaura a kaina ina kici-kicin ɗaura bokatin kunun a kaina. Baban Adnan ya zo wuce wa har ƙasa Umma ta durƙasa tana gaishe shi tare da yi masa addu'ar a dawo lafiya, kalamanta na ƙarshe su suka fi komai shayar da ni ruwan mamaki. "Allah ya yi wa Adnan albarka, ya raya shi bisa turban addini. Al'umma su yi alfahari da shi". Daɗin addu'ar ya sanya Baban Adnan washe baki yana amsa da amin wani na bin wata. Sai da Maman Adnan ta fizgi hannun rigarsa ta ja shi waje kana ya rufe bakinsa. Babu kunya Umma ta miƙe ta kakkaɓe jikinta ta yi ciki Abba ya ce na dakata daga fita tallan ya rufa mata baya ina daga tsaye ina jiyo abin da suke tattaunawa. "Hafsatu ki ba ni hankalinki mu yi magana na fahimta ba na jin daɗin abin da kike yi min a cikin gidan nan, musamman wannan tallan da kike ɗaura wa Amatullah. Ba mu rasa abin sawa a bakin salati to mene ne na tada hankali?". Ta ya wata doguwar tsaki kafin ta zarce da cewa"Cimar gidanka da kullum babu canji, buhun masara ce in ka jingine ta sai kuma ta ƙare a kawo wata ina shi ne alfaharinka?. Da an yi magana ka ce ba mu rasa ci ba ba mu rasa sha ba. Dole na nema kuɗi kuma wajibi ne na ɗaura wa Amatullah talla". "Yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan? Kin kasa sawa ƴarki ta cikinki albarka balle ki yi mata fatan gama wa da duniya lafiya amma ki na yi wa ɗan wasu. Kullum cikin jifan ta kike yi da munanan furuci, Hafsatu ke uwa ce bakinki yana da tasiri akan Amatullah shi yasa nake tsoron ranar da DAFIN HARSHEnki zai kama ta". Cikin ɗaga sauti na ji ta mayar masa da martani kamar za ts rufe sa da duka. "Dole kuma aka ce idan zan sa mata albarka sai na yi a fili kowa ya gani? Ka san adadin abubuwan da nake roƙa mata a cikin sujjadana?". Daga nan ban ƙara jin muryar Abba ba sai ganin Umma na yi ta fito daga ɗakin kamar an jefo ta na zabura na matsa gefe. "Don ɗiban albarka har yanzu kina tsaye ba ki tafi ba? Allah na gode maka ni kam. Kowa yana haihuwa don ya huta amma ni kam ko kusa ko alama, tsinanniya mai baƙin hali". Ta ƙare zancen tana suran murfin tukunya da nufin wurga mini, babu shiri na fice ƙafafuna suna harɗewa cikin ɗaurin zanina. A ƙofar gidan na iske raguwar mazajen gidan zaune akan taburma suna zaman sa ido, kaina a ƙasa na wuce ta gabansu sai dai hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsu yana kaina ba har na fice daga layin. Na nema wani waje na zauna tare da zabga tagumi na faɗa cikin duniyar tunani na yi nutso sosai da har ya hana ni jin sallamar da matashin saurayin da yake bisa kekensa yake yi, sai da ya tafa hannayensa kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. "Na nawa kake so?". Na jefa masa tambayar ina ciki-cikin ɗauro robar da zan zuba masa. Amsar da ya ba ni ya dakatar da ni daga abin da nake yi, na cira kai ina bin sa da wani irin kallo. "Mai kunun nake so". Kallon da na tsare shi da shi ya sanya sa ɗage mini ido guda yana ci gaba da cewa. "Ayi min farashi ko nawa ne zan biya. Don kyawunki ya kai a kashe ko nawa ne". "Dalla! Malam ba na son maganar banza, idan za ka saye ka faɗin na nawa kake buƙata. In kuma ba saya zaka yi ba ka ba wa masu saya waje". Kallon da yake bina da shi yana lashe baki kamar tsohun maye ya ƙara ƙular da ni na doka tsaki ina ci gaba da zancen. "Malam ka matsa mini daga ka, kana wani lashe baki kamar maye". "Ke kar ki yi min rashin kunya don kawai na yaba ki". Na taɓe baki kafin na ce"idan sarki bai ji kunyar hawa jaki ba ai kuwa jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba". Ya sauƙo daga kan keke ya nufo ni gadan-gadan yana zazzare idanu, nima na miƙe tsam na kamfato kunun na watsa masa a fuska. Kafin ya yi wani yunƙuri na tattari kayana na saɓa hanya. Sai da na yi nisa na fice daga layi gabaɗaya kana na waiwaya na sauƙe ajiyar zuciya. Ganin ba ya bibiyata gida cikin faɗuwar gaba izuwa yanzu mazan da suke zama a ƙofar gidan duk sun watse kowa ya tafi harkokinsa. Kamar ƙadangaruwar bayan murhu kana na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka. Na yi kiciɓus da Ummi a zaure tana zance da wani mayatatcen saurayinta da inda ya zo tun safe har yammaci bai kula ta na sa kai na yi wucewa ta. Na dire bokitin a ƙofar ɗakinmu yayin da duk ragowar matan da suke waje suka kafe ni da na mujiya. Na tsinkayo amon Umma daga bayana na waiga tana riƙe da buta ta fito daga banɗaki ta washe baki kamar gonar auduga. "Ba shakka! Tsuntsu daga sama gashashshe. Amatullah har kin sayar da kunun kenan?". Ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta ajiye butar da ke hannunta ta nufo inda na ajiye bokiti, turus ta tsaya ganin kunun shaƙe taf a cikin bokitin. "Me nake gani haka?Wani irin ɗanyen aiki haka kika jiƙa min Amatullah? Don tsabar mugunta da baƙin hali yanda na ɗaura miki haka kika dawo min da shi, shegiya ƴar iska wacce ba ta gaji abin azurki ba". Tana rufe bakinta ta jayo ni ta rufe ni da duka kamar ba za ta bar ni da rai ba, matan gidan duk suna tsatstsaye suna kallo amma cikin su aka rasa samun wacce za ta kawo mini ɗauki. Tun ina ihu da kururuwar neman taimako har na gaza samun ƙarfin yin hakan, Anty Maryam ce kaɗai ta kawo mini agaji da ƙyar ta ƙwace ni daga riƙon da Umma ta yi mini tana tambayar ba'asi, Umma ta daka mata tsawa. "Ki kauce ki ba ni waje kafin ke ma na haɗa da ke. Ki ba ni waje na lillisa wannan ƴar iskan yarinya mai baƙar zuciya. Kowa yana abin kansa amma ban da ni, kunun dubu biyu kacal ki kasa sayarwa ban da lalaci da mutuwar zuciya". Umma ta yi bayanin tana ƙoƙarin kai mini mari na kauce, Anty Maryam ta mai da ni bayanta. "Haba ke kuwa Maman Amatu ki yi haƙuri mana ki fara sauraran dalilin da ya sa ta dawo kafin ki yanke hukunci. Sannan kin ga wannan furucin da kike yi mata sam bai dace ba a matsayin na uwa. Yau idan ta zama ƴar iskan sai kin fi kowa shiga damuwa". Kafin ta kai aya Umma ta dakatar da ita"kin ga Malama ba zamanki nake yi balle ki zaunar da ni kina faɗa min abin da zan yi ko wanda zan bari. Kuɗin haya mijinki yake biya ni ma haka mijina yake biya don haka babu abin da za ki nuna min. Ki ji da abin da yake gaban ki, ban da lalacewar zamani da samun wuri wai har wacce ba ta taɓa haihuwa ba ce za ta faɗin yadda za a yi tarbiyan ƴaƴa". Cikin tushewar numfashi Anty Maryam ta ce"Allah ya ba ki haƙuri, ga Amatullah idan kin ga dama ki ɗauko wuƙa ki daddatsa namanta ki zuba a tukunya, ki sulala". Tana gama maganar ta bar wajen ya koma ɗakinta. Umma ta hau bambami kamar za ta yi aron baki. [6/11, 11:58 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 0️⃣2️⃣ Ina tsaye a wajen hawaye suna wanke mini fuskata tsabar laushin da jikina ya yi mini na gaza motsa ko da ƴatsun hannuna. Sallamar Baban Adnan shi ya dakatar da Umma daga feshin masifar da ta yunƙura za ta furzo mini. Cikin rawar jiki ta zube har ƙasa tana yi masa sannu da zuwa. Fuskarsa a washe yake amsawa kafin ya tambayi dalilin ganin mu cirko-cirko da ya yi Umma ta kwashe komai ta labarta masa. "Na wane kuɗin kunun gabaɗaya? Sai na ba ki kuɗin gudun kar ayi asararsa". "A'a Baban Adnan ayi haka? Ai kawai ka bar ni da ita tun da ita ƴar duniya ce zan nuna mata na dame ta na shanye". Ya yi saurin taran numfashinta"A'a ai ba za a yi haka ba". Yana dasa aya ya zaro wasu kuɗi daga aljihun uniform ɗinsa ba tare da ya irga ba ya miƙa wa Umma yana faɗin"ga wannan na san zai isa". Bakinta har kunne ta miƙa hannu za ta karɓa sai dai kafin ta kai ga yin hakan aka fizge kuɗin. Duk muka ɗaga kai muna duban Maman Adnan da ta faɗo cikin gidan kamar an cillo ta ko kallabi babu a kanta balle hijabi, rabin kanta a kitse rabi a tsefe. Asabe da take bayanta tana zarrare idanu ya tabbatar mini da hashashen zuciya na cewar ita ta bi Maman Adnan har gidan kitso ta shaida mata abin da yake faruwa kasancewar gidan kitso muna kusa da shi. "Me nake gani haka Ibrahim? Yaushe ka dawo gidan? Sannan wannan kuɗin mene ne kake ba wa wannan matar?". Sai da ya ƙare mata kallon tsaf kafin ya ba ta amsar da ta ƙara tunzura ta ta cika ta yi fam tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis rana ta buge shi ya tashi ya yi fum. "Kunun da ta yi ne na saye gudun kar a yi asararsa". "Me ye haɗinka da ita ta balle kunun da take sayar wa? Ko kuma kai kaɗai ne ka san zafin asara da kake gudun ta yi sa? Idan sau gudu ɗari za ta dama kunun ya yi kwante sai me ye Ibrahim". Ya tsoka mata tsawar da ta tilasta mata yin shuru ba tare da ta gama furzar da takaicin da ya ƙunsa mata ba. "Ke Safina! Me ye haka za ki tara min mutane kamar wanda ya yi sata. Ko wani aikin ashsha kika ga muna aikatawa da ita iya tijarar da za ki yi min kenan". "Ai da wannan munafurcin gwara ma ku aikata komai". Bai yi wata-wata ba ya ɗauke ta da marin da ya ba da sauti mai ƙarfi ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa. Sai dai bakinsa ya gaza cewa komai illa rawar da jikinsa yake yi. Ya fizgo hannunta ya ja ƙofar ɗakinsu sai da ya sa makulli ya buɗe kana ya wurga ta ciki ya rufa mata baya ya turo ƙofar. Ihu da kururuwarta ya cika wa kowa kunne jibgarta yake yi da dukan ƙarfinsa kamar ya sama baiwa ko kuma jaka, Adnan ya zo ƙofar ɗakin yana bubbugawa yana kuka. Kamar gidan babu kowa babu wanda ya yi yunƙurin taimakawa Maman Adnan kowacce mata ta gama harkan gabanta, ga wanda ihun ya dame su kuwa suka ja hijabi suka fice wasu suka shige ɗakunan su. Tausayin Adnan ya kama zuciyata na ja ƙafafuna da ƙyar na nufi wajensa kafin na ƙarisa Umma ta dakatar da ni cikin kakkauran amo. "In kika ɗaga ƙafarki guda kika isa wajen yaron nan sai na saɓa miki kamamnin. Munafuka mai baƙin hali sai an yi magana ki yi fiƙi-fiƙi da ido kamar shege a rabon gado". Simi-simi na juyo zan shige ɗaki kalamanta a karo na biyu suka sanya ni yin mutuwar tsaye. "Ina kuma kike ƙoƙarin shiga? Wannan kunun da kika bar ni da shi gidan uban waye zan kai shi?. Ai wallahi tun da na dama kunun nan sai ki sayar da shi kin kawo min kuɗina cas babu gara bin zago". Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna muryarta a dushashe na soma cewa"Umma na ga yanzu Baban Adnan ya saye gabaɗaya kuma ya ba ki abin da ma ya fi karfin kuɗin kunu...". Hararar da ta watsa mini ya tursasa mini haɗiye raguwar kalaman ba tare da na furta su ba. "Maman Amatu halin nan yana burge ni. Wani lokacin har mamaki nake yi anya ba ki haɗa jini da yarabawa ba kuwa? Don son kuɗina kin dama ni kin shaye". Furucin da Sahura ta yi kenan da ya sanya Maman Ebuka ɗago labulen ɗakinta tare da yaɓa wa Sahura magana. "Ko wani ƙabila suna da son kuɗin ba sai yarabawa ba. Ko hausa ma akwai mutanen da suka fi ku son kuɗi, ku da har mutum kuna iya yankawa akan kuɗi". "A'a Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni". Sahura ta furta tana wurga mata harara a faƙaice, ba ta ce komai ba ta saki labulen ta koma ɗakinta. Sallamar Amira ɗiyar Sahura da take fita tallan waina da miya ya dakatar da Umma daga zancen da ta yunƙura za ta furta. Tsam! Sahura ta miƙe tamkar wacce aka yi alluran doki ta sauƙar wa Amira kulan dake kanta, ta ja mata kujera ta zauna kafin ta ce"ya na ga yau kin dawo da wuri? Ko dai dawa ce ta yi nama?". "Mama ai na gaya miki ko wainar dubu ɗari kika yi min sai na sayar ta ita cas. Ina fita ko awa guda ban yi ba na sayar, daman mun haɗu da Bilyamin ne shi yasa amma da tun ɗazu na dawo". Guɗa Sahura ta rangaɗa yayin da Amira ta sinco kuɗi daga gefen zaninta ta miƙa mata. Ta karɓa tana riƙa su ƴan dubu-dubu da su. Tsabar murna rawa ce kawai ba ta daka ba amma ta rumgume Amira da ci mata albarka ya fi a irga. "Allah kai ne abin godiya daman an ce da haihuwar gwamna gwara haihuwar matarsa. Duk da Allah bai azurta ni da haihuwar ɗa namiji ba ya ba ni mace mai kamar maza wacce za ta huce min takaici ta share min hawaye. Ni kam na yi farar haihuwa ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba". Sake da baki Umma take bin Sahura da ido kuɗin da Amira ta kawo kuwa cas sai da ta irga su, duk kusan tare suka irga da Sahura. Kamar kububuwa ta juyo kaina. "Dan ubanki za ki ɗauki kunun nan ki tafi ko sai na lahanta ki? Shegiya ƴar iska mai mataccen zuciya. Kowa yana abun kansa amma ban da ni, ni kam na haiho ruwan dafa kaina gantafalalla ɗan kurciya da gashin baki". Babu shiri ya suri bokitin na ɗaura a kaina har ina ƙoƙarin cin karo da Baban Adnan da ya fito fu ya fice daga gidan kamar iska. Har yanzun Ummi da saurayinta suna zaune a zaure ina jin ta tana tambayata lafiya na fito ina kuka ko kanzil ban ce da ita ba sai tsaki da na ja saboda mau kallon da Saurayin natan yake bi na da shi na yi ficewa ta. Tun da na fito daga gida na rasa takamanmen inda zan nufa a saye kunun haka na yi gararamba a titi daga ƙarshe da na gaji na nema gefen hanya na zauna na tisa bokatin kunun a gabana na zabga tagumi. Ko dai maganar da Umma take faɗa na cewar ina da matacciyar zuciya gaskiya ce? Tun da gashi tun fitowata daga gida babu wanda ya sayi kunun ko na sule biyar. Sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina bin bokitin kunun da kallo har na kai hannuna na taɓa ya yi sanyi ƙalau yanzu kam ina da tabbacin duk wanda ya saya ba zai ji daɗi sha ba. Sallamar da na yi a tsakiyar kaina ya dawo daga ni duniyar zahiri daga karatu wasiƙar jakin da na faɗa. Na cira kai ina duban matar dake tsaye a gabana tana riƙe da hannun ɗanta da alama daga makaranta ta ɗauko shi don yana cikin cikakken shirgar kayan makaranta har da kulan abinci riƙe a hannunsa. Sai a lokacin na ankara lokaci ya ƙure kuma ina da islamiyya ƙarfe biyu. Kafin ta yi magana ta riga ta. "Na nawa za a zuba miki?". Ta kafe ni da ido"ba kunu nake so ba, mai sayar da kwankwan can nake tambaya". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na ƙara cewa komai mai sayar da kwankwan ya zo wajen ta juya za ta bi bayan sa bayan ta sanar da shi na adadin kuɗin da take buƙata. Na marairace ina roƙonta tare da yi mata magiya. "Don Allah Hajiya ki saya ko na Naira hamsin ne, wallahi tun safe da na fito ko naira biyar ban yi ba. Ki taimake ni ki yi mini rai". Ta waigo tana duba na kamar ba za ta yi magana ba sai kuma can ta ce"zuba min na ɗari biyar". Ta zaro kuɗin daga jakarta ta miƙa mini, jikina yana rawa na amsa zan zuba mata ta dakatar da ni. "Ki raba wa waɗancan almajiran". Na gyaɗa kai ina jeranta mata godiya kamar kyauta ta ba ni kuɗi. Almajiran suka taso su ma suka dinga yi mata godiya. Na zuzzuba musu na zauna zaman jiran su shanye su ba ni kwanon da ludayin. "Ƴan matan me ye sunan ki ne?". Furucin mai sayar da kwankwan ya ratsa kofofin kunnuwana. "Amatullah". Na furta a taƙaice da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da zuba kamar ƴaƴan magarya. "Kyakkyawan

Chapter 1 of 24