Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sun san cewa tana nuna brave face ne a waje amma a zahirin gaskiya she is crumbling inside. Kallonsu tayi taga duk sun zuba mata ido cikin tausayawa, haushin hakan taji ba kad’an ba ta dubesu rai a 6ace ta fara magana. “Meyasa zaku tasani a gaba kuna kallona kamar nice abun tausayawa? Shine abun tausayawa shi da ya gudu ya bar gidansu akan wata banzar magana tashi. Babu abunda zai sake damuna in dai akan Abul ne, ya je duniya kad’ai zata koya mishi hankali.” “Karki masa baki Laila.” Haydar ya kwa6eta ta harareshi kana ta tashi ta shige d’akinta. Mas’ud ya mik’e tsaye ya isa gurin Haydar ya dafa kad’arshi ya fita daga gidan. Ajiyar zuciya ya sauk’e kana ya tashi yabi Laila d’aki ya sameta a bakin gado, shigowarshi yasa ta kawar da kanta gefe tana share hawayen fuskarta. Zama yayi a kusa da ita ba tare daya matso jikinta ba yace, “I’m sorry.” “Kayi hak’uri na muku tsawa.” Itama da bashi hak’uri. “Zai dawo gida kuma zai gyara halayensa Insha Allah.” “Allah yasa. Amma dolena na rage damuwa a kanshi tunda na lura yana hakan ne don ya bak’anta mini ya tayar mini da hankali. Zanyi ta mishi addu’a bazan fasa ba, amma abun yana cina a zuciyata Haydar, ina jin bak’in cikin abunda yake yi. Wallahi kullum halin Abul yana raina bana mantawa dashi.” Ta fashe da kuka tana rufe fuskarta. Matsawa yayi kad’an ya kwantar da kanta akan k’irjinshi yana shiru ba tare daya k’ara cewa komai ba. Sai data fitar da abunda take ji sannan ta goge hawayenta ta tashi daga kanshi. “Na jik’a maka riga.” “Ba komai.” Yace da ita kana ya kalleta kad’an yace, “Ina kike tunanin zai je?” “Babu wanda zai nemeshi saboda ba samunshi za’a yi ba. Duk ranar daya ga dama zai dawo gida babu wanda ya sani. Bashi kad’ai na haifa ba balle bak’in cikinshi ya kasheni.” “Zai dawo.” “I hope so Haydar, I hope so.” Ta share hawayenta. Text message ne ya shigo wayan wani mutum ya karanta kamar haka. ‘Ina yaron?’ ‘Ya shiga mota zuwa Abuja, yanzu haka ina seat d’in bayanshi.’Ya mayar da martani shima ta text. ‘Karka bari ya 6ace maka, duk inda ya shiga ya fita ka bishi sannan ka tabbatar ka jefa kwaya a cikin jakarshi.’ ‘An gama yalla6ai.’ Washe gari da yake saturday ne har k’arfe taran safe Laila da Haydar basu tashi ba suna bacci. Bugun k’ofar falonsu da ake yi yasa Haydar ya farka yana mutsike idanu. Barin jikinta da Haydar yayi yasa itama ta farka ta tashi ta shiga band’aki shi kuma ya zura jallabiyarsa ya fita yana goge fuskarsa. “Ana zuwa.” Ya fad’a da k’arfi sai dai hakan bai hana duk wanda yake buga k’ofar cigaba da bugawa ba. A fusace ya bud’e amma yana ganin wata dattijuwar mata sai ya sake fuskarsa yana cewa, “Sannu da zuwa. Ki iso.” “Munafuki algungumi dole kace mini sannu da zuwa mana tunda kayi ikonka ka kori jikana daga gidan. Ina Lamlar take? Wallahi kin ji kunya mai auren d’an cikinta. Kin ajiye yaro a matsayin mijinki yana yanda yaso dake, tirr da wannan hali da bak’ar k’addarar. Ina take?” “Ohh tana fitowa.” Ya shige d’aki ya barta a gurin tana masifa. “Wacece waccar matar Laila? Me dangantakarku?” Laila da fitowanta kenan daga bandak’i ta fara goge fuskarta data watsawa ruwa tace, “Umma ce, Kakarsu Sabrin.” Tana fad’in hakan ta fita shi kuma ya zauna yana sauraron hayaniyar Umma. A tsakiyar falon Laila ta sameta tana ta fad’a ita kad’ai. “Umma ina kwana? Ki zauna mana.” “Ba zan zauna ba kuma ba amsa gaisuwarki nazo yi ba. Ina jikana Abul?” Laila ta samu guri ta zauna ta dubeta tace, “Nima ban sani ba.” “Ban gane baki sani ba!Dolenki ki sani tunda a gurinki yake kin k’i barin kowa ya ra6eshi.” Shiru tayi kanta a k’asa tana jiran Umma ta gama abunda zata yi ta tafi domin ta saba mata hakan musamman in Abul ya dad’e bai je ya gaisheta ba. Dama kuwa Umma bata saka Sabrin a layin jikokinta tunda Aliyu ya saka mata sunan Maman Laila. “Kin cuceni Laila, kin 6oye mini shaye-shayen da Abul yake yi gashi har ya gudu ya shiga duniya saboda son zuciya da rashin kamun kai irin naki. Wallahi nayi dana sanin ranar da Aliyu ya ganki yace yana so, daa ya san zaki yi sanadiyyar lalacewar d’ansa da ko kallonki ba zai yi munafuka mai kyawun d’an maciji.” Haydar da yake d’aki yaji d’acin wannan batu ya taso ya fito ya samu Laila tayi k’asa da kanta bata ko motsi. “Hajiya inaga hakan ya isa tunda ba ita ta kaishi bakin duniyan tace ya shiga ba. Sannan duk damuwar da kike ciki baki kaita ba ita da take mahaifiyarsa. Idan baza ki tausaya mata ba ba kuma zaki zo ki tayar mata da hankali a cikin gidanta ba.” “Haydar don Allah kar kayi magana.” Laila ta fad’i hakan hawaye na taruwa a idanunta. “Ni zaka yiwa fitsara? Yaro k’arami da kai sa’an jikana? Dama daga ganinka na gane kalar kwad’ayi ne kai, kuma da wannan munafurcin naka ka kori Abul a gidan nan. Kar ka sake shiga maganata domin da Lamla nake ba da kai ba mijin tace mijin Hajiya, mai jira a samu a bashi shi da uwarshi.” Runtse ido yayi domin yaji zafin maganarta kana ya bud’esu ya sauk’e a kanta. Cikin nitsuwa yace, “Na san Laila tana girmamaki kasancewarki uwa ga mijinta na daa, so zan bari wannan karon duk abunda kika yi ya wuce amma gaba bazan bari ko da wasa ki zageta ki d’aga mata hankali ba tare dana saka hukuma ta shiga tsakaninku ba. Laila matata ce kuma nine mai kareta idan har buk’atar hakan ta taso. Ki fita daga gidan nan sannan karki k’ara zuwa idan har kinsan ba abun arziki ne ya kawoki ba.” Sake baki Umma tayi tana kallonshi shima yana kallonta domin bazai ta6a juran aci mutuncin Laila a gabanshi ya share ba, she is his wife and he promised to protect her. “Haydar da baka tanka mata ba, ta saba yin hakan idan ta gama zata tafi.” “Wannan karon ba sai an jira ta gama ba, ni zan dakatar da ita.” Daga bakin k’ofa aka yi sallama sai ga Nazifi tare da Muna sun shigo. “Laila kije ki saka hijabi.” Fad’in Haydar. Ba musu ta tashi ta shiga d’aki Nazifi yabi bayanta da ido. Gyaran murya Haydar yayi wanda yasa hankalinsa ya dawo kanshi, Haydar ya d’aure fuskarsa tamau yana masa magana ta ido ‘karka kuskura ka k’ara kallon bayan matata.’ Nazifi yayi kasak’e yana kallon ikon Allah, yaro d’an cikinshi ke mishi haka? Ko da ya lura babu wasa a fuskarsa sai ya maida dubanshi ga Umma wacce ta fara kuka tana buga k’irji tana cewa, “Ya zageni yaci mutuncina don nazo jin ba’asin inda jikana ya shiga.” “Umma kiyi hak’uri kiyi shiru, wai meya kawoki gidan ne tun farko?” “Na fad’a maka taji labarin shaye-shayen da Abul ya keyi ne, sannan da cewa ya gudu ya bar gida.” “Bake na tambaya ba kuma ki rufe mini baki, kar in sake jin kin tanka.” Ya gwatsaleta kana ya isa gurin Haydar ya mik’a mishi hannu suka gaisa yana tambayarshi meya faru tunda ya lura Umma kuka hani’an take yi bazata iya magana ba. “Ta shigo ta fara zage-zage shine nace ta daina d’agawa Laila hankali tunda ba ita tace ya gudu ba. Idan bazata kwantar mata da hankali ba bai kamata ta k’ara d’aga mata shi ba. Sannan nace bazan lamunci hakan ba domin Laila matata ce, ko da wasa bazan bari a shigo har cikin gidanta a zageta ba.” “Kuma kayi gaskiya. Umma ki tashi mu tafi gida, idan kin nitsu sai ki dawo kuyi magana kan yanda zaku shawo kan al’amarin.” “Bazan tafi ba sai ta dawo mini da jikana yanzun nan.” “Hakan zai yi wuya Umma. Muna d’auka mata ledan goronta mu tafi.” Muna ta sunkuya ta d’auki ledan wanda garin masifa Umma ta jefar a k’asa. Shi da kanshi ya jata har bakin k’ofa Haydar yabi bayansu yana cewa, “Sai anjima.” Ya kulle k’ofar bayan sun fita. Komawa d’aki yayi ya samu Laila ta shiga wanka ya fita zuwa kitchen ya d’aura musu abinci yana jin tausayin wannan rayuwar tasu da ba’a kwana biyu sai sun had’u da tashin hankali. Mum Fateey 👌 RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 ko katin Airtel na N100 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300. (30) Wunin ranar Haydar bai je ko’ina ba yana tare da Laila wacce take harkokinta cikin sanyin jiki babu walwala. Bai matsa mata dole sai ta washe fuskarta ba domin yasan tana cikin damuwa sosai wanda barkwancinsa ba zai fito da ita daga ciki ba. Sai dai yana iya bakin k’okarinsa wajen ya kwantar mata da hankali don ta rage damuwa. Har yamma suna zaune a gida babu labarin Abul, sau biyu Mas’ud na zuwa yana fad’a musu halin da ake ciki na cigiyar Abul wanda duk magana d’aya yake kawowa wato ‘babu wanda yasan inda ya shiga.’ Bayan la’asar Mas’ud ya dawo gidan Laila ya sameta tare da k’awayenta Hajiya Maryam da Hajiya Shatu wanda Haydar ya kirasu don su tayashi bata baki. Bayan ya gaishesu ya maida dubansa kan Laila wacce ke waya da Sabrin, “Ban ga amfanin zuwan naki ba Sabrin, ko kin zo ba samunshi za’ayi ba. Kiyi zamanki a gidanki, kin ji?” Haydar da a lokacin yake fitowa daga d’aki yayi shirin fita yace, “Ki barta tazo Laila, tana buk’atar kasancewa dake a wannan lokacin.” “Shikenan ki zo.” A nan Mas’ud ya nemi Haydar ya fito su tafi wanda dama zuwa yayi ya d’aukesa. Sallama suka musu suka fita Laila ta biyo bayan Haydar zuwa bakin k’ofar falon. Kallon fuskarta kad’ai da yayi ya gane cewa she’s grateful daya kira su Hajiya Maryam. “Yaushe zaka dawo?” “Sai nine ko nine thirty.” “Ina zaka je haka?” Hannunshi ya d’aura a kan kumatunta yace, “Take care.” Ya shiga motar Mas’ud suka tafi. Jikinta a sa6ule ta koma ciki gurin su Hajiya Shatu suka cigaba da kwantar mata da hankali tana sauraransu har Sabrin ta zo. Daga gidan Laila su Haydar suka wuce gidan Madu inda zasu yi magana da Ummii. Kai tsaye sashenta suka nufa. Mas’ud ne ya shige d’akinta don yayi kiranta Haydar kuma ya samu guri a k’asa ya zauna yana jiran fitowarsu. Basu jima ba suka fito tare Ummii na masa barka da zuwa. Bayan ta zauna ya gaisheta, sai a lokacin Mas’ud ya bata labarin halin da ake ciki wanda aka k’i fad’a mata tun jiya. “Ina jira ne inga waye mai hankali a cikinku da zai fad’a mini abunda yake faruwa.” “Mun d’auka zamu sameshi ne tun a jiyan shiyasa bamu fad’a miki ba Ummii.” Mas’ud ya bata hak’uri. “Tun a jiyan Madu ya fad’a mini. Allah ya tsareshi ya kuma sa ya bayyana cikin aminci.” “Ameen.” Suka amsa duka. “Dama ina son zan kira Khalii Abdi ne kan maganar Abul sai kuma na fasa domin kinsan yanzu sai ya d’aura laifin a kan Laila ba tare da ya saurari me yake tafe dani ba. Shine nake son ki kirashi ki fad’a mishi halin da ake ciki ko akwai abunda za’a yi.” K’arfe tara da wasu mintuna Mas’ud ya ajiye Haydar a gida ya shiga ciki. A kwance a d’aki ya samu Laila amma bata yi bacci ba, sannu da zuwa ta mishi ba tare data tashi ba. “Kinci abinci?” Ya tambayeta yana zama a gefenta. “Bana jin yunwa.” Bai ce komai ba ya tashi ya fita falo ya d’ebo abinci sannan ya dawo ya k’ara zama a gefenta yana cewa, “Tashi kici abinci.” Matsa mata yi dole taci sannan ya koma falo ya barta a d’aki domin ta fad’a masa bacci take ji. Wannan karon shi d’inne ya kasa cin abincin domin ya rasa appetite d’insa baya marmarin komai. Zama yayi yana tunanin hanyar da zai bi a ga Abul hankalin Laila ya kwanta, domin idan tana cikin damuwa shima ba zai ta6a yin walwala ba. Bayan kwana biyu da haka Laila tayi wankan sallah Haydar ya nuna kamar bai gani ba ya cigaba da sha’anin gabanshi. Sannan har a lokacin ba’a ji labarin inda Abul yake ba. A daren ranar bayan sun kwanta Laila ta kira sunanshi, “Haydar.” “Na’am.” “Nayi wanka.” “Na gani.” Ya k’ara jawo bargo ya lullu6a. Daga nan suka yi shiru har bacci ya fara d’ibanshi ta tashi ta zauna, a fusace tace, “Baka ji mena fad’a maka bane?” Juyowa yayi a kasalance yace, “Laila naji mana, kuma na baki amsa.” “So?” “So? Ban gane me kike so in fad’a ba bayan nan.” Komawa tayi ta kwanta shima ya k’ara juyawa wannan karon har yana gyara pillow yace, “Sai da safe.” Bata ce komai ba har yayi bacci tana jin minsharinshi yana fita a hankali. Tashi tayi ta zauna ta dafe kanta da hannunta biyu tana jin zuciyarta na zafi domin har yau tunanin Abul na ranta. Ita ta haifeshi, ta raineshi ta bashi tarbiyya daidai iyawarta sannan ta bishi da addu’ar Allah ya shirya mata shi, amma lokaci d’aya, cikin k’ank’anin lokaci al’amura sun canja wanda har halayyar Abul ma ya canja. Ina yake? A wani hali yake? Hannun wa yake? Me ya sameshi ko me zai sameshi? Duk bata sani ba. Sannan zuciyarta na kawo mata images kala iri daban-daban wanda take hasko mata Abul a cikin yanayin maye yana fad’a da mutane wanda watak’ila su masa illa ko su kasheshi gaband’aya. Tana cikin tashin hankalin da babu mai iya gane yanda take ji sai wanda hakan ya faru dashi. Hawaye ne ya sauk’o kan kumatunta tana tausayin rayuwarta da kuma ta Haydar wanda a yanzu yafi kusanci da ita a kan kowa. Ta san ba k’aramin hak’uri yake yi da ita ba, kuma tana ganin k’ok’arinsa da dattakunshi. “Haydar.” Ta kira sunanshi wanda hakan yasa ya farka ya fara lalu6arta cikin duhu. “Meya sameki Laila? Bakya jin dad’i ne?” Kuka ne ya ku6uce mata don Haydar is too good for someone like her, meyasa ya kasance mara son kai? Meyasa yake da hak’uri kuma yake son mace irinta? “Why me?” Ta tambayeshi a lokacin da yake tashi zaune ya kunna bedside lamp kana ya ganta a zaune babu alamar rashin lafiya a tattare da ita. “Kin tsoritani, I thought baki da lafiya ne.” Ya matsa gurinta yana jawota jikinshi ta dakatar dashi. “Why me?” Daburcewa yayi domin bai gane inda maganarta ta dosa ba. “Ban gane ba Laila.” “Meyasa ka za6eni a matsayin wacce kake so ka kuma yarda ka aureni bayan duk red flags d’in da ka gani kafin hakan?” “Saboda hakan ne zai kasance.” “This is not enough.” Ta share hawayenta tana kallonshi ido cikin ido. “Because I love you Laila, damn it woman. Me kike so nace? In fad’a miki cewa ke nake so nake kuma burin samu kuma Allah ya kar6i addu’ata ya bani ke ko yaya? Ko kuma so kike in fad’a miki ke cewa ke kad’ai nake da burin yin rayuwa har abada kuma I don’t give a fuck wace rayuwa kike ciki ko kike fuskanta ba?” Wuyanta ya rik’o ta baya ya tashi ya d’aura guiwoyinsa a kan gadon ya sassauta muryarshi yace, “Once I’m in, I’m in for better and for worse. I love the whole you Laila, I know you are not perfect but you are fucking perfect to me, ina son kayana a haka. Kuma I’m not going anywhere ina tare dake har abada till death do us part.” Bakinsa ya d’aura a nata yayi kissing d’inta na wasu sakanni sannan ya tashi ya sassauta rik’on da yayiwa wuyanta tace, “Why?” “Because I love the whole package and what comes with it.” “Haydar...” “Shssshh.” Ya d’aura yatsunsa kan lips d’inta wanda suka fara yin ja dalilin kissing d’inta da yayi. “I love you.” Yace da ita yana had’e goshinsu guri d’aya. “I love you too.” Itama ta fad’a tana sak’ala hannayenta a wuyashi yayi hugging d’inta yana shafa bayanta. Sun jima a haka sannan suka rabu suka tsaya kallon juna fuskarsu d’auke da murmushi. Sunkuyar da idanunta tayi k’asa tace, “Nayi wanka.” “Munyi maganan Laila.” A fusace ta d’ago da kanta har ta manta da abunda ya faru yanzu tace, “Don meyasa ba zaka nemi hak’k’inka?” “Saboda baki shirya ba, kuma bazan miki dole ba. And I want you to need me ba wai ki bani kanki don sauk’e hak’k’ina dake kanki ba. Kin fahimceni?” Bata ce komai ba amma ta fahimceshi tsaff, gyad’a kai tayi ta koma ta kwanta shima yabi bayanta yana jawota jikinshi. “Ki samu kiyi bacci kinji? Ki barwa Allah komai shi zai gyara a lokacin da bakya tsammani.” Hannunshi daya mak’ala a k’ugunta ta d’ago tayi kissing kana ta rungume a k’irjinta. Shima kissing d’in tsakiyar kanta yayi yana murmushi sannan yace, “Good night matar Haydar.” “Good night Ruwan Zuman Laila.” Washe gari da safe Haydar ya tafi aiki kamar kullum Laila kuma ta wuce shagonta domin ta fara zuwa bayan mijin nata ya hanata zaman gida. Bai jima da zama a office d’insu ba aka fad’a mishi wai Alhaji Abdul na kiransa. Wannan ne karo na farko da zasu had’u bayan aurensa da Laila. D’an aikan yana fita shima yabi bayanshi fuskarsa a had’e domin baya so ko kad’an wata magana ta k’ara had’ashi da Alhaji Abdul, ya dawo yin aiki k’ark’ashin shi ne domin rashin samun aiki da kuma Ammi da Laila, the most important people in his life da zai iya yin komai domin ganin farin cikinsu. Sai dai yayi alk’awarin da zarar ya fad’a mishi magana wacce bata gamsheshi ba zai bar aikin, in yaso ko gadi zai fara a kantin daya bari. Yana shiga office d’in ya sameshi yana waya ya bashi baya, a gefe ya tsaya yana kallonshi har ya gama sannan ya juyo da murmushi a fuskarsa yace, “Ashe har ka shigo. Ga guri ka zauna.” Haydar ya zauna fuska ba yabo ba fallasa yace, “Morning sir.” Wata irin dariya Alhaji Abdul yayi kana yace, “Morning Aliyu Haydar. Sorry bamu baka hutu na aurenka ba saboda abun yazo mana a k’urerren lokaci ne, kuma baka jima da fara aiki damu ba.” Shiru Haydar yayi yana kallonshi, Alhaji Abdul ya gyara zamanshi kana yaci gaba, “Dama a farkon fara aikinka mun fad’a maka cewa da zarar mun ga yanayin jajircewarka zamu k’ara maka matsayi. Bayan duba da muka yi da k’ok’arinka yasa muka baka matsayin Assistant Manager na wannan company.” “Bana buk’atan hakan.” Ya amsa masa flatly kana ya mik’e tsaye zai tafi. “Ban sallameka ba Aliyu Haydar, sannan baka fad’a mini dalilin da yasa baka son k’arin girman ba, wanda nasan mutane da dama jira suke yi su samu wannan damar su kar6a.” “Ba nine na dace da wannan seat d’in ba saboda ban jima da fara aiki daku da har zaku d’auki babban matsayi irin wannan ku bani ba. Sannan akwai wad’anda suka cancanta wad’anda suka jima suna muku aiki tuk’uru. Zai zama tamkar na shiga gonar da ba tawa bace idan na k’ar6i wannan k’arin girma.” Shiru Alhaji Abdul yayi yana kallonshi shi kuma yana tsaye yana jiran a sallameshi ya tafi. A ransa kuma haushi yake ji da yana da wani hanyar samun aikin da ya bar wannan. Sannan bai gane manufar Alhaji Abdul ba, menene dalilinsa na k’ara masa matsayi alhali bai cancanci hakan ba? “Ka yarda da cewa ka cancanci hakan. Secretary na da manager zasu nuna maka sabon aikinka, sannan zaka saka hannu a wasu papers da zasu baka. Zaka iya tafiya.” Fita Haydar yayi ba tare da yace komai ba, sai dai a maimakon yayi hanyar office d’insu sai ya fita daga company d’in baki daya ya hau achaba ya koma gida. “Sir ya fita daga company.” Secretary Alhaji Abdul ta sanar masa. “Zai dawo. Zai dawo because I’m the one playing the strings now.” Ko da Haydar ya isa gida bai samu Laila ba kamar yanda yayi tsammani, zama yayi a kan kujera ya dafe kanshi wanda yake jinshi kamar an d’aura masa dutse. Dalili irin wannan yasa tun farko ya nunawa Laila cewa ba zai koma aiki k’ark’ashin Alhaji Abdul ba, saboda yasan he will try to control him, wanda shi kuma ba zai d’auki hakan ba koda wasa. Ya kai minti talatin yana zaune yana tunani yaji an bud’e gate Laila ta shigo da motarta. Bai d’aga kanshi ba har ta shigo ta sameshi, a kusa dashi ta zauna kana ta dafa kafad’arshi tace, “Wai me yake faruwa ne? Kuma ina ta kiran wayarka ka k’i d’auka.” “Babu komai.” “To meyasa Alhaji Abdul yayi ta kirana? Sai daga baya yake cewa wai kunyi magana dashi ka tafi cikin fushi. Wace magana kuka yi?” A fusace ya tashi tsaye yace, “Don meyasa zaki yi magana dashi? Na hanaki d’aukan wayarsa wanda sai da kika gindaya mini sharad’inki na yarda dashi, kuma shine zaki koma kuna waya dashi? Me yake fad’a miki? Meyasa kike d’aukan wayarsa?” “Haydar....” “No, karki fara. Kin karya dokata Laila, just doka d’aya dana saka miki kin kasa bi.” Yana fad’in hakan ya fice daga gidan ya barta hawaye na taruwa a idanunta. Me ta mishi? Meyasa ba zai saurareta ba? Me yake damunshi? Me yake shirin faruwa dasu? Dama zai iya fushi da ita? Fitansa a gida ya rasa ina zai yi, hawa achaba yayi yace ya kaishi kantin su Nasir domin shi kad’ai ne zai iya fad’a masa matsalarsa a yanzu ba Ammi ko Laila da zasu bashi shawaran ya koma bakin aikinsa ba. Bayan ya gaisa dasu yake tambayarsu ina Nasir, “Kut! Bai fad’a maka ya samu aikin gwamnati ba? Ai kwananshi uku rabonshi da nan.” “Inaga bai samu zama bane. Bari zan masa waya.” Da haka ya fita yana jin ba dad’i a ransa, meyasa Nasir bai fad’a mishi wannan abun farin cikin ba? A waje yayi ta kiran wayarshi bai d’auka ba, daya gaji ya hak’ura ya k’ara hawa achaba zuwa gidan Ammi. A rumfarta ya sameta tana d’aura ruwan zafi a kan camping gas. “Ali yau baka je aiki bane?” “Naje, bana jindad’i ne na dawo. Ina kwana.” Ya gaisheta yana shiga d’akinta. “Lafiya dai kam? Me yake damunka?” Ta biyoshi tana tambayarshi. “Ammi kaina yake ciwo ina so na kwanta nayi bacci.” “To, meyasa baka koma gidanka ba?” Kwanciya yayi a kan gadonta yace, “Laila bata gida kuma bazan ji dad’in zama ni d’aya ba.” “To Allah ya sauwak’e.” Da haka ta fita ta barshi shi kuma ya gyara kwanciyarshi ya rufe idanunshi. An fara kiran sallah azahar Ammi ta tasheshi kan lokacin sallah yayi. Duba wayansa da zai yi yaga missed calls d’in Laila dana Nasir da yawa. Nasir ya kira yana fitowa daga d’akin Ammi, “Ina ka shiga haka?” “Wallahi nayi bacci ne. Kana ina ne?” “Ina gidanmu.” “Ina zuwa.” Ya kashe wayarsa ya dubi Ammi dake alwala yace, “Ammi na tafi. Sai anjima.” Dakatar da alwalan tayi tace, “Anya kuwa lafiya kalau kuke? Ko dai fad’a kuka yi da Hajiya Lailan? Ali bana son saurin fushi fa, matar nan tana k’ok’arin yi maka biyayya don Allah karku fara samun matsala tun daga yanzu. Zaman aure hak’uri ya gada, dama zo mu zauna zo mu

Chapter 8 of 32