An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
RUWAN ZUMA 09023713064
RUWAN ZUMA đŻ
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
(22)
Ummii ce ta fito tsakar gidan bayan an kai mata rahoton gida babu lafiya ana ta hayaniya.
Laila ce ta fara hangota tayi saurin barin jikin Haydar ta koma kusa da Masâud tana ganin yanda Madu ke yiwa Alhaji Abdul magana kâasa-kâasa daga baya ya dâauka masa wayarsa da ya watsar a kâasa ya sanya masa a aljihu.
âMe yake faruwa ne naji ana ta hayaniya?â Ummii ta kâariso gurinsu tana tambaya cikin kullewar kai.
Alhaji Abdul ya gaisheta kana ya fice daga gidan cikin sauri ba tare da yace komai ba, hasalima ko kallon inda Laila da Haydar suke bai yi ba.
Madu yayi wa Laila kallon tsana yace,
âWannan butulun ce ta fasa aurenta da Alhaji Abdul ta auri wannan yaro da suke yawon barikancisu tare. Laila kin bani mamaki kin kuma cuci kanki.â Yana fadâin hakan shima yabi bayan Alhaji Abdul.
Ummii ta dubi Laila hannunta na rawa tace,
âMe nake ji Laila? Masâud me yake faruwa?â
Ganin haka yasa Masâud yayi saurin isa gurinta ya jata zuwa dâakinta bayan ya fadâawa kowa a basu guri zasu yi magana.
Laila da har ta fara tara kwalla sanin Ummii baza ta ta6a amincewa da wannan aure nata ba ta bi bayansu jiki a sanyaye.
âHaydar ka shigo.â Masâud ya kira Haydar wanda shima ke tsaye amma hankalinsa na kan Laila wacce take cikin damuwa. Ko dai wannan shine dalilinta na kâin aurensa?
Dukkansu suna zaune a kâasa yayinda Ummii ke zaune a kan kujera tana ta kallon Haydar wanda ta tabbatar cewa shine mijin Laila. A nan Masâud ya bata labarin duk abunda ya faru kana yayi shiru ya barta tana tunani.
âAllah ya sanya alkhairi yasa gidanki ne na har abada. Hakan yayi daidai.â Fadâin Ummii kenan wanda yasa kowa ya dâago da kanshi cikin mamaki don basu tsammaci zata dâauki abun cikin saukâi haka ba.
âUmmii kina nufin hakan ya miki?â Laila da bata gaskata kunnenta ba tayi wannan tambayar tana zura mata ido.
Gyadâa kai tayi ta murmusa kadâan wanda tsufan fuskarta ya bayyana tace,
âAuren kowa yake so kiyi kuma kinyi, batun a za6a miki wanda zaki aura ba hurumin kowa bane sai naki ke kadâai. Auren mutumin da bashi da kirki da hali mai kyau babu riba sai fadâuwa, idan bai lalata miki rayuwa ba zai iya lalata ta zuriyar da zaku haifa.â
Duk âyan dâakin suka gyadâa kai cikin yarda da maganarta, a nan ta kâara mayar da hankalinta kan Haydar tace,
âKa kula da ita.â
Da haka Ummii ta tashi ta shige dâakinta bayan ta kira Laila suka shiga tare.
Ganin hakan yasa Masâud yace su fita su jirata a waje tunda ya lura magana zasu yi.
A kusa da motar Masâud dâin suka tsaya, kana Masâud ya amsa kiransa da ake yi tun a falon Ummii. Bayan ya gama magana da wanda ya kirashi ya shiga motarshi yana cewa Haydar.
âAbokaina suna jirana Haydar, once again congratulations.â Ya mikâa mishi hannu suka yi musabaha suna murmusawa dukkansu.
âNagode Masâud, nagode kwarai.â Ya amsa kana yaja da baya zai cire garen Masâud ya dakatar dashi.
âKa barshi a jikinka.â Yana fadâin hakan ya fice daga gidan ya bar Haydar tsaye jiran Laila.
Minti goma da haka Laila ta fito sanye cikin laffaya golden da yayi matukâar mata kyau sai walwali take yi, sai dai jikinta a sanyaye yake tamkar wacce bata da lafiya.
Wannan karon Haydar tsayawa yayi yana kallonta ba tare da yaji kunya ko fargaba ba saboda ta zama matarsa halalinsa. A take yaji kishi ya shigesa dalilin tun farko baya son yaga ta saka laffaya saboda yana fitar da shape dâin jikinta sosai ba kadâan ba. Lokaci yayi da zai hanata sakawa domin ba zai so kowa ya kâara kallon manyan cinyoyin matarsa ba.
Tana isowa ta mikâa mishi key dâin motarta ya kâar6a yana hadâawa da hannunta wanda tayi saurin janyewa ta zagaya ta shiga baya ta zauna.
Karkadâa kai yayi yana murmushi mai bayyana hakwara shima ya shiga motar ya kunna suka fara tafiya.
âAmarya babu magana ne?â Yace da ita yana mai juyowa kadaâan yanda zai ganta.
âHaydar ka kalli gabanka karka hadâu da wata motar.â
âTunda bakya son in hadâu da wata motar meyasa kika shiga baya? Sai ki dawo nan gefena ta yanda zan dinga ganin duk motsinki.â
âHaydar!â Ta kwa6eshi ganin bai daina juyowa yana kallonta ba.
âIdan kina so in daina juyowa tell me you love me.â Ya kâara lekâata da danna masa harara fuskarta babu alamar wasa.
Ko kadâan hakan bai damesa yaci gaba da damunta wai sai ta fadâa mishi tana sonshi. Ganin abun nashi bana kâarewa bane yasa ta rufe fuskarta da gyalenta tana tuna maganganun Ummii wanda sune suka hanata yiwa Haydar fadâa.â
âIdan a daa dâan dâakinki ne yanzu kuma ya dawo mijinki kuma shugabanki duk da kâankâantar shekarunsa. Kamar yanda zaki yiwa mijinki wanda ya fiki biyayya haka shima zaki yi mishi ba tare da kinyi laâakarin kin fishi ba. Ki guji bashi umurni tamkar ke kika ajiyeshi, karki manta miji ko jariri ne shine babba a kanki Laila.â
Shawarwari da fadâan da Ummii tayi mata basu daina yawo a kwakwalwarta ba tana jin zuciyarta a cunkushe tamkar aurenta da Haydar bai kamata ya faru ba. Ta kasa gane farinciki take ciki ko bakâin ciki domin har lokacin bata ji wani sanyi da dadâin da taji a lokacin da aka fadâa mata an dâaura mata aure da Aliyu uban âyayanta ba. Ko dai wannan auren is not meant to be? Ko dai tayi gaggawar amsa aurensa ta biyewa zuciyarta da tsoron abunda Masâud zai aikata ne? Shin aurenta da Haydar zai zama alkhairi? Wani irin zama zasu yi? Ta yaya zasu fara? Hankalinta bai kwanta da wannan auren ba! Ko dai ta nemi ya saketa?
âMun iso Amaryata.â
Tayi saurin yaye gyalen nata tana gyara zamanta zuciyarta na bugawa.
Ganin mutane cirko-cirko da tayi a tsakar gidan yasa tayi saurin budâe marfin kâofar ta fita tana tambayar ko lafiya.
âDâazu Abul ya dawo hankalinshi a tashe ya shiga dâakinsa yana fasa abubuwa kuma munyi kâokâarin budâe kâofar ya kulleta ta ciki.â Fadâin Ajidde wacce daga ganinta hankalinta a tashe yake ba kadâan ba.
âInnalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Abul yaji labarin auren nan.â
Da haka ta shige cikin gidan da sauri âyan uwan nata suka rufa mata baya.
A bakin kâofar dâakin Abul ta samu Sabrin zaune tana buga masa tana kuka tana kiran sunanshi.
âDon Allah Yaya Abul ka budâe kar ka jiwa kanka ciwo.â
Tana ganin mahaifiyarta ta tashi da sauri ta yiwo kanta ta kama hannunta tace,
âMama wai da gaske yaron nan kika aura? Ki fadâawa Yaya Abul kâarya ake masa ya budâe kâofar nan kafin ya yiwa kanshi illa.â
Laila bata amsa mata ba ta isa bakin dâakin ta fara kwankwasawa.
âAbul ka budâe kâofar nan yanzu kar ka bari raina ya 6aci.â
Haydar dake waje ya lura da wani irin mugun kallon da wasu mata âyan uwan Laila suke mishi wanda bai ga dalilin hakan ba.
Zare key yayi shima ya fita daga motar yabi bayan Laila domin yasan ba lafiya ba.
Yana shiga ya sameta a bakin kâofar Abul tana sauraron abunda yake cewa tana hawaye,
âKin cuceni kuma kin cuci kanki Mama, ki rasa wanda zaki aura kaff mazan duniyan nan sai wannan dâan iskan mai shegen kwadâayin? Wallahi ji nake yi kamar in kasheshi kuma in kashe kaina. Baki san a wani hali kika jefani a ciki ba. Bazan zauna a gidanki ba duniya zan shiga!â
Yana fadâin hakan ya finciko kâofar har Laila na buguwa da gini yayi hanyar fita daga gidan Laila da Sabrin suka bishi a baya suna kiran sunanshi amma bai tsaya ba.
Yana zuwa bakin kâofa yayi kici6is da Haydar wanda ke shigowa suka tsaya kallon kallo, zuciyar Abul na tafarfasa tamkar zata kâona masa kâirji.
Laila dake binshi a baya ta iso zata kar6e jakar hannunshi yayi saurin janyeta yayi gaba yana cewa,
âSai kayi dana sanin auren mahaifiyata wallahi.â
Da haka yasa gudu ya fice daga gidan Laila na kwala masa kira tana hawaye.
Sabrin ce itama ta fito dâauke da gyalenta da jakarta tana kuka tazo zata fita Laila ta rikâota,
âSabrin ina zaki je?â
âMama bazan zauna ina kallon wannan abun kunya da takaicin ba.â
Laila na jin hakan ta sake mata hannu tace,
âKi je.â
Bata kai da fita ba Ajidde ta rikâota cikin fushi tace,
âAshe kema zaki iya zama butulu ga mahaifiyarki? Wani irin wahala da sadaukarwa ne bata muku ba? Kar ki biyewa Abul ki zama mara hankali kema Sabrin. Karki jawowa kanki fushin Allah akan abunda yake sunna ta maâaikinsa.â
Rufe idanunta tayi kana ta budâesu ta saukâe kan Haydar wanda jikinsa ya gama yin sanyi sosai domin bai ta6a zaton abunda Laila take gudu ya kai haka ba. Wata muguwar harara ta watsa masa kana itama ta fita daga gidan tana share hawayenta.
âIâm sorry.â Laila ta jiyo muryar Haydar a sanyaye.
âBa laifinka bane, laifina ne.â Tana fadâin hakan ta shige cikin gidan.
Ajidde da take babba a gurin ta yiwa sauran mutanen magana kan su koma ciki, aka barta ita da Haydar wanda yake jin zafi a zuciyarsa ba kadâan ba.
Matsawa suka yi gefe ta fara magana kamar haka,
âBa kowa ke murna da wannan auren naku ba, amma hakan bashi zai sa kayi dana sani ko kaji auren ya fita a ranka ba. Ban san labarinku ba amma ka zama garkuwar Laila saboda tana son âyayanta bata son abunda zai rabata dasu. Ka zama namiji a gidanka karka bari maganar mutane ya ta6a rayuwar aurenku ko ya lalatashi gabadâaya. Kar ka manta kowanne dâan Adam bai tsira ba, wallahi babu wanda ya tsira daga bakin mutane. Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da shaidâan tsakaninku.â
âAmeen, Nagode.â Kawai yace da ita kana ya fito da key dâin Laila ya mikâa mata ta kâarba.
Da haka ya juya ya fita daga gidan jikinshi a sanyaye tamkar bashi ne yake jin kuzari dâazu ba. Ashe haka bakâin ciki yake hana mutum gane jindadâin rayuwa?
Acha6a ya tara ya koma gidansu, a tsakar gida ya samu Ammi tana rikâe da radio tana jin labaran rana, rage volume tayi kana ta dubeshi ta kyau tace,
âAli kai kuma daga zuwa dâaurin aure sai kaje kayi zamanka? Tukunna ma rigar waye a jikinka kamar wani sabon ango?â Ta kâarishe maganan cikin zolaya tana murmushi.
âAmmii bani dari da hamsin in akwai a gurinki.â Yace da ita yana mai kwa6e garen tare da hular.
âAli lafiya dai ko? Ya na ganka haka jiki a sanyaye? Ko don auren da Laila tayi ne? Ta mikâe tsaye ta iso gurinshi.
Kadâa kai yayi yace,
âAmmi bani kudâin in bawa dâan acha6a.â
Shiga dâaki tayi ta dâauko dâari biyu ta mikâa mishi kana ya fita ya bawa mai acha6a ya dawo ya zauna akan tabarmar dake shimfidâe a rumfar tasu.
âAli ka sakawa ranka dangana domin Laila ta maka nisa yanzu ta zama matar wani. Allah zai baka wacce ta fita da yardarsa.â
âAmmi an dâaura mini aure da Laila yau bayan ta fasa auren ubangidana Alhaji Abdul.â Yayi saurin fadâa mata domin kar ta zauna cikin duhu.
Dafe kâirji Ammi tayi cikin kadâuwa tace,
âKai Ali!!â
Murmushi yayi wanda akace yafi kuka ciwo kana ya bata labarin duk abunda ya faru zuciyarsa a cunkushe.
Shiru tayi na tsawon sakanni tana tunani kuma tana kallonshi tamkar bata gaskata labarin da ya bata ba.
Da ya lura da hakan yace,
âAmmi baki yarda ba ko?â
Kadâa kai tayi kana saukâe hannayenta tace,
âAli ina mamakin yanda Allah yake sauya lamarinsa yanda yaso kuma a lokacin da yaga dama.â Murmusawa tayi irin na jindadâi taci gaba da magana.
âNa tayaka murna Ali, Allah ya sa hakan shine alkhairi a gareku baki dâaya. Nayi murna kwarai. Amma dai anyi auren nan babu shiri, yanzu ni dâin uwar ango ce shine nake zaune haka cikin zanin da ya kodâe? Bari in shiga makwabta in sanar dasu wannan labari su zo a yi wunin biki. Zan fasa asusun da nake tarawa ka sayo kayan abinci, tukunna ma a ina zaku zauna?â Ta dakata da lissafinta ta nemi kâarin bayani.
âBan sani ba Ammi domin yanda kika ji labarin nan a sama nima haka kâaninta yazo ya sameni da maganar auren. A yanda mutane da dama suka tsani auren nan zai yi wuya yayi tsawo Ammi. Zai yi matukâar wuya.â
âMe kake so kace?â Ta dubeshi ranta a 6ace.
âIdan har ta bukâaci rabuwa dani zan bata takardarta Ammi domin ita kanta bata cikin farinciki.â
Fadâa Ammi ta fara masa yayi shiru yana jinta ba don yana gane me take fadâi ba, domin gaba dâaya hankalinsa na can kan Laila wacce yaga tsantsar nadama da dana sani a idanunta. Tana matukâar son âyayanta wanda hakan shi ya hanata aure duk tsawon wannan lokaci gudun kar su bar hannunta. A yanzu kuma da ya shigo ya tarwatsa wannan tsari nata yasan aurensu tamkar mutum ne mai tafiya akan kwai.
Yana jin an fara kiran sallah Jummâah ya tashi yana cewa,
âAmmi zanyi wanka in tafi masallaci.â
âWato maganan da nake fadâa makan ne ba zaka saurara ba?â
âBa haka bane Ammi, idan na dawo zan zauna mu tattauna.â Da haka ya shige dâakinsa ya barta a nan tana godewa Allah da yasa Alinta yayi aure ba tare da anyi masa gorin mahaifi ba.
Bayan ya gama kimtsawa ya fito zai tafi masallaci Ammi ta tsayar dashi ta mikâa mishi kudâi da yawa a hannunsa. Tace.
âGa kudâin dana fara tarawa don aurenka, tunda har an dâaura babu amfanin cigaba da ajiyeshi. Ka sayo shinkafa da kayan miya zamu yi jollof na biki.â
âAmmi ai kun makara da yin gayya da dâaura tukunya, ni bana so ki fadâawa kowa a unguwan nan har sai naga yanda Allah zai yi. Don Allah ki daina kawo zancen nan.â
Fuskar Ammi ta kwaye alamar bata ji dadâin hakan ba ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan kujeran tsugunno shi kuma ya tsugunna ya fara magana,
âYaushe zaki fita da kanki a tsakar ranar nan kina bin makwabta kina cewa dâanki ya dâaura aure? Yaushe kuma suka yarda da zancenki har suka taso suka zo gidan nan suka tayaki dâaura girki? Karki manta mata na fita ne da izinin mazajensu, a wannan lokacin kuma duk namiji ya tafi masallacin jummaâa, kina son su fito ba tare da izinin mazajensu bane don kawai su tayaki farinciki Ammi?â
âNaji tashi ka bani guri. Amma ko gobe ne sai anyi wannan wunin.â
Murmushi yayi mai sauti yace,
âKudâinki baza su isa a sayi shinkafa da kayan miya ba kuma ni bani da ko sisi, kâarshe ma yanzu ke zaki bani kudâin zuwa masallaci. Da haka ya zari dâari biyar ya fice a gidan yana mata dariya domin duk cikin kudâin dâari biyar ce babba.
âAli ka dawo mini da kudâina.â Ta fadâi hakan cikin fadâa amma fuskarta ya bada ita saboda murmushin da take yi.
âAllah ya kare mini kai daga sharrin masu sharri ya hana makâiyanmu ganinka har abada.â Ta bishi da adduâan da ta saba yi masa kullum in ya fita.
A can gidan Laila kuwa Ajidde ta fadâawa danginsu kan su koma gidan Madu inda zaâa kai amaryar Masâud a yi bikin kawai a can.
Sauran kâawayen Laila su Hajiya Maryam da Hajiya Shatu da abokan harkokinta kadâai aka bari a gidan, suma suna cin abincin rana suka musu sallama aka basu souvenirs suka tafi.
Kafin laâasar gida ya rage daga Laila sai kâawayenta biyu wanda su suke bata baki tare da kwantar mata da hankali.
Ita kuma damuwarta kaff na kan Abul wanda take kiran wayarsa amma tana jinshi a kashe. Tasan ba zai bar wayar a kunne ba kuma kâarshenta wannan karon ma da kyar su sameshi da kansu har sai ya bayyana don kanshi.
Tana son kiran Masâud ta fadâa mishi halin da ake ciki amma kuma ta fasa domin yau ne ranar farin cikinsa bai kamata ta 6ata mishi ba.
Da yake tun farko tare suka ajiye lokacin da zaâa dâauko amaryarsa, ai kuwa lokacin yana yi ta dâauko laffayanta ta saka zata fita Hajiya Shatu ta tambayeta ina zata je.
âZamu je dâauko matar Masâud ne, ko kun manta?â
âSai ki tambayi mijinki idan ya barki sai ki fita.â Fadâin Hajiya Maryam tana gyara zamanta domin bata da niyyan fita.
Sake baki Laila tayi tana kallonsu cikin mamaki da kuma haushi,
âYanzu fitan da zan yi sai na kira Haydar ya bani izini?â
Gyadâa kai Hajiya Shatu tayi kana tace,
âKin jima baki yi aure bane amma baâa canja wannan tsarin ba har yanzu, kuma kinsan hukuncinki idan kika fita babu izininshi. Karki nemawa kanki tsinuwar Allah tun baâa je koâina ba.â
Dâaga musu hannu tayi alamar surrender tace,
âNaji, naji.â Kana ta shige dâakinta ranta a 6ace tana tunanin yanda zata kashe wannan aure ba tare da ran kowa ya 6aci ba.
Su Ajidde ne suka dâauko Naana amaryar Masâud aka kawota gidan Madu aka yi budâan kai da yamma, ana sallan magriba aka kaita gidan da Masâud ya gina shi da kanshi shima a cikin Jakara wanda tafiyar minti uku zai kawoka gidan Laila.
Bayan isha kowa ya watse aka bar amarya da kawayenta kafin angwaye su shigo.
Daga masallacin jummaâa Haydar yaje gurin aikin Nasir wanda tun bayan abunda ya faru da Laila ya ja baya dashi, wai yana tsoron kar a kulleshi.
Yana ganinshi suka yi musabaha cikin dâokin ganin juna kana ya gaisa da sauran mutanen gurin suka zauna.
âKana nan abunka?â Fadâin Nasir yana mikâa mishi coke mai sanyi.
Haydar ya kâarba tare da yin godiya yace,
âIna nan. Yau aka dâaura aurena da Laila.â
Nasir da ya kur6i Coke dâinshi ya shakâe ya fara tari Haydar kuma yaci gaba da sipping nashi a hankali tamkar bai ga Nasir ba.
âKai mugu ne dâan iska.â Nasir ya fadâa tsakanin tari.
âMaganin mai gudun abokinsa don tsoro. Wallahi kaji kunya! Yaushe rabon da kazo gidanmu? Tunda Ammi ta dawo gida baka kâara zuwa duba jikinta ba.â
âBa ina maka waya ba?â Ya amsa masa bayan tarin ya tsagaita.
âWaya bai isa ba.â
âSue me.â
Haydar ya ajiye goran coke dâin a saman counter yace,
âWallahi ba wasa nake maka ba. An dâaura mini aure da Laila yau.â
A nan ya bashi labarin abunda yaga zai iya fadâa masa ba tare da ya fadâi abunda âyayan Laila suka yi ba, saboda 6oye sirrin âyayanta.
âKai Haydar!â
âBaka yarda bane?â
âTo uban me kake yi a nan kana Ango dâanye shataf?â
âIna kake son in je?â Ya tambayeshi yana tsura mishi ido.
âI donât know, amma dai ba nan ba kuma ba cikin tsofaffin kaya ba.â
âSue me.â
Bai bar gurin ba sai bayan isha bayan ya nacewa Nasir ya rokâi ubangidansu ya dawo dashi aiki a kantin tunda ya daina aiki a Luâa Ventures.
Yana isa unguwarsu yaga motar Masâud a kâofar gidansu yayi saurin shiga don jin meya kawoshi.
Samu yayi Masâud na zaune a kan tabarma shi da wani abokinsa dâaya suna hira da Ammi cikin yaren Shuwa wanda har yau shi bai iya ba.
Sallamar da yayi yasa suka dakata da maganan da suke yi kana suka amsa ya samu guri ya zauna yana mikâa musu hannu suka yi musabaha.
âAli ina kaje tun dâazu ana ta nemanka? Masâud bana fadâa maka ana yin isha zai dawo gida ba?â
Masâud ya gyadâa kai yana kallon Haydar yace,
âAi kuwa Ammi.â
Haydar dai shiru yayi yana jiran da wacce suka zo domin har cikin ranshi ya raya cewa Laila ce ta aikosu ya bata takardarta tun kafin auren ya kwana.
âKa hadâa kayanka ku tafi.â Cewar Ammi tana mikâewa ta shige dâakin Haydar don tayashi hadâa kayansa.
âWhat? Ammi ban gane in hadâa kayana ba sai kace wata mace.â Yabi bayanta yana mata magana amma har ta fara jawo kayanshi masu dotti da wankakku tana ajiyewa a gefe bata ce mishi kanzil ba.
Dariya Masâud yayi amma yayi saurin kâunsheta yana kasa kunne shi da Hamidu abokinsa.
âMu da aka kai mana mata shi kuma shi zaâa dâauka a kaiwa matarsa. Bari mu ga ko zai yi kuka in yazo rabuwa da Maman nashi.â Masâud ya kâara fashewa da dariya yana sauraron draman Ammi da Haydar.
âAmmi don Allah karki ta6a mini gajerun wandunana masu dotti, ki bari zan hadâa kayan da kaina. Ammi!.â Ya fadâi hakan yana kwacewa daga hannunta cike da kunya.
âAmmi nifa babu inda zan je in barki ki kwana ke kadâai.â Ya fadâi hakan bayan sun gama hadâa kayan.
âYau na saba kwana ni dâaya? Lokacin da ka tafi bautar kâasa a can kudu da waye nake kwana? Dâauki jakanka ku tafi karka 6ata musu lokaci.â Fadâin Ammi kenan tana turashi gaba.
âAmmi ki bari gobe zan je da kaina muyi maganan inda zata zauna, zan nema mana gidan haya.â
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 32