Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“Mas’ud yace ya baka gefenshi ka zauna a gidan tare da matarka har Allah ya hore maka kayi naka.” “Amma kuma bai yi shawara dani ba ina matsayin namiji sai ke yake fad’awa hakan?” “Tun bayan magriba suke gidan nan, yana son maganan da kai amma baka nan wayarka ma bata shiga, shiyasa suka zauna zaman jiranka.” K’arshe dai haka suka fito daga d’akin Mas’ud na k’unshe dariyarsa domin hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, kuma ya samu abun tsokanan Haydar kenan. “Haydar kar kayi kuka fa, kasan rabo da iyaye akwai zafi, amma kullum zaka dinga zuwa kana ganinta ai. Ko Ammi?” Ammi ta shafa kanshi tamkar k’aramin yaro tace, “Kwarai kuwa. Ai bamu yi nisa ba.” Haydar ya rufe idanunsa na sakanni goma yana danne 6acin ransa domin yasan da gayya Mas’ud ke mishi haka. Tun kafin suyi bankwana da Ammi ya figi jakarsa yayi waje yana cewa, “Sai da safe Ammi.” “To ka tsaya kuyi bankwana da kyau mana, ko baka son a ga kukan da kake yi ne?” Fad’in Mas’ud yana zura takalmansa yana kecewa da dariya. Ammi da har lokacin bata gane gayya ake yiwa d’anta ba jikinta yayi sanyi tace, “Kuka yake yi ko? Allah sarki Ali.” “Babu komai zamu rarrasheshi. Ai kamar kunya yake ji ma.” Haydar da yake waje duk yaji maganganunsu ya cije le6e cikin takaici. Har waje Ammi ta biyosu ta musu bankwana kana ta koma gidanta ta rufe cike da kewan d’anta tilo data fi so a duniya. A hanya Mas’ud ne ke tsokanan Haydar amma ko kad’an bai nuna yasan yana yi ba, k’arshe wayarsa ya d’auka ya fara danne-danne gudun kar ya mayar masa da martani domin bai mance halaccin daya masa yau ba na bashi auren Laila. A Pharmacy d’insu suka yi parking suka fito Haydar na mamakin me ya kawosu gurin. Sai da suka shiga Mas’ud ya sallami duk masu aikin gurin akan sai gobe su zo su bud’e shagon. Shagon ya rage daga Mas’ud, Hamidu da Haydar wanda tun shigowarsu ya samu guri ya zauna. “Angon Laila.” Mas’ud ya kirashi cikin tsokana yana zama kusa dashi da syringe a hannunsa. “Mallam me zaka yi da wannan d’in?” Haydar ya tambayeshi yana matsar da fuskarsa baya. “Zamu gwada jininka ne ko kana da STDs, bazan kaiwa Laila kai haka ba tare da an maka gwaji ba. Domin kafin a d’aura auren ma an buk’aci ganin takardunka na asibiti nace duk na sani.” “I’m clean man, bani da ko malaria balle HIV.” “Bani hannunka domin bazai d’auki minti goma ba.” Haydar ya mik’a hannunshi ba tare da tsoro ba aka ja jininshi. Minti sha biyar da haka Mas’ud ya fito daga d’an k’aramin Lab d’insu dake cikin shagon yana cewa, “You are clean.” Daga nan shagon aski suka wuce, shi dai Haydar na kallon ikon Allah yana kuma binsu ne kawai. A can aka masa aski da gyaran fuska wanda Mas’ud yaso a kwashe sajenshi Haydar yace in aka cire masa shima sai ya cire na Mas’ud. Da dariya suka fito daga gurin tamkar wasu abokai kana suka wuce gurin sayan kazar Amarci. “In ba don kai ba da yanzu na jima a d’akin matata wallahi.” Fad’in Mas’ud yana biya musu kud’in kajin da drinks d’in da suka sayo. Bayan sun dawo cikin mota ne Hamidu ya mik’awa Mas’ud wani kullin magani a takarda yace, “Goga kar ka manta da ita fa.” Mas’ud yayi saurin k’ar6a ya barbad’a a bakinsa ya shanye haka ba tare da yasha ruwa ba. Haydar ya kallesu cikin rashin yarda yace, “Wannan d’in menene?” “Maganin zaman lafiya ake bawa angwaye a daren farko. Ko zaka sha?” Hamidu ya mik’a mishi wata takardar Haydar ya girgiza kai yace, “Nagode.” “Ka bada maza wallahi, tsoro kake ji?” Fad’in Mas’ud yana k’ara barbad’a wani garin a bakinshi. Jin wannan kalma ta ‘tsoro’ da ya tsana yasa ya wafci uku daga hannun Hamidu ya had’iyesu duk a lokaci d’aya suka dubeshi suna zare ido. “D’aya ko biyu ake sha ba uku ba.” Fad’in Hamidu cikin kad’uwa yana maida sauran cikin aljihunsa. “I challenge you Mas’ud ka k’ara d’aya in ba tsoro kake yi ba.” Haydar yayi challenging Mas’ud. D’an zaro ido kad’an yayi ya dubi Hamidu wanda yayi saurin girgiza masa kai tare da masa alamar yanke kai, kana ya kalli Haydar yace, “You won.” Haydar yayi dariya yana jin kanshi suka cigaba da hira irin tasu ta maza. Sai da suka iso gidan Laila sannan ya dawo hayyacinshi ya fara tunanin yaya Laila zata kar6eshi da auren nasu gabad’aya. Hamidu da dama shi yake driving aka barshi a mota, Mas’ud kuma ya rako Haydar har cikin falon Laila ya zauna. Mas’ud ya shiga part d’inshi na daa ya kulle kana ya dawo ya kulle d’akin Sabrin dana Abul ya jefa keys d’in a aljihunsa ya shiga d’akin Laila. A bakin gado ya sameta rik’e da waya tana danne-danne. Ganin Mas’ud da tayi yasa ta ajiye wayar a gefe da k’ak’alo murmushi tace, “Ango me kake yi a nan? Na d’auka tuni ka shiga gidanka.” “Na kawo miki naki Angon ne tunda na lura kunya kike yi baki tambayeshi ba.” “No karka mini haka, kace mini wasa kake yi.” Ta fad’i hakan tana dafe k’irjinta. “Yana can falo. Sai da safe don bacci nake ji sosai.” Ya fad’i hakan yana gyara garenshi kana yayi saurin fita daga d’akin. Haydar ne ya rakashi har bakin mota kana Mas’ud ya lek’o ta window yace, “Abunda kasha d’in nan yayi maka yawa, ka tabbata ka rage zafi idan ba haka ba wallahi gobe zaka kasa fitowa cikin jama’a, kaji na rantse maka.” Yana fad’in hakan Hamidu yaja motar suka fita daga gidan suna kyakyatawa da dariya. Haydar da sai a lokacin ya gane me yasha yayi saurin dafe kanshi cikin dana sani. Yafi minti biyar tsaye a gurin yana tunanin me zai yi amma kwata-kwata hankalinshi bai bashi idea d’aya kwakkwara ba. K’arshe juyawa yayi ya koma cikin falon ya samu Laila zaune a kan kujera ta dafe kanta hawaye na tsiyaya a idanunta. Mum Fateey 👌 RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300. (23) Ko da Haydar ya shigo ya samu Laila tana hawaye tsayawa yayi daga bakin k’ofa yana kallonta domin bai san dalilin kukanta ba. Zuciyarsa ce ta karaya na wannan hali da suka tsinci kansu a ciki. Laila ta d’ago ta dubeshi tana share hawayen fuskarta tace, “Dama tun farko burinka kenan ka auri babbar mace?” “Ban gane ba.” Ya iso cikin falon ya zauna a gefenta cikin d’aurewar kai. “Duba nan.” Ta mik’a mishi wayarta ya kar6a ya fara karantawa. A shekarar daya gabata ne wato 2019 a shafin Twitter wata babbar mata ta auri saurayi k’asa da shekarunta mutane suke ta kushewa, wasu sun maida hakan abun dariya wasu kuma suna ganin hakan bai dace ba, a cewarsu yafi kamata mace ta auri namijin daya fita a shekaru saboda wasu dalilansu. A cikin wannan muhawaran ne Haydar shima ya tsoma baki yake cewa, ‘Ni banga abun kushewa a nan ba, shi yaga mata yace yana so kuma ya aureta. Kowanne mutum da ra’ayinsa, bro Allah ya baku zaman lafiya.’ A k’asa abokinsa Nasir ke cewa, ‘Kai kam dama tun farko kafi son matan da suka girmeka. Ko In tayaka neman sugar mummy ne ta riritaka Alhaji?’ Haydar yace, ‘I hope to find one.. bana son yara ne kawai, I dislike their inexperience and lack of understanding of life. Sai ya zama kamar kana raising yaro ne ana ta maka shirme a gida.’ A nan hirar ya k’are ya ajiye mata wayan a gefenta. “Yes burina kenan saboda bana son yarinta ko kad’an. ” Ya bata amsa yana kallon cikin idanunta domin ta yarda dashi. “Kenan tun farkon had’uwarmu k’udurinka kenan?” Girgiza kai yayi yace, “Ganinki na farko da nayi nasan kin fi k’arfina kuma ban kawo hakan a raina ba ko kad’an. A zaman da muka yi tare ne na fad’a sonki ba tare da nayi shawara da zuciyata ba.” Shiru suka yi na wasu sakanni sannan tace, “Ka duba sauran links d’in da aka turo mini ka shiga kaga abunda aka fad’a a kanmu.” Haydar ya d’auki wayar ya duba yaga har yayi locking kansa, “Me password d’in?” Ya tambayeta. Daburcewa tayi na ‘yan sakanni kamar mara gaskiya tace, “Aliyu. Wani Aliyu? Shine bai sani ba kuma bashi da niyyar tambayanta domin bashi bane a gabansu ba. Yana bud’e wayar ya shiga text messages d’inta ya duba links d’in da aka turo yabi d’aya bayan d’aya yana karanta mummunan sharrin da aka musu, ana had’awa tare da hotunansu da aka d’auka a kwanakin baya wanda take bashi labari. Yana karantawa ransa na 6aci zuciyarsa na k’una tamkar zata fashe saboda k’azafin zina da aka musu tare da sharri kala-kala. ‘Gulma da d’umi-d’uminta. Wannan shine Aliyu Haydar matashi d’an shekara ashirin da biyar da aka kamashi turmi da ta6arya tare da Hajiya Laila mai shekara arba’in kuma mai zaman kanta. Sakamakon kamasu da aka yi ne Alhaji Abdul CEO Lu’a Ventures ya fasa aurenta bayan ya samu labarin cewa tana can tare da Haydar a wani Hotel da sunan sun je yiwa juna bankwana, kenan ba yau suka fara aikata alfasha ba. Saboda gudun tonon asiri yasa kaninta da yayanta suka d’aura mata aure da yaron ba tare da saninta ba. “Waya juya zancen nan haka Haydar? Wa yake son 6ata mini suna ne? Me na yiwa mutane?” Tayi tambayar idanunta na tara wasu hawayen tana jin bak’in ciki mara misaltuwa. “Yanzu kowa yaga wannan abun, abokan kasuwancina, ‘yan uwana har da surkina da yake ganin girmana yanzu shima zai fara wasiwasi a kaina. Wallahi ban ta6a zina ba, ban ta6a yinta ba Haydar.” Haydar kwantar da kanshi yayi saman kujera ya runtse idanunshi yana maimaita sharrin da aka musu tare da maganganun mutane, wanda wasu sun yarda da hakan har suna tsine musu wasu kuma fatan shiriya kawai suka musu. Ya za’ayi ya goge wannan abun daya faru ya zama tamkar ba’a ta6a yi ba? Yasan za’a soki aurensu tunda yana ganin irin hakan a social media sau da yawa, amma bai ta6a kawowa a ransa za’a jefesu da k’azafin zina ba. D’ago da kanshi yayi yaga ta d’auki wayar tana cigaba da karanta sak’onnin mutanen yayi saurin kar6ar wayar ya ajiyeta a gefe. Hakan da yayi yasa hankalinta ya dawo kanshi tana kallonshi cikin mamaki. Gyara zamanshi yayi ya dubeta cikin nitsuwa yace, “Laila.” Kamar baza ta amsa ba amma ganin yanda ya nitsu sai taga ya mata kwarjini ainun tamkar ba Haydar d’in da take yiwa kallon yaro ba. “Na’am.” Ta amsa tana kawar da idanunta gefe. “Tambayarki zanyi ina son ki bani amsoshinsu. Kin ji?” Gyad’a mishi kai tayi yace, “Good. Shin a cikin duniyan nan akwai wanda ba’a ta6a zaginshi ba?” “Babu.” “Shin a cikin mutanen da kika sani kike tare dasu kuke harkokin yau da kullum zaki iya bugan k’irji kice dukkansu sonki suke yi na gaskiya?” “A’a.” Ta fad’i hakan a sanyaye tana jiran taji ina maganarshi ta dosa. “Shin d’an Adam yana iya kaucewa k’addararshi ko kuma ya rayu ba tare da Allah ya jarabceshi ba?” Wanna karon girgiza kai tayi tana jin wani nauyi da yake kanta na raguwa, domin ita take yiwa mutane tuni da hakan amma yau gashi ita ake yiwa tuni. “Shin kin ta6a aikata abunda ake zarginki a kai?” “Ban ta6a ba.” “Kenan bai kamata ki damu har kiyi kuka da idanunki don wani bawa yaga daman miki sharri ba. Kowanne mutum da kika gani a duniya yana tafiya ne da tashi jarabawar, sannan komin mulkin mutum, iliminsa, kyawunsa, arzikinsa ko sa6aninsu ba zai ta6a kaucewa maganan mutane ba sai an samu wanda zasu zageshi, koda kuwa tunda yazo duniya bai ta6a aikata laifi ba. Kiyi duba ga Annabi Muhammad SAW masoyin Allah, wanda aka yi duniya dominsa amma a hakan wasu suna zaginsa suna binshi da sharri, har aka samu masu iya jifanshi da duwatsu. Ki fad’a mini idan har shi aka iya mishi haka mu kuma su waye da zamu kaucewa hakan? A tunaninki Allah ba zai kwato mana hakkinmu bane a kan sharrin da aka mana? Ko kuma gaskiya ba zata fito ba duk daren dad’ewa?” Ya kamo hannunta wanda yau ne karon farko da ya fara yin hakan a rayuwarsa. Wannan lokacin kallonshi take yi cikin yadda da maganganunsa ba tare da ta mance ko kalma d’aya ba. “A hakan Laila ba’a rasa wanda suka k’aryata sharrin da aka mana ba suka fad’i gaskiya ba, kamar yanda na wancan mutanen ya wuce har aka daina maganarsu muma watarana haka za’a daina yayin maganarmu kuma zai zama tamkar ba’a yi ba. Mutanen social media haka suka zama, kowa ya 6uya a bayan keyboard ne yana fad’in k’arya da gaskiya don kawai ya jawo hankalin mutane kanshi, ko kuma don wata manufa tashi ta daban. Abunda zakiyi ki karya guiwar masu yin hakan shine ki nuna hakan bai dameki ba, ki nuna musu kin fi k’arfin su fad’i k’arya a kanki har yayi affecting rayuwarki. Ke ba yarinya bace Laila, kina da experience na rayuwa sosai, kiyi amfani da hakan sannan ki barwa Allah komai, shi zai tona asirin duk mai yin hakan. Kina jina?” Gyad’a mishi kai tayi tana zare hannunta daga nashi kana ta share sauran hawayen dake fuskarta tana jin k’arfi a jikinta da kuma cikin zuciyarta gabad’aya. “Nagode.” Kawai ta iya furtawa tana matsawa kad’an daga gurinshi. Hakan da tayi bai mishi dad’i ba domin ya lura kamar bata son ya ta6ata ne. Ko dai ta manta shi mijinta ne a yanzu? “Waya turo miki links d’in?” Ya tambayeta yana maida kanshi jikin kujeran domin yaji alamar maganin da yasha ya fara aiki. “Ban san waye bane kuma bani da numbern. Ina gwada kiran layin Abul naga an turo mini message d’in, ni bana ma Twitter amma nabi ta link d’in nayi downloading.” Haydar gyara zamanshi yayi ya k’ara d’aukan wayar ya shiga True caller ya duba sunan mai numbern yaga suna ne wanda bai gane ba, koda ya nuna mata itama cewa tayi bata san me sunan ba. “Ki basu kwana biyu zasu yi su gaji su daina. Zan bincika duk wanda yayi hakan domin d’aukan pictures d’inmu da ake yi har ana editing bai mini ba.” “Ka bari kawai ba sai ka bincika ba, koma waye ne ya yiwa kanshi.” Tayi saurin katseshi domin bata son yaje ya bincika ya gane Abul ne yake mata haka ko kuma Madu. Ina zata kai wannan kayan kunyan ace duk wannan bak’in cikin na jikinta ne ya aikata musu haka? Haydar da baya ganewa jikinsa ya tashi tsaye yana bata baya yace, “Ina band’aki? Zan yi wanka.” Laila ta mik’e tsaye tana cewa, “Sorry, muje.” Tayi hanyar side d’in Mas’ud amma tana k’ok’arin bud’ewa taji k’ofar a gark’ame. Ta k’ara jijjiga k’ofar ta gane key aka saka aka kulle. To waye ya kulle? Shi kuma Haydar bai zauna ba illa ma kawar da kanshi da yayi ga barin kallonta, saboda kallonta kad’ai na k’ara jawo masa matsala. D’akin Abul da Sabrin duk ta gwada bud’ewa amma a rufe, a nan ta tabbatar wannan aikin Mas’ud ne. Me yake nufi da hakan? Shin bai san halin da suke ciki bane da zai yi tunanin had’asu a d’aki d’aya? Wayarta ta d’auko tayi dialing numbernshi amma a kashe. Extra keys d’in d’akunansu kaf a side d’in Mas’ud d’in ake ajiyewa incase wani ya jefar da nashi. Ya zata yi? Haydar ta har lokacin yana tsaye ya kasa gaba ko baya yace, “Lafiya?” “Muje d’akina, sauran d’akunan a kulle suke.” Da haka tayi gaba yabi bayanta da kallo yana jin tamkar ya fasa ihu. Mas’ud da Hamidu kuma tun d’azu yake tunanin me zai musu ya rama abunda suka mishi idan sun had’u gaba saboda sun cuceshi. Sai da ya tabbatar ta shiga d’akin sannan ya bi bayanta yana doro tamkar mai ciwon baya. Yana shiga ya samu ta kwaso wasu kayanta a cikin band’akin ta jefasu a ciki wardrobe d’inta da sauri. Halin da yake ciki yasa bai ma lura da yanayin d’akin nata ba ya tasamma cikin band’akin ba tare da ya bari ta kalleshi da kyau ba. Yana shiga ya fara kwa6e kayan jikinshi kana ya sakarwa kanshi ruwan sanyi na minti biyu kafin nan yayi wanka. Ya jima tsaye ruwa na dukanshi sannan ya kashe shower ya nemi towel ya d’aura a k’ugunshi kana ya fito. A cikin d’akin ya samu Laila ta kawo mishi jakarshi har ta shimfid’a k’aton bargo a k’asa ta ajiye pillow a kai. Tashin da zata yi ta hangoshi a bakin band’aki ya hard’e hannayensa a saman k’irjinsa yana mata kallon ‘me kike nufi’? Zuciyarta ce ta buga da k’arfi ta nemi nitsuwarta ta rasa domin ba k’aramin kyau da kwarjini ya mata. Da sauri ta fita falo ta bashi guri domin ya kimtsa, a can falon kuma wayarta ta d’auka ta gwada kiran Abul amma bai shiga ba wanda dama hakan ta san zai faru. Sai da ta tabbatar Haydar ya gama abunda zai yi sannan ta shiga d’akin da sallamarta ya amsa, zaune yake a kan kujeran dressing mirror yana sanye da jallabiya fara sol wacce tayi masa kyau ba kad’an ba a idanunta. Wai me yake damunta ne? Ta yiwa kanta tambayar tana kawar da kanta gefe ta bud’e wardrobe tana d’auko kayan baccin da zata saka. “Kinyi regretting aurena?” A bazata ta jiyo tambayar wanda yasa tayi saurin juyowa tana kallonshi a razane. Tashi yayi ya tako har gurinta kana ya tsaya a gabanta ya k’ara cewa, “Kinyi regretting aurena? Zaki iya za6ana a karo na biyu a rayuwarki?” “Haydar...” Zata fara magana ya katseta. “Just answer me. Ina son sanin matsayina ne a gurinki domin na lura tamkar ba aure kika d’auki aurenmu ba. Kamar an miki dole ne alhali ke da kanki kika yi choosing d’ina.” “Bana dana sanin saninka ko aurenka Haydar, but halin da nake ciki a yanzu ina buk’atar space domin abubuwan da suka faru a yau sun yi mini nauyi a zuciyata. Ka daina tunanin hakan a zuciyarka.” Ta k’arishe maganan tana ra6ewa ta gefenshi zata wuce ya kamo hannunta. “Kenan kina sona?” Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta. “Daa bana sonka da bazan amince in aureka ba.” “Then say it.” Ya k’ara k’arfin rik’on daya mata. Laila tabi hannunsu da kallo yanayinta na canjawa, damuwarta na barin zuciyarta ta d’ago ido tace, “Yes, I’m in love with you. Shikenan?” Haydar dawo da ita yayi gabansa murmushi na su6ucewa a bakinsa a karon farko tun da ya shigo gidan amaryar tasa. “I’m in love with you too.” Ya fad’i hakan yana had’e goshinsu guri guda yana lumshe idanunsa tamkar mai jin baccin. “Haydar.” Ta kira sunanshi cikin kwa6a amma a hankali jin ya sumbaci kunnenta tare da wuyanta. “Shshh.” Yayi shushing d’inta yana jawota jikinshi yayi hugging d’inta tsamm tamkar za’a kwace mishi ita. Laila bata kwace jikinta ba domin tasan yana buk’atar ko sau d’aya ne ya gane cewa da gaske ya aureta ba mafarki yake yi ba. Ganin labarin na neman canja salo yasa tayi saurin barin jikinshi ta shige band’aki jikinta na rawa, duk inda ya kai hannunsa a jikinta sai da tabi ta ta6a tana jin zuciyarta na tsananta bugawa, wai yau ita ce d’aki d’aya da Haydar a matsayin mijinta? Kenan mafarkan da tayi kwanaki zasu iya zama gaskiya? Ta jima a cikin band’akin sannan tayi wanka ta saka silk nighty d’inta ta fito. Turaren humra da bata rabo da sawa ta shafawa jikinta sannan ta fita falo zuwa gurin Haydar jin yayi kiranta. Wai da gaske ta zama matar Haydar? A kan sallaya ta sameshi kamar wanda ya idar da sallah yace, “Kiyi alwala muyi sallah.” D’an k’aramin murmushi tayi tana mamakin k’arfin halinshi, haka ta koma d’aki ta d’auko hijabinta tare da sallaya suka yi sallah, a ranta kuma so take ta bashi wannan daman da zai ji ‘eh shima Ango ne ko da kuwa wani abun ba zai shiga tsakaninsu ba. Bayan sun idar ya juyo ya mata addu’o’i ida dai kanta a k’asa, tama rasa me take feeling a lokacin a cikin kunya ko jindad’in auren wanda take so a karo na biyu. Bayan ya gama addu’o’in ya jawo ledar daya shigo da ita ya bud’e musu yana cewa, “Naji ance yau wuni kika yi baki ci abinci ba.” “Bana jin cin komai ne.” Ta bashi amsa tana yamutsa fuska. Hakan da tayi kuwa kyau ta masa ba kad’an ba, murmushi yayi mai k’ayatarwa yace, “So cute.” Dariya sosai Laila tayi shi kuma ya tallafe ha6arshi yana kallonta tamkar ta zama tv yana jin dad’i a ransa daya iya kore mata damuwarta har gashi tana dariya. Ganin ya k’ura mata ido ne yasa Laila ta tsagaita dariyar tace, “Kana da abun dariya.” “Don nace kinyi kyau?” “Haydar.” Ta kwa6eshi a karo na ba adadi. “Naga alama sunan yana miki dad’i.” Ya fad’i hakan cikin zolaya. Murmushi tayi tana tuno maganganun Ummii wanda su suke k’ara nitsar da ita akan aurenta da Haydar Idan ta tuna. Minti kad’an da haka suka rufe kazar Laila ta d’auka tayi kitchen da ita shima Haydar yabi bayanta. A can ya wanke bakinsa tace, “A nan kayi alwala ko?” “Yes. Na lek’a d’akin na samu kina ta shafe-shafe sai na fito.” Ya bata amsa yana kashe wutan kitchen d’in suka fito. Juyowa Laila tayi tana zaro idanunta, shi kuma gaba yayi ya barta a gurin yana murmushin mugunta. “Kace mini wasa kake yi.” “Ni da matata. Menene a ciki?” Ya shige d’aki ya barta a gurin baki a bud’e. Sai data kashe wutan falon sannan ta shiga d’akin ta sameshi a kan shinfid’arsa yana danna wayarsa yana murmushi. Wani irin kishi ne ya tsaya mata a makwogoro da tayi tunanin ko da wata mace yake chatting. Rai a 6ace tazo ta wuceshi ta hau kan gadonta tare da kashe wutan d’akin gaba d’aya tana jin d’aci a harshenta. “Laila.” Ya kira sunanta cikin duhu. “Na’am.” “Nifa ban saba kwana a k’asa ba.” Ya fad’i hakan yana tashi tsaye ya hau kan gadon tare da jawota jikinshi. A tare suka yi ajiyar zuciya kana ta fara k’ok’arin barin jikinshi ya tsayar da ita yace, “Just in jiki a jikina nake so and nothing more.” Mum Fateey 👌 RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (24) Bayan Haydar ya hau gadon Laila ta lura da halin da yake ciki amma tayi kamar bata gane ba. Lokaci-lokaci yana tura kanshi jikinta numfashinsa na fita cikin sauri-sauri, ta taga abun ya fara canja mata yanayi ta matsa daga jikinshi ta koma can gefe tana cewa, “Munyi magana akan hakan, I need space.” “I’m sorry.” Ya juya mata baya amma minti kad’an da haka taji ya fara juye-juye ya kasa bacci. Ita kanta babu baccin a idanunta amma why not yayi hak’uri har zuwa lokacin da taga hakan ya dace? Tun k’arfe sha biyu yake juye-juyensa har biyun dare bai daina ba, ita kuma gyangyad’i take yi tana farkawa saboda motsinshi na hanata bacci. “Laila.” Ya kira sunanta cikin wata murya abun tausayi. “Umm.” Ta amsa ba

Chapter 2 of 32