mai rad’a.
“Kin k’i bani dama ne amma da tuni na nuna miki k’ok’arina.”
Tuni jikin Laila ya d’auki sak’onshi ta lumshe idanunta kana ta bud’esu taga ya koma baya yana mata murmushin cin nasara, kana lokaci d’aya fuskarsa ta zama so serious ya d’auki spoon ya d’ebi abincin yace,
“Oya bud’e bakinki in baki abinci, idan kuma kinyi gardama in d’auko bulala kuma da gaske nake ina zane marasa jin magana. Haaa.”
Ba k’aramin dariya hakan ya bata ba ta toshe bakinta har kwalla na taruwa a idanunta. Abunda yafi bata dariya shine yanda ya tamke fuska tamkar da gasken zaneta zai yi.
“You are funny.”
Sake fuskarsa yayi shima yana murmusawa ya k’ara mik’a spoon d’in bakinta yace,
“Yanayin adadin spoon d’in da kika yi yanayin adadin nawa. Idan kin tsaya nima zan tsaya. Bud’e bakinki.”
Ba musu ta bud’e bakinta ya saka mata abincin tabi da hannunta ta saka sauran tana son yin dariya.
“Baka iya bawa mutum abinci ba.” Ta fad’i hakan bayan ta had’iye na bakinta.
Loma ya kai bakinsa yace,
“Ki barni in koyi komai a kanki.” Ya k’ara mik’a mata wani spoon d’in ta kawar da kanta gefe domin maganarsa ta k’ara hargitsa mata lissafi. Shin yasan halin da yake sakata kuwa? Komai ya fito daga bakinsa sai ta masa fassara, fassaran ma dirty one.
“Mun k’oshi ne?” Ya tambayeta yana lek’en fuskarta a ransa kuma farin ciki yake yi domin plan d’insa na tafiya yanda yake so.
Dolenta haka ta k’ar6i abincin suna ci tare, har sai data k’oshi ta shafa tumbinta tace,
“Don Allah haka ya isa.”
“Nima na k’oshi.” Ya fad’i hakan yana ajiye spoon d’in.
“Better.” Ta fad’i hakan tana mik’ewa tsaye.
“In fad’a miki wani abu?” Ya dawo da ita ta zauna tana kallon cikin idanunshi.
Kad’a kai tayi yace,
“Kin iya girki sosai. Thank you.”
Wani dad’i ne ya lullu6eta ta k’ara mik’ewa tana tattara kwanukan tace,
“Welcome.”
Da haka ta d’auki used plates d’in shi kuma ya d’auki kulolin ya bita kitchen dasu.
A can ya samu ta bud’e ledojin daya dawo dasu tana ajiye komai inda ya dace fuskarta d’auke da annuri.
“Kamar kasan sune abubuwan da bamu dasu a gida. Allah ya k’ara bud’i.”
“Ameen.” Ya amsa yana bin bayanta da kallo.
“Ohh dama baka manta da Agwalumana ba? Thank you.” Ta ajiyesu a gefe ta cigaba da adana sauran kayan abincin.
Sai data gama ta juyo tana kallonshi taga kanshi a k’asa. Girgiza kai tayi kana ta sunkuya ta bud’e drawer ta d’auki cup da spoon.
D’agowan da zatayi ta jishi a bayanta ya zagaye hannunsa kan tumbinta yana tura kanshi cikin wuyanta.
“Haydar.”
“Just a moment.”
Seconds goma da haka ya saketa da sauri ya fita daga kitchen d’in. Itama halin daya shigan ne take ciki, jikinta a sanyaye ta fara 6are agwaluman tana sakawa a cikin kofi. Sai data gama ta zuba sugar kad’an ta dama sannan ta fita falo ta sameshi yana kallo.
“Zaka sha?” Ta fad’i hakan tana zama a kujera mai kallon nashi.
“Mutum sai rowa. Sha kayanki.” Ya fad’i hakan yana mik’ar da k’afafunshi kan 3 sitter.
Murmusawa tayi kana ta fara shan abunta tana lumshe ido. Binta yayi da kallo kana yace,
“Zo kiji.”
D’an zaro idanunta tayi tace,
“What?”
“Zan nuna miki wani abu ne.”
Girgiza kai tayi tace,
“Bana so.”
Zai bud’e baki yayi magana aka kwankwasa k’ofar falon tare da turowa aka shigo.
Sabrin ce idanunta jawur tare da mijinta Salman yana rik’e mata da jakanta.
Ganin Haydar ba riga yasa tayi saurin juyawa shi kuma ya tashi ya shiga d’akinsu ya saka jallabiya ya fito.
Yana dawowa falo ya samu Sabrin a jikin Laila tana kuka, ita kuma tana buga bayanta tana cewa tayi shiru.
“Lafiya?” Ya tambayesu cikin d’aurewar kai.
Salman ne ya mik’a mishi hannu suka gaisa cikin mutunci sannan suka maida hankalinsu kan mata biyun.
“Mama kiyi hak’uri ki yafe mini.”
“Nace ya isa haka na yafe miki duniya da lahira Sabrin. Ki daina kukan nan haka, tashi ki share hawayenki.”
Da haka ta mik’ar da ita zaune Salman yayi saurin mik’a mata handky ta kar6a tana goge fuskarta.
Yarensu na shuwa Sabrin ta fara yi Laila na girgiza kanta.
“Ya wuce, kinji?”
Ta kad’a kanta tana goge hancinta kana ta dubi Haydar wanda shima su yake kallo tace,
“Ina wuni.”
Zai iya rantsewa Wannan shine karon farko da magana mai dad’i ya ta6a shiga tsakaninsa da Sabrin. Murmusawa yayi yace,
“Lafiya kalau, Hamdallah. Kuna lafiya?”
“Lafiya kalau.”
Da haka kowa yayi shiru a d’akin kana Haydar ya mik’e yace,
“Zan fita.”
Laila zata tashi ya dakatar da ita yace,
“No, kiyi zamanki.”
“A dawo lafiya.” Tace dashi kana ta maida dubanta kan Sabrin wacce ke son yin magana tun d’azu.
“Amm Uncle Haydar kayi hak’uri kan abubuwan da nayi maka a baya.” Ta fad’i hakan tana sunkuyar da kanta k’asa.
“Babu komai Sabrin.”
Da haka ya fita daga falon Salman ya bishi a baya ya tsayar dashi suka fuskanci juna.
“Sunana Salman, thou nasan ka ganeni. What I want to say is; I’m not against your marriage illa ma murna da nake yi da yasa Mama tayi aure. Mutumiyar kirki ce bata aikata abunda ake zarginta dashi. Sai dai yau dana duba naga an cire hotunanku da duk wani batu da akayi a akanku.”
Ba k’aramin dad’i hakan yayiwa Haydar ba, domin saboda gudun 6acin rai yasa ya daina shiga duk wata social media da yake yi.
“Kun gani kenan?”
“Yes.” Ya bashi amsa yana kad’a kai.
Haydar ya mik’a mishi hannu yana cewa,
“Mun gode.”
“Anything for Mama.”
Da haka suka yi sallama Salman ya shiga motarshi ya tafi shi kuma Haydar ya isa bakin titi ya tari achaba ya nufi gurin abokinsa kwalli d’aya tak, wato Nasir.
Bayan fitan mazan ne Sabrin ta k’ara kwaye fuska tace,
“Mama ki gafarceni don girman Allah kar Allah ya kamani da laifin saka mahaifiyata kuka.” Ta fad’i hakan wasu hawayen na taruwa a idanunta.
“Na fad’a miki na yafe miki Sabrin. What change your mind cikin k’ank’anin lokaci haka? Na d’auka ai kin rabu dani ne.”
Share hawayen fuskarta tayi kana tace,
“Har duniya ta nad’e bazan ta6a samun wanda zai soni kamarki ba Mama, kuma bazan ta6a canjaki ba. D’azu Uncle Mas’ud yaje gidana ya bani labarin da ban sani ba game dake, dama uwa tana iya sacrificing farin cikin rayuwarta don ‘yayanta? Ashe haka kika wahala damu har muka kawo wannan lokacin Mama? Wallahi bamu miki adalci ba da muka kasa baki goyan baya akan abu guda da kika nuna kina so ba. Ki yafe mana don Allah.”
Shiru Laila tayi domin itama hawayen ne a idanunta ba tare data bari sun zuba ba, can tace,
“Kina da labarin Abul?”
Gyad’a kai Sabrin tayi kana tace,
“Yana can gidan abokinsa Micheal, munyi waya dashi yace kar na bawa kowa numbernshi. Kar ki tayar da hankalinki Mama, yana nan lafiya kuma monday zai je school.”
Laila ta godewa Allah a zuciyarta tana jin sanyi a ranta. Kenan Abul d’inta yana nan cikin k’oshin lafiya ba tare da yaje ya yiwa kanshi illa ba.
Da haka suka cigaba da hiran tsakanin uwa da d’anta cikin farin ciki, domin kaso sittin na damuwar Laila ya kau babu shi. Burinta da fatanta har gobe bai wuce ace ‘yayanta na jikinta tana ganinsu ba.
Sai bayan isha Salman yazo ya d’auki matarsa suka tafi. A nan Laila ta samu kanta ta fara tunanin ina Haydar ya shiga.
Wayarshi ta kira ya d’auka yana cewa,
“Matar Haydar.”
Murmushi tayi ta zauna tace,
“Ina ka shiga?”
“Kina tsoron a sace miki ni ne?”
Wani murmusawan ta sake yi wato yasan duk yanda zai yi ya sakata nishad’i.
“Ka dawo gida.” Tace dashi kana suka yi sallama.
Bayan ya dawo sun ci abinci take bashi labarin abunda ya faru, yanda yaga take farinciki da sanin inda Abul yake ya tabbatar ba k’aramin so take yiwa ‘yayanta ba kamar yanda Mas’ud ya bashu labari.
Suna cikin hiran Mas’ud yayi sallama ya shigo da Naana wacce ke kumbure-kumbure kamar bata son zuwan.
“Amaryar ka d’auko ka kawo? Baza ka bari gobe inje gidan naku ba?” Laila ta fad’a cikin mamaki.
Domin d’azu ta rana ya shigo take Fad’a mishi cewa gobe zata je taga gidansa da amaryarsa yace to. A nan take tambayarshi key d’in sashensa yace bai san a ina ya ajiye ba.
“Na kawo miki ita ki ganta ne domin baku ta6a had’uwa ba.” Ya fad’i hakan yana zama kusa da Naana.
Da haka suka gaggaisa ita dai Naana fuskarta sam babu fara’a, ko da Laila ta lura da hakan sai ta raya a ranta cewa ko dai jikin ne irin nasu na Amare, domin kuwa yarinya ce wacce bazata wuce shekara ashirin zuwa ashirin da biyu ba.
Haydar da Mas’ud hiransu suke yi akan wata sabuwar cuta data 6ullo wai Corona Virus wacce a kanta har gwamnatin Nigeria na cewa zata rufe makarantu, kasuwanni da duk wata ma’aikata.
“Ni ban yarda da wannan cutar ba.” Fad’in Mas’ud kenan in conclusion.
Laila k’ok’ari take yi taja Naana da tad’i amma sai ta nok’e tak’i ta sake da ita.
Basu jima ba Mas’ud ya tashi wai zasu tafi.
“Don Allah Mas’ud gobe ka zauna a gidanka karka dawo nan. Yau sawunka uku gidan nan.” Fad’in Laila cikin fad’a.
“Zan dawo sai dai karki bud’e mini k’ofa.” Yana fad’in hakan yaja hannun matarsa suka fita yana dariya.
Laila har bakin k’ofa ta musu rakiya kana ta koma ciki.
Su kuma suna shiga mota Naana ta 6ata ranta sosai tana kumburi. Ko da Mas’ud ya lura da hakan yace,
“Yaya dai Amarsu?”
Bata kulashi ba har suka iso gida yana cakalarta da tsokana sai basarwa take yi. Tana fita daga motar shima ya fito yayi saurin isa gurinta yana jawota jikinshi.
Da k’arfi ta fisge jikinta tana cewa,
“Don Allah ka barni.”
Daya lura da gaske take sai ya saketa suka shiga falonsu a haka, a nan ne ya nemi ta zauna zasu yi magana, taso ta mishi musu amma data dubi kwayar idanunshi sai taga shima babu wasan a fuskarsa.
“Mena miki Naana? Naga lafiya kalau muka fita amma tun muna can na lura kamar wani abu ya 6ata miki rai.”
“Jiya-jiya aka d’aura aurenmu amma yau sawunka uku gidan yayarka ka kasa zama a gidanka. A yanda kowacce amarya ke samun hankalin mijinta ni ban samu ba Mas’ud, da safe ka fita ka barni sai da kayi awa biyu kafin ka dawo, da rana ma haka ka fita ka barni kaje gurinta sai la’asar ka dawo gida. Yanzu kuma kazo ka tilasata mini akan sai mun je gidanta na gaisheta, nifa Amarya ce, kamata yayi ni za’a zo gidana ba wai ni in fara bin gidajen mutane ba. Na rasa meyasa gabad’aya hankalinka baya kaina.”
Shiru yayi yana tunani sannan can ya d’ago yace,
“Naji ban kyauta ba kiyi hak’uri amma na fad’a miki da safen karyawa naje d’auko mana.”
“Zaka iya yin order ba dole sai a gidanta ba.” Ta bashi amsa cikin hargowa.
Runtse idanunsa yayi na wasu sakanni kana ya bud’e yace,
“Bai kamata daga aurenmu har mun fara samun sa6ani ba Naana, sannan Kalti da kike magana da ita na tashi na rayu a matsayin abokiyata kuma yayata, gaskiya bazan ji dad’in tun daga farko ki fara nuna bakya sonta ba.” Yana fad’in hakan ya shige d’akinsa ya barta a nan cikin mamakin wai wani irin so mijinta yake yiwa yayarsa?
Bayan tafiyarsu Mas’ud Laila ta koma falo ta samu Haydar ta kira sunanshi ya juyo yana kallonta. Sai data zauna sannan tace,
“Dama d’azu ne Alhaji Abdul ya kirani muka yi magana.”
Yana jin ta ambaci sunan fuskarsa ta canja, shiru yayi bai ce komai ba. Ganin hakan yasa taci gaba da magana cikin sanyi.
“Ya fad’a mini ya kiraka yace ka koma bakin aikinka kace baka so, shine yace in fad’a maka cewa in ma jin nauyinshi kake yi ka daina ka koma bakin aikinka domin ya yarda da k’addara yasan ni ba matarsa bace.”
“Duk wannan maganan shi ya fad’a kuma kina saurarenshi? Kuma yaushe na fad’a mishi ina jin kunyarsa?” Ya tambayeta yana zuba mata ido amma ita kanta ta gane ranshi ya 6aci.
“To ya zan yi? Kar yace na wulak’antashi.”
“Bana son ki k’ara d’aukan wayarshi Laila.” Ya fad’i hakan gaba gad’i wanda yasa ta dubeshi da kyau ko wasa yake yi.
Ganin da gaske yake yi yasa itama taji ranta ya fara 6aci, yana nufin juyata kenan zai yi? Zai dinga k’afa mata sharud’d’a tana bi?
Data lura zasu iya yin fad’a sai ta tashi ta shige d’akinta ta rufe, kamar zai bita amma ya fasa yayi zamanshi a gurin yana kallo amma hankalinshi na kanta.
Sai da yayi awa d’aya zaune shi kad’ai sannan ya tashi ta rufe musu gidan ya kashe wutan falon ya shiga d’akin nasu.
A saman gadonta ya sameta ta kwanta jikinta sanye da farar doguwar riga ta bacci mai tsantsi, a yanda ya lura da ita tana son saka fararen kaya.
Shimfid’inshi ya gani a k’asa ya tsallakeshi ya isa bakin gadonta kana ya tu6e jallabiyarsa ya bar boxers kad’ai. Hawa gadon yayi a hankali ya kwanta kana ya jawota jikinshi yana cewa,
“Ni mijinki ne Laila, ina kishinki sosai yanda bakya tsammani. Karki manta tun kafin in aureki na bar aiki a gurin saboda ganinshi kad’ai zai iya saka mini hawan jini idan na tuna cewa ya sameki ni ban samu ba. Yanzu ma ko sunanshi bana son ana kira, so kiyi hak’uri ki daina d’aukan wayarshi, shi ba danginki bane balle ace ya zama dolenki, kamar yanda kika yanke huld’a da duk zawarawanki haka shima ya kamata ki yanke dashi. Kina jina?”
Kad’a mishi kai tayi bata ce komai ba. Sumbatar kanta yayi ya k’ara rungumeta yace,
“Yauwa Matata ta kaina. Nasan kina tayani kishin kanki.”
“Amma da sharad’i d’aya.” Ta fad’i hakan kai tsaye.
Gyaran murya yayi kana yace,
“Wani sharad’i kenan?”
Juyowa tayi ta fuskanceshi kana tace,
“Zaka koma gurin aikinka domin ka sameni Haydar shi kuma bai samu ba. A k’arshe idan ka koma aikin ma kai kayi winning bashi ba. Fargaban me zaka ji idan ka ganshi alhali kasan ka bar matarka a gidanka? Shine sharad’ina.”
Shiru yayi yana kallon sama tana jiran amsarshi. Ganin zai iya fand’arewa yasa ta d’aura hannunta kan sajen fuskarshi tana shafawa a hankali.
“Haydar look at me.”
Ya sauk’o da idanunsa yana kallonta amma ta gane ta fara samun kanshi.
Cigaba tayi ta isa har kunnenshi tana shafawa a hankali ta fara magana,
“Yanzu kai idan ka sake wannan aikin naka wanne zaka yi? Karka manta kai kake ciyar da Ammi, ga kuma nima na zama iyalinka. Wallahi tun farko bana sonshi, wannan karon ma pressure yasa na amince da aurensa har Allah ya ku6utar dani my knight in shinning armor yazo ya aureni a lokacin da nake tunanin na rasashi. Ka koma aikinka in yaso duk lokacin da ka samu wani sai ka barshi. Kaji?” Ta shafo tsakar kanshi ya lumshe ido yana rik’ota.
“Baka ce komai ba Ruwan Zumana.”
Bud’e idanunsa yayi yana murmushi mai bayyana hakwara yace,
“Say it again.”
Dariya tayi kana ta matso ta bakinta saitin kunnenshi ta hura kad’an tace,
“Ruwan Zumana.”
“Shikenan, zan koma.”
Mum Fateey 👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
(26)
“Shikenan zan koma.” Fad’in Haydar yana zungurin goshinta a hankali, dad’i da farin cikin da yake ciki shi kanshi bazai iya fasaltawa ba.
Itama Laila dad’in taji a ranta domin har ga Allah bata so ya sake wannan aikin nashi. A yanda samun aiki ke da wahala a wannan zamanin ina d’an talaka zai samu?
“Nagode Haydar. Baka San farincikin da naji ba game da hakan. Ya ka samu Ammi?”
“Tana lafiya tace a gaishe da amarya.”
“Ina amsawa, nasan yanzu tana can tana kewarka.” Ta fad’i hakan zata matsa daga jikinshi ya hanata motsi.
A hankali ya matso da kanshi fuskarta kana ya d’aura lips d’inshi kan nata, sakan biyar da haka ya d’age yana murmusawa.
“Tell me about yourself Haydar. A ina kuka zauna before ku zo nan Kano?”
“Ruwan zuman fa? Ko har kin daina kirana dashi?” Ya fad’i hakan yana mata cakulkuli tana zillewa.
“Wallahi ba’a mini cakulkuli. Ka bari kar in suma.” Ta fad’i hakan cikin dariya da kuma k’arancin numfashi.
Barinta yayi ta matsa daga jikinshi tana haki tana danna mishi harara. Shi kuma bakinshi a washe domin hakan kad’ai da yayi ya samu ya kashe k’ishin ruwa na son ta6a jikinta.
Sai da ta dawo hayyacinta sannan yace,
“Zan fad’a miki amma sai lokacin da kika shirya kar6an aurenmu.” Ya dubeta cikin nitsuwa yana murmushi.
Ta gane me yake nufi don haka ta kad’a kai tana sauk’e idanunta k’asa tace,
“Amma ina fatan zaka yafe mini ka mini uzuri domin nasan hakan da nake yi zunubi nake kwasawa kaina.”
Kamo yatsun hannunta yayi yana mata kwas kwas yace,
“Na yafe miki Laila, I know to back off when a lady says No. Amma make it fast domin ina gudun kar na rasa hankalina. Ina buk’atar matata.”
Gyad’a kai tayi kana ta kamo nashi yatsun tana mishi abunda ya gama mata.
“You know what?” Ta tambayeshi.
Girgiza kai yayi tace,
“I’m glad I meet you. Sannan ina godewa Allah da yasa ka zama mijina ba wani ba. Anya kana sona kamar yanda nake sonka?”
Jawota yayi ta dawo kanshi yayi caging d’inta da k’afafunshi domin ya lura tana son zillewa ne.
“Haydar ka sauk’eni, ina da nauyi fa.”
“Baki da nauyi Laila, asalima in banda wannan....” ya ta6a bayanta. “...babu wani abu mai nauyi a jikinki. Wai meyasa baki yi k’iba irin na manyan matan nan bane?”
“Kana son mace mai k’iba ne?” Ta kwantar da kanta kan k’irjinshi domin ta gaji da resisting feelings d’inta domin shi d’in mijinta ne halalinta.
“No, nafi son mace daidai ke. You are perfect.”
Murmusawa suka yi kana suka yi shiru na wani lokaci, can yace,
“I love you Laila.”
“I love you too.” Tayi kissing k’irjinshi ta mayar da kanta ta kwanta tana jin tsantsan farin ciki a tattare da ita.
“Fad’a mini abubuwan da kike so da wanda bakya so.”
A haka suka raya daren suna fad’awa juna hakan and their favorites.
Ranar monday Haydar ya shirya zuwa gurin aiki, Laila ce ta kaishi da motarta akan in ya tashi zata biyo ta d’aukeshi su koma gida.
Yana shiga ma’aikatar ya lura da kallon da colleagues nashi suke masa, yasan dalili ko basu fad’a ba. Sai dai su ba damuwarsa bane saboda yayi hitting jackpot Maigidansu ya kasa.
Kanshi a sama ya isa office d’insu wanda yake sharing da mutane uku suka gaisa ya fara aikin daya kawoshi. A daa ya fara sabawa dasu har suna tad’i amma wannan karon sun yi shiru sun k’i masa magana bayan gaisawan da suka yi.
Yana tashi daga aiki Laila tazo ta d’aukeshi suka koma gida, a nan yake bata labarin abunda ya faru a office d’in.
“A yanzu ne suke maka haka amma ka basu kwanaki kad’an zasu sake ku dawo yanda kuke daa.” Ta kwantar mishi da hankali tana turashi band’aki zai yi wanka.
“Ki mini wankan.”
“Baka da kunya ko?” Tace dashi tana barin gurin.
Da yamma Haydar ya tuk’asu zuwa gidan Ammi bayan Laila ta nemi zuwa ganinta. Murnan da Ammi tayi har ba’a magana, sai nan da nan take yi da Laila ta kasa nitsuwa.
“Dama d’azu da rana muke magana da ‘yan unguwa kan ranar jumma’a zamu je mu ga gidan naku.” Fad’in Ammi ga Laila.
Haydar dake zaune a gefenta ya dubeta cikin mamaki yace,
“Ammi me zasu je su yi? Nifa bana son yawan gulma.”
“Ji mini Ali da maganar banza, don mutane zasu je su gidanka shine ya zama gulma? Hajiya kina mishi fad’a kuwa?” Ta dubi Laila kamar itace tayi laifin.
Dariya kawai tayi ta sunkuyar da kanta k’asa domin tasan Haydar ya wuce fad’a a gurinta sai dai lallashi.
“Ammi kenan, bari in bar muku gidan ku ji dad’in maganata da kyau.” Ya tashi ya fice daga gidan.
A nan Ammi ke fad’awa Laila irin dad’in da taji da aka yi aurensu. Laila kuma kunya take ji sanin Ammi ta zama surkuwarta a yanzu.
Daga gidan Ammi gidan Mas’ud suka je, bayan gaishe-gaishe suka yi hira kad’an suka koma gida. Duk wannan yawo da suka yi Haydar da Laila tad’insu suke yi gwanin ban sha’awa.
Suna dawowa gida suka samu Abul a falonsu yana tsaye yana tangad’i ga kayan Haydar a watse a k’asa.
Yana ganinsu ya fara zage-zage yana nuna Haydar da yatsa,
“Munafuki mai kwad’ayin banza kawai. Uwarka tayi asarar haihuwa mara asali kawai.” Ya fad’i hakan cikin tangad’i irinta mashaya.
Tuni Laila ta fara kuka ta yiwo kanshi ya d’aga mata hannu sama har yana yin baya tamkar zai fad’i.
“Uwar me zaki zo kiyi a gurina? Me zaki fad’a mini? Ni zaki nunawa iyeyi? Ba kwanciya da yaron kike yi ba kin manta damu bakya sonmu.”
“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Abul kayan maye ka fara sha? Abul me kake son ka mayar da kanka?”
Ta isa gurinshi ta kamo hannunshi ya fisge ya cigaba da tangad’i a falon yana magana wanda kwata-kwata basa ma gane me yake fad’a.
Haydar da tun shigowansu bai yi magana ba yace,
“Ki kira Mas’ud ya zo, ina ga ba haka banza yake wannan abun ba.”
Tana kuka ta ciro wayarta a cikin jakarta ta fad’a masa halin da ake ciki. Minti hud’u da haka ya bayyana a gidan hankalinshi a tashe ya shigo falon.
Kai tsaye yayi kan Abul ya jawoshi yana kiran sunansa.
Wani wari ya shak’a wanda ya gane na giya ne, cikin takaici da bakin ciki yace,
“Bayan wiwin da kasha yanzu kuma giya ka fara sha?”
“Dama ya ta6a shan abun maye ne ban sani ba? Yaushe Abul yasha wiwi?” Wannan karon cikin k’araji Laila tayi tambayan ga Mas’ud tana juyo dashi ya fuskanceta.
Cikin rashin gaskiya ya bata labarin yanda aka yi Abul yasha wiwi aka masa duka har Alhaji Abdul yazo ya d’aukesa ya kaishi gidansa.
“Don meyasa zaku mini k’arya ku 6oye mini ainihin abunda ya faru da d’ana? Meyasa za’a had’a baki da kai Mas’ud a munafurceni? Wallahi baka kyauta mini ba, daa nasan Abul yasha wiwi da ban d’auko maganar yin aure ba. Kaico, wai d’ana na cikina ne ke shan wiwi da giya?” Wasu hawaye masu zafi suka sauk’o kan k’uncinta.
Mas’ud shiru yayi yana damk’e da hannun Abul wanda ke fisge-fisge yana neman kwace kanshi.
“Nayi hakan ne don kar in tayar miki da hankali Kalti, amma ke kinsan baza a ta6a had’a baki dani a munafurceki ba.”
“To menene amfanin 6oye mini da kayi? Yanzu ba gashi giya ma yasha ba wiwi ba? Me aka fasa Mas’ud? Ka duba yanda yaron nan yake tangad’i yana suratan banza.”
Haydar ne yayi saurin yin magana ya matso gurinsu yana cewa,
“Ka sakashi a d’akinsa sai ka fitar da duk wani abun da zai iya jiwa kanshi ciwo dashi, sai a zauna ayi shawaran yanda za’a 6ullowa wannan al’amarin.”
Gyad’a kai Mas’ud yayi ita kuma Laila bak’in ciki take ji both na Abul da Mas’ud wanda ya 6oye mata wannan babban al’amarin. Zama tayi a kan kujera ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana kuka.
Da taimakon Haydar suka sakashi a d’akin Sabrin domin nan ne babu tarukuce, rufeshi suka yi a ciki kana Mas’ud ya mik’awa Haydar keys d’in gidan da wanda ya cire a aljihun Abul ya damk’a mishi.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 32