abun da ka ambata kana yi Abul?” Laila ta fad’a hawaye na tsiyaya a idanunta tana jin kamar ta kurma ihu, ina ma bata tambayi Abul wannan tambayar ba, ina ma ta zauna cikin duhu tun da har Allah yasa ya daina ya shiryu! Sai kuma tsoron Abul d’in ya shiga zuciyarta amma bata bari ya gane hakan ba gudun kar ya fasa fad’a mata komai.
“Mama zan miki rantsuwa da Allah wallahi ban ta6a yin manyan aikin ba, ban ta6a yin transactions na human trafficking, child pornography, drugs da kuma arms and ammunitions ba. Na san na ta6a creating website da ake jawo mutane masu kwad’ayi a kwashe duk abun da yake cikin bank account d’insu bayan an musu alk’awarin ninka kud’in da suke dashi, sannan na ta6a watsa nudes d’in wani Senator anonymously ba tare da an gane waye yayi hakan ba duk da cewa daga baya an yi k’ok’arin hacking d’in account d’in tare da Laptop d’ina. Mama duk sanina da computer ban yi shaharar da za’a nemeni in yi wad’ancan manyan ayyukan ba, dama kuma nima na yi alk’awarin bazan ta6a yin irinsu ba.”
“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.” Fad’in Laila tana sunkuyar da kanta daga barin kallon Abul.
“Mama ban d’aukeki a hoto ba, haka kuma bani na watsa hotunanki ba, sai dai nine na saka Micheal ya turo miki link na comments d’in mijinki a Twitter don ki ga ainihin k’udirinsa na auren babbar mace kuma mai kud’i, shima kenan irin mutanen nan ne da ake kira da Gigolo. Bayan an watsa hotunanku nine nayi shiga da ficena tare da Sadistic Faruk muka umurci accounts d’in da su goge wannan pictures d’in ko mu 6ata musu account d’in gabad’aya. Bayan mun nuna musu misali shine suka tsorita suka goge, duk irin haushi da takaicin aurenki da nake yi ba zan bari mutane su ci mutuncinki suna miki k’azafin zina ba.”
“Ya Salam, abun ya wuce tunanina Abul. Duk wannan lokacin ni ina nake da har ka fad’a cikin k’azamar rayuwar nan ban sani ba?” Laila ta yi maganar tana tashi tsaye don ji ta yi kanta na sarawa ta kuma kasa gaskata duk abun da ke fitowa daga bakin d’an nata.
Shiru Abul yayi domin babu yanda za’a yi ta san yana cikin wannan rayuwar ko da kuwa bata laptop d’in yayi ta kwana tana bincike a ciki.
“Ina jinka.” Fad’in Laila tana tsayuwa a kanshi shi kuma kanshi na k’asa.
“Bayan aurenki wasu mutum biyu daga cikin members d’inmu na dark web suka turo pictures d’inku suna mini dariya a kan cewa kin auri yaro k’arami wanda kwanaki tare dani aka yiwa wasu couples irin haka kaca-kaca a internet. Na yi mamakin yanda aka yi suka ganeni saboda muna aiki ne anonymously Micheal ne kad’ai ya sanni, sai daga baya Sadistic Faruk ya fad’a mini cewa bakinshi d’aya da su domin shi ya bayyana musu identity na. A nan suka yi alk’awarin watsa videos d’in first night d’inku wanda na san zasu iya aikata recording saboda sun fini kayan aiki da kuma kwarewa. Sadistic Faruk shi ya taimakeni ya hanasu bayan ya basu kud’i mai tsoka.”
“Waye ne shi yaron nan da kake ta kiran sunansa ya taimakeka?”
“Shine wanda na fara sani a dark web bayan Micheal, kuma a gidansu a Abuja na zauna bayan na gudu daga shagon Uncle Mas’ud. Sannan shi ya mini lahani ya kusa kasheni bayan na yi betraying d’insa unknowingly.” A nan ya bata labarin zamanshi a gidan Faruk da abun da ya mishi da tarihin zamanshi tare da Banney har Haydar ya sameshi ya dawo dashi gida bai 6oye mata komai ba.
Laila ta kai kusan minti biyar tana kallon Abul tana share hawayenta amma wasu na zubowa, sai da ta nitsu sannan ta ce,
“Abun da ya faru ya wuce ba zan maka fad’a a kai ba saboda duniya ta koya maka hankali kuma ka nitsu, sai dai ina son ka mini alk’awari da girman Allah cewa baza ka sake komawa wannan rayuwar taka ta baya ba. Ka mini alk’awarin ka bar dark web da duk mutanen cikinta har abada Abul. Wallahi tsoro ya shiga zuciyata, ni kad’ai na san me nake ji da naji wannan rikitaccen labarin naka Abul. Kai Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un, wannan zamani da abun cikinta rashin amfaninsu yafi amfanin yawa.”
“Mama na fad’a miki ne don ki gane na shiryu kuma har abada ba zan sake maimaita abun da nayi a baya ba. Da kuma zan ci gaba da bazan fara fad’a miki ba balle ki saka mini ido ko kuma ki hanani ba. I regret everything I do kuma ina rok’an Allah ya yafe mini kurakuraina da cutar da mutane da na yi.”
“Abun kam babu dad’i don baka san mutane nawa aka cuta a dalilin hakan ba, sannan baka san mutane nawa ne suka kalli tsiraicin wannan Senator d’in ba. Kowanne kana da kason zunubi ba zan maka karya ba Abul, wallahi kana da kason zunubi, kawai ka cigaba da istigfari Allah kuma ya ji tausayinka ya yafe maka.”
Sun dad’e suna magana sannan Laila ta jiyo kukan Mas’ud J ya farka, cikin sauri ta shiga d’akinta ta d’aukoshi domin zai iya birgima ya fad’i k’asa. A ranar daga ita har Abul haka suka yini sakaka jiki babu kuzari, hatta shago waya ta yi ta fad’a musu baza ta samu zuwa ba su kula da gurin. Sai dai yinin ranar bakinta bai daina motsi ba dalilin addu’an da take ta yi Allah ya tak’aita musu wahala da shiga jarabawar rayuwa irin haka.
Haydar da Alhaji Abdul suna isa Abuja direban Baba ya zo ya d’aukesu a airport suka wuce gida. Ammi ce ta taryesu cikin farin cikin ganinsu tare kamar yanda taci buri, Haydar kuma kallonta kawai yake yi yana murmushi dalilin kyawunta da yake bayyana wanda a daa talauci da wahala ya 6oyeshi. Ya san mamanshi kyakkyawa ce amma bai ta6a tsammanin she’s that elegant ba, a yanzu tana cikin kwanciyar hankali tana kuma samun kulawa da soyayya daga Baba wanda har a yanzu bai daina kiranta da suna Lu’a ba.
Sai k’arfe tara da rabi na safe Baba ya tashi daga bacci ya zauna tare da yaran nashi shima farin ciki fal a fuskarsa ganin yanda suke hira tsakaninsu kamar wata matsala bata ta6a shiga tsakaninsu ba.
Babu 6ata lokaci Alhaji Abdul ya sanar dashi dalilin zuwansu Haydar ya k’arishe da cewa,
“Ina son conflict d’in da yake tsakanina da yaron ya kau ko kuma ya ragu, sannan mahaifiyarshi tafi son ya koma makaranta a kan ya fara sana’a kamar yanda yace zai yi.”
Gyaran murya Baba yayi kana ya ce,
“Shekarun da yawa rabon da na had’u da Senator Gambo Umar amma zan nemi ganawa dashi mu gani ko za’a dace.”
Bayan Haydar ya samu ke6ewa da mahaifiyarshi ya dubeta ya ce,
“Ammi kin daina kewata ko?”
“Me ka gani?” Ta tambayeshi tana shafa hannunsa dake cikin nata a hankali tana murmushi.
“Kusan wata kenan rabonki da Kano, da kuma bakya iya yin sati biyu sai kin zo kin ganni.”
“Rashin zuwan nawa ya samu asali ne kan ina son mayar da Meenat gida k’arshen watan nan, Babanta yace ya gaji da zamanta babu miji kuma ya k’i yarda a sakata a University. Yanzu maganar da nake maka cewa yayi ya sama mata miji ta koma gida su daidaita.”
“To Alhaji Abdul d’in fa?” Haydar yayi saurin fad’a cikin rashin jin dad’in wannan labarin.
“Na fad’a mishi ya isa gurin mahaifinta amma ya k’i don ita yarinyar ma ko maganan bai ta6a mata ba. Ban san zuciyarta ba amma idan ya zo nan tana yawan son girka mishi abun da zai burgeshi amma baya nuna ya ji dad’i ko ya yi mata magana mai nuna alamar so. Da na takurashi da zancenta cewa yayi zai maka magana idan ka yarda zaka shiga gaba wajen nema masa auren to zai yi.”
Haydar girgiza kanshi yayi yana murmusawa kad’an domin yayanshi ya shiryu ba kad’an ba, yana sane da duk wani shiga da ficensa wanda baza a kirashi stalking ba sai dai kulawan d’an uwanshi. Ya daina neman mata sannan duk wata harka da zata had’ashi da mace baya shiga, in kuma ya zama dole ya shiga sai ya tabbatar akwai wani namiji tare dashi da zai tsaya tare dashi har ya gama. Wannan mataki ne da Alhaji Abdul ya d’auka don gujewa komawa ruwa.
Da yamma Baba ya musu jagora zuwa gidan Senator Gambo Umar bayan ya samu ganinshi daga wani abokinsa da suke mutunci. A falonshi aka sauk’e su ya fito da kyar yana rik’e da sanda dalilin ciwon k’afa da yake fama dashi, Haydar da Alhaji Abdul da suke zaune a k’asa suka fara gaisheshi bayan ya zauna kana Baba ma ya d’aga mishi gaisuwa yana tambayar lafiyar k’afarsa.
“Alhaji ka ga wannan k’afar canjata ne kawai ba’a yi ba saboda nayi yawon hospitals da dama a k’asashen duniya amma ba’a samu waraka ba, sun hanani cin jan nama tun da jimawa yanzu maganar da nake magana duk wani nama da ka sani sun hanani ci. Abubuwa da dama na nau’in abinci sai dai in gansu in kawar da kai saboda sun zama haramiyata, idan kuma na kuskura na ci to sai dai in farka a wata k’asar an kaini asibiti. Talaka yana can yana neman kud’i ya d’auka sune jindad’in duniya bai san cewa ya fi mu kwanciyar hankali da lafiya ba.”
Baba ma labarin ciwon k’afarsa ya bashi yana kuma kwatanta mishi wata asibitin da ya je a India wata uku da suka wuce aka bashi magani har ya samu sauk’in k’afar ya fara taka mota. Su Haydar dai Suna zaune ba uhm ba um um suna jin labarin ciwon k’afa wanda Alhaji Abdul ya ji kamar ya tsayar dasu su yi abun da ya kawosu amma bai isa ba.
“Kayi contacting asibiting tukunna a tsara komai sai ka je.” Fad’in Baba ganin Senator Gambo ya kwadaitu da zuwa asibitin.
“Wannan tafiya ai kai zaka mini jagora Alhaji Sammani, in zaka iya raka tsohon abokinka kenan.” Senator Gambo ya k’arisa maganan cikin raha yana dariya.
“Ai shikenan Allah ya kaimu lokacin dama matata tace k’asar na burgeta bata gaji da zagawa ba.” Fad’in Baba shima yana darawa.
Maganar bata k’are ba sai da suka tsara yanda tafiyar zata kasance wacce za’a yi nan da sati biyu masu zuwa.
“Kace wad’annan d’in duk ‘yayanka ne Alhaji Sammani?”
“Har yanzu kana mamaki ne Senator?” Baba ya kwashe da dariya yana kallon ‘yayan nashi cike da alfahari.
“Kayi sa’an ‘yaya Alhaji, ni ban ga ‘yayan bama balle har in samu su rakani wani guri irin haka. Dalilin da yasa kaga na nace maka ina son tafiyar da kai saboda sun ce sun gaji da yawon asibitoci da ni ne, wai in hak’ura ciwon tsufa ne dashi zan mutu. Basu damu dani ba Alhaji, duk irin gwamutso da wahalar tara kud’in nan da nayi domin su yanzu basa gani saboda kowa yayi fiffike ya tashi zai bautawa matarsa da ‘yayansa.”
“Kayya abun bai yi dad’i ba, yaran yanzu sai addu’a Senator. Allah ya karkato da hankalinsu gida yasa su gane gaskiya.”
“Amin Amin.”
Sai a lokacin Baba ya sanar dashi dalilin zuwansu wanda Senator yana jin cewa d’ansa Faruk ne ya kwacewa jikan Alhaji Sammani Laptop d’insa ya hau fad’a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
“Ka ji ko Alhaji? Shi yaron nan menene ban mishi ba don kawai ya dawo gida ya zauna kusa dani? Kwanaki shi ya saka na mayar da lambun gidan nan nashi shi kad’ai wai yafi son guri da babu hayaniyar mutane saboda kukan tsuntsaye yafi mishi dad’in sauraro a kan maganar mutane. To yanzu maganar da nake maka ya tafi yau wata shida kenan ban san ina yayi ba, yaran nan gaba d’aya sun lalace na rasa gane yaya aka yi hakan ya faru.”
Haydar da yake jin duk abun da yake faruwa ya ce a ransa ‘dama idan aka ciyar da yaro da haram aka kuma nuna mishi so babu kwa6a dole iyayensa su yi kuka a k’arshe’.
Senator Gambo shi ya kira direban Sadistic Faruk da yake shi yafi kowa sanin shiga da ficensa ya tambayeshi ko Faruk d’in ya ta6a yin bak’o wanda ya tafi bai d’auki kayansa ba.
“Yalla6ai ya ta6a kawo bak’o a matsayin abokinsa amma rabuwarsu bata yi dad’i ba. Shine wanda nake baka labarin a kwanakin baya.”
Dafe kai Senator Gambo yayi cikin jin kunyar wannan abun saboda shi yana da labarin duk abun da d’ansa yake yi ta hanyar Direbanshi ba tare da shi Faruk d’in yasan ana kai rahotonshi ba, sai dai duk abun da Faruk d’in yake yi Senator Gambo baya iya mishi fad’a saboda yana tsoron kar ya tafi ya barshi kamar yanda sauran ‘yayan nashi suka gujeshi. Su kuma su Baba basu da masaniyar ainihin abun da ya faru, abun da suka sani shine Laptop d’in Abul na tare da d’an Senator Gambo.
“Ka je gidan nashi ka d’auko duk wani abu da ka sani na wannan yaron ne ka kawo nan.”
“To Yalla6ai.”
Bayan fitansa Senator Gambo yayi ta basu hak’uri musamman ga Haydar da aka fad’a masa cewa d’an matarsa ne. Minti ashirin da haka Direban ya dawo hannunsa d’auke da jakar Abul wacce ta k’unshi suturunsa da kuma laptop d’insa. Ganin magriba ta yi yasa Baba ya mishi sallama suka tafi Senator bakinshi bai daina basu hak’uri ba.
Suna shiga cikin mota fuskar Baba ta murtuk’e ya dubi ‘yayan nashi ya ce,
“Me kuke 6oye mini game da wannan case na Abul da Faruk? Yanda ubanshi yake ta bada hak’urin nan ba banza ba.”
Alhaji Abdul ya kalli Haydar wanda shi kuma ya fad’a musu duk yanda suka yi da Abul. Kad’a kai Baba yayi ya ce,
“Duk maganar su iri d’aya ne cewa sun yi rabuwar rashin dad’i amma shi Abul ya k’ara da cewa shi Faruk d’inne yayi masa lahani a k’afarsa. Ku yi booking flight d’in gobe da ni da Amminku da kuma Meenat, zamu koma Kano tare ina son jin duk abun da ya faru daga bakin yaron, idan har sun zalunceshi ni zan tsaya masa har kotun koli sai an kwato mishi hak’k’insa.”
Mum Fateey 👌
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
Littafan Marubuciyar
1-Matar K’abila
2-Fatu a Birni
3-Ruwan Zuma
Visit my wattpad profile at https://my.w.tt/IKR4zCOYfbb
Sayen nagari mai da kudi gida. Ina masu Neman Ingantaccen man kad’anya gangariya daga Niger state? Ku tuntube mu ta wannan layi domin siyan d’aya ko sari. Sai an gwada a kan san na kwarai. 07065577810.
(54) End
Washe gari flight d'in safe suka hau suka koma Kano, a gidan Alhaji Sammani suka fara sauk'a aka ajiye Meenat da Ammi sannan Baba da Haydar suka wuce gidan Laila don ganawa da Abul, Alhaji Abdul shi ma bai bi su ba domin yace baya son k'ara had'uwa da wani mai fushi dashi kamar Madu.
Laila da dama Haydar ya fad'a mata yana zuwa da Baba tuni ta shirya gidan ko'ina ya d'auki k'amshi kamar kullum. Mas'ud J kuwa an mishi wanka yayi shiga ta alfarma amma ya koma bacci saboda baya tashi da wuri sai tara ko goma.
Suna isa maigadi ya bud'e musu gate suka shiga, Baba tsayawa yayi a waje Haydar ya fara shiga sannan ya mishi iso suka shiga tare. A falon Haydar suka zauna Laila ta kawowa Baba kunun madara irin wanda Shuwa Arab suke yi kana ta koma k'asa ta zauna suka fara gaisawa.
"Amminku tana yawan mini wannan kunun, na yi zaton ita ta fi kowa iyawa ashe Maman Mas'ud ma ba baya ba." Fad'in Baba cikin yabawa surkarsa.
Laila murmushi ta yi cikin jin dad'i ta ce,
"Nagode Baba."
"Ina yaron naku yake? Na ji an ce ya dawo, kira mini shi mana."
Laila tsoro ne ya kamata tana fatan ba wani abun Abul yayi a bayan idonta ba, bacci ta samu yake yi ta tayar dashi tana tambayarshi me yayi.
"Mama ban gane me nayi ba, tun da na dawo nake gidan nan in banda gidan Sabrin babu in da na je. Waya fad'a miki nayi wani abu?" Ya tambayeta cike da damuwa da kuma magagin bacci.
"Baban Haydar ne ya zo daga Abuja wai yana son magana da kai. Don Allah in wani abun kayi ka fad'a mini in shirya yanda zan basu hak'uri." Ta k'arisa maganan tana kallonshi kamar zata yi hawaye.
"Wallahi babu abun da nayi. Idan kuma akwai zaki ji sai ki mini duk hukuncin da ya dace dani."
Wannan magana yasa Laila ta ji sanyi a ranta ta d'aga hannu ta shafa fuskarsa cikin so da k'auna ta ce,
"I believe you Abul. Mu je."
Suna shiga falon shima Abul ya samu guri a k'asa ya zauna kana ya fara gaishe da Baba sai Haydar cikin ladabi, yana mamakin kamannin mutane biyun. Baba ne ya fara magana yana murmushi ga Abul ya ce,
"Jikana da fatan ka san waye ni ko?”
Gyad’a kai Abul yayi kana ya ce,
“Baban mijin Mama.”
Amsar tashi ta bawa Baba dariya ya dara kad’an sannan ya ce,
“Jiya mun je gidan Senator Gambo Umar mun kar6o maka kayanka da ke can, amma jin yanda shi uban yaron yake bamu hak'uri yasa na gane akwai wani abu da aka maka wanda ya munana. Duk da ban san menene ba raina ya 6aci kuma ina da niyyar tsaya maka har sai na kwato maka hak'k'inka. Kar kasa a ranka kai ba jikana bane na jini, da kai da Mas'ud J duk d'aya kuke a gurina kuma ba zan bari wani ya zalunceku ya zauna lafiya ba."
Tirk'ashi!! Laila zufa ne ya fara taruwa a goshinta duk da sanyin a.c da yake falon, Abul kuma baki ya sake yana kallon yanda Baba ya murtuk'e fuska ranshi babu dad'i. Ashe akwai mutanen da zasu nuna mishi k'auna irin wannan bayan Mamanshi da Mas'ud? Duk irin rashin mutuncin da ya yiwa Haydar ashe tafiya yayi har Abuja ya d'auki babanshi suka je suka kar6o mishi laptop d'inshi? Wani abu yayi musu da ya cancanci wannan alkhairin da jajircewan?
Laila kuma tsoro ta ji a ranta don bata son kowa ya ji k'azamar labarin da Abul ya fad'a mata a kanshi, tana son wannan ya zama sirri tsakaninta dashi ba sai duniya sun san ainihin abun da ya faru dashi ba, wanda har tsufanshi wasu baza su daina aibantashi ba. Da kuma ta san cewa Haydar ya tafi Abuja ne don Laptop d'in Abul da ta hanashi saboda sai yanzu ta ji ta gwammace Abul yayi sana'ar ko da kuwa ta sayar da Yalo ne a kan ya koma harkan computer. Dubanshi ta yi wanda hakan yasa shima ya kalleta ya kuma karanci fuskarta ya juya ga Baba ya ce,
"Alhaji na gode sosai da wannan d'awainiyar taku a gareni, amma in don ta nine wallahi komai ya wuce a gurina saboda Allah ne ya koya mini darasi a kan halin da na saka kaina a ciki, ai bariki ba kamar gida bane kuma duk wanda ya za6i bariki a sannu duniya zata koya mishi hankali. Lahanin da ya mini kuma karnuka ya sakar mini har suka karya mini k'afa suka ji mini ciwuka bayan mun samu sa6anin ra'ayi ni dashi. Nagode sosai da wannan soyayya Allah ya bar girma ya k'ara tsawon rai."
Laila tari ta fara babu kyakkyautawa dalilin shak'ewa da tayi ta yawunta da ta ga yanda Abul yake magana cikin nitsuwa da kuma bawa mutane girma kamar bashi ba, ai zata iya rantsewa ko a daa da yake cikin hankalinsa baya kallon mutane da girma kamar yanzu. Lallai gaskiya ne da ake cewa 'duniya tafi koyawa mutum hankali sama da wanda aka ajiye a aji ake gwada masa'.
Ganin hankali ya dawa kanta ne yasa ta tashi tana cewa zata je ta sha ruwa sannan zata duba Mas'ud J. Tana tafiya Haydar ya kawo jakar Abul ya mik'a mishi shi kuma ya taso ya kar6a yana k'ara musu godiya sannan ya koma ya zauna.
Baba ne yake janshi da hira wanda yawanci akan karatunshi da ake son yaci gaba da yi ne ganin mate d'insa sun wucesa da shekara d'aya. Suna zaune Laila tayi sallama ta shigo da Mas'ud J wanda ya sha kunu ya k'oshi yana zare idanu, Yayansa Abul ya fara hangowa a falon ya fara k'ok'arin sauk'a daga jikin Laila zai tafi gurinsa, ganin haka yasa Laila ta ce,
"Gurin Baba na kawoka kana neman zuwa gurin Abul, kalli, ga can Daddy da Baba suna kiranka."
Bai yarda ya kalli in da take gwada mishi ba sai da ya ga Abul ya rik'eshi sannan ya d'aga ido ya hango Babansa da kuma kakansa da bai cika gani ba. Barin jikin Abul yayi ya rarrafa gurin Babanshi yana gwalantoyi wanda hakan ya bawa 'yan falon dariya ciki har da Abul da yake jin sanyi da kuma dad'i a ransa wanda ya rasa gane menene dalilin.
Baba ya k'ara minti goma a gidan yana wasa da jikansa sannan ya tashi zai tafi yana cewa,
"Muna zuba idon ganinka Abul. Idan ka tashi zuwa ka taho mana da wannan mayunwacin." Ya k'arisa maganan yana nuna Mas'ud J da ya dawo hannun Abul d'in.
"Insha Allah zamu zo Alhaji. Mun gode.”
Direba ne ya mayar da Baba gida shi kuma Haydar ya shiga motarshi ya tafi office bayan ya k'ara minti biyar a gidan.
"Wow." Fad'in Abul yana zama a kan kujera shi da Mas'ud J.
"Wow kam." Laila ta amsa itama tana zama a gefenshi har da share imaginary gumi a goshinta.
"Haka suke Mama? Haka suke treating d'inki?"
"Sabrin bata baka labari bane? Yanda ka san jikarsu haka suka d'auketa dama kasan ita bata samu kulawar Umman babanku ba sai kuwa Ammi ta zame mata Kakar da ta rasa."
"Ta fad'a mini amma sai na d'auka tana fad'in hakan ne don wani manufarta ta daban, yanzu kam nima na gani and I'm happy Mas'ud J have a family like this."
"Kaima family d'inki ne saboda Ammi 'yar uwarmu ce ta jini."
"Haka ne I'm happy Mama. And I'm happy for you too."
Laila gyara zamanta ta yi ta dubeshi with serious face ta ce,
"Yanzu da suka dawo maka da Laptop d'in me kake shirin yi?"
Abul saukar da Mas'ud J yayi a k'asa sannan ya jawo jakar ya ciro komai da yake ciki, suturunsa ne da wasu k'ananan abubuwansa wanda ciki har kayan mayen da ya saya bai gama sha ba da kud'ad'en da ya sata a shagon Mas'ud.
Laila saurin d'aukan kayan mayen ta yi kana ta shiga kitchen ta kwararar a sink sannan ta saka ruwa ya wuce dashi. Tana dawowa ta samu Abul ya jona laptop d'in a charge ya kunnata tana booting.
"Baka ce mini komai ba Abul."
"Kiyi hak'uri ina son nuna miki abun da zan yin ne."
Murmusawa Laila ta yi kana ta gyara zamanta tana kallon duk abun da yake yi har computer ta bud'e aka nuna hoton Abul da Sabrin a matsayin screen saver. Arrow ya kai kan wani folder ya ce,
"Duk wani information, videos, pictures da kuma links da nake samu daga dark web a wannan folder nake ajiyewa kuma nayi deleting d'inshi." Ya danna 'delete' kana ya shiga cikin trash ya k'ara gogewa.
A haka ya dinga shiga da fice yana nuna mata duk abu mara kyau da yake ciki yana gogewa sannan ya shiga ainihin site d'insu na members d'in k'ungiyar ya fitar da kanshi bayan ya canja sahu ta in da baza su sake turo mishi invite ba har abada.
"Na goge komai Mama, na bar wannan rayuwar har abada saboda ina son na zama kyakkyawan misali ga Mas'ud J ya tashi yana alfahari da kasancewata yayansa."
"I’m so proud of you habibi. Allah ya maka albarka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 32