Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wato Kaala Abdi duk tsufansa sai da yayi kuka yana shafa fuskar Ammi yana cewa ta yafe mishi, itama kukan take yi tana neman yafiyarsa ana basu hak’uri. Sai da ka nitsu ta basu tarihin rayuwarta ta kuma fad’a musu d’anta Haydar shi yake auren Laila, ‘yan uwa sun yi mamakin wannan abun domin shi Kaala Abdi tun had’uwarshi da Haydar lokacin da suka kawo Abul yaji yaron ya kwanta mishi, ganin irin yanda yake k’ok’ari a kan d’an Laila, ashe jikanshi ne bai sani ba. Murmusawa kawai Laila take yi har Mas’ud ya gama bata labari, ya k’arisa da cewa, “Sai dai Abul ne da aka bashi labarin muka kasa sanin halin daya shiga. Daa yana mayar da martani ga mutane cikin rashin kunya amma yanzu duk abunda aka fad’a mishi baya tankawa, kai ko kallonka ba zai yi ba.” Cikin firgici Laila tace, “Don meyasa zaku fad’a mishi? Sannan me hakan yake nufi kenan? Kar duk wahalan da aka sha ya dawo sabo fa!” “Kaala Abdi ne da kanshi yace a fad’a mishi, kuma yace mu rabu dashi kar mu damu.” Gyad’a kai kawai Laila tayi amma zuciyarta na waswasin wannan mataki da Kaala Abdi ya d’auka. Ita a ganinta yafi a ce an bari sai ya nitsu sai a fad’a mishi duk abunda yayi missing na rayuwarsu. Zama gida ya fara damun Laila domin yau wata d’aya da sati biyu kenan Haydar baya nan, a lokacin da suka bayar ta tambaya mai d’auke da cigiya gurin Mallam Nafi’u tayi tsammanin baza a kwana biyu ba zai dawo, amma gashi har yau babu shi babu labarinshi. Alhaji Abdul na yawan kiranta yana tambayar ko Haydar ya dawo, kullum dai amsar d’aya ce. Karshenta cewa tayi ya daina kiranta akan idan Haydar d’in ya bayyana ita da kanta zata kirashi. A daren ranar Laila ce kwance a d’akinta misalin k’arfe takwas da rabi na dare, a yanzu har ta daina hira mai tsawo domin ta hak’ura da jiran Haydar a falo wai ko zai dawo. Sai kuma yanzu ta fara laulayin ciki amma nata na kwad’ayi ne da bacci da kuma son kasancewa tare da mijinta, wanda kullum bata iya bacci sai ta da tufafinsa a hancinta. Kiran wayar Haydar tayi a karo na ba adadi taji an ce wayar a kashe take kamar kullum, cikin saduda ta kira wayan Kaala Abdi tace tana son magana da Abul wanda ta dad’e bata nemi hakan ba. Babu musu Kaala Abdi ya bada wayar aka kai sashen da aka rufe Abul aka mik’a mishi wayar ya k’arba ba tare daya tambayi waye bane. “Abul.” Ta kira sunanshi cikin sanyin murya. “Mama.” Shima ya kirata amma bai k’ara cewa komai ba. “Ya kake? “Gani nan dai.” “Ina fatan ka daina tsanata don na kaika gurin da zaka shiryu?” Shiru yayi na wasu sakanni sannan yace, “Ina mijinki?” Murmusawa tayi wanda aka ce yafi kuka ciwo tace, “Ya tafi ya barni Abul. Nasan zaka ce ‘I told you so’ amma laifi nayi ya yanke wannan hukuncin.” “Na san komai Mama. Duk abunda ake ciki na sani an fad’a mini. Mijinki jikan Kaala Abdi ne sannan k’anin Alhaji Abdul ne. Yaushe zaki fad’a mini wannan babban al’amarin Mama? Shin har yanzu baki yarda dani bane kamar yadda kika kasa yarda dani a baya? Zaki iya tuna abunda ya fara tunzurani na bar gidanki? Saboda kin mini k’azafin d’aukanki a hoto ne tare dashi wanda wallahi wallahi bani nake yi ba. Idan nace kin tsaneni sai kice karya nake yi amma gaskiya ne bakya sona tunda har yanzu baki yi trusting d’ina ba.” Tashi zaune Laila tayi domin rabon da Abul ya mata magana irinta masu hankali har ta manta. Wai yau itace take magana da Abul babu zagi babu bak’ar magana? “I’m so sorry Abul, amma nayi hakan ne don karka sake tunzura tunda bana gane me yake pushing d’inka. Sannan zan k’ara baka hak’uri kan d’aura maka laifin da nayi alhali ba laifinka bane duk na Alhaji Abdul ne.” A nan Laila ta bashi labarin komai bata 6oye mishi ba saboda tana son gaining trust d’insa. Shiru yayi yana sauraranta har ta ida aya sannan ya fara magana cikin tsananin fushi har yana huci yace, “Basu fad’a mini cewa duk makircin Alhaji Abdul bane Mama, ki fad’awa Kaala Abdi ya sakeni in dawo in kasheshi. He dared used me as a bait don ya sameki, na zama tamkar pawn a wasansa. Wallahi sai na kasheshi.” Ya k’arisa maganan cikin k’araji yana hawaye. Tsoro sosai ya bawa Laila wacce ta fara kiran sunansa tana cewa ya nitsu yayi shiru amma inaa! Sai hauka ya k’ara yi k’arshe wanda aka aikan ya kwace wayar ya fita ya kulleshi yaje kiran Kaala Abdi wanda shi kad’ai yake saisaitashi in ya fara wannan abun. Kafin Kaala Abdi ya zo Abul ya yiwa kanshi rauni da jikin k’ofa domin buga kanshi yayi har sai da ya fashe. Sai da aka wanke mishi ciwon ya nitsu yayi bacci sannan Kaala Abdi ya kira Laila wacce dama tun d’azu take kiran wayarsu amma basu d’auka ba yace, “Me kika fad’a mishi?” “Mas’ud ya fad’a mini kun labarta mishi komai akan abunda yake faruwa shine na k’ara maimaita mishi, na kuma sanar mishi cewa duk makircin Alhaji Abdul ne wanda ashe ku baku fad’a mishi ba.” “Shikenan sai da safe.” “Kaala Abdi na 6ata muku shiri ko?” Ta tambayeshi hawaye na taruwa a idanunta. “Babu komai, kawai abun ne yazo mishi a bazata. Kafin gobe da safe zai dawo yanda yake.” Da haka suka yi sallama tana addu’a a ranta Allah yasa bata 6ata abun da suka dad’e suna gyarawa ba. A haka tayi bacci cike da mafarkan Haydar wanda ya zame mata d’abia, wannan karon mafarkin yafi mata dad’i domin kwanciya yayi a bayanta ya rungumeta sosai yana shafa cikinta yana kuma kiran sunanta a kunnenta. A haka ta farka tana murmushi amma jin mutum da tayi a bayanta yasa zuciyarta ta fara bugawa da k’arfin gaske tace, “Haydar!!!” “Shhhh, kiyi shiru karki tayar da Babyn Haydar.” RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Wannan page is dedicated to Masoyan Ruwa Zuma na paid group, irinsu Suwaiba Haruna, Hajara Baba, Hadiza, Ummu Mahir, Safiya Jalo Gani, Ummiiterh, Haseenah, Hannatu, Aishatu Umm Ra’if. Halima k’awar Khadija Sidi, Namiji kanin ajali 😆 da kuma Ruqayya. Next post Insha Allah na Masu comments ne. I Love you all.😍 (48) “Haydar!!” Laila ta sake kiranshi with disbelief in her voice tana neman juyowa amma ya rik’eta k’amm ya hanata motsi. “Stop struggling Laila, Baby zai tashi.” Ya fad’a yana cigaba da shafa cikinta a hankali wanda ya lura ya tashi kad’an yayi tauri sosai. Sheshshekar kuka ta fara ta rik’o hannunsa dake shafa cikin nata ta rik’eshi a k’irjinta, hakan yasa Haydar ya juyo da ita suka fuskanci juna ba tare da ya bari ta bar jikinshi ba yace, “Me abun kuka Laila?” “It’s really you.” Ta fad’a tana shafa fuskarsa da jikinshi. “It’s me.” Ya juya kad’an ya kunna bedside lamp suka k’urawa juna ido, cikin sauri Laila ta tura kanta cikin wuyanshi tana shinshinarshi tana rufe ido. Bai hanata ba illa dariya da abun ya bashi domin yasan k’amshinsa na d’aya daga cikin addiction d’inta, shinshinarshi da take yi kuma yana mishi kamar cakulkuli ake mishi amma haka ya hak’ura har sai da tayi mai isarta sannan ta koma ta kwanta tana jan wata doguwar ajiyar zuciya tace, “Ka gujeni Haydar.” Shiru yayi bai amsa ba domin ya sani gudunta yayi da duk wani nashi don yaje ya warkar da zuciyarsa daga ciwon da aka saka mata. “I’m sorry amma ban zubar da cikin ba wallahi. Tun kafin wayewar gari nake jin kamar bazan iya zubarwan ba amma a hakan na fita naje asibitin. Abunda na fara sanar da Doctor shine ya duba mini lafiyar cikin da kuma girmansa don in sani in kuma sanar da kai cewa I will keep the pregnancy. Ka zo ka samu ana mini scanning wanda ya sakani hawaye dalilin ganin abunda yake cikina kamar wani beans, kenan shi zai girma ya zama d’an mutum gudan jininka. A wannan lokacin naji babu abunda nake so irin in bar wanann abun ya rayu in haifeshi in rik’eshi a hannuna ina kallon abunda muka haifa ni da kai. Haydar baka saurareni ba ka tafi, baka bani chance da zan yi explaining kaina ba. Kayi hak’uri da duk abunda na maka daga farkon zamanmu har rana mai kamar ta yau, don Allah ka mayar dani d’akina wallahi na maka alk’awarin haihuwa duk shekara har in kai menopause d’ina. I wouldn’t give a damn akan abunda mutane zasu ce saboda na gane kai ne farincikina basu ba. Please give me another chance, wallahi wallahi bazan sake kauce umurninka ba just stay with me don girman Allah karka sake guduna Haydar.” Ta tashi zaune tana k’ara rik’o hannunshi kamar an ce mata zai gudu, idanunta kuwa cike suke da hawaye wanda wasu ke gudu freely a k’uncinta. Haydar ya tashi shima ya zauna ya dunk’ula hannunsu guri guda ya sumbaci nata ya d’ago fuskarsa yana kallon yanda ta bi hannun da kallo kamar shine the most prized possession yace, “I’m not going anywhere Laila.” “Abun da ka fad’a kwanaki kenan Haydar amma still ka k’ara tafiya ka barni. Yaya kake son in yarda da maganarka alhali kana sa6a alk’awarinka.” “Saboda zaman da nayi babu ke Laila wallahi ban ta6a jin dad’insa ba ko na second d’aya. Idan na tuna cewa na rabu dake sai in ji kamar in yiwa kaina hukunci saboda nayi aikin gaggawa kuma nayi dana sani. A tunanina ko na dawo ba zaki yarda da aurena ba shiyasa nayi ta zamana har Allah yasa yau naji sak’on da kika bayar ga Mallam Nafi’u, wanda tun bayan tafiyana ban k’ara sauraron wa’azinsa ba sai yau. Ina cikin bin episodes d’in da nayi missing naji sak’onki wanda yasa na fito a lokacin ba tare da nayi la’akari da cewa dare yayi ba. Tun ranar dana tafi ina cikin Kano a wani hotel wanda su suke kawo mini abinci daga restaurant d’insu idan na buk’aci hakan, bana fita waje ko kad’an domin hatta sallah a cikin d’akin nake yi. Na nisanta kaina da duk wani abu na jin dad’in rayuwa sai ibada da nake yi ina jiran ranar da zan ji I’m ready to move on with my life. Wallahi Laila every minute without you ina jinshi kamar har abada ne, ina son dawowa amma idan na tuna bazaki kar6eni ba da kuma abunda nake tsammanin kin yiwa gudan jinina sai in ga gwara inci gaba da zama a can saboda bakya sona.....” “Wallahi ina sonka Haydar, ina maka son da ni kaina ina mamakinshi. You have no idea yanda sonka ke yawo a jinin jikina wanda ya hanani samun sukuni all this while da baka nan. Na fika shan wahala saboda kullum da hawaye a fuskata nake bacci, sai dai idan na tuna cewa ina tare d’anka sai inji sanyi a raina in gane cewa I’m not alone, someone is there for me. I’m sorry once again, I’m so sorry please forgive me.” With shiny eyes wanda suke sparkling dalilin hawayen daya taru a cikinsu Haydar ya kalli Laila yace, “I forgive you, ina fatan nima zaki yafe mini tafiya da nayi na barki da abunda yake cikinki.” “No, wallahi baka da laifi saboda na kaika bango ne kuma baka san cewa ban cire cikin ba. Laifin duk nawa ne kuma ni ya kamata in baka hak’uri in nemi gafarka. Please ka dawo dani matarka, please.” “Ke matata ce tun lokacin dana saka k’afa na shigo cikin gidan nan na kwanta a kan gadonki, na dawo dake d’akinki tunda na kai hannu jikinki. You are still my wife.” Ya fad’i hakan yana shafa fuskarta cikin tsantsar sonta da yake d’awainiya da zuciyarsa. Kwantar da kanta Laila tayi akan tafin hannun nashi sannan ta d’aga ido ta kalleshi tayi saurin had’e kansu guri guda tana kissing d’inshi, Haydar da yake restraining kanshi yaji ya kasa hak’uri ya rik’o wuyanta suka fad’a duniyar ma’aurata. Minti biyar da haka tace, “Haydar....don’t crush..my....my Baby.” “I won’t, I will be gentle Laila.” Bayan komai ya lafa Haydar ya jawota jikinshi yana shafa kanta cikin tsananin farinciki da yake ciki yace, “I love you and I can’t live without you Laila, please stay with me.” Hancinta ta saka a wuyanshi tana shak’ar k’amshinsa wanda a yanzu ya had’u da gumi kad’an dalilin k’ok’arin daya gama yi a lokacin, tace, “Ina nan tare da kai Haydar thou na ji Mallam ya baka shawaran ka k’ara aure, idan zaka yi bazan hanaka ko in tayar maka da hankali ba, sai dai ina tsoron kar ka auro budurwa ka wulak’antani a kanta ko kuma ka rabu dani saboda ni na tsufa. Amma in zaka zauna dani tsakani da Allah zan zauna da kai ko da uku ka k’aro a kaina.” Shiru Haydar yayi na wasu sakanni sannan yace, “In fad’a miki wani abu zaki rik’eshi a matsayin sirri har k’arshen rayuwarki kuma ba zaki gujeni ba?” Laila tashi tayi zaune tana jawo zanin da suka rufe jikinsu zuwa k’irjinta, amma Haydar na ganin hakan ya janye yana cewa, “Nafi son ganinki haka. Amma dad’ewan da nayi bana nan shi yasa naga sun k’ara girma ko dai idona né.” Murmusawa kawai Laila tayi tana buge hannunsa da ya kai k’irjin nata tace, “Cikin ne yasa suka k’ara girma. Now mu koma maganarmu na d’azu, me zaka fad’a mini? Sannan ka sani sirrinka sirrina ne, har abada bazan ta6a kwaye maka zani a kasuwa ba.” Gyad’a kai Haydar yayi ya dubeta with so much seriousness yace, “I’m Gerontophile Laila.” Tattare fatan saman goshinta Laila tayi cikin rashin fahimtar me yake nufi da wannan kalmar. “Menene Gerontophile d’in? Kamar ba common word bane.” Kallonta yayi sosai kana yayi ajiyar zuciya ya sunkuyar da kanshi k’asa yace, “Mutum ne who has a sexual attraction for people who are older than themselves. I like older women Laila, ‘yan mata basu ta6a burgeni ba wallahi balle har inji ina son tarayya dasu. Amma ke idan na tuna cewa kin girmeni sannan a hakan nake pinnng d’inki down ina faranta miki shi yake sakani farin ciki da nishad’i. Don Allah karki gujeni a yau dana fad’a miki deepest secret d’ina, ko Ammi bata sani ba and ina son ya tafi a haka saboda su baza su ta6a ganewa, k’arshenta tsorita zata yi tace aljanu ne suke d’awainiya dani. People like me exist Laila sannan bani na za6awa kaina hakan ba, haka na tashi na ganni.” Haydar da har lokacin kanshi na k’asa ya d’ago kanshi da yaji shirun yayi yawa, a ranshi kuma yana tunanin ko itama ta tsorita ne zata gujeshi. Sai dai ganinta yayi tana murmushi bakinta har kunne yasa shima fuskarsa ta washe yace, “Why are you grinning?” “Saboda yanzu hankalina zai fi kwanciya idan na tsufa, duk macen daka gani mai k’uruciya baza ta ta6a zama threat a gurina ba. I think we are one perfect couple shiyasa Allah ya had’amu ya kuma k’ara mana da albarkan samun zuriya. Wallahi baka san yanda wannan maganan ya d’auke mini wani k’aton nauyi a zuciyata ba, kullum idan na tuna cewa zan tsufa kai kuma zaka iya fara kula k’ananan yara sai inji kamar an yamutsa mini zuciyata. I’m happy that you are geron.... gerenta? Whatever! I’m glad.” Tana fad’in hakan ta rungumeshi tsam a jikinta tana fatan in ma hakan rashin lafiya ne kar Allah yasa ya warke ya zauna a haka, and yes, she is that selfish. “Hajjaju kina tsokanata kuma I don’t want to hurt you or the Baby.” Ya fad’i hakan yana ganin yanda take neman birkita mishi lissafi. “Waya fad’a maka zaka yi hurting d’ina ko Baby? Doctor yace a dinga yiwa Baby yayyafi ana bashi vitamin D.” “Then be my guest.” Ya amsa suka k’ara tafiya wata duniyar. Washe gari misalin k’arfe goma da wasu mintuna Laila ta farka ta ganta kwance a k’irjin Haydar wanda ke bacci sosai. Tsayawa tayi tana kallonshi wai wannan d’in duk nata ne ita d’aya, kyakkyawar fuskarsa da kuma k’arfin da Allah ya masa ya isa a kirashi da gwarzon d’a namiji domin duk wani k’ishinsa da ta dad’e tana ji sai da ya cire mata jiya. “I love you so much it hurts.” Ta fad’a a hankali kana ta tashi ta shige band’aki ta sillo wanka ta fito. Jikinta ta fara shafawa crème mai had’e da kulacca sannan ta bi da humra wanda yasa nan da nan d’akin ya bule da k’amshinta. Kwalliya ta zanawa fuskarta mai kyau da sauk’i sannan ta saka wata doguwar riga da Haydar yace tana mishi kyau. Jikinta ta k’ara feshewa da turare sannan ta juyo zata fita taga Haydar ya farka yana kallonta. “Ina kwana Baban Baby.” Cikin seconds uku ya iso gurin da take ba tare daya damu da rashin kaya a jikinsa ba. “Say it again.” Ya fad’a yana kissing wuyanta tare da shafa cikinta. “Baban Baby?” Ta tambayeshi tana zaro hannunsa daga cikin rigarta. “Eh.” Ya bata amsa yana cire mata kallabinta. “Baby yana jin yunwa, bana kai war haka ban karya ba fa.” Tayi saurin fad’a ganin zai k’ara janta zuwa wata duniyar. Yana jin hakan ya bar jikinta ya koma can gefe yace, “A bawa Baby abinci. Ni zan iya jiran nawa abincin sai anjima.” Yana fad’in hakan ya shige band’aki ya bar Laila a gurin wacce take jin kamar ta bishi. Sai dai tunawa da tayi cewa she needs real food yasa ta kad’a kanta ta fita zuwa kitchen. Tuwon da mai aikinta ta mata jiya shi ta d’umama ta sakawa Haydar a warmer sannan ta fito ta ajiye a dinning table tare da plate da serving spoon. Komawa kitchen tayi ta had’o tea sannan ta dawo ta fara cin tuwon tana kur6an tea d’in. Duk wannan abun da take yi murmushi da annuri bai bar fuskarta ba, haka kawai sai taji kamar tayi ihu tsabar murnar data samu kanta a ciki. Lokaci-lokaci kuwa tana duba k’ofar d’akin da Haydar yake ciki don ta k’ara tabbatarwa cewa ya dawo gareta. Tana gama cin tuwon ta wanko hannunta kana ta d’auko fruits d’in da Mas’ud ya kawo mata jiya ta fara sha bayan ta yayyankasu. Buga k’ofar falon da ake yi yasa ta tashi taje ta bud’e ta ga Mas’ud ne hannunshi d’auke da leda wanda ta tabbatar wani abun ya kawo mata. “Baka gajiya da d’awainiya.” Ta fad’a tana jefa kankana a bakinta sannan ta bashi guri ya shigo amma shi kuma ita yake kallo. “Kalti yau kina cikin farin ciki." Shine abunda ya fara fad’a yana ajiye ledan a kan dinning table. Zama tayi a kujera shima ya zauna yana kallonta yana murmushi, kafin ta bud’e baki tace wani abu suka ji an bud’e k’ofar d’akinta Haydar ya fito sanye da jumfa da wando har da hula sai zuba k’amshi yake yi. Mas’ud sake baki yayi yana kallon ikon Allah yana nuna Haydar da yatsa amma ya kasa cewa komai. “Ya dawo jiya da dare.” Laila ta bashi amsa duk da bai furta tambayar ba. K’arshenta Haydar ne ya iso gurinsu ya rufe masa bakin sannan Mas’ud ya farga ya daki kafad’arsa yana cewa, “Ina ka tafi duk tsawon wannan lokacin?” Laila na ganin hakan ta taso ta shiga tsakaninsu tana cewa, “Calm down Mas’ud. Abun bai kai haka ba.” Ya ma rasa me zai ce illa tsayawa da yayi yana ganin yanda Laila ta kare Haydar shi kuma yana bayanta yana aiko mishi da gwalo. “Dukana zaka yi ne?” Haydar ya fad’a yana barin bayan Laila yaje ya zauna kusa da Mas’ud wanda har lokacin bai daina kallonshi ba. “Daa zan iya daa yanzu na fasa maka baki amma saboda Kalti zan barka, so welcome back the runaway husband. Wato kai haka rayuwarka zata k’are daga a kaika d’akin matarka sai ka daka yaji?” “Wai a hakan kai kawuna ne.” Mas’ud na jin hakan yayi dariya kana ya mik’a mishi hannu suka yi tafa cikin farin cikin ganin juna. “I’m glad you are back man. Karka sake mana irin haka please.” “Kuyi hak’uri na sakaku a cikin zullumi, hakan ba zai k’ara faruwa ba.” Shima ya fad’a sincerely. “Kalti ki bashi abinci ya rame da yawa.” Fad’in Mas’ud yana jawo warmer d’in ya bud’e. Ganin farin cikin da Mas’ud yake ciki yasa Haydar yaji wani abu ya zo ya tokare mishi a makwoshi kamar zai sakashi hawaye, saboda irin wannan soyayyar yake burin gani ana yi mishi tun tashinsa. Meyasa ya tafi ya barsu bayan an sanar dashi cewa sune danginshi da ya dad’e yana mafarkin samu? Mas’ud ne da kanshi ya saka mishi tuwon a plate ya tura gabanshi yana cewa, “Ka cinye duka, ina son ka murmure kafin Ammi ta ganka.” Laila dake tsaye a gefe tana kallonsu sai taji ta k’ara son Mas’ud domin shi mutum ne wanda idan ya soka to zai soka ne da dukkan zuciyarsa kuma baya iya 6oyewa. Ta lura ya k’ara k’aunar Haydar tunda aka gane cewa shi d’in jininsu ne kuma d’an cousin d’insu. Sai da Haydar ya cinye tuwon sannan Laila ta kawo mishi bowl da ruwa ya wanke hannunshi yana kallonsu duka yace, “Irin wannan so da kulawan da ake nuna mini sai yasa in k’ara gudu gobe.” “Don’t even try it.” Fad’in Mas’ud. Laila kuma tace, “Zaka k’arisani kenan?” Murmusawa yayi ya kad’a kanshi kana yace, “Ina Ammi take?” Nan suka nitsu Laila ta musu jagora zuwa falo suka zauna, shi dai Haydar bin su yake yi da ido domin bai ga dalilin da zai sa daga tambayar ina Ammi take ba sai su nemi ya dawo falo a zauna, kenan magana mai muhimmanci za’a yi. Kasa hak’uri yayi dalilin zuciyarsa data fara tsoritashi a kan cewa ko Ammi tana kwance ne bata da lafiya yace, “Me ya samu Ammi?” “Babu abun da ya sameta amma bayan tafiyanka abubuwa da yawa sun faru Haydar, ciki har da bayyanar mahaifinka.” K’ura musu ido Haydar yayi yana karantar su, ganin babu alamun wasa a fuskarsu yasa yace, “Da gaske kuke yi? Ina mahaifin nawa?” Zuciyarsa kuma tuni ta tsananta bugu amma a waje sai ya dake yana jiran amsarsu. “Alhaji Abdul yayanka ne babanku d’aya.” “No, no. Ta yaya? Yaya hakan zai kasance?” Ya cire hularsa ya ajiye a gefe yana jin gumi na tsatstsafo mishi ta ko’ina a jikinshi. A nan Mas’ud ya fad’a mishi duk abunda ya faru bai rage komai ba sannan ya k’arisa da cewa, “Yanzu Ummii da Ammi suna can Maiduguri.” Shi kuma Haydar kallon Laila yake yi da yaji labarin har gayyatar Alhaji Abdul tayi gidanta bayan duk munafurcin daya mata ya lalata mata d’anta, yace, “Meyasa zaki nemeshi Laila? Bakya tsoron ya k’ara cutar dake?” “Yayi nadama Haydar, yana k’aunarka yanda baka tsammani a yanzu. Try and get to know him shi da Babanka a nan zaka gane irin son da suke maka bana wasa bane.” A nan itama ta bashi tarihin Alhaji Abdul wanda ya fad’a mata har ta yarda da cewa ba zai ta6a gigin cutar dasu ba. Shiru Haydar yayi yana tunani sannan yace, “Bazan ta6a yafe mishi halin daya saka Abul a ciki ba, wannan cutar tafi kowanne bak’anta mini rai Laila. Ya cuci rayuwarsa wanda hak’uri yayi kad’an ya gyara 6arnan da yayi. Zan nemi mahaifina amma tsakanina da Abdul babu zumunci har abada.” Shiru su Mas’ud suka yi domin a yanzu da yake kan gadon zuciya ko menene suka fad’a mishi ba zai sauraresu ba. Amma idan lokaci yayi shi da kanshi zai neme Abdul d’in saboda su ‘yan uwan juna ne wanda ruwa ba

Chapter 24 of 32