Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
safe k’arfe shida Laila ta gama karyawa ta d’auka ta nufi sashen Haydar. Sanin cewa ya rufe k’ofar dake tsakaninsu yasa ta d’auki makullin main door d’in dake waje ta fita kai masa abincin tunda jiya ya fad’a mata cewa zai yi tafiya. Tana bud’e k’ofar ta kutsa kai ciki ta isa inda take ajiye mishi abincin taga wanda ta ajiye masa jiya ma bai ci ba, d’akin da yake kwana ta nufa tana neman kalmomin da zata yi amfani dasu still ba tare da ta amince da abunda yake so ba. Tana son fahimtar dashi me take gudu ko wannan karon zai gane idan ya saurareta da kyau. Kwankwasa k’ofar tayi tana sallama amma ba’a amsa mata ba, murd’a hannun tayi ta shiga sai dai bata ga Haydar kamar yanda tayi tsammani ba. Ba dai har ya tafi ba? Shine zai tafi bai mata sallama ba? A kan katifar tashi taga kud’in daya ajiye mata wanda ta sani na cefene da kuma in buk’atarta ta taso ne. Zama tayi a bakin katifar zuciyarta na mata rad’ad’i domin kamar tana cutar da yaron. Ita kanta ta sani yana kula da ita da kuma nuna mata tsantsar soyayyar da take tunanin har abada ba zai iya had’a soyayyarta da wata ‘ya mace ba. Amma shin ita tana masa wannan k’ok’arin da kuma jajircewar akan sonshi? Ta masa adalci kuwa? Shin ta kyauta masa? Yaya zata yi? Kwantar da kanta tayi akan pillow tana shakar asalin scent d’inshi na d’a namiji wanda yake mata dad’i. A maimakon hakan ya sakata farin ciki ko ya yaye mata damuwarta sai k’ara mata yayi taji idanunta sun cika da hawaye, a take suka fara sauka ta gefen fuskarta tana tuno rayuwarsu da matsalolin da suka fuskanta tun daga ranar d’aurin aurensu har rana mai kamar ta yau. Haydar kuma suna isa Abuja suka sauk’a a Hotel mafi kusa da inda zasu yi aikin daya kawosu. Tafiyar ranar ya yishi ne cikin shiru wanda abokan aikinsa wanda suka fara mutunci suna tsokanarshi wai ko yayi missing Madam ne? Murmushin k’arfin hali ya musu kana ya rufe idanunsa tamkar mai bacci wanda hakan yasa suka daina tsokanarshi suka cigaba da tad’insu. Bayan ya kimtsa a d’akin da aka bashi ya sauk’a k’asa gurin receptionist desk ya kira Ammi da telephone d’in gurin. Bayan sun gaisa ya fad’a mata sun isa lafiya. “To Alhamdulillah, Allah ya amfana ya bada sa’ar abunda aka je nema. Amma meyasa baka yi amfani da wayarka ba?” Ta tambayeshi domin bak’uwar number da ta gani. “Wayar babu charge ne Ammi, kawai zamu dinga gaisawa ta nan yafi arha tunda ba biyansu zan yi ba.” Dariya tayi mai sauti kana tace, “Ban sanka da son banza ba Ali. Ka huta gajiya.” “Ammi.” Ya kira sunanta wanda yasa ta tsaya daga kashe wayar da tayi niyyar yi. “Na’am Ali. Yaya dai?” Ta tambayeshi cikin maida hankalinta kaf kanshi domin taji muryarsa ta canja. “Ina sonki Ammina.” Ya fad’i hakan cikin murmushi. Ajiyar zuciya Ammi ta sauk’e kana tace, “Shiririta kawai. Ka ga gwanda kai, domin ni abinci zan tashi na d’aura.” Itama zallar murmushi da farinciki a tata fuskar. “Eh naji you love me too. Sai anjima.” Da haka ya kashe wayarsa yana jin d’an dama-dama a ranshi. Laila bata tashi a gurin ba sai k’arfe goma na safe dalilin baccin daya d’auketa a gurin wanda bata yi ba a daren jiya. Sai da ta kimtsa masa d’akin sannan ta fita bayan ta d’auki rigar daya cire ta manna a hancinta tana shak’ar k’amshin jikinta. Da haka ta koma sashenta ta samu kiran mutane barkatai ciki har dana ‘yan shagonta. Duk missed calls d’in ta tsallake ta sauk’a kan sunan Ruwan Zuma ta kirashi, sai dai nan take matar tace mata wayar is switch off. A iya saninta Haydar Sim d’aya gareshi bashi da wata, to yanzu ta yaya zata sameshi? Tana wannan tunanin aka k’ara kiranta wanda Mas’ud ne yake fad’a mata Ummii bata da lafiya har an kwantar da ita a gadon asibiti d’azu da safe. “Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. A wani asibiti kuke?” Ta tambayeshi cikin kid’ima tana bud’e wardrobe d’inta ta d’auko hijabi. “In da muke kaita kullum.” Ya bata amsa kana taji ya fara magana da wasu a gefe. Hakan yasa ta kashe wayar ta saka hijabinta tare da d’aukan jaka ta saka duk abunda zata buk’ata a ciki kana ta fita daga gidan. Sai dai minti biyar da fitanta da dawo ta d’auki T-shirt d’in Haydar da ta d’auko daga sashensa ta manna a fuskarta ta k’ara fita. Ummii da jikin nata yayi sauk’i aka sallameta a ranar suka koma gida har da Laila wacce idan ta samu sarari sai ta kira layin Haydar wanda har lokacin a kashe take jinta. Bayan sun koma gida Mas’ud ya tafi ya bar Laila na kula da Ammi kafin Ya Madu ya dawo daga tafiyar da yayi shi da uwargidansa wacce dama ita ke kula da Ummiin. “Ummii meya faru ne ciwonki ya tashi?” “Allah ba zai jarabci bawansa da cuta ba sai da dalili?” Ta mayar mata da amsa cikin tambaya tana kwanciya akan gadonta da taimakon Lailan. “Naga wai sai ranki ya 6aci ne ko kuma kinga abunda bai miki ba.” “Laila tunda tace babu komai ki bar maganar kawai, tunda ta samu lafiya Alhamdulillah. Nima zan wuce gida, idan Ya Madu ya dawo ki kirani ki fad’a mini.” Fad’in Yayarta Ajidde wacce ke shirin tafiya. “Shikenan.” Da haka Ajidde ta musu sallama ta barsu zaune su kad’ai basa magana. Dama dangantakar dake tsakaninsu yana da rauni fiye da tsakanin Ummii da sauran ‘yayanta. Sai gab da magriba sannan su Ya Madu suka dawo wanda kai tsaye sashen Ummii suka shigo a lokacin da Laila ke tambayar Ummii, “Tun kwanciyarki asibiti banga amaryar Ya Madu ba, kuma naga da ita suka barku a gidan da kuma yara. Bata nan ne?” Ummii bata kula Laila ba illa k’ok’arin amsa sallamar Madu ta take yi duk da cewa muryarta bata fitowa sosai. Har cikin d’akin Madu ya shigo ya tsugunna a gefen gadon yana tambayarta lafiyar jikinta. Nan take Ummii ta fara hawaye wanda yasa hankalinsa ya tashi yana tambayarta meya sameta. Shi d’in ma bata fad’a mishi abunda yake damunta ba amma kalamansa yasa ta sauk’o ta daina hawayen kana ta juya musu baya alamar bata son damuwa. Laila dake tsaye a can gefe tare da Uwargidan Madu suna ganin komai ta bud’e bakinta ta gaishe da Yayan nata. Bai amsa ba kamar yanda tayi tsammani domin tun bayan aurenta da Haydar ya daina mata magana ya kuma daina amsa gaisuwarta. A take taji kamar ba’a buk’atarta a gurin, ita da mahaifiyarta amma tsakaninsu babu shak’uwan dake tsakanin d’a da mahaifiyarsa. Meyasa ita hakan ya kasance da ita? Sallama ta musu ta fita tana jin duniyar ta mata zafi domin a yanzu ta rasa tudun dafawa ga damuwa sun taru sun mata yawa. Bayan rashin Abul da halin Ummii yanzu kuma ya had’u da cewa Haydar ma na fushi da ita wanda a yanzu ta gane kashe wayar yayi don kar ta nemeshi. Mas’ud ne abokinta kuma mai taimaka mata a irin wad’annan yanayin da take shiga, to shima yanzu yayi aure wanda bai kamata da k’ara masa damuwa akan na iyalinshi ba. Ina zata yi? Wa zata samu suyi magana? Tana shiga motarta ta kama hanyar gida, sai dai kafin ta isa ta canja akalar motarta ta kama hanyar gidan Ammi wacce take tsammanin ita ce kad’ai zata iya magana da ita taji sauk’in abunda take ji a zuciyarta. A bakin k’ofar gidan tayi parking kana ta fito hannunta d’auke da kayan lambun da ta tsaya ta sayawa Ammi. Da sallamarta ta shiga gidan ta samu Ammi na sallah Magriba. Abun hannunta ta ajiye kana itama ta d’auki buta ta kewaya band’aki ta fito. Tana cikin alwalan tana tunanin mijinta taji muryar Ammi daga can gefen da take. “Hajiya kune a gidan namu?” Murmushi Laila tayi kana ta maida idonta kanta tace, “Wallahi kuwa Ammi.” “Marhaban sannunki da zuwa.” Ta fad’i hakan tana tashi tsaye ta d’auko mata tabarma da sallaya a d’akinta zata shimfid’a mata. Ganin haka yasa Laila tayi saurin isa gurinta ta kar6a ta shimfid’a da kanta dama ta gama alwalar. Sai da Laila tayi sallah sannan ta gaishe da Ammi wacce ke jingine da bangon d’akinta tana kallon Lailan. Bayan sun gama gaisawa Ammi ke cewa, “Ali kuma sai yayi tafiya Abuja? Yau da sassafe ya shigo ya mini sallama tare da fad’a mini tafiyar da zai yi.” “Wallahi kuwa.” Fad’in Laila tana sunkuyar da kanta k’asa domin bata so Ammi ta mata wata tambaya akan Haydar ta kasa bata amsa har ta fahimci halin da suke ciki. “Alhamdulillah tunda sun isa lafiya. Munyi waya d’azu bayan sun isa.” Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e domin an amsa mata tambayarta ba tare data furta ba. Wai duk dama cewa tunanin abunda ya faru da uban ‘yayanta yayi sauk’i a zuciyarta dalilin tsawon lokacin da aka d’auka, bai hanata jin d’arr ba matuk’ar wani nata yace zai yi tafiya. Basu jima ba Ammi ta kawo musu tuwo wanda Laila tace ta k’oshi, Ammi bata matsa mata ba ta kawar da abincin gefe suka cigaba da hiransu wanda jefi-jefi suna sako maganar Haydar wanda Laila ke jin dad’in hakan kwarai. Sai bayan isha Ammi tace ta koma gida kar dare ya mata a hanya tunda mijinta baya gari. Laila da bata so hakan ba ta tashi ta mata sallama amma a ranta ta ayyana zata dawo washegari domin magana da Ammi na yaye mata k’uncin da take ciki. Bayan ta koma gida ta gama abunda zata yi ciki har da kiran Ummii domin jin yanda jikinta yake, kana tayi shirin kwanciya ta jawo wayarta ta kira Haydar. ‘The number you have dialed is switch....’ Kafin matar ta k’arisa Laila har ta kashe wayar tare da jifa da ita kan gadon. Me yake nufi da zai kashe wayarsa? Fushin nashi har ya kai ya k’i yin magana da ita bayan yayi tafiya? Gyara kwanciyarta tayi kana ta kashe wutan d’akin tana jin zafin abunda Haydar ya mata. K’arar da wayarta take yi yasa tayi saurin mirginawa ta d’auka tana tunanin me zata fad’awa Haydar ya gane bai kyauta mata ba. Bak’uwar number ta gani wanda tayi saurin d’auka tace, “Salamu alaikum.” “Mama.” “Abul.” Itama ta kira sunanshi wani abu kamar kibiya na sukarta a k’ahon zuciyarta. “Kina sha’aninki kin manta dani ko? Watak’ila ma murna kike yi dana tafi na baku guri ke da mijinki.” “Allah ya shiryeka Abul, Allah ya nuna mini ranar da zaka yi hankali ka gane kanka kake cuta ba kowa ba.” Ta fad’i hakan tana jin hawaye na taruwa a idonta ba tare data bari muryarta ta canja ya gane ba. “Zaki jima kuwa.” Da haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo domin ya jima bai kirata ba. Sannan ta sani ko da ta kirashi bazata sameshi ba sanin kashe wayar zai yi ya kuma jefar da layin. A hankali wannan karon ta ajiye wayar abubuwan daya faru a ranar na yawo a kwanyarta, da suka mata yawa ta fara zubar hawaye tana addu’an Allah ya gyara mata rayuwarta ya yaye mata bak’in cikinta. Awannni uku da haka ta mik’e tsaye kamar wacce aka yiwa duka ta isa bakin mirrow inda ta ajiye jakar data fita dashi. Rigar Haydar data saka a ciki ta ciro kana ta shimfid’a akan pillow d’inta ta kwanta tana mamakin wannan sudden addiction d’in. Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (37) “Yanzu kam kin daina zuwa shago ko?” Ammi ta tambayi Laila wacce ke zaune a gefenta tana mata yankan alayyaho. Laila ta dakata da abunda take yi na wasu sakanni sannan ta murmusa tace, “Ina buk’atar hutu ne shiyasa na barwa Sabrin kula da gurin. Na fara damunki ko Ammi?” Ta k’arishe maganan cikin zolaya. Ammi ta dara tace, “Ni bance ba, naga yau kwana hud’u kenan a nan kike yini tun safe sai dare zaki koma gidanki. Ai bazan k’i abokin hira ba tunda kin d’auke mini Ali.” A kunyace Laila ta sunkuyar da kanta tana murmushi amma bata yi magana ba. Ko da Ammi ta lura da hakan sai ta canja musu hiran tana cewa, “Yanzu kam ya kamata in ziyarci mahaifiyarki mu gaisa, yoo in ba don zamani ya kawomu irin wannan lokacin ba ya za’a yi ace bamu ta6a had’uwa ba alhali ‘yayanmu na auren juna? Na fad’awa Ali ya kaini tun aurenku baiyi sati biyu ba amma kullum sai yace mini sai ya shirya. Inaga kawai gobe ki rakani mu je tunda shi bai san yakamata ba.” “Ammi nace wai da kin bari sai ya dawo d’in kawai. Kinga kar yace munyi abu ba tare da sanin shi ba. Watak’ila akwai abunda yake son aiwatarwa ne kafin nan.” Fad’in Laila cikin sauri domin bata son k’ara aikata wani abu da zai tunzura Haydar. “Ke d’in ma biye mishi zaki yi? Shikenan sai muyi ta zama haka har sai lokacin da kuka ga dama.” “Ammi ba haka bane wallahi, Ummii ma tana son zuwa gurin naki to ita ba lafiya ne ya isheta ba shiyasa aka hanata fita unguwa. Amma da zarar ya dawo zan tuna masa in nuna masa ya dace ku gana d’in. Kiyi hak’uri.” “Babu komai, Allah ya dawo dashi dai lafiya.” “Ameen.” Laila ta amsa kana tabi wayar Ammi da ido wacce ke ruri. Ammi ta d’aga wayar ta kara a kunnenta bakinta d’auke da sallama. Laila na ganin yanda fuskar Ammi ta washe ta tabbatar Haydar ne ya kirata domin kullum sai ya kirata, a gabanta zasu gama hiransu ya kashe. Idan Ammi ta masa magana cewa ga Laila a gidanta sai yace zai kirata da dare lokacin da suke waya, alhali bai ta6a kiranta ko sau d’aya ba. Bayan sun gama wayar Ammi ta dubi Laila tana fara’a tace, “Kinji wai gobe zasu dawo ko?” Laila da taji maganar a bazata sai ta maske tace, “Haka dai yake fad’a mini.” “Me tsakaninku da Ali ne Hajiya Laila? Dukkanku na lura akwai wani abu da kuke 6oye mini.” Daburcewa Laila tayi domin bata yi tsammanin Ammi ta gane akwai matsala tsakaninsu ba. Kararen alayyahon data gama yankawa ta fara tattarawa tana turasu cikin leda amma zuciyarta bugawa take yi had’e da jin kunyar Ammi wacce ke kallonta tsam. “Ammi ba wani abun tashin hankali bane, rashin fahimta ce amma Insha Allah zamu gyara.” Ta fad’a ba tare data bari sun had’a ido ba. Girgiza kai Ammi tayi tace, “Na sani wani lokaci Ali yana da zuciya, don haka ke sai kiyi amfani da naki hak’urin da aka san babba yana dashi. Wallahi bana son ko sau d’aya naji wani abu ya faru tsakaninku, burina ku dauwama cikin farin ciki da walwala. Duk da bansan laifin waye bane kuma bana son ji zan mishi fad’a dole, bana son yawan fushinsa yayi yawa.” “Ammi ba tarar numfashinki nayi ba amma daa kin bari kar kiyi masa magana, domin zai gani kamar k’ararsa na kawo.” Fad’in Laila cikin magiya domin bata son koda wasa Ammi ta san dalilin fad’ansu domin bazata ta6a goyon bayanta ba, saboda ita uwarsa ce kuma itama tana da burin ganin jikokinta. Kai duk wand’anda ma ta sani baza su bata gaskiya ba, dalilin ba lallai su gane halin da take ciki ba. “Na bari. Allah ya daidaita tsakaninku amma don Allah ku dinga hak’uri kuna kai zuciya nesa.” “Ameen Ammi. Kuma Insha Allah zan gyara.” Suna idar da sallar la’asar Laila ta tattari kayanta tace zata tafi gida, Ammi ta rakota har bakin k’ofa suka yi sallama. Wani irin d’okin ganin Haydar Laila take yi, sai take ganin kamar goben ya mata nisa. Ko data koma gidan kasa aikata komai tayi domin gidanta a gyare yake, girkin da zata tareshi dashi kuma dole zai gobe zata yi. Haka kawai taji tana son burgeshi idan ya dawo don haka ta nemi ganyen zogale ta markad’ashi da wani ajiyayyen nonon rak’umi, tasha tana toshe hanci tana tsayawa. Bata jima da sha ba taji danshi-danshi a jikinta amma ba wanda take muradi ba, cikin sauri ta shiga band’aki ta duba jikinta taga al’adarta ce ta dawo kenan wannan watan ma ta tsallake rijiya da baya ruwan gishiri yayi amfaninsa. Duk da cewa taji dad’in hakan amma ta wani guri bata so hakan ba wanda ya sakata cizon yatsa. Washe gari tun da safe masu aikinta suka gama mata sharan gidan, itama ta shiga side d’insa ta share masa had’e da canja masa bedsheets. Kafin azahar ta gama duk abunda zata yi na tar6an mijinta Ruwan Zumanta sai jiran isowarsa kad’ai take yi. Kwalliya da shigar da tayi har ita kanta sai data yaba. Tana zaune tana jin nishad’i ta tuna rana irin haka da take jiran Aliyu ya dawo gareta amma sai sak’on mutuwarsa aka kawo mata. “Allah kaji k’aina kar ka jarabceni da mutuwar miji again, Allah ka kareshi mini shi a duk inda yake.” Ta fad’i hakan a bayyane tana d’aga hannunta sama. Tun tana zaune zaman gayu har ta kishingid’a dalilin gajiyar da tayi da zaman jiranshi, ya kamata ace daga Abuja zuwa Kano ya iso ko da kuwa basu taso da wuri ba. Farkawa tayi daga baccin daya d’auketa jin ana buga k’ofar falonta. Yaushe bacci ya d’auketa? Shine bata sani ba. Rigar Haydar dake kan cinyarta ta 6oye bayan throw pillow dake kan kujeran kana ta gyara kallabinta da zaman rigarta ta tashi ta bud’e k’ofar da murmushi a fuskarta sanin cewa Haydar ne tunda ta bar key a jikin falonsa ta ciki yanda bazai iya bud’ewa ta waje ba. Annurin fuskarta ne ya d’auke ganin Mas’ud tsaye a bakin k’ofar wanda daga ganinshi kamar a birkice yake. Apology letter data rubutawa Haydar wanda zata bashi ta jefar a k’asa kana ta rufe bakinta da tafukan hannayenta tana zare idanu wanda nan take suka cika da hawaye. “Kalti lafiyanki?” Fad’in Mas’ud cikin sauri ya nufota yana kama hannunta d’aya. “Shima ya mutu ko?” Tayi saurin tambayarsa tana kwace hannunta daga nashi. “Waye ya mutu? Wai lafiyanki kuwa? Me yake faruwa?” Ya tambayeta cikin d’aga murya domin abun nata ya fara d’aga mishi hankali. “Haydar, Haydar d’ina. Ina yake?” Sai a lokacin ya gane me take nufi yayi ajiyar zuciya yace, “Kalti babu abunda ya samu Haydar, asalima yana nan lafiya a Abuja. Ki daina kawo irin haka a zuciyarki.” Minti biyu da haka ta dawo cikin hayyacinta bayan Mas’ud ya fad’a mata cewa yanzu suka gama waya da Haydar wanda shine ma ya aikoshi. “Ban gane ya aikoka ba. Shi d’in ina yake? Yau yace zai dawo fa.” Ta fad’i hakan tana yarfe hannu domin ta daina gane komai. “Kud’i ya turo mini yace in kawo miki kuma in kaiwa mamanshi domin zai k’ara kwana biyu ko uku kafin ya dawo. Ina bacci ya tasheni wallahi ko abincin rana ban ci ba yau ina hutawa a gida.” Laila bata k’ar6i kud’in ba illah tashi da tayi ta nufi d’akinta tana jin zafi a ranta, kenan duk shirin da tayi ya tashi a banza? Meyasa ba zai kirata yace ya fasa dawowa ba? Kuma yaushe ta fad’a masa cewa tana buk’atar kud’i? Shi take so take kuma buk’ata ba kud’i ba. “Kalti yaya dai?” Mas’ud ya tambayeta yana tashi tsaye shima yabi bayanta. A bakin gado ya sameta ta d’auki wayarta tana dannawa can kuma ta kara a kunnenta. Abu aka fara fad’a ta cikin wayar tayi saurin ajiyeshi a gefenta tana dafe kanta. “Kalti Meya sameki kuma wai me yake faruwa ne? Me haka?” “Kawai zuwan naka ne triggered some memory.” “Shi ya matsa mini in kawo miki kamar wacce kika ce baki da ko sisi a hannunki. I’m sorry.” “It’s ok ba laifinka bane. Nima lokaci yayi da zan cire wancan abun a zuciyata.” “Amma akwai wani matsala bayan nan ko?” Girgiza kanta tayi tana d’age hannunta daga fuskarta. “Tell me Kalti. Ina gane yanayin ki. Wa kike dashi wanda zaki fad’awa damuwarki sama dani? I’ll always be your best friend, so tell me.” “Haydar haihuwa yake so ni kuma bana so shine ina taking birth control ya ganni yayi fushi.” Ta fad’i hakan cikin sauri kuma cikin numfashi d’aya tamkar wacce aka shak’eta ta fad’a. “Kina nufin ba yanzu kike son haihuwan ba kenan?” “I mean not ever.” Ta fahimtar dashi. “Wasa kike yi ko?” Ya tambayeta yana murmushi. Kallonsa tayi fuskarta babu alamun wasa tace, “Babu maganar wasa Mas’ud.” Murmushin dake fuskarsa ce ta gudu nan take, ya gyara tsayuwarshi yace, “Saboda meyasa kenan? Baki da lafiya ne?” “Lafiyata kalau, amma Mas’ud ko kaine zaka bani shawarar k’in haihuwan dalilin na girma, gashi na aurar da ‘yata wacce itama kwanan nan zaka ji ance tana da ciki. Sannan ga matsalolin dake gabana da yawa bana son k’arawa kaina wani abun.” Mas’ud ya hard’e hannayensa kan k’irjinsa ya zuba mata ido ba tare da yace uffan ba. Ganin haka yasa Laila taji ta tsargu ta kawar da kanta gefe tana cewa, “Kayi shiru baka ce komai ba ka tsura mini ido.” “Ina tuna yaushe kika zama irin haka ne.” “Irin haka.... kamar yaya kenan?” “Mutum mai son kansa.” “Dama nasan ba dole ku goyi bayana ba saboda babu wanda yasan me nake fuskanta kullum idan na fita cikin jama’a. Kowa kanshi ya sani.” “Maganar jama’a yana kan kowa har da su jama’ar masu yi basu tsira ba, kenan idan kika biye musu numfashi wannan sai kin daina domin wani cewa zaiyi kin fi kowa shak’ar iskan. Ban san ko kina da wata hujja ba amma wanda kika fad’a mini ban d’aukeshi a matsayin hujja ba.” Bata k’ara cewa komai ba har ya gama tsayuwarsa yace mata zai tafi. “Ka gaishe da Naana.” “Zata ji. Amma ki zauna ki nitsu kiyi tunanin wannan al’amarin Kalti. Ana aure ne don ibada kuma don a hayayyafa, Haydar da yake matashi kuma wanda bai taso cikin ‘yan uwansa ba zai so ganin ya haihu. Idan kuma kika hanashi haihuwa bana tunanin Allah zai yi farin ciki dake domin ba rashin lafiya mai barazana ga rayuwa ce zata hanaki haihuwa ba illa wani reason d’inki mara ridge. Idan kuma da gaske bakya son haihuwa sai ya k’ara aure ya kawo yarinyar da zata tara masa ‘yaya ke kuma kuci gaba da zama a haka. Amma in hakan bazai yiwu ba to gaskiya kullum zaku rayu ne cikin rashin zaman lafiya da tashin hankali.” “Yayi duk abunda yake so ni bazan hanashi ba.” Shine kad’ai abunda ta fad’a cikin zafin rai. Mas’ud yayi mamakin duk zancen daya gama fad’a bata amsa ko d’aya ba sai wanda yace Haydar ya k’ara aure. Murmusawa yayi wanda bai kai zuci ba amma a gaba yana hango draman da za’ayi idan Haydar yayi niyyar k’ara aure. “Halinku duk d’aya; ga can Naana ma tana wata maganar banza wai sai mun shekara kafin ta d’auki ciki wai kafin nan mun k’ara sabawa mun san juna! Can you imagine? Wani irin sabo ne wanda ya wuce mu zama ma’aurata muna sharing shimfid’a d’aya? Na rasa gane me yake damunku da k’in haihuwa alhali mazajenku na so kuma they can take care of the child expenses na rayuwarsa gaba d’aya. Wallahi daa ba don bani da ra’ayin mata biyu ba dana k’ara aure bayan aurenmu da sati d’aya. Banga amfanin k’in haihuwa da wurin ba tunda dama don a hayayyafan akayi auren, ku canja halayenku amma ko nine bazan d’auki wannan zancen ba Kalti. Ke babba ce kin girma kinsan mecece rayuwa, idan har zaki yarda ki bud’e idanunki ki ga gaskiya kema zaki san baki kyauta masa ba, sam baki mishi adalci ba.”

Chapter 14 of 32