yawan kiranta da wannan sunan, ta kuma tsani sunan da dukkan zuciyarta.
Kwana biyu suka yi basa kula juna sannan daga baya suka sasanta, sai dai duk da hakan bata daina tambayarshi yaushe zai amince mata ba, shi kuma sai ya samu sabon salo na fad’a mata cewa wai ba yanzu ba.
Yau dai gashi sun sake a karo na uku, wanda alama ya nuna ranshi ya 6aci sai dai itama ranta ya 6aci. Tana masa biyayya ba tare data dubi yawan shekarunta ba, tana k’ok’arin ganin bata karya dokarshi ko ta munafurceshi ba domin zata iya zuwa tayi ba tare daya sani koya gane ba. Sai dai ai Allah na ganinta, abunda akayi a rashin gaskiya kuma dole watarana sai Allah ya bankad’a sirrin, abunda zai biyo baya kuma ba dole a san adadin illan da zaiyi ba.
Haydar yana fita ya tari achaba ya kaishi gidan Ammi wanda dama yau da yake asabar ne bai je ya gaisheta ba.
A cikin d’akinta ya sameta da Meenat suna hira suna dariya, wanda hakan ya masa dad’i ba kad’an ba, domin bayan ya rabata da waccar mata mai ‘yayan sai ya zamana Meenat yini take a gidansu sai dare take komawa gidansu.
Bayan Meenat ta gaisheshi ta fita daga gidan tana cewa Ammi,
“Zan dawo anjima.”
Sai data fita sannan Haydar ya zauna a kan kujeran daya mata guda biyu wanda zasu iya shiga d’akin nata. Bayan ya gaisheta yake cewa,
“Wai meyasa kullum idan nazo sai ta fita daga gidan kamar wacce zan gutsireta?”
“To kai daka k’ita don meyasa zata zauna tare da kai alhali tasan ba aurenta zaka yi ba?”
“Namiji mijin mace hud’u ne kuma ba’a san gaba ba.”
“Sai ta zauna jiran taga me gaban zai haifar tana sauraronka ko? Yaushe ma kayi auren da har zaka fara maganan k’ari. Haydar bana son jaye-jaye fa.”
Dariya yayi yana cewa,
“Ammi ni na fad’a miki zan k’ara aure? Cewa nayi namiji mijin mace hud’u ne, kuma ba’asan me gaba zata haifar ba.”
“Hmm.” Kawai tace tana kallonsa.
Canja musu hiran yayi a nan take tambayarsa batun Abul d’an matarsa Laila.
“Har yanzu shiru babu labarinsa Ammi. Amma yana kiran Maman nashi wai yaji ko ta kashe aurenta ya dawo.”
Ammi ta tafa hannu tana salallamai kamar yau ta fara jin hakan tace,
“Yau ka gane mini k’addara don Allah. Tausayinta nake ji sosai wallahi. Kullum na kawo mata zancen sai naga fuskarta ta canja wanda uwa ce kad’ai zata gane halin da take ciki. Allah yasa taci wannan jarabawar, shi kuma Allah ya bayyanshi ya kuma shiryeshi.”
“Ameen Ammi.”
“Jiya bayan tafiyanka da yamma Maman Zunnu ta kawo mana ziyara.”
“Ammi bazaki rabu da wannan matar ba ko?” Fad’in Haydar yana jin ba dad’i a ranshi.
Ya zo gidanta ne don ya huce daga abunda ya faru tsakaninshi da Laila amma itama da alama zata tura mishi wani. A wancan lokacin ya samawa matar gidan haya ya kuma bata jari daidai aljihunsa kan ta fara sana’a ta dinga ciyar da ‘yayanta. Sai dai Ammi bata so hakan ba domin taso su zauna ne tare, bayan tafiyarta kullum maganar Ammi Maman Zunnu wanda tasan Haydar baya son ji. Haka kawai ya tsani matar har cikin zuciyarsa ba tare da shi kanshi yasan dalili ba.
“Ya za’ayi In rabu da ita? Ai mutum rahama ne balle ita abun tausayawa. Ni ya kamata ma inje in dubosu tunda sau d’aya na ta6a zuwa gidan.”
Yana jin hakan ya mik’e tsaye domin gidan har ya gundureshi.
“Zan koma gida akwai abunda zan yi.” Da haka ya mata sallama ya fita daga gidan ya koma gidansa.
Daga bakin k’ofa yake jin hayaniya wanda yasan bana kowa bane sai Umma Kakar su Abul, tun 6acewar Abul yau zuwanta na hud’u kenan gidansu tana musu d’iban albarka. Ya so kai k’ararta gurin hukuma amma Laila ta nuna bata yarda ba domin Umma was once her mother in-law, ko menene take mata bai kai ta kaita gurin hukuma ba, ai abun da kunya da kuma nauyi ace ta kai mahaifiyar Aliyu police station.
Yana shiga ya samu Laila zaune a kan kujera ta sunkuyar da kanta k’asa tana sauraron zagi da cin mutuncin Umma, wanda a kullum tazo haka zata gama bambaminta Laila bata cewa ko kanzil. Sai shi Haydar d’inne yake magana idan yaga abun ya fara mishi yawa.
Wayarsa ya ciro yayi dialing number Nazifi wanda ringing biyu ya d’auka yana cewa,
“Umma tana gidanku ko?”
“Eh, ta zo.”
“Kuyi fa hak’uri zan zo na d’auketa. Basa ankara take fita ba tare data fad’a musu inda zata je ba.”
Minti goma da haka Nazifi ya shigo gidan bayan Haydar ya masa iso.
“Munafukai, algungumai. Nasan jikana bazai 6ata haka kurum don kinyi aure ba, waya sani ko sayar dashi ko tsafi kika yi dashi don aikata mugun nufinki? Lamla tsakanina dake Allah ya isa ban yafe ba, wallahi nayi dana sanin aurenki da Aliyu yayi, Allah kar ya k’ara nuna mini bak’in rana irin ranar da Aliyu ya had’u dake. Kin cuceni kin salwantar da rayuwar jikana. Allah ya isa muguwar mata mai bak’ar aniya.”
“Umma ya isa haka don Allah. Kizo mu tafi.” Fad’in Nazifi yana isa gurinta ya kamo hannunta.
Ai da sauran k’arfinta ta fisge hannunta, fad’an kuma nan take ya dawo kanshi.
“Ni yarinya ce da matsiyacin can zai kiraka kazo ka mayar dani gida? Me kuke d’aukeni? Wallahi Nazifi idan ka sake matsa mini sai na d’aga maka nono. Saboda rashin zuciya irin taka d’an k’aninka suka sayar amma ka kasa d’aukan mataki a kansu. Da Aliyu ne yake da rai sai inda k’arfinsa ya k’are akan iyalinka amma kai har na fara tunanin har da had’in bakinka a ciki.”
Wannan magana ta Umma ya sosa ran Nazifi domin tana yawan masa gorin da kuma nuna masa tafi son Aliyu a kanshi. Shekaru sun yi yawa wanda shima har ya fara tsufa amma har gobe yana jin zafin kwatantashi da take yi da k’aninshi.
Laila tana jin hakan ta tashi ta shige d’akinta ba tare da Umma ta lura ba domin tasan Nazifi bazai ta6a bari ta bita cikin d’akinta ba. Haydar kuma da yake zaune yana danna wayarsa bai ko d’ago ya kallesu ba domin har ya saba da cin mutuncin Umma kuma duk abunda ta fad’a baya kai zuciyarsa balle ya 6ata masa rai, shi dai hayaniyar ce baya so sannan ya k’i jinin ta d’agawa matarsa hankali.
“Allah ya huci zuciyarki Umma, amma ya kamata mu tafi gida ba wai tilasta miki zan yi ba.” Fad’in Nazifi ciki rarrashi.
Fashewa tayi da kuka alamar itama ta gaji da maganan tana son hutawa, da haka ya jata suka fita waje tana tsinewa Laila da Haydar albarka da kuma zuriyarsu gabad’aya.
Minti biyu da fitarsu gidan yayi shiru, Haydar da yake danna waya bai san ma Ina yake shiga ba domin hankalinsa na kan Laila wacce ya sani yanzu haka tana can tana kuka. Zuciyarsa ce ta karye na tsantsan tausayinta domin dalilin aurensa da tayi duk wannan abun yake faruwa.
Mik’ewa yayi ya shiga d’akin ya sameta kwance a kan gado tana share hawaye a fuskarta. Zama yayi a gefenta kana ya d’agota ta zauna tana rufe fuskarta wanda ya 6aci da hawaye.
“I’m sorry domin nina jawo miki hakan. I’m so sorry.”
Bata ce komai ba sai dai kukanta daya yawaita wannan karon har numfashinta na sark’ewa. Hugging d’inta yayi tsam a jikinsa yana buga bayanta a hankali yana kwantar mata da hankali.
“Karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki domin hakan take so ya kasance. Abul kuma da yardar Allah zai dawo gareki kuma ya shiryu. Don Allah ki daina kukan nan domin har cikin zuciyata nake jin zafin hakan.” Ya d’ago fuskarta zai share mata hawaye ta kawar da kanta tana sharewa da hannunta.
“I’m so sorry.” Da haka yaci gaba da lallashinta har ta kimtsa kanta sannan ya bata maganin ciwon kai ta sha bayan ta fad’a mishi kanta na ciwo. Kwanciya tayi ta rufe idanunta shi kuma ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa.
Da yana da iko daya binciko duk inda Abul yake a duniya ya kwankwasa masa hankali a kwakwalwarsa ko don Laila ta daina damuwa. Yana yawan tunani da kuma jin zafin gudun Abul wanda idan ya tuna har d’aci yake ji a mak’oshinsa, hakan yasa yake k’ara tausayawa Laila domin yasan abunda take ji ya ninka nashi sau dubu saboda ita d’in uwa ce. Shi kanshi ya sani ba k’aramin k’okari take yi wajen ganin abunda ya faru da ita ya shafi aurensu ba, yasan tayi jarumtaka kuma ta cancanci duk wani farin ciki na duniya saboda hak’urinta.
Yana zaune a gefenta har bacci ya d’auketa tana rik’e da kanta wanda tace yana sara mata kamar zai tsage. Addu’a ya mata kana ya tofa mata a kan nata ya tashi ya fita daga d’akin don d’aura musu abincin rana, zuciyarsa kuwa cunkushe take da tunani kala-kala da kuma neman mafita ta wata hanya daban.
Kwana biyu da haka Laila ta dawo normal yanda take, wanda dama duk ranar da Umma tazo sai mode d’inta ya canja na wasu kwanaki.
Haydar bai yi k’asa a guiwa ba ya nemi biyan buk’atarsa ta kuma bashi kanta ba tare data masa maganan Planning ko wani abu ba. Sai dai yana gama abunda zai yi ta tashi ta d’aura zaninta ta fita zuwa kitchen. Curiosity yasa ya bita a baya domin a daa takan d’an huta kafin ta tashi ta shiga wanka.
A kitchen ya samu ta jik’a ruwan gishiri zata sha.
“Laila me wannan d’in?” Ya tambayeta yana k’ar6an kofin daga hannunta.
Bata nuna ta razana ba illa ficewa da tayi ta barshi a kitchen d’in yana rik’e da kofin nata. Bin bayanta yayi yana tambayarta tayi shiru bata ce dashi komai ba, shiga band’aki tayi yabi bayanta yana cigaba da demanding dalilinta na shan ruwan gishiri. Mutuwa take son yi ko dai maganin hana d’aukan ciki ne?
“Magana nake miki kinyi banza dani, me zaki yi da ruwan gishiri?”
Laila ta kunna shower ta fara wanka bayan ta juya mishi baya.
“Duk abunda zaki yi baza ki hana hukuncin Allah ba Laila. Sannan baza ki hanani haihuwa ba domin ina so sai dai in Allah ne yayi bazan haihu ba. Sannan idan kika k’ara amfani da maganin hana d’aukan ciki na barki da Allah.” Yana gama fad’in hakan ya ajiye mata k’ofin nata a k’asa ya fita daga band’akin yana jin wani irin mugun zafi a zuciyarsa.
Wardrobe d’insu ya bud’e ya ciro kayansa kaff da yake ciki ya kaisu d’akin Mas’ud na da, wanda babu komai a ciki sai katifa da wardrobe. Da haka ya dawo ya d’auki sauran tarkacensa Laila na kallonshi bata ce mishi uffan ba domin itama haushinsa take ji bana wasa ba.
Dawowansa na biyu ya shiga band’aki ya d’auki abubuwansa dake ciki ya fito zai fita tace,
“Ina zaka je?”
“Away from you tunda kin tsaneni.” Kafin ta k’ara yin magana ya fita.
Zama tayi a bakin gado tana jin duniyar ya fita a kanta dalilin halin da suka tsinci kansu da kuma aurensu a ciki. Dama akwai ranar da Haydar zai iya raba musu makwanci? Meyasa ya kasa fahimtarta? Saboda shi an daina tsokanarsa da kuma aibatashi akan aurenta da yayi? Har yanzu, kuma har gobe wasu mutane basu fasa yi mata bak’ar magana kan auren Haydar da tayi ba. Ya zata d’auki cikinshi tayi yawo dashi mutane na nunata da yatsa ana cewa yaro ne ya mata ciki? Da girmanta ta yaya zata iya haihuwa? Ga uwa uba ‘yarta Sabrin wacce itama yau ko gobe za’a iya cewa tana da ciki. Ina zata kai wannan abun kunyar ace tana tura cikin Haydar, Sabrin ma na tura ciki? Surukinta yazo gaisheta ya ganta da ciki yana yana ayyanawa a ranshi Haydar ne ya mata. Wannan abun kunya har yaushe? Yanzu ma da take aurenshi bata huta ba, idan kuma ta kuskura tayi ciki abun zai fi haka domin Umma ma kad’ai ta isa tasa taji ta tsani duniyar da duk abunda yake cikinta.
Bata shirya d’aukan ‘yayansa ba, kuma bata tunanin zata iya haihuwa dashi. Yayi hak’uri ya zauna a haka ko kuma suyi adopting yaro ko yarinya daga Orphanage.
Ko dai zai ce zai k’ara aure tunda ta k’i haihuwa dashi? Saurin girgiza kanta tayi dalilin d’acin da taji a mak’oshinta data hasko wata mace tare da Haydar d’inta ba ita ba.
“Ba zai iya rayuwa da kowacce mace ba sai ni.” Ta furta da fatar bakinta wanda ya isa kunnenta ya aikawa kwakwalwarta ita kuma ta hau kan zancen ta zauna daram da6es.
“Ni kad’ai na isheshi rayuwa domin ina da tabbacin ba zai iya had’a soyayyata da kowacce mace ba.”
WATA RAYUWA...
Abul ne tsaye a bakin wani chemist sanye da kod’addun kaya yana jiran mutanen da suka zo sayen magani su watse kafin ya shiga ya sayi abunda ya kawoshi.
Idan ka ganshi a wannan lokacin bazaka ta6a cewa shi bane dalilin rama da kuma kod’ewar da yayi wacce ta saka ya zama baki kamar wanda ya k’one a gobara.
Fuskarsa ta tanik’e kumatunsa sun burma ya zama tamkar k’ashi da rai yana yawo kwararo-kwararo neman abinci da kuma kud’in da zai sayi kayan maye. Abunda ya faru a rayuwarsa a baya shi kanshi baya son tunawa dalilin bak’ar wahala da azabar da yasha.
Yana nan tsaye har mutane suka k’are sannan yaja k’afarshi da yake d’ingisawa ya shiga Chemist d’in.
“A bani Codein.” Shine abunda ya fara fad’a musu bayan ya shiga.
Wani irin wawan kallo masu shagon suka watsa masa sannan d’aya daga cikinsu wanda daga ganinshi kaga Ustaz yace,
“Akwai amma ba zamu baka ba saboda amfani dashi da zaka yi ka 6atar da hankalinka. Ka gyara rayuwarka ka tuba zuwa ga Allah domin wannan rayuwar daka jefa kanka a ciki baza ta haifar maka mai kyau ba.”
“Banza shashasha. Wa’azin uban me zaka mini da wani gemunka kamar bunsuru ka d’agashi sama kana mak’e murya? Idan ba zaku sayar mini ba akwai Chemist dubbanni da zasu sayar mini.”
D’ayan mutumin wanda k’ani ne ga wanda Abul ya zaga ya tashi a zuciye zai gaurawa Abul mari yayanshi Ustaz d’in ya dakatar dashi.
“Idan kace zaka dinga saurin 6ata rai da irinsu to da kai dasu baku da banbanci, idan basu da hankali kai kayi amfani da naka hankalin kar ka biye musu.”
“Yen yen.” Fad’in Abul yana barin shagon bayan ya tofar musu da yawu a bakin k’ofa.
“Yaya kana gani ya zubar mana da yawu kan tiles?”
“Ka barshi, ka kuma mishi addu’a Allah ya shiryeshi domin yana cikin jarabawar rayuwa. Alhamdulillah bi ni’imatil lah.”
Jikin k’anin ne yayi sanyi tunowa da yayi da rayuwar yayan nasa kafin ya zama Ustaz d’in. Shima ya fuskanci jarabawa ta sace-sace kafin Allah ya shiryeshi, ya zamana kaff yaran gidansu babu mai hankali da kuma nitsuwarsa.
“Hakane Yaya. Allah ya shiryeshi da kuma masu hali irin nashi.”
“Ameen thumma Ameen.”
Abul yana barin gurin ya koma ainihin unguwar da yake zama da k’afa tsabar rashin kud’i. Dalilin da yasa yaje wancan Chemist d’in shine wanda yake sayar musu a unguwar nasu yana binshi bashi har na dubu daya amma bai biyashi ba. Kuma yace matuk’ar bai biyashi duka kud’insa ba bazai sake sayar mishi da magani ba.
Yanzu dolenshi zai je ya rok’i Imaa ya taimakeshi ya bashi saboda babu inda ya sani inda zai je a bashi magani babu prescription. Zaman Abuja kenan sai wanda ya shirya.
A bakin shagon Imaa ya samu abokan shashancinsa suna shan taba ya wucesu ba tare daya musu magana ba.
“Imaa bani Codein mana.”
“Sai ka biyani kud’ina don ubanka.”
“Nace ka daina zagin ubana, ka zagi uwata amma banda wancan daya mutun.”
“Gerrout before a bash your head for this wall.” Wannan karon cikin fushi yayi maganar domin ya tare mishi k’ofar tsukakken Chemist d’in wanda ta nan yake shan iska.
“Please na, kaga yau nazo da kudina zan biyaka.” Ya ciro d’ari biyu da hamsin wacce aka bashi bayan kwadagon da yayi a kasuwa.
Kamar walkiya Imaa ya wafce kud’in ya soketa a cikin aljihunsa yana zare masa ido.
Abul da sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa yayi saurin shiga shagon yana cewa Imaa ya bashi kud’inshi amma tuni Imaa ya hankad’oshi waje, sai gashi ya zube a k’asa a gaban abokan nashi.
“Dan iskan yaro lalatacce ni zaka nunawa rashin kunya?” Fad’in Imaa yana naushin cikinshi da k’arfin da Allah ya bashi.
Wata siririyar k’ara Abul yayi mai tattare da wahala ya dunk’ule guri d’aya yana rik’e da cikinshi. Wanda suke zaune a bakin shagon suka tashi tsaye suna kallonshi sai dai sun san shiga fad’an Imaa death wish ne, domin zai iya had’asu duka yaci uwarsu ba tare daya gaji ba ko kuma suyi nasara a kanshi ba.
K’ato ne, bak’i mummuna kuma mai tsayi. Baya shan kayan maye amma ya fisu hauka dalilin rashin imaninsa da kuma rashin tsoro. Wata naushin ya k’arawa Abul wacce tasa ya fara kakarin amai, Imaa na ganin hakan ya jawo kwalar rigarshi ‘kiiii’ ya kaishi bakin kwatan unguwar ya watsar dashi.
Amai Abul ya fara yi wanda yake fitowa kore kamar ganyen bishiya kuma mai yauk’i. Yanda yake aman kamar ranshi zai fita ya bawa Banney tausayi, ya tako ya iso gurinshi ya tsaya a kanshi.
Sai daya gama aman da taimakon Banney ya mik’e tsaye suna layi dukansu suka wuce d’akin da suke kwana wanda shago ne k’arami, k’ofar shagon da yake na katako ne k’asan ya bangare yanda mutum ko dabba zasu iya shiga koda kuwa an kulle.
Banney ya watsar da Abul kan tsummokaran kayansu kana ya koma lungun da yake kwanciya ya toni rami ya d’auko chocolate snickers ya bawa Abul.
“You are sick man. Typhoid ne yake damunka daga ganin aman da kayi. You should see a Doctor asap.”
Murmushin yak’e Abul yayi kana ya 6are chocolate d’in ya fara ci bai yi magana ba. A ranshi kuma cewa yake yi duk cutar da take jikinshi sai dai ta kasheshi saboda bashi da kud’in neman magani.
Banney da shima k’addarar rayuwa ta jefashi a halin maye ya dubi Abul yace,
“Ka koma gida, zaman nan bai dace da kai ba.”
A fusace Abul ya juyo yace,
“Kai don uwarka meya hanaka komawa? Da yanzu ka zama d’aya daga cikin successful Doctors d’in da ake ji dasu a Nigeria.”
“Do not bring my past into this.” Yayi warning d’in Abul yana masa mugun kallo.
“Nima karka sake mini maganan komawa gida. I have no family left.”
Da haka suka yi shiru Kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, a yayin da Banney ke tuna dalilinshi na barin gatanshi shi kuma Abul tuna wahalar da yasha yake yi har rana mai kamar ta yau kamar haka;.....
Mum Fateey👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300.
(35)
Bayan Abul ya fakaici idon Mas’ud da yaran shagonsu sai ya fara d’aukan kud’i ba tare da sun gane ba. A ranar daya shirya gudu, ya d’auki jakarsa ta Laptop ya sanya kayansa kala uku a ciki da kud’in daya sata sannan suka tafi shago shi da Mas’ud kamar kullum.
Mas’ud bai kawo komai a ranshi ba game da jakar Abul saboda ya san shi mayen Computer ne kuma yana fita da ita kullum. Lokacin sallar azahar yana kawowa ya bud’e Laptop d’in ya fara danne-danne mutanen gurin na tsokanarsa wai Computer Guru yana murmushi.
Har suka yi alwala domin gabatar da sallar azahar shi yana zaune bai daina aikin da yake yi ba. Hakan yasa Mas’ud da sauran suka tafi suka barshi a kan in ya tashi ya rufe shagon su sun wuce masallaci.
Sai daya tabbatar sun isa masallacin sannan ya bud’e jakarsa ya juye kaf cinikin da aka yi a ranar ya fita daga shagon a hankali kamar ba wanda yayi 6arna ba. Daga nan bai nufi tasha ba domin yasan zasu iya bin kadinshi su gane motar ina ya shiga.
Babban titi na k’arshen gari ya nufa ya tsaya can motoci manya da k’anana na zuwa suna wuceshi ba tare da sun tsaya kamar yanda yake d’aga musu hannu ba.
A nan ne ya kira Laila da sabuwar sim d’in daya saya ta d’auka yace,
“Nine Abul. Kuma ina miki albishir da cewa na bar garin Kano da zama kwata-kwata har sai kin kashe aurenki da wannan matsiyacin yaron sannan zan dawo. Kar kusha wahalar nemana domin ba zaku ta6a sanin ina nayi ba.”
“Allah ubangiji ya shiryeka.” Shine kad’ai abunda Laila ta samu fad’a ya kashe wayarsa.
SIM card d’in ya cire ya karya sannan ya watsar a cikin ciyawin bakin hanyar. Daga nan ya kai awa biyu tsaye sannan da kyar ya samu wata Sharon da zata je Abuja ta tsaya aka d’aukeshi. A takure ya isa Abuja domin motar cike take da Lawashi da Albasa a bayan booth da kuma seat d’in baya. Seat d’in tsakiya ne kad’ai mai d’auke da mutane hud’u sai shi da Driver a gaban motar.
Suna isa tasha ya d’auki jakarshi sannan ya sanya wata sabuwar Sim Card ya kira abokinsa Faisal d’an wani hamshak’in mai kud’i a nan Abuja. Mota zugegiya aka zo aka d’aukeshi da ita wanda Faisal na bayanta yana busa Shisha yana sauraron wak’ar Naira Marley.
Suna ganin juna suka tafa kowannensu d’auke da murmushi domin wannan ne karo na farko da suka ta6a had’uwa.
“Sai gaka a Abuja. I’m glad you come Man.” Fad’in Faisal yana komawa cikin motar.
Daga nan suka wuce gidansu Faisal a wata unguwar masu ji da kud’in Nigeria, gida ne babba wanda daga gani zaka gane na wani hamshak’in mai kud’i ne wanda baya jin zafin kasheta.
Faisal d’a babba a gidan Cabin house aka gina masa a can lambun gidan wanda babu mai zuwa gurin sai shi da kuma wad’anda ya gayyata. A can aka sauk’e Abul wanda yake bin tsari da kyawun gurin. Living room ne babba guda d’aya sai d’akuna biyu da toilet guda d’aya dake tsakanin d’akunan.
Furnitures d’in da suke ciki masu kyau da tsada wanda basu cika yawa a ba dalilin mai Cabin d’in baya son hayaniya a tsarin gurin zamansa.
“You live here?” Abul ya tambayeshi yana zama kan Sofa dake cikin falon.
“Ina son zama a secluded area shiyasa Babana ya gina mini nan, sometimes na kan manta a cikin gari nake domin bishiyoyin da suke zagaye dani kan sa in d’auka a real forest nake. Bana son damuwa da hayaniya, bird chirps sun fi mini dad’in sauraro akan maganan mutane. Da fatan baka da surutu? Domin bazan shirya da kai ba.”
“No. Nima bana son yawan magana nafi son zama a gaban Computer like you.”
“Yeah.” Da haka Faisal ya isa gurin wani cabinet dake falon ya d’auki wata wayar hannu ya nunawa Abul.
“Duk abunda kake son ci ko kake buk’ata na rayuwa ka rubuta ka tura a nan za’a kawo maka a lokacin da kake so, zasu ajiye maka a bakin k’ofa domin na hanasu shigowa gurina in ba weekly cleaning ba. Ina da bak’uwa a d’akina, don’t disturb us.” Da haka ya fara takawa ya isa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 32