jikinta ba'a barni ba dalilin al'ada irin tamu ta hana Amare fita daga yin aure, sai dai kullum k'annena na zuwa suna fad'a mini halin da take ciki. Sati d'aya da aurena aka kawo mini labarin cewa ta gudu an nemeta an rasa." Ummii ta share hawayen fuskarta taci gaba,
"Duk laifina ne da nake kareta idan tayi laifi za'a mata hukunci. Kuma nayi dana sani ba kad'an ba shiyasa kaf yarana ban nuna musu wannan son ba gudun kar hakan ya faru dasu, duk da cewa wani lokacin k'addara ce daga Allah ba don iyaye sun kasa bawa yaran tarbiyya nagari ba. Kaala Abdi sai daya samu cutar shanyewar gefen jiki bayan guduwanta, sannan ya hana kowa cigiyarta yace a bari duniya zata koya mata hankali. Har sai dana haifi Mas'ud sannan Allah ya bashi lafiya, cigiyarta kuma munyi a 6oye har muka hak'ura dalilin ko sau d'aya ba'a ji wani yace ya ganta ba sai yau data bayyana don kanta."
Tsit d'akin yayi ana kallon Haydar wanda yake zubar da hawaye yana kallon Amminshi tamkar wata halitta yake gani ba ita ba.
"Hakane Ammi?"
Gyad'a mishi kai tayi yayi saurin sunkuyar da kanshi yana 6oye fuskarshi daga garesu. Bai yi tsammanin labarin haka bane, ya d'auka kurciya aka mata, ya d'auka korarta aka yi daga gida ko kuma a gidan marayu ta girma ta gudu. Bai yi expecting ita da kanta ta gudu ta barsu ba, sannan bai yi tsammanin zata aikata zina ba. Kenan shi shege ne, dalilin da yasa bata son fad'a mishi kenan?
"Na aikata laifi mafi muni a rayuwata Haydar, hakan yasa abunda nayi yake bibiyata har na so rasa raina tare da naka a lokaci daban-daban. Kuma yanzun ma ba tsira nayi ba, ina tsoron sanar da kai ka nemesu su kashe mini kai."
"Ki fad'a mini." Shine abunda ya fad'a yana d'ago kanshi yana share hawayen fuskarsa cikin dakewa.
Laila dake gefe nan take ta fara jin tausayinshi domin babu wanda zai so yaji shi shege ne. Kenan itama shegen ta aura, kuma a matsayin d'anta yake tunda Ammi 'yar kawunsu ce (cousin). Ji tayi kamar ta isa gurinshi ta rarrasheshi, ashe shi d'in wani sashe ne na jikinta da gaske ba gamuwar jini bane kad'ai.
"Ban san ya aka yi na tsinci kaina a halin da nake ciki ba, kawai na san da cewa a gida kowa yana sona, k'anin matar Babana ne ya fara nuna mini hanyar lalata tun ina k'arama ba tare daya bari na fad'awa kowa ba. A haka na tashi cikin gur6ataccen rayuwa ba tare da nayi tunanin abunda nake aikatawa babu kyau ba, bayan kowa ya sani ni da kaina na yanke shawarar gudu da naji labarin za'a had'amu aure da wanda aka gannì tare dashi. Kud'in da nake tarawa na kwashe babu wanda ya lura na tafi tasha na shiga mota, saboda gudun kar a sameni yasa ban tsaya a gari d'aya ba nayi ta hawa mota ina yawo har kud'ina ya k'are a Pot Harcourt. A nan ne tsoro ya shigeni dalilin bani da gurin kwana sannan ban san ina zan je ba. Wani gurin sayar da abinci naje na raku6e a bayan ginin ina kallon mutane masu shiga da fice. Sai da duhu ya fara yi na k'ara tsorita, dalilin nasan bazan kwana da rai ba muddin na kwana a tasha, hakan yasa na fara kuka wanda ya k'ara jawo hankalin mutane kaina. Kamar daga sama naga wata mata musulma tana mini magana da hausa wanda bana ji sosai sai yarenmu na Shuwa kad'ai. Jin tayi yaren Shuwa yasa nayi saurin tashi na isa gurinta ina fad'a mata damuwata tare da neman ta taimakeni tun kafin in fahimci me take son fad'a mini. Sai dana gama magana ta nuna mini so take yi in tashi in bar gurin saboda ina tara mata jama'a wajen sana'arta, A nan na gane ita ce mai gurin. Cigaba da rok'anta nayi kan cewa zan mata kowanni irin aiki ne in ta bani gurin kwana. Da kyar ta yarda a kan cewa zata taimakeni, a madafinsu na zauna tare da sauran ma'aikatanta har lokacin tashinsu yayi suka kulle gurin muka dawo gidanta wanda gida ne na haya mai d'auke da d'Akuya k'anana ashirin da biyu, kuma duk gidan matane. Ban jima tare da ita ba na fad'a rayuwar da kowa yake yi a gidan nima aka bani d'akina daban ina biyan haya idan maza sun biyani. Babu buk'atar in fad'i duk abunda ya faru a wannan zaman amma duk abunda yake faruwa da karuwa wacce ta bar gidansu ya faru dani. Mata sun dakeni idan na kwace musu samarinsu, maza sun dakeni idan na nemi rabuwa dasu ko fad'a ta shiga tsakaninmu, wulakanci na rayuwa babu wanda ban gani ba amma hakan bai saka na koma gida ba. Shekarata sha biyu a pot harcourt na dawo Kano dalilin wani Alhaji dana biyo wanda tun had'uwarmu naji ina sonshi. A farkon had'uwarmu shima ya nuna yana sona amma da aure dalilin shi baya bin karuwai, dama abokinshi ya rako d'aukan mace a gidanmu ya had'u dani. Ganin na k'i yarda da batunshi yasa ya biye mini muka fad'a ga halaka. Bayan sun gama aikin daya kawosu pot harcourt sai ya nemi in bishi zuwa Kano, a nan ya nema mini gida na zama tamkar matarshi duk da cewa ya so muyi aure tun farkon had'uwarmu amma na k'i. Watana uku a Kano watarana yazo gidana cikin gaggawa yace in tattara kayana in tafi Abuja matarshi ta samu labarinmu, ban k'ara awa d'aya ba na bar gari na tafi Abuja zuwa wani gidansa da yasa wani ma'aikacinsa ya kaini. Sai da nayi sati uku bai zo ba wanda har na fara tsoron ko matarshi ta kasheshi a yanda yake bani labarin tana da zafin kishi, hakan yana d'aya daga cikin abunda yasa yake son aurena domin idan ni matarshi ce duk kishinta zata hak'ura ta barmu. A ranar daya dawo na lura da karaya a hannunshi yake fad'a mini ban jima da tafiya ba matarshi ta shigo gidan suka yi fad'a har ta kwad'a mishi Tv ta gurd'a mishi hannu. A nan yake rok'ana kan in amince in aureshi domin babu wanda ya bashi gaskiya akan abunda ya faru sannan mutuncinsa na zubewa a idon jama'a. Nice mace d'aya daya ta6a nema sannan bayana ban ta6a ji ko ganin ya nemi wata mace ba. Da na nuna rashin amincewata sai ya nemi mu rabu, son da nake mishi yasa naji tsoron rabuwa dashi domin ko na rabu dashi zuciyata baza ta barni in zauna lafiya ba, hakan yasa na amince da aurensa." Dakatawa Ammi tayi kana taci gaba,
"A ranar daya zo ya koma Kano akan sai na gama Istibra'i kafin a d'aura mana aure. Wata uku da haka ya dawo ya nemi in koma gidanmu ya nemi aurena a can amma nak'i yarda, hakan yasa aka d'aura mana aure a nan Abuja ba tare da dangina ba. Sai a wannan lokacin na gane cewa rayuwar da nayi a baya bata da fa'ida, dalilin kwanciyar hankalin dana samu kaina a ciki a matsayina na matar aure, Alhaji yana nuna mini so na hak'ik'a wanda ni kaina na sani. A wannan zaman ne na samu cikinka Ali, wallahi kai ba shege bane. Farin cikin da muka yi a ranar dana gane ina d'auke da juna biyu ba'a misaltawa dalilin Babanka bashi da 'yaya da yawa. Cikina yana munzalin wata bakwai Babanka yaje Kano akan zai dawo bayan sati biyu, washe gari ina kwance naji ana kwankwasa k'ofa maigadi ya bud'e, daga nan ban k'ara jin motsi ba sai ji nayi ana kwankwasa k'ofar falo. Ban kawo komai a raina ba saboda makwabtana suna shigowa nima kuma ina zuwa musu. Ina bud'ewa naji naushi a fuskata wacce tasa na fad'i tsabar gigicewan da nayi. "Munafuka algunguma ashe da gaske har ciki kika d'auka." Shine abunda na fara ji a lokacin da nake k'ok'arin dawowa cikin hayyacina. Maza biyu na gani tsaye a kaina gefensu kuma mace ce wacce na tabbatar matar Alhaji ce. Daga nan duka na dinga ji ta ko'ina amma na dunk'ule guri d'aya gudun kar a bugi cikina, duk kuka da ihun da nake yi kuwa babu wanda ya kawo mini d'auki saboda babu mai jina. Sai da suka jikk'atani sannan tasa suka d'aureni a jikin kujera tare da toshe mini baki don in daina rok'arsu gafara. Ina gani ta d'auko wuka na fara girgiza kaina ina hawaye, tsaga mini k'afafuwa tayi da wuk'an jini na zuba a jikina sannan daga baya tace zata yanka cikina ta ciro d'an cikina. A nan ne ta cire mini tsumman da suka toshe bakina na fara bata hak'uri ina rok'anta kar ta kasheni ko d'an cikina. A nan ta bani za6in in 6ace daga rayuwar mijinta ko kuma ta kasheni a wannan lokacin, banyi k'asa a guiwa ba na yarda da cewa zan tafi saboda nasan Wallahi zata aikata kasheni. A gabansu na had'a kayana na fita daga gidan, daga nan kuma Zaria nayi ina jinyar jikina a wani hotel. K'udin hannuna yana k'arewa na fito gari neman aiki har na samu wanke-wanke da shara a wani gida saboda bana fatan sake komawa rayuwata ta baya. A haka na haifeka na saka maka sunan Aliyu Haydar ba tare da sunan uba ba, kana da shekara d'aya maigidan da muke zaune a gidansa ya rasu wanda hakan yasa na rasa aikina na dawo ina yawon neman aiki da gurin kwana. A nan ne kuma na had'u da wannan abokin Alhaji daya had'amu ya fad'a mini cewa Alhaji yana nemana in zo ya mayar dani gida. Tuna irin kisan gillan da matarshi zata mana yasa na fad'a masa zan shirya kayana gobe mu koma. A ranar ban kwana a Zari'a ba sai Lagos. A can naci gaba da zama ina talle a bakin titi bayan na samu gida a Squatters wani unguwa na kazo nazo. A Lagos na saka Haydar a makaranta har zuwa lokacin da na gaji da zaman garin naso komawa arewa dalilin fyade da wani ubangidana ya mini. Garin neman kud'in mota na had'u da Alhaji a yayin da yake mik'awa Haydar kud'i bayan mun yi k'aryar cewa ni makauniya ce. Ina ganinshi na ja Ali muka gudu muka 6ace masa, daga nan kuma muka koma Jos da zama har Ali ya gama secondary school. Duk da cewa bana fita cikin gari in ba ya kama dole ba amma sai naji kamar tsawon zaman da nayi a Jos zai sa a gane inda nake. Hakan yasa rana d'aya muka bar garin muka dawo Kano saboda nasan Alhaji bazai ta6a tsammanin zan dawo cikinta ba. Sannan duk nemana da zai yi ba zaiyi a cikin Kano ba. A nan na sayi gidan da nake ciki na fara tallan k'osai da doya a bakin hanya har Ali ya gama university, kuma ya had'u da Laila ya aureta ba tare da sun san cewa su 'yan uwan juna bane. Wannan shine rayuwata a tak'aice bayan na tafka kuskuren da bana yiwa ko mak'iyina fatan irinsa."
Jikin kowa a d'akin yayi sanyi musamman Haydar da bai ta6a kawowa a ranshi cewa mahaifiyarshi ta ta6a rayuwar karuwanci ba, ko a daa da yake tambayarta cewa ko shi shege ne bai sa a ranshi ita ta kai kanta ba, yafi zaton fyad'e aka mata aka koreta a gida shiyasa bata son fad'a mishi. Ashe labarin rayuwarta yayi munin da har abada ba zai so ya k'ara zama a labarta mishi ba.
Ummii ce ta fara magana da cewa,
"Tun farko kin yi kuskuren barin gidanku, sai dai za'a alak'anta hakan da yarinta da kuma sangartar da kike taso a cikinta. Allah ya yafe miki kura-kuranki ya kuma gafarta miki. Sai dai da tun wancan lokacin da kika tuba kin waiwayi gida, wallahi babu mai korarki ko da kuwa da cikin shege kika dawo Suwaiba. Wannan labarin data bayar kar wani ya fitar dashi, duk wanda ya tambaya a fad'a mishi yawace-yawacen da tayi na garurruwa ba tare da an labarta k'azantar da yake ciki ba, sai kuma labarin aurenta da kuma abunda ya sameta har ta bar mijin don kare kanta da d'an cikinta. Madu kira mini Kaala Abdi in sanar dashi wannan kyakkyawan labarin." Ummii ta gama maganar fuskarta cike da tsantsan farin ciki.
"Don Allah karki fad'a mishi zai kasheni idan ya ganni." Fad'in Ammi cikin tsoro.
"Sanin daa kika yiwa Babanki, amma daga baya shi da kanshi ya saka cigiyarki, kuma har rana mai kamar ta yau bakinshi bai daina furta sunanki ba. Girma ya zo masa Suwaiba kuma yayi nadamar rashin nemanki da wuri da yayi."
Haydar daya lura hankalin kowa ya koma kan Ammi ya mik'e ya fice daga falon, Laila ce kad'ai taga fitansa tayi saurin bin bayanshi tana kiran sunanshi amma bai waiwayo ba har ya fita daga gidan bayan ya jefar da key d'in motarsa a k'asa. Yana zuwa bakin k'ofar gidan ya tsaya yana kallon bakin titi. A nan Laila ta sameshi tana cewa,
"Ina zaka je Haydar?"
Hannu ya mik'ar mai achaba ya tsaya kana ya dubeta yace,
"Babu amfanin kasancewata tare daku, sannan nasan zaku kula da Ammi. A yau na rasa wani part na rayuwata sannan na samu wani sashe na rayuwata wato sanin wanene ni. Kuma nasan a yanzu da kika ji labarin mahaifiyata zaki fi tsanar had'a zuriya dani, don haka ni Haydar na sakeki." Yana gama fad'in hakan ya hau acha6a suka tafi y bar Laila a daskare a gurin kafin ta fad'i a k'asa sumammiya.
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
(44)
A idon Mas’ud Laila ta fad’i ta suma, cikin sauri ya iso gurinta ya durk’usa yana kiran sunanta. Madu daya biyo bayansu don ya yiwa Laila magana ya zo ya samesu a haka, tare suka cicci6i Laila suka shigar da ita cikin gidan.
A falon Ummii suka kwantar da ita, su Ammi na tambayar meya sameta cikin tashin hankali. Ruwa aka yayyafa mata ta farfad’o tana kallon mutane ta fara zubar da hawaye zuciyarta na mata zafi.
“Shima ya tafi Ammi, ya gudu kuma ya sakeni.” Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da dukkan hannayenta.
Salati Ummii ta saka cikin fargaba tana tambayarta abunda ya faru, kafin ta bada amsa Madu ya fita daga falon kai tsaye kuma ya shiga motarshi ya fita daga gidan gaba d’aya.
“Sai ki fad’a musu laifin da kika mishi har ya sakeki Kalti.” Mas’ud ya fad’a cikin sanyin murya don jikinshi ya mutu da yaji Haydar ya saki yayarsa.
“Laifin me ta mishi Mas’ud?” Ummii ce tayi tambayar ganin Laila ta kasa bada amsa sai hawaye kawai take yi tana girgiza kai.
Ammi kuma tuni ta matsa gefe tana kiran wayar Haydar cikin tsoron abunda zai aikata, addu’a take yi a ranta kar ya gudu ya barta bayan ya gama jin labarin k’azamin rayuwarta. Wa zai so ya gane cewa uwarsa karuwa ce kuma kowa ya sani?
“Cikinshi ta zubar saboda wai ta tsufa da haihuwa. Bata ji kunyar kwanciya dashi ba sai kunyar yawo da cikinshi take yi.” Mas’ud ya bawa Ummii amsa kamar ya kaiwa Laila duka.
“Waye ya fad’a maka na zubar? Yana jikina ban zubar ba, shi kuma bai tsaya muka yi magana ba balle in fad’a mishi cewa ban aikata ba. Mas’ud ka nemoshi kar yayi nisa don Allah.” Ta fad’i hakan wasu hawayen na sauk’a a k’uncinta.
“Ke kika fad’a mishi zaki zubar da cikin?” Ummii ta yiwa Laila tambayar cikin takaici.
“Eh amma wallahi daga baya ban iya na aikata ba Ummii.” Laila ta furta cikin tsoron fad’an Ummii don bata so taji labarin ba kwata-kwata.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Laila wani irin zama kike yi da yaron nan? Ina fatan ba ke kika zama mijin a auren naku ba don kinga kin fishi shekaru? Ashe zaki iya bud’e bakinki ki furta mishi zaki zubar da ciki bakya jin tsoron Allah da kuma kunyarsa? Ashe baki da mutunci baki san mutum mai miki halacci ba Laila?”
Ummii fad’a take yi ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, Ammi ce kad’ai ta dawo kusa dasu tana bata hak’uri amma hankalinta na kan Haydar wanda ta kira wayarsa taji a kashe take.
Mas’ud kuwa tuni ya fice daga gidan neman Haydar tunda yaji abunda Laila ta fad’a. Gidansu ya fara zuwa ya tambayi maigadi ko Haydar yana ciki, maigadi yace masa yanzu ya fita da jakan matafiya bai yi ko minti biyu ba.
Cikin tsoro Mas’ud ya isa bakin titi ko zai hango Haydar a hanya amma bai ganshi ba, haka yayi ta yawo a tashoshin mota yana dubawa ko zai ganshi amma bai ga alamarshi ba. K’arshe dole ya hak’ura ya dawo gida jikinshi a sanyaye ya samu Laila da Ummii a falo suna zaune zugum-zugum basa magana.
“Ina Ammi?” Shine tambayar daya fara don bai ganta ba.
“Tana d’aki tana ta gwada wayar Haydar. D’azu ya turowa Laila sak’on sakinta da yayi sannan yace a bawa mamanshi hak’uri ya tafi kar asha wahalar nemanshi.” Ummii ta bashi amsa tana hararar Laila kamar zata bugeta.
“Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.” Shine abunda Mas’ud ya furta yana jin zuciyarshi na mishi zafi kamar yayi hawaye.
Wannan wani irin abu ne yake faruwa a zuriyarsu? Daga wannan ya 6ace sai wannan shima ya 6ace? Meyasa baza su zauna as one big happy family ba? Meyasa suke tunanin 6acewarsu zai magance halin da suke ciki? Meyasa Haydar ya tafi alhali dashi ake k’ok’arin dawo da hankalin Abul gida? Meyasa kullum a kwanan rayuwarsu sai sun had’u da wani tashin hankali?
Shima guri ya samu ya zauna ya dubesu yace,
“Shikenan shima ya gudu, don nima na nemeshi ban sameshi ba.”
Wannan magana yasa Laila tayi dana sanin furta cewa zata zubar da ciki, me amfanin rayuwarta babu Haydar a ciki? Meyasa ma tun farko ta kasa hak’ura ta raini cikinta albarkar aurenta da Haydar? D’aura hannu tayi a cikinta tana jin tausayin kanta da duk abunda yake ciki idan har ya tashi babu uba a kusa dashi.
A makeken falon Alhaji Abdul aka yiwa Madu iso ya samu guri ya zauna yana jiran maigidan ya fito. Minti biyar da haka Alhaji Abdul ya fito yana takawa d’ai-d’ai ya zauna a kujera mai fuskantar Madu cikin izza da isa yace,
“Ya aka yi?”
“Albishir na taho maka dashi Alhaji.” Madu ya fad’a yana washe baki.
“Na me kenan?” Alhaji Abdul ya tambaya without any interest.
“Yaron nan ya saki Laila sannan an gano mahaifiyarshi ‘yar uwarmu ce data gudu ta bar gida.”
Da sauri Alhaji Abdul ya gyara zamanshi cikin tsananin farin ciki yana godewa Allah da wannan kyakkyawan labarin.
“Da gaske kake yi?”
“Kwarai da gaske, a gabana aka yi komai kuma nayi recording duk abunda ya faru na tura maka.” Ya bashi amsa yana jin kamar yayi abun kwarai.
Alhaji Abdul kasa zaune ko tsaye yayi sai safa da marwa yake yi a falon yana fad’in irin farin cikin da yake ciki duk da cewa yasan kafin Laila ta amshi soyayyarsa sai ya jima, amma zai jirata ko da zuwa tsufansu ne.
Kyauta mai tsoka ya yiwa Madu kana ya koma cikin d’akinsa inda ya bar matar daya kwana tare da ita a kan gado. Yana shigowa ta farka tayi mik’a sannan ta dubeshi taga yanayin da yake ciki wato na murna. A zatonta duk a
dalilinta ne irin bajintar data mishi jiya, hakan yasa tayi k’asa da murya tace,
“Baby murnar me kake yi?”
Bai ko kalli inda take ba ya zauna kan sofa dake can k’uryar d’akin yace,
“Haydar ya saki Laila.” Kana ya fara bud’e wayarsa don nemo wannan recoding d’in da Madu ya turo masa.
D’iff annurin fuskarta ta d’auke tana jin mugun kishi a ranta dalilin tsanar Laila da tayi domin ita take son Alhaji Abdul ba Laila ba. A kan son da take yi mishi yasa ta auri Madu yayan Laila don kawai ta juya hankalinshi ya tilastawa k’anwarshi auren Alhaji Abdul duk da cewa a ranta bata so hakan ba. A kanshi ta kasa zaman aurenta ta kuma k’i haihuwa da Madu duk don ko watarana idan ya samu auren Laila zai tausaya mata itama ya aureta. Saboda sonshi da take yi yasa take yawan neman izinin zuwa garinsu gurin mahaifanta na k’arya duk don ta kasance da Alhaji Abdul, wanda yau kwananta biyu kenan tare dashi kuma sati biyu tace zata yi a garin nasu. A kan sonshi ta dinga fad’in k’arya akan Laila duk don ta rasa manema Alhaji Abdul ya aureta kamar yanda suka tsara tun farko. Sai dai a lokacin da Laila tayi aure zuciyar Jamila ta samu salama har tana tunanin zai nemi aurenta, a lokacin kuma taso ta kashe aurenta amma ya hanata yace ta jira akwai abunda yake son kullawa kuma yana buk’atar ta kasance a cikinsu don aikin ya tafi daidai. A tunaninta Laila ta mishi nisa shiyasa ta hak’ura ta zauna a gidan Madu zuwa lokacin da Alhaji Abdul ya karaya ya gane cewa ta ku6uce mishi sai ta kashe aurenta ta aureshi. Ashe hak’anta ba zai cimma ruwa ba, domin yanzu wani sabon zaman za’a sake kafin Laila ta waiwayi Alhaji Abdul tunda a wancan karon ma sai da tayi shekara ashirin kafin ta yarda zata aureshi, sai dai wannan karon Jamila bata jin zata iya jiranshi dalilin tsufan data fara, duk bleaching creme ya k’ona mata fata bata da wani mamora sai gayyan tsufa da tarin zunubai.
“Yanzu ni ya zaka yi dani? Wani abu ka tanadar mini a gaba?” Ta tambayeshi tana tashi tsaye ta fara mayar da kayan jikinta.
Wani wawan kallo yayi mata yana ganin surar jikinta yanda ya fara jemewa, in ba don yana son zamanta tare da Madu ba bai ga abun so a jikinta ba da har zai ji sha’awarta. Tunani yayi cewa ya kamata ya rabu da ita don ya lura she’s obsessed with him, kar ta kawo mishi cikas a gaba. Ajiye wayar hannunshi yayi kana ya dubeta da kyau yace,
“Lokaci yayi da zamu daina huld’a tsakaninmu domin bana son Laila ta gano ina kwanciya dake matar yayanta. Yanzu ma bani da daraja a idonta kuma bana son abun ya wuce haka. Ina so daga yau karki sake ki nuna kin sanni, idan kina son cigaba da zaman aurenki babu ruwana kuma bazan hanaki ba amma ki nisanceni. Zan tura miki million goma a matsayin tukuicin k’ok’arin ki a gareni, zaki iya tafiya.”
Tashin hankali ya hango k’arara a fuskar Jamila wacce ta sukwano ta durk’ushe a gabanshi tana cewa,
“Don Allah Abdul karka mini haka, a kanka babu wahalar da ban yi ba duk don ka samu farin cikinka ko nima zaka tausaya mini daga baya. Na rok’eka don son da kake yiwa Laila kar ka raba tsakanina da kai don kai nake so ba kud’inka ba.”
Shiru yayi yana kallonta tana mishi magiya har kuka take yi da idanunta, a maimakon yaji tausayinta sai yaji haushin dalilin da yasa duk tsawon wannan lokacin meyasa bai rabu da ita ba?
A yanzu da yake son ya nitsu yaji labarin uwar Haydar baya son takura da kuma ihun da Jamila take mishi. Hakan yasa ya d’auki wayarsa yayi danne-danne kana ya dubeta yace,
“Na tura miki kud’in. Sannan na baki minti biyar ki fita mini a gida kafin in saka securities suyi waje dake.”
Tana jin hakan ta share hawayen fuskarta a zuciye ta dubeshi tace,
“Ka jira kaga ni kuma me zan yi.”
“Ni kike fad’awa haka? Uban me zaki yi? Wallahi kika kuskura kika 6ata mini plan sai na saka an shafe babinki a doron k’asa kuma kin san zan aikata. Don haka zan baki shawara ki 6ace a garin nan gaba d’aya kar in sake jin d’uriyarki, aurenki da Madun ma ya k’are
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 32