Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Haydar ya cire a ranar da zai tafi. Hawaye masu zafi suka gangaro kan k’uncinta har na wani lokaci mai tsawo kafin bacci 6arawo ya saceta. Washe gari da rana Alhaji Abdul ya isa gidan a wata Taxi wacce ta tsaya tana jiranshi a waje, maigadi na ganinshi ya bud’e mishi k’ofa kana ya nuna mishi wasu fararen kujeru biyu a can gefe yace ya zauna Hajiya na fitowa, wato kenan ba zai shiga cikin gidan ba. Yana zaune amma zuciyarshi na d’ar-d’ar domin ba wai ya gama yarda da Laila bane, zai iya yiwuwa had’a baki tayi da Madu don ya ritsashi a gidanta amma haka ya daure ya zo domin shine mai neman taimakonta. Ya kai minti biyar a zaune sannan Laila ta fito jikinta sanye da hijab har k’asa fuskarta babu annuri ko kwalliya ko kad’an. A can nesa dashi ta zauna kana ta dubeshi tana jinjina k’ok’arin Madu wajen lahantashi da ya kusa yayi, wanda har yanzu goshinsa a rufe take da bandage sannan hannunsa a d’aure yake bai warke ba. “An wuni lafiya?” Ya fara aika mata gaisuwa wanda ta share kamar bata ji ba. “Ta yaya zaka nemoshi?” Shine abunda ya fara fitowa daga bakinta tana tsareshi da ido. “Shiyasa nake buk’atar taimakonku domin ni ban san ina zai iya zuwa ba, ina kuke tunanin zai je?” Shima ya mayar mata da tambaya. “Duk inda muke tsammanin zai je baya nan.” Shiru Alhaji Abdul yayi yana tunani sannan can yace, “Menene ainihin abunda ya tunzurashi ya tafi? Tarihin mahaifiyarshi ce ko kuma wani abun ne daban? I need to know.” Laila ta tashi tsaye a fusace ta dubeshi tace, “That’s none of your business, idan zaka yi abunda kace zaka yi kayi in kuma dama k’arya kake yi ka fita mini a gida.” A take a lokacin kuma fara dana sanin sauraronshi tun farko, domin sai a yanzu taji baza ta iya yarda dashi ba har abada. “Laila ki saurareni, wallahi yanda kike son Haydar ya dawo haka nima nake son ya dawo. Ki zauna in fad’a miki abunda baki sani ba a kaina. Kiyi hak’uri.” Yayi maganar a sanyaye cikin lallashi. Zama tayi bayan ta mishi wani mugun kallo kana tace, “Ina jinka” “Bayan an bayar da aurenki ga Aliyu Rufa’i Babana ya turani America na je na k’arasa karatuna, sanin cewa ko na dawo bazan sameki ba yasa nayi zamana a can ban dawo ba sai dana samu labarin mijinki ya rasu. Kafin nan ina son ki san irin relationship d’in da yake tsakanina da mahaifina. Baba yafi mahaifiyata sona sannan yafi kula dani da kuma bani lokacinsa fiye da ita. Hakan yasa na tashi nima bana son 6acin ranshi wanda a dalilin hakan nayi hak’uri na barwa Aliyu Rufa’i ke, na kuma bar muku k’asar gabad’aya. Wallahi Laila in ba don Ina gudun 6acin ran Babana ba daa a wancan lokacin na yiwa Aliyu abunda bazan iya furtawa ba. Bayan na dawo daga America na samu mahaifina a wani irin hali na damuwa wanda na alak’anta hakan da rashin matarsa wato mahaifiyata wacce ta rasu ina America. Ko dana mishi zancen k’ara aure yake fad’a mini ainihin abunda yake damunshi wato na rashin matarsa ta biyu da kuma cikin data tafi dashi na wata bakwai. Nayi mamakin yanda ban ji labarin Babana yayi aure har matar ta gudu ba saboda a lokacin ina Kano ina secondary school, kenan an 6oye mini maganar ne. It turns out lokacin da mahaifiyata take gadon ajalinta ta nemi gafarar Baba bayan ta sanar dashi abunda ta aikata ga matarsa wanda hakan yasa ya nisanceta har ta koma ga mahaliccinta bai k’ara zuwa inda take ba. Bayan na samu labarin ni da kaina naci gaba da bincike wanda babu nasara a ciki ko kad’an illa kashe kud’i da muke yi a banza amma ban fasa ba. Nasan mahaifiyata ta cucesu amma ina son in nema mata gafararsu, sannan ina son nima in ganni tare da wani wanda za’a iya kiranshi d’an uwana saboda ni kad’ai iyayena suka haifa na rayu yayin da sauran biyun Allah ya amshi kayansa tun kafin su zo duniya. Sai dai duk da halin da muke ciki ni da mahaifina na rashin masoyanmu bai hanani aikata mugunta a gareki ba tare da iyalinki. Sai gashi Allah ya kamani yasa Haydar da nake yiwa mugunta shine k’anina da nake nema duk tsawon wannan lokacin. Nayi danasani na kuma yi nadama akan duk abubuwan dana muku da kuma wanda nake shirin aikatawa amma Allah bai nufa ba ya tona mini asiri, I hurt someone wanda nake son karewa da dukkan k’arfina and hakan ya koya mini darasi ne kan cewa; abunda baka so kar ka yiwa d’an uwanka, sannan munafurci dodo ne yakan ci mai shi. Bayan Madu ya kawo mini Audio na tarihin Ammi na gane wacece ita domin mahaifina bai rage mini komai ba daga labarin yanda suka had’u, da irin yanda ya samu labarin d’aure maigadinta da aka yi da kuma jinin daya 6ata falonta. Baba kasa hak’uri yayi ya saka muka kamo hanyar Kano a ranar ba tare dana huta ba, a hanya na fad’awa Baba abunda na muku har da k’anina Haydar ban 6oye mishi komai ba. Baba yayi fushi dani, fushi mai tsanani saboda ya sha mini nasiha kan cewa kar in cuci d’an Adam da arzik’in da Allah ya bani wanda shi ya tara ya dank’a mini ragamar dukiyar a hannuna bayan na dawo daga America. Muna shigowa gari a gidanku muka sauk’a har Madu ya samu daman mini haka. Laila har yanzu Baba bai daina fushi dani ba, saboda yana ganin a dalilina d’anshi ya k’ara shiga duniya. Ina son nemo Haydar ina son nunawa Baba cewa ni bazan ta6a cutar da jininshi ba.” Ya k’arishe maganan yana kawar da kanshi kamar wanda baya son Laila ta ga fuskarshi. A sama yaji muryar Laila tana mishi magana, tace, “Haydar yana son tara iyali tunda ya taso ya ganshi shi kad’ai, hakan yasa ya nemi in haihu ni kuma na nuna sam ba haka ba. A hakan na samu ciki na kuma nemi zubarwa har na tafi asibiti ya bini a baya, ya zo ya samu ana mini scanning sai ya d’auka na zubar da cikin ne yayi fushi ya tafi gidan Ummii, a nan kuma ya tarar da labarin mahaifiyarsa wanda bai mishi dad’i ba wanda wad’annan abubuwa biyun ne suka mishi yawa ya tafi.” “Ciki kike dashi?” Abun da Alhaji Abdul ya fara fad’i kenan cikin tsananin mamaki yana duban Laila. Gyad’a mishi kai kawai tayi ranta a 6ace domin bata ga abun mamaki a ciki ba. “Kuma baki zubar ba har yanzu yana jikinki?” Ya k’ara mata wata tambayar yana gyara zamanshi. “Eh ban zubar ba, kuma daa a yanzu zan samu seconds uku tare da Haydar abunda zan fad’a mishi kenan ya dawo gareni don nasan ba zai ta6a gudun d’ansa ba.” “Alhamdulillah!” Shine abunda Alhaji Abdul yayi ta maimaitawa idanunshi na tara hawaye yana kallon Laila wacce itace wannan karon take kallonshi cike da mamaki. Wani irin so yake yiwa Haydar? Kafin tayi magana taga ya d’auko wayarsa a aljihu ya kira Babanshi wanda shi ya fara magana amma bata ji ba, sai ji tayi Alhaji Abdul na cewa, “Ba’a sameshi ba Baba. Amma zan maka albishir ne ko hankalinka zai kwanta kad’an. Matarsa Laila na d’auke da ciki, zaka ga jikanka Baba.” Bata ji me Baban ya fad’a ba sai gani tayi ya mik’o mata waya yana murmushi amma ta k’i ta amsa. Duk yanda yayi da ita bata kar6a ba don wani kunya da kuma haushin Alhaji Abdul d’in take ji na saurin sanar da Baba batun cikinta da yayi. “Baba yace zai zo ya dubaki anjima tunda kin k’i kar6an wayar.” Ya fad’i hakan murna fal a fuskarsa wanda Laila kuma take jin kamar ta kifeshi da mari. “Don Allah ka bashi hak’uri saboda kwanan nan bana ganewa kaina sannan a yanzu ni ba matar d’ansa bane. Damuwata da kuma burina a yanzu shine a samu Haydar.” Gyad’a kai Alhaji Abdul yayi sannan yace, “Shin akwai wani programme da Haydar yake yawan gani wanda baya wucesa?” Tunani mai zurfi Laila tayi sannan ta d’ago da kanta fuskarta cike da annuri idanunta na tara kwalla, cikin sanyin murya tace, “Meyasa ban yi tunanin hakan ba? Wannan shine hanya mafi sauki da zan aikawa Haydar sak’o. Akwai wa’azin wani Malami da yake kallo kowanne sati ranar asabar. Akwai.” Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) (47) K’arfe hud’u da rabi Sheikh Nafi’u Kano ya fara wa’azi wanda ake kallo Live a gidan television d’in Nagari na kowa, wanda wa’azi ne game da hukunce-hukuncen sallah yana had’awa da misalai. K’arfe shida tana cika ya dakata akan cewa wata sati zai k’arisa sannan a shiga wani babin. Alaramman shi ne ya fara karanta tambayoyi shi kuma yana amsawa. Tambaya ta uku aka fara karantawa kamar haka, ‘Assalamu alaikum, Allah ya biya Mallam da alkhairi ya kuma bamu ikon gyara halinmu da ibadunmu Amin. Mallam ni na kasance babbar mace wacce ta bawa shekara arba’in baya, hakan yasa da mijina ya nemi in haihu na k’i amincewa har Allah ya nufeni da samun ciki na kuma nemi in zubar, naje asibiti da niyyar a zubar amma Allah ya canja mini ra’ayina naji ina son cikin. Mijina ya zo asibitin ya samu ana mini scanning sai ya d’auka zubar da cikin nayi yayi fushi ya tafi bayan ya sakeni saki d’aya, Mallam don Allah a rok’eshi ya dawo gareni don wallahi har yanzu cikin yana jikina ban cire ba. Mallam shi almajirinka ne saboda wa’azinka baya wuceshi kowanne sati. Nagode.’ “Wato Mallam wasu matan basa amfani da hankalinsu.” Wannan shine abunda Mallam Nafi’u ya fara fad’a fuskarsa babu alamun wasa. Mutanen da suke cikin masallacin suka kaure da cewa, “Allah ya bada lada. Allah ya gafarci Mallam. Allahu Akbar.” “To gaskiya ne mana. Ina hankali a cikin maganar k’in haihuwa don kawai kin fi shekara arba’in? Rashin lafiya ne zai hanaki haihuwa ko kuma don tsabar raina Rahamar Allah ne? Gashi nan kina gani wasu neman haihuwar suke yi amma har su mutu Allah baya basu, amma ke saboda rashin godiya da jan ido shine kike neman kashe halittarsa daya baki ba tare da ikonki ko taimakonki ko na sisi ba! Ba zan ce ya dawo ba, kuma ko ya dawo ni ina bashi shawaran ya k’ara aure tunda ke cikinki bana haihuwa bane sai na tara abinci.” “Allahu Akbar.” Aka k’ara tada kabbara. “Yanzu kuma sai kaji tace bata son kishiya.” Fad’in Mallam Nafi’u yana kallon mutanen masallacin. “To bakya son kishiya, bakya son haihuwa wa zai zauna dake a haka? Mata kuji tsoron Allah domin wata mijin baya sani take zuwa take zubar da cikin, da ke da mai kashe mutum da wuk’a wallahi duk hukuncinku d’aya kuma zaku gane baku da wayo idan kuka tsaya a gaban Allah ranar gobe k’iyama. Kuma shin kina da tabbacin yaran da kika tara zasu rayu ne? Wallahi komin yawansu Allah zai iya d’aukansu a lokaci guda idan ya so. Sau nawa kike jin iyali miji, mata da ‘yayansu sun mutu a dalilin hatsari, gobara, 6arayi masu fashi da makami da sauransu? Kin tabbatar ke da iyalin naki kun tsira daga dukkan wad’annan jarabawar ne? Kar ku bari rud’in duniya da wasu dalilai marasa kan gado su jawo muku fushin Allah. Wallahi kuji tsoron Allah ku sani cewa yana sane da duk abunda kuke yi na 6oye da kuma na sarari. Alaramma karanta tambaya ta gaba.” Laila da take zaune a falonta tana jin wa’azin jikinta yayi matuk’ar sanyi game da kalaman Mallam Nafi’u. Ita yara biyu gareta wanda d’ayan hanyar daya d’auka bata tunanin ko ta mutu zai mata addu’a, sannan ina take da tabbacin Sabrin zata kai har tsufanta ko kuma zata ci moriyarta? Wato Allah yana sonta kuma yana mata Rahama da tanadi amma ita duk bata gani sai neman fushinsa da take yi a kanta. Hawaye ne ya taru a idanunta tana istigfari tare da addu’ar Allah yasa shirin su da Alhaji Abdul yayi aiki, wato Haydar yaji wannan sak’on ya dawo gida. Tana ji a ranta cewa daga yau asabar zuwa gobe lahadi zai iya dawowa a kowanne lokaci matuk’ar ya saurari wa’azin. Tana zaune har aka gama aka fara kiran sallah magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah ta k’ara gyara fuskarta domin har kwalliya tayi domin dawowar Haydar, a falo ta k’ara zama tana waya da Sabrin wacce duk nauyin Laila Beauty ya dawo kafad’unta, “Mama yaushe su Ummii zasu tafi Maiduguri? Kwanaki Uncle Mas’ud ya zo dubani yake bani labari.” “Ina ganin nan da kwana uku ne, ranar Tuesday ko Wednesday. Zaki bisu ne?” Laila ta mata tambayar cikin tsokana. “Ina son ganin Yaya Abul ne Mama. Kullum idan na tunashi sai naji babu dad’i a zuciyata.” Tayi maganar cikin sanyin murya cike da damuwa. “Kici gaba da mishi addu’a ki kuma rage damuwa a ranki. Insha Allah komai zai zo ya wuce tamkar ba’ayi ba. Batun zuwanki kuma ki bari sai na tashi zuwa mu je tare. Wannan zuwan su Ummii daban ne ba wai na duba Abul bane.” “Kaala Abdi zai rasa inda zai da kanshi idan ya ganta.” Sabrin ta fad’a cikin farin ciki. “Don Allah waya fad’a miki?” Laila ta tambayeta cikin mamaki domin sun 6oye bayyanar Ammi ga mutane da dama bayan Ammin tace haka take so. “Uncle Mas’ud ne ya fad’a mini tunda ke baki yarda dani ba kin 6oye mini. Mama hankalina ya k’ara kwanciya akan aurenki da Uncle Haydar tunda naji cewa su jininmu ne. Allah ya bayyanashi ya kuma shiryi Yaya Abul.” Laila kasa cewa komai tayi illah, “Amin.” Suka yi sallama ta kashe wayarta tana cewa inama Abul ya yarda da aurenta da Haydar kamar yanda Sabrin ma ta yarda dashi, ai da matsalolin su da dama basu faru ba. Har aka idar da sallah isha Laila na zaune ta kasa motsi domin kar Haydar ya dawo ya buga k’ofa bata kusa. ‘To in kuma a wani gari can nisan duniya yake fa?’ Wata zuciyar ta raya mata wanda ta samu amsarta nan take wato, in dai a wani gari yake zai yi wuya ya iso yau sai dai gobe ko kuma jibi. Zata jirashi, zata kuma cigaba da addu’a har ya bayyana ta nuna mishi soyayyar da bata ta6a mishi irinta ba. Tana tashi zata shiga d’aki tayi sallah taji ana kwankwasa k’ofa wanda yasa tayi saurin isa ta bud’e tana fatan Haydar d’inta ne. Ganin Mas’ud da tayi yasa jikinta yayi sanyi tace, “Kai ne?” “Dama waye kike tsammani?” Ya mayar mata da tambaya yana shigowa cikin falon bayan ta bashi hanya. Bata ce komai ba har ta zauna shima ya bita ya zauna yana karantar yanayinta. “Wa kike jira Kalti? Sannan yau na ganki different.” “Ka ga nayi kwalliya ko?” Ta tambayeshi tana murmushin dole wanda iyakarsa fatar baki. “Yes, kin yi kwalliya.” Ya amsa babu 6oye-6oye. “Ina son in fad’a maka wani abu amma kar kaga laifina domin ni d’in mai nema da lalu6e ne a cikin duhu.” Gyad’a kanshi kawai yayi yana kallonta kwakwalwarsa ta kasa bashi abu d’aya da take son fad’a mishi. Ko dai tafiyan Haydar ya fara rud’ata ne? A nan Laila ta bashi labarin yanda ta kira Alhaji Abdul da kuma tambayar da suka aika ga Mallam Nafi’u, aka karantashi ana uku bayan dubbannin tambayoyin da ake jiran amsarsu tun na wancan satin. Shiru yayi bai ce komai ba har na tsawon minti d’aya yana kallon gefe yana tunani. Ganin shirun yayi yawa yasa ta dubeshi fuskarta cike da damuwa tace, “Nayi kuskure ko?” “Ko kad’an. Duk wanda yake cikin hali makamancin naki abunda zai yi kenan, zai kar6i duk wani opportunity da yazo gurinshi don ganin ya cimma nasara. Allah yasa hakan ya zama sanadiyyar samun shi.” Ya fad’i hakan yana kallonta fuskarsa babu alamun 6acin rai ko kad’an. “You are not mad at me?” Ta k’ara tambayarshi domin kamar bata yarda da furucinshi ba. “Why would I be mad at you Kalti? All you are trying to do is to bring your husband back. Sai dai nan gaba duk abunda zaki yi let me know muyi shawara tare, kuma ba zan hanaki duk hukuncin da kika yanke ba, ko na nuna shawaran naki bai mini ba I will support you a yi yanda kike so.” “I’m sorry ban fad’a maka da wuri ba, naga yanda ka d’auki Alhaji Abdul da fushi yasa nayi tunanin baza ka ta6a yarda in yi magana dashi ba.” “You are right, na tsaneshi.” Shiru suka yi na wani lokaci sannan Mas’ud ya dubeta yana cewa, “Dama nazo miki sallama ne gobe zamu tafi Maiduguri dasu Ummii, sannan jiya an kama Madu akan kud’in marayun daya cinye. K’arshenta gidan da yake ciki da wasu k’adarorinshi za’a sayar a biya marayun kud’in gadonsu, wannan labarin da Ummii taji yasa ta nemi tafiya gobe saboda bata son cigaba da zama a gidan haram ana ciyar da ita da haram.” “Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un. Abun har ya kai haka?” Laila shiga cikin rud’u lokaci guda. Gyad’a kai Mas’ud yayi kana yace, “Hajja ma ta kwashi yaran ta tafi dasu gidan iyayenta shekaran jiya.” “Ita kuma menene ya had’asu?” Laila ta tambaya cikin mamaki sanin halin Hajja na hak’uri. “Tun lokacin da ya gane Alhaji Abdul ya nemi Jamila ya kasa zama a gidanshi ya kuma daina basu kulawa, hatta kud’in cefene da wani buk’atunsu na rayuwa ni nake basu idan naje gaishe da Ummii. Dalilin da yasa aka kamashi kuma yaje sayar da shagon daya ragewa marayun ne suka kaishi k’ara aka rufeshi. Abun dai babu dad’in ji kawai don wasu abubuwan ma babu amfanin fad’a.” Dafe kai Laila tayi tana jin bak’in ciki a ranta don ko babu komai Madu yayanta ne, uwa d’aya uba d’aya take dashi. Ko a baya da Hajiya Shatu take kawo mata k’orafin abunda Madu yake yi da kud’in marayun bata san yakai har haka ba. “Yanzu wa zai tsaya mishi tunda kai zaka tafi Maiduguri gobe?” “Abokansa da suka ci kud’in tare kuma suke mara mishi baya su suke kanshi.” Ya bata amsa yana tashi tsaye. “Amma Mas’ud bai kamata mu watsar dashi ba, yana buk’atar taimakonmu.” “Idan zaki yi bazan hanaki ba amma Ummii tace in fad’a miki bata yarda ki fita ba sai da dalili mai k’arfi na rashin lafiya ko neman abinci wanda nasan bazaki nema ba har inje in dawo, kwana biyu kad’ai ni zan yi. Idan Haydar ya dawo kiyi saurin sanar dani don Allah, komin dare zan zo.” Gyad’a kai Laila tayi tana murmusawa don ta lura hatta shi Mas’ud d’in yana d’okin ganin Haydar, ashe ba ita d’aya bace wacce take kewanshi. “Allah yasa ya dawo d’in. Idan ka dawo ka d’auko mini motar Haydar a ajiye a nan.” Ta fad’a tana binshi a baya. Bud’e k’ofa yayi yace, “Shikenan. Ina ganin kafin mu wuce su Ummii zasu zo su dubaki, kiyi tsammaninsu da safe.” Da haka suka yi sallama Laila ta rufe k’ofar ta shiga d’akinta don gabatar da sallan isha. Bayan ta idar ta k’ara dawowa falo ta zauna zaman jiran tsammani, har ta fara gyangyad’i daga zaune bata hak’ura ba. K’arfe sha d’aya da rabi ta farka daga baccin da tayi a gurin zuciyarta na bugawa cikin sauri domin bata san tayi baccin ba, duba agogo ta fara yi tayi salati kana ta mik’e jiki a sanyaye ta rufe falon ta shige d’akinta. Washe gari da safe k’arfe bakwai su Ummii da Ammi suka sauk’a a gidan Laila don mata sallama. Bayan sun gaisa Laila ke cewa, “In kun tafi sai yaushe kenan zaku dawo.” “Sai Mas’ud ya nema mana gurin zama, sauran kayana da suke cikin gidan Madu kuwa zai kai store d’in gidanshi idan ya dawo.” Ummii ta bata amsa. “Ummii wai ke kika hana a bi sawunshi?” Laila ta sake mata wata tambayar don bata so hukuncin da Ummiin ta d’auka ba. “Ni ce, kuma ban yarda wani ya sa6a ba. Suwaiba tashi mu tafi.” Ta fad’i hakan tana mik’ewa tsaye. Ammi da take ta kallon Laila tun shigowarta tayi zamanta tana cewa, “Kuyi gaba zan d’an yi magana da ita.” Sai da su Ummii suka fita sannan Ammi ta dubi Laila wacce kanta ke k’asa ta k’i su had’a ido tace, “Yanda na zo na sameki na kuma lura dake kina cikin damuwa, nasan dole zaki damu amma karki bari yayi yawan da zai jawo miki matsala ke da d’an cikinki. Babu abunda zai fi yiwa Haydar dad’i irin yaji kin lura da cikin nan tamkar yana nan, ki dinga kula da cin abinci domin naga kin rame kamar ba ke ba. Don Allah ki kula ki kuma lura da kanki, Allah ya rabaku lafiya. Wata nawa ne cikin?” Laila kunya taji kamar ta nitse k’asa domin bata yi tsammanin maganar da Ammi zata mata ba kenan. Daburcewa tayi ta fara murmushi nervously tace, “Ya shiga na uku.” “Ikon Allah. Kuma duk wannan lokacin baki sani ba?” Ammi tayi tambayar cikin mamaki domin ai ciki yana k’arami yafi sauk’in cirewa, kenan Laila bata san dashi ba sai yanzu. Wannan karon shiru Laila tayi tana jin nauyin tambayar da Ammi ta mata, wanda ta lura ita kwata-kwata abun bai bata kunya ba. “Tsakanina dake babu kunya ko surkunta Hajiya Laila, ni a matsayin yayarki nake kuma abokiyar wasanki. Kina jina.” “To Ammi.” Kawai Laila ta iya fad’a amma har cikin zuciyarta bata tunanin zata iya daina jin kunyar Ammi. Sannan ta yaya zata iya bud’an baki ta fad’a mata cewa period d’inta bai daina zuwa ba sai wannan watan? Ai abun da kunya wallahi. Sallama Ammi ta mata data lura Lailan ta kasa sakin jiki da ita. Har bakin mota ta rakasu suka tafi tana jin kamar ta bisu itama. Can da rana misalin k’arfe biyu da kwata Alhaji Abdul ya kira Laila ta d’auka tace, “Bai dawo ba.” “Na sani, don Allah karki kashe wayar magana nake son yi dake.” Yayi saurin fad’a daya lura tana son kashe wayar. “Akan me kenan?” Ta tambayeshi tana jin wayar na gundurarta. “Akan Ammi ce. Wallahi tun da ta dawo rayuwar mahaifina ya kasa sukuni yana zuwa gidan Ummii don su gana amma ta k’i sauraransa. Nasan tana mishi hakane duk akan abun da na yiwa Haydar d’anta. Ki fahimtar da ita cewa na canja, wallahi na canja bana yiwa Haydar mugun fata ko mugunta. Ko wani ne ya ta6ashi a yanzu wallahi sai inda k’arfina ya k’are. Ki bata hak’uri kar ta mishi hukunci akan laifin da ba nashi ba, laifin da bai ma san anyi ba sai ranar data bayyana. Don girman Allah ki taimaka mini kar abun ya mini yawa, yana fushi dani don abun da na yiwa Haydar yanzu kuma ya k’aru da cewa Ammi ta k’i sauraronshi.” Ajiyar zuciya Laila ta sauke kana tace, “Yanzu kam Ammi bata nan yau ta tafi Maiduguri don ganawa da mahaifinta. Magana a waya kuma ba zai yiwu ba sai dai idan sun dawo.” “Shikenan, zan fad’awa Baban kawai yaje ya sameta a can gaban iyayenta zai fi mutunci.” “Kar ka kuskura kace ni na fad’a maka.” Tayi warning d’inshi domin bata son koda wasa a san tana waya dashi. “Insha Allah bazan fad’a ba, nagode.” Yana fad’in hakan ta kashe wayarta tana jin zullumi a ranta kan wannan al’amari. Shin ya Haydar zai d’auki wannan maganan wai cewa Alhaji Abdul Yayanshi ne wanda suke uba d’aya? Sannan ya matsayin auren Baba da Ammi yake a yanzu da yake neman ta dawo gidanshi a matsayin matarsa? Yaya Haydar zai yi? Sai da Mas’ud ya dawo daga Maiduguri Laila ta samu labarin duk abunda ya faru a can.

Chapter 23 of 32