dama ni na had’aku. In kuma kika mini shirme wallahi tallahi zaki gwammace baki had’u dani ba.” Ya k’arisa maganan yana nuna ta da yatsa tamkar zai kifeta da mari. Amma kuma a zuciyarsa yana fargaba yana kuma addu’an Allah yasa taji tsoro ta fita a harkarsa gaba d’aya.
Jamila bata ce komai ba bayan nan ta had’a kayanta ta fice daga gidan Alhaji Abdul cikin bushewar zuciya da kuma alk’awarin lalata mishi rayuwa kamar yanda ya 6ata mata lokaci a rayuwarta.
Bayan tafiyarta Alhaji Abdul ya saka aka bita a baya akan idan tayi yunk’urin tona mishi asiri a mata lahanin da zai hanata magana ba tare da an kasheta ba tunda bai ta6a sawa a kashe mutum ba. Gyara zamanshi yayi ya kunna recording d’in yana ji zuwa can annurin fuskarsa ta d’auke ya daskare a gurin yana cewa,
“No way!!!” Da k’arfi.
Fitan Jamila daga gidan Alhaji Abdul banki taje ta kwashe duk kud’inta dake cikin account d’inta sannan ta koma gidan Madu. A tsakar gidansu ta had’u da yaran kishiyarta suna kallonta da mamaki domin kwana biyu kenan da tafiyarta garinsu amma shine har ta dawo? Nan k’aramin cikinsu mai shekara biyar ya gudu d’akin mamanshi yana fad’a mata.
Hannatu (Hajja) uwargidan Madu bata saurari yaron ba illa kwa6anshi da tayi tana cewa bata son gulma, kana taci gaba da harkar gabanta domin halin Jamila babu wanda bata sani ba illa zaman hak’urin da take yi da ita. Daga baya ‘yarta budurwa mai shekara sha hud’u Hanifa itama ta kai mata gulmar cewa Jamila na kwashe-kwashe a d’akinta, itama kwa6arta tayi tace babu ruwansu suyi harkan gabansu.
Duk abunta mai muhimmanci Jamila ta kwashe a gidan Madu kana ta fito da akwatunanta biyar cike da kaya tasa yaron Hajja ya kira mata taxi a waje. Bai yi musu ba ya fita da gudu don dama basu so dawowanta da wuri haka ba. Hajja ce ta fito tana tambayar Jamila ko lafiya don sauk’e hakk’in zaman tare ba don tana son hakan ba. A wulak’ance Jamila ta dubeta tace,
“Nisa zan yi. Idan uban yaran ya dawo kice ya duba cikin wardrobe d’ina akwai sak’on shi a ciki.” Da haka tasa sauran yaran suka fitar mata da akwatunan ta bisu a baya Hajja na kallon ikon Allah.
Jamila tana shiga Taxi wanda aka aika bibiyarta ya kira Alhaji Abdul ya sanar dashi cewa ta kwashe kayanta ta bar gidan.
Shi kuma Alhaji Abdul da yake cikin kid’ima yace,
“Ka rabu da ita, sannan kazo zamu tafi Abuja yanzun nan.”
Daga gidan Madu airport Jamila ta wuce tana fatan Allah yasa ta samu jirgin zuwa Niger Republic, tana ga lokaci yayi da itama zata waiwayi gida ba tare da Alhaji Abdul yasan ina ta shiga ba har abada. Cikin sa’a ta samu jirgin da zai je Niamey tayi booking ta gama komai, kafin jirginsu ya d’aga ta tura sak’onni a family whatsapp group d’in zuriyar mijinta irin wanda ta barwa Madu a d’akinta.
Alhaji Abdul bai samu jirgin zuwa Abuja daga Kano ba, hakan yasa dashi da driver tare da Right hand man d’insa wanda ke aikata duk abunda ya buk’ata suka kama hanyar Abuja da mota wajen k’arfe sha biyu na rana. Basu isa ba sai bayan la’asar wanda babu 6ata lokaci suka yi hanyar gidan Baban Alhaji Abdul, wanda ya koma Abuja da zama cikin tsohon gidanshi bayan ya dank’awa d’anshi ragamar dukiyarsa duka.
Suna shiga farfajiyar gidan suka sameshi zaune a veranda yana karatun jarida. Gilashin idanunsa ya cire yana kallon d’anshi da yake fitowa daga mota yace,
“I’m not expecting you Abdul sai next week.”
Alhaji Abdul ya iso gurinshi yana cewa,
“Baba mu shiga ciki muyi magana.”
“Na me?” Tsohon ya furta yana kallon Abdul wanda yake son takura mishi.
“Mu shiga ciki Baba sai muyi maganan a can don Allah.” Yayi maganar muryarsa cike da rok’o don yasan tsohonsa akwai taurin kai idan ya so.
Mik’ewa Baban yayi ya tu6e takalmansa a bakin k’ofar yana cewa,
“Kar ka shigo....”
“....mini da takalma.” Alhaji Abdul ya k’arisa maganan shima yana tu6e takalminshi.
Suna shiga falon ya tsaya kallon gurin kamar yau ya taba shigowa, carpet ne ja malale a falon gaba d’aya sai kujeru k’irar zamanin 19’s masu kafafun katako, sai akwatin tv shima irin na zamanin da tare da set na dinning table da kujerunsu duk na katako. Yanayin tsaruwar falon zai sa kayi tunanin ko kayi amfani da Time traveling machine ne ya mayar da kai shekarun baya.
A kujera Baba ya zauna kana ya dubi Alhaji Abdul wanda ya nemi guri a k’asa ya zauna yana kallon baban nashi.
“Ina wuni Baba?” Ya gaisheshi cikin girmamawa.
“Lafiya kalau, meya kawoka Abuja yau?”
“Baba magana ce tafe dani amma ban san tabbatuwarta ba har sai ka tantance, Ina so ka saurari wannan audio d’in don watakila burinka na shirin cika.”
Cikin rashin fahimtar inda maganar Alhaji Abdul ya nufa Baba ya tsaya yana kallonshi yayin da shi kuma yake danna wayarsa har ya zo daidai inda Ammi ta fara magana.
Hawaye ne ya taru a idon Baba jikinshi ya fara karkarwa ya mik’a hannu ya kar6i wayar ya manna a kunnenshi, lumshe idanunshi yayi hawaye suka zubo a fuskarsa yace,
“Muryar Lu’alu’a ce.”
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
(45)
Madu sai yamma ya dawo gida kamar kullum in aka tashi daga kasuwa, Hajja ce ta shiga sashenshi ta samu yana waya wanda sai daya gama ta mishi sannu da zuwa tare da tsiyaya mishi ruwa a kofi ya sha.
“Ya gida ya yaran? Ban ga babana ba.” Yayi maganan yana washe baki wanda ya bata mamakin meya sameshi haka.
“Cewa nayi su barka ka huta sai zuwa anjima su shigo su maka sannu da zuwa.”
“Hakan yayi. Nikam kinji yaron nan ya saki Laila ko?” Ya fad’i hakan annurin fuskarshi na k’aruwa.
Hajja da a yanzu ta daina mamakin tsanar da Madu yake yiwa Laila tace,
“D’azu na shiga sashen Ummii naji labarin. Abun bai yi dad’i ba.”
“Maganinta kenan, in banda son zuciya irin nata me zai sa ta auri yaron da ta kusan haifa? Duk abunda ya biyo baya laifinta ne kuma Allah ne ya kamata data yaudari Alhaji Abdul. In banda rashin mutunci a ranar aurensu tace wai ta fasa? Ai wannan babu abunda ya kaishi cin fuska.” Ya k’arishe maganan cikin 6acin rai.
Shiru Hajja tayi domin a yanzu ta daina kare Laila a gurin Madu dalilin fad’an da suke yi muddin ta nuna Laila ta fishi gaskiya. Sanin halinsa yasa ta koyi karatun zama dashi domin tasan sun fi kusa tunda uwa d’aya uba d’aya suke, kenan ita ce bare. Sai a lokacin ta tuno da sak’on Jamila ta fad’a mishi.
“Jamila kam ba kwana uku da suka wuce ta tafi garinsu ba? Me kuma ya dawo da ita kuma ta k’ara tafiya? Jeki ki d’auko mini.” Ya fad’i hakan cikin mamakin wannan al’amari.
Hajja fita tayi zuwa d’akin Jamila, kayan falonta komai yana nan sai dai cikin d’akinta ne a wargaje suturunta a k’asa ta watsar. Ta6e baki Hajja tayi tana mamakin wannan abu domin Jamila bata ta6a barin d’akinta a bud’e ba in zata yi tafiya, amma wannan karon gashi har key ta bari a jikin k’ofar falonta.
Wardrobe ta bud’e taga babu komai a jiki sai wata katuwar envelope ta d’auko ta fito da ita zuwa sashen Madu, taso ta bud’e amma wata zuciyar ta haneta ta kai mishi ya k’ar6a yana cewa,
“Me wannan d’in kenan?”
“Wallahi nima ban sani ba don ban bud’e ba.” Ta zauna a gefenshi.
Cikin d’aurewar kai ya bud’e envelope d’in ya zaro wasik’a, hotuna da kuma Disk. Hotunan ya fara dubawa ya danna wata muguwar ashar yana mik’ewa tsaye ganin Jamila matarsa ta sunnah kwance a k’irjin Alhaji Abdul wanda yake bacci bai ma san an d’aukeshi ba.
Wani hoton ya duba yaga bai fito sosai ba amma Alhaji Abdul ne tsirara akan mace wacce ya tabbatar Jamila ce ganin kod’add’un k’afafunta da yayi a gefe da gefen Alhaji Abdul, kenan video ne aka mayar dashi hoto.
Haka yaci gaba da ganin sauran hotunan zufa na keto mishi a goshinsa yayin da zuciyarsa ta tsananta bugawa yana jin kamar ya mutu tsabar takaicin da yake ciki. Watsar da hotunan yayi kana ya jawo wasik’ar ya fara karantawa kamar haka,
‘Nasan kafin kaga wannan wasik’ar nayi nisa a duniya inda baza ka ta6a samuna ba, so don’t even try. Kafin ka aureni ni budurwar Abdul ce wacce take bashi jikinta da kuma zuciyarta a duk lokacin daya buk’ata sai dai ashe shi ba zai ta6a sona ba. Saboda irin son dana ke mishi ya had’amu har ka aureni ba tare dana daina kwana a gadonshi ba, sannan ba tare daka gane ba. Sai dai irin son da yake yiwa k’anwarka yasa na gane har abada bazan samu soyayyarsa ba shiyasa na yanke shawarar rabuwa da kai da kuma shi. Kamar yanda aka had’a baki da kai ake cutar Laila haka muka had’a baki muke cutar da kai yana baka kud’i kana k’ara mishi aiki. Na tafi na barka idan kaga dama ka sakeni in kaga dama kar ka sakeni domin dama ban d’auki aurenka a bakin komai ba. Video da hotuna kuma dama ina ajiye dasu don 6acin rana irin haka, sannan ganinsu zai sa ka tabbatar da abunda nake fad’a.’
Hajja tunda ta lek’a taga abunda hoton ya k’unsa tayi shiru da bakinta bata ce kanzil ba, domin dama tana lura kamar Jamila na huld’a da maza duk da bata zaton cewa Alhaji Abdul ne, saboda tsoron kar aurenta ya mutu ne yasa ta barwa Allah komai ta kuma cigaba da hak’urin zama da Madu domin baza taso ta barwa Jamila tarbiyyar ‘yayanta ba. Domin Madu yana son Jamila baya son abunda zai 6ata mata rai, sau da dama in suka samu matsala Jamila yake bawa gaskiya. Wannan dalili yasa take zama a gidan Madu ba don tana jin dad’insa ba.
A gigice ya isa bakin kayan kallonshi ya saka dvd d’in ya kunna suka fara kallon abunda za’a iya kira da blue film amma wannan na Jamila da Alhaji Abdul. Videos ne kala-kala wanda wani tsayinshi bai fi seconds talatin ba wani ma k’asa da haka domin gudun kar Alhaji Abdul ya gane tana aikata hakan, kenan shima ta shammaceshi ne. Sai daya gama kallon duk abunda yake ciki wanda ya d’auki tsawon minti goma yana hawaye yana huci kamar zaki. Hajja da take gefe ita ke rufe idanunta idan taga wani abun yayi yawa domin kayan aikin Alhaji Abdul da ake nunawa.
“Ina take?!” Madu yayi k’araji yana duban Hajja.
“Tun da hantsi ta tafi bata dawo ba.” Ta bashi amsa cikin tsorita da yanayinsa.
“Sai na kashesu, sai na kashesu dukansu. Sun ci amanata kuma wallahi ba zan barsu ba.” Ya fad’i hakan cikin k’unan rai yana ficewa daga falon kamar zai tashi sama.
Hajja na ganin ya fita ta tattara abubuwan gudun kar ‘yayanta su gani ta kai mishi d’akinshi ta ajiye domin bata son tayi laifi. Amma a zuciyarta taji dad’in abunda ya faru ko ba komai alhakinta dana Laila ne ya kamashi, saboda tana sane da k’untatawa Laila da yake yi da kuma mata sharrin aikata alfasha ba don tana yi ba, wai yana hakan ne duk don tayi zuciya ta auri Alhaji Abdul. To yau ya gane waye fasik’i tsakanin Laila da wanda yake marawa baya, tunda iskancin Alhaji Abdul bai tsaya a kan kowa ba sai matarsa ta sunnah. Fatan Hajja a yanzu shine Allah yasa Jamila bata saka musu cutar HIV ba domin infection kam suna dashi dukansu, kuma magani ya gagara aiki don Madu yace ba zai je asibiti ba.
Madu yana fita gidan Alhaji Abdul ya nufa bayan ya 6oye wata shafceciyar katako a cikin babbar rigarsa, ana kiran magriba ya isa gidan sai dai abun bak’in ciki maigadi ya fad’a masa cewa baya nan yayi tafiya Abuja.
“Yaushe zai dawo?”Madu ya tambaya kamar zai mutu a gurin tsabar takaici da bak’in ciki.
“Wallahi bai fad’a mini ba domin cikin gaggawa yayi tafiyar.” Maigadin ya k’ara bashi amsa don yasan Madu abokin uban gidanshi ne.
A zuciye ya koma cikin motarshi ya daki siterin ya fashe da kuka kamar k’aramin yaro, wanda zai iya cewa ko ubanshi daya mutu bai mishi kuka irin haka ba. Ya kai minti goma a haka sannan yayi tunanin kiran Alhaji Abdul yaji ko yasan abunda Jamila tayi, in bai sani ba kuwa zai barshi a duhu har sai ya dawo ya masa lahani kamar yanda yaci buri. Kiran wayarshi yayi wacce ringing biyu Alhaji Abdul ya d’auka ba tare daya san me yake faruwa ba yace,
“Madu ya aka yi?”
Sai a lokacin Madu ya fara ganin rashin girma da Alhaji Abdul yake gwada mishi, saisaita muryarsa yayi kana ya amsa,
“Na zo gidanka ance ka tafi Abuja, yaushe zaka dawo?”
“Yanzu ma haka ina kan hanyar dawowa zan ganka nan bada jimawa ba, sannan ina tafe da albishir wanda zaku yi mamaki.” Ya fad’i hakan with excitement in his voice.
“Nima akwai abunda zan maka albishir dashi idan ka dawo.” Fad’in Madu yana ji kamar ya shiga wayar ya kasheshi nan take.
“To Allah ya kaimu.” Alhaji Abdul ya amsa ba tare daya kawo komai cikin ranshi ba domin shi yama manta da wata Jamila.
Yinin ranar sukuku su Laila suka yi ta, magana wannan wahala yake bata sai addu’a kawai da take tayi tana danne zuciyarta dalilin su Ummii sun hanata kuka. Mas’ud kuwa tun daya kawo musu labarin cewa bai samu Haydar ba ya k’ara fita bai dawo ba sai bayan magriba. A nan ya samu Ammi na cewa zata koma gidanta.
“Ba zan sake barin kiyi nisa damu ba, a nan zaki cigaba da zama har Haydar ya bayyana. Sai dai anjima in anyi sallar isha Mas’ud zai kaiki gidan ki d’auko kayanki da zaki buk’ata.”
Ammi bata yi musu ba ganin Ummii ta gama yanke shawara, Mas’ud guri ya samu ya zauna yana tambayar lafiyarsu suka amsa da ‘Alhamdulillah.’
“Shiru har yanzu babu d’uriyarsa ko?” Ammi tayi tambayar ga Mas’ud with hopeful eyes.
Girgiza kanshi yayi yace,
“Wallahi duk inda nake tsammani bai je ba, ga wayarshi bata shiga. Ammi ki kwantar da hankalinki Haydar ba yaro bane, idan ya sauk’o zai dawo gida Insha Allah.”
“Allah yasa amma ina tsoron zuciyar Ali duk da cewa yana da hak’uri, amma wannan karon abun ya taru ya mishi yawa ne.”
Laila na jin hakan ta sunkuyar da kanta k’asa domin ko ba’a fad’a ba tasan har da laifinta a 6acewar Haydar.
Babu wanda ya k’ara cewa komai falon ya k’ara yin shiru kowa da tunanin da yake yi a zuciyarshi. A nan ne Mas’ud ya d’auko wayarshi ya shiga whatsapp don turawa Haydar sak’o amma sai yaga messages da yawa a family group d’insu wanda ‘yayan Ummii da surakananta mata ne kad’ai a ciki babu yara. A nan yaci karo da munanan hotuna da videos d’in da Jamila ta tura bata ko kunyar cewa itama za’a kalli tsiraicinta, don muradin asirin Alhaji Abdul da Madu ya tonu bata damu da a ga jikinta ba after all dama karuwa ce.
“Subhanallah.” Mas’ud ya furta yana karanta dogon rubutun da Jamila ta bari wanda yake bayyana duk kullace-kullacen da Alhaji Abdul yayi da kuma wanda Madu yayi.
“Lafiya Mas’ud?” Ummii ta tambayeshi tana dubanshi.
“Ha.... fad’a ake yi a wani gari aka turo hotunan a group. Kalti duba wayarki ki gani.” Yayi k’arya don baya son Ummii taji wannan k’azantar daya k’ara faruwa da zuriyarsu.
Laila bata motsa ba balle ta kai hankalinta kansu, hakan yasa Mas’ud ya kira sunanta da d’an k’arfi ta d’ago ido tana kallonshi fuskarta blank kamar wacce bata da emotion.
“Check our family whatsapp group please, it’s important.” Ya zuba mata ido wanda hakan yasa ta gane abunda yake son ta gani mai muhimmanci ne.
D’auka wayar tayi ta kunna data kana ta shiga ta fara cin karo da duk abunda Mas’ud ya gani tana kawar da kanta, don ita kam ta kasa playing videos d’in tayi saurin scrolling k’asa zuwa dogon rubutun. Tana karantawa hawaye ya fara gangarowa daga idanunta zuwa k’uncinta tana jin bak’in ciki da kuma takaicin aka yi ta kasa gane cewa duk wani 6atanci da ake yiwa rayuwarta laifin wad’annan mutane biyun ne. Wani irin tsana suke yi mata da har zasu yi sanadiyyar lalacewar d’anta? Wannan shine son da Alhaji Abdul yake cewa yana yi mata? Sannan meyasa Madu ya tsaneta tun tasowarta? Laifin me ta mishi?
Mas’ud ne yayi mata alama da ido kan su fita waje, shi ya fara fita Laila tabi bayanshi zuwa farfajiyar gidan inda suka yi parking d’in motocinsu.
“Mas’ud wani laifi muka yi muke ganin bak’in ciki irin wannan a rayuwarmu? Anya kuwa ba asiri aka yiwa zuriyarmu ya fad’i a kaina nake shiga garari da tashin hankali ba? Me wannan? Don girman Allah menene wannan? Matar yayana fa take zina da wanda ya nemi aurena! Wanda tun farko an d’aura auren nasu ne don kawai a samu galaba a kaina. Wayyo ni Laila ina zan sa kaina?!” Ta k’arisa maganan tana durk’ushewa a gurin tana kuka kamar ranta zai fita.
Sai a lokacin ta samu tayi kukan rashin Haydar da kuma duk abunda yake nuk’urk’usanta duk tsawon wannan lokaci da take yawo dashi with a brave face.
Mas’ud bai ce komai ba illa isa gurinta da yayi ya dafa kafad’arta yana mugun jin tausayinta a ranshi. Gaskiya ne yayarshi tana cikin jarrabawa sai dai ya mata addu’an Allah yasa taci. Sai da tayi mai isarta sannan ya mik’a mata hannu ta tashi yana bata hak’uri.
“I’m sorry da duk abunda yake faruwa a rayuwarki and I hope you’ll be strong, a yanzu da asirinsu ya tonu baza su sake gigin aikata wani abun ba. Sai dai baza mu barsu haka ba, zamu kai k’ararsu hukuma a kwato miki hak’k’inki duk da cewa hakan zai sa a ta6a Madu.”
Girgiza kai Laila tayi da sauri tana share hawayen fuskarta tace,
“Babu k’ararsu da zan kai domin duk hukuncin da za’a yanke a kansu ba zai kai rabin illar da suka yiwa rayuwata ba. Sun mini cutan da in ba Allah ba babu wanda zai kwato mini hak’k’ina. Wallahi na barsu da Allah saboda sun mini zaluncin da babu wanda ya ta6a mini irinshi. Sun cuceni cuta mafi muni Mas’ud, wallahi ban yafe musu ba.”
Gyad’a kai yayi cikin yarda da magananta domin tayi gaskiya. Sai dai zasu iya yiwa Alhaji Abdul abunda ya yiwa Laila ta hanyar watsa hotunansu a yanar gizo.
“Zan watsa hotunan shima yaji abunda kika ji.”
“Karka yi don Allah, saboda duk wanda yaga tsiraicinsu kana da kason zunubi, Allah kuma babu ruwanshi da cewa ramawa kayi saboda ka yad’a alfasha ne a gurinshi. Tunda muka barsu dashi nasan gaba zai saka mini.”
“Allah ya k’ara miki hak’uri.” Ya mata addu’a cikin ganin jajircewarta don tayi tawakkali ba kad’an ba.
“Amin. Ka kira su Yaya Ajidde dasu Safa ka fad’a musu su goge sannan kar su fad’awa Ummii don wannan abun zai iya tayar mata da ciwonta, yau ma nayi mamakin da babu abunda ya faru.”
A gabanta Mas’ud ya kira ‘yan uwan nasu ya sanar dasu halin da ake ciki tare da hukuncin da suka yanke, Marwa da dama tuntuni ta gani tace,
“Ni dana gani tsoro naji na kasa kiranku.”
Yayarsu Ajidde da dama bata damu da shiga whatsapp d’in ba tambayar lafiyar Ummii ta fara yi don a tunaninta kota sani, Mas’ud ya sanar mata cewa baza su fad’a mata ba sannan ya sanar da ita duk halin da ake ciki har na bayyanar Ammi ‘yar kawunsu.
“Don meyasa tuntuni baku sanar dani ba? Ina take yanzu?”
“Wallahi ita Ammin ce ta hana a fad’awa kowa akan cewa tafi son ta fara zuwa Maiduguri su ganta. Ba laifina bane kiyi hak’uri, ke d’in ma karki fad’awa kowa.”
Bayan sun gama waya ya kira Naana matarsa itama yace ta goge chats d’in duka. Daga nan magana Laila da Mas’ud suka yi mai tsayi akan abubuwan da suka faru da kuma damuwar da Laila take ciki akan Haydar, sosai ya kwantar mata da hankali domin yanzu tausayinta yake ji bana wasa ba.
“Come for a warm hug.” Yace da ita yana ware hannayensa domin yasan she likes someone to hug her idan damuwa ya mata yawa.
Bata musa ba ta isa yayi caging d’inta da hannayensa ta rufe idanunta tana Ajiyar zuciya.
“You don’t smell like him.” Tace da Mas’ud tana barin jikinshi.
Murmushi yayi yace,
“Saboda ni k’aninki ne ba Haydar ba. Kuma next time don’t expect a hug from me.”
Itama murmushin tayi tana kallon k’anin nata cikin k’aunarshi saboda no matter what baya ta6a fushi da ita na tsawon lokaci, kuma duk abunda tayi ko bai mara mata baya a lokacin ba daga baya he’ll support her. Mas’ud shine meaning na ‘who got your back’.
Motarshi ya shiga kana yace,
“Ki fad’awa Ammi ta fito in kaita gida ta d’auko kayan nata.”
Laila tana shiga ta sanar da Ammi sak’on Mas’ud tana k’asa da kai cike da kunyar abunda ta aikatawa d’anta, sannan har lokacin Ammi bata mata maganar cikin ba balle ta nuna ranta ya 6aci.
Minti talatin da fitansu Mas’ud suka dawo gida, a nan suka tarar da Ummii na yiwa Laila fad’a kamar dama jira take yi su fita. Tana ganinsu tayi shiru amma bata bar hararar Laila ba, ganin haka yasa Ammi ta fara magana,
“Kalti ki daina mata fad’a tunda abunda ya faru ya riga daya faru, sannan ku bakwa ganin girman laifinshi ne daya saketa? Wallahi nafi ganin laifin Ali fiye dana Laila duk da cewa itama bata kyauta ba. Sannan shi da kanshi yayi niyyar tafiya babu wanda yace ya tafi, kenan duk lokacin da yaji ya huce zai dawo babu wanda ya sani. Ba zai ta6a yin nisa ya barni ba duk da cewa nima na mishi laifi, saboda Ali yana sona kuma yana tausayina ya kuma san zan shiga damuwa idan baya kusa dani. Insha Allah ba zai jima ba zai dawo, Insha Allah.” Tana gama fad’in hakan ta shige d’akin Ummii dalilin hawayen daya taru a idanunta, don wannan maganar da tayi kamar tana jaddadawa kanta ne basu ba.
Laila da tasan zaman gidan ba zai mata dad’i ba k’arfe goma ta fara neman inda jakarta yake zata koma gida, a d’aki ta samu su Ummii da Ammi suna magana ta musu sallama ta dawo falo gurin Mas’ud zasu tafi. A nan suka ji wasu maza na sallama a tsakar gida Mas’ud ya amsa yana cewa,
“Bismillah ku iso.”
Alhaji Abdul suka fara gani ya shigo sannan bayanshi babanshi ne wanda ya tsufa amma da sauran k’arfi a jikinshi.
Sanin daraja irin ta manya yasa Laila da Mas’ud basu yiwa Alhaji Abdul rashin mutunci ba, ko ba komai yaci albarkacin ubanshi. Gaisheshi suka yi suna hararar Alhaji Abdul kana Laila ta shiga d’aki ta fad’awa Ummii tayi bak’i,
Ummii bata jima ba ta fito tana musu maraba tana tuna cewa rabonta da Baban Abdul tun rasuwar mijinta da yazo ya mata ta’aziyya. Bayan sun gaisa d’akin yayi tsit ana jiran aji dame suka zo. Su Laila kuwa fargaba suka shiga dalilin basa so Ummii tasan abunda yake faruwa na matar Madu, suna kuma mamakin tsaurin ido na Alhaji Abdul da ya iya shigowa gidan bayan cin amanar daya musu, ba tare da sun san cewa shi bashi da masaniya akan abunda Jamila tayi ba.
Baban Abdul ne ya fara magana bayan yayi gyaran murya yace,
“D’azu Abdul yaje Abuja yake gwada mini wani recording wanda na gane d’ayan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 32