Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tace, “Yana gidan Mas’ud ko?” Laila ta gyad’a kai tana share hawayen fuskarta. “Ki barshi a can d’in, zan kira kawunku Abdi ya nema mishi magani, in ma turashi can za’ayi sai Mas’ud ya kaishi a killaceshi a can, shi da kanshi zai k’i kayan maye ko ajiyewa aka yi a gabanshi. Na rasa gane me yake damun yaron nan, haka kawai ka k’i jinin mahaifiyarka tayi aure? Ki kwantar da hankalinki, da yardar Allah zai daina kinji.” “Allah yasa Ummii. Sai ina ganin kamar ban kyautawa Aliyu ba dana bari d’anshi ya fara shaye-shaye.” “Wannan ba iko ko sakacinki bane Laila. Kici gaba da mishi addu’a domin ke uwace, addu’arki bazata ta6a fad’uwa a k’asa banza ba.” Sai da Ummii ta tabbatar Laila ta nitsu wanda ita kanta Lailan mamakin yanda Ummii ta sake da ita take yi. “Ya zamanku ke da mijin naki?” ‘Dan daburcewa tayi na wani lokaci sannan tace, “Lafiya, muna zaman lafiya.” Ummii ta kalleta da kyau wanda Laila ta k’i su had’a ido tana kawar da kanta gefe. “Laifi biyu baya gyara d’aya Laila. Sannan ki gyara ayyukanki sai Allah ya kar6i addu’o’inki.” “Ummii..” “Shawara na baki ban buk’aci sanin komai daga gareki ba. Amma ki daina rik’o, abunda ya wuce ya wuce kisa a ranki haka Allah yaga dama yayi kuma ya fiki sanin me yake yi. Komai da kika ga ya faru akwai dalili, ki bi yanda Allah yayi sai kiga kin tsira kin kuma yi nasara a k’arshe.” Sunkuyar da kai Laila tayi k’asa tana aikin tunani, a nan ta gane har lokacin akwai halinta da bata daina ba wato al’amarin ‘yayanta na affecting life d’in makusantanta ba tare da tayi la’akari da suma suna buk’atar kulawarta ba. Sannan ta yaya Allah zai amsa mata addu’arta alhali ita da kanta ta tauyewa wani bawa hakkinsa? Ina laifi biyu zai gyara d’aya? Ummii ta fita gaskiya kuma zata gyara nata domin itama Allah ya gyara wanda take neman ya gyara mata. “Shukran Ummii. Sa’usluhu.” “Allah ya kad’a fitina ya shiryeshi shi kuma.” “Ameen Ummii.” Sai data k’ara awa d’aya a gidan sannan ta kira Haydar tace ta gama abunda zata yi. “Ki jira bari in tashi a aiki sai in biyo in d’aukeki.” “Amma kai kace inna gama in kiraka, kuma ina son komawa gida in d’aura maka abinci ne.” Ta dafe goshinta domin yana neman saka mata ciwon kai. “Na d’auka baza ki jima bane, amma yanzu na kusa tashi ki jirani ina zuwa bayan azahar.” “Baka ji me na fad’a bane?” “Me kika ce?” Wani haushi ne yazo ya tsaya mata a wuya tace, “Shikenan sai ka zo.” “Baki fad’a mini abunda ban jin ba Laila.” “Don Allah mu bar maganan sai ka zo kawai.” Tana fad’in hakan ta kashe wayarta tana rufe idanunta. Ummii ta bita da kallo tana murmusawa domin hakan ya tabbatar mata cewa Laila na k’ok’arin yin biyayya ga mijinta. “Kin fasa tafiya yanzun kenan?” Laila ta d’ago ido ta dubi Ummii wacce har lokacin ke murmusawa sai itama taji dariya yana son kwace mata. “Wallahi Ummii haushi ya bani yau, kafin in fito na kirashi na fad’a mishi zan fita yace zai zo ya d’aukeni nace ya bari, duk don ina tausaya masa kar ya fito yasha wahalan kaini kuma ya koma office. Wai daga baya yake cewa wai kar in fita da laffaya in saka hijabi, kiji mini kinibibi fa Ummii.” “Mijin naki ne yake kinibibi Laila? Ashe baki d’aukeshi shugaba kuma babba a gareki ba?” A nan Laila tayi dana sanin fad’awa Ummii wannan batu, domin ganin murmushin da take yi ne yasa ta fad’a mata ba don tana tunanin zata goyi bayanta ba. Fad’a ta mata sosai tamkar dama jira take yi, ita dai kanta na k’asa tana bata hak’uri. “Ayi hak’uri Ummii bazan sake ba.” Da haka suka yi shiru suka koma gidan jiya wanda dama magana mai tsayi bata shiga tsakaninsu. Bayan an idar da sallah Haydar yayi sallama ya shigo falon, yanda Ummii ta k’ar6eshi cikin farin ciki da mutuntawa yasa Laila tayi rolling idanunta tana shiru. Wani kallo Ummii ta watsa mata bayan sun gama gaisawa ta dubi Haydar tace, “Sannu da zuwa, ya hanya?” “Lafiya kalau. Ya kike samesu?” Ciki-ciki ta amsa kana ta kawar da kanta gefe tana neman inda ta ajiye jakarta. “Karka yarda ka bari tana juyaka kana yin abunda take so domin kaine babba kuma shugaba a kanta. Idan tayi laifi ka gyara mata kar kaga yawan shekarunta domin matarka ce a k’ark’ashin k’afarka take. sannan idan ma hukunci ne ya kamata ka mata daidai da laifinta. Allah ya k’ara had’e kanku ya kauda fitina.” Shi dai Haydar kanshi na k’asa sai kad’awa yake yi yana cewa, “Insha Allah, Insha Allahu Ummii.” K’atuwar ledar daya shigo da ita ya kai mata gabanta ya ajiye tana saka masa albarka. Ganin haka yasa Laila ta mik’e tsaye tayi mata sallama ta barsu a falon domin taji haushi ba kad’an ba. A yanzu ma Haydar na nuna mata ikonshi inaga yanzu kuma da Ummii ta mara masa baya? Ta kai minti biyar a waje sannan ya fito yana washe baki ya shiga motar ba tare daya kulata ba. Tana ganin hakan ta shiga baya ta zauna amma ya k’i kunna motar. “Laila ki dawo gaba.” “A nan nake son zama.” Fita yayi daga motar ya bud’e k’ofarta kana ya shiga bayan ya zauna yace, “Dama baki san yanda nayi missing d’inki ba, hijabin ya miki kyau sosai.” Ya fad’i hakan yana tura hannunshi cikin hijabin nata. Mutsu-mutsu ta fara dolenta ta fita daga motar ta koma gaba ta kunna motar zata yi driving. Shima fitan yayi ya shiga gaba ya zauna yana kallonta yana murmushi. Sun fara tafiya ta juyo kad’an ta dubeshi taga ya gyara zama yana kallonta kawai. “Me Ummii ta fad’a maka kake ta murna?” “Kawai ta mini nasiha ne tare da bani wasu shawarwari.” Kwafa tayi taci gaba da tafiya yace su shiga wani restaurant zai musu take away. Ba musu ta tsaya ya shiga ciki, dama tayi niyyar kyaleshi ne taga gudun ruwansa idan ya koma gida bai ga abinci ba. Minti kad’an ya fito daga gurin wasu ‘yan mata biyu suka biyo bayanshi suka tsaya suna magana. Wata irin mummunar fad’uwar gaba Laila taji data lura yana musu magana yana murmusawa kuma yana shafa sajensa. Ko da ya dawo mota ya samu ta dawo gefe ta bar mishi driving d’in. Bai ce komai ba ya kunna motar yana bata labarin yanda abincin gurin yake da dad’i shiyasa ya saya musu. Ko uffan bata ce masa ba har ya gama surutunsa yayi shiru, can kuma yace, “Meya faru Laila? Bakya jin dad’i ne?” “Eh.” Ta bashi amsa domin har lokacin zuciyarta na k’una Idan ta tuno yanda yake yiwa ‘yan matan dariya suna binshi da kallo. “Bari mu koma gida kici abinci kisha magani sai ki kwanta.” Suna komawa gida ya zagaya ya bud’e mata k’ofa ya kar6i jakanta suka shiga falo, yanda yaga take cije fuska ya tabbatar bata jin dad’i. “Ki shiga d’aki bari in d’auko tray sai in kawo miki abincin.” Ba musu ta shige d’aki shi kuma ya wuce kitchen da ledojin hannunsa. Band’aki ta shiga ta canja pad sannan ta fito ta sameshi a k’asan carpet yana danna wayarsa. Fita tayi ta jefar da pad d’in a dustbin sannan ta dawo ta zauna a gefenshi ta jawo abincinta. “Nikam d’azu menene ya hanaki tashi daga kan gado kika ce sai na dawo zaki fad’a mini?” “Period d’ina ne ya dawo.” “Menstruation?” Ya tambayeta. “Eh.” “Kwana nawa yake miki Laila?” “Bakwai.” Taci gaba da cin abincinta. Ajiye cokalinshi yayi fuskarsa a kwaye ya tashi ya fita daga d’akin. “Baza kaci abincin bane?” “Na koshi. Ga maganinki a kan tray.” “Kai ka sani.” Ta fad’a a hankali yanda bazai ji ba tana dariya. Bayan ta gama cin abincin ta kira Mas’ud kan labarin Abul. “Yana nan tare dani a Pharmacy, babu inda zai je balle ya samu abunda yake so.” Wata ajiyar zuciya ta sauk’e har idanunta na taruwa ta hawayen farin ciki tace, “Nagode Mas’ud. D’azu naje gurin Ummii take cewa Khalii Abdi zai bashi magani ko kuma a aikashi can su kula dashi.” Sun jima suna magana sannan ta kashe wayar tana jin sanyi a zuciyarta tamkar ta bud’i ido an fad’a mata Abul ya shiryu. Abincin ta kwashe zata kai kitchen ta samu Haydar a falo yana kwance ya kwa6e kayanshi ya bar boxers kad’ai wanda dama haka d’abi’arsa take kamar Inyamuri. Har zata wuce ta dawo ta zauna kusa dashi bayan ta matsar da k’afafunshi tace, “Meya hanaka cin abincin?” “Na k’oshi ne.” “Ka tashi kaci abinci nasan yunwa kake ji.” Ta fad’i hakan tana dariya k’asa-k’asa. Bai kalleta ba yace, “Ina jin dariyan da kike yi kuma kici gaba da yi.” “Yi hak’uri Ruwan Zuman Laila, tashi in baka a baki.” Da kyar ta lalla6eshi ya tashi yaci abincin yana harararta. “To mena maka ne kake ta hararata? In ban manta ba d’azu kai ka mini laifi kuma ina cike da kai.” “Me na miki?” Gyara zamanta tayi ta fuskanceshi fuskarta so serious tace, “Haydar saka laffaya shigata ce na tun asali kuma shine suturar yarenmu. Bai kamata rana d’aya ka hanani sakawa ba sannan kayi tunanin zan kar6a haka kawai ba. Gaskiya ka daina mini irin haka, domin tun daa a hakan ka ganni kace kana sona, bai kamata kuma kazo kana hanani wasu abubuwa dana saba dasu ba matuk’ar hakan bai kaucewa shari’a ba.” “Kina nufin juya duwawu da kike yi maza na binki da kallo ba haramun bane? Karki manta ke matar aure ce wacce in banda fuska da tafin hannu da ka k’afarki duk jikinki al’aura ce. Gaskiya ko a daa abun yana ci mini tuwo a kwarya don dai kawai banida ikon hanaki ne, amma a yanzu da nake da iko dake na hana fita da laffaya sai hijabi.” Takaicin da taji ba’a iya fasaltashi, kallonshi kawai ta tsaya tana yi tana mamakin yanda ya juye ya zama rik’ekk’en mutum ba Haydar mai sunkuya mata idan zai gaisheta ba. “Yayi kyau, duk laifina ne.” Ta fad’i hakan cikin harzuk’a. “Da kika yi me?” Ya tambayeta yana nazarinta a lalace. “Wasu ‘yan iskan yaran ne na ganka tare dasu kuna tsaye a bakin restaurant?” Ta canja maganan domin itama tana son mishi iyaka kamar yanda ya mata. “Laila karki musu shaidar iskanci domin yaran kirki ne.” Ashar ta kwaza a ranta kana ta tashi zata bar gurin ya rik’ota ta fad’o k’anshi. “Ashe ana kishina haka?” Ya fad’i hakan yana dariya. “Ka sakeni Haydar, bana son wasa.” Ranta a 6ace tayi maganar tana neman kwace kanta. “Don ki fini nama a jiki bashi zai sa ki fini k’arfi ba. Ki gama kokawar idan kin gaji zaki daina.” Ya k’ara k’arfin rik’on daya mata yana lasar wuyanta wanda take jin hakan kamar cakulkuli. “Bana so Haydar.” “Ni kuma ina so.” Yanda yake mata yasa ta fara dariya tana nok’ewa sai ya canja guri. Sosai take dariya har tana k’ok’arin fad’ar dasu daga kan kujerar ya d’auketa yayi d’aki da ita tana cewa zai fad’ar dasu. “Jiya kuma ai baki fad’i ba.” Ya bata amsa yana rufe k’ofar. A kan gado ya direta yana murza hannayensa yace, “Ashe dai kina da nauyi.” Matsawa tayi can gefe ta fara had’e fuska tuno da abunda ya mata duk a yau na 6acin rai. Shima hawa gadon yayi ya kashe wutan d’akin ya jawota jikinshi yana cewa, “Baki san yanda maza suke kallon bayanki bane idan kika saka laffaya Laila. Wallahi idan naga wani na kallonki a yanzu da kike matata sai na fasa mishi kai, shiyasa maganin bari kar ma a fara. Amma bazan hanaki sakawa gaba d’aya ba, idan zaki fita shagonki ko gidan bikinku na mata ki saka, amma In har kinsan zaki shiga gari ko kasuwa inda wani namiji zai ganki to ban yarda ba. ‘Yan matan nan kuma ‘yan ajinmu ne wanda muka yi jami’a tare, maganar da muke yi kuwa murna suke mini na auren da nayi har suke fad’a mini suma an saka ranar aurensu zasu aiko mini kati. Haydar naki ne ke d’aya sai yanda kika yi dani.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kana tayi shiru tana jin yanda yake bin jikinta da hannunsa yana ta6a duk inda ya masa. “Bacci nake ji.” Tace dashi tana kawar da hannunsa daga k’irjinta. “Yau kam a tausaya mini ko dabarun matan a mini.” “Haydar.” Ta kwa6eshi tana jin jikinta na canja yanayi. “Please Laila.” Juyowa tayi ta kalleshi taga yanda yayi kalar tausayi kamar bashi yake auna mata doka d’azu ba. “A tausayawa Ruwan Zuman Laila.” Murmushi tayi kana tace, “Kaje kayi wanka tukun.” Kafin ta rufe baki ya tashi da sauri ya shige band’aki. Sai daya wanke jikinshi tsaff sannan ya fito ya sameta zaune a kan gadon hannunta d’auke da goran Zuma tana lasa. “A ajiye wannan abun.” Ya fad’i hakan yana hawa kan gadon. “No, dashi zan maka dabarar tamu ta mata.” Mum Fateey 👌 RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (29) Bacci sosai Haydar da Laila suka bayan nan wanda sai bayan la'asar ta tasheshi yayi wanka yayi sallah, kana ya zauna a gefenta yana tsokanarta tana basarwa. "Idan kaci gaba da mini haka bazan sake maka ba." Ta fad'i hakan tana harararsa. "Wallahi na daina. Kin ga ma fita zan yi, zan je gidan Ammi yau ban ganta ba." Ya fad'i hakan yana kissing kumatunta. Bayan fitarshi Laila ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana jin wani mugun kunya, wai ita ce ta yiwa Haydar wannan abun? Haydar d'in k'anin bayanta? Sai dai ta sani age is just a number, saboda ko a ina ne Haydar shine babba a kanta a yanzu. Motarta ya d'auka ya tafi gidan Ammi, tare da bak'i ya sameta wasu 'yan unguwarsu suka mishi fatan alkhairi a aurensa ya amsa kana ya shiga d'akinsa wanda yake jin yayi kewarsa. Sauran kayayyakinsa masu kyau ya tsinta kana ya had'a tsoffin guri d'aya da sauran tarkacen da baya so zai bawa Ammi ta kyautar ga masu buk’ata. Sai da mutanen suka tafi sannan ya fito ya samu Ammi ya zauna a gefenta sai washe baki yake yi. "Ali yau me ka samu kake ta murna haka?" Dariya yayi kana ya gaisheta ta amsa tana tambayar lafiyar Laila. “Lafiyanta kalau Ammi.” "Yau dai fara'arka ta daban ce, Allah yasa ka dauwama a cikinta." Ta k'ara fad'i tana jin dad'i a zuciyarta ganinshi cikin farin ciki da tayi. "Baza ki gane bane Ammi. Ameen Ameen." "Aikin banza." Tace dashi tana tashi zata d'aura tuwo tana murmushi. Yau aka haifeta ne da zai ce baza ta gane ba? "Ammi ki bar dafa abincin bari in fita in sayo miki." "Kaima kasan abincin waje ba burgeni yake yi ba, nafi son inyi tuwo da miyana gobe in samu na d'umame." "Dama ke ba'a miki gwaninta. Amma akwai wani abu da kike buk'ata ne?" Ya tambayeta yana kishingid'a a jikin gini. "Babu komai Ali. Ina da kayan abinci Alhamdulillah sai fatan Allah ya k'ara maka bud'i." "Ameen. Irin abun girkin baturen nan nake son saya miki ki daina hura murhu." "Gas cooker?" Ta tambayeshi. "Ammi a ina kika san gas cooker? Ni cylinder mai irin tray a saman nan nake nufi." Tsaki Ammi ta ja kana ta fara had'a itace tace, "Ka manta inda muka taso ne? Wani lokacin in bani da aiki ina shiga kitchen gurin Maman Iyabo kuma dashi suke girki." "Ohh haka dai. Gobe kema zan saya miki ki fara amfani dashi. Idan kuma aka yi salary next month zan nema miki wata mata wacce zata dinga kwana dake tana miki aiki." "A'a bana son mai aiki. Zama zanyi haka kurum Ina kallonta tana mini aiki? Ni me zan yi kenan? Ai zama guri d'aya ciwon jiki zai saka mini." Dafe kai Haydar yana jinta tana ta surutai wai bata isa ta zauna bata motsa jiki ba. Sai da tayi ta gama sannan tace, "Muna zuwa gidanka fa ranar jumma'a." "Ku nawa zaku zo?" "Mu goma dai haka zuwa sha uku." "Ammi duk mutanen unguwan zaki kwaso? Haba mana don Allah." Yayi maganar yana tashi zaune don bai ji zai amince da hakan ba. Bata ce komai ba taci gaba da aikin gabanta yana binta da ido. Can ta shiga d'akinta ta fito da kud'i tace, "Ka sayo mini attarugu da albasa na ashirin, daddawan ashirin, sai cittan goma da kuma kafi zabuwa na goma." "Ammi bazan saya miki kafi zabuwa ba. Wallahi cewa ake yi yana saka cancer da ciwon k'oda." "Kai Ali yaushe kaji hakan?" Ta dafe k'irjinta tana kallonsa. Dariya yayi cikin ranshi ya fara mata k'arya. "Jiya a office muna zaune wasu mutane suka zo irin masu wayar da kan al'umma d'in nan. Su suka fad'a mana cewa da kitsen alade ake had'awa kuma kinsan cinsa haramun ne a musulunci." "Kai Ali!" Ta k'ara zaro ido wanda ya bashi dariya sosai. "Da gaske Ammi. Yanzu haka ma na hana Laila sakawa a abincinmu." "Yanzu hanata abu kake yi kai tsaye ko dai shawara kake bata in taga dama ta d'auka?" Girgiza kai yayi yana murmusawa yace, "Ammi kenan. Kina son kiga d'anki bashi da iko da iyalinshi ne? Bai isa yaga abun gyara ya gyara musu ba?" "A’a. Allah ya k'ara had'e kanku." Kawai ta fad'a kana ya fita zuwa aikanta tana murmushi. Bai jima ba ya dawo ya kawo mata abunda ta aikeshi. "Ya ka sayo mini albasa da daddawan da yawa?" "Saboda sayan gutsil-gutsil d'in bashi da riba. Tunda su suna dad'ewa a ajiye sai ki dinga sayan attarugun kad'ai." Albarka ta saka masa kana ya mata sallama ya tafi gurin abokinsa Nasir. "Ya kamata yau kazo mu je gidana. Ko har yanzu tsoro kake ji?" Dariya kawai Nasir yaya yace, "Yau kam nine da aiki babu dama in fita, amma ranar jumma'a da zan zo in ga Amarya." Suka kwashe da dariya suka tafa. Bai jima ba a gurin ya koma gida ana kiran sallan magrib, sai da yayi sallah a waje sannan ya shigo gidan ya bud'e k'ofar falon. K'amshin turaren wuta ne ya fara dukan hancinsa ya lumshe idanunsa kana ya bud'e ya k'arisa shiga ciki. A kitchen ya sameta tana tuk'a tuwo tayi wanka ta canja kayan jikinta ta saka wata farar doguwar riga mai laushi mai guntun hannu. "Ka dawo?" Ta fad'i hakan bayan ta amsa sallamarshi. "Eh." Ya isa gurinta ya rungumeta ta baya ya kwantar da kanshi a kafad'unta. "Haydar ka mini nauyi kuma tuk'a tuwo nake yi." "Kiyi a haka." Bata k'ara kulashi ba har ta gama tuk'awa duk inda tabi yana bayanta yana binta. "Wallahi ban san haka kake da son jiki ba." Ta isa bakin dinning table ta ajiye kulolin hannunta shima ya ajiye plates d'in da ta bashi. "Da baki aureni ba ko?" "Ban ce ba. Ka zauna kaci abinci." "Ke fa?" "Bana jin yunwa sai anjima." "Nima sai anjima. Amma wannan abun zuman nake so a k'ara mini." Ya d'aga kanshi yana lek'en fuskarta. Murmusawa tayi suka nufi falo ta zauna ya fara mata massage a kafad'unta. "Wallahi kamar kasan shi nake buk'ata. Yauwa ta nan." Ta lumshe idanunta yaci gaba da mata yana kallon fuskarta yanda ya zama so calm. "Nima a biyani." Ya fad'i hakan bayan ya gama mata. "Ban iya ba." "Ki koya a kaina." Dariya tayi ta koma saman kujeran tana jin kanta cikin nishad'i ta fara masa yana lumshe idanunsa. "Bamu yi maganan kayan aure ba har yanzu Laila." A bazata taji maganan domin ita koda wasa hakan bai zo ranta ba. Wanda Alhaji Abdul ma ya mata ta da duk kud'in da ya bata na aurensu ta mayar mishi da kayanshi. Ko da yace ya yafe itama tace bata buk'ata ya rik'e kayanshi. "Na yafe maka Haydar, dama kuma budurwa ake yiwa ba bazawara ba." "Kema budurwa ce a gurina." Dariya kawai tayi ta kad'a kai taci gaba mishi da matsan idanunshi a rufe. "I'm serious Laila." "About what?" "About maganan budurwan." "Sai ka jira kaji tukunna kafin ka yanke hukunci." Bud'e idanunsa yayi ya juyo da jikinshi kana ya jawota kan cinyarshi yace, "Yaushe?" Buge k'irjinshi tayi tana neman tashi ya rik'e kunkuminta da kyau ya had'e goshinsu guri guda. "Don Allah yaushe?" Shiru tayi idanunta a rufe amma a ranta mamakin yanda Haydar ya canjata take yi, tun tana jin kanta babbar mata har ta daina ta bashi girman yana yin yanda yaga dama da ita. "Sai na gama." "Wayyo Allah." Yayi ihu ya fara rawa daga zaune. "Wallahi baka da kunya ko kad'an Haydar." Ta tashi ta bashi guri yana mata signa yana kashe ido. Dariya tayi ta shige d'akinta ta barshi a gurin yana ta murna. Ranar friday su Ammi suka zo kamar yanda suka fad'a, Laila ta tar6esu hannu bibbiyu kana ta kawo musu abun sha da abinci. Shi kuma Haydar bayan ya gaishesu ya fita zuwa waje inda Nasir yake suka tsaya a nan suna hira. Sai da su Ammi suka tafi sannan Haydar ya shigo da Nasir bayan yasa Laila ta saka hijabi. Yanda Nasir ya gaishe da Laila yana sunkuyar da kai ya bawa Haydar dariya amma bai ce komai ba. Daga nan kan dinning suka nufa suna cin abinci ita dai Laila ta shige d'akinta ta barsu a nan. "Kai mutumina kana hutawa fa. Ga k'aton gida ga hutu sannan ga sam6aleliyar mata kyakkyawa." Tsuke fuska Haydar yayi kana yace, "Watch your mouth Nasir. Matata kake magana a kai, bana son haka." Dariya Nasir yayi nervously kana yaci gaba da cin abincinsa bayan ya canja zancen. Bayan Nasir ya gama cin abinci Haydar ya rakashi bakin titi ya hau achaba ya tafi. Yana dawowa cikin gida kafin ya shiga cikin falo wayarshi tayi ringing ya d'auka ganin sunan Mas'ud ne. Suka gaisa sama-sama, Haydar yaga kamar akwai matsala yace, "Lafiya kam?" "Abul ya gudu bayan ya kwashi kud'i a shago." "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ina zan sameka yanzu? Ina son mu je mu nemoshi kafin Laila taji hankalinta ya tashi." "Gani a mota gidan naku nake son zuwa yanzu. Bana son in k'ara 6oye mata wani abu game dashi saboda a baya da nayi bata ji dad'i ba. Sannan bazamu ta6a sanin ina ya shiga ba." "Gani a cikin gidan nima, sai ka iso." Bayan Mas'ud ya shigo ya samu Haydar har lokacin bai shiga ciki ba yana jiranshi. "Yanzu ya za'a yi? Zaka fad'a mata ne?" "Babu amfanin 6oye mata." Shiru Haydar yayi yana jin d'aci a zuciyarsa yana kuma tunanin wace hanya zasu bi Haydar ya shiryu. Yana son Laila kuma yana son 'yayanta tunda ba zai so uwa ya k'i 'yayanta ba. Duk da cewa sun girma sun mallaki hankalin kansu bai k'i ace akwai ranar da zasu bud'i ido su d'aukeshi a matsayin uba a garesu ba duk da k'ank'antar shekarunsa. Tare suka shiga cikin gidan suka samu Laila na rubutu a cikin wani Memo da take yawan rubutu a ciki. Ganin Mas'ud yasa ta fad'ad'a fara'arta suka gaisa. Bata tambayeshi ya Abul ba kamar yanda kullum take yi sai ma ta d'auko wani hira daban tana mishi. Haydar bai ce komai ba yayi shiru yana kallonta amma ya lura tana cikin damuwa. "Kalti magana nazo muyi." "A kan guduwan Abul?" Ta tambayeshi cikin basarwa. "Waya fad'a miki? Haydar kai ka fad'a mata?" "Ban shiga gida ba tunda muka yi magana." "Abul ya kirani a waya da wata sabuwar number yake fad'a mini ya bar Kano, sannan duk ranar da na kashe aurena zai dawo gida." Shiru kawai suka yi suna kallonta, dukkansu

Chapter 7 of 32