Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi auren da har zamu fara fad’ace-fad’ace irin haka Haydar? Kuma idan ka fahimceni ba wai bana son haihuwa da kai bane Haydar, tsoron haihuwar nake yi da kuma abunda zai je ya dawo gaba a ganni tsofai-tsofai da ciki ina yawo. Wallahi daka aureni a younge age d’ina dana haifa maka yara koda goma ne bazan damu ba saboda wannan ne daidai lokacin haihuwar mace without risk. Don girman Allah wannan karon ka fahimceni ka kuma saurareni muyi magana d’aya a ajiyeta.” Ta k’arisa maganar hawaye na taruwa a idanunta tana d’aura hannunta kan k’afarshi. “Menene result d’in?” Shine abunda ya tambaya ba tare daya juyo ba. “Ka tashi muyi magana ina so ne muyi magana ta fahimtar juna.” Ta fad’i hakan cikin lallashi. Bai musa ba ya tashi ya zauna yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa amma da zata d’aura hannayenta kan k’irjinsa zata tsorita dalilin bugawar da zuciyarsa take yi. He is restless ta ciki domin ya k’agu yasan result d’in. “Haydar result d’in ya nuna ina d’auke da juna biyu.” Ta fad’i hakan tana kallon cikin idanunshi wanda lokaci d’aya suka zama glassy alamar hawaye na taruwa a cikinsu. Haydar kasa motsi yayi domin ya rasa me zai ji a wannan lokacin, farin ciki ko bak’in ciki dalili kuwa first; yasan hakan na nufin yana haihuwa kenan, second; ba lalle bane Laila ta bar cikin tunda ta nuna ta tsani haihuwa a yanzu. Wannan mixed feelings d’inne yasa hawaye ya zuba a k’uncinsa amma nan take ya goge fuskarsa ta zama normal tamkar bashi bane yayi losing guard ba. “Ya zaki yi da cikin?” Ya yiwa Laila tambayar da take tsoron ji domin amsarta bata da dad’in sauraro ga Haydar. In-Ina ta fara ta rasa me zata fad’a guda d’aya tak’amaimai, “Shine nace zamu yi magana tunda kwanaki kace ka hak’ura da maganar haihuwar, kenan yanzu ma maganar bata canja ba. Haydar ina fatan zaka mini kyakkyawan fahimta?” Gyad’a kai yayi ya hard’e hannayenshi a k’irjinshi yace, “Ina jinki.” Shiru ta sake yi wannan karon itace ta fara hawaye kana ta matso daf dashi tace, “Zan zubar da cikin.” Mummunan kallon da bata ta6a ganin Haydar yayi mata ba wannan karon shi ta gani a kwayar idanunsa, numfashinsa ne yake fita da sauri k’irjinshi na hawa da sauk’a dalilin bak’in cikin kalaman Laila da kuma tausayin kanshi da yake ji. Nuna Laila yayi da yatsa ya fara magana cikin murya mai amo, “Karki kuskura ki kashe mini d’ana Laila, domin daki kasheshi gwanda ni kin kasheni.” Kamar walkiya kuma muryarsa ta koma ta rarrashi yaci gaba yana had’e hannayensa guri guda alamar rok’o, “Don girman Allah laifin mena miki da kike gudun haihuwa dani Laila? Me kuka zan miki kiyi hak’uri ki bar mini d’ana ya fito duniya? Wallahi zan miki duk abunda kike so zan kuma nuna miki son da ba’a ta6a yiwa wani kamarsa ba in har kika bar cikin nan Laila. Ki tausaya mini ki cika mini wannan babban burin nawa.” Zuciyarta ce ta k’arye ganin Haydar na zubar kwalla har yana k’ok’arin sauk’owa daga kan kujerar zai rok’eta, itama hawayen ta fara tana girgiza mishi kai amma bai daina magana ba, “Na rantse zan kareki daga duk wanda zai miki ba’a akan cikin nan Laila, Karki bari maganar mutane ya hanaki rainon albarkar aurenmu domin d’an halal ne ba shege ba. Ki tausaya mini don Allah Laila.” Ya k’arisa maganan yana rik’o hannayenta duka biyu fuskarsa abar tausayi. “Haydar shine maganan da nake son muyi tun d’azu saboda kai da kanka kace ka hak’ura....” bata k’arisa ba ya katseta. “Saboda a wancan lokacin baki da ciki ne Laila, amma yanzu ga cikin a jikinki and it will kill me idan kika ce zaki zubar dashi.” “I’m sorry Haydar, amma bazan zauna da cikin nan ba. We have to face reality saboda tun farko na nuna maka bana son haihuwa kai kuma ka nuna mini kana so. Wannan shine abunda nake jin haushi akai saboda munyi aure cikin rushing ba tare da munyi wannan maganar mai muhimmancin ba. It has to be done and I’m sorry.” A hankali ya d’age hannunsa daga na Laila fuskarsa with so much hurt yayin da zuciyarsa yake jin kamar ana hura mata wuta. Nan take yaji gumi na karyo mishi yayi saurin tashi tsaye yayi hanyar d’akinsa na daa. Har yaje bakin k’ofa ya tsaya ya juyo ya dubi Laila wacce itama a cikin tashin hankalin take, yace, “Idan har zaki iya kashe abunda yake cikinki duk soyayyar da kike nuna mini k’aryace. Sannan wallahi kika kuskura kika cire cikin nan daga ni har ke baza mu ji dad’in abunda zai biyo baya ba.” “Aure zaka ce zaka k’ara ko?” Ta tambayeshi kafin ya bud’e falon. “Wannan mai sauk’in kika fad’a.” Ya bata amsa yana shigewa ya rufe k’ofar ya barta zuciyarta na dukan uku-uku tana tunanin me zai iya aikatawa. Me zai mata daya wuce yace zai k’ara aure? Kenan abunda zai mata zai fi haka? Rabuwa da ita zai yi kenan? Shin Haydar zai iya rabuwa da ita? Wannan karon tasan ta wuce gona da iri, sannan tana tsoron abunda zai faru dasu. Haydar yana shiga falon ya zauna a kujera ya dafe kanshi da hannunsa biyu zuciyarsa na tafarfasa, Laila tana son 6aro musu aiki, idan kuma ta aikata abunda tace zata yi dukansu zasu yi dana sani. Haka Haydar yayi ta kwancewa yana sak’awa domin yayi tunanin ya kai k’ararta gun mahaifiyarta tunda ya lura tana tsoronta. Da asuba Laila na zaune akan sallaya ta gama sallah Haydar ya shigo d’aki yana d’aukan kayanshi. “Ina kwana?” Ta gaisheshi kamar yanda take yi kullum. “Lafiya.” Ya bata amsa a takaice kana ya shiga band’aki ya d’auki brush d’insa ya fita. K’arfe bakwai da rabi ya shigo falon cikin shirin tafiya office ya samu Laila na jera abinci a kan dinning table yace, “Kin hak’ura ko har yanzu kina kan bakanki na kashe mini d’a?” “Ka daina kiran kisa kamar wuk’a zan d’auka in kashe mutum, sannan cikin wata d’aya ne wanda ko fara mishi halitta ba’a yi ba balle a busa mishi rai.” Ta fad’i hakan cikin 6acin rai ganin yana k’ok’arin kiranta murderer. “Duk d’aya ne. Ki bani amsa.” “Ban fasa ba.” “Then ki saurari hukuncin da zan yanke.” Ya fice daga falon ba tare daya k’ara cewa komai ba. Hankalin Laila ne ya tashi tayi saurin samun guri ta zauna tana dafe k’irjinta, me Haydar zai iya aikatawa? Can kuma wata zuciyar ta fad’a mata cewa kuri kawai yake yi babu abunda zai yi saboda yana sonta ita kanta ta sani. Bata jima ba itama ta fita daga gidan zuwa asibiti tana fad’in a ranta duk abunda zai faru ya faru. Haydar yana fita ya wuce kai tsaye gidan Ammi, bayan ta bud’e mishi k’ofa ya shiga har d’akinta ya zauna akan kujera ya dafe kanshi, a haka tazo ta sameshi tana tambayarshi lafiya cikin tashin hankali. “Ki zauna tukun Ammi.” Yace da ita ba tare daya d’ago kanshi ba. Babu musu ta zauna a gefenshi amma bata fasa tambayarshi ba, “Ali me yake faruwa ne?” “Ammi jiya na miki k’arya don a tunanina zan shawo kan matsalar da nake ciki ba tare da kowa ya sani ba. Amma wannan karon abun yafi k’arfina domin Laila ce ke k’ok’arin zubar mini da cikina Ammi. Na rarrasheta har barazana na mata amma bata daddara ba zata kasheshi. Ammi kije gidan mahaifiyarta ki sanar mata halin da ake ciki ta hanata kafin lokaci ya k’ure tunda ni ban isa in kafa mata doka ba.” “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Lailan ce ta fad’a maka da bakinta?” “Ehh.” Shiru Ammi tayi tana tunani yanda za’a 6ullowa wannan al’amarin, ba tare da an kai maganar gidansu ba. “Nasan Laila zata ji maganata bazata tsalleka ba, mik’o mini wayata a k’ark’ashin pillow in kirata. D’auko mata wayar yayi yana fatan Laila taji kunyar Ammi ta bar mishi d’anshi da rai. Ammi ta kira layin Laila amma aka ce mata wayar a kashe. Haydar yana jin haka hankalinshi ya k’ara tashi domin yasan ta kashe wayar ne don kar a nemeta. “Ammi kin gani ko? Ta kashe wayarta ta tafi.” Yanda yayi maganar sosai ya bawa Ammi tausayi domin tasan yana mugun son yara, yasha fad’a mata cewa zai cika mata gida da jikoki sai ta ture saboda baya son ya k’arisa rayuwarsa bai ganshi cikin zuriyarsa ba. “Yanzu ko naje gidan nasu mahaifiyarta bazata sameta a waya ba Haydar tunda ta kashe, ka koma gida ka duba in bata tafi ba ka d’aukota ka kaita gidan nasu sai kuyi maganan a can.” “Ammi ni nasan Laila ta bar gidan amma bazan miki musu ba zan je na duba, amma kema kije gidan nasu ko akwai abunda za’a yi.” Yayi maganar kamar zai yi kuka. Ammi shiru tayi tana kallon yanda d’anta ya birkice lokaci d’aya, tausayinshi ne taji sosai har ta fara dana sanin rabashi da abunda yake so a yanzu, sai dai tayi hakan ne don shi ya rayu ba tare daya gane cewa itama tayi sacrificing wani sashe ne na rayuwarta ba. A k’ofar gidan Ya Madu Haydar ya sauk’e Ammi kana ya shigar da ita har sashen Ummii ya barta a tsakar gidan tana sallama. Daga ciki aka amsa mata tare da mata iso ta kutsa kai cikin falon da d’an murmushin ta, sai dai Matar data gani zaune a kujera yasa ta d’auke fara’arta lokaci guda cikin kid’imewa. “Suwaiba?” Shine abunda Ummii ta fad’a tana tashi tsaye Ya Madu dake zaune a gefenta yayi saurin rik’ota don kar ta fad’i dalilin ba lafiya bane ya isheta. “Ummii lafiya? Kin santa ne?” Madu ya mata tambayar yana kallon Ammi da har lokacin ta kasa furta ko kalma d’aya. “Suwaiba ce, Suwaiba nake gani Madu. ‘Yata ce, baka ganeta ba?” Ta fad’i hakan tana takawa kusa da ita tamkar bata gaskata idanunta ba. Madu da dama bincikensa akan Haydar yasa ya gane Ammi yace, “Ummii wannan ai mahaifiyar mijin Laila ce ba wacce kike tunani ne ba.” “Taimaka mini in zauna Madu ina jin hajijiya.” Fad’in Ummii ba tare data k’arisa gurin Ammi ba dalilin sarawan da kanta ya mata nan take. Haydar gida ya koma amma bai samu Laila ba kamar yanda yake zato duk da cewa wani gefe na zuciyarsa na fad’a mishi tana nan. “Shikenan ta tafi.” Ya furta yana lalumo wayarshi ya kira Mas’ud wanda babu 6ata lokaci ya d’auka amma muryanshi a ciki da alamar bacci yake yi yace, “Kai baka gaji bane da ba zaka kwanta kayi bacci ba?” “Mas’ud wani asibiti Laila take zuwa in bata da lafiya?” “Bata da lafiya ne? Meya sameta?” Shine abunda ya tambaya yana sauk’owa daga gadonshi har yana k’ok’arin fad’uwa. “Lafiyanta kalau amma ta tafi zubar da cikina ne.” “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.” “Ka fad’a mini wani asibiti take zuwa?” Ya k’ara maimaita tambayan cikin gaggawa domin baya son 6ata lokaci. “Asibitin da aka kwatar da Abul, ka jirani.....” bai k’arisa maganan ba Haydar ya kashe wayarshi yayi saurin fita daga gidan ya shiga motarshi kamar wanda bashi da hankali a jikinshi. Yanda yake sharara gudu a kan titi saura kad’an ya had’a hatsari amma a haka ya isa asibitin cikin mintuna bakwai, bai yi parking mai kyau ba ya fito yayi cikin asibitin zuwa office d’in Doctor don watakila a nan zai samu Laila. Bai kwankwasa ba ya bud’e k’ofar ya shiga ya tsaya a gurin yana kallon abunda yake faruwa. Laila ce kwance akan gado yayin da Doctor da Nurse d’aya mace suke kanta suna mata wani abu tana hawaye. “Shikenan kin zubar kin huta Laila.” Shine abunda ya fad’a suka juyo suna kallonshi idanunshi sun kad’a sun yi ja. Cikin sauri ya fita daga office d’in ya koma bakin motarsa yana jin duniyar gaba d’aya ma ta fita a kanshi. Hawaye masu zafi ne suka sauk’a kan k’uncinsa yayi saurin gogewa amma bai hana wasu zubowa ba. Minti d’aya da haka Mas’ud yayi parking a gefenshi ya fito daga motarshi yana cewa, “Ina Lailan?” “Ban zo da wuri ba, sun cire mata cikin.” Amsar da Haydar ya bashi kenan yana share hawayen fuskarsa. “Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un.” Mas’ud kasa cewa komai yayi saboda yasan wannan karon Yayarshi ta kai mak’ura, kuma ta cancanci duk hukuncin da za’a mata. “Kayi hak’uri Haydar.” “Idan kaine hakan ya faru da kai ya zaka yi? Shiru Mas’ud yayi domin yasan zai iya dukan mace idan ta mishi haka, sai dai bazai furtawa Haydar hakan ba saboda yayarshi ce ta aikata. “Kayi hak’uri.” Kawai ya k’ara nanata mishi yana dafa kafad’arshi ba don hak’urin da yake bashi zai sa yaji sassauci a zuciyarsa ba. Wayar Mas’ud ce ta fara k’ara ya duba yaga sunan yayansu Madu, da kamar bazai d’auka ba amma yayi tunanin ko jikin Ummii ne ya tashi. Yana d’aukan yaji muryar Madu na cewa, “Kaje gidan Laila ku zo gida yanzu.” “Ummii ce bata da lafiya?” Mas’ud yayi tambayar cikin tashin hankali domin ko Ummii bata da lafiya ba’a ce mishi yazo gida sai dai a fad’a mishi nan take. Ko dai wani abun ne ya sameta? “Tana lafiya, ita ke nemanku.” Bai jira me Mas’ud zai ce ba ya kashe wayarsa. Mas’ud da hankalinshi bai kwanta da wannan kiran ba yace, “Haydar zamu je gida Ummii tana nemanmu ni da Laila, Inaga gidan ba lafiya ne.” Haydar na jin hakan ya tuno ya bar Amminshi a can yace, “To.” Kana ya kunna motarshi ya fita daga asibitin domin d’auko Ammi saboda babu amfanin zamanta a can. Mas’ud kuma shiga cikin asibitin yayi ya duba in zubar da cikin da Laila tayi bai fara galabaitar da ita ba su tafi gida. Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Wannan littafi na kud'i ne a N100 kacal, zaku turo kud'inku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana ko kuma katin Airtel, sannan ku mini magana tare da turo evidence ta wannan number 09023713064. (43) "Suwaiba kece?" Fad'in Ummii bayan ta zauna a kan kujera da taimakon Madu. "Nice Kalti." Kuka Ummii ta fara yi yayin da Ammi ta tako ta zauna a gefenta itama tana kukan. "Ina kika shiga ko sau d'aya baki waiwayi gida ba?" Shiru Ammi tayi dalilin kukan daya ci k'arfinta, Madu dake zaune a gefe sai yanzu ya gane wacece ita. Zuciyarshi ta buga da k'arfin gaske shima ya zauna a gefensu yana kallonsu yana mamakin wannan al'amari. Can kuma ya d'auki waya ya kira Laila amma wayarta a kashe take, hakan yasa dole ya kira Mas'ud yace mishi ya d'auko Laila ta zo taga abunda taurin kai ya haifar mata. "Haydar d'anki ne na cikinki Suwaiba?" Ummii ce ta yi wannan tambayar tana share hawayen fuskarta. "D'ana ne na cikina Kalti. Wallahi d'ana ne." "Wannan aure an yishi cikin rashin sani cikin duhu. Kash!" Fad'in Ummii tana kama kanta. Mas'ud yana shiga asibitin ya hango Laila na tahowa yayi saurin yin kanta ranshi a 6ace ya fara magana, "Wallahi kin bani mamaki, duk k'ok'arin da mutumin nan yake yi a kanki baki gani ba sai da kika saka mishi da mummunan abu, you are my sister amma wannan karon I hate what you did. Kuma Allah ba zai barki ba saboda kin zalunceshi Kalti." Laila kallonshi tayi sau d'aya kana taci gaba da tafiyarta ganin hankalin mutane na komawa kansu, Mas'ud kuma fad'a ya dinga mata yana bin bayanta har suka isa bakin motocinsu. Ganin ko sauraron shi bata yi yasa a zuciye ya fad'a mata sak'on Madu, "Ummii tana nemanki yanzu-yanzu a gida." Bai jira me zata ce ba ya shige motarshi ya barta a gurin yana jin zafi a zuciyarshi don ya lura babu ko d'igon nadama a fuskarta. Bai san yaushe yayarsa ta zama muguwa haka ba kuma wannan karon zai nuna mata laifinta ko da hakan zai jawo mummunan fad'a tsakaninsu. Haydar ne ya fara isa gidan Madu ya kira Ammi a waya, jin muryarta yayi tana kuka tana cewa, "Ka shigo cikin gidan." Nan take zuciyarshi ta bashi cewa had'uwa tayi da Madu ya mata rashin mutunci, ai nan take fuskarsa ta k'ara had'ewa da tsananin fushi yana ayyana me zai yiwa Madu. Da sallama ya shiga falon ya samu Amminshi zaune a k'asa kusa da Ummii tana share hawayen fuskarta, nan ya tabbatar da abunda yake zargi domin shima Madun gashi can a gefe yana kallonsu fuskarsa babu yabo babu fallasa. "Me ka yiwa mahaifiyata?" Shine tambayar da Haydar ya fara yi yana shigowa yayi kan Madu. "Me zai sa in yiwa mahaifiyarka wani abu?" Madu shima ya mayar mishi da tambaya yana mamakin tsaurin idon yaron. "Ali zo nan." Fad'in Ammi tana yafutoshi. Wani mugun kallo ya aikawa Madu irin 'bamu gama ba', sannan ya matsa gurin Ammi ya durk'usa yana tambayarta me aka mata, ya ma manta a gaban surukarsa yake domin ya k'i jinin abunda zai ta6ata don a yau ya gane cewa babu mai sonshi sai ita kad'ai. Ummii kuma kallon Haydar kawai take yi tunda ya shigo, sai yanzu ta gane dalilin da yasa tun farkon ganinta dashi bata kushesa ba, illah ma d'aura Laila da tayi akan mishi biyayya, ashe jikanta ne jininta. "Babu abunda aka mini Haydar, ga dangina da kake son sanin ina suke." "Ban gane ba Ammi." Ya fad'i hakan yana zama mai kyau cikin rashin fahimta. "Kalti Falmata k'anwar Babana ne, a gabanta na tashi tun kafin tayi aure, kamar mahaifiyata na d'auketa saboda irin so da kuma kulawan dana samu a gurinta." "Ammi me kike nufi? Kina nufin sune dangin da kike gudu kuka kika k'i fad'a mini?" Gyad'a mishi kai tayi wanda hakan yasa idanunshi tara hawaye ya d'aga ido ya dubi Ummii yace, "Ke dangin Ammi ce?" "Eh, ni Kakar ce Haydar." Ta bashi amsa tana shafa kanshi cike da tausayinshi don tasan ba zai ji dad'in labarin mahaifiyarsa ba ko kad'an. "Ina mahaifina yake?" Ya k'ara wata tambayar yana kallon Ummii don ya lura ita baza ta 6oye mishi ba. Ummii ta kalli Ammi wacce nan take kanta yayi k'asa tace, "Ban san waye mahaifinka ba Haydar, amma mune dangin mahaifiyarka gaba da baya." "Ammi ina mahaifina?" Ya juyar da kanshi gareta yana tambayarta abunda ya rantse bazai sake tambaya ba. "Mu bar maganar ba yanzu ba." Tace dashi ta k'i had'a ido dashi. A nan ne Mas'ud ya shigo tare da Laila suka tsaya suna kallon ikon Allah ganin Ammi wacce ke share hawaye ga Haydar zaune kusa da Ummii. Guri suka samu suka zauna suka fara gaishe da 'yan falon ba tare da sun tambayi me yake faruwa ba saboda sun d'auka akan zubar da cikin da Laila tayi ne. Madu ne ya fara magana yace, "Laila kin ta6a jin labarin 'yar Kaala Abdi wacce ta bar gida?" "Na sani, meyasa kake tambayana?" Ta amsa cikin rashin fahimtar inda maganar tashi zata dosa. "To gata nan itace Uwar mijinki, d'anta kika aura." Ya fad'i hakan kamar mai karanta jarida babu alamar emotion a muryarsa. Nan Mas'ud da Laila suka mayar da dubansu ga Ammi tare da Haydar, sai yanzu suka ga dalilinsu na zama kusa da Ummii. "Ummii da gaske ne wai itace?" Mas'ud ne ya samu k'arfin halin magana Laila kam kasa cewa komai tayi sai bakinta da yake motsi alamar addu'a take yi. "Haka ne. Jininku ce 'yar uwarku, Haydar kuma d'a yake a gurinku." Madu murmusawa yayi yana kallon yanda Laila ta daburce tana had'a d'aya da biyu suna bata amsar da baza taso furtawa ba, wato mijinta shege ne. "This escalates quickly." Fad'in Mas'ud yana kallon 'yan falon kamar bai gaskata abunda yake faruwa ba, wannan wani irin abu ne kamar a film? "Ammi tunda ba zaki sanar dani waye mahaifina ba ki fad'a mini dalilin da yasa kika guji gida da kuma danginki. Me suka miki? Sannan meyasa kika kasa komawa gida duk tsawon wannan lokacin alhali kin san inda suke? Meyasa kika rabani dasu?" "Saboda ko na koma ba zasu k'ar6eni ba." Ta bashi amsa cike da nadama. "What really happened? Ammi don girman Allah wannan karon karki 6oye mini komai tunda da alama kowa yasan labarinki nine ban sani ba." Ya fad'i hakan with desperation in his voice. "Baza ka so jin labarina ba Haydar, k'azantar dake cikinta da yawa yake." Ta fad'i hakan itama cikin rok'onsa. "Suwaiba ki sanar dashi saboda babu amfanin 6oyewan." Fad'in Ummii tana dafa kafad'unta. Ammi ta dubi Haydar taga hankalinshi gabad'aya na kanta cikin son jin labarinta. Share hawayen fuskarta tayi ta dubi Ummii tayi magana ta yarensu wanda Haydar bai ji ba, hakan kuma k'ara masa takaici yayi amma bai ce komai ba. Sai ji yayi Ummii ta fara magana, "Suwaiba itace 'ya ta farko a gurin Kaala Abdi wanda mahaifiyarta ta rasu gurin haihuwarta. Ko da Kaala Abdi ya k'ara aure sai ya kasance bai k'ara haifan d'iya mace ba sai maza zallah. An haifeta lokacin da nake da shekaru tara, da yake a cikin gidanmu yayana yake, sai ya kasance kullum tana hannuna ina kula da ita tunda rainonta ya dawo gurin mahaifiyarmu. Zan yi mata wanka, in saka mata kwalli sannan in goyeta muyi ta zaga gidanmu ana cewa Suwaiba d'iyata ce. Bani kad'ai ba, hatta Kaala Abdi ya d'auki son duniya ya kwallafa mata ba tare daya san cewa ita ce kad'ai 'ya mace da zai haifa ba. Hakan yasa Suwaiba ta taso cikin so da kulawa matuk'a wanda ya kai ga kowa yayi dana sanin aikata hakan. Lokacin data kai shekara takwas a lokacin halayyanta ya fara canjawa dalilin yaba kyawunta da ake yi ga mutanen gidanmu har ma dana waje. Sannan ko a cikin yara tayi fad'a da wani nice mai bata gaskiya koda kuwa itace bata da gaskiya saboda k'aunar da nake mata. Da ta fara girma sai tayi wanka tayi kwalliya ta samu guri ta zauna kowa yazo sai ya yabata, hakan yasa da naga kin fara irin haka naji tsoron ko kema zaki zama kamarta ce Laila, nayi tsammanin bada hannu da nayi wajen gur6acewar tarbiyyar Suwaiba shi zai dawo kan zuriyata. Hakan yasa na zareki a jikina, a zatona duk ranar da kika 6ace bazan shiga halin da Kaala Abdi ya shiga ba bayan 6acewar 'yarsa." Ummii ta k'arisa maganan tana kallon Laila wacce idanunta ya tara hawaye dalilin an mata hukunci akan abunda bata ma san tayi ba. Ummii taci gaba, "Tana da shekara goma ta fara tara samari a k'ofar gida wanda hakan yasa kowa ya farga aka hanata tsayuwa dasu dalilin k'ank'antan shekaruta. Sai dai hakan bai mata dad'i ba dalilin an hanata abunda take so wanda a daa duk abunda take so ake yi mata. Takurar da yayi yawa sai ta fara fita ba tare da an sani ba, hakan kuma yaci gaba da faruwa har ta kai shekara sha uku sannan magana ta fito fili kan tana zuwa d'akin samari suna amfani da ita suna bata kud'i. A yinin bikina aka kamata tare da wani saurayi wanda uban yaron ne ya kawosu dukansu har gaban Kaala Abdi yace a musu hukunci yana kuka. A ranar an ga tashin hankali domin Kaala Abdi duka ya mata sai data suma ya farfasa mata jiki. Shima saurayin aka mishi bulala d'ari kamar yanda shari'ar musulunci ta tanadar. Bikin da aka k'arisashi babu armashi kenan aka kaini gidana nan cikin unguwarmu, sai dai gaba d'aya hankalina yana kan Suwaiba saboda a lokacin da ake mata bulala sai da aka rik'eni. Kwana uku da haka Kaala Abdi ya aika gidan su yaron kan cewa ya basu aurenta idan ta gama istibra'i za'a d'aura musu aure. Duk yanda na kai ga son zuwa gida in dubo

Chapter 19 of 32