ya kalleta, kashe Laptop d’in yayi ya yafutota da hannu ta iso wajenshi.
“Yau ban fad’a miki cewa kinyi kyau ba ko? Kin fi koyaushe kyau amma a cire kallabin nan.” Yasa hannu ya cireshi, gashinta data 6oye ya zubo ta goshinta da kuma bayanta “Kinfi kyau a haka.”
“Yawanci wannan ne kitsona a wancan lokacin, last kitson da nayi irinshi nayi shiyasa daka ce inyi banyi musu ba. Ina son wannan memory ya gushe a zuciyata ya zamana duk lokacin da zanyi kitso bazan tuno wancan ranar ba.”
“Insha Allah. Shi kuma Allah yaji kanshi ya mishi rahama.”
“Ameen Ya Rabbi. Kana k’ara burgeni, baka da halin wasu maza na kishin mazajen matayensu da suka mutu.”
“In kinga namiji na kishi da marigayin mijin matarsa ki tabbata tana had’asu wajen halayya ko kuma na rayuwar yau da kullum. Babu namijin da zai so yaji matarsa tana kusheshi sannan tana yabon wani namijin ko da kuwa matacce ne. Sai dai bana son a yawaita yin maganan saboda gujewa fitina.”
Gyad’a kai kawai tayi kana ta kwantar da kanta kan k’irjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa. Wayarsa ce ta fara ringing ya d’auka ganin sunan Amminshi ne.
Sallama ya mata kana yayi shiru yana sauraranta amma yanayin fuskarsa kad’ai ya isa a gane ranshi ya 6aci.
“Gaskiya hakan bai mini dad’i ba Ammi. Bai kamata ki gayyaci mutane su zauna a gidanki ba tare da munyi shawara ba. Baki san daga ina suke ba, baki san halinsu da manufarsu a kanki ba. Ammi yanzu ba lokacin da zaka bari tausayi yasa kayi gaggawan yanke hukunci bane. Su koma inda suka fito, idan na samu fitowa jibi zan zo in gansu sai a san me za’a musu.”
Da haka ya k’ara shiru yana sauraronta, can kuma ya kama kanshi da yatsunshi biyu yace,
“Allah ya taimaka. Sai anjima.” Ya kashe wayar.
“Yaya dai?” Laila ta tambayeshi tana tashi zaune.
“Matar can da kwanaki suka je gidan Ammi neman abinci shine yau suka sake dawowa wai an koresu a gidan hayan da suke ciki basu da gurin zuwa. Damuwata a nan shine; Ammi bata san mutanen nan ba, bata san nufinsu a kanta ba. Sannan meyasa suka tsallake duk gidajen dake unguwar suka sauka a gidanta? Ba wani gida mai kyau bane balle ace sun ga alamun tana da wadata ba. Bana jin dad’in saurin yanke hukuncin da take yi.”
Shiru Laila tayi har na tsawon minti biyu, sai data tabbatar ya fara sauk’owa sannan tace,
“Mu mata haka muke da tausayi da kuma rauni. Kayi addu’a Insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi. Idan Allah ya kaimu ka samu fita sai ka biya ka dubasu, in ka yarda dasu sai su zauna da ita, in baka yarda dasu ba sai a nema musu wani gidan hayan su koma can.”
“Hakan zai fi, hankalina zai fi kwanciya.”
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
(33)
Washegari Haydar ya samu sauk’i sannan ya fita zuwa office wanda zai dinga zuwa sau uku a sati. Sabon ID card d’inshi wanda aka mishi k’arin girma shi yake nunawa ana bud’e masa hanya.
K’arfe biyar na yamma suka tashi dalilin aikin daya kwacu6e musu na kwanakin baya. Gidan Ammi ya tasamma wanda da kyar ya samu Sojoji suka barshi ya wuce, yana shiga gidan ya sameta a rumfarta tana duba talgen tuwo.
“Ali ya akayi ka samu ka fito?” Shine abunda ta fara tambayarshi tana rufe tukunyar.
Murmushi kawai yayi domin ganinta kad’ai da yayi ya sanyashi cikin farin ciki, yayi kewar mahaifiyarshi bana wasa ba.
“Na jima ban ganki ba Ammi.” Ya iso cikin rumfar yana jawo gujerar tsugunno ya zauna kusa da ita.
“Sakali kawai.” Ta fad’a tana dariya amma ita kanta taji dad’in ganin tilon d’anta kuma farincikinta.
Kafin su gaisa wata mata ta fito daga cikin d’akin Haydar na daa yaranta maza guda biyu suna biye da ita a baya. Sannu da zuwa ta yiwa Haydar ya amsa yana dubanta da kyau, a tabarma ta zauna sannan ta d’aga masa gaisuwa ya amsa a karo na biyu.
“Itace matar da nake baka labari ai, wallahi mijinta ne ya gudu ya barta da ‘yaya biyar take kula dasu ita kad’ai. Gashi bata da dangin uwa ko na uba, mijin nata dai shine abun dogaronta kuma ya gudu ba’a san inda ya shiga ba.”
“Allah ya kyauta. Malama me sunanki kuma daga ina kike?” Haydar ya tambayeta bayan ya gama sauraron labarin Ammi.
“Zaliha ake kirana, na fito ne daga Tal’udu a can nike aure.”
“Kina nufin idan naje Tal’udu inda kika zauna na tambayi mutanen gurin zasu iya ganeki?”
“Ehh zasu iya, amma sai dai ba can ne kad’ai muka ta6a zama ba, mun zauna a unguwanni da dama muna bin gidajen haya.”
“Ammi tace baki da ‘yan uwa, shin haka kika tashi kika ganki ko dai? Sannan ina dangin mijinki?”
“Kai Ali bana son yawan tambaye-tambaye, ta fad’a mini komai a kanta, wanda hakan yasa naji zan iya zama da ita in taimaketa kafin mijinta ya waiwayeta ita da ‘yayanta.” Ammi ta katse musu filin tambayoyin.
“Ina son sanin information ne a kanta ba wani abu ba Ammi. Don Allah ki barni nima inyi part d’ina tunda kinyi naki.”
“Saboda baka yarda da hukuncin dana yanke ba ko?Nayi rayuwa ni d’aya tun kafin kazo duniya kar ka girma kayi wayon da kake ganin wani abunda nayi bai dace ba.”
“Ammi abun bai kai haka ba, Allah ya baki hak’uri ni zan wuce gida.”
“Maman Ali da kin barshi munyi magana, ai a zamanin nan yanda ba’a yarda da mutane yanda da gaskiya da yake son sanin asalina.”
Haushin maganar matar yaji sosai, don meyasa zata tsoma musu baki a maganarsu? Tashi yayi tsaye ya shige d’akin Ammi can kuma ya fito yace,
“Na ajiye miki abu a k’ark’ashin pillow, idan kina da buk’atar wani abun ki mini waya duk ranar da zan sake fitowa sai in kawo miki.”
“Sannu to, Allah ya tsare. Ka gaishe da Hajiya Laila.”
Sallama ya mata ya fita yana jin ba dad’i a ransa, haka kawai baya son zaman matar a gidan Ammi. Gashi Ammi ta hanashi bincikenta ya gane gaskiyar labarinta, zai yi hak’uri yanzu amma idan ya sake juyowa zai san yanda zaiyi ta fad’a mishi ba tare da Ammi ta katsesu ba.
Daff da magriba ya koma gida domin tsayar dashi da akayi ana binciken dalilin fitowarsa.
Yana shiga falon gidan ya fara jin k’amshin turaren wuta wanda yawanci Laila bata rabo da sakawa, sai dai na yau ya masa dad’in k’amshi bana wasa ba.
A kan kujera ya ganta a hakimce tayi kwalliya sai walwali take yi dalilin stoneworks d’in dake gaban rigarta.
“You know what? I miss this.” Shine abunda ya fara fad’i bayan ta taso ta nufoshi.
Atampa green ce a jikinta d’inkin Bubu wanda yawanci shi take yiwa suturunta, kwalliyar da ba’a raba fuskarta dashi yau ma tayi sai kuma kallabinta da ta yiwa d’aurin zamani wanda Haydar bai ta6a ganin tayi irinshi ba sai yau.
“Sannu da dawowa.” Shine abunda ta fad’a tana aika masa da murmushi ganin irin kallon da yake mata.
“D’azu kamar na gaji amma yanzu bana jin gajiyar Laila.” Ya ajiye jakar Laptop d’inshi a k’asa ya kamo k’ugunta ya had’a jikinta da nashi.
“I missed you.” Ya rad’a mata a kunnenta yana kwantar da kanshi kan kafad’arta.
Bata ce komai ba ta sak’ala hannayenta kan wuyanshi ya samu damar hugging d’inta tsam a jikinshi. Sai a lokacin tace,
“Same here, gidan babu dad’i babu hayaniyarka.”
Muntsinin fatar bayanta yayi tayi ‘yar k’ara tana matsawa gefe tana harararshi cikin wasa.
“Zan rama.” Tana fad’in hakan ta sunkuya zata d’auki jakar laptop d’in ya dakatar da ita,
“Ki tsaya a haka.”
Laila da bata gane me yake nufi ba da d’ago ido ta dubeshi, sai a lokacin ta gane inda hankalinsa yake.
“Baka da kunya.” Shine abunda ta fad’a tana murmushi ta d’auki Laptop d’in tayi hanyar d’aki shima ya bita a baya yana tsokanarta.
Bayan yayi wanka sunyi sallah ya fara bata labarin abunda ya faru dashi a office a ranar. Nitsuwa tayi tana sauraronshi domin ta lura kullum yana k’ok’arin fad’a mata abunda ya faru dashi a ranar koda kad’an ne. A yayin da wasu maza ke 6oyewa matansu harkokinsu shi kuma fad’a mata yake yi ba tare data tambayeshi ba.
“Bayan mun gama meeting d’in muka tashi na wuce gidan Ammi, daga nan kuma na dawo gida.”
“Ya ka barota? Tana lafiya?”
“Lafiyanta kalau, and naga matar da take zaune da ita. Amma Ammi tak’i barina inyi dogon bincike a kanta.” Ya k’arishe maganan yana kawar da kanshi gefe yana cizan la66ansa.
Laila ta lura bai ji dadin hakan ba, don haka ta canja musu hirar saboda tana son ya hak’ura da hukuncin mahaifiyarsa koda kuwa shi bai so hakan ba. Ita uwarsa ce ta fishi sanin rayuwa da kuma mutanen cikinta, don haka duk hukuncin data yanke ya k’arba ya kuma yi addu’ar Allah yasa hakan alkhairi ne.
Suna hira aka kira sallah isha, Haydar ya mik’e tsaye yace,
“Kizo muje muyi alwala.”
“Ina da alwalata tun na magriba.” Ta bashi amsa tana gyara zamanta a kan kujera.
“Ya kamata kema in karya miki taki, saboda ance yawan alwala ma lada ne.” Kafin ya k’arisa maganarshi Laila ta tashi tsaye da sauri tana gyara rigarta tace,
“Haydar kul ka mini haka don Allah.” Sai dai dariyan da take yi yasa ya nufota gadan-gadan tana ja da baya.
“Ko kin gudu zan biki, amma in kika tsaya watak’ila zan iya hak’uri in barki.”
Hannunta ta mik’ar tsakaninsu yanda zata yi saurin tareshi in zai ta6ata tana cewa,
“Shikenan na tsaya, but please don’t do it.”
A jikin gini ya taradda ita tana mishi magiya yana dariya don hakan na mishi dad’i bana wasa ba.
“Haydar.”
“Laila.”
“Don Allah karka mini haka, wallahi bana son 6ata kwalliyata ce shiyasa na iya rik’e alwala.”
“Ni kuma baki san kallonki kad’ai na karya mini alwala ba ko?” Ya fad’i hakan yana rankwafowa jikinta ba tare daya ta6ata ba.
“Ni ban sani ba.” Ta bashi amsa numfashinta na neman kwace mata.
“Well, yau kin sani. Sannan ki sani ba k’aramin hak’uri da kawar da kai nayi ba kafin ranar nan. I’m just trying to be a gentleman ne Laila, amma yau ina jin duk wani restrain d’ina babu shi. Ki fad’a mini, you still ready?”
Gyad’a kanta tayi ba tare data furta mishi ba, saboda maganganunsa na neman karya mata jiki.
Kamar walkiya ya matsa a gefenta yana murmushi mai k’ayatarwa tare da kashe mata ido daya, sannan ya juya ya shiga d’akinsu don yin alwala.
Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e tana mamakin yanda yaron yake tafiya da imaninta, sannan ya iya mata matured soyayya da kowacce mace take fatan samu.
Sai data saisaita kanta sannan ta koma falon ta shimfid’a musu darduma tana tuna irin gyaran da take yiwa jikinta don wannan ranar ba tare da Haydar ya sani ko ya gane ba.
Yana fitowa ya saka jallabiyarsa ya tayar da sallah Laila tabi bayansa. Bayan sun idar ya gama addu’oinsa ya juyo yana cewa,
“Hajiya yau ba kaza fa, a bini bashi.”
Dariya tayi mai cike da kunya tana cewa,
“Don Allah ka daina sakani jin kunyarka, kuma ka daina mini irin wannan kallon.”
“Someone cannot look at his wife in peace? Ni da matata.”
“Haydar.”
“Laila yau kam ki canja mini suna.”
Tashi tayi tana cire hijabin jikinta tace,
“Sai da safe.” Tayi saurin shigewa d’akinta ta rufe k’ofar.
Kad’a kanshi yayi yana murmusawa ya tashi ya rufe gidan tare da kashe wutan falon ya tasamma d’akin matarsa.
Yana bud’e k’ofar ya hangota zaune a akan gado ta lullu6a da gyale kamar yanda yaci burin ganin hakan a rayuwarsa. Bai yi tsammanin zata tuna tayi ba amma he’s greatful data cika masa burinsa.
“Amarya bakya laifi.” Ya fad’i hakan bakinsa har kunne domin irin farin cikin da yake ciki kamar bai ta6a jin wani abu wai shi bak’in ciki ba a rayuwarsa.
A hankali ya taka ya isa bakin gadon ya zauna a gefenta, kana ya saka hannu ya yaye lullu6in yana jin kanshi a sama kamar yafi kowa sa’a a duniya.
Tsabar zumud’i hannunshi har rawa yake wanda itama Laila sai data lura, murmushi ta masa tana cewa,
“I’m not going anywhere Haydar.”
10mins later
“Haydar, it’s been a while....”
“I know, and I’ll be gentle Laila.”
Washe gari da kyar Haydar ya bar Laila ta fito zata d’aura musu breakfast, ko minti biyu bata yi a kitchen d’in ba ya biyota ya kwantar da kanshi a bayanta yana lalu6ar jikinta.
Kamar zata yi ihu haka taji, amma ta kwantar da muryarta tace,
“You know we have to eat ko?”
“Bana son abinci.”
Shiru tayi bata tambayeshi me yake so ba domin tasan amsar da zai bata. Can kuma tace,
“Haydar....”
“One more please.” Yayi saurin katseta yana juyo da ita.
Yanda taga idanunshi ya kad’a ya canja yasa ta sauk’e ajiyar zuciya amma zuciyarta bugu yake yi domin ita kad’ai tasan wahalar da take sha.
Ruwan data d’aura ta kashe kana ta fara tafiya yabi bayanta yana mata godiya.
“Idan ka kasheni zaka huta.” Ta fad’i hakan a hankali yanda ba zai ji ba.
Shi kuma bai ma lura ba balle yaji domin hankalinsa na can wani gurin daban.
Girkin da ba’a d’aura ba kenan sai k’arfe sha sha d’aya na safe, nan ma Haydar ne ya tashi ya d’aura ya bar Laila na bacci. Yana girkin yana rawa yana juyi sai murmushi yake dokawa shi kad’ai d’inshi.
Bayan ya gama ya kwashe a food flask ya shiga d’aki ya samu Laila bata kan gadon, hanyar band’aki yayi ya bud’e ya shiga ya sameta zaune cikin baho da alama ta gama wanka ne.
“Laila me kike yi a cikin baho?”
A firgice ta d’ago ido ta dubeshi tsaye a bakin band’akin yana kallonta. Maida kanta tayi k’asa ta rufe fuskarta da hannayenta tsabar kunya da takaici.
“Don Allah ka fita.”
“Sai kin fad’a mini me kike yi, ko nima inzo in shiga.”
Shiru tayi can kuma yaji kamar tana shekshekar kuka yayi saurin sake k’ofar ya yiwo kanta. Amma kafin ya iso ta dakatar dashi tace,
“Ka bani space please. Zan fito yanzu.”
Dakatawa yayi na wasu sakanni sannan ya fita jikinshi a sanyaye ya zauna a bakin gado yana jiranta.
Bata jima ba ta fito d’aure da bathrobe kanta a k’asa bata son had’a ido da Haydar.
Shi kuma ganin ta fito yasa ya gyara zamanshi yace,
“Laila laifi na miki ko dai nayi hurting d’inki?”
Zama tayi a hankali kan kujeran mirrow d’inta sannan ta dubeshi tace,
“I don’t know. Nima ban san me yake damuna ba.”
“Wannan ba amsa bace, ki fad’a mini laifin da nayi in baki hak’uri kuma in kiyaye gaba.”
“Wallahi nima ban san meya faru ba, haka kawai naji ina son yin kuka. I think canjin da jikina ya samu ne ya sakani haka.”
“Can I hug you?” Ya tambayeta domin ya lura kamar space take so hankalinta da jikinta ya saba da sabuwar rayuwar data shiga.
“No.” Tayi saurin fad’a sannan ta marairaice fuska tace, “Yunwa nake ji.”
Wannan magana tata yasa ya yarda da tunanin da yayi domin shima har da laifinsa da yayita nace mata ana abu d’aya tun jiya.
Abincin ya zuba mata a plate sannan ya zuba nashi ya tsaya yana kallon yanda take saurin tura lomar a bakinta.
“I’m sorry na barki da yunwa, I drained your energy kuma na hanaki cin abinci. This is all my fault.” Ya ajiye abincinsa domin yaji har ya koshi.
Dakatar da cin abicin tayi tace,
“It’s okay, yanzu ba gashi ina cin abincin ba. Kaci abincinka please.”
“Na k’oshi.” Yace da ita jikinshi a mace.
Murmushi tayi ta tako ta zauna a gefenshi kana tace,
“Trust me baka yi laifi ba, this is your first time wanda yawanci maza na wannan d’okin da rashin kula da wasu abubuwan. Nima kuma zan iya cewa emotions d’ina ne suka taru suka wargaza mini lissafi nayi wannan abun. Ka d’auki abincin mu ci.”
“Na k’oshi.”
“Idan baka ci ba nima bazan ci ba I swear, kuma kasan yunwa nake ji.”
D’aukan abincin yayi suka cigaba da ci yana binta da kallon k’auna domin haka burinsa yake tun da, wato ya auri babbar mace mai hankali da experience na rayuwa. Ya rarrasheta ta rarrasheshi, ya sakata a hanya itama ta sakashi a hanya, ya bata shawara ta bashi shawara kuma ta zama uwar ‘yayansa kuma matarsa har a Aljannah.
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
(34)
A kwana a tashi asarar mai rai, yau wata hud’u kenan da auren Haydar da Laila. Soyayya suke gwadawa juna tsaftatacciya wacce tasa suka shak’u da juna bana wasa ba.
Laila sosai take kula da mijinta tana kuma iya bakin k’ok’arinta ganin ta sauk’e duk wani hak’k’insa dake kanta. Tun tana mamaki da kuma kunyar ta auri wanda tafi a shekaru har ta daina ta fara ganinshi a matsayin babban mutum kuma mai daraja a gurinta.
Kamar yanda Haydar yaci burin auren babbar mata kuma Allah ya bashi, sai ya kasance shima ya zama version na mijin da Laila take so, wanda hankali, dattaku da kuma sanin yakamata na cikin qualities d’insa.
Har a wannan lokacin babu labarin Abul ko kuma inda ya shiga, duk da cewa kuwa Mas’ud da Haydar sun saka a nemeshi ba tare da sanin Laila ba.
Duk wanda yasan Laila yasan tana cikin zullumi da kuma bak’in cikin guduwan d’anta Abul, sai dai bata bari hakan ya k’ara ta6a rayuwar aurenta ba kamar yanda Abul d’in yaci buri. Ta yarda da addu’an da take yi bazai ta6a fad’uwa k’asa banza ba, komai daren dad’ewa Abul zai bayyana matuk’ar yana raye. Fatanta da kuma burinta shine Allah ya shiryashi kafin lokaci ya k’ure masa, saboda ita mutuwa bata sallama balle ta bawa mutum damar tuba ko sallama ga ‘yan uwansa.
Ana tsaka da hakan ne aka cire lockdown wanda ya bawa Laila damar komawa shagonta da tayi kewa. Haydar kuma har lokacin yana aikinsa a company Lu’a Ventures, wanda zai iya cewa yawancin aikin company a kansa yake. A yanzu da albashinsa ya k’ara yawa sai ya kasance ya hana Laila sayan kayan abinci na gidan ya zamana kowanne wata zai tura mata kud’i tayi musu shopping tare da Amminshi. Sannan yace duk wani abu da take buk’ata ta fad’a mishi ba sai tayi amfani da kud’inta ba.
Laila data saba kashe kud’inta ba tare data tambayi kowa ba sai hakan ya zame mata takura bana wasa ba, domin tana jin nauyin ta tambayeshi kud’i sai take ganin hakan bai mata tsari ba.
“Haydar na saba biyawa kaina buk’atar rayuwa ba tare dana tambayi wani kud’i ba for almost 20years, zai bani wahala yanzu rana tsaka in fara nema daga gareka. Tunda ka kar6i sayan provisions ka barni inyi sauran tunda nima Allah ya hore mini kuma kamar taimaka maka zan dinga yi. Da fatan ka fahimceni?”
Girgiza kanshi yayi ba tare daya kalleta ba yace,
“Laila, a yanzu inada rufin asirin da zan iya d’aukan duk nauyinki na dole, tunda nace ga yanda nake so sai ki bini a hakan saboda hak’k’inki dake kaina nake son sauk’ewa.”
“Idan kuma nace na hutashsheka fa?”
“Baza ki mini wannan wayon ba.” Ya fad’i hakan yana zuge zip d’in rigarta.
“Yaya dai Mallam?” Ta tambayeshi tana rik’e rigarta.
“Abunda kika gani.”
“Ka tsaya muyi magana.”
“A zaune ma nake.” Ya bata amsa bayan ya samu nasarar rabata da kayan jikinta.
“Haydar yaushe zaka bari inje asibitin muyi Planning d’in.”
Dakatawa yayi da abunda yake yi yayi shiru bai ce komai ba. Jin yayi shiru yasa Laila ta k’ura mishi ido tana jiran amsarta domin tana son sanin ainihin me yake ransa game da Birth control d’in da take son yi.
“Haydar kayi magana.” Ta kamo hannayensa wanda ya sauk’e a jikinta seconds uku da suka wuce.
“Sai gaba.” Ya bata amsar da kullum shi yake fad’a mata.
“Yaushe kenan?” Ta k’ara insisting.
“Idan lokacin yayi zan fad’a miki.” Ya fad’i hakan yana kwanciya a kan gadon ya bata baya.
“Don Allah ka tashi yau kam muyi maganan nan. Kullum kenan amsarka ‘sai gaba’, Ina k’ok’ari wajen ganin ban munafurceka ba naje nayi ba tare da saninka ba, amma kai ka kasa fahimtata kuma ka k’i mu zauna mu tattauna.”
“Bakya son haihuwa dani ne?” Shine tambayar daya mata wanda bata yi tsammaninshi ba.
“Ya za’a yi kayi tunanin haka Haydar? Don meyasa zan k’i son haihuwa da kai?”
“Ki bawa kanki amsa sai nima in san dalilin da kika takura dole-dole sai kin hana haihuwa dani.”
“Haydar abun bai kai haka ba.” Ta fad’i hakan cikin sanyin muryar domin ta lura ranshi ya 6aci sosai.
Tashi yayi ya zauna ya fuskanceta fuskarsa zallar 6acin rai yace,
“Ina lura kullum na nemi biyan buk’atana dake sai kin kawo mini maganar Planning da kike son yi, saboda kina son in amince miki koda banyi niyyar hakan ba. Don meyasa kike son yin planning in ba k’in haihuwa kike dani ba Laila? Baki san bak’in cikin da nake ji ba Idan kika kawo mini wannan zancen, wallahi har na fara waswasi a zuciyata kan irin son da kika ce kina mini.”
“Me kuma ya kawo wannan maganan don Allah? Na sha fad’a maka dalilina cewa saboda na girma ne tsufa yazo mini Haydar. Na jima ban haihu ba wanda dole a yanzu idan zan haihu zan wahala sosai sannan ga jikin tsufa.”
“Wannan ba hujja bace Laila, mata da dama wanda suka fiki shekaru suna haihuwa kuma lafiya kalau. Wahala kuma da kike maganarta dama dolene ki sha tunda kowacce mace sai ta d’and’ana kafin ta kawo ‘yayanta duniya. Me kike nufi dani? In zauna banida ‘yaya har k’arshen rayuwata alhali matata zata iya haihuwa? Gaskiya baki so zaman lafiya dani ba muddin baki canja wannan k’udirin naki ba.”
Yana fad’in hakan ya sauk’a daga kan gadon ya maida kayanshi ya fita daga d’akin. Tana ji ya bud’e k’ofar falo ya fita daga gidan ma gaba d’aya. Zuciyarta bugu ta fara domin duk ranar data kawo mishi wannan maganan sai duka ransu ya 6aci.
Meyasa ya kasa fahimtarta? A yanayin shekarunta da kuma dad’ewanta bata haihu ba zata sha wahala sosai Idan ta d’auki ciki. Tun ranar da suka fara had’uwa ta nemi ya dinga inzali a waje saboda amma ya mata dad’in bakin wai ba zata d’auka ba tunda ta jima bata san d’a namiji ba. Saboda gudun cecekuce a yayin da yake zumud’i da farin ciki sai tayi shiru bata mishi musu ba amma tayi addu’a sosai kan Allah yasa bata d’auki cikin ba. A wannan watan akan kwai take tafiya domin Haydar yak’i amincewa da k’udurinta sannan ga bak’ar jaraba daya tasata a gaba dashi, wanda har fata take a d’age lockdown kowa ya kama harkar gabansa.
Wata na kaiwa k’arshe al’adarta ta dawo wanda tsabar murna har sujadar godiya tayi ga Allah. Haydar kuma daya samu labarin fuskarsa ba yabo ba fallasa, hasalima bai nuna mata komai ba sai kewarta da yace zaiyi a kwanakin da zata yi tana jinin.
Tana gamawa ya cigaba daga inda ya tsaya wannan karon ta bashi shawarar yayi amfani da protection, karantar fuskarsa kad’ai da tayi yasa tayi saurin gyara zancenta da cewa taji wasu mazan haka suke yi idan sun hana matansu amfani da birth control.
“Allah ya hanani amfani da Condom Laila, ni da matata sai na sanya labule tsakaninmu sai kace da karuwa zan kwanta?” Wannan shine amsar daya bata wanda yasa taji haushi don meyasa zai kira sunan karuwa. Dalili kuwa a kwanakin baya ana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 32