Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
muryar Matata ce.” Cikin rashin fahimta suka bishi da kallo suna tunanin me had’insu da wannan magana? Saboda It doesn’t even make sense. Ummii ta dubeshi tace, “Alhaji ban gane ba.” “Suwaiba ‘yarki matata ce sannan Haydar d’ana ne. Na gane hakan ne bayan naji murya da kuma labarinta data baku a yau, don Allah idan tana kusa ku kira mini ita in tabbatar ita ce kuma ba mafarki nake yi ba.” Salati da kuma Innalillahi ne ya tashi a falon Ummii har tana tafa hannu kana ta kwalawa Ammi kira wacce tun shigowarsu ta gane muryar mijinta amma ta k’i fitowa tsabar kukan daya ci k’arfinta, da kuma tsoron abunda zai faru gaba idan matarsa taji ta dawo cikin rayuwarsa. Shin yau wace irin rana ce da abubuwa suke bayyana kamar dama jiranta ake yi? “Lu’alu’a.” Baba ya kira Ammi da sunan daya rad’a mata tun a wancan zamanin soyayyarsu. K’in fitowa tayi haka bata amsa duk kiran da ake mata ba. Laila da abun ya fara mata yawa taji kanta na juyawa tana neman gurin kwanciya. Mas’ud ne ya lura da hakan yayi saurin zama a hannun kujeran da take zaune ta kwantar da kanta a jikinshi hawaye na silalowa a fuskarta, wai Haydar d’inta k’anin Abdul ne? Wani irin kwamacala ne wannan auren nasu ya bankad’o? Ummii ce da kanta ta tashi ta shiga d’akin ta yiwa Ammi magana sannan ta fito ta samu guri ta zauna ba tare data kalli kowa ba. Hakan yasa Baba ya kira sunanta, “Lu’a.” Yanayinsa kamar mai shirin zubar da hawaye. Ammi ta d’ago idanunta sai kuma wani kukan ya kwace mata tana girgiza kanta tana cewa, “Don Allah kar kace ka ganmu, zata saka a kashe mini yaro.” “Wacce kike magana a kanta ta rasu tun da jimawa bayan ta fad’a mini abunda ta aikata, sannan ta bani wasiyyar duk lokacin dana ganki in nema mata yafiyarki da fatan zaki yafe mata domin tayi nadaman abunda ta aikata a gareki da d’an cikinki. Ina d’ana yake Lu’alu’a? Ban ganshi a tare daku ba sannan tun d’azu Abdul yake gwada kiranshi wayar bata shiga. Ina son ganinshi, ku kira mini shi yazo yaga babanshi.” Ya k’arisa maganan cikin tsantsar farin ciki yana kallon Ammi kamar yaje ya d’auketa. “Bayan ya saurari tarihin rayuwata ya tafi bamu san ina ya shiga ba.” Difff annurin fuskar Baba ya d’auke ya sunkuyar da kanshi k’asa yana addu’an kar Allah ya maimaita mishi 6atan iyalinshi. Ihun da Laila tayi yasa kowa ya d’ago ido yana kallonta tana nuna bakin k’ofa da hannunta bakinta ya kasa magana, suna juyawa suka hango Madu ya kaiwa Alhaji Abdul duka a bayanshi da wani k’aton katako, Alhaji Abdul cikin kid’imewa ya tare da hannunshi ya bada wani k’ara ‘katttt’ alamar hannun ta karye. Mas’ud ya tashi da gudu yana kiran sunan Madu zai kwace katakon hannunshi amma kafin ya isa Madu ya k’ara laftawa Alhaji Abdul a goshinshi, nan da nan jini ya fara zuba yayi azaman tashi yana neman gurin 6uya. “Yaya Madu baka da hankali ne?” “Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun.” “Mas’ud rik’eshi karka bari ya isa gurinshi.” “Abdul ka fita daga gidan an rik’eshi.” “Kar ka ta6ashi nace, Madu nace karka ta6ashi.” “Ummii ki hanashi kar ya kasheshi.” “Zai kasheni, bashi da hankali ku rik’eshi.” “Madu ni nake maka magana ka nitsu ka saurareni.” “Wannan wani irin tashin hankali ne yake faruwa damu?” Haka d’akin ya kacame da ihun mutanen cikinsa, Alhaji Abdul yana dafe da goshinsa dake zubar da jini ga Madu na k’ok’arin yin kanshi Laila da Mas’ud sun rik’eshi, Ammi ta kwace katakon hannunshi tana tare Alhaji Abdul wanda yake 6uya a bayanta. Ummi kuma magana take yi tana son nitsar da Madu yayin da Baba yake gefe yana kallon wannan abu kamar a mafarki ya rasa me zai yi d’aya. “Ku barni in kasheshi in kashe banza, matata yake zina da ita a bayan idona. Nace ku sakeni in kasheshi.” Fad’in Madu yana yin kan Alhaji Abdul wanda Ammi ke tarewa tana son fitar dashi waje. Ai kuwa yana samun hanya ya fice daga gidan da gudu zuciyarsa na azalzalarshi bisa wannan kayan takaici da kunyan daya sameshi. Baba na ganin haka shima ya fita yana cewa, “Bari mu kaishi asibiti.” Sai da Mas’ud ya tabbatar sun bar gidan sun yi nisa sannan ya sake Madu wanda ya samu guri ya zauna idanunshi sun kad’a sun yi jaa kamar garwashi sai huci yake yi kamar zai ci babu. Nan kowa ya samu guri ya zauna amma banda Ummii da take tsaye a kanshi tana kallonshi. Sai da numfashinsa ya daidaita sannan Ummii ta fara tambayarshi cikin sanyin murya, “Madu me yake faruwa ne? Meyasa ka aikata wannan abun kunya da rashin hankalin?” “Munafuki ne Ummii, ashe tun kafin in had’u da Jamila suke watsewarsu tare har muka yi aure basu daina ba. Ita da kanta ta bayyana bayan ta gudu.” Shiru d’akin ya sake yi baka jin k’aran komai sai na fanka kad’ai. Ummii ce ta ja ajiyar zuciya kana ta nisa tace, “Na gane Jamila na bin maza sai dai ban ta6a tsammanin da abokinka zata k’are ba. Kwanaki da kuka yi tafiya da Hajja bak’in cikin abunda naji take fad’a a waya yasa na kwanta rashin lafiya har gadon asibiti, shiyasa daka dawo na ganka nayi hawaye don tausayinka da nake ji. Bani da tabbacin abunda take aikatawa shiyasa ban ta6a yiwa wani daga cikinku maganan ba, sai addu’a dana dage a kai kan cewa Allah ya tona asirin duk mai cutar da iyalina. Yanzu gashi Allah yasa ta bayyana ita da kanta ba tare da an mata dole ba.” “Ummii addu’ar taki ce ta kar6u shiyasa da Jamila ta tashi tonon asirin bata tsaya a nata ba sai da ta fad’i irin tuggu da makircin da Madu da Abdul suka yi ta kullawa akan Kalti.” Fad’in Mas’ud yana yiwa Madu kallon tsana da takaici. “Mas’ud nace kar ka kuskura ka d’auko magana nan.” Fad’in Laila tana girgiza kai. Cikin rashin fahimta Ummii ta dubi Mas’ud tace, “Wani tuggu suka had’a mata?” “Mas’ud don girman Allah kar mu d’auko wannan maganar a yau. Abubuwan da suka faru sun isa kar mu k’ara, wallahi na gaji, na gaji da komai ina son in kwanta kar in tashi har abada.” Ta k’arishe maganan tana yarfe hannayenta idanunta sun kasa zubar da hawaye tsabar ta gaji, saboda tun safe shi take yi. “Mas’ud fad’a mini komai kar ka 6oye mini.” Ummii ta bashi umarni fuskarta babu alamun wasa. Mas’ud kallon Laila yayi wacce ke girgiza mishi kai kana ya fara magana, “I’m sorry Kalti don bazan tsallake umurninta ba. Ummii Jamila ce ta turo hotuna marasa dad’in gani a whatsapp family group d’inmu wanda yake nunata tare da Abdul a hali na kaico. Daga nan kuma tayi rubutu kamar haka;....” Ya zaro wayarsa daga aljihunshi ya fara karantawa... ‘Na dad’e ina jiran rana mai kamar ta yau da saurayina Alhaji Abdul zai juya mini baya in gwada mishi wacece ni, aurena da Madu shi ya had’a ba tare da Madu ya san cewa ni dadironsa ba ce. An yi auren ne don in zama mai fad’awa Abdul duk abunda yake faruwa a zuriyarku musamman a kan Laila wacce yake yiwa soyayya mai had’e da mugunta. Abdul shi ya ta6a fad’awa Madu cewa Laila na bin maza wanda ba tare da yayi bincike ba ya d’auru a kan hakan saboda tsanar da yake mata tun a daa. Hakan yasa duk inda ya zauna ko kuma ya had’u da ita yake jifarta da k’azafin zina har Uwarku ma ta fara yarda da hakan tana matsa mata da maganan aure, wanda hakan shine burin nashi. Duk yanda Madu ya kai ga binciken rayuwar Laila don ya kamata a halin fasik’anci ya gagara, hakan yasa Haydar yana shigowa rayuwarta yasa aka fara bibiyarta ana d’aukansu a hoto yana tura mata duk don ya tsoritata ta nemi aure wanda suka tabbatar Alhaji Abdul zata za6a a k’arshe. Sai dai da yake Allah ya fisu, Laila da Haydar basu rabu ba. Alhaji Abdul shi ya bawa Micheal abokin Abul kud’i don ya kaishi club yasha giya, hakan yasa bayan yayi caca yayi losing aka dakeshi aka kira Alhaji Abdul yazo ya d’aukeshi. Ina hankalinku yake da kuka kasa gane wannan makircin? Ya za’ayi su samu number Alhaji Abdul kuma su kirashi kai tsaye yaje ya d’auko Abul? Da alama kuma bakwa amfani da iliminku. Ban san ya aka yi aka gane halin Alhaji Abdul a ranar aurensa da Laila ba, abunda na sani shine; umurninshi ne da aka saka kwaya a jakar Abul bayan ya gudu a ranar auren, haka yasa aka yi ta bibiyarsa har rayuwarsa ta lalace sannan ya tura Haydar Abuja ya kuma aikeshi ya kar6o mishi wani aika a kasuwan dasu Abul suke kwadago don ya ganshi ya dawo dashi gida, saboda ya lura da cewa bayan Abul ya 6ace Laila bata shiga damuwar da zai 6ata aurenta ba wanda dama hakan shine target d’insa. Abdul shi ya biya mutumin da yake sayarwa Abul kayan maye kan ya musu k’azafin sata sannan ya musu duka don ya lura Haydar na bibiyar Abul, kuma yasan da yaji abunda ya faru zai dawo dashi gida wanda hakan zai k’ara hatsaniya tsakanin Laila da Haydar. Wani abunda baku sani ba shine, Abdul ya k’arawa Haydar matsayi ne a office d’insu don su sakar mishi aiki ya dinga wahala sannan daga baya suna k’ok’arin mishi k’azafin satan kud’in company wanda zai kaishi prison, sai dai hakan bai faru ba saboda lokacin da suke shirin yin hakan bai zo ba. Sannan a yau Madu ya sanar da Abdul mutuwar auren Laila wanda cikin murnar hakan ya koreni a rayuwarsa saboda na gama aikina. A k’arshe Madu yana yiwa Abdul aiki ne don kud’i da yake bashi wanda shi kuma yake kaiwa marayun daya cinye dukiyar mahaifinsu wato ubangidanshi. Da ni da Abul an yi amfani damu ne don wargaza wannan zuriya kuma a k’arshe basu ci sa’a ba. Wannan kad’an kenan daga cikin sharri da makircin da wad’annan mutane biyun suka k’ulla. Na barku lafiya.’ Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 😩 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) (46) Tun lokacin da Mas’ud ya fara yiwa Madu tonon asiri a gaban Ummii shi Madun ya sunkuyar da kanshi k’asa yana jin kamar k’asa ta tsage ya shige tsabar kunya da kuma takaicin abunda yayi, wanda sai yanzu da aka kamashi kuma Alhaji Abdul yaci amanarshi ya fara nadama. “Duk abunda Mas’ud ya furta gaskiya ne?” Ummii ta tambayi Madu cikin kid’ima da kuma rashin yarda. Shiru Madu yayi bai d’ago kai ba haka kuma bai furta komai ba, k’arshe mik’ewa yayi zai fita Ummii ta dakatar dashi ta hanyar mishi tsawa wanda dukkansu sai da suka tsorita don basu ta6a ganinta cikin 6acin rai haka ba. “Ka amsa mini!!” Ta kafeshi da ido wanda hakan yasa ya koma ya zauna yana zare ido yace, “Ummii zamu yi maganar daga baya, kuma wani abun da Jamila ta fad’a k’arya ne wallahi, abunda nayi kuma saboda in kare Laila ce tunda ita lallashi da shawara baya aiki a kanta.” “K’arya kake yi Madu. Furucinka k’arya ne. Ka cuceta, da bakinka an cuci k’anwarka. Ban ta6a zaton zaka yiwa jininka haka ba. Ka bani mamaki kuma nima ka zalunceni da kasa na fara zarginta ina hantararta.” Ummii ta furta hakan a hankali hawaye na taruwa a idanunta na takaici da bak’in ciki. “Ummii....” Madu ya tashi tsaye yana k’ok’arin mata magana ta dakatar dashi ta hanyar d’aga mishi hannu, “Ka fita ka bani guri, wallahi bana marmarin ganinka” Tana fad’in hakan tayi hanyar d’akinta Mas’ud yayi saurin yin kanta shima ta d’aga mishi hannu tace, “Kowa ya koma gidanshi. Duk wanda yayi nagari kansa, wanda yayi akasinsha kuma shi da wanda ya halicceshi. Tashin hankalin ya isa haka, bana son ji komai.” Tana gama fad’in hakan ta shige d’aki Ammi tabi bayanta tana kama kafad’arta domin karkarwa data fara yi tana had’a hanya. “Mas’ud ina tsoron kar ciwon Ummii ya tashi.” Fad’in Laila tana hawaye tana kallon k’ofar d’akin Ummii. “Babu abunda zai faru in Allah ya yarda, idan ma jikin ya tashi Ammi zata yi waya. Mu tafi.” Mas’ud haka ya tasa Laila a gaba har suka shiga motocinsu suka kama hanyar gida. Sai daya tabbatar ta shiga gidanta sannan shima ya kama hanyar gida yana ayyanawa a ranshi cewa basu ta6a ganin rana irin wannan ranar ba. Domin kuwa rana ce mai tsayi, mai cike da hatsaniya da tashin hankali kuma baya fatan su k’ara cin karo da makamanciyarta. A cikin zuriyar Ummii kuwa duk wanda yace yayi bacci mai dad’i a wannan ranar yayi k’arya. Washe gari da safe Laila na shirin zuwa gidan Ummii taji wayarta na k’ara tayi saurin d’auka zuciyarta na bugawa ganin sunan Ummii a jikin screen d’in. “Ummii jikin ne?” Abunda ta fara fad’i kenan bayan ta d’agar wayar tana dafe kirji. “Lafiyata kalau. Kar kice zaki zo, ki zauna a gida ki kuma dinga tunawa da matsayinki a yanzu.” “Zan zo in dubaki ne Ummii.” Laila ta fad’a duk da tasan cewa Ummii baza ta canja maganarta ba. “Bana so. Ki zauna a gidanki.” Ajiyar zuciya Laila tayi kana ta gaisheta tare da tambayar lafiyar Ammi suka yi sallama. Wasa-wasa yau sati d’aya kenan da 6acewar Haydar wanda har sun daina nemanshi saboda sun san cewa shi ba yaro bane zai bayyana duk lokacin da yaga dama. Sai dai za’a iya cewa Laila tafi kowa shiga damuwa bayan Ammi dalilin cewa wai sakinta Haydar yayi sannan ya tafi ya barta da cikin d’ansa, zamanta a gidansu kuwa zama take yi na iddah wanda k’arshensa shine in ta haihu. Kullum Mas’ud sai yazo gidanta sau biyu ya dubata ya mayar da hakan kamar dolenshi, akwai ranar da yazo da daddare ya sayo mata tsire da fruits tunda yaji ance masu ciki suna da kwadayi, “Na sayo miki tsire amma ban san ko bakya son k’amshinsa ba, hope ba zai sakaki amai ba?” “Mas’ud kenan. Ni ban ta6a yin amai ba, ina ganin shiyasa ban ta6a kawowa cewa ciki nake dashi ba. Mik’o mini tsiren don wallahi tun shigowarka k’amshinsa yake bugan hancina.” Ta mik’a hannunta ya bata. A gabanshi ta bud’e yana mata hira har ta cinye bata mishi ko tayi ba, shi dai kallonta kawai yake yi yana jin mugun tausayinta a ranshi wanda har yake jin kamar wani abu mai d’aci ya mak’ale mishi a wuya. In ba don yasan abunda ta aikatawa Haydar ba daa yanzu ya tsaneshi saboda baya son abunda zai 6atawa yayarsa rai. Tana shan fruits d’in ya mata sallama ya tafi akan washegari da safe zai dawo ya ga lafiyar jikinta kamar yanda ya saba kullum. Sati d’aya da haka wanda ya cika sati biyu da 6acewar Haydar, watarana Mas’ud na shago ya ga kiran Alhaji Abdul a wayarsa yayi ringing har ya gama bai d’auka ba. Haka aka sake kiranshi har sau uku bai d’auka ba, daga k’arshe sai yaji shigowar text ya d’auka ya karanta kamar haka, ‘Na san ni mai laifi ne a zuriyarku gabad’aya, sannan na so in zo muyi magana da kai ne amma naji an ce Madu nemana. Kayi hak’uri ka d’auki wayata muyi magana, wallahi ba cutar daku nake da niyyar yi ba, ina so ne in gyara wani abu a cikin dubbannin da na 6ata. Sannan karka manta Haydar k’anina ne wanda a yanzu nake jin bayan mahaifina babu wanda nake so sama dashi, bayan 6acewar mahaifiyarsa mun nemeta ni da mahaifina har muka hak’ura muka barwa Allah komai. Haydar is all I have don bana tunanin zan yi aure har abada. Please help me make this right, please.’ Mas’ud yana gama karantawa ya ja doguwar tsaki yana ajiye wayar a gefe. A wancan ranar da Alhaji Abdul ya samu ya gudu daga hannun Madu, sun ji labarin ya bar gari ya tafi jinyar hannunshi daya karye da kuma goshinsa da aka fasa wacce aka yiwa d’inki biyar. Madu kuma kamar dole bai fasa neman Alhaji Abdul ba, sai ya zama kamar wani zautacce yau yana wancan garin, gobe yana wancan garin inda yake tsammanin zai samu mak’iyinshi. Jamila kam ba’a maganarta domin daga Alhaji Abdul har Madu babu wanda ya nemeta saboda sun san ta musu nisa har abada, ita ba dak’ik’iya bace da zata zauna a kusa in da zasu ganeta. Awa biyu da tura wannan text d’in Alhaji Abdul ya sake kiran Mas’ud amma yana gani ya k’i ya d’auka. Wayar tana k’ara ringing Mas’ud ya d’auka a fusace yana cewa, “Duk munafurci da cin amanan da kayi bai isheka ba shine yanzu kake tunanin zaka k’ara wasa da hankalina don ka sake a karo na ba adadi? Kai kam baka jin kunya ne? Ko kuma don kaga bamu d’auki mataki bane yasa kake raina mana hankali? Wannan karon ya zama na k’arshe da zaka k’ara kirana ko kuma ka mini text kana damuna, I have no business with you. Don Haydar yana k’aninka kuma ba damuwata bace, I don’t give a fuck ko kai ubanshi ne.” Yana gama fad’in hakan ya kashe wayarsa yana huci domin sai yanzu yake jin bak’in cikin hanashi d’aukan mataki da Laila tayi. Shikenan sun barshi kenan ya cucesu? Sai dai tunawa da yayi cewa sun barwa Allah hukunci yasa yaji d’an dama-dama a ranshi. A ranar da yaje gidan Laila da dare yake fad’a mata yanda suka yi da Alhaji Abdul tayi shiru tana sauraranshi, bayan ya gama bata labarin tace, “Ko dai da gaske yake yi yayi nadama yana kuma son neman Haydar? Mas’ud ka gwada sauraranshi mana.” “Ke har zaki iya yarda da wannan munafukin after all abunda yayi? He is the reason why your son is in rehabilitation! Shine munafukin da ya hanaki kwanciyar hankali duk tsawon wannan lokacin, shine zaki ce a saurareshi? Me zai ce ko kuma me zai mana? Wallahi ba zan ta6a yarda dashi ba Kalti.” Tagumi kawai Laila tayi tana kallon yanda Mas’ud yake huci kamar ya daki abu, sai daya huce sannan ya fad’a mata Ammi da Ummii zasu tafi Maiduguri nan da sati d’aya. “Amma kana ganin har yanzu Kaala Abdi bai ji labarin an sameta ba?” Laila ta tambayeshi. “Babu wanda ya fitar da maganar, jiya na kirashi har muka gaisa da Abul amma ban ga alamar ya sani ba.” Kad’a kai Laila tayi domin itama jiya ta kirashi don taji lafiyar Abul yake fad’a mata ana ganin alamun nasara a tattare dashi, sai dai ita ta daina cewa a bata yaron su gaisa dalilin bak’ak’en maganganun da yake fad’a mata wanda suke damunta. “Ni zan tafi, kina buk’atar wani abu ne?” Mas’ud ya tambayeta yana tashi tsaye. “Babu komai, Alhamdulillah. Amma don Allah ka daina zuwa gidan nan da daddare saboda kana shiga hakk’in matarka. Ka duba yanzu k’arfe goma da kwata wanda yaci ace har kun yi bacci amma kana nan. Ko ni a daa bana son Haydar yayi dare.” “Itama tun last week take fushi dani bata kulani wai nafi fifitaki akan ita matata. Tace idan naga dama in dawo gidanki da zama ta yafeni.” Ya kwashe da dariya ba tare da ya ga halin da Laila ta shiga ba daga jin kalamanshi. Tsagaita dariyarsa yayi yana duban Laila da take kallonshi fuskarta cike da damuwa tace, “You are making a huge mistake ba tare da ka sani ba Mas’ud, kuma matarka gaskiya take fad’a maka ban ga laifinta ba.” Tana gama maganar yayi saurin taran numfashinta yace, “Ni ban ma san ya aka yi bakina ya su6uce na fad’a miki ba. Sai da safe.” Yayi hanyar k’ofa zai fita Laila ta dakatar dashi suka fuskanci juna. “Ina sonka Mas’ud shiyasa zan fad’a maka gaskiya, ina kuma sonka shiyasa zan ku6utar da kai daga fushin Allah. Wallahi kafin Allah ya tambayeka yanda kake kula dani sai ya fara tambayarka yanda ka kula da iyalinka daya baka amanarsu a hannunka. Bata da kowa sai kai, a k’arkashinka take, ita d’in nauyinka ce top priority Mas’ud, ni kuma on the other hand Haydar ne mai mini duk wannan dawainiyar ba tare da ya fara yiwa kowa ba sai ni. So karka 6ata rayuwar aurenka don neman faranta mini, kar kuma ka wofintar da amanar da Allah ya baka don kana sona, domin kuwa ita ta fini matsayi a gurinka a idon Allah. I’m your sister ita kuma matarka ce wacce aka halicceta daga hakarkarinka. Ina lura kuna yawan fad’a da ita wanda yawanci duk a kaina ne saboda irin fifitani da kake yi a kanta, wallahi dole tayi fushi saboda tafi buk’atar ta samu soyayya da kulawa daga gareka sama dani. She deserve your love, time and affection more than me, karka 6ata rayuwar aurenka a kaina don bazan ta6a son hakan ba. Please ka kula da matarka kar fushin Allah ya sauk’a a kanka, please Mas’ud.” Laila ta k’arisa maganan tana kamo hannunshi cikin son ya d’auki maganarta yayin da shi kuma yake kallonta baya ko kiftawa can yace, “Kin yi gaskiya and Insha Allah zan yi k’ok’arin in gyara kuskurena. But, Kalti wannan shine babban reason d’in daya hanani aure tun shekarun baya, nasan ba kowacce mace bace zata ga yanda nake baki kulawa mu zauna lafiya ba, she will want me all by herself ba tare dana had’ata da kowa ba. And hakan ba zai yiwu ba saboda dani dake babu mai rabamu saboda a tare muka tashi muke kula da junanmu sama da kowa a gidanmu. Zan gyara and thank you.” Yana fad’in hakan ya zare hannunsa daga nata ya fita daga gidan. Ajiyan zuciya Laila tayi kana ta koma ta zauna taci gaba da tunanin Haydar da kuma halin da take ciki kamar yanda ta saba kullum, wani mugun kewarshi take ji har tana tunanin muddin ya kai wani lokaci bai dawo ba zata iya shiga halin rashin lafiya mai tsanani wanda a yanzu ma dauriya take yi a gaban mutane, amma idan ta kad’aice sai ta zubar da hawaye musamman in ta zo bacci. Haydar ya samu gurbi mai yawan gaske a zuciyarta ba tare da ta gane ba sai data rasashi. Ashe haka take sonshi? Sannan ina zata sameshi? Ya za’a yi ta gyara duk zaman da suka yi tana cutar dashi? Kamar wacce aka tsikara ta tashi tsaye ta shige d’akinta ta d’auki wayarta ta danna kiran wani number, “Laila!” Shine abunda aka fara fad’i cikin rashin yarda da kuma mamaki. “Ka fad’awa Mas’ud cewa kana son neman Haydar duk inda ya shiga, idan da gaske kake yi I will help, amma idan ka kuskura ka munafurceni ko kad’an ne wallahi, wallahi sai na watsa videos da pictures d’inka kai da Jamila, a nan ne mutanen duniya zasu gane wanene kai. So what do you say?” Yawu Alhaji Abdul ya had’iye mai kauri cikin fargaba, domin shi har yanzu yana mamakin dalilin da ya hanasu tona mishi asiri duk da cutar da yayi musu. A yanzu da yake neman gyara kuskurenshi he’ll never crossed the line again, har ya samu Haydar ya kuma nemi gafararsa saboda yana son k’aninshi tun lokacin da yaji labari a gurin babanshi cewa yana da k’ani ko k’anwa. “Ina son baki hak’uri amma nasan hak’uri yayi kad’an akan abunda na miki, sai dai zan nemi yafiyarki idan zaki iya yafe mini.” “Baka bani amsa ba.” Laila ta katseshi saboda ta gaji da surutunsa. “Na yarda.” Ya amsa mata kana ta fad’a mishi ya zo ya sameta a gida gobe da rana. Tana gama wayar ta koma falo ta kulle gidan wanda a yanzu take jin ya mata girma ita d’aya. Ina ma Haydar ya dawo su zauna su kad’ai! D’akinta ta shiga ta rage kayan jikinta sannan ta kwanta tana shinshinar kayan da

Chapter 22 of 32